Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 15

Auren wata ukku by sameena - Chapter 15

Auren wata ukku by sameena Chapter 15: Auren wata ukku by sameena Chapter 15. A zuciye Asshe ta katseta "Kar ki sake cewa na cuceki.. Ke kika cuci kanki..…

4,322 words

A zuciye Asshe ta katseta "Kar ki sake cewa na cuceki.. Ke kika cuci kanki.. Magana akan cuta.. Shin tsakanin ni da Ke waye ya cuci wani..? Ni da naima D'ana auren cikan buri da 'yarki ko kuma keda kika cuceni kika sakani a tsaka mai wuya, nai jagoranci wajen aura ma d'an 'Yaruwata wann 'yar taki mai lullub'e da Illan asiri da farar k'afa.. shin ki fad'a mun… Tsakanin mu biyun waye ya cuci wani..? Rayuwan d'ana yana tsaka mai wuya a nan.. Idan Haidar Ya Mutu 'yarki ce Sila.. Shin banyi adalci ba da nace zata zauna na tsawon watanni uku..?!"

Umma taci gaba da hawaye tana duk'e wajen.

Asshe taci gaba "Ki gode ma Allah.. 'Yarki bazata fuskanci tozarci na mutuwan aure a daren aurenta ba.. Ki gode ma Allah bayan duk abubuwan da kikayi 'yarki zata zauna k'ark'ashin Inuwan aure na tsawon watanni uku.. Ki gode ma Allah bazaki fuskanci dariya da gori harma da wulak'anci idan har auren 'yarki Ya Mutu a daren yau ba.. Domin kuwa duk wani Sirrinki da naji sai na bankad'e.. Kuma Kinsan me..?" Ta k'arashe tana mai duk'awa gaban Umma dake duk'e tana hawaye "Zaki amar da duk wasu kud'ad'en da na kashe wajen nema ma D'an 'Yaruwata auren 'yarki. Kaf ko kobo bazan bari yai ciwon kai ba.. Kin shirya biya.?" Ta k'arashe tana tsare Umma sosai da ido.

Inna Dije ta k'arada "Daga nan kuma sai kiyi bankwana da Mijinki Suwaiba bayan kin rasa yaranki. Dan bayan abinda Ya faru ki sani zan d'auke D'anuwana na masa jinya bazan barshi tsakanin mata guda biyu da Babu Allah cikin zukatansu ba..!"

Umma ta d'ago idanunta masu zuban ruwa tana duban Dije da Asshe "Dan Allah.. Kar ku jefa rayuwata cikin garari.. Kuji tsoron Allah.. Kuji tausayin rai.. Ku tuna kuma iyaye ne.. Kuma burin ko wace uwa ta kai 'yarta d'akin miji."

"Kar kiyi mana maganan zama iyaye a nan.. Domin kaw baki tab'a zama uwa ga 'ya'yanki ba Suwaiba.. Kuma yau zaki fara girban duk abinda kika shuka..!" Dije ta k'arashe tana sakin huci.

Asshe ta gyara tsayuwarta "A tsakanin watanni ukun ma inada sharud'a.. Dan Kinsan a daren nan zan iya kashe auren 'yarki Suwaiba haka ne..?!" Ta k'arashe tana duban Umma kannare da idanu.

Umma ta share hawayenta tana kuma jinjina kai a hankali kaman marainiyar mage.

Asshe ta jinjina kai "Shradina shine bazakiyi magana da Ummul ba har na tsawon watanni Uku. Ina nufin iyakacin wa'adin zaman da zatai da D'anmu. Keda had'uwa da ita kuma sai kwangilar D'ana Ya k'are randa Ya cika aikinsa ya warware auren.. Ni kuma zan d'auko 'yarki da kaina na kawo miki ita cikin mutunci. Kin amince..?"

Umma ta d'ago a raunane tana duban Asshe jin da gaske dai Auren wutin gadi Ummul tayi ba kaman yanda taci mata buri ba. Sann ga wasu dokoki da sharud'a Wanda aka gindaya na datse alak'arta da 'yarta "Dan Allah kar kiyi haka.. Kiyi hakuri… Kar ki rabani da Ummul.. Wllhi Ina son 'Yata.."

