Auren wata ukku by sameena - Chapter 6
Auren wata ukku by sameena Chapter 6: Auren wata ukku by sameena Chapter 6. Khulsumu ta k'araso ta rungume mahaifiyarta. Cikin rawar murya take furta "A'a…
4,500 words
Khulsumu ta k'araso ta rungume mahaifiyarta. Cikin rawar murya take furta "A'a Umma duk abinda ke faruwa tuntuni rubutacce ne.. Allah ya nufa hakan dole sai ya kasance.. Wann itace k'addaran ahalinmu.. Auren Adda Ummul kuma ko ya Faiz na raye ko baya raye bazai tab'a faruwa ba sai lokacin da Allah yaso. Umma kiyi k'ok'ari kiyi tawakkali da sannu Allah zai kawo mana mafita kinji Umma ta… In sha Allah Abba zai samu lafiya kuma farin ciki zai dawo cikin ahalinmu da izinin Allah.!"
Umma ta rungume 'yar tata kuka na kuma kufce mata.
Tamkar wacce aka sinkara haka Umma ta janye jiki daga na khulsum. Ta shiga girgiza Kai tana duban Khulsum d'in "Yaya tayi gaskiya Khulsumu, Anya ba wani mugun k'addara bane yake bibiyan 'yar uwarki..? Meyasa Fa'iz ya Mutu kafin yakai ga aurenta.? Meyasa tin bayan da Fa'iz ya bar duniya duk wani maneminta basa kaiga aure maganar ke watsewa.. Shin Anya ba alak'ar Ummulkhairy da Fa'iz bane yai Ajalin Fa'iz..? .. Anya ba wann dalilin bane ya raba tsakanin 'yan uwa biyu..? Ina nufin mutuwar Fa'iz shine ya raba tsakanin Mahaifinku da 'yaruwarsa.. Anya ba Ummul ce tayi sanadin Fa'iz ba.?!"
SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU.!*
*09*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Saurin rik'e bakin Umma Khulsum tai tana girgiza Kai "Haba Umma wace irin magana ce wann.. Umma magana kike fah kaman bakiyi imani da k'addara ba..Umma na zaci ciwon Abba ya dawo dake hayyacinki daga wann rashin tawakkalin.. Haba Umma saikace ba musulma wacce ta yarda da k'addara ba.."
A zafafe cikin zuban hawaye Umma ta katseta "Ki gaya mun cikin abunda nace wanne ne ba haka ba..?! Ki gaya mun Khulsum..!" Taci gaba da kuka mai sauti tana girgiza Kai "Bak'in K'addaran Ummul shine yai ajalin D'an 'yaruwar mahaifinku Fa'iz..! Bak'in k'addaran Ummul shine ya raba tsakanin mahaifinku da 'yaruwarsa.! Bakin k'addaran Ummul shine ya jefa mahaifinku halinda ya tsinci Kansa ciki..! Bak'in k'addaran Ummul shi yake sa ko wani namiji ya guje ta..! Bak'in k'addaran Ummul shi ya jefa ahalinmu cikin yanayin da muka tsinci kawunanmu ciki..!"
Kaman daga sama sukaga Mama ta d'age labulen parlorn. Ta jinjina Kai tana duban Umma "Na gode ma Allah da yasa kika furta duka wad'ann da bakinki Suwaiba.. 'yarki Ummul itace tai sanadin Fa'iz.. Yaron kirki aka lik'a masa annoba aka rabasa da rayuwarsa.. Toh wllhi kinji na ranste Miki da Allah bazan bari 'yarki ta kuma kusantar mijina ba balle ta lashe nasa kurwan.. Kai kaf d'inku babu mai kusantar min miji.."
Khulsum dake faman sakin huci goge hawayen dake kwance saman fuskrta tai ta k'araso gaban Mama "Wllhi wllhi banga Wanda ya isa ya hanamu ganin mahaifinmu a asibiti ba.."
Badia ce ta k'araso ta tsaya gaban mahaifiyarta tana murmushi tana duban Khulsum dake ci gaba da sakin huci. Lokaci guda ta d'ago hannunta dake rik'e da wayar salulanta. Take tai playin recording d'in muryar Umma da tai sanda take fad'in Ummul ce tai sanadin mutuwan Fai'z harma da ciwon mahaifinsu. Tana gama playing suka kuma sakin murmushi itada Mama. Mama taci gaba "Ko Kotu aka tafi wann kad'ai ya ishemu shaida… Badia shige mu tafi wajen mahaifinku.." Daga haka sa Kai sukai zasu shige Khulsum ta yunk'ura zatabi bayansu Umma tai saurin dakatar da ita tana girgiza Kai hawaye na fita mata dan kukan nata ya daina fita da sauti.
