Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 7

Auren wata ukku by sameena - Chapter 7

Auren wata ukku by sameena Chapter 7: Auren wata ukku by sameena Chapter 7. Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta "Malam mai haka yake nufi ya za'ayi…

4,486 words

Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta "Malam mai haka yake nufi ya za'ayi yayi Aure bai sani ba.?"

"Koda yasan da Auren baya cikin hayyacinsa akayi Auren. Aure ne da aka k'ulla akan sihiri. Aure ne da aka k'ullashi a Fadan dodon tsafi. Aure ne da aka masa k'ulli uku mai K'arfi.. Aure ne da akayi sa dan a masa farrak'u da Iyayensa.!"

Jikin Mommy ya d'auki rawa. Zufa ya shiga keto mata ta ko ina "Malam.. Auren sihiri fah kenan. Na shiga uku ni Kwaise.. Haba biri yayi kama da mutum. Na fad'a Haidar baya cikin hayyacinsa. Malam wace shed'aniyar ce ta shigo rayuwar d'ah na dan ta rabamu..?"

Ya kuma zana k'asa yana fesa ruwan bakinsa saman yashin "Saninta bazai miki amfani ba dan D'anki bazai tab'a bud'e baki ya sanar dake gameda wann auren nasa ba."

Mommy ta soma girgiza kai "Malam duk yanda za'ayi a karya wann mugun sihiri da aka masa. Ni kuma nayi alk'awarin ko nawa ne zan kashe domin na dawo da d'ah na cikin hayyacinsa."

Girgiza kai ya soma yana aje wani igiyan guru saman tray d'in "Abinda k'asa ya hasko min shine an bisne wann asiri a wani waje yanda ita kanta wann matar da yake tareda ita matsayin matarsa bata san yanda tukunyar sihirin yake ba. Wani wanda yakeda burin ganin bayan d'anki da ma ahalinki gaba d'aya ya mallaki tukunyar ya mata ajiya mai nisa. Dan a yanda k'asa ya hasko mun ita kanta wann matar da umarnin wani take aiwatar da komai.. Har sai wann tukunyar ya fashe kurwan d'anki da aka d'aure ciki ya kub'uta."

Zufa yaci gaba da karyowa Mommy "Na shiga uku ni Asshe waye mai burin ganin bayan ahalinmu irin haka..? Yanzu Malam ba yanda za'ayi a fasa wann tukunyar.?"

Ya kuma zana k'asa sau uku sai kuma ya d'ago ya dubi Mommy "Da sihiri ake karya sihiri.. Akwai hanya d'aya tak da za'abi a karya wann sihirin."

Daga Asshe har Mommy rige rigen tambayar hanyar suke.

"Wani Auren shi zai karya wann Auren.. Sabida asirin ajikin d'anki akayi..!"

Mommy ta girgiza kai "Kana nufi idan yayi wani auren shikenan asirin zai karye."

Shiru yai kaman mai nazari sai kuma ya jinjina kai "Aure ne ba kaman ko wani Aure ba. Aure ne da yake k'unshe da sharudd'a.. Aure ne da za'ayisa domin warware wani auren. Aure ne da ba ko wace irin mace za'a aura ba sai macen da ta cika k'a'idodin da zan sanar daku. Aure ne da yakeda iyaka wa'adin da zai rayu. Aure ne da zai wanzu a tsakanin watanni uku tak.. AUREN WATA UKU..!"

SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU.!*

*11*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Mommy da Asshe suka dubin juna cikin k'ullewan kai.

"Malam sharud'a kuma.. Wasu irin sharud'a kenan..? Sann Kaman ya AUREN WATA UKU.?" Asshe ta tambaya tana dubansa.

Ya kuma d'auko wasu layu da guru ya jera saman layin da ya shata akan farantin. Ya k'irga carbin dake hannunsa yace Mommy ta kama ta zab'i guda d'aya.

Mommy ta d'an juyo tana duban Asshe a d'an tsorace. Asshe ta jinjina mata kai alamun tai yanda yace. Hannu na rawa Mommy tasa ta kama guda d'aya. Ya kamo daidai yanda Mommy ta rik'e bayan ta sake. Ya jinjina kai yace "Kin canki irin macen da zata warware sihirin dake k'ulle da d'anki da kanki."