"Na zata kinfi so tayi aure tayi nesa dake… Ko ba haka bane..?" Asshe ta katse ta.

Umma ta kuma rintse idanunta tana hawaye.

Muryar Inna Dije ya katseta "Burinki Ya cika Suwaiba.. Mata mazan 'yarki tayi aure.. Amma aure mai gibi.. Wanda bada jimawa ba angulu zata koma gidanta na tsamiya.." Ta murmusa kafin taci gaba "Inama zanga Tani na bata wann babban Albishir..!"

Umma ta shiga d'ago hannaye daga duk'e tana rok'on Dije "Dan girman Allah ki rufa mun asiri Dije.. Kar abinda Ya faru yau ya fita ko ina.. Dan Allah Ku rufa mun asiri.. Wllhi na amince zanyi duk abinda kukace.. Amma kafin nan dan Allah ku barni nai Sallama da Ummul.. Ku barni nai Sallama da 'Yata..!"

Dije da Asshe suka dubi juna kafin Asshe ta jinina kai "Kinada minti talatin kacal kiyi Sallama da 'yarki.. Sann ki aje wann a ranki.. Kaman dai yau nan da watanni uku zaki sake had'uwa da 'yarki.. Watak'ila had'uwa ta Har abada.."

Umma ta shiga jinina kai tana godiya. Jiki Babu laka ta mik'e ta nufi sashen da aka aje Ummulkhairy.

Umma tana shigewa Dije ta juyo tana duban Asshe duban irinta gogaggu. Dukansu biyu suka tsare juna da idanu. Kai da gani zaka fahimci wann ta naima wann kallon biri ne waccan tanai ma d'aya kallon ayaba. Ko wacce irin duban da take ma juna kenan.

Dije ta murmusa tace "Kin d'auki kasada mai girma ma d'anki dukda na sanar dake ga abinda Ya samu nawa d'an.. Meyasa..? Meye dalinlinki..?"

Asshe ta murmusa irinta gogaggun wayayyu "Aw.! Baki yarda da hujjata bace..? Cewar auren kwangila na tsawon watanni uku mukai da 'yarku.?"

Murmushi Inna Dije Tai "Kar kiyi zaton wayewarki zaisa ki shashashantar Dani kamar yanda kika shahsantar da Suwaiba.. Ni ba Suwaiba bace.. K'ar nake kallonki.. Dan haka Ki sanar dani meye asalin dalilinki.. Dan babu wanda zaiji abinda na fad'a Ya kuma amince D'ansa ko wani nasa yai tarayya da Ummul.. Bayan jifa na asiri dake jikinta ita d'in barazana ce ga rayuwarsa.. Anya akwai wacce zata amince wani nata Ya zauna da Ummul matsayin matar aure..? Ko da yake ba d'anki da kika haifa bane.. D'an 'Yaruwarki ne.. Tabbas akwai banbanci.!" Ta k'arashe shu'umin murmushi saman fuskarta.

Asshe ta murmusa "Jifa na asiri..? Toh kodai kece kikai jifan.. Dan idan Har Zan amince D'an 'Yaruwata ya auri 'yarku mai tawaya na asiri.. Bana jin akwai wacce zata tona ma 'yar D'an uwanta asiri irin haka.. Kaman dai yanda kikai ma Ummul.. Da ni dake dukanmu 'Yanuwa ne ga iyayen Ummul da kuma Haidar.. Haka ne..?"

Dije Tai shiru tana duban Asshe. Ta kula su duka biyun Sun k'ware a iya buga wasan. Tabbas kuskure kad'an zatai gaban matar nan ta sha k'asa.. Koda wasa bazata bari hakan ta kasance ba. Gwara ta gyara d'amararta da kyau.

Murmusawa Dije tai tace "Af! K'warai haka fah.. Magana ake na gwaggwani da Innoni.. Wanda yafi nuna kula ga nasa.. Tabbas shi zai d'auki kambin.. Mai zai faru idan na tafi na samu 'yaruwarki na sanar da ita ga abinda kika shirya ma D'anta… A bayan idonta..?" Ta k'arashe tana tsare Asshe da idanu ga muguwar murmushi saman fuskarta.