Khulsum ta dubi Umma. Ta rasa k'unci ne ko takaicin mahaifiyar nata ne k'unshe cikin Zuciyar "Haba Umma.. Haba Umma, kinga ga irin abinda nake fad'a Miki.. Yanzu makirar matar nan zatayi amfani da wann damar ta iya cutar da mahaifinmu.. Umma dan Allah wai sai Yaushe zaki daina maganganu marassa kan gado fisabilillahi.. Umma a gabanki matar nan da yaranta suke lissafin mai Abba zai Mutu ya bari. A bayyane take so suke mahaifinmu ya Mutu.. Umma mai zai faru idan sukai amfani da wann damar suka k'arasa mahaifinmu dake kwance gadon asibiti.. Umma kin cuce mu wllhi idan Mama da yaranta suka k'arasa Abba ba kowa ne Sila ba face ke.!"
A guje Umma tabi bayan su Mama tana rok'onsu su rufa mata asiri kar sukai ma hukuma muryarta da Badia ta nad'a cikin wayarta.
Takaici ya kuma Kama Khulsum dan tasan yanzu Mama da 'yarta Badia Sun samu makamin shashantar da Umma dole su tilasta mata yin duk abinda suke so musamman da sukaji tana tsoron wai sukai recording d'in da Badia tai ma hukuma. Khulsum ta bud'e murya tana kiran mahaifiyar tasu. Lokaci guda take furta "Umma ki bi bayansu su Kai ki ma hukumar kinga 'Yaruwata ma ta huta da muggan kalaman da kike jifanta dasu duk wayewar garin Allah.!"
Tau!!! Taji sauk'an mari saman k'uncinta. Ta d'ago da mamaki tana duban Ummulkhairy data d'auketa da Marin. Lokaci guda take furta "Shin Kinsan girman mahaifiya Khulsum..! Shin Kinsan matsayin mahaifiya..? Shin Kinsan darajarta Akan 'ya'yanta..?"
Cikin huci Khulsum take duban Ummul lokaci guda take furta "Akan na fad'i gaskiya shine zaki mareni.. Mahaifiyarmu tana buk'atar mai tunasar da ita.. Mahaifiyarmu tana buk'atan mai nusar da ita..!"
"Ya isheki Khulsum.!" Ummulkhairy ta dakatar da ita kafin taci gaba "A haka ne zaki nusar da ita kina d'aga mata murya kina fad'in ta cucemu mu 'ya'yanta har Kina cewa taje hukuma su kamata.. Mahaifiyarki Khulsum.?!" Tai birki tana girgiza Kai tana duban Khulsum cikin rashin yarda "Mahaifiya ce zaki fad'a mata haka.. Ina karatunki na islamiya ya tafi..? Kin mance cewa ko nasiha za'a ma iyaye cikin kwantar da murya da lallama ake. Kin mance k'issan bawan Allah Junaid da ya keb'e kansa a wajen gari yana bautan Allah. Mahaifiyarsa tazo ta kirasa yana ibada bai amsa ba. Akai haka har sau uku a na uku tace Allah ya had'asa da sharrin 'ya mace daga k'arshe wann bawan Allah saida ya had'u da sharrin mace. Karuwa taje tai . Bayan Allah ya wanke shi daga sharrin karuwa da ya fad'a . Daga baya mahaifiyarsa ta fad'i cewa wann bakin da tai masa shine ya kamasa.. Kinga darajan mahaifiya dukda ba sab'on Allah yake ba bautan Allah yake saida bakinta ya bisa saida yai tasiri akansa.. Wann itace Uwa Khulsum.. Ba'a wasa da al'amarin iyaye.."
Khulsum ta jinjina Kai tana hawaye "Na yarda Miki 'Yaruwata.. Shin koda ace mahaifiyarka zata apka ma b'ata sai ka k'yaleta..? Ummul sanin kanki ne rayuwar Umma akwai gyara cikinta.. Sanin kanki ne Umma bata yarda da k'addara ba.. Shin bakiji yanda ta d'aura alhakin komai akanki ba har Mama da yaranta suka sami hujja.. Ummul rayuwar mahaifinmu na cikin had'ari a wann gab'ar dole na nusar da Umma kuskuren ta.."
