Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 8

Auren wata ukku by sameena - Chapter 8

Auren wata ukku by sameena Chapter 8: Auren wata ukku by sameena Chapter 8. Muryar Mommy ya sinkayo tana tausan mijin nata da yaji bayanan d'an nasa ya…

4,469 words

Muryar Mommy ya sinkayo tana tausan mijin nata da yaji bayanan d'an nasa ya kuma sauraresa.

Kaman bazaice komai ba sai yai masa nuni da hanyar da zai sadaka da study d'insa daga nan cikin parlorn.

"You can leave it over there. Maybe, I'll go through it when I'm less busy…" Daddy yace yana mai rufe magazine d'in had'i da zame farin glasses na k'ara k'arfin gani "I just hope it is not one of your foolishness."

Haidar ya rintse idanunsa yana jin abun har cikin k'ahon zuciyarsa. Bai kuma juyowa ya dubi mahaifan nasa ba yasa kai ya shige cikin sauri kafin zuciya ta d'ibeshi.

Yana shigewa Mommy ta mik'e tabi bayansa da sauri dan wani tunani ne ya fad'o mata wanda k'ila damarta kenan akansa.

A waje yanda ya aje motarsa ta cimmasa. Ta bud'e murya ta kirawo sunansa.

Kaman bazai tsaya baya, sai kuma ya dakata ba tareda ya juyo ba yana mai furzar da huci a hankali.

Mommy tai saurin k'arisowa yanda Haidar ya kaikaito yana dubanta.

"What now.? Kin mance ne baki bani naki insults d'in ba shine kika biyoni waje..?" Ya fad'i idanunsa akan mahaifiyarsa.

Mommy tai k'ok'arin dannewa dan yanzu ta tabbata he's not in his right state of mind.

"Kaga Haidar I'm not your enemy here.. In fact taimakonka nake so nayi.. Naga yanda kake matuk'ar so kai handling project d'in nan… Kuma nima na tabbata kai kafi cancanta kayi d'in… I can be your ally until your achievement."

Murmushi Haidar yai hannayensa dafe da kunkumi yake duban Mommy. Sai kuma ya girgiza kai yace "Seriously Mommy.. You wanna be my Ally..? Since when Mommy..? Yaushe kika fara damuwa dani da abinda ya shafe ni..?"

Mommy ta zuba masa idanu.

Haidar yaci gaba "Kinsan meye damuwarki Mommy.. Shine ya amince na jagoranci aikin sabida personal interest d'inki. Kinsan na jima da sanin ni a wajenki ba komai bane face weapon. Makaminki.. Kuma kar ki mance na fad'a miki bazaki sake amfani dani ba wajen cimma wasu mnufofinki. Wancan Aliyun ya Riga ya mutu Mommy.. He's long been dead.!"

Yana ida fad'in haka yasa kai ya shige motarsa sai sakin huci yake.

Zai bud'e marfin motar kenan Mommy tai saurin dafa hannunta saman nasa. Hawaye suka soma gangaro mata. Cikin tsananin rawar murya take furta "Haidar… What did they give you.. What have they done to you to turn you against us like this..?"

Cikeda k'osawa ya zame hannun Mommy daga saman nasa "Ba hawayen da zaki zubar da zaisa na yarda dake Mommy. You destroyed that bond tin da jimawa. So kar ki saka ma kanki ciwo Mommy.. I do not give a damn about this family. I'm doing this project for my own personal interest of course. Kuma bazaki tab'a sani ba until my mission is accomplished." Yana ida fad'in haka yasa kai zai shige motarsa.

Mommy ta bud'e murya tace "Idan ni ce Matar Aliyu Maitama har sai kazo nan ka amince da buk'ata ta kafin ya saka hannu da sunanka saman project d'in nan.!" Tana ida fad'in haka tasa kai ta juya cikin gida ba tareda ta kuma sauraronsa ba.

Juyowa yai yana duban Mommy yana so ya fahimci mai take nufi cikin kalamanta. Yasan mahaifiyarsa tinda ta fad'i haka tanada wani babban dalili a k'asa tana kuma so ya tank'wara shi ne yayi wani abinda take so. Zaiyi duk yanda zaiyi ya tabbata bai fad'a tarkon da take k'ok'arin d'ana masa ba.

