Auren wata ukku by sameena - Chapter 10
Auren wata ukku by sameena Chapter 10: Auren wata ukku by sameena Chapter 10. Saida suka d'ibi lokaci a haka kafin ta soma fad'in "Bazan tilasta maka ka so…
4,455 words
Saida suka d'ibi lokaci a haka kafin ta soma fad'in "Bazan tilasta maka ka so Haidar ba. But please just this once.. Alfarma nake nema.. Be a father to him.."
Ya d'an dubeta sai kuma ya kauda kansa kad'an "Ban tab'a cewa ni ba mahaifinsa bane Kwaise. D'anki shi ya zab'i ya cire kansa daga cikin ahalin nan."
Ta d'an sauk'e ajiyan zuciya kafin ta mik'e sosai tana gyara zamanta "Aure nake so a masa.."
Daddy ya dubeta da mamaki "Aure.? Cikin yaran Business partners dina kike so na nemar masa matan.?"
Ta girgiza kai alamun a'a "Na riga na samar masa mata a garin Kano. 'Yar gidan mutunci wacce bata da bud'ewan ido da wayewa da yawa balle a samu matsala along the way. Ba babban Aure nake so ba, ba auren da za'a wallafa a mujalla ko a gayyato manyan mutane ba. No aure nake so ayi a sauk'ak'e. Kawu na dake can Maiduguri zai iya wakiltanka dan shi na wakilta akan komai. Ga Asshe ma a can Kanon. So dik wani necessary bincike da Ya kamata a gudanar an gudanar.."
Dakatar da ita yai ta hanyar d'aga hannu "Idan keda 'yanuwanki kun gudanar da duk abinda ta kamata kuyi so meye nawa kuma. Ni dai kin sani bazan tab'a karb'ar ma D'anki Aure ba Kwaise. Kuma abinda ya shafi rayuwarsa ba damuwata bane. The only alak'a dake tsakanina dashi shine abinda ya shafi Kasuwancina. Kampanina da ci gabanta."
Mommy ta rintse idanunta tana jin wani zafi na ratsa cikin k'irjinta. Tasan za'a Rina haka tinda dai ta jima da sanin duk wani abinda ya danganci Haidar wofi ma ya fisa mutunci a idon mahaifinsa. Ya zama dole ta tabbata anyi auren nan at all cost. Tinda tasan wann ba komai bane face sharrin mugun asirin da aka jefesu dashi. Ta tabbata tinda Malaminsu ya sanar dasu da zaran anyi auren matsalan dake cikin ahalin zaizo k'arshe gwara tayi komai domin ta tabbata auren ya yuwu.
Ta numfasa kad'an "Auren bazai yuwu ba saida yarda da amincewarku.. Ina nufin kaida Haidar.."
Ya kuma dubanta da mamaki "What exactly do you mean.?"
"Ina nufin Yarda da amincewarka shine kawai zai karkato Haidar Ya amince da wann Auren. Kasan halinsa za'a iya masa auren mu daina ganinsa har abada, bazai yarda ya zauna da matar ba. Yanzu haka ma Gaba yake damu tinda gashi ya daina zama gidan nan."
"Wanda yafi k'arfin zaman gidan iyayensa ne zai zauna ma Auren da zaki masa.? Ke kanki kinsan D'an naki baida mutunci bai ganin kowa da mutunci daga ni har Ke."
"Amma yana mutunta aikinsa.!" Mommy ta dakatar dashi da fad'in haka.
Daddy ya tsareta da ido.
Taci gaba da jinjina kai "Musamman project d'in nan da yaketa kai komo akai. Naga yanda ya dage yake matuk'ar so Ya jagoranci aikin.. Idan har muna so ya amince da auren zamu iya amfani da wann damar. Ina nufin zaka amince ya jagoranci aikin matuk'a zai amince da Auren. Daga baya na tabbata zai so Yarinyar kuma zasu gina family tare. Zai tara hankalinsa waje guda. A yanda matsalar.."