Cikin sanyi jiki Ummul ke duban Khulsum. Sai kuma ta girgiza Kai tace "Watak'ila gaskiya Umma ta fad'a.. Itace ta haifeni.. Tafi kowa sanina.."
Khulsum ta k'araso ta dafa 'yaruwarta "Ubangijinki da ya halicceki yafi kowa saninki 'Yaruwata.. Dan Umma tana mahaifiyarki bai zama hujja akanta ta dinga kausasa harshenta Akan k'addararki ba.. Sabida Dani dake da Umma dama duk wani mahalik'i bamuda ikon canza k'addararki.. Allah shi yake k'addara rayuwar mu yanda yake so ya kasance.. Iayakacin namu shine addu'a Allah yai mana tsari da k'addara mai muni.. Ki daina kuka 'Adda Ummul.. Da sannu Ubangijinmu zai daidaita mana al'amranmu ya kuma bawa mahaifinmu lafiya.. Kuma na Miki alk'awari zan bawa Umma hak'uri nai mata nasiha cikin lallama da kwantar da murya." Sai suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi da tsuma zuciya.
Shiru shiru Umma bata dawo cikin gidan ba. Ummulkhairy tace subi bayan Umma su dubata.
Koda suka fito ma wayam basuga Umma ba. Ummul da Khulsum sukai tsaye suka jimami.
Khulsum tace "Kar dai Umma tabi su Mama ne..? Mai zai faru yanzu Adda..?"
Ummul ta rasa abin fad'i. Sukai tsaye suna duban mutane masu giftawa.
Daga can nesa suka hango mashin d'in mijin Azeema ya nufosu ga Azeema zaune d'amas saman babur d'in.
Suka k'araso sukai parking. Ta dafe shi ta sauk'o sai karairaya take "Yauwa Habibi, da alama mun kusa mallakan mota dan na gaji da babur din nan. Kar ka damu na maka alk'awarin da an bani kaso na na gado zan biya maka duk bashin da ake binka..!" Ta k'arashe tana aikawa su Ummul wulak'antaccen kallo.
Khulsum ta dubi Ummul mamaki kwance saman fuskrta. Wai mahaifin su ke kwance gadon asibiti Azeema ke wann maganar. Daga ita har mijin nata kaman sunga kashi haka suka dubi su Ummul.
"Habibi bara na shiga na fito da kaya na mu tafi tinda mun hadu da Mama a hanyar asibiti." Azeema tace bayan ta dira daga bayan Babur d'in. Haka ta k'araso ta shige ta gaban su Ummul tana watsa masu wulak'antaccen kallo.
Khulsumu tai saurin Shan gabanta "Adda Azeema kinga Ummanmu tareda Mama ne.?"
Azeema taja tai birki tana watsa ma Khulsum banzan kallo "Ajiyanta kika bani da zaki tambayeni ko na ganta..?"
Ummul ta girgiza Kai cikin sanyin muryarta tace "A'a Azeema gani mukai ta biyo bayan Mama kuma munji kince kin hadu da mama a hanya Shiyasa muke tambayarki.."
"Mahaukaciya ce ita ko k'aramar yarinya ce ita..! Tinda ku kanku kunsan cewa mahaifiyar taku b'elb'el ce sama Sama ce sai ku nemi igiya ku d'aureta a gida ko ku Sakata a turu maganin hauka…" Kafin takai aya taji saukan tagwayen maruka d'aya bin d'aya.
Azeema ta malmalo wani ashar tana duban Khulsum dake sakin huci wacce itace tai Marin.
Cikin huci Khulsum taci gaba "Baa haifi wacce zata ci mutuncin mahaifiyata na barta ba bari kiji na fad'a Miki..!"
"Ni kika Mara Khulsumu.. Toh wllhi yau idan baki kwana cell ba wllhi ba sunana Azeema ba.. Dan uwarki Suwaiba sama sama daga kaina kin gama rashin kunya..!" Ta k'arashe tana ihu tana k'walla kiran Habibi..
Kan kace me mutane sunyi caa a wajen.