Mommy da Asshe suka kuma duban juna.

"Tooooh Malam wace irin Mace ce haka..?"

"Itace Budurwar da maza ke so kuma suna gudunta.."

Suka kuma duban juna cikin k'ullewan kai "Budurwar da maza ke so Kuma suna gudunta a lokaci guda..?" Mommy tace cikin rashin fahimta.

Jinjina kai Bokan yayi "K'warai itace Budurwar da makarin sihirin da akayi ma D'anki ke jikinta.."

"Malam ita wann Budurwar ya za'ayi mu tantanceta.. Ayi mana bayani.." Cewar Asshe.

Ya kuma gyara zamansa "Itace Budurwar da maneman aurenta ke guduwa. Ita ce Budurwar da sai gashi kaman zatayi aure har an kawo gab'an sai kuma wani abu ya gifta.. Ita wann irin Budurwar tanada farin jini a idon maza dan duk guje ma aurenta da mazan suke basu fasa neman Aurenta. Ita wann Budurwar itace makarin sihirin. Kaman yanda maza ke guje mata haka d'anki zai guje ma wancan shed'aniyar da ta jefesa da guban asiri koda dafin asirin yana sakashi yaji yana son kasancewa da ita. Yanda maza masu neman wann Budurwar suke guje mata haka d'anki zai guje wancan shed'aniyar matar, za kuma ta fita daga rayuwarsa fita ta har abada kaman dai yanda mazan suke fita daga rayuwar ita makarin asirin toh haka d'anki zai fice daga rayuwar wancan hatsabibiyar da ta jefesa da dafin asiri matuka ya mu'amulance wann budurwar da aka aura masa cikin watanni Uku na Aurensu."

Ganin sun zuba masa idanu kaman basu wani fahimci mai yake nufi ba yasashi kuma gyara zamansa "Kunsan ance Aure halitta ne mai rai.. Aura masa irin wann Budurwa da na gabatar maku shine zai kashe aurensa da wancan matar da aka k'ulla ta hanyar sihiri. Amma saidai…" Sai kuma yai shiru yana dubansu.

Mommy tace "Saidai mene Malam..?"

Ya zana wani dogon layi tsakiyan guru da laya sai yai crossing "Rayuwa ne a tsakanin mutuwa.."

Mommy ta zaro ido waje "Malam rayuwa tsakanin mutuwa. Inji ba d'a na ne zai mutu ba..?!"

Ya girgiza kansa kad'an "Duk wacce kuka nemo.. Ina nufin duk Budurwar da kuka karya wann asirin dake jikin d'anki da ita zata mutu kaman yanda wancan Auren nasa zai mutu.. Shiyasa na fad'a maku Aure ne amma na watanni uku kacal.. Ita d'in ta riga ta zama MAKARIN ASIRI.. Zata mutu tareda wancan Auren. Shiyasa duk wacce zaku nemo ku sani K'addararta na tsakanin AUREN WATA UKU ne.!"

Mommy da Asshe suka dubi juna. Mommy ta dubi bokan tace "Amma Malam ba yanda za'ayi a karya sihirin sai anyi Auren..? Kuma ni Malam bana so a halak'a kowa wajen ceton nawa d'an.. Dama za'ace ita wancan da tai masa sihirin itace zata mutu ba wacce ta karya sihirin ba ai da kaman sauk'i.. Malam bana son abinda zai ja min farrak'u da nawa mijin dan idan har a k'arshe yasan abunda nayi zai rabu da ni ne rabuwa ta har abada…" Ta d'an mumfasa duk zuciyarta a dame kafin taci gaba "Kuma Malam ni a gaskiya ba ko wace shara zan kawo cikin rayuwar d'a na ta rayu dashi har na tsawon watanni uku ba. Musamman da ka fad'a irin wann budurwar ai ta riga ta zama shara bola juji wanda mutane ke guje mata."

"Duk dalilan da kika lissafo su suka sa ta zama makarin sihirin dake jikin d'anki." Ya bata amsa kai tsaye.

