Auren wata ukku by sameena - Chapter 9
Auren wata ukku by sameena Chapter 9: Auren wata ukku by sameena Chapter 9. Ta zauna nan parlorn k'asa tv na aikinsa waya manne kunnenta "Aunty Kwaise…
4,486 words
Ta zauna nan parlorn k'asa tv na aikinsa waya manne kunnenta "Aunty Kwaise bakida wata matsala fah. Ni na fad'a miki na kuma yarda da aikin wann Malamin dan kaman tafiya muke da solution d'in matsalar mu. Matar nan dai da muka bige"
Ta d'anyi Shiru alamun tana sauraro daga b'angaren Mommy. Sai taci gaba "A'a Haba Aunty Kwaise nasan fah abinda nake. Ai tuni nasa Yunusa yaro na ya binciko mun komai kanta. Duk wani abinda Ke wakana tsakanin ahalinta. Yazo gidan sauki tinda nan cikin Kano ne. Ai bazai yuwu mu d'ibo ko wace iri mu jajib'a ma Haidar ba koda kuwa Auren na wata UKU ne kawai. Yanzu zuwa gobe idan Allah ya kaimu zakiji duk bayanan da Yunusa zai kawo mun dalla dalla duk yanda akai. Idan ta kama a miki scanning information d'in ne a tura miki ta mail duk za'ayi Aunty Kwaise. Haba abu ne za'ayisa cikin wayewar kai. A yanda na fahimta bakin aljihu ne kawai zai bayani wann kuma nasan ba matsala bane." Ta d'an dara tana kuma kod'a Mommy da mata kirari irin na matan Manya. A haka sukaci gaba da tattaunawar tasu.
Bayan sun ida waya Asshe ta mik'e ta lek'a Suwaiba. Nan ta tadda Umma tuni ta baje saman gado bacci yayi awon gaba da ita harda su minshari.
**
Hisham yai Shiru yana sauraron mahaifiyarsa. Sai kuma ya girgiza kai kad'an "Hajja ba yanda na iya ne. Tafiyar ce ta taso mun babu shiri." Ya d'an matso kusanta had'ida kamo hannayenta cikin nasa "Na bar amanan Ummul hannunki Hajja. Dama tare na ganku nai maku karambani ko nace zuciyata tai karambani…" Sai ya d'anyi fasali "I will come back for her Hajja.. Zan dawo, dawowa na musamman domin Ummulkhair.. Please kici gaba da kula da al'amranta har na dawo. Bazan d'auki lokaci ba wann karan in sha Allah.. Kinji Hajjata." Ya k'arashe cikeda rauni.
Dubansa ta d'anyi duka duka yaushe yazo har zai tafi. Ita kam ta fara gajiya da wann aikin nasa.
A hankali ta jinina Kai "Shikenan. Allah yaci gaba da tsareka yayi maka albarka. Bazan dakatar dakai ba koda ina son yin hakan. Ummul kuma ka barta cikin aminci da yardar Ubangiji. Fatana Allah yasa kar ka d'auki lokaci mai tsawo."
Hisham ya murmusa cikeda jin dad'i yana jin zuciyarta at ease. Fitan sassafe zai wanda ba lallai ya samu ya kuma ganinta ba balle suyi sallama. Amma yayi alk'awarin da zaran ya isa zai kira Hajja ta had'asu a waya.
SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU..!"*
*14*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Mommy ta kuma duban Daddy Wanda fitowarsa kenan cikin shirin fita Squash game. Hannunsa rik'e da jakan kayan motsa jikinsa d'aya hannun Racket ne na buga wasan. Sunada private court d'insu da suke bugawa da abokansu.
Ta d'an sauk'e ajiyan zuciya a hankali "Engr, kan maganar namu..? Nasan idan har na bari sai ka dawo ce min zakai ka gaji." Ta k'arashe da d'an shagwab'a cikeda kissa.
Tab'e baki yai kad'an had'ida girgiza kai "Kwaise I thought mun gama magana. Kinga wann D'an naki na cire hannuna cikin rayuwarsa. So yayi aure ko kar yayi aure is non of my business. The only thing I care about is my company tareda ci gabanta.. " Har ya d'an soma tafiya ya juyo "My tea should be ready kafin na dawo.. Please." Ya k'arashe yana mai ficewa.