Bata kai aya ba ya katseta "A'a dakata dakata Kwaise amma ba dani Aliyu Maitama za'ayi wann shiriritar ba.."
"Engr dan Allah ka min wann alfarmar a rayuwa.. Just this once.."
Ya gyara zama sosai yana dubanta cikin rashin yarda "Seriously.. Wann ai hauka ne.. Kwaise a ina kika tab'a jin anyi abu makamancin wann..? Are you asking me to put my company at risk here.?"
Mommy ta silalo daga saman kujera ta duk'a gaban Daddy saman gwiwoyinta. Ta shirya sadaukar da komai domin ta ceto ahalinta.
Cikin muryar kuka take furta "Zanyi ko menene Engr.. Zan duk'a a gabanka na rok'eka sabida inada yak'inin Auren nan zai zama silan shiriyar Haidar da kuma kwanciyar hankalin ahalin nan cikin yardar Ubangiji.."
Saurin d'agota yai yana fad'in "You don't need to do this Kwaise."
"A'a ka kyaleni na duka gabanka idan har hakan zaisa ka amince da buk'ata ta."
Daddy ya soma girgiza kai "Kwaise, babu abinda zakiyi da zaisa na damu da d'anki ko na damu da al'amarin shi.. Kaman yanda ban d'auke shi da mahimmanci ba haka ban d'auki wann auren da kika dage sai kin masa da mahimmanci ba. Amma idan har haka kika zab'a ki sani I won't get myself involved cikin nema ma d'anki aure." Sai ya d'auki wayarsa ya shiga dialing layin Haidar. Haidar yana d'agawa Daddy ya sanar dashi yazo gida ya samesa yana jiransa.
Koda Haidar Ya k'araso zaune ya taddasu a parlon. Iyayensa guda biyu. Yayi zaton magana zasuyi da Ya shafi Kasuwanci shida mahaifinsa tinda har wann ranar baice komai ba gameda proposal da Haidar ya kawo masa the other day. Har k'uri'a akai a company kan waye ya kamata ya jagoranci aikin wanda yake har kawo wann lokacin pending matter sabida shugaban kampani baiyi nasa zab'en ba. Idan Har mahaifinsa a matsayin shugaba a Kampanin Ya zab'esa ko shakka babu ya lashe k'uri'u mafi rinjaye. Idan har mahaifin nasa ya hau kujerar nak'i dole haka yana Ji yana gani aikin ya tafi k'ark'ashin kulawar waninsa. Duk shirinsa na son ganin bayan mahaifinsa da Kampanin zai tashi a banza.
Like always he's not welcome. Ya bud'e murya Ya gaishe su cikin rashin tabbacin za'a amsa masa ko baza'a amsa ba.
Daddy ya jinjina masa kai had'ida nuna masa kujerar gefensa "Have a seat."
Ba musu ya k'rasa ya zauna yana satan duban b'angaren mahaifiyarsa dan a yanda Ya gansu jikinsa ya basa wani abun ake shiryawa akanshi. Ya jima da sanin su biyun tarayya suke wajen k'untata ma rayuwarsa.
Daddy ya dubesa "Are you sure you can handle the project.?"
Haidar yaji tambayar a bazata. Ya d'ago yana duban mahaifin nasa. Maimakon ya basa amsa kai tsaye sai ya girgiza kai yace "Do you still have your doubts.?"
Mommy ta tsaresu da idanu jin Daddy ya tambayi Haidar amma sai Haidar d'in Ya amsa masa da tambaya. A cikin zuciyarta tace like father like son.
Daddy ya jinjina kai "The project is to be commenced in three months time. Idan har ka shirya kuma kana so kayi da gaske zan sauk'a daga kujeran veto and give you and your team the green light… But on one condition."
Haidar ya dubesa da mamaki sai kuma ya dube mahaifiyarsa wacce tin shigowarsa ta kafesa da idanu. Ya maidoda dubansa ga mahaifinsa "What's your condition.?"
Daddy ya dubi Mommy "Go ahead Kwaise. Tell your son the condition."