Asshe ta d'an d'auki lokaci tana dubanta. Dukda bugu da zuciyarta keyi bai hanata tattaro natsuwarta ba dan bata so ta bama Dije k'ofan da zata d'ago rauninta. ta murmusa tace "Wai ance da D'an gari akanki gari.. Kin tab'a jin an shiga gari yak'i Anci yak'in ba tareda taimakon D'an gari ba..? Ina nufin kinada masaniyar wace irin yarda ce tsakanin 'yanuwa biyu.?" Ta k'arashe tana tsare Dijen da idanu itama.."

Su dukansu biyu suna duban juna. Asshe ta murmusa ganin Dije bata bata amsa ba. Ta k'araso ta dafa Dije kad'an "A shawarce "Kowa ya tsaya a masarautarsa , Ina nufin kiyi yanda kikaso da Suwaiba harma da D'anuwanki.. Kar ki shiga tsakanina da 'Yaruwata.. Dan nasan bazaki so yin wasa da wuta ba.."Ta k'arashe murmushi saman fuskarta.

Dije ta murmusa "D'iyar mak'eri bata shakkan wuta.. Hasalima ta saba wasa da wuta.. Kiyi tunani kan abinda na sanar dake. Domin kuwa kaman yanda kika amshi bak'oncina cikin gidanki ba tareda kin gayyaceni ba. Toh ina mai tabbatar Miki zan kai ziyara ma 'yaruwarki ta birnin tarayya.. Ina nufin mahaifiyar surkinmu." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta.

Shiru Asshe tai zuciyarta na kuma bugawa. Lallai wann matar babbar barazana ce a gareta. Dan tabbas idan ta tafi ta samu Kwaise ta sanar da ita abinda ke faruwa toh fah tata ta k'are. Sosai tai nisa cikin duniyar tunanin yanda zata b'ullo ma wann Dijen wacce ta zamto babban threat a gareta.

Inna Dije ta gyara zaman mayafinta "Kiyi tunani da kyau.. Ni zan tafi.. Dare yana yi.. Amma kafin na tafi ki zuba mun lambobinki a nan.. Sabuwar k'awata.." Ta k'arashe tana duban Asshe da ta zama deep in thoughts.

Asshe ta dubeta irin duban baki kai ki shiga jerin matsayin kawayena ba.. Sai kuma ta murmusa abinka da gogaggiya "K'awa..? Oh haka ne… Ta bayan fage..!" Ta k'arashe maganar tana Shafa kwantattun gwalgwalan dake zube wuyanta zuwa kunnuwanta da hannayenta. Dije sai dubanta take tana jinina barikin matar nan. Watau bazata fad'a mata matsayinta da baki ba saidai yanayin shigarta da suturan dake jikinta Ya tantance hakan.

Lokaci guda ta d'auki wayarta ta mik'a ma Inna Dije "Zuba min lambobinki a nan.."

Inna Dije ta murmusa kafin ta dubi wayar kaman zata amsa sai kuma ta tabe baki tace "Baki tunanin ban Saba da rik'e irin wayoyin nan naku ba.. K'awa..!" Ta k'arashe tana juya mata gajiyayyar wayar dake rik'e hannunta harda d'aurin robber ring jiki.

Asshe ta murmusa tace "Gashi Ba hand sanitiser kusa, bara na sanar dake da baki sai ki juye a naki wayar.. Ya Miki.."

Dije ta jinjina kai "Kar ki damu.. matuk'a bazaki lank'wasa harshe ba.. Anyi alimantari an samu na zama cikin Al'umma.. Kar ki mance lambobin gaske zaki bada dan idan ba haka ba. Zan riga ki isa wajen 'yaruwarki." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta.

A haka dai sukai exchanging phone numbers kowa tana watsa ma juna bak'ar magana da sako a dunk'ule.

Inna Dije zata fice Asshe ta dakatar da ita "Ina Miki ta'aziyar D'anki.. Ina kuma fata hakan bazai faru da nawa D'an ba.."

Inna Dije ta murmusa "Fata mai kyau.. Allah yasa.. Idan kuma fatanki bai amsu ba.. Sai ki tanadi farin k'yalle nan da watanni uku.. Watak'ila akwai cin gumba gidan k'awata.."