Mommy ta furzar da huci tana girgiza kai "A'a Kwaise bazaki karaya ba. You need to do this.. You must.. Ya zama miki dole. Ta k'arashe tana neman layin Asshe.
Shi kuwa Daddy zaune suke a court d'insu shida Alhaji Gimba suna hutawa daga motsa jikin da sukai.
Alhaji Gimba Ya d'an girgiza kai kad'an "Engr Ya kamata kaji maganar iyalinka.. Nima na jima da wann tunanin, inaga Aure shi ya kamata a masa.. Shi zaisa ya tara hankalinsa waje d'aya. Kasan meye idan bazaka iya zuwa ka nemar masa Aure ko ka karb'ar masa ba. I can represent you then. Zaka iya wakiltani nai komai ma Haidar. After all, nima uba ne a gare shi."
Daddy ya d'an dubesa, baice komai ba saima k'ok'arin bud'e bottle water dake cikin hannuna da yake.
**
Washe gari Umma ta karya da karin kumallo mai kyau. Ga kaya na alfarma da Asshe ta aiko mai aiki ta kawo mata. Tai wanka ta cancand'e cikin atampar da bata tab'a mafarkin saka irinta ba. Ta dubi kanta jikin madubi tana mamaki. Ta mik'e ta shiga zaga d'akin ta yaye lalube tana kallon kyaun gidan da aka sauk'eta.
A haka Asshe ta shigo ta taddata. Ta saki murmushi tana dubanta "Maman Ummul har kin shirya abinki… Na aiko Marka ta tambaya ko akwai abinda kike so.." Tai maganar tana shigowa d'akin.
Umma ta girgiza kai tana washe baki "A'a babu abinda nake buk'ata.. Kin ganni na d'age labule kallon Aljannan duniya nake. Ire iren gidajen nan saidai kaita hangosu daga kwalta ashe Inada rabon bacci cikinsu."
Asshe ta murmusa tana jinjina lamarin Umma "Ai wann gidan ba komai bane gaban gidan 'yaruwata Hajiya Kwaise dake birnin tarayya. Wann saidai a kirasa da gidan sauk'an bak'insu ko ma nace miki na ma'aikatansu."
Umma ta zaro ido waje "Gida kaman wann za'a kira gidan Ma'aikata..?"
Asshe ta kuma murmusawa "K'warai kuwa.. Kinga kalli nan.." Tai mata nuni da fuskar wayarta. Umma tai k'uri tana duban hoton matar da Asshe Ke nuna mata wacce tai mata lak'abi da Matar manya cikin zuciyarta.
Asshe tace "Da wa ta miki kama.?"
Kafin Asshe ta rufe baki Umma tace "Da Matar marigayi tsohon shugaban k'asa Maryam Abacha."
Asshe ta jinjina kai tace "Toh wann sunanta Hajiya Kwaise Maitama. 'Yaruwata ta ce da muka fito ciki guda. Ke da ganinta ba sai ance miki Matar manya bace."
Umma ta jinina Kai "K'warai kuwa babu shakka."
Asshe ta jinjina kai tana mai kuma gyara zama "Kaman yanda na fad'a miki Aure take so d'anta yayi kuma ta bani wuk'a da nama na zab'ar masa Matar kirki a nan gida Kano dan bata son ya auri matan dake rubibinsa a bariki wanda akasarinsu girman Turai ne. Ni kuma a yanda kika bani labarinki na tausaya miki. Dake da 'yarki kuna cikin yanayi na k'unci da damuwa. Watak'ila Allah ne ya dubi halinda kuke ciki. Da duk abubuwan da kuke fuskanta kama daga kan kishiryarki har izuwa jama'an unguwa. Ya share miki kukanki. Zanso 'yarki tayi Aure na gani a fad'a.. Auren da za'a bigi k'irji a kirasa Aure. Auren da duk masu jifanku da munanan kalamai sai sunyi d'an da na sani. Domin kuwa Ummulkhairinki ta amsa sunanta Uwar Alkhairi.. Ta kawo miki alheri da ma danginku gaba d'aya. Dan nayi imani katafarin illahirin danginku Ke harma da jama'an layinku babu budurwar da tayi irin Auren da Ummul zatayi. Babu wacce tai dacen miji irin na Ummul d'inki. Yaro d'an gata d'a d'aya tilo ga Attajirin d'an kasuwan da kasuwancinsa ya zaga gida Nigeria da ma k'asashen k'etare." Ta kuma gyara zama "Ke Maman Ummul duk yanda zan miki bayanin dacen da 'yarki tayi bazaki fahimta ba. Ke kanki guje gujen rab'arki za'a fara yi ba ma Ummul da ake gudunta ba. Domin kuwa kin zama sirkar Manyan mutane. Mutanen da ake haskosu a manyan mujallu da talabijin. JINKIRIN Ummul d'inki ya zame maku alheri. Ke fah Maman Ummul wllhi Kakarki ta yanke sak'a."