Mommy ta kuma girgiza kai "Kai inaa, shi kansa Haidar na san ba lallai ya amince ya zauna da macen da zan aura masa har wata mu'amala ta gifta tsakaninsu a tsakanin watanni uku.. Yanzu haka ma gaba yake dani toh ta ya zan iya janyo ra'ayinsa har ya amince da wann Auren.?"

Girgiza mata kai yai "Ba wace hanya sai wann hanyar.. Saidai kuma idan zaki hak'ura da d'anki ki sallamasa ma wancan hatsabibiyar.."

Asshe tai saurin girgiza kai "Gafarta Malam gaskiya sharud'an sun mana tsauri da nauyi bana tsammanin zamu iya.. Kar garin neman gira aje a rasa ido. Aunty Kwaise tashi muje." Ta k'arashe cikin k'ok'arin mik'ewa.

Bokan ya dakatar dasu da fad'in "Toh kuwa ku shirya rasa d'anku rashi na har abada.." ya tsaida idanunsa akan Mommy "Ba d'anki kawai ba harta ahalinki da dukiyar mijinki da dik wani abinda kika mallaka kike tak'amada a duniyar nan kaf zaki rasasu domin kuwa kar ki mance na sanar dake ita kanta matar da ta aure d'an naki ta hanyar sihiri ture ce a cikin rayuwarsa. Akwai babban shed'ani a sama wanda shine ummulhaba'isan komai.. Kuma bazai sarara ba sai yaga bayan ahalinki.. Dan k'asa bazata tab'a mana k'arya ba. Allah bamu alheri..!" Mushirikin Ya k'arashe yana k'ok'arin mik'ewa cikin tafiyarsa da yafi yanayi da durk'uso.

Har zai shige cikin wani k'ofa nan cikin bukkan wanda yake kaman shige a durk'ushe tsaban k'ank'ancin k'ofar Mommy tai saurin dakatar dashi "Malam dakata.. Na amince..! Na amince da sharud'anka..! Na Amince zanyi ma d'a na AUREN WATA UKU..! Na amince zan kub'utar da ahalina koda za'a rasa rai..! Na amince zan kashe ko nawa domin na tabbata ban rasa masarautar da na Jima na d'ibi shekaru ina ginawa ba.. Idan irin macen da ka fad'a itace makarin sihirin dake jikin d'a na zan nemota duk yanda ta shiga ta fita.. Idan kud'i zai sayeta zan sayeta dasu domin d'a na da ahalina su tsira..!" Ta k'arashe cikin jaddada kalamanta har wani huci da tururi take fitarwa.

Dattijon ya kaikaito yana duban Mommy. Sai ya kad'a ya dawo da baya da baya ya zauna a mazauninsa. Ya buga k'asan gabansa ya dubi Mommy "Ke da kanki kika zab'i nau'in Budurwar da makarin Asirin da aka jefi ahalinki ta jikin d'anki yake tattare da ita… Kar ki mance dole macen ta cika wann sharud'an idan aka samu sab'ani ko akasi ki sani tashin hankali ne maras misaltuwa biyeda ahalinki."

Ya mik'e cikin tafiyarsa da yafi kama da durk'uso. Ya d'auko wani bak'in ruwa cikin wani k'ok'o mai launin ja. Suka zuba masa idanu yanda yaketa tsifface tsiffacensa cikin ruwan.

(Allah kai mana tsari da b'ata ka tsare mana imaninmu. Ameen).

Har suka baro wajen bokan jimamin abun suke. Ta ya za'a soma neman irin wann matar wacce Auren Haidar ke nufin Ajalinta.? Shin wacece zata sadaukar da rayuwarta dan rayuwar nata d'an ya inganta..? Idan ma sun samu irin wann Budurwar shin Haidar zai amince da ita..? Kai abun da kaman wuya wai gurguwa da Auren nesa. Mommy ta dubi Asshe "Asshe ta ya za'a ce dole sai irin wann budurwar ce lak'anin ke jikinta.. Wai dama ana haka..?"