**

Kano.

Waya ta ida yi da Marka yanda ta sanar da ita Matar ta farka amma bata cewa komai. Kuma bata fad'i yanda danginta suke ba balle a nemsu. Ga dukkan alamu idan ba mai tab'in kai bane k'ila had'arin ya tab'a mata kai.

Hilal ne ya tuk'ota zuwa asibitin. Ta dubi Marka ta dubi matar wacce Ke ta zabga kuka saman gadon asibiti.

Marka taci gaba da fad'in "Ayya Hajiya 'yan jikokina suna gida basu ganni ba tun jiya. Wllhi duk na gaji gida nake son zuwa ga wann asibitin babu mutane sosai balle likitoci kinsan yanda asibitin kud'in nan suke zuwan likita nada k'aida da lokaci. Tak'i magana tinda ta tashi kuka take. Inaga Hajiya kawai idan likita yazo ruwan da aka d'aura mata ya kare kisa a sallameta ai kunyi naku Allah ya gani."

Hilal ya girgiza kai yana duban Matar cikeda tausayi "No Ammi. Ba haka za'ayi ba. Inaga kamata yayi akaita wajen k'wararru su sake dubata. Watak'ila ta sami wani internal injury. Kamata yayi akaita a dubata a bata all the treatment that's needed. Idan ya kama mu mik'a case d'inta ma hukuma su zasu bincika yanda danginta suke. But we can't abandon her not knowing ina danginta suke. Watak'ila sunata nemanta tin faruwar had'arin."

Asshe ta katsesa "Kai Hilal nayi na musulunci tinda har asibiti mun kawota. Har wacce zata kwana da ita na bari. So bazanyi treating ciwon haukanta ba. Tafiya take tsakiyar kwalta dama can k'ila da guntun haukarta." Ta dubi Marka tace "Marka jeki abinki zan fad'awa nurses d'in da suke bakin duty da zaran likita yazo suna iya sallamarta."

Marka tai godiya da fatan samun sauk'i ta fice.

Hilal ya girgiza kai zai kuma magana ta nuna masa waje "Fita mota ka sameni ina zuwa zanyi magana da mutanen asibitin."

Ba Don yaso ba ya girgiza kai ya fice.

Asshe zata take masa baya kenan ta sinkayo muryar Matar tana fad'in "Lafiyata garau. Kuma duk ina sauraronku. So nake ku d'aukeni ku kaini can babban asibitin koyarwa yanda mijina yake ko zan samu na ganshi. Tani ta hana ni ganin shi tace nida Ummul mu muka taru muka saka masa ciwo.. Ta ina zan soma neman kud'ad'en da Tani tace na nemo na jinyar Malam. Tani takai mak'ura wajen makirci da zalunci." Ta soma kokawan sauk'owa daga gado dikda drip dake d'aure hannunta. Fad'i take "Na tabbata tana can ta d'aura laifin komai akan Ummul da bak'in k'addarar da yai ma rayuwarta dabaibayi."

Asshe tai saurin k'arisowa ta dakatar da ita.

Umma ta d'ago ta dubeta sai ta fashe da kuka "Wllhi lafiyata k'alau ina cikin hayyacina. Sun kasa gane banida wani buri da ya wuce naga Ummul a d'akin mijinta. Toh meyasa Tani zata d'aura alhakin ciwon Malam akaina da Ummul.?" Taci gaba da rera kuka irin na wanda damuwa ya masa dabaibayi.

Asshe ta janyo farar kujera a gefe ta zauna tana duban Matar "Sunana Hajiya Asshe, mun bigeki da mota akan hanyarmu."

"Yaya Tani ce tace lallai lallai sai na nemo kud'ad'en da za'ayi ma mijinmu jinya idan har ina so na sake ganinsa. Ta nad'i sautin muryata cikin waya itada Badi'a sunce ko Kotu akaje ya iashesu Hujja."