Mommy da idanunta Ke a k'ek'ashe kaman ba ita ce taci kuka a while ago ba tace "Sharad'in shine Aure.. Zaka auri matar da muka zab'a maka kuma ka zauna da ita matsayin matarka.!"
Tamkar sauk'an aradu haka Haidar yaji batun. Ya dubi mahaifiyarsa da tsananin mamaki Ya kuma dubi mahaifinsa. Lokaci guda yake girgiza kai alamun maganan tana kuma ringing cikin kwak'walwarsa "Unbelievable.! This is unbelievable.. What is this.. Aure.. Sharad'in Aure..? Mommy seriously..?!" Ya k'arashe yana duban mahaifiyarsa. Har lokacin ya kasa yarda.
Mommy ta jinina kai "Eh Haidar.. Aure shine sharad'in idan har da gaske kana so ka jagoranci aikin.."
Ya kuma juyowa yana duban mahaifinsa yana jiran ya k'aryata amma sai yaji Shiru bai ce komai ba.
"Wann shine kiran.?" Ya tambaya yana duban mahaifinsa.
"Abinda mahaifiyarka take so kenan. If it was to me kaima ka sani da yin aurenka da rashin yin Aurenka duk ba matsala ta bane. Talkless of wacece zaka aura. 'Yar waye.? Daga ina take.? Duk wann ba matsala ta bane."
Meye yake ji kaman hawaye na neman cika idon shi.. Anya wad'ann mutanen sune suka haifesa? Anya akwai iyayen da zasuyi ma d'ansu mugun k'iyayya irin wann.? Abinda yakeda mahimmanci a cikin ahalin kasuwancin ahalin ne kawai Wanda za'a yi komai domin bunk'asarta. Amma duk wani abinda ya shafi ahalin baida mahimmanci musamman ma shi in particular.
Muryar Mommy ya kuma katsesa "Idan an maka aure a yanda ka d'auke mu nasan zaka iya cewa an d'aura ma wofi ba lallai ka zauna da matar ba tinda yanzu ma ba ganinka muke ba. Wann dalili yasa muka zab'i gindaya maka sharud'a.
"Ki gyara zancenki Kwaise kika zab'ar masa dai. Amma bani Aliyu Maitama ba. And one more thing.. I can't gamble my company away. Idan kuma har company na zai shiga ki sani naki AUREN ma zai shiga."
Mommy ta dubesa da tsananin mamaki "Aurena kuma Engr.. Mai hakan yake nufi..?"
"Hakan yana nufin it will be the end of our marriage if things go wrong with my company.. Kuma wann fake family d'in zai watse… Ina nufin babu sauran ahali.. So think carefully for the repercussions of what you are about to decide.!"
Zuciyar Mommy yai wani irin bugawa kaman an sauk'e mata guduma jin irin hukuncin da mijinta Ya yanke. Yayinda Haidar ke ci gaba da dubansu cikin tsananin mamaki.
Mommy ta nuna kanta tana duban Daddy "Kana so kace my marriage and the family that I spent years Ina iyaka k'ok'arin naga bai ruguje ba zai lalace..?"
"Of course yes.!" Mijinta ya bata amsa. Yaci gaba "So before you make your final decision sai ki tantance wanne ne yafi mahimmanci wajenki.. Auren D'ank'i ko naki Auren.!"
Haidar yaci gaba da girgiza kai yana dubansu. This is unbelievable! Ya kasa aminta wad'ann mutanen sune wai iyayensa. Ya tsaida idanunsa wanda suka rine zuwa ja kan Daddy "Really Daddy.. Is this what's like to be born into wealthy and influential family..? Everything is about business and making money..? Da gaske Daddy..? Shin ba wani abinda yakeda mahimmanci ne cikin ahalin..?" Ya d'an d'aga murya wann karon "What are we to you..? Is that what you think of your family..? Like we are some sort of business ventures..?"
Ya mik'e tsaye jijiyoyinsa na kuma tashi yana duban duka iyayen nasa "Are we supposed to.."