Suka sakar ma juna murmushi Wanda yafi kama da yake. Kafin daga bisani suka kuma yin Sallama. Asshe ta juya idanu cikeda k'osawa Har Inna Dije ta fice.

Zama Tai cikin kujera tana mai furtawa a fili "Oh ni Asshe wasu irin mutane na jajib'o mana ne wai.. Ita Suwaiba nayi zaton abin nata a shashanci da wauta kawai ya tsaya ashe Shegiya wawiyar gangance 'yar boka. Ga Tani daga can gefe mai cinye gadon miji yana raye.. Ita kuma wann Dijen da alama itace tafi kowa hatsabibanci cikin ahalin domin kuwa idan har banyi da gaske ba zata zame min babban barazana..!"

Ta mik'e cikin sand'a ta nufi d'akin da Umma ke ban kwana da Ummul d'inta. Jikin k'ofa ta mak'ale tana sauraron tattaunawar 'ya da Uwan.

Umma tai k'ok'arin saita kanta tana duban Ummul dake dubanta cikin rashin yarda hawaye kwance saman k'uncinta. Sosai Umma ta sha mur kaman ba ita ba. Cikin zuciyarta kaw k'ok'arin danne raunin nata kawai take dan k'arfafa gwiwar 'yar tata. Cikin kakkausan murya ta ambato sunan Ummulkhairy snn taci gaba "Ina so ki mun alk'awari guda d'aya Ummulkhairy.. Watak'ila shi kad'ai ne alfarmar da zan nema daga wajenki.!"

Ummul ta kuma duban mahaifiyar tata jiki a matuk'ar sanyaye. Murya na tsananin rawa take furta "Umma kin wuce ki nemi alfarma wajena.. Kar ki mance ke mahaifiyata ce.. Ko me kike so nayi matuk'a bai sab'a wa Ubangijina ba zanyi… Dan cikan burinki… Zan zan Miki Umma..!" Ta k'arashe cikin sautin kuka.

Dukda kuka da yazo ma Umma amma sai tayi k'ok'arin danne kukanta "Ummulkhairy kar ki neme ni… Kar ki tako yanda nake Har na tsawon watanni uku.. Ko a waya kar ki kirani.. Ki min alk'awarin.!"

Da tsananin mamaki Ummul ke duban mahaifiyarta. Ta shiga girgiza kai cikin rashin yarda "Umma.. Mai hakan yake nufi..? Umma zaki yanke duk wata alak'a dani ne..?"

Umma ta jinjina mata kai alamun eh "K'warai Ummul.. Kuma kema kimin alk'awarin yanke alak'arki damu.. Ina nufin da d'aukacin ahalinki na tsawon watanni uku.. Kimin wann alk'awarin..!" Ta k'arashe tana duban Ummul d'in.

Girgiza kai Ummul keyi tana duban mahaifiyarta "Umma.. Kin kaw ji abinda kike fad'i mun..? Umma yanke alak'a da iyayena harda mahaifina dake kwance yana jinya..? Umma Anya.."

Katseta Umma tai "Na tsawon watanni uku kacal.. Dan Allah ki mun wann Ummul..!" Ta k'arashe tana kamo hannayen Ummul d'in alamun rok'o hawayen da taketa k'ok'arin dannewa na kwaranyo mata.

A hankali Ummul ta zame hannayenta tana girgiza kai "A'a Umma.. Baki tunanin Kin tafi da nisa Umma.. Bazan iya ba.. Bazan iya abinda kike nema daga wajena ba.. Bazan iya yanke alak'a da ahalina ba.. Menene dalilinki Umma..?"

Umma taci gaba da matsan k'walla. Sai kuma ta mik'e tana huci "Wann Shine kad'ai abinda na nema daga wajenki Ummul.. Kar ki nemeni, kar ki tako yanda nake Har na tsawon watanni uku.. Idan kuma kika nemi ni ko kika tako yanda nake kafin wata uku ban yafe miki ba.!" Tana ida fad'in haka tasa kai ta fice kuka na kuma b'alle mata.