Asshe ta zuba mata idanu jin yanda taketa maganganu marassa ma'ana. Labarun da yafi kama da wanda ke cikin depression. A hankali ta d'an jinjina kai ta dubi Matar "Akwai yanda yake miki ciwo ne. Kina so na kira Likita.?"

Umma ta girgiza mata kai alamun a'a"Baiwar Allah ni fah lafiyata lau. Yaya Tani ce ta yanka ragon hauka ta d'aura mun dan kawai Ummul ta kasance 'yata." Sai ta d'anyi fasali ta kuma duban Asshe "Amma wacece ke.?"

Asshe ta k'ura mata idanu tana karantarta sai tace "Toh ma sha Allah. Tinda kince babu yanda yake miki ciwo." Tai fasali dan sosai take so taji labarin Matar musamman da taji abubuwan dake fita bakinta shan cikin Matar bazai mata wahala ba "Ki kirani maganin matsalolinki.!" Ta matso had'ida d'aura hannunta saman na Umma "Ki yarda dani zaki iya sanar dani duk damuwarki. Ni ba muguwa bace nasan zaki fahimci haka tinda bayan bigeki da mukayi bamu k'yaleki ba saida muka tabbata mun d'aukoki mun kawoki asibiti. Kuma ban barki ke kad'ai ba har saida na ajiye wacce zata kula dake. A nan muka shigo da yarona kikaji yana cewa kar mu kyaleki har sai mun tabbata kin isa ga ahalinki lafiya. Wann kawai ya isheki ki yarda mu mutanen k'warai ne ba masu cutarwa ba. Kuma a yanda yanzu duniya ta koma babu yarda tinda har ni nayi shahada na yarda dake ya kamata nima ki d'auki duk yarda ki bani. Watak'ila Allah ne ya dubeki ya had'aki da maganin matsalolonki."

Da mamaki Umma Ke dubanta "Maganin matsalolina ni Suwaiba..?" Tai maganar tana nuni da kanta. "Baiwar Allah anya kaw kinsan matsalolina..? Ai inaji kaf fad'in garin Kano da kewaye babu matar da ta kaini matsaloli tinda har na kasance mahaifiya ga Ummulkhairi.!"

Asshe ta kuma gyara zama cikin son jin taji komai "Wacece Ummulkhairy.?"

Umma ta kamo bakin zaninta tana share hawayen dake kuma zubo mata "Ummulkhairi, 'Yata da na mata lak'abi da Uwar alkhairi..! 'Yata da naci mata buruna da dama." Ta kuma duban Asshe sai ta girgiza kai wasu hawayen na kuma gangaro mata "Amma babu buri guda d'aya da ya cika. Kinsan dalili..?"

Asshe da ko kifta idanu batayi saurin girgiza kai tai alamun a'a.

Umma taci gaba "Sabida mutane sun canfa mun ita.. Duk namijin da yazo neman aurenta guduwa yake. Kodai wani abu ya gifta a fasa Auren. Amma fah dukda wann guje mata da mazan keyi basu fah fasa neman aurenta ba. Kinsan meyasa..?" Tai tambayar murmushi mai ciwo saman fuskarta kafin taci gaba "Sabida Ummul d'ita tubarkallah ce san kowa k'in wanda bai samu ba." Sai kuma ta fashe da kuka "Amma meyasa ta kasa Auruwa..? Meyasa duk masifa da nake fuskanta a nawa gidan Auren ta dalilinta ne.? Meyasa maza ke guje mata. Meyasa k'addararta yazo a haka." Ta k'arashe cikin gunjin kuka.

Asshe ta kamo hannayen Umma cikin nata tana k'ok'arin kwantar mata da hankali "Ki daina kuka. Shi Aure lokaci ne. Baya duba matsayi ko kyaun halitta. Wata da komai ta rasa miji wata ba komai Allah ya bata. Shi Aure kaman hab'o ne da zaran lokaci yayi sai kiga anyi.."