Babu shiri Mijin Azeema ya ko k'araso yana fad'in wllhi baiga ballagazar da zata marar masa mata ya barta ba. Fad'i yake wllhi sai ya d'aure Khulsum.. Kan kace mai ya d'ale mashin d'insa ya bar wajen.
Ummul sai kuka take tana rok'on Azeema tai hak'uri ta bari suji da ciwon mahaifinsu da kuma b'acewar mahaifiyarsu.
Azeema kaw sai tsalle take tana jijjiga tana fad'in wllhi yau bataga uban da ya isa ya hanata d'aure Khulsum ba.
Bakin Khulsum bai Mutu ba fad'i take wllhi Azeema ta kuma gigin zagar mata mahaifiya sai ta k'ara mata da wasu marukan. Kuma idan ta haifu kar ta fasa rufeta a gidan yari.
Wasu daga cikin 'yan gidan masu goyon bayan Azeema sai dad'a ingizita suke. Wasu kaw cewa suke Ummulkhairy da 'yaruwarta kullum cikin jaza masu fitina suke. Idan kaji ana bala'i da rikici a gidan toh ba kowa bane face su biyun.
Allah sarki Ummulkhairy idan ka ganta dole ta baka tausayi. Jim kad'an motar police ya k'araso tafiya da Khulsum.
Mijin Azeema na gaba yana fad'in idan zai kashe k'arshen kud'insa sai ya k'watarwa matarsa hakkinta.
Ummul kaw ganin za'a tafi da 'yaruwarta da gaske ya sanyata saurin k'arasawa tana rok'on Habibu mijin Azeema da yai hak'uri ya taushi Zuciyar Azeema ko dan halinda mahaifinsu ke ciki a asibiti.
Haka akai ayari anai masu rakiya yayinda wata 'yarsanda ta tasa k'eyar Khulsum zuwa cikin motar su.
Ummul ta kamo 'yaruwarta tana kuka shar shar tana rok'onsu dan Allah su k'yale mata 'yaruwarta.
Sergeant d'in ta bige hannun Ummul tana tsawa wa Khulsum ta shige mota.
Azeema da mijinta suka d'ale babur suka take masu baya.
Durk'usawa Ummul tai a wajen wani irin marayan kuka ma taso mata. Hannayenta biyu ta d'aura akai jikinta kaw har wani irin rawa yake. Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un..! Wann wani irin jarabawa ne.. Wani irin iftila'in rayuwa suke gani.. Ba'a gama da wann ba a fad'a wann..! Ta rintse idanunta hawaye na kuma ambaliya a fuskarta. Da wanne zata fara mahaifinta dake kwance asibiti.? Mahaifiyarta da bata san ina ta tafi ba.? ko kuwa 'yaruwarta da aka tafi da ita police station.? "Hasbunallah wa ni'imal wakil..! Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifli khairan minha..!" Ta furta cikin tsananin rawar murya. Ta mik'e tamkar zautacciya tana Neman ta hanyar da zata nufa.
Batasan ina take tafiya ba k'afafunta kawai take jefawa. Bata tsinci kanta a ko ina ba sai gidan Hajja Fannah.
Da tsananin mamaki Hajja Fannah ke duban Ummulkhairy wacce ko magana bata iya yi.. Hajja Fannah tai saurin kamo hannun Ummulkhairi "Subhannallahi Ummul meke faruwa..?"
Ummul bata iya amsata ba saima kifa kanta da tai cikin jikin Hajja Fannah marayan kuka na taso mata.
Hajja Fannah ta rungumeta sosai cikeda tsananin tausayinta. A haka suka nufi cikin gidan.
Ta zaunar da Ummul saman kujera wacce ta koma tamkar mutum mutumi bata um bata um um sai hawaye dake ci gaba da gangarowa saman kumatunta.
Hajja Fannah ta mik'e da zummar kawo mata ruwa ganin ta mata tambayar duniya kan ta sanar da ita meke faruwa ta kasa. Idanunta suna kafe waje guda sai zuban ruwa da suke.