Ummul Tai zaune tamkar wacce aka dasa. Ta nemi kuka ta rasa. Sai ta shiga tambayan kanta Wacece ita..? Meyasa rayuwa yazo mata a haka..? Shin ita kad'ai ce take fuskantar k'alubale irin nata..? Shin Anya Umma itace ta haifeta..? Anya uwa takan haifi 'ya tayi watsi da ita irin haka.. Tin daga tasowarta Umma bata tab'a damuwa da al'amarin rayuwarta ba. Ta mata aure a wulak'ance. Daga k'arshe ta datse alak'a da ita ba tareda dalili ko hujja ba.. Anya ana samun irin wann uwar.. Anya ko a labarai ta tab'a cin karo da uwa irin Umma..? Ta shiga girgiza kai tana duban d'akin da aka ajeta. Lokaci guda ta mik'e tana takawa a hankali. Daidai gaban madubi taja ta tsaya tana duban kanta cikin madubin.

Take zuciyarta Ya shiga karanto mata wacece ita. Tin daga lokacin k'uruciyarta har kawo girmanta. Duban kanta take cikin mirror hawaye na zurarowa daga cikin idanunta d'aya na bin d'aya.

A hankali ta silale a wajen cikin kuka maras sauti tana jin tamkar bata a duniyar.

**

Umma ta kusan ficewa kenan taji an damk'o hannunta an janyota wani d'akin.

Asshe ta gani tsaye tana sakar mata murmushi "Kinyi abinda ya kamata."

Jinjina kai Umma tai tana duban Asshe "Ki sani da ace nasan irin auren da zakuyi ma D'anku da Ummul kenan tun farko da ban amince ba. Amma saidai idona Sun rufe Allah Ya barni da iyawata a lokacin da na Shafa'a da neman zab'i daga gareshi. Watak'ila wann shine hukunci na." Ta share hawayen da suka zubo mata kafin taci gaba "Nayi abinda kuke so.. Na yanke alak'a na wucin gadi da Ummul kaman yanda kukai auren wucin gadi da ita.. Alak'ata da 'yata zai dawo ne bayan sharud'anku Sun cika.. Wann lokacin kuma.. Nayi alk'awarin sabanta alak'ata da 'Yata.. Nayi alk'awarin bata kulan da ban bata ba tsawon rayuwarta.. Nayi alk'awarin nuna mata soyayya irin Wanda na hana mata a matsayin uwa tsawon rayuwarta… Na.." Kuka ya hanata ci gaba da magana.

Da k'yar ta iya saita kanta kafin taci gaba "Iyakacin abinda zan rok'a daga wajenki shine ki kula mun da Ummul .. Dan Allah kar kici amanata Asshe.. Ke kad'ai na sani cikin ahalin da Ummul zata shiga na watanni uku… Dan Allah Ki kular mun da ita.. Kuma ki rike amanata kar ki tab'a tona sirri na ma Ummul… Kar ki sanar da ita AUREN WATA UKU tayi kuma inada masaniya. Dan Allah kimin wann..!" Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka hannayenta had'e waje guda alamun rok'o.

Asshe tab'e da baki take duban Umma babu ko alamun tausayi. Cikin zuciyarta take ayyana dan ma baki san dalilin auren 'yar taki shine ta karya sihiri ba. Sann auren yana nufin ajalinta. Ki gode ma Allah itama ta zama barazana ga rayuwar Haidar Wanda hakan zaisa ki sake had'uwa da 'yarki bayan wata uku. Dan bazan tab'a bari Haidar ya kusanci wann 'yar taki ba. Ta murmusa kad'an "Kin kware wajen iya wasan kwaiwayo Suwaiba.. Ban Miki alk'awarin komai ba… Dan bayan amanata da kikaci bansan mai zai faru a tsakanin wata uku ba..!"

Cikin zuban hawaye Umma ta shiga jinjina kai tana k'ok'arin mik'ewa. Jiki a matuk'ar sanyaye tasa k'afa zata fice Asshe ta kuma dakatar da ita.

Umma taja ta tsaya Har lokacin hawaye take.

Asshe ta k'araso tana duban Umma daga sama zuwa k'asa. Lokaci guda tasa hannu ta shiga janyota da k'arfin gaske . A haka suka isa gate.