Cikin zuciyar Asshe fal mamaki. Ganin abun take kaman almara. Abinka da mai b'atacciyar zuciya sai ta kuma gaskgata aikin bokansu. Gashi tin ba'aje ko ina kaman sun had'u da makarin sihirin dake jikin Haidar a sauk'ak'e. Sai ta kuma yarda gaskiya Malaminsu ya fad'i ta mance cewa wann duk zai iya zama jarabawa daga Ubangiji mai komai ya baka abinda kake nema d'in a kan gab'ar da kake nema. Wani shikenan sai ya kuma dulmiya cikin b'ata. (Allah kai mana tsari da shirka. Ameen)

Ta saki murmushi tana duban Umma "Ummulkhairinki zatayi Aure. Aure na bajinta. Aure irin na kece raini. Auren nuna ma duniya.!"

Umma ta dubeta da mamaki. Sai ta girgiza kai tace "Anya kuwa Ummul d'ina nada rabon Aure a wann duniyar.?"

Asshe ta murmusa "Idan har kika aminta dani Ummul d'inki zatayi Aure.." Tai maganar cikin jaddada kalamanta.

Hilal ne yai knocking ya lek'o jin shirun yayi yawa. Nan ya hangi mahaifiyarsa da patient d'in kaman sun jima da sanin juna. Mamaki ya cika Hilal. Ya d'an girgiza kai yana mamakin saurin yarda da juna da mata keda shi saikace ba Ammi bace ta gama cewa su tafi su kyale matar. Bai gama mamaki ba saida yaga Amminsa sun fito tareda Matar dan dama da ya shiga tace masa bari likitan yazo ya masu sallama tinda taga isowar motarsa. Shidai Hilal haka ya tuk'a su suka nufi gida tareda Matar dasu Ammi suka bige wacce ta zamto bak'uwar Ammin tasa.

Suna isa gida Hilal ya tareta "Ammi Wai meke faruwa ne. Meyasa kika taho da matar nan.. Ammi I thought danginta za'a nema.. Nowadays fah mutane ba abun yarda bane. This whole thing zai iya zama shiri bigeta da kukayi, kaita asibiti da duk wani maganganun da zata sanar dake. Ammi yanzu fah har gida ake ture a sace mutane. Ammi Abba sanannen mutum ne a garin nan. Iyalansa zasu iya zama target."

"Kai dallah rufe min baki. Duka duka yaushe ka sauk'a k'asar balle ka fad'a min abinda Ke faruwa cikinta. Nafika sanin meke faruwa. Ina zuciyar taimakon taka? Inji kai ka fara cewa we shouldn't abandon her. Toh Shiyasa na taho da ita. Kuma ko mahaifinka yazo gidan nan ba ruwanka kar ka sanar dashi komai kaji na fad'a maka."

D'an girgiza kai yai "Fine, yanda kikace Ammi." Hilal yasa kai yai shigewarsa.

Yana shigewa ta d'aga waya tai dialing wani layi. Ana d'agawa ta soma fad'in "Hello Yunusa kanajina. Zan turo maka information kan wata mata. Yanda take zama sunan mijinta da sauransu. Inaso ka gudanar min da binciken k'wak'waf kan ahalinta da abinda Ke faruwa dasu. Bana so a d'auki lokaci. Ayi komai cikin gaggawa."

**

A can b'angaren su Ummul kuwa hankulansu yakai matuk'a wajen tashi. Dik yanda ake tunanin za'a sami Umma anje ba'a sameta ba. Hisham kaw da shi ake aiwatar da komai tuni sun bada cigiyan Umma.

Yai k'uri yana duban Ummulkhairy dake ci gaba da kuka da gaske wann karon. Duk k'ok'arin ganin bata d'aura alhakin iftila'in dake faruwa cikin ahalinsu akanta ba saida zuciyarta ta raya mata hakan. Da wanne zasuji? B'acewar mahaifiyarsu ko kuwa mahaifinsu dake kwance gadon asibiti wanda har wann lokacin bai san yanda yake ba. Ga likitoci sun tabbatar masu idan har treatment d'in da ake masa yaci gaba da failing jikinsa ya kasa amsa then he must have to undergo Cardiac surgery wanda zaici mak'udan kud'ad'e ga had'arin dake tareda hakan.

Hisham ya d'anyi gyaran murya cikin k'ok'arin kwantar mata da hankali. Amma kaman cewa yai ta k'ara. Ringing d'in wayarsa yaja hankalinsa.