Asshe ta murmusa "Aunty Kwaise kenan.. Kin mance akan bawa mutum lak'ani na arziki ta irin matar da za'a gindaya masa ya aura.. Wata cewa za'ayi sa'arka na tareda ita shiyasa sai kiga duk yanda irin wann matar take mutum ya tafi ya nemo. Ai a duniyar nan babu abinda ba'ayi.. Fatanmu mu samu irin budurwar da Malam yace cikin gaggawa.

Mommy ta jinjina kai a hankali Tana tsaka da tunanin taji Asshe da driver suna karaton salati. Bata ankara ba sai gani tai mutum kwance gaban motar saman kwalta sun bige wata mata. Tuni Mommy ta fara salallami tana fad'in Driver ya fita ya duba matar da suka bige ko tana numfashi.

**

A b'angaren su Ummul kuwa sun zaga police station kusan guda uku a na hud'u sukayi dace.

Hannayen Ummul rik'e cikin na 'yaruwarta Khulsum wanda k'araffan k'ofan cell ya raba tsakaninsu. Ta kuma share hawayenta tana duban Khulsum.

Khulsum ta girgiza kai kad'an tace "Adda meyasa kika tak'ura kanki wajen nema na..? Wann hukunci na nake karb'a.. Nayi addu'a wa mahaifiyarmu cikin b'acin rai. Nace Allah yasa jami'an tsaro su kamata sai gashi ba'je ko ina ba addu'a na ya dawo kaina. Take naga ishara . Sai na zamto ni ce wacce jami'a tsaro suka Kama.. Lallai na kuma yarda iyaye ba abun wasa bane. Kuma al'amarin su al'amari ne mai girma. Ban tab'a mafarkin zuwa police station ba dukda taran rikici irin nawa sai gashi kausasa harshe da nai Akan Umma yasa nazo police station kuma har gark'ame ni anyi.. Snn 'Yaruwata da muke uba d'aya bama bare ba itace ta zamto Sila.."

Ummul ta jinjina Kai a hankali ta kuma share hawayenta "A littafin Allah mai tsarki wajaje da dama yayi umarni da a kyautata ma iyaye Khulsum. Yazo a hadisin Abdullahi bin Mas'ud yanda yake tambayan Manzo S.A.W wane aiki ne yafi soyuwa wajen Allah. Bayan sallah akan lokacinta sai biyayya ma iyaye ya biyo. Har ila yau matsayin uwa yazo a hadisin Abu Huraira wani mutum ya tambayi manzon tsira S.A.W wanene yafi cancanta yayi kyakkyawan zama dashi.? Manzo S.A.W yace mahaifiyarka. Ya sake tambaya ya sake amsa masa da mahaifiya.. Saida akayi haka sau uku yana cewa mahaifiya kafin a na hud'u yace mahaifi.. Har ila yau Manzo S.A.W ya fad'a cikin hadisin da Tirmidhi ya rawaito cewa ' Yardan Allah na tareda yardar iyaye haka fushin Allah na tareda fushin iyaye.' Kinga Hakan kawai ya ishe mutum ya fahimci girma da k'ima da iyaye ke dashi musamman mahaifiya.. Shiyasa kikaga dukda abubuwan da Umma ke fad'i akaina daidai da rana guda ban tab'a fatan na sab'a mata ba. Sabida ita d'in mahaifiyata ce.. Kuma zanci gaba da mata addu'a har Allah ya fahimtar da ita. Naji dad'i da kika fahimci haka Khulsum. Kar ki damu yanzu zamu tafi kinji.. Zaki fita daga wajen nan." Ta k'arashe da murmushi saman fuskarta.

A can gaban kanta kaw Hisham sai fafatawa yake da 'yansandan dake duty. Sun dage bazasu bada beli ba a cewarsu ba huruminsu bane. Kai da ganinsu kasan wani Abu suke son tatsa jikinsa musamman da sukaga yanayi akwai tattare dashi.

Hisham ya murmusa dan shima ya d'ago jirginsu. D'an matso da fuskarsa yai kafin yace "Officer kenan. Tell me your bank details . Let's settle this once and for all."

D'ayan ya dubi d'ayan "Mai ka maida mu.. Gurb'atattun 'yansanda ko me..? Don't abuse our uniform."