Ta d'an numfasa "Amma fah ni taimako nai niyyan yi sann tun had'uwa na farko naji na yarda dake na aminta dake. Bugu da k'ari labarinki da kika bani ya tab'a min zuciya dole duk mai imani ya tausaya miki daga Ke har 'yarki. Kuma yanda Ummul d'inki ta juri kyara da tsangwama baisa ta lalace ba ko ta bijire ma iyayenta na kuma aminta ta cika yarinyar kirki wacce kowa zaiso ta zama Matar d'ansa. Amma idan kinaga kunada wani zab'i ko ita Ummul d'in tanada wani bazan tak'ura ki ba sai na nemasa wata dukda na masa sha'awar Ummul."
Ai kafin Asshe ta rufe baki Umma tai tsalle ta toshe mata baki "A'a haba Hajja Asshe.. Har wani zab'i Ummul kedashi.. Ina laifin wanda yaso taimakon ka ya tasamma rufa maka asiri. Ni damuwana Allah yasa 'Yaruwar taki da d'anta su amince idan sukaga hoton ita Ummul d'in.
Asshe tai murmushin cin nasara. Lallai wann matar ta tabbata shashasha yanzu take kuma gasgata duk bayanan da Yunusa ya kawo mata akanta da 'yarta. Wann ko ta fad'a mata mak'asudin auren ba damuwa zatayi ba. Ta murmusa a fili kafin tace "Karki damu 'yaruwata batada matsala ita burinta kawai D'anta ya samu mata ta gari ba wad'ancan 'yanmatan dake sonsa dan kwad'ayin abin hannun iyayensa ba. Shima D'an nata yaron kirki ne mai biyayya mai bin umarnin iyayensa. Na miki alk'awari baza'a sami matsala daga b'angarenmu ba. Amma saidai kinsan ance Aure d'an bincike ne, yanar gizo kawai zaki d'ale ya tantance Miki komai. Kinsan su manyan mutane a yanar gizo ake bikcikosu." Ta k'arashe tana kuma dulmiyar da Umma.
Umma ta shiga girgiza kai "Wllhi ni na yarda dake d'ari bisa d'ari na aminta dake sabida a zamanin nan samun mutanen kirki irinku yayi k'aranci.. Da ace Ke mai cutarwa ce tin a lokacin da kuka bigeni da mota da kunyi tafiyarku Kun barni wajen. Bakiyi haka ba kika d'aukeni kika kaini asibiti kikayi d'awainiyata kika kuma kawoni gidanki. Idan ba kin aminta dani ba na tabbata bazakiyi haka ba."
Asshe ta murmusa "Alhamdulillah, na d'auki haka matsayin yarda da amincewarki. Yanzu ki sake kwana ki sake samun sauk'i da hutu. Mu kuma ci gaba da tsara abubuwa da yanda zasu kasance."
Umma ta katseta "Ko dan sabida idon masu ido da hassadan masu hassada"
Asshe ta jinina Kai "Kinga zuwa gobe ko jibi idan na tuntub'i 'Yaruwar tawa aka samu matsaya sai muje asibiti a biya duk wasu kud'ad'en jinyar mijinki. Sai ki kaini kuma naga surkata Ummulkhairi. Cikin satin nan da yardar Allah magabata zasu taho daga can Abuja sai ayi maganar tsaida ranar Aure. Nafi so ayi komai a gaggauce kafin masu mugun ido su kuma jifan al'amarin da idonsu."