Abokin aikinsa ne kuma amininsa Haidar me kira. Ba tareda ya bar wajen ba dan baisan barinta ita kad'ai farfajiyan asibitin suke yayinda Khulsum ke can wajensu mama sun hanata koda lek'a Abba ne.

Daga d'aya b'angaren Sautin kuka ne yai Sallama ma Haidar. Ya d'anyi still kafin yace "Wait..What's that noise.. Where exactly are you..?"

Hisham ya dubeta sanda take k'ok'arin mak'ale kukan nata bayan taji alamun yana amsa waya "You seem to forget things easily nowadays Engr. Ka mance na tafi gida ne."

Haidar ya d'an d'aga gira yana mai jinjina kai "I hope dai lafiya ka samu gidan. I mean lafiya ka samu Hajja..?"

Hisham yace "Yeah lafiya.." Ya k'arashe yana mai d'an jan kalamansa.

Haidar ya kuma tambaya "So who's making that noise.?"

Ciki Zuciyar Hisham ke ayyana isa da jin kan Haidar. Wato bazai iya tanbayarsa wacece ke kuka next to him ba shine wai hayaniyar me yake ji. D'agowa yai Ya dubi Ummul wacce ke k'ok'arin tsagaita kukan nata. Ya d'an mik'e ya matsa gefe kad'an . Ya saki murmushi mai kyau yana mai d'an rage murya "Let's call her Someone.. Someone Very special.. Ka gane I'll call you back."

D'an tab'e yai "Let's talk business." Yace cikin katse Hisham d'in.

Hisham ya d'an kuma satan kallanta sanda Haidar ke sanar dashi sunada ganawa ta musamman gobe a Kampani. Ya zama dole ya katse hutunsa.

Hisham ya girgiza kai kad'an "Wait what meeting Haidar.?"

"Tomorrow by 9:00am.. Design Architect Hisham.!" Abinda kawai Haidar yace kenan.

Hisham ya soma girgiza kai cikin rashin yarda "You know I can't make it to the meeting Haidar.. I mean I'm not the only design architect in your team..." Bai tsaya d'aukan excuse d'in Hisham ba ya katse kiran.

Furzar da huci Hisham yai yana shafan fuskarsa da tafukan hannayensa. Jiki a matuk'ar sanyaye ya dawo yanda ya baro Ummul. Ta ya zai barta ya tafi a lokacinda take tsananin buk'atarsa. He needs to stay.. But what about aikinshi.. Baiso wani yai taking place d'insa. Sun jima suna aiki tuk'uru kan wann project din wanda yake da tabbacin idan ya zama a successful one ba darajan Kampaninsu kawai zai d'aga ba. Zai taimaka wajen daidaita relationship d'in Amininsa da mahaifinsa wanda a kullum yake burin faruwan hakan. Bayan haka Haidar is counting on him. Abokinsa needs him now. Amma kuma Ummul fah. Shin zai iya barinta ya tafi.? Shin waye zai kyale ciki su biyun.

SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU.!*

*13*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Akan idon su Mama Hisham yai ma Ummul sallama ya rakota har wajen Khulsum. Saidai bai sanar da ita batun tafiyarsa ba.

Mama da Azeema ko harma da Badi'a ko k'ifta idanu basuyi. Musamman da sukaga zankad'ed'en Saurayin dake tare da Ummul. Mama tace "Toooh shi kuma wann d'in wai waye.?"

Badi'a tace "Wa ya sani masu ne Mama. Amma kaman saurayin Ummul.."

Mama ta bige bakinta "A gidan uwar waye ya zama saurayin Ummul. Wann yafi k'arfin Ummul inaga dai yayi zaton mabaraciya ce ya taimaka mata musamman da yaga tana cikin damuwa."