Katsesa Hisham yai da fad'in "Nasan matsalar ka.. Take this.." Ya k'arashe yana janyo hannun police d'in had'ida dunk'ula masa kud'i masu d'an yawa. Gajeriyar murmushi saman fuskarsa.

Gurb'ataccen D'ansandan ya bud'e hannunsa yana duban yawan kud'ad'en take ya shiga washe baki harda sara ma Hisham. Ya dubi d'ayan d'ansandan wanda da gani assistant d'insa ne ya daka masa tsawa.

Take ya k'ame yana amsa masa.

"Maza shige ka bud'eta.."

D'ansandan ya jinjina Kai ya wuce cikin sauri.

Nan da nan aka fito da Khulsum. Tai tsaye tana duban mutumin da ya taimaka aka fitar da ita.

Saidai ganinsu da tai tareda Hajja Fannah yasa tai zaton ko wani nata ne.

Khulsum ta kariso a hankali kafin ta risina ta gaida Hajja Fannah da mutumin da ta gansu tare had'ida masu godiya.

Murmushi saman fuskar Hajja Fannah ta girgiza mata Kai alamun ta daina masu godiya. Ta shiga tanbayan da fatan babu dai abinda suka mata.

Ta girgiza kai tace basu mata komai ba.

Ummul dai duban fuskar 'Yaruwar tata tai da mamakin yanda yai luhu luhu alamun yasha tafi. Tasan duk yanda akai bazai wuce wann 'yarsandar da sukazo suka tafi da Khulsum d'in bane ta mammareta. Batadai ce komai ba tinda Sun samu an fitar da ita. Gwara suyi gaggawan barin wajen kafin su bisu da wani sharrin.

Asibiti suka nufa daga nan wajen Abba. Saida aka fafata da Mama kafin ta bari su Ummul suka shiga wajen Abba. Dan saida Hajja Fannah tai da gaske kafin Mama ta bari. Ya tabbata Umma bata asibiti wajen Abba. Hankulansu ya kuma tashi ga duhun dare da ya riga yayi.

Hajja da Hisham suka kwantar masu da hankali da fad'in za'a sami mahaifiyarsu cikin yardar ubangiji. Hisham yace idan har bata zo asibitin a daren ba zuwa gobe zai filing missing person report ma 'yansanda tinda ma ba'a sanar da cigiya a dokan yansanda sai after 24hrs.

Bayan sunyi sallama da Hajja da nufin dik yanda ake ciki gobe idan Allah yakai rai da abun zasu tashi Ummul ta d'ago ta dubi yaron Hajja Fannah da taji ta kirasa da suna Hisham.. Cikin sanyin murya take masa godiya na taimakon da yai masu musamman da ya kasance zuwansa garin kenan ko hutu bai samu ba matslolint suka tarbesa.

Murmushi saman fuskarsa ya girgiza mata kai "It's nothing. Ki daina min godiya.. I'm glad I helped out.. Ummul-khair."

Yanda ya ambaci sunan nata da wani irin siga sai yasa ta sadda idanunta kad'an.

A d'an daburce tai masa sallama had'ida komawa wajen Khulsum cikin sauri.

Shi kaw kallo ya bita dashi har saida ta b'ace ma ganinsa kafin ya nufi mota yanda Hajjarsa ke jiran karasowarsa.

SameenaAleeyou📚

*AUREN WATA UKU.!*

*12*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Tinda suka koma gida ya gaza samun sukuni. Tunaninta ya addabesa. So yake ya tambayi mahaifiyarsa gameda ita. Sosai yaji yana son sanin labarinta.

A parlor ya tadda Hajja tana had'a wasu kayan d'inkinta. Ya zauna daga gefe.

Ta d'ago ta dubesa "Har kaci abincin kenan..?"

D'an furzar da fuci yai kad'an yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa "Naci Hajja ya isheni.."

Ya d'anyi gyaran murya kad'an yana duban kayyayakin dake gabanta "Wai Hajja har yanzu bazaki hak'ura da d'inkin nan ba. Yanzu fah Allah ya rufa mana asiri I can take care of you , you don't need to do all these things."