Amma koda ta kawo ruwan ma kasa sha tai har lokacin idanunta na duban b'angare guda ga hawaye na kwaranyo mata. Hajja Fannah ta kyaleta bata tak'urata ba har saida suka d'ibi lokaci a haka kafin Ummul ta soma fad'in "Komai ya hargitse, sunce ni ce sila.. Sunce bak'in k'addarata da haukan mahaifiyata shi yai sanadin ciwon mahaifinmu.. Hajja Umma ta tafi bansan ina ta tafi ba.. Abba yana asibiti amma sun hanani ganinshi.. An.. An kama Khulsum… Tana ofishin 'Yan sanda..!" Sai tai boasting cikin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Hajja Fannah ta d'an kauda fuskarta tana matsan k'wallan da suka cika idanunta. Ta jinjina kai a hankali tana shafa bayan Ummul alamun kwantar da hankali "Yi kuka Ummul.. Kukan zaisa kiji relief…"
Saida ta bata lokaci tana kukar da abinda ke k'unshe k'irjinta kafin tai gyaran murya "Let them say whatever they want. Su fad'i duk abinda suke so. Amma koda wasa kar kiyi abinda zaija miki matsala a rayuwa. We are all human beings, kuma Allah ya haliccemu daban daban. Level of tunaninmu bazai zama daidai da juna ba. Ko a makaranta ne cikin aji d'abi'un yara da halayyarsu ya banbanta. Akwai yaron da kana koyar dashi abu bugun farko ya d'auka. Wani kuma sai anyi da gaske ya gane. Akwai fast learners akwai slow learners. Malaman makaranta da suke koyar da yara suka san d'abi'unsu su zasu fad'a miki wann. Akwai yaran da suke fuskantar wani ciwo da iyayensu ma basu san suna dashi ba kaman irinsu Attention deficit hyperactivity disorder (ADHD). Sai kiga a gida anata jibgan yaro ace jaki ne baya son karatu baya gane karatu wanda ba haka bane ya samu d'an wani matsala ne da idan aka tafiyar dashi sannu a hankali yanda yake d'in idan abun ba mai tsanani ne sosai sai kiga ba sai anje ga ganin likita ba. Wata uwar fah da kanta take abusing d'an da ta haifah ko ince wasu iyayen. Kar kice d'an rik'o ko goyo a'a D'an suka haifa zasuyi abusing a nasu tunanin wai soyayya suke masa. Wani yaron tsananin matsi da tak'ura da tsanani shi yake traumatizing d'insa. Kiga uwa ta dasa ma yaranta tsoronta. Yes ta haifar da fair tsakaninta da yaranta duk wai ita a dole tarbiya take masu batasan ta kashe kanta bane a staye. Bai jima ba na gani da idona ba jiyau ba wani yaro yayi hanging kansa sabida tsoron yayi laifi. Kuma kar kice wani babban laifi a'a minor laifi ne amma sabida tsoronta da ta haddasa masa yasa ya d'auki rayuwarsa. Toh kinga dik ire iren wad'nn sukan haddasa ma yaro ya dinga wasu d'abi'u kaman na mai tab'in hankali tin yana k'uruciya har kawo girma. Ba'ace kar ka tsawatar ma yaranka ba amma idan aka tauna sai a d'an sake haka shi yaro yake. Sann ire iren wad'ann cututtuka na kwak'walwa akwai mutanen da dama manyan mutane da suka zama madubi ga al'umma sun fuskanta a lokacin k'uruciya idan kika bibiyi tarihinsu kafin nasarorinsu. . Akwai mutane masu special needs cikinmu 'yanadam. Mutanen da suke buk'atan kulawa ta musamman. Ba zallan wanda muke ganinsu da nakasa ta zahiri a fili ne suke buk'atan taimako na musamman ba. Wato mutane masu disability da muke iya gani mu tantance. Akwai wasu d'abi'u da zaki kula mutum nayi wasu lokutan kaman d'an tab'in k'wak'walwa. Abun minor ne baiyi tasiri a jikinsa ba. Idan aka ja yaro jiki ko mutum mai irin wann matsalan ka tafiyar dashi yanda ya dace sai kiga abun yayi sauk'i ba sai an kaiga neman magani ba. amma mutanen da suke rayuwa dasu sai susa abun ya girma har ya koma kaman hauka. Sai kiji ance miki mutum ya koma hauka tuburan. Mutane suna hantaran shi mutum mai irin wann matsalan. Ko kiga daga an ganshi sai a fara dariya ana manna masa hauka. Mutane suna kiransa da sunaye barkatai Wawa, a'a shashasha lusari maras hankali. Dama k'wak'walwar nasa da gaske akwai d'an matsala sai kiga yayi giving up ya yarda da abinda mutane ke fad'a akanshi sai kiga ya fara abu irin na masu tab'in hankali. Irin wad'ann sune mutane masu Emotional and mental health needs. Wasu zaki samu through life experience suka had'u da wann matsalan. Wasu zaki samu stress ne ya maidasu haka. Some have history of abuse musamman idan cin zarafin da suka fuskanta a lokacin k'uruciya ne. trauma or neglect. Wasu an wofantar dasu. Dik suna contributing kiga mutum ya samu wann Matsalar. Wasu kuma biological factors ne ma'ana gadon cutan sukai ko kuma dai cuta ne kawai daga Allah. Amma a matsala irin na mahaifiyarki zai iya zama Desperation na ganin ta aurar dake ko ta halin k'ak'a zai iya haifar mata wann matsalan kinga kuma rashin tawakalli da karban k'addara yanda tazo ma Bawa ya shigo ciki. A akasarin lokuta desperate individuals sukanyi wasu bubuwa wanda normally thinking person bazai fahimta ba. Because they are desperate sukan aikata wasu abubuwa da yafi kama da hauka or illogical. A wasu lokutan Yakan sa mutum ya cutar da kansa har ma yakaiga yayi yunk'urin kashe kansa."