"Shut up!" Mahaifinsa Ya katsesa kafin yaci gaba "Don't you dare raise your voice at me.. Da kai da rayuwarka babu guda da yakeda mahimmanci wajena. If I take your proposal into consideration, it's because your Mom insisted.. Now get out..! Get out of my sight.!"
Haidar yaci gaba da girgiza kai yana duban mahaifin nasa disbelievingly. A haka ya juya ya nufi k'ofa a fusace zuciyarsa na masa mugun d'aci.
Mommy ganin damarta na k'arshe zai kufce mata Ya sanyata bin bayan Haidar a d'ari tana k'ok'arin dakatar dashi.
Anisa ta mik'e tana lek'en window jin irin kiran da Mommy ke ma Haidar. Nan ta hangesu sun fito daga side d'in Daddy. Haidar na tafe kaman zai kifa yayinda Mommy ke take masa baya.
Mommy ta rik'esa sosai "Haidar don't do this.. Just listen to me.. Bazai yuwu ka rasa project d'in nan ba.."
Yai murmushi mai ciwo "Oh Shiyasa kika tareni ranan a nan.. Kike cewa ni da Ke zamu had'a kai.. Wann shine had'in kan naki da d'anki.. C'mon Mommy.. I always knew baki tab'a yin abinda bazakiyi benefiting a ciki ba.. What I don't understand here shine Auren kike so nayi ko kuma dai wann project d'in ne a ranki..?"
Mommy ta jinjina kai "Both Haidar.. But my top priority is the project.. Idan har baka amince da auren ba bazai tab'a baka project d'in ba. Think about it Haidar you are his only son. Tilon magajin shi. bazan tab'a bari wani Ya d'auki place d'inka a wann Kampanin ba."
Ya murmusa yana dubanta "Na sani to him I'm his failed investment. And to you… Your weapon.. Rayuwana baida wani amfani a wajenku.."
Zai shige Mommy ta dakatar dashi da fad'in "Three month marriage.. AUREN WATA UKU Haidar.. Project d'in zai fara nan da watanni uku. Idan ya riga Ya d'auraka akai ka riga ka fara aikin he can't cancel the agreement. Zaka iya rabuwa da yarinyar.. Ni dai kawai damuwata shine ya baka wann project d'in..!"
Yai Shiru yana duban Mommy. Watau akan abinda take so zata iya zuwa ko wani mataki. Ya matso sosai yana dubanta "Har haka kike son project d'in Mommy..? Shin yakai ki saka naki Auren cikin had'ari ma AUREN WATA UKU. Kawai dan ya bani wann project d'in.?"
Ya kuma girgiza kai "But Mommy this doesn't make any sense. Ke kikayi kid'anki kikayi rawarki. Da kunnuwanki Kinji ya fad'a. Idan a nasa ra'ayin ne bai damu nayi Aure ba ko kar nayi. Duk ba matsalarsa bace. Kece kike son Auren kaman yanda yace.. Toh meyasa Auren Ya zama hujja.?"
Mommy ta jinjina masa kai "I couldn't just sit back and watch you lose your chance. Na kula abinda yake so kenan. Koda bai fad'a ba deep inside yana so kayi auren ne.. Kaima kasan ba don yana so kayi Auren ba bazai tab'a saka Kampaninsa on the line ba. Kayi tunani Haidar we are talking about your Dad here.. Mutumin da zai iya bada rayuwarsa ma wann Kampanin. Rana tsaka dan ina so kayi Aure sai ya amince cewa ka jagoranci aikin.. Aikin da future na Kampanin Ya ta'allak'a akansa. Think Haidar. Wllhi da ace mahaifinka baison kayi wann aure bazai tab'a yarda da sharad'in ba. Mahaifinka yana sonka Haidar kawai bazai iya nuna maka bane ko kuma lokacin nuna maka d'in ne bai ba.."
"Well I don't give a damn..!Ya soni ko kar Ya soni.. Ban damu ba kuma bana ma so naga ranar da zai so ni.."