Umma tai Shiru kaman mai nazari sai kuma tace "Tooh amma Hajja Asshe wani hanzari ba gudu ba. Kinga shi mahaifin Ummul yana kwance asibiti baisan yanda kana yake ba. Anya baza'a jira ya farka daga wann jinyar nashi ba."
A dak'ile Asshe take dubanta kafin tace "Haba Maman Ummul ya kike magana haka saikace ba k'arni na ashirin da d'aya muke ba. Na Miki ta bakin bature yace 21st century. Shin ita Ummul batada dangin mahaifi ne da zasu iya bada aurenta. Yaushe za'a tsaya jiran tashin mahaifinta dake tsananin jinya. Waye yasan yaushe Allah zai tada shi. Yarinya ta samu miji shikenan sai ace sabida mahaifinta ba lafiya bazatayi aure ba. A ina ake haka. Yanzu fah mazan wahala suke Shiyasa da zaran an samu gwara a kauda. Baki ganin akasarin Auren da ake yanzu daga zuwa tambaya ba bakin kowa sai kiji an d'aura ai duk sabida gudun masu neman jifanka da sharri ne balle wani abu ya gifta a fasa auren. Kinga 'Yaruwata yanzu take so D'anta yai aure dan a cewarta yaro da kudi hannunsa ba mata had'ari ne. Kinga bazai yuwu mu tsaya jiran mahaifin 'yarki dake jinya Ya samu lafiya ba kafin ayi auren. Kinga bazamu bari namu yaron ya lalace ba. Kawai idan wann aure bazai yuwu ba.."
Saurin mik'ewa Umma tai ta daka tsalle ta tumu gaba Asshe. Ta d'ago hannaye biyu "Ki rufa min asiri kar ki k'arasa maganarki. In sha Allahu fashin auren Ummul ya k'are. An daina k'irga mata fashe fashen aure. Za'ayi aure da zaran magabata sunzo. Ayi tambaya take a d'aure tun kafin mak'iya suji labari." Sai kuma ta fashe da kuka wiwiwi babu k'akk'autawa.
Asshe ta dafata kad'an "Lafiya Maman Ummul Ya da kuka kuma keda zakiyi farin ciki burinki zai cika Ummul d'inki zatakai ga d'akin miji."
Umma ta d'ago tana murmushi ga hawaye na bin k'uncinta "Kukan farin ciki nake Hajja Asshe. Burina zai cika Ummul d'ita zatayi Aure. Zata bar gidan mahaifinta. Zan daina kwana kullum ina tashi na ganta gabana.. Wayyo ni Suwaiba Ashe wann rana zaizo..?" Taci gaba da rera kuka.
Asshe ta zuba ma sarautar Allah ido ganin yanda Umma ke sunbatu tana fad'in Yaya Tani zakici goron Auren Ummul.
**
A b'angaren su Mama kuwa Tasi'u yazo da wasu takardu yanda ya gabatar masu matsayin sabbin takardun shagon Abba. Harda sabbin makullai. Kai da ganinsa kaga maras gaskiya.
Ya dubi Mama da Badi'a a yanda suka keb'e daga can k'asar wani bishiya wajen asibtin.
"Yauwa nace mu had'u a nan sabida 'yan sa ido. Mai saye zai iso yanzu da kud'ad'ensa naira dubu d'ari uku kaman yanda muka tsaida magana.
Badi'a tace "Haba Tasi dubu d'ari uku saikace na sata.?"
Tasi'u yace banda abinki abu ne ake a sirrance kuma ko ina kikaje kayan magada karyawa ake. Ku gode ma Allah ma da muka samu mai saye dan na tabbata shima rahusa yaji shiyasa bai tsnanta bincike ba amma da zaran yasan Mai shagon na numfashi bai cika ba kinsan bazai sayi gaibu ba. Ni fah taimako nake a nan."
Mama tace "Kyaleta me ta sani wann. Ni fah da kike gani so nake ayi komai a gaggauce kafin Suwaiba ta bayyana. Dan na ranste kwandala bazasu samu ba daga ita har yaran nata."