Ummul ta dubeta sai ta tuna sanda Umma tai yunk'urin fad'awa rijiya zata kashe kanta dikdai sabida k'addararta.
Muryar Hajja Fannah ya dawo da ita "Ni ba likita bace sann kuma ban karanci halayyan d'an adama ba. Ina fad'a miki wasu abubuwan ne base on experience. Ni uwa ce da ta raini d'anta ba uba. Mun fuskanci k'alubale da dama a baya wanda yasa na zama exposed da ire iren matsalolin nan.." Ta d'an numfasa kafin taci gaba "Ko ma wanne matsala mahaifiyarki ke fuskanta Ummul kija mahaifiyarki a jiki. Kar ki tab'a hantararta koda ta kasance mai tab'in hankalin ko shashasha kaman yanda mutane ke fad'i. Iyaye ko a bola suke yawo iyaye ne. Allah yakan k'addari rayuwar wasu cikin rayuwarmu domin ya zame mana jarabawa. Kibi umarnin Allah kiyi mata biyayya cikin abinda babu sab'onsa. Kiyi k'ok'arin tafiyar da ita yanda take d'in. Na tabbata ko haukan ne, ko ganganci ne ko ma menene Allah bazai tab'a bari ki tab'e ba matuk'a kin fawwala masa lamiranki kuma baki fasa addu'a da neman zab'insa ba." Ta kuma kamo hannayenta "Dik tsanani yana tare da sauk'i. Inada yak'inin Umma ba b'acewa tai ba. Khulsum zata dawo gida Abba kuma zai samu lafiya cikin yardar Ubangiji. Tashi muje ba zama zamuyi ba."
Suna k'ok'arin mik'ewa sukaji sallama.
Hajja Fannah tai birki tana dubansa. Tilon d'anta da aiki ya rik'e mata shi can birnin tarayya.
Bai kulada budurwar dake zaune gefe saman kujera ba ya k'araso ya rungume mahaifiyarsa yana fad'in yayi kewarta.
SameenaAleeyou📚
*AUREN WATA UKU..!*
*10*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Sautin kukan Ummul dake fita a hankali ne ya d'auki hankalinsa. Ya d'an kaikaito yana dubanta. Kanta a kife saman gwiwoyinta.
Ya maida dubansa ga mahaifiyarsa "Hajja wacece wann..?"
"Kaga Hisham jeka aje jakanka. Zuwa kai akan gab'a daidai lokacin da nakeda buk'atan hakan dikda zuwan ba zata ka min."
Zai kuma magana ta shiga turasa tana fad'in "Kaje kawai ba lokacin bayani bane yanzu.. Allah yasa da motarka kazo."
Ya jinjina mata kai yana mai nufan hanyar d'akinsa. Yana tafe yana waigowa yana duban Ummulkhairi da har lokacin kanta a kife yake.
Fitowan Hisham yai daidai da mik'ewarsu tsaye. Yai mutuwan tsaye yana kallon budurwar. Fuskarta fayau alamun kuka da damuwa. Bai tab'a ganinta tareda mahaifiyarsa ba balle yayi tunin ko 'yaruwarsu ce. Danginsu ma gaba d'aya ai suna Maiduguri so baya tunanin 'yaruwar mahaifiyarsa ce.