Badi'a ta harari Mama yayinda Azeema ke hararar Khulsum tana cika. Lokaci guda ta katse Mama da fad'in "Saurayinta ne mana shine yayi belin wancan k'aramar 'yariskar a police station bayan ta mareni.. Wllhi bazata saku ba. Ai na biya kud'in kwananta a cell amma bata kwana ba.. Toh wllhi komawa zanyi ayi duk rikicin da za'ayi. Ni da kaina na lale kud'ad'e na bawa Habibu ya biya 'yansandan cewa su rufeta ta kwana. Wllhi komawa zanyi ko su biyani kudina ko su sanar dani dalilin bud'eta. Ai ko Kotu akaje akwai kud'in mari. Idan har ba biyana akayi ba wllhi rikicin nan bai k'are ba ehe. Ta k'arashe tana mik'ewa fuuu.

Mama tai k'ok'arin dakatar da ita da fad'in "Ke ke.. Ke ina zaki Azeema..?"

Ko juyowa batai ba Azeema balle ta amsa ta. Saima dialing layin Habib da tai tana k'arawa a kunne.

Mama ta dubi Bad'ia bayan Azeema ta shige. Ta janyota suka keb'e "Yauwa Kinga d'aga waya ki kira Tasi'u yazo ayi maganar sayar da shagon Malam da d'an sauran abinda Ke ciki. Kinga naji d'azu likitocin nan suna bayanin aikin da za'ayi ma Malam mak'udan kud'ad'e zai lak'ume wanda ko gaba d'aya Kantin da kayan dake ciki aka sayar ba isa zasuyi ba. Kinga kafin Wann shago da abinda Ke ciki tsautsayin jinyar Malam ya hau kansu gwara mu dafe su tunda wuri dan bazai yuwu mu zuba d'an abinda zamu samu ma jinyar Malam ba wanda su kansu likitocin k'irdado suke amma ga dukkan alamu ciwon Malam ba na tashi bane.

Bad'ia ta jinjina kai "Kuma ma Mama ai wanda suka fi cancanta su nemo kud'in jinyar Abba wanda sukai masa sanadin ciwon ne. Ina nufin wancan annobar da uwarta." Tai nuni da yandasu Ummul Ke zaune.

Mama ta jinjina kai "Alhamdulillahi ina jin dad'in yanda kike fahimta. Maza kirawo Tasi'un."

Tuni Badi'a ta d'aga wa ta shiga dialing layin Tasi'u mijinta.

Khulsum ta dubi 'yaruwarta Ummulkhairi cikeda tausayawa "Adda yau d'in fah duka baki saka komai cikinki ba. Dan Allah kiyi hak'uri ki tashi haka nan mu tafi gida yamma ta riga tayi."

Ummul naci gaba da hawaye ta girgiza mata kai "A'a Khulsum bazan iya tafiya gida ba. Watak'ila Umma zata zo nan wajen Abba..!" Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.

Muryar Mama suka sinkayo akansu "Au har yanzu Uwar taku bata bayyana ba. Ta tabbata dai Angulu ta koma gidanta na tsamiya."

Suka d'ago suna duban Mama da Badi'a tsaye kansu sai aika masu kallon wulak'anci suke.

Ummul ta girgiza kai "Mama Umma b'acewa tai bamu san yanda take ba."

Sai Mama ta shiga tafe hannaye tana salallami "Na shiga uku ni Tani. Ta nan Suwaiba ta b'ullo..? Ta rasa abinda da zatai sai ta guji Malam sabida jinya ya kamasa ya zama kaya. Watau Suwaiba bazata iya jinyar Malam ba dai shine ta guje ta k'yaleni da wahalar jinya.. Yanzu da zataji labarin Malam ya cika dik yanda take zata fito tazo amsa sunar matarsa dan ta amshi rabonta na gado."

Sai sann Khulsum ta finciki hannunta daga rik'on da Ummul ke mata cikin k'ok'arin dakatar da ita. Sai huci take.

Badi'a ce ta janyo hannun Mama hango mijinta Tasi'u da tayi sai buga sauri yake ya nufosu "Muje Mama kar ma kiyi hayaniya dasu balle a ba ma masu gadi hujjar koranmu. Ganin Abba ne sai a k'iyama idan sunada rabon had'uwa a k'iyamar.

Khulsum ta kuma fincika zatabi bayansu Ummul ta kuma dakatar da ita.

Cikin kuka Khulsum ke furta "Haba Adda Ummul. Haba ke kuwa.. Wai dan Allah meyasa kike dakatar dani.? Mutanen nan fah yaren da kawai suke fahimta kenan."