"In that case ka yarda ka amince kai AUREN WATA UKU. A lokacin da zaka fara project d'in sai ka rabu da matar ba tareda mahaifinka ya fahimci komai ba. Tinda dama Auren yake so kayi d'in. Toh kayi a wuce wajen. Dan ka rabu da matarka bazai ce meyasa ka saketa ba. Since we all believe ana aure ana rabuwa. Sann bazai tab'a yuwa A amshe aikin daga hannunka ba tinda abu ne base on agreement Wanda Ya k'unshi saka hannu daga duka b'angarorin."
Shiru Haidar yai yana dubanta. Yasan mahaifiyarsa akan abinda take so. Sann shid'in tamkar makaminta ne da take amfani dashi wajen kare kanta. Idan Har ya amince da wann Auren za'a basa project d'in and everything he's long been planning for zai samu damar aiwatar dasu. He can finally have the chance to ruin his Dad and his so called company. After all, the marriage is just for three months. Sann idan komai Ya wargaje auren iyayensa ma zai wargaje kowa zai kama gabansa a wann ahali da babu komai cikinsa face k'unci da k'arya. Zai d'auki matarsa Dareen suyi nesa da wann ahalin Wanda basuda hurumin saninta ko rashin saninta because bai d'auki ahalin matsayin ahali ba. Kaman yanda suma baida mahimanci a wajensu. Haka zalika bai damu yaji waye zasu aura masa ba. Dan yayi imani da zaran an basa jagorancin wann project d'in sun aura ma banza ne da wofi dan ko kamanninsa bazai tab'a bari matar ta sani ba.
"Fine Mommy.. Na amince,na amince da AUREN WATA UKU kaman yanda kikace.!"
Mommy jin abun tai a bazata. Wai Ya amince zaiyi wann Auren Wanda bata sanar dashi k'udirinta da mak'asudin Auren ba. Ta tabbata a nasa tunanin ta zab'i yayi wann Auren ne sabida project d'in da yake matuk'ar so ya jagoranta. Ta tabbata kafin ya saki Matar tama riga ta jima da rabuwa dashi idan har aikin Malaminta ya cika. Zuwa wann lokacin kuma asirin ya karye hankulan ahalinta zai dawo jikkunansu. Daga nan sai su bud'e sabon babin rayuwa mai dad'i ita da ahalinta.
Ta k'araso ta rungume Haidar tana hawaye tsananin farin ciki da Ya lullub'eta.
Anisa dai sai lek'ensu take, tana mamakin yau Mommy ce harda rungumar Haidar haka. Lallai something's going on.. She needs to find out. Saurin sauk'owa tai sanda Mommy da Haidar suka kuma shigewa sashen Daddy.
Mommy bakinta har kunne take duban mijinta "Engr, Haidar Ya amince.. Ya amince da sharad'inmu. Ya amince da batun Auren."
Zuciyar Anisa dake daf k'ofan katafaren parlorn yai wani irin tsinkewa. A fili ta furta "Aure.? Aure kuma..?"
Daddy ya d'ago yana duban Haidar Wanda ke tsaye gaba gareshi cikin parlorn Ya nad'e hannayensa kansa a karkace. Shid'in ma mahaifinsa yake duba. Irin duban nan na your days are numbered.
Cikin zuciyarsa yake furta ' This is the beginning of an end for you Daddy.. K'arshenka and your so called company.. Komai zaizo k'arshe a tsakanin wata uku. This project will turn out to be a great disaster for you and your company. On the day of launching the project, a wann ranan zan gayyato maka manyan bak'i Daddy.. I'll make sure to invite EFCC for you.. All your assets will be seized. Ba a nan zai tsaya ba. You will fall in front of everyone.. I'll make sure they sue you and your company for poor Workmanship.. Zan tabbata they impose sanctions for your company ta yanda zai zama ba kai ba shigo da wasu manyan kayan gine gine na zamani cikin k'asar nan. After all this Daddy. Ni, Aliyu Aliyu Maitama, your never wanted son will personally charge you for a series of discriminations while working under your company. Duk wasu cin mutuncin da ka mun a wann Kampanin naka sai nasa ka cinyesu gaba d'aya. I'll make you lose everything. Alk'awari ne.!'