Yai tsaye daga gefe yana sauraron mahaifiyarsa dake kuma kwantar ma budurwar hankali.
Agogon hannunsa ya duba yaji ana kiraye kirayen sallar la'asar. Ya d'anyi gyaran murya wanda yasa Hajja juyowa tana dubansa. Sai ta maida dubanta ga Ummul tace "Yanayin kinnan anya ma kuwa kin saka wani abu cikinki Ummul."
Girgiza mata kai tai. A hankali cikin Sanyin muryarta ta furta "Kiyi hak'uri Hajja na k'oshi bana jin yunwa. Bazan iya cin komai ba."
Hajjah Fannah ta fahimceta dan wani tashin hankalin ya wuce gaban komai. Dafata ta d'anyi "Maza shiga d'akina kiyi sallah. Zan shigo na sameki."
Ta jinjina mata kai tana mai shigewa jiki a sanyaye.
Hisham ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta har ta shige. Ya rage daga shi sai mahaifiyarsa. Ya d'an bud'e hannayensa yana d'aga gira kafin tai masa tayin abinci "I'm still full.. Don't worry about me." Ya shiga nuna k'ofan d'akin yana tambaya a hankali "Hajja who is she..?"
Kunnensa guda ta kamo ta shiga janyosa tana fad'in "Ban gama da kai ba zaka sanar dani dalilin da ya hanaka sanar dani kana tafe."
Ya d'an saki k'ara yana k'ok'arin dafe kunnensa "Yi hak'uri Hajjata.. Idan na sanar dake kuma ai bai zama bazata ba."
Ta murmusa tana dubansa. Su duka biyun duban juna suke cikeda shauk'i "Watau dai bazaka daina min bazata ba. Kaidak bazaka girma ba."
Ya murmusa "Na jima wann karon banzo na ganki ba shiyasa." Suka soma sabon gaisuwa Hisham na kuma tambayarta wacece wann budurwar.
Ta d'an dubesa "Naga alama ka k'agu kaji ko wacece ita. Yanzu dai kaje kayi sallah police station zaka kaimu.."
Ya d'an dakata da nad'e hannun rigarsa da yake "Hajja police station kuma.. Meke faruwa ne wai.?"
Ta d'an lumshe idanunta had'ida furzar da huci "Je kayi sallah Hisham."
Ya jinjina mata kai kafin yasa kai ya fice yana tunanin mai zaikai mahaifiyarsa ofishin 'yansanda.
A natse take sanar da Hisham abindake faruwa game da kama 'yaruwar Ummulkhiairi da akayi. Mahaifinta dake kwance gadon asibiti ga kuma mahaifiyarta da suke tsammanin b'acewa tai. Saidai bata sanar dashi sanadin faruwar komai ba. Tinda ba huruminsa bane. Wann ma dole ne ta sanar dashi.
Hajja ta mik'e "Jiramu a waje muna fitowa. Barin duba Ummul d'in." Ta fad'i tana nufan k'ofan d'akin da Ummul ke ciki.
Ta tadda ta ida sallar. Ta linke abin sallan kafin ta dubi Hajja dake tsaye tana jiranta. Hajja ta sakar mata murmushin k'arfafa gwiwa kafin ta sanar da ita bak'on da ta gani D'anta ne dake aiki can Abuja. Yazo hutun aiki ne. Yanzu haka yana waje yana jiransu zai kaisu police station ayi belin Khulsum sann ayi filing report na missing person idan har b'acewa Umma tai.
Ummul ta jinjina kai a hankali tana ma Hajja Fannah godiya. Hajjah Fannah tace ta daina mata godiya ita 'ya ta d'auketa.
Koda suka fito Hisham na tsaye jikin motarsa yana waya. Sam ita bazama tace ta iya tantace shi ba dan har lokacin ba wai ta dawo cikin hayyacinta bane. Karfin hali ne Kauai. Tasha jin labarin ana cewa Hajja Fannah nada D'ah saurayi amma baya zama garin kano zuwa yake lokaci zuwa lokaci domin ya duba mahaifiyarsa. Duk zuwa gidan da take bata tab'a arba dashi ba sai wann karon.
Back seat Hajjah Fannah ta bud'e mata ta shige yayinda ita Hajjar ta shige mazaunin mai zaman banza gefen d'anta.