Murmusawa tai "Ban raina k'ok'arinka ba Hisham. Amma kasan idan ba idona ne ya tafi ba ko k'arfina ya k'are bazan iya daina sana'ata ba. Sana'ar da na raineka da ita har ka zama abinda kake a yau cikin k'udirar Ubangiji. I love being independent kai kafi kowa sanin hakan."

Ko shakka babu ta tuna masa zamansu a Maiduguri, hardships da suka fuskanta da ma duk wani k'alubale na rayuwa. Ya d'an jinjina kai ba tareda yace komai ba.

Ta kuma d'agowa tana dubansa. Sai ta aje abinda take ta bada hankalinsa akansa sosai. Ta ambacesa da sunansa na yanka. Ya d'ago yana dubanta. Taci gaba "Ni a halin yanzu nafi buk'atan ka gina naka ahalin. Ka haura talatin already. Kayi karatu ka samu aiki mai kyau. Rayuwarka ta inganta Mai kuma yayi saura bayan iyali. Bazan tak'ura maka ba ko na tilasta maka amma ni a nawa tunanin ya kamata ka fara making efforts. Kaga yanda kake tafiya ka barni ni kad'ai d'in nan sai ka barni da abokan wasa."

Ya d'an murmusa dan ya d'ago mai take nufi.

"Toh Hajja ki sama min Matar mana kawai a nan tinda ni dai har yanzu ban samu ba."

Tab'e baki tai tana mai ci gaba da abinda take "Idan na zab'a maka zaka amince da zab'ina ne.. Kasan ku yaran zamani ba'a maku katsalandan a wann sha'ani. Yanzu sai ku ba wa mutum kunya."

Ya kuma murmusawa "Haba Hajjata. Nasan bazaki tab'a zab'a min abinda zai cutar dani ba. So na baki wuk'a da nama."

"Ta d'an kuma tab'e baki "Na Jika dai.. Amma tina kace haka shikenan.. Ka jira kaga.. Next zuwa da zakai zaka tadda iyalinka na jiranka ne.."

Ya d'an zaro ido waje "Hajja ina kika tab'a jin anyi aure Ango bai halarta ba..?"

"Za'a fara akanka tinda Wakili kawai zan tura ya karb'ar maka. I already have someone in mind dama."

Ya d'an fito daga cikin kujeran cikin zak'uwan san jin yaji ko wacece "Da gaske Hajja.. Who's she.. A ina take..?"

Ta d'an dubesa "Idan lokacin yayi ka ganta."

Ya kuma murmusawa kad'an. Shiru kaman babu mai cewa komai sai Hisham yai gyaran murya kad'an "Nikam Hajja nace… Ita yarinyar nan Ummul-khair…"

Hajja ta zuba masa idanu jin yanda yake maganar cikeda kulawa ga wani k'alk'ala na musamman da ya ambaci sunan Ummul dashi "Umhum ina sauraronka." Ta fad'i still tana dubansa.

"Wai dama kun jima da sanin juna ne.. Or do you have any relationship with her family.?"

Hajja ta d'an murmusa " Banda abinka Hisham yanzu ak'alla shekaru hudu fah muke nema a garin nan. Kaga ai ya kamata na saba da mutane kuma idan baka mance ba na sanar dakai ina koyar da sana'ar d'inki ma 'yanmata. Toh Ummul tana cikin d'alibai na."

Hisham ya jinjina kansa a hankali "And she's from around this neighborhood..?"

Hajja ta kuma murmusawa kad'an dan ta lura da curiosity na d'an nata gameda Ummul. Ita idan har abinda take hasashe ya tabbata zatafi kowa farin ciki. Dan Ummul yarinyar kirkici wacce jarabawa da k'alubalen rayuwa sukai marfi ma rayuwar nata.

Gyara zamanta ta d'anyi ta kaikato sosai tana duban Hisham "Naga alama dai tambayoyi ne kazo dasu wann karon.. Amma ka bari har Allah ya wayi gari lafiya kaga yanda ranar yau d'in ta kasance mai tsawo. Idan ka samu ka huta zuwa gobe da safe idan Allah ya nufemu da kaiwa sai na amsa maka duka tambayoyinka.. Maza tashi kaje ka kwanta haka ka huce gajiya kuma. Kaga nima kwanciya zanyi haka nan." Ta k'arashe tana k'ok'arin tattare kayan.