Muryar mahaifiyarsa Ya sinkayo tana fad'in irin farin cikin da take ciki burinta yana gab da cika. Sai kuma ya hango Daddy wanda tuni ya nufi study d'insa. Cikin sauri yabi bayan mahaifin nasa.
Daddy ya d'ago yana dubansa. Haidar ya shigo cikin study d'in sosai. Su duka biyun suna duban juna. Daddy yace "What now.? Mai kuma kake nema.?"
Zama Haidar yai saman kujeran dake gaban table d'in Daddy. Ya d'auki pen ya zara plane sheet mai d'aukeda alama, adireshi had'ida sunan company dake bisa table d'in. Ya mik'a ma Daddy. Lokaci guda yake furta "You and I are both businessmen Daddy. And we know how things work a duniyar kasuwanci. Since everything here is about business Daddy. Zamuyi shi a rubuce, sann mu saka hannu to avoid business pitfalls.."
Daddy ya tsaresa da idanu yayinda Haidar yaci gaba "We will both sign this agreement tabbacin babu janye yarjejeniya daga baya."
Daddy ya amsa takardan kafin ya ketata gida biyu "Na riga na gama yarjejeniya da mahaifiyarka. Bana magana biyu. If things go wrong, believe me your Mom will face the consequences." Yana ida fad'in haka Ya nuna masa k'ofa.
Haidar yai Shiru yana mai jinjina kansa. Har cikin ransa yake jin babu abinda zaisa Ya janye duk wasu k'udirinsa gameda wann wofin ahalin.
** A b'angaren Mommy kuwa ta kira Asshe ta sanar da ita yanda sukai da Daddy harma da Haidar.
Asshe tai Shiru kaman mai nazari "Amma Aunty Kwaise na fara tsoro da lamarin nan. Ta ya zaki saka aurenki on the line..?"
"Ta ya bazan saka nawa auren at risk ba Asshe.? Har yaushe zan jira na gyara ahalin bayan ga dama ya sameni. Asshe na shirya sadaukar da komai domin ceto ahalina."
Asshe ta furzar da huci "Aunty Kwaise I find it strange wai Haidar Ya amince tashi guda. Shin har haka yake son wann project d'in.. Anya son da yake ma aikin yakai yai making huge decision irin wann..? Kuma shi Engr yasan Auren wata kika shirya yi ma d'ansa.?"
Ta girgiza kai kaman Asshe tana dubanta "Ta Ya zai sani Asshe..? Haidar ma na fad'a masa zai iya rabuwa da matar a wata uku ne dan na samu amincewarsa a sauk'ak'e. Amma kinsan su duka biyun Babu Wanda yasan mak'asudin auren. Dukkansu kafin su ankare aikin gama ya gama."
Asshe ta kuma jinjina kai "Ciniki ta fad'a kenan. Yanzu zamu iya zuwa asibiti mu biya kud'in jinyar mahaifinta.."
Mommy ta kuma jinjina kai "K'warai.. Bana so a d'auki lokaci Asshe. Kawu Bana da mutanensa zasu zo su sameki ku tsara komai. Su karb'i auren a nad'o makarin asirin a kawota. Kud'i ba matsala bane Asshe. Zan kashe ko nawa ne domin wann buri nawa Ya cika."
Asshe ta kuma jinjina kai "Shikenan Aunty Kwaise. Bakida matsala, zan tsaya ra'ayin daka Har Allah ya shige mana gaba."
Mommy suna ida wayan ta fito parlor yanda ta tadda Anisa ta kifa kanta sai kuka take.
Mommy ta k'araso a birkice tana tambayarta meke faruwa.
Anisa ta d'ago tana dubanta dan tinda taga Haidar yazo gidan gashi taji ana batun Aure. Bugu da k'ari akan idonta Mommy ta shige d'aki tana magana da Amminta a waya Wanda ta tabbata bazai shige zancen auren suke ba. Shin iyayenta basu fahimci irin son da take ma Haidar bane. Idan har ba auren Haidar zatayi ba toh ma zaman me take a gidan. Take ta mik'e tana kuma fashewa da kuka ba tareda tace da Mommy komai ba.