Suna isowa gate tai jifa da Umma gaban securities. Asshe ta shiga nuna masu Umma "Ko me kamannin matar nan kar ku bari ta kuma shigowa gidan nan.."

Umma dake watse k'asa kaman kayan wanki ta d'ago idanunta da kyar tana duban Asshe dan yanzu ta daina mamakin abubuwa.

"Asshe…"

"Shiiii..!" Asshe ta dakatar da ita tana mai d'ora yatsa ta guda saman labb'anta "Duk draman da akayi mijina baida masaniya Suwaiba.. Ni Ina son mijina kuma ina daraja aurena.. Ni ba irinki bace wacce ta watsar da mijinta dake kwance yana jinya sabida cikan burinta. Bazan bari mace irinki ta lalata mun aure ba.. Dan haka bake ba ni. Dama kema kinsan hanyar jirgi ba daidai bane da na mota. Ni da Ke ba d'aya bane. Ciniki Ya had'amu kuma ta k'are. Babban goro sai magogin k'arfe bayan wata uku zaki sake haduwa da 'yarki idan d'anmu Ya gama kwangilarsa dan ita ba ajinsa bane. Zaren ba kalar yadin bane. Tashi ki fice kafin nasa su fitar dake..!" Ta k'arashe tana nuna mata k'ofa.

Jiki Babu k'wari Umma ta mik'e tana ganin duhu na gauraye mata k'wayan idanu. Ta shiga had'e hanya tana takawa da kyar tana jin wani abu mai zafi na yawo cikin k'irjinta.. A haka Umma ta fice daga gidan ga duhun dare ba tareda tasan ina take zuwa ba.

SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU.!*

*22*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

A b'angaren Inna Dije kaw koda ta fice sai ta tadda Khulsum a yanda tace ta zauna ta jirata. Dan dama lokacin da Umma ta kori Khulsum daga wajen Ummul Inna Dije ta had'u da ita a k'ofan gidan tana kuka. Nan take sanar da Inna Dije ga yanda sukai ita da Ummanta hakan yasa Inna Dije Tai mata umarni da ta jirata Har ta shiga ta fito zasu tafi tare.

Basu zarce ko ina ba sai asibiti wajen Abba.

Inna Dije ta k'ura ma D'anuwanta dake kwance idanu. Ta shiga jinjina kai tana mai furtawa a fili "Lallai Yaya ka gamu da jarabawan shed'anun Mata.. Amma da izinin Allah ba macen da zata saka samun damar cutar dakai cikinsu.. Bazan bari hakan ta kasance ba.. Na maka alk'awari D'anuwana." Ta k'arashe tana dafe hannunsa guda.

Khulsum dake zaune gefe ta goge hawayen da suka gangaro mata tana jin ciwon abinda mahaifiyarta da abokiyar zaman mahaifiyar nata sukai ma mahaifinta Wanda Babu mijin da Ya cancanci mata Irinsu.

Mama Dije ta matso ta rungume Khulsum tace "Kar ki damu Khulsumu. In sha Allahu mahaifinki zai samu lafiya, zan d'auke shi daga nan.. Zamu tafi gaba dayanmu.. Zamu fara sabuwar rayuwa gaba d'ayanmu tare.. Su kuma Suwaiba da Tani ko waccensu zata girbi abinda ta shuka ne.."

Khulsum bata iya cewa komai ba sai kauda fuskanta gefe da Tai tana mai kuma goge hawayen dake zubo mata. Dan Allah ya gani dukda Umma ta kasance mahaifiyarta sai taji sam bata ko k'aunar a ambato mata sunan mahaifiyar tata musamman bayan rabuwar da sukai a daren yau d'in.