Ummul ta jinjina kai tana kuma share hawayenta "Abinda suke so kenan Khulsum kiyita biyesu kuna tashin hankali. Ki tuna Abba dake kwance cikin asibitin nan. Ki tuna halinda yake ciki. Sann ki tuna Umma da halinda take ciki. Dan Allah ki daina biyewa Mama da yaranta. Allah ya fisu Khulsum. Mu fawwala masa komai da sannu zaiyi ikonsa akan kowa. Da sannu zai ba ma Abba lafiya ya tashi kafad'unsa kuma suna kallo. Muci gaba da yi masu add'uan shiriya har kullum domin su d'in ahalinmu ne komin lalacewarsu. Muje Khulsum, mu tafi gida mu kai kokenmu ga Rabbil izza wanda shike yaye dukkannin damuwa ya kuma kawo sauk'i da maslaha." Tana ida fad'in haka taji natsuwa ya sauk'a cikin zuciyarta. Jiki a sanyaye suka fice daga asibitin. **

Tasi'u yau harda risinawa yake gaida Tani. A mutunce yau d'in ya fito masu dan batu ake na kud'i.

Mama kaw sai hura hanci take dan ba Wai ta masa afuwan musguna ma 'yarta Badia yake bane. Yanzun ma dan Badi'an ta nace ne sai an sako Tasi'un cikin hidiman, ta tabbata amfani yayi da son da Badi'a Ke masa ya saye zuciyarta da kalamai har ta aminta dashi. Dan dai ita kam har yanzu bawai ta yarda da tubansa bane. Tasan tuban D'anmuzuru ne. So yake a bawa Badi'a kasonta su lak'ume tare da zaran kudi sun k'are yaci gaba da mata iya shege.

Ta dubi mai sayen shagon da Tasi'u yazo dashi dan tinda Badi'a ta sanar dashi cikin waya ya taho da mai cinikinsa dan dama tuni ya tanadi mai saye tinda aka soma batun.

Mama sai cika take tana batsewa tana ciniki da mai sayen shago. Tasi'u yana daga tsakiya a matsiyinsa na dillali sai gyaran waje yake. Mama ta narka masa harara ganin zak'ewarsa.

"Amma dai Tasi'u ka tab'a dillanci ko..?" Cewar Mama tana dubansa a dak'ile.

Tasi'u ya Washe baki "Yo Mama banda abinki meye ba'a tab'awa ai duk abinda aka samu bugawa ake baka san ta yanda wutan zai kawo ba." Sai faman Washe baki.

Ita kaw Hajiya Badi'a sai karkad'a k'afafu take tana Jin kanta. Daga yanzu ta samu makamin rik'e Tasi a hannunta. Tinda zata samu kud'i abinda yafi naira dubu d'ari aiko sai yanda tai da Tasi dole ta zama itace mijin itace mai basa doka da order. Tin yanzu ma biyayya yake mata balle ta dafe kud'ad'enta.

Aka tsaida cinikin Kantin Abba. Mai saye yace gobe suzo da takardu a saka hannu.. Nan fah Mama ta soma zare idanu dan bata San yanda ya aje ba. Tasi'u yace wann ai ba abun tada hankali bane washe gari zaije yai sabbin takardu a gama komai. Yanda yake ladabi wa Mama da Badi'a kai ka ranste yaron gidansu ne

**

A can station Habibu mijin Azeema sun keb'e da sergeant d'in da suka tafi sukai arresting Khulsum dan dama budurwarsa ce, ta cika tayi fam sai hura hanci take "Ni fah ba matsala ta bace dan an mari matarka. Yo a kasheta ma mana ai banida asara. Ni wllhi ba don ka min alk'awarin aure ba wllhi kaji na ranste da bazanje nai arresting kowa ba. Kuma kafi kowa sanin sabida kai nai. Toh ya Oga na zai yanke hukunci tazo nan tana kawo mana hauka. Ce mata akayi nan tasha ne. Ko ka d'auki matarka ka tafi ko a banza na jefata cikin cell a lakad'a mata duka dan bazan bari ta mun sanadin aikina ba. We are talking about my superiors here. Ita har ta isa tazo nan tana mana zage zage da hauka. Tasan me ake kira hukuma ma kuwa. Na ranste maka Habib idan bakai controlling d'inta ba zata gane ita k'aramar mahaukaciya ce dan yanzu zata tabbata mahaukaciyar da Dawanau ma ya kasa mata." Ta k'arashe tana jijjiga sai sakin huci take tana tsuma tana kad'a kulkin cikin hannunta.