Mommy tabi bayanta da kallo kafin ta tab'e baki tace "Sangarcin sun motsa kenan." Bata kuma bi takan Anisa ba taci gaba da sabgoginta dan yau Ji take tamkar kaf damuwarta na gidan duniya Ya yaye.
**
Asshe ta dubi Umma wacce ta cakare cikin tsadaddan leshi d'anubansu, Tai far da idanu "Wow Umman Ummul kinga kuwa yanda kika fito kikai kyau.. Kyaunki na asalin k'abilar Fulbe Ya kuma bayyana.. Gaskiya kud'i zasu amshe ki.. Kin ganki kuwa wa zaice kin haifi Ummul.."
Umma ta ci gaba da wahse baki tana juyi gaban madubi tana duban kanta "Allah ko Hajja Asshe.. Toh ai gwara kar na Saba tinda ba samun irin wann tufafi zanyi kullum ba."
Asshe ta kuma murmusawa "Inji waye.. Ai saidai ki dinga kyautan su ma. Ke ai yanzu kin girmi irin wad'nn ma saidai na order daga k'asar waje.. Kekam fah yanzu kin zarce sa'anninki 'Yarki taci sunanta Uwar alkhairi ta bud'e Miki k'ofofin alkhairi.. Ke fa yanzu da matan gwamnoni zaki dinga jerawa.."
"Na shige tsaran Yaya.." Umma tace tana kuma washe baki.
Asshe tace "Waye kuma Yaya..?"
"Tani kishiyata.." Umma ta bata amsa.
Gajeren tsaki Asshe tai tace "Saidai ta soma kiranki da Yaya daga yanzu dan kin Riga kin amshe girman. Ummul d'inki ta k'wace Miki girman.." Ta aje mata hanshak'in handbag shak'e da kud'i 'yan dubu dubu ciki tace "Wann naki ne ki razani Tani dasu." Dan tinda Asshe ta gane Suwaiba ba kwad'ayayya bace burinta kawai shine ta burge kishiyarta harma da sauran jama'an dake tsangwamar 'yarta su shiga taitaynsu sann Ummul d'inta Tai irin auren da yaran Tani basuyi ba ta k'udiri niyyan cika ma Umma wann buri nata. Dan sosai matar ke sakata nishad'i.
Asshe ta fice tana fad'in bara ta duba Hilala ko ya shirya dan shine zai kaisu.
Umma ta jinjina Kai tana kuma murmusawa. A fili take furtawa bayan Asshe ta fice "Tani kenan.. Dake da 'ya'yanki Kun gama mana wulak'anci.. Yau idanunki zasu gane Miki abin mamaki.. Yau zakiyi nadaman duk wasu abubuwan da kika jima kina min cikin gidan nan.. Ummulkhairy da kike aibatawa Har kina ambatonta da Ummulsharri toh yau sharrinki zai koma kanki Tani.. Ki jira bayyanata.!"
SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU..!*
*16*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Safiyar Washe gari gidan Hajja Fannah suka fara nufa ko an samu wani bayani gameda Umma. Saidai har kawo wann ranar babu Umma babu labarinta babu wani bayani tak'amaime da ita. Ummul sai juya wayar Umman take cikin hannunta nokia k'irar 3310 duk taji jiki ta kod'e. Hawaye suka kuma gangaro mata. Gashi sun tadda Hajja Fannah ma bataji dad'i ba kwance take lik'is dan tin bayan tafiyar Hisham jikinta ba dad'i k'ok'ari kawai take. Ummul ta dubeta tace "Hajja ko dai asibiti zamuje.?"
Hajja Fannah ta murmusa cikeda jin dad'in yanda Ummul ta damu da damuwarta "A'a Ummul, ba sai naje asibiti ba.. Zuwa anjima zazzab'in zai sauk'a in sha Allah."
