Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 16

Auren wata ukku by sameena - Chapter 16

Auren wata ukku by sameena Chapter 16: Auren wata ukku by sameena Chapter 16. Inna Dije ta murmusa, cikin sigan rad'a ta bata amsa da fad'in"Ki bari mu isa…

4,481 words

Inna Dije ta murmusa, cikin sigan rad'a ta bata amsa da fad'in"Ki bari mu isa can zamuyi ciniki a tsanake." Sai ta murmusa tana k'are ma Asshe kallo harda kashe mata ido "Kar ki damu k'awalliya zamu sha hirarmu ta k'awaye a mota." Ta k'arashe tana d'aka ma Asshe bugu a cinya harda kecewa da dariya. Ta dubi driver tace yaja mota su tafi kar rana yai masu a hanya. Driver kaw yai yanda tace dan dai Asshe kam ta kasa katab'us cikin motan. Abun matar Ya koma bata tsoro. Ta d'auki Suwaiba shashasha amma wann kam ko shakka babu gogaggiya ce . Tanaji tana gani suka d'auki hanya tareda Dije babu kuma yanda ta iya. Abinda take tsoro ne yake gab da aukuwa. Mai zai faru idan wann matar da ta zame mata k'arfen k'afa ta bud'e baki ta sanar da uwar Haidar komai. Ta tabbata Kwaise zata iya d'aureta Har igiya yayi saura sann asirinta gaban miji da kishiyoyi harma da yaranta Ya tonu. Lallai Ya zama dole ta san yanda zata b'ullo ma wann matar. Idan ta kama ta b'atar da ita tun akan hanya ne kafin su isa zatai hakan. Dole ta canza salon yanda zata tunk'ari wann mahaukaciyar Matar da burin fansan ran D'anta Ya rufe mata ido. Haka dai Asshe taita sak'awa tana kwancewa cikin mota. Gaba d'aya kallo d'aya zaka mata ka gane a birkice take.

**

A b'angaren Umma kaw sassafe da rabon fad'an yaran Mama ta tashi. Badia da Azeema sai tona ma juna asiri suke Azeema na fad'in sai Badia ta nemo B'arawon mijinta yanda ya shiga ya fita. Yayinda Badia ke fad'in gwara nata mijin a sata Ya tsaya ita kaw Azeema ba Wanda baisan Habibu k'aton kwarto bane Wanda baya raina mai d'ankwali. Nan dai akaita fad'a Umma na k'ok'arin rabiya amma inaa saida dai akai chaa a k'ofan b'angaren nasu kaman ko yaushe ana bama ido abinci.

Azeema taci gaba da fad'in "Oho dai gwara ni mijina baiyi sanadin rufe uwata a police station ba. Hasalima fad'i tashi yake ba dare ba rana dan ya fidda mahaifiyarmu da wann macucin mijin naki ya jefata ciki.. Kuma wllhi idan Har baki fito da Tasi ba zan tona miki asiri wajen Jami'an tsaro dan ba Mama bace kawai ta saka hannu a takardun bogin da mijinki ya kawo na saida Shagon Abba harda ke macuciya azzaluma.!"

Haba nan fah Badia ta janyo Azeema dambe ya kaure tsakaninsu. Umma ta shiga tsakiya tana k'ok'arin rabiya aikaw akai jifa da ita gefe. K'um kakeji jini ya b'alle a goshin Umma. Ta dafe kanta dake juya mata tana shafan jinin dake zubowa daga goshinta. Da rarrafe Umma ta bar wajen ta shige d'aki dan ba mutan gidan kawai ba har mak'ota lek'ensu suke suna Allah wadai irin wann ahali. Saikace ba jiya akai auren Ummul ba wacce kowa yake tunanin sabida ita ahalin suka gaza samun kwamciyar hankali. Sai gashi yau an wayi gari babu Ummul da akai mata lak'abi da annoba cikin gidan amma da tashin hankali suka wayi gari kaman dai ko yaushe.