Tasi'u yace "Ah toh magana kenan.. Yauwa gashi can ya k'araso." Yai masu nuni da mai sayen shagon Wanda Tasi'un bai jima da masa kwatance yanda zai samesu cikin waya ba.
Yana k'arasowa Tasi'u ya warware takarda "Wann takardan yarjejeniyar mallakar fili ne.." Ya saka yatsa a baki ya dangwali halshensa kafin ya d'aga d'aya takardan "Wann kuma takardun fili ne Wanda local government ta saka hannu akai, ga saka hannun sarkin Kasuwa. Kunsan ko wace kasuwa tana k'ark'ashin local government d'in da take ne."
Ya dubi Mama "Yauwa Mama nan wajen shine wajen saka hannun magada watau masu sayarwa kenan. Nan kuma wajen saka hannun mai saye ne. Nan kuma wajen saka hannun shaidu."
Badi'a ta katsesa "Amma shi mai sayen baizo da shaidu ba."
Tasi'u ya Washe baki "Wani aiki sai Badidi ta. Banda abinki meye amfani na. Ai duk dai a rubuce ne kawai ake abin ni duk zan iya saka hannu na zame maku shaidu.. Eh ai duk abun a rubutu ne kawai."
Ya dubi mai saye yace "Mutumi na ai sai ka saka hannu ko.." Mutumi Ya amshi takarda Ya saka hannu.
Tasi'u Ya kuma Washe baki yace "Ai shikenan ka mallaki shago a garin Kano.. Burinka Ya cika.. Allah yasa ma kasuwa Albarka." Sai Washe baki yake dan dama mutumin k'auye ne irin Wanda ko cirani basa fita cikin kauye suke kasuwancinsu burinsa Ya mallaki nasa shagon cikin garin Kano nan yai gamo da Tasi'u.
Tasi'u ya dubi su Mama "Yauwa Mama ga wajen da zaki saka hannu."
Mama ta dubesa a dak'ile "Banida hankali ne zan saka hannu banga kud'ad'e ba."
Tasi'u yace "Banda abinki Mama Tani waye yake yawo da kudade masu yawa irin haka. Ai sai b'arayi su bi mu. Haba shi fah kud'i d'an sirri ne."
Mutumin Kauyen yace "Wann gaskiya ne. Daga nan zamuje tareda shi surkin naki Ya amsa kud'in."
Tasi'u yace "Ahtoh tare zamu tafi takardu suna hannuna bani damk'a masa takardun Har sai ya dank'a min kud'ad'en. Ko nima baki yarda dani bane. Na tabbata da baki yarda dani ba da baki bani 'yarki Badi'a ba."
Mama ta jinina kai "Shikenan.." Ta dubi Badi'atu tace ta nuna mata yanda zata saka hannun. Tasi'u kaman zai kamo hannayenta yake nuna mata. Yace Badi'a ma ta saka duk suka saka.
Tasi'u yace su koma asibiti wajen Abba shi zai k'arisa ji da komai. Zuciyar Mama ba wai ya kwanta ba suka nufi cikin asibiti. Sam rawar k'afan da Tasi'u yake ba wai ta yarda dashi bane. Sai ta soma tunanin anya batayi gangancin barin Tasi'u su tafi su biyu da mutumin amsar kud'ad'en ba. Koda yake ya Santa ya san halinta ita ba Badi'a bace tsaf kwabo yai ciwon kai sai ta tatse. Da wann tunanin suka shige cikin asibiti.
(Rayuwar Duniya kenan. A wann babi munji yanda Matan Abba Wanda ke kwance gadon asibiti sukai cinikin dukiyarsa da kuma 'yarsa. Mama dai tayi cinikin dukiyarsa yayinda Umma tayi cinikin 'yarsa. Fad'in Manzon Allah S.A.W cikin hadisin Abdullahi ibn Amr . 'Duniya jin dad'i ne kuma mafi alkhairin jin dad'inta shine samun mace ta gari.' Sahih Muslim 1467. Tabbas babban rahama ne Allah ya baka Matar kirki wacce zata tsare maka mutuncin kanta iyalanka da kuma dukiyarka Wanda suke amana a hannunta. Allah kasa mufi k'arfin zukatanmu. Ameen).
SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU.!*
*15*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Mama dai ta gaza zaune ta gaza tsaye tin bayan tafiyar Tasi'u da mai sayen shagon Abba. Ta dubi Badi'a dake shafen shafen waya tace "Ke kira min Tasu'u shirun nan nashi yayi yawa.. Karb'an kud'i saikace karb'an bashi.. Maza kirasa naji ina ya makara ne wai."
Badi'a ta d'an girgiza kai "Haba Mama ko fah awa d'aya baiyi da tafiya amma kin d'aga hankali a kirasa. Nasan halin Tasi barsa da shaye shayensa amma banda sata."
Zuciyar Mama yai wani irin bugawa. Ta dubi Badi'a a zabure tace "Badi'atu ina hankali na da tunani suka tafi Har na mance Tasu'u Ya tab'a shaye shaye.. Yo ina ake dank'a amanan kud'i hannun d'an wiwi Bad'ia..!"
"Mama mijin nawa ne d'an wiwi..? Ya tuba fah."
"Idan ba d'an wiwi ba d'an uwarki ne..!" Mama tace tana danna mata dak'uwa.. Zufa ya shiga keto mata ta ko ina "Na shiga uku.. Na kashe kaina ni Tani. Wani b'atan basira ne ya d'ebeni na dank'a amanan dukiyar nan hannun Tasu'u."
Badi'a tai tsaki "Yo tsaban kina sauri mana a kauda shago kar ya shiga jinyar Abba ko Umman su Ummul ta dawo amsan hakkinta da na yaranta.."
Mama taci gaba da safa da Marwa "A'a Tasu'u bazai tab'a min wann gangancin ba. Wllhi akan kud'in nan sai na cajesa daga hula har takalmi ba abinda ya shalleni ehe. Bayani d'aya na sani na kud'ad'ena.." Ta kuma duban Badi'a "Ki sake kiransa nace.. Ungo kirasa da nawa wayan..!"
Badi'a taja dogon tsaki tana mitan Mama ta isheta.
Wasu nurses suka fito suka tambayan iyalan Malam Isubu. Mama ko takansu batabi ba ita dai damuwarta kud'inta. D'aya nurse d'in da ya ganesu Ya k'araso yana fad'in "Hajiya ashe kuna nan. Muna can munata nemanku a ward."
Mama wacce gaba d'aya take a daburce ta dubesa a harzik'e tace "Toh gashi ka ganmu ai me akayi..?"
Nurse d'in ya d'an tab'e baki ganin yanda ta hayayyak'osa "Dama wasu magani da drip za'a saya shine akace a sanar daku.."
Bai kai aya ba Mama ta katsesa "Da uwar me za'a sayi maganin inyi.. Kai kaga mun maka kalan masu bada kud'i.? kuje ku masa abinda zaku iya mu nan bamu maganin k'wandala ehe..!"
Ta dawo kan Badi'a tana fad'in ko batir d'in wayar mutuwa zai kar ta fasa kiran Tasu'u.
Nurse d'in Ya kuma bud'e murya yace "Ku fah muke jira Dr zai iya shigowa round.."
"Kai bana son fi'ili wai bakaga tashin hankalin da muke ciki bane?"
Nurse yace "Wann matsalar ku bari idan Kun bar nan sai ku warwareta dan Allah. Yanzu dai ku sayi abinda aka ce ku saya dan a samu a ceci rayuwar majinyacin."
Muryar Badi'a yaja hankalin Mama alamun ta samu Tasi a waya. Badi'a ta juyo tana duban Mama da murmushi saman fuskarta "Ki kwantar da hankalinki Mama barin saka miki shi a speaker kiji."
Daga d'aya b'angaren Tasi'u Wanda daga jin yanda yake kana iya sauraran k'aran ababen hawa alamun yana bisa kwalta kenan. Fad'i yake cikin d'aga murya irin na Wanda ke bisa abin hawa musamman babur "Mama ina bisa hanya ne shiyasa bani iya d'aga kiran. Gasu na karb'o su.. Go slow ne ya tare mu kinsan ana fashe fashe sabida k'ara manyan titi.. Eh gani na ma kusa k'arasowa kenan."