Mama Dije sai duban Khulsum take tana sak'a abubuwa cikin zuciyarta 'Tabbas sai ta cika Zuciyar Khulsum da tsanar mahaifiyarta.. Suwaiba zata rasa yaranta gaba d'aya.. Bayan ta rasa Ummul zata rasa Khulsum ma. Zata rasa ahalinta gaba d'aya dan mijin ma ta rasa shi kenan rashi na Har abada.. Sai ta tabbata rayuwa yayi k'unci ma Suwaiba, k'uncin da sai ta gwammaci mutuwa da wann rayuwar… Kaman yanda ta rasa Fa'iz d'inta D'anuwanta tilo Ya kuma k'ullaceta sabida soyayyan Suwaiba da ya rufe masa ido. Ta rasa soyayyan D'anuwanta na tsawon shekaru zata tabbata tayi amfani da wann damar ta dawo da shak'uwa da soyayya dake tsakaninta da D'anuwanta.. Snn zata rattaba Auren Ummul ya Mutu kafin wa'adinsa ya cika. Bayan auren ya Mutu ta bi ta sanar da Ummul irin auren tozarci da Suwaiba tai mata. Sai ta kwance ma Suwaiba zani kasuwa gaban 'ya'yanta. Dik irin biyayya da Ummul ke ma Suwaiba sai ta tabbata ta masu farrak'u bayan ta kashe wulak'antaccen auren da tai ma Ummul. Suwaiba zata zama batada tsuntsu batada tarko. Zata rasa kowa tin daga kan Yayanta Isubu da zata masa jinya a yanzu wanda makahon soyayyan da yake ma Suwaiba ya hanasa ganin aibun Suwaiban har dai suka sami sab'ani mai muni duk sabida Suwaiba har izuwa kan yaranta guda biyu Ummulkhairy da kuma Ummulkhulsum.. Wann alwashi ne da ta d'auka ma kanta. Ta saki murmushi a hankali tana jin zuciyarta na mata sanyi al'amara suna tafiya mata yanda take so.

**

Ikon Allah ne ya kawo Umma gida. Tana isowa ta hangi fitilan d'akin Tani a kashe. A nata tunanin Tani ta kwanta bacci tinda tasan kaman yanda Dije tace bazata kuma barin d'aya daga cikinsu ta kusanci Abba ba tasan bazata bar Tani ta zauna can asibiti wajen Abba ba. Hakan yasa ta shiga sand'a a hankali alamun bata so Tani taji dawowarta.

Kaman Wata b'arauniya haka ta shige d'akinta cikin sand'a tana addu'an Allah yasa ta tadda Khulsum na bacci. Saidai koda ta shige d'akin babu Khulsum Babu alamunta. Umma ta silale ta zauna da kyar tana duban gadon yaran nata da angle din da ko wacce ta Saba kwanciya.. Sai ta tuna irin rabuwar da sukai da Khulsum duk Akan Auren Ummul. Datse alak'a tai tsakaninta da 'yarta Khulsum. Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un tana cikin hayyacinta ta aikata makamancin wann abu. Sai ta soma tunanin toh ina Khulsum ta shige.? Take zuciyarta ta bata amsa da fad'in tana wajen mahaifinta a asibiti kaman yanda kika koreta daga gareki. Khulsum bata da wajen zuwa da ya shige wajen mahaifinta. Umma ta silale a hankali hawaye na kuma b'alle mata. Sai tana jin wani abu da yafi yanayi da tashin hankali na ziyartarta… Yau dai Babu Ummul a cikin gidan, wacce a kullum idan ta bud'e idanu ta ganta cikin gidan Babu aure zuciyarta ke mata ciwo, hankalinta ke tashi. Haka zalika taita kausasa harshenta Akan k'addarar 'yar tata. Meyasa bataji ciwon ya tafi ba..? Meyasa duk tulin damuwar da Tai a baya Wanda a nata zaton ganin Ummul ne a gida ba tareda aure ba ya haddasa mata. Meyasa taji babu abinda ya ragu a k'uncin da takeji cikin ranta sai ma abinda ya k'aru..? Meyasa..? Meyasa abubuwa suka kwabe meyasa auren Ummul da tai zaton zai zamto mabudin farin cikin ta da na ahalinta meyasa bai zama haka ba.. Meyasa auren Ummul ke barazanan zama mabudi da Mafarin tarwatsewar Ahalinta.. Ta rintse idanunta wasu hawayen masu tsananin ciwo suna zubo mata. Saida Umma tai kuka mai isanta ita kad'ai cikin d'aki with no shoulder to lean on. Babu wanda zaiji sautin kukan nata balle Ya lallasheta.. Ita kadanta cikin d'aki tasha kukanta. Dakin ya mata girma, daren ya mata tsayi… Haka Umma taci kukanta a d'aki cikin dare tamkar marainiyar kenwa.