Umma ta matse bakinta tana jin kukan gaske mai k'arfi na taso mata musamman da taji abubuwan da mutane ke fad'i. Ta kuma shafan goshinta taga jini. Ta rintse idanunta tana tunanin 'ya'yanta a daidai lokacin da jini ke fitowa daga goshinta. Ta aurar da Ummul bisa son zuciyarta sann ta kori Khulsum. Ummul take hangowa tana share mata jinin goshinta cikin tsananin nuna soyayya da kulawa yayinda take hango Khulsum tsakiyan Azeema da Badia tana k'ok'arin k'watar wa mahaifiyarta hakkin rauni da sukai mata a goshi.

Umma ta fashe da wani irin kuka mai ciwo. Lallai mutum baya gane kiman wani ni'ima da Ubangiji yai masa baiwa dashi sai ya rasa wann abun.

A haka Umma taci kuka da suntumemmen goshi ita kad'ai a d'aki.

Rayuwa kenan ko babu rabuwa akwai mutuwa. Mu zama masu godiya ga d'imbin rahamomin ubangijinmu garemu tun kafin daman hakan ya kufce mana. Tomorrow is not promised. Mu so juna muyi hakuri da juna. Mutanen da Allah ya albarkace mu dasu cikin rayuwarmu. Walau iyaye, 'ya'ya, miji, mata abokan zama da sauransu. Rayuwar duka batada tsawo. Abinda hak'uri bai kawo shi ba tashin hankali bazai bayar ba. Allah ya mana muwafak'a duniya da lahira. Ameen.

**

A can b'angaren Mama Tani kuwa yanda taga rana haka taga dare a police station. Fuskarta ta kumbura suntum sakamon Mari da tasha hannun tsagerun 'yanmatan da aka had'asu cell d'aya. Sallah ne kawai yake ceton Mama daga bugun da take sha hannun tsagerun nan.

Saiga Mama tana sallah cikin cell harda nafilfili. Har bata fatan ta ida sallah gudun kar su ci gaba da cutar da ita. Yara k'anana Har tausa suke sa ta masu idan batayi ba taci bugu.

Ta kula ko neman agaji take wajen 'yansandan basu kawo mata d'auki musamman wann matar da ta gansu da Habibu.

Ta nemi a fitar da ita zataje fitsari. Da k'yar da sid'in goshi aka fitar da ita tinda bata jima da fita alola ba. Addu'a take Allah Ya had'ata da Habibu Ya sanar da ita yaushe za'a fiddata. Kaman daga sama ta bayan d'akin da aka kaita fitsari yanda band'akin suke a jere ta soma jin maganganun ta wata 'yar window. Muryar Habibu takeji daga window d'in yana kwantar ma 'yarsandar hankali da fad'in shi fah ba taimakon Mama Tani zai ba. Dama yayi zaton zai cimma Tasi'u ne kafin abubuwa su lalace. Dan haka bazai jefa kansa a uku ba dan wann bakwaiye Ya rantse har kotu sai an tafi. K'arshe gidan Kasu Tani zata tafi babu ranar fita. 'Yarta kuma babu amfanin da take masa saima cike masa d'aki da tai dan haka a yau d'in nan zai rubuta mata takarda tinda Tasi'u Ya gudu da kud'ad'en. Aure zaiyi Ya saka amaryarsa a d'akin.

Sai ga Mama tana sakin fitsarin jikinta. Ta kama k'arfen window ta d'ale tana dubansu "Habibu.. Irin cin amana da yaudara da zakai ma Azeema kenan..! Amma Habibu Allah Ya tsine maka albarka. Ka cuceni ka cuci Azeema. Habibu Allah bazai barka ba. Kan wann kilakir ka wulak'anta Azeema.?"