Hisham ya amshe yana linke mata su . Dan yanda ya kwana biyu baya tareda ita d'in nan dik abinda zaisa ya samu albarkanta baya wasa da wann abun komin k'ank'ancinsa.

**

Sassafe Mommy ta fito da zummar komawa Abuja dan dama day trip tayi niyyan yi amma sabida accident da suka d'an samu dole ta bari sai Washe gari bayan an duba lafiyan motar an tabbatar zata iya tafiya.

Ta dubi Asshe "Na bar miki wuk'a da nama amma ki tabbata wacce duk za'a samu tanada futures da qualities da zamu iya jan ra'ayin Haidar dasu in just a short time. Lafiyayya wacce batada wani cutan da zai iya shafan d'ana."

Asshe ta d'an numfasa "Bakida matsala Aunty Kwaise ai kaman yanda kikace ne a duniyar nan babu abinda kud'i bazai sai maka su ba. Ni yanzu damuwata matar da muka bige wacce har yanzu Ke asibiti gashi babu wani means of identification tareda ita balle a samu wani nata."

Mommy tace "Aff kinga ni na mance ma da batun wann matar. Yanzu tareda waye aka barta a asibiti.?"

Asshe tace "Mai aikina Marka ita ta kwana da ita suna can tare yanzu haka.."

Mommy ta jinina Kai dan dama wani private hospital suka kaita "Duk abinda ake ciki dai kin sanar dani. Ni yanzu tafiya ya kamani, dan kinsan na fad'a miki Engr baisan na taho ba shima baya nan ya tafi Lagos tafiyar da ta shafi Kasuwancinsa.. So bani so ya dawo gidan ya tarar bana nan. Anisa ce kawai gidan kinsan kuma yanda take saitin da sauk'i.

Asshe ta kuma jinjina kai "Zakiji komai in sha Allah Aunty Kwaise. Allah ya tsare hanya."

Suna tsaka da sallaman Hilal ya k'araso wajen. Mommy ta dubesa "Bazan amsa goodbye d'inka ba tinda har zaka zo hutu k'asar nan kuma jirginka ya sauk'a a Abuja ka kasa zuwa ka dubani.. Inji kaima kabi sahun d'an uwanka Haidar ne.?"

Hilal matashin saurayi d'a ga k'anwar Mommy Wato Asshe ya d'an murmusa yana shafa kansa. Baifi sati da zuwa Nigeria ba karatu yake a k'asar Cyprus. Ya samu zangon hutu.

"Haba mana Mommy ta kinsan bazan miki haka ba. Tareda Abba da matarsa muka dawo Kano daga Abuja shiyasa. Nasan duk Anisa ce ta had'ani dake. Amma kafin hutuna ya k'are zaki ganni in sha Allah. I still have 2 weeks here."

Mommy ta murmusa "Toh shikenan sai na ganka.. Ina nan Ina zuba ido."

Hilal ya murmusa yana tabbatar mata zaizo. Ya nufi wajen driver yana tambayarsa hope motar bata samu matsala ba.

Mommy ta dubi Asshe ta d'anyi k'asa da murya "Oh kiji min Hilal wai Abbansa da matarsa. Kinji yaro na taya mahaifiyarsa kishi."

Asshe ta tab'e baki "Yo yarinya ce k'arama Anisa ma ta fita Kinga kuwa yaushe zai wani bata matsayi."

Mommy tai yar bazawarar dariya "Allah ya rufa asiri dai bai had'eku gida d'aya ba dan nasan da sai an kwashi 'yan kallo tsakanin yarinyar da Anisa wataran."

Asshe ta kuma tab'e baki "Ai Anisa gaba take da Uban nasu tinda yayi wann jarababben Aure. Sun had'e kai da sauran 'yanuwanta 'yanmata yaran uwar gidana suna gaba da ubansu ya auro sa'arsu. Shiyasa ma bata cika son zaman Kano yanzu ba tafi son zama can Abuja wajenki to avoid seeing her father here."