Mama saida ta silale ta zauna dirshan a k'asa tana dafe k'irji "Yauwa yanzu naji batu" Ta marairaice murya tunanin yanzu kud'inta na hannun Tasi'u dole ta bisa a sannu kafin ta dafesu "Ayya ayya Tasu'u na.. Sannu da k'ok'ari kaji d'an albarka.. Muna nan muna jiranka.. Allah iso da kai lafiya."
Nurse da ya zuba ma sarautar Allah ido ganin Ya zo masu da muhimmin batu amma hankulansu na kan wani abu daban yace "Amma Hajiya kun saurari abinda na fad'a kuwa.?"
"Mun saurara mana. Meye.? Ko so kake mu maimaita maka ka tabbatar mu ba kurame bane."
Ya d'an girgiza kai "Hajiya gaskiya ina ganin girmanki kuma ni aikina nake k'ok'arin yi a nan. Ya kamata ki dinga tantance kalamanki."
Mama ta tab'e baki dan a halin yanzu hankalinta ya kwanta taji labarin kud'ad'enta "Kaga k'aramin likita wllhi fah saidai ku k'yalesa mai aukuwa Ya auku dan nan da kake gani bamuda abinda zamu bada."
Nurse d'in yace "Ban gane mai aukuwa Ya auku ba. Ya kukeso ayi yanzu.? Kunsan cewa kud'in kwanakin da aka biya masa ma sun kusa cika. Kwanan nan za'a buk'aci k'arin kud'i musamman duba da irin jinyar da majinyacin ke fama dashi. Jinya ne babba kuma mai cin kud'i.."
Mama ta dubesa galala "Au dama ba gwamnati bane Ke biyan kud'in jinyar nasa.?" Dan ita a nata zaton alfarmar gwamnati Abba ke ci tinda dai tasan tin zuwansu kwabo ba'a amsa wajensu ba.
Nurse ya girgiza kai cikin rashin yarda gajeriyar dariya na neman kufce masa "Mama kenan, a K'asar mu ta gado kike fah ko kin mance ne na tuna miki. Nothing is free in this country."
Mama ta tab'e baki "Kai kasan me kace. Ni dai na fad'a maka gaskiya bamu maganin fici ehe."
Nurse yace "Amma ina wann mutumin da yai settling bills d'inku yake.. Ina nufin ina mutumin da ya biya kud'ad'en..?"
Mama ta dubesa da mamaki "Wane mutumi kenan..?"
"Wanda na ganshi nan ya rako wasu 'yanmata biyu.. Ina tsammanin 'ya'yan majinyacin ne.."
Mama tace "Toooh.." K'irjinta na bugawa "Kar dai ace wai su Ummul kake nufi. Uban wa ya biya kud'in toh..?"
Badi'a ta katseta "Wann mutumin mana da suke tare wanda har Azeema tace Miki saurayin Ummul ne kuma shine yaje yayi belin Khulsumu a police station. Ta tabbata dai saurayin Ummul ne."
Mama ta dafe k'irji cikeda mamaki. idan har Wanda aka ambata da saurayin Ummul ya biya tulin kud'ad'en nan watau mai kud'i kenan wann karon Ummul ta samo. Toh wllhi bazata saku ba wai bindiga a ruwa. Yanda sauran batun auren suka lalace shima wann haka zai lalace yabi iska. Bari ta gama da batun kud'ad'enta ta tabbata sun shiga lalitarta. Ya zama dole ta bincika tasan waye shi daga ina yazo dan tasan yanda zata b'ullo ma al'amarin amma bazata zuba ido Ummul ta k'are a gidan maik'o ba dukda wann canfi da aka mata.
Nurse yace "Ku nake sauraro."
Mama tace "Yo ina kaw zaku gansa. Dama yaran karuwai ne yaje yayi abinda zaiyi dasu ne shine ya biya ladan jinyar ubansu. Sai ku jira su zo su baku dan nasan yanda Uwarsu ta tafi nata yawon suma ba zama zasuyi ba qila sun had'e a bayan gari. Ku jira Zasu zo so su kuma biyanku wasu kud'ad'en. Idan Har kuma basu samu ba sai Malam ya jira har ta Allah ta cimmasa. Idan kuma lokacinsa baiyi ba har wa'adin kwanciyar sa saman gadon asibitin ya cika sai a maidasa can gida saman katifarsa ya cika a can."