Kafin takai aya taji sauk'an tagwayen Mari a fuskarta. 'Yar sandar Habibu ce tai mata Marin "Ki iya bakinki kisan a ina kike." Cewar budurwar Habibu Yayinda Habibu ke mik'a mata farar takarda "Tazo gidan sauk'i tinda kina kusa. Ga wann ki bawa 'yarki idan gantalinta Ya d'ebota ta nan tinda ba mutuncinki suke gani ba balle suzo dubiyanki. Kar na koma gida na tadda tsummokaranta cikin d'akina. Sak'o na baki ki sanar da ita. Gyara zan fara a gaggauce dan amarya ta zan aje ciki." Ya k'arashe yana kashe 'yarsandarsa da murmushi.

Mama sai Tai mutuwar tsaye tana juya takardan da Habibu Ya mik'a mata cikin hannunta. Bata san meke wakana ba har saida 'yarsandar da tai mata rakiya fitsari ta tasa k'eyarta.

Fitsarin da ta juyesa jikinta kenan ba tareda taje band'aki ba. Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un. Meke faruwa da ita da yaranta? Daga wacce miji Ya bata sak'on sakinta ta hannun mahaifiyarta sai wacce miji Ya cuta ya kuma gudu Ya barta. Sann a dalilinsa aka kame uwarta aka gark'ame. Shin wann wace irin rayuwa ce. Sai ga Mama tana kuka shar shar da hawaye hannaye biyu aka "Wayyo ni Tani naga takaina.! Habibu kaji tsoron Allah. Ka tuna ko mutuwa na kunyar idon uwa. Yanzu da wani bakin zan goranta ma Suwaiba ni Tani. 'Yar Suwaiba ta tafi d'akin Miji ni nawa yaran Sun dawo a jere. Wllhi bazata saku ba. da na koma na fuskanci tozarci yo gwara na Mutu a nan.!" Ta kuma kurma kururwa.

Tsawa budurwar Habibu ta daka ma abokan aikinta cewa su shige da Tani cikin cell d'inta su gark'ame.

**

Abuja

Tsaye suke a can construction site d'insu, yanda zasu gudanar da babban project na Kampaninsu.

Dukansu sanye suke da kaya irinta k'wararrun Engrs. Reflective safety jacket kalan d'orawa mai ratsin bak'i sai safety helmet mai d'aukeda tambarin kamfaninsu daga gaban *MB*

Su kusan hud'u sunyi tsaye gaban wani tapkeken sketch. Design Architect Hisham sai kwararo bayani yake yayinda sauran ke jinjina Kai kowa yana fad'in abinda ya k'ware akai.

Hisham na hankalce da Haidar Wanda Sam hankalinsa bai tare dasu. Excusing Kansa yai ya k'araso yanda Haidar ke tsaye jingine jikin mota. Shima d'in cikin shiga irin tasu yake saidai shi babu jacket saman rigarsa sai ko helmet.

Hisham yai masa k'uri hannayensa zube cikin aljihun jeans d'insa. D'an k'arasowa yai kusan Haidar d' in had'ida jingina jikin motar. Ba tareda ya dubi Haidar d'in ba ya soma fad'in "This is not like you Engr. Ban Saba ganin ana aiki jikinka a mace ba.. I expect to see Haidar mai jajircewa da na sani dan ban tab'a tsammanin Dad d'inka zai mik'a maka ragamar aikin nan cikin sauk'I ba.. Snn kaji yanda abokinsa yake yabawa team d'inmu baice komai ba baiyi yunk'urin dakatar dashi ba kaman yanda ya saba a baya. Kawo yanzu sun hango future ma Kampanin tareda kai. Zan iya ce maka na hango yau d'in a k'awayar idanunsa. Ko bai furta maka ba he's proud of you.."

Furzar da huci kad'an Haidar yai yana mai gyara tsayuwarsa hannayensa zube cikin aljihunsa yake duban masu tonon k'asa daga gefe "But unfortunately I'm not a perfectionist, a workaholic like my Dad." Ya karkato yana duban Hisham sosai "Ban damu ba yayi alfahari dani ko kar yayi. I don't give a damn.."