**

Washe gari sassafe ake shirin tafiya da Amarya Ummulkhairi gidan mijinta dake Abuja.

Asshe ta fito taci uwar gayu yayinda Ummul ta kasa fitowa sai shesshek'ar kuka take Wanda ya riga ya zame mata jiki. Tin Daren jiya take aikin abu d'aya Akan dole Asshe ta tilasta ma cin abinci ma saida tai da gaske kafin ta saka ruwan shayi a cikinta. Kallo guda zaka mata ta baka tausayi. Asshe sai sababi take tana fad'in haka za'a Kai amarya a k'anjale jiki duk yunwa kaman wata kazar mayu. Cikin ranta kuwa addu'a take Allah yasa Ummul tafi haka lalacewa ko dan kar idon Haidar da hankalinsa ya sauk'a kanta.

A haka suka fito da k'yar bayan Asshe ta sanar da Ummul kar ta mance kud'in Aurenta shine kud'in jinyar mahaifinta dan haka tafiya gidan Miji ya zame mata dole idan har ba so take su janye komai ba.

Ummul na hawaye take janyo k'afafunta. Tabbas wann auren sadaukarwa ne ga illahirin ahalinta. Bayan datse alak'a da ita da Umma tai a daren jiya na tsawon watanni uku na farkon aurenta bata jin Umma zata tab'a yafe mata idan tace ta fasa wann aure. Ta rintse idanunta zuciyarta na tausarta da cewa irin nata k'addaran kenan. Watak'ila hakan shine alkhairi ga d'aukacin ahalinta. Idan tai nesa dasu Watak'ila farin ciki da kwanciyar hankali zai wanzu cikin ahalin irin Wanda basu samu a baya ba.

Fitowar da zasuyi da zummar shiga mota kenan suka sinkayo wata murya.

"Ku dakata ku dakata. Direba a dakata ga pasinja d'aya.!" Ta k'arashe tana kuma mak'ale k'aramar jakar Ghana must go d'inta a hammata sai faman buga sauri take.

Asshe ta zaro ido tana duban matar nan shaye da tsananin mamaki "Dije.!" Ta furta da k'arfi.

Inna Dije taci gaba da sakin murmushi tana duban Asshe "Haba k'awa ban gane wasa tare ci banban ba. Haka kika shirya tafiya da 'yarmu babu wani nata. Ce Miki akai batada dangi ko tsawa akai ta fad'o da zaki rufeta ki kaita kamar wata maras gata."

Ummul tai saurin yaye rufin kanta hawaye na kuma b'alle mata "Inna Dije." Ta furta a hankali tana duban Dije. Dije tai saurin k'arasawa ta rungumi 'yar D'anuwanta "Ni ce nan Goggonki Ummul.. Innarki Dije, bazan bari a kaiki gidan miji kamar maras gata ba. Shige muje.!" Ta k'arashe tana mai shigar da Ummul cikin mota.

Har lokacin mamaki Ya kasa sakin Asshe. Watau matar nan ta ranste sai ta tona mata asiri. Inaa bazata bari hakan ta kasance ba.. Kafin Tai aune taji Inna Dije ta janyo hannunta ta jefata cikin mota. Fad'i take "Direba tada mota muje birnin tarayya ba nan kusa ba."

Asshe ta matse hannun Inna Dije da k'arfi tana k'ok'arin fiddota waje amma sai taji Inna Dije ko gizau bata motsa ba. Saitin kunnen Asshe take rad'a mata "Kar kiyi wann ganganci dan tsaf zan kwance Miki zani a Kasuwa. Kama daga kan mijinki da kishiyoyinki Har izuwa kan 'yaruwarki. Dan haka cikin salama ki shige mu tafi.!" Ta k'arashe tana firfito da idanu waje.

Asshe ta had'iyi abinda Ya tsaya mata a mak'oshi da k'yar. Cikin sigan rad'a take tambayarta "Fad'a mun nawa kike so.?"

Readers Also Read