Mommy tai shiru tana tuna case d'in dake nata gidan. Ta d'an numfasa "Gwara su idan sunyi gaba da Ubansu sunada dalili." Tai maganar tana k'ok'arin shigewa mota suna kuma sallama da 'yaruwarta.

Kasancewar fitan sassafe tayi yasa ta samu isowa da wuri. Tuni tasa ma'aikata an soma dafe dafen abincin da za'a tarbi Daddy dasu.

Suna zaune shida ita a parlor bayan ya ida cin abinci magazine rik'e cikin hannunsa yana dubawa.

Mommy dai sai digesting maganganun da boka ya sanar da ita take. Ta rasa ta yanda za'ayi ta soma sanar da mijinta batun. Toh ma mai zata soma sanar dashi. Cewa d'ansu yayi Aure ba da saninsu ba.? Kodai mugun asirin da aka jefesa dashi.? Ko kuma auren da Malaminta yace a masa wanda shine makarin sihirin. Ta ina zata faro. Tana tsaka da tunanin kaman wanda aka jefo sa suka sinkayo sallamansa.

Yau Mommy ta rasa duban tausayi take masa ne ko duban sakacinta akansa.

Kallo d'aya mahaifinsa ya masa ya watsar.

Ya k'ariso hannunsa rik'eda shud'in Folder mai d'aukeda logo na Kampanin mahaifinsa jiki Wato (MB).

Gaisar da iyayen nasa ya soma yi daga nan yanda yake tsaye bayan kujera dan yasan he's always not welcome. A gidan da ya kamata ya kira da home.

Mommy ce ta amsa gaisuwarsa yau d'in da sakin fuska. Ga wani mugun sanyi da tayi. Mahaifinsa kaw bai samu zarafin amsa masa ba.

Mommy ta d'anyi murmushin da yafi kama da yak'e tana duban mijin nata da kacaukam hankalinsa Ke bisa Magazine d'in dake hannunsa. Wani article ne ya d'auki hankalinsa yanda aka rubuta 'FG to approve the billion dollars bridge project to Maitama Builders.' Project din da Haidar keta fad'I tashi akai ganin an zab'esa matsayin Project Manager.

Mommy ta d'anyi gyaran murya "Engr Haidar na gaidaka."

Har lokacin idanunsa naga magazine d'in "Na ganshi ai.. Sai ya fad'i abinda ya kawo shi. Yai maganar ko kallon yanda Haidar yake baiba.

Haidar ya had'iyi bak'in cikin da ya tokare masa mak'oshi.

Mommy dai gaba d'aya jikinta a sanyaye yake yanzu tinda Malaminta ya sanar da ita abinda Ke faruwa. Ya zama dole ta bada himma wajen had'in kan ahalinta bazata bari azzalumai suyi nasara akansu ba. Ta dubi Haidar wanda ya kafe mahaifina da ido kaida gani kasan ba kallon komai yake masa ba face tsana. Ta k'ak'aro murmushi "Haidar you heard your Dad.. Ka shigo ka gabatar masa abinda ya kawo ka nasan ya shafi aiki tinda ga company's folder hannunka.

Bai dubi Mommy ba tinda dukansu haushi suke basa ya k'arasa yanda mahaifinsa yake. Ya aje folder d'in gefensa kad'an "This is the new proposal my team and I have been working on.. It contains all the details, the construction deliverables.. The scope and budget of the project.." Ya d'anyi fasali jin bai amsa sa ba kafin yaci gaba "You..can go through it and see, before we present it to the board of directors.."

Har lokacin bai amsa sa ba. Kaman ba dashi yake ba haka Daddy yayi. Haidar ya kuma had'iyan k'uncinsa. Duk abinda mahaifinsa zai masa akan wann project d'in ya zama dole ya shanye. Alk'awari yayi sai yasa mahaifinsa ya cinye duka kalamansa. He never backs down. He must fulfill all his promises. Zai wanke kansa zai kuma sa mahaifinsa ya cinye kalamansa sann daga k'arshe he will personally take the company down to the ground. To the last kobo. Ya ranste sai ya tarwatsa mahaifinsa da kansa.

Sai matse file d'in yake cikin hannuna jijiyoyin jikinsa na kuma tashi kaikace ketata zai.

Readers Also Read