Hisham ya d'an girgiza Kai yana duban Haidar d'in "So tari mukan kasa ganin blessings da Allah ya mana baiwa dasu har sai mun rasa. Ka gode ma Allah Haidar ka girma da iyayenka biyu a raye kuma suna tareda kai. In my own case is a different story. Ban samu daman sanin mahaifina ba. Ban samu daman had'uwa dashi ba." Ya d'anyi fasali kafin ya murmusa "But it's fine I'm not complaining. Alhamdulillah, At least I have my Mom with me. And to me she's more than enough you know." Ya kuma murmusawa yana jinina Kai "Bazamu iya k'irga d'inbin ni'imomin Ubangijinmu garemu ba."

Dukda sanyi da jikin Haidar yai sai ya kauda Kai gefe dan shi gani yake da mahaifinsa da babu shi duk d'aya ne gwara ma ace babun Watak'ila bazai masa irin k'iyayyan da yake masa a yanzu ba. Duban abokan aikinsu yai kana ya kauda zancen da fad'in "Komai ya kammala saura fara aiki. Soil test ya rage. You take care of the report while I'm away.."

Hisham ya zuba masa ido shaye da mamaki. Ya d'an girgiza kai "While you are away.? What does that mean..? What do you mean by that.?"

Murmushi Haidar yai "It's good to take a break, don't you think."

Har lokacin dubansa Hisham yake da mamaki "Seriously.! Ina zaka Haidar.?"

"To Cuba. Jirgina gobe da safe ne in sha Allah.."

"Business trip.?" Hisham ya tambaya yana dubansa.

"Am I using business terms here.? Bakaji mai nace maka bane. Vocation zan tafi of course."

Hisham ya d'an Ware idanunsa. Kafin ya soma magana Haidar ya dakatar dashi "Don't even start."

Hisham ya jinjina Kansa a hankali "Bazaka saurareni ba na sani. But why Cuba.? Jiya fah nake gani a labarai Hurricane killed at least 6 people there… Couldn't she think of a better place." Ya tambaya yana duban Haidar d'in tinda yasan wann bai wuce aikin Matarsa Dareen ba wacce yayi imani tarayyarta da Haidar d'in Babu wani alheri tinda aure ne da Har yau iyayensa basuda labari.

K'ok'arin bud'e motarsa ya soma "Zamuyi magana kaikam.."

Har ya bud'e motar zai shige Ya juyo ya dubi Hisham murmushi saman fuskarsa "C'mon haka zaka barni na tafi bazaka min fatan alheri ba. What if this is the final goodbye. What if hurricane ya ritsa dani a can.?"

Hisham ya k'araso ya d'an punching muscle d'in Haidar guda "You shut up jerk.!"

Dariya sukayi su duka biyun kafin suka rungume juna Hisham na fad'in zasuyi aikinsu tareda nasara cikin yarda da ikon Ubangiji. A haka sukai sallama kowa naji a cikin zuciyarsa zasuyi kewan juna.

Hisham yai tsaye yana bin bayan motan Haidar da kallo. Murmushi ya saki yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa tinda ba wani aiki mai tsanani da zasu fara yanzu zai tafi Kano. Ya kuma sakin murmushi sanda yake hango beautiful innocent face d'inta a k'awayar idonsa. Ya shirya tafiya neman aurenta wann karon. Ya shirya sanar da ita abinda yakeji gameda ita. Even though he's not expert a wann b'angaren but zaiyi iya k'ok'arin sa ya tabbata bata kufce masa ba. He's been rejected so many times wanda hakan yasa neman aure da 'yanmatan suka fita Kansa. But wann karon ya shirya yak'in Neman auren Ummulkhairi da duka k'arfinsa. Ya kuma sakin murmushi mai kyau zallan k'aunarta na d'awainiya dashi.