Suna tafe saman kwalta suna kowa yayi jigum jigum. Hisham bai saba zama haka shiru da mahaifiyarsa ba. Zai iya cewa they are best of friends shida mahaifiyarsa sabida tsananin shak'uwa dake tsakaninsu. Yau d'in duk sai yaji babu dad'i. Sai ya sata kallon Ummul ta cikin mirror yanda ya hangi Siraren hawaye basu daina sauk'a saman k'uncinta ba.
Ji yai ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta. Rabin hankalinsa naga kwalta rabi naga Ummulkhairi.
Hajja Fannah takai dubanta ga mirror yanda Hisham ke satan kallon Ummul. Bata kuma cewa komai ba sai d'an sauk'e ajiyan zuciya da tai. Sosai yarinyar ke bata tausayi.
** Lexus ce bak'a wul taketa kutsawa cikin k'ungurumin daji. Kai da gani kasan ba lafiya ba kaga motan manyan mutane irin wann na ratsawa cikin daji.
Saida sukai tafiya mai nisa daga bakin kwalta zuwa wani k'ungurumin k'auye da yake tsakiyan daji kafin Mommy ta juyo ta dubi driver dinta tace ya fita ya basu waje zasu tattauna. Driver yai yanda Mommy tace. Juyowa tai tana Duban k'anwarta Asshe dake zaune gefenta cikin motar "Asshe kin tabbata aiki yakeyi mai kyau..."
Asshe ta murmusa "Aunty Kwaise kenan. Ni ina zama ya ganni kishoyoyi sun sakani tsakiya. dole na kutsa nasan duk wani malami mai tashe da yake aiki kaman yankan wuka. Sha yanzu magani yanzu."
Asshe itace kanwar Mommy dake aure garin Kano. Mijinta D'an kasuwa ne da kasuwancinsa ya zaga garin Kano harma da wasu jihohin Arewa. Su uku ne wajen mijin nasu tanada uwar gida da amarya itace ta tsakiya. Itace kuma mahaifiyar Anisa sai d'an uwan Anisa mai suna Hilal.
Zaune sukai gaban gasunk'umin bokan da ya ari sunan malanta ya yafa. Sumarsa furfura ya cika kama daga kansa dake rufe cikin hulan sak'i har izuwa sajensa da ya zagaye fuskansa.
Wani k'aton faranti ne gabanshi mai lallausan yashi a ciki. Hannunsa guda nad'e cikin doguwar carbin da takai tsawonsa koma tafi. D'an bukkan kuwa ko ta ina shirgi ne da tsummokara.
Asshe ta gyara zama "Allah gafarta Malam itace 'yaruwata da kwanaki na labarta maka tana so a mata aiki akan d'anta."
Hannu guda ya d'aga ya dakatar da Asshe yaci gaba da jan doguwar carbin yana furta wasu kalmomi da basu iya tantancewa.
Lokaci guda yasa hannunsa ya shafi k'asan ya zana wasu layi kusan guda uku.
Sai ya soma jinjina kai yana duban farantin "Naga AURE cikin rayuwar d'anki."
Asshe da Mommy suka dubi juna.
Mommy ta girgiza kai cikin rashin fahimta "Aure kuma Malam..?"
Mutumin ya jinjina mata kai cikin tabbatarwa.
"Malam anya kuwa..? Aure cikin rayuwarsa..? A gaba kenan dan a halin yanzu ko maganar mace baya so a masa balle aure da aje iyali."
Wani kwanon sha ya d'auko wanda tsatsa tai mata dabaibayi ta ko ina ya nuna mata cikin kwanon mai cikeda ruwa. Take fuskar Haidar ya bayyana.
"Wann ba shine D'anki Aliyu ba..?"
Mommy tai saurin jinjina kai alamun eh "Eh.. Eh shine Malam."
Ya kuma kad'a kai "Tabbas D'anki yayi Aure ba tareda saninku ba.."
Mommy ta dafe k'irji cikin d'imauta "Na shiga uku Ni Kwaise..!" Ta dubi Asshe jikinta har rawa yake "Asshe tsanar da Haidar ke min har yakai yai aure ba tareda sanina ba.. Innalillahi wa inna'ilaihi raj'iun..!"
Bokan ya katseta "Shi kansa baisan yayi auren ba.!"
Suka dubi juna itada Asshe shaye da mamaki.