Ummul ta jinina kai suna masu mata fata da addu'an samun lafiya itada Khulsum.
Khulsum ce ta soma mik'ewa yayinda Ummul ma ta mik'e suna mata Sallama da fad'in zasu biya Asibiti wajen Abba su dubasa daga can zasu k'ara komawa police station ko an samu wani batu gameda mahaifiyarsu.
Ummul ta d'an dubeta "Hajja zamu iya barinki ke kad'ai naga kaman yau jikin naki da d'an nauyi."
Hajja Fannah ta murmusa tana mai mik'ewa zaune sosai dan hankalin Ummul d'in Ya kwanta "Kinji Ummul nifa zazzab'i ne ke damuna nasan kuma bazai shige typhoid d'in nan da ya sakani gana kwana biyu ba. Banison zuwa asibiti ne su tara min magani dan bana shiri da had'iye k'waya Shiyasa ko Hisham ban sanar dashi ba dan nasan yanda kika dage naje asibiti haka shid'inma zai dage. Toh kafin ku min taron dangi gashi can na dafa ruwan zogale ma inata sha dan nafi gane wann." Ta k'arashe cikin k'ok'arin nuna jarumta irinta maras lafiya.
Ummul ta murmusa kad'an. Sosai take jin Matar har cikin ranta. Sun mik'e suna kuma mata Sallama ta k'araso hannunta rik'eda 'yan kud'ad'e ta mik'a masu "Ungo nan kuyi kud'in abun hawa."
Dukansu biyu girgiza kai suke suna fad'in a'a ta barshi.
Ta d'an b'ata fuska tana fad'in "Au baku d'aukeni uwa ba kenan idan har zan baku abu kuk'i karb'a." Ta dubi Khulsum "Ungo nan karb'a maku ita Ummul ai tasan karonmu. Idan bata amshi kyauta na matsayin malamar ta ba ai ta amsa matsayin 'Yata." Can k'asar zuciyarta kuwa Matar D'anta ta kirata.
A dole dole suka amsa dukda dama basuda ko sisin da zai kaisu asibiti wajen Abba balle Har su tafi police station maganan case d'in Umma.
Suka kuma mata godiya had'ida fatan samun lafiya kafin suka fice.
Suna tafe cikin adaidaita Khulsum ta dubi Ummul "Adda mai zai hana mu fara zuwa police station d'in tinda kinga asibiti ko munje ba Lallai Mama da yaranta su bari mu shiga wajen Abba ba."
Ummul ta girgiza kanta "A'a Khulsum, koda zasu hanamu mu je d'in dai. Muji ya jikin nasa Ya kwana tinda idan muka tafi maganan neman Umma ba Lallai mu dawo da wuri ba har sai munji yanda al'amarin Ya kwana. Kinsan ofishin 'yansanda cases da yawa. Inaji a jikina da izinin Allah yai za'a samu Umma." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya irin na Wanda Ya gama karaya amma tawakkali Ya hana furta hakan.
Khulsum ta jinina kai tana amsawa da Allah Ya sa a samu Umma ya kuma bawa mahaifinsu lafiya. Ummul ta amsa da Ameen daidai sansa mai adaidaita Ya diresu k'ofan asibiti.
Suna dosowa haraban ward d'in suka hango Mama da Badi'a. Ga Azeema a gefe harma da mijin Azeemar Habibu. Sai wallahi tallahi suke baka ma gane mai suke fad'i dukda wai k'asa k'asa sukeyi basa d'aga murya kar ajisu a fatattake su.
Azeema fad'i take "Wai kuna so kuce mun tun yammacin jiya kud'ad'en suke hannun Tasi'u kuma wayansa a kashe.?"
Habibu yaci gaba da salati yana tafa hannu. Ya dubi Mama wacce ko iya cewa komai batayi. Huci kurum take. Fuskar Tasi'u ne kawai ke mata gizo cikin ido. Allah ya gani da zataga Tasi'u yanzu a gabanta zata iya shak'esa Har sai an k'wacesa.