Badi'a tace "Ahtoh magana kenan.."
Mamaki ya cika nurse d'in. Wai dama a duniya akwai mutane irin haka. Shikam yasha cin karo da mutane daban daban a aikinsa na asibiti amma bai tab'a cin karo da mutane irin wad'ann ba. Girgiza kai kurum yai yasa kai ya shige zuciyarsa fal tausayin Malam Isubu.
**
Abuja.
A fusace Daddy Ke dubanta "Wai meyasa kike son b'ata mun rai ne Kwaise. How many times do I have to tell you this.. Duk abinda ya danganci wann D'an naki bai shafeni ba.."
Mommy ta soma girgiza kai "Why.? Meyasa..? Aliyu D'anka ne Engr.. He's your flesh and blood.. Meyasa kake masa irin wann k'iyayyar haka..? Su waye suka shiga tsakaninka dashi har haka..?!"
Cikin tsawatarwa Daddy ya katseta "Har sai kin tambaya waye ya shiga tsakani na dashi Kwaise.. Meyasa a kullum kike son tuna mun baya.! Kinfi kowa sanin wann D'an naki only reminds me of my sin. He reminds me nothing but my past Kwaise. Kuskure mafi muni da na tafka a baya… All because of you and your selfishness..!"
Mommy na hawaye take girgiza kai ganin hannun mijin nata Har na rawa yake nunata. Cikin kuka take furta "Ni ce na maka laifi ba Haidar ba. Amma ka daina hukunta Haidar kan laifin da baida masaniya akai.." Muryarta yaci gaba da rawa "Haidar Ya taso cikin k'unci da tsangwama. A baya Nayi zaton izuwa wann lokacin zaka k'aunace sa kuma ka mance komai sann ka zama mahaifi a gareshi kaman yanda ko wani uba yake. He's your only son our only son…"
Katse ta yai ta hanyar d'aga mata hannu "This family can never be like a normal family Kwaise.. Kinfi kowa sanin haka. Farin ciki bazai tab'a wanzuwa cikin wann ahalin ba.."
Cikin rawar murya tace "Nayi zaton ka yafe mun.?"
Ya jinjina mata kai "Na yafe miki amma idan Har zanga d'anki sai na tuna Kwaise!"
Mommy ta girgiza kai hawaye na kuma zubo mata. Tabbas an shiga tsakanin D'anta da mahaifinsa. Dan idan ba aikin asiri ba ba yanda za'ayi Ya d'auki laifinta Ya d'aura kan d'anta Wanda baida masaniyar laifin har yai masa irin wann k'iyayyar.
Ta kuma share hawayenta "Meyasa kake zaune damu ni da Haidar.. To build your image a duniyar kasuwancinka.?" Taci gaba da huci "Fine.. Mun cika maka wann burin.. Kanada iyali da duniya zata d'aga ido ta kalla ta kirasu da ahalinka. Amma babu komai cikin ahalin face k'arya da k'unci.. Nothing is real here..!"
"Kwaise.!!!" Ya ambaci sunanta cikin d'aga murya.
Mommy na hawaye taci gaba "Eh kasuwancinka shine kawai gaskiyarka.. But your family.."
"You are right… I only care about my business because it's the only thing that keeps me moving bayan tarwatsani da kikayi years back..!"
Ta lumshe idanunta hawaye na kuma gangaro mata. Sai kuma ta sassauta murya "I endured everything.. I even lost my own son without even realizing it. Thinking maybe wataran zaka k'aunacesa.. But than… I failed..! I failed as a mother and I failed as a wife..!" Kuka yaci k'arfinta sanda ta duk'a k'asa tana mai isarta.
Ta d'an d'auki lokaci a haka kafin taji hannun Daddy saman kafad'unta. A hankali ya d'agota. Kaman wacce akace ta k'ara kuka.
Ya d'an shafi fuskarsa ganin yanda take kuka sosai tana fad'in ta gaza ta ko wani b'angare. Ta gaza protecting ahalin. Rungumeta yai ta b'angaren jikinsa kad'an yana fad'in Ya isa ta daina kuka. A haka yai masu masauk'i suka zauna saman kujera.