Ya murmusa yana shafa hab'a lokaci guda yana lek'en bayansa kar Azeema ta k'araso wajen. Ya sassauta murya "Haba kurtuwata. Kema kinsan duk duniya babu macen da nake so sama dake.. Da kikaga ina biyeta amfani zata min. Yo banda abinki ni kaina sau nawa ina lakad'a mata d'anbanzan duka kuma duk akanki toh dan an mare Azeema har wani damuwa zanyi. Wllhi yanda kika san an mari wofi haka naji.." Ya kuma shafa fuskarsa yana lek'en bayansa irin yanda marassa gaskiya keyi kafin ya matso da fuskar nasa saitin fuskan 'yarsandar "Kinga ita Azeema Ubanta na asibiti rai hannun Allah. Ta tabbatar mun mutuwa zai. Kuma da zaran ya Mutu aka raba masu d'an abinda zasu samu zan amshe komai nata. Tana mallaka min zan koreta da kud'in gadon Uban nata zan aureki Kurtuwata." Ya k'arashe yana wani washe baki yana wani kashe mata idanu "Toh d'an yi mun murmushi mana na gani sahibata.. Inye kaga Kurtuwa Amaryar Habibi.." Ya k'arashe kaman zai rungumota.

Yatsine fuska ta d'anyi had'ida turasa baya "Easy mana Alaji wajen aiki na muke.. Shikenan tinda haka kace.. Amma wllhi idan Kai ga gangancin kawo mun bariki wllhi babu abinda zai hanani cin uwarku daga Kai har matar taka kasan sharri na karanta a banza zan maida police station gidan hutun matarka."

Saurin toshe mata baki yai yana "Wllhi bama ta sanki ba har yanzu. Bata san wace budurwar tawa ba.. Kwantar da hankalinki kafin ma ta sanki ta tsufa gidan marigayin mahaifinta. amma sai na tabbata na amshe d'an abinda uban nata zai bari mata.."

Ta kuma yatsina fuska kafin ta tura k'ofar ta fito tana karkad'a sandan dake hannunta sai faman d'age hanci sama take. Azeema ta bita da kallo dan haka kurum hankalinta bai kwanta da 'yarsandar ba musamman da ta hango Habibu ya fito daga bayanta yana fad'in "Nifa Rankidade Sam bazan yarda ba wllhi sai an shiga kotu an k'watarwa matata hakkinta..!"

Azeema ta k'araso gareshi ta shige jikin mijinta tana fad'in wllhi a tafi kotu kawai.

Sai ya fara kokarin kwantar ma Azeema hankali da fad'in idan yana a matsayin mijinta sai an tafi Kotu.

Sergeant d'in kuwa banda watsa ma Azeema wani wulak'antaccen kallo bata komai.

Da kyar Habibu ya shawo kan Azeema ta amince suka bar police station d'in da sharad'in case din bai k'are nan ba. Sai aika ma 'yarsandar mugun kallo take dan ta kula da wani kallan k'asa k'asa da Habibu ke binta dashi.

**

A can b'angaren su Umma kaw d'aki maiji da lafiya aka sauk'eta. Umma ta zauna saman gado tana lotsawa tana jin taushin latifa ga sanyin AC na bugata. Ai sai Umma ta yab'e baki tace "Kai kaji taushi kaman ina saman gajimare. Tirk'ashi. Lallai masu kud'i suna sha'aninsu."

Asshe dake lab'e daga k'ofa tana karantar duk wani motsin Umma waya manne kunnenta wanda ko shakka babu da Mommy take wayan. Sauk'owa k'asa tai dan upstairs aka sauk'i Umma.

Readers Also Read