**

Yanda Mommy keta faman shiga da fice saida abun yai mugun d'aure ma Anisa kai. Mommy fah tarba na musamman taketa faman shirya ma masu kawo Amaryar Haidar. Jikin Anisa gaba d'aya ya mace, zuciyarta ta karaya ganin yanda Mommy keta d'aukin wann aure. Ta tabbata ko wacece matar Haidar ta gama samun gurbi mai girma cikin zuciyar Mommy dan sosai take son wann aure. Ita gani take Ammi b'ata lokacinta kawai take dan Mommy bazata bari Haidar Ya rabu da matar nan ba cikin watanni k'alilan kaman yanda Ammin nata ta sanar da ita.

Suna jin shigowar Mota Mommy tai saurin mik'ewa tana fad'ad'a murmushinta. Lokaci guda ta dubi Anisa tace maza su sauk'a k'asa ga matar Haidar ta iso.

Saurin rik'o Mommy Anisa tai tana murmushi da yafi Kama da yak'e "A'a haba Mommy. D'an dakata mana kefa uwa ce. Ki bari ni na sauk'a. Ma shigo miki da ita."

Bata jira cewar Mommy ba ta nufi k'asa tana mai rausayar da ido had'ida furzar da huci dan wani mugun takaici ne Ya cika mata zuciya yacce kasan 'yar gwal za'a kawo gidan.

SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU.!*

*23*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Mommy ta gaza zaune ta gaza tsaye. Zuciyarta sai harbawa yake, ta rasa sukuni ne zuciyar nata ya samu sakamakon kawo makarin asirin Haidar da akayi kokuwa yarda da amincewan Haidar Wanda batada tabbas akai ne. Koma dai tsoron abin ya k'unshi rasa rai ne. Sai ta fara tuhumar kanta anya bata kasance mai son zuciya ba. How could she kill another person's child for her own to survive. Saurin girgiza kai tai dan bata son irin tunanin nan su shige kanta. Dole ne yasa tayi hakan. Ance so so ne amma son kai yafi. She needs to save her only son no matter the cost, koda kuwa Ya k'unshi rasa rai ne. Da wann tunanin zuciyarta ya samu natsuwa. Tai zaune cikin kujera tana jiran shigowarsu.

Inna Dije na rik'e da hannun Ummul gam take k'are ma katafaren gidan kallo Wanda ta masa lak'abi da fadan shugaban k'asa.

Suna shigowa wani irin k'amshi ne da zatace hancinta bai tab'a karo da irin shi ba tsaban dad'i shi ya daki hancinta, nan ta hangi wata hamshak'iyar mace wacce kallo guda zakai mata ka tabbata tayima babu bugun girma. Tana ganin Asshe jik'akk'iyar mace wayyaya sai taga ashe gaban Hajiya Kwaise Asshe ba komai bace. Kama daga yanayin suturan dake jikinta muhallinta harma da gogewar fatar ta. Dije ta jinjina kai tana kuma tabbatarwa. Waima Tani bataga wann daula da Ummul ta shiga ba kenan koda kaw ace na wutin gadi ne. Dole Tani ta zauce ta haukace.

Mommy ta fad'ad'a murmushinta tana fad'in su k'araso su k'araso bismillah.

Yayinda Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa. Har lokacin kanta rufe yake cikin mayafi.

Daga yanda take zaune saman carpet tana jin yanda su Inna Dije dasu Aunty Asshe suke gaisuwa da muryar wata mata mai yanayi da shige dana Aunty Asshe. Nan gaisuwar tasu ta sauya salo zuwa yaren k'abilar shuwa arab tsakanin Asshe da 'yaruwarta.

Ita dai Inna Dije tinaninta da k'wak'walwarta sun gaza tantance tsananin kyau da tsarin gidan. Sai juye juye take tana mamakin koda ace auren kwangila na wata uku d'ansu zai da Ummul meyasa sai Ummul a wann irin arziki da suke dashi. Meyasa basu nemo mace da Babu aibu tattare da ita ba sai Ummul. Itafa wann aure Sam bata amince iyaka cin gaskiya Asshe ta sanar dasu ba. Dik yanda akai akwai wata a k'asa. Tunaninta ne Ya katse sanda taga matar ta k'araso gaban Ummul murmushi fal saman kyakkyawar fuskarta.

Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa sanda taga hannun matar saman nata.

Lokaci guda Mommy ke ci gaba da fad'in "Welcome my daughter. Sannu da zuwa cikin ahalinmu. I can't believe this is happening.. Finally Matar Aliyu na ta iso." Sai ta k'arashe tana rungume Ummul daga zaune.

Anisa da Tai mutuwar zaune tana dubansu. Sai ta rausayar da ido cikeda k'osawa tana mai aika ma Amminta wani kallo wacce itama jiki a sanyaye take duban Mommy dake rungume da Ummul tana ayyana farin cikinta a fili.

Mommy kaw cikin zuciyarta take ayyanawa 'Zan kula dake a tsawon watanni uku da zakiyi damu. Sabida kin cancanta. You are my son's savior. Kin sadaukar da rayuwarki dan rayuwar nawa d'an Ya inganta koda ace bakida masaniya akan hakan. This is the least I can do for you bayan sadaukarwa mai girma da kika mana. Zan baki dukkan soyayya da kulawa Har kawo lokacin da zaki warware mugun k'ullin da akai ma D'ana harma da ahalina.' Ta k'arashe tinanin nata idanunta harda guntun k'walla. A hankali ta saka hannu ta yaye rufin da akai ma Ummul. Wani ikon Allah Sai Zuciyar Mommy ya kuma karaya. Fuskar yarinyar take kallo.. She looks so innocent and totally naive. She couldn't help but to feel guilty.. Meyasa rauni Ya cika zuciyarta a kallon farko da Tai ma fuskar yarinyar a zahiri. Tai k'ok'arin saita kanta tana fad'ad'a murmushinta "Barka da zuwa Ummulkhairi, d'ago ki kalleni.. Sabuwar Mamanki..!" Ta k'arashe tana mai tallafo fuskar Ummul wacce ta kasa d'ago idonta ta dubi matar amma jin kalamanta na k'arshe yasa ta soma k'ok'arin d'ago idonta masu cikeda rauni hawaye tab cikinsu.

Dubanta Mommy take Har lokacin tana rik'eda hab'arta murmushi saman fuskarta.

Sai Ummul taji kuka da gaske na zuwa mata musamman da taji matar ta ambaceta da sabuwar Mamanta. Shin tasan Ummanta ta datse alak'a da ita ne..?

Mommy ta soma girgiza mata kai alamun banda kuka. Ta shiga share mata hawayen tana fad'in ta daina kuka ta saki ranta kaman tana cikin Ahalinta.

Mik'ewa Anisa Tai cikeda k'osawa tana rausayar da ido. Ta dubi Amminta ta furta a hankali "I'm tired of this drama.!" Tana fad'in haka tasa kai ta shige.

Su Inna Dije Anci an sha an masu tarban girma ta kuma yarda Lallai Ummul gidan girma ta arziki ta shigo dan ko matar nan bata masu tarba da kayan arziki ba tarban fuska da ta masu da yanda ta amshi Ummul kawai sun isa ta shaida gidan girma da arziki Ummul ta shigo. Koda yake amma Asshe ta sanar da ita Auren na wata uku ne sann ga dalilin auren cewa kwangila suke so a bama d'ansu a kampanin mahaifinsa mahaifin nasa yace bazai bada ba har sai ya kawo masa mata ma'ana Har sai yayi Aure. Shin duk akan AUREN WATA UKU matar nan tai masu irin wann tarba ta kuma karb'i Ummul hannu bibbiyu kaman 'yarda ta haifa.. Anya kuwa..? Ita fah duka abubuwan dake faruwa Sun fara kwance mata kai. Ji take ta gaza fahimtar komai. Koda sukazo tafiya da Ummulkhairi b'angaren Haidar Mommy ce ta rik'e Ummul da kanta tace ita zatai ma 'yarta rakiya. Kan Inna Dije Ya kuma d'aurewa. Suka dubi juna itada Asshe. Asshe ta k'ifta mata ido alamun kar tace komai.

A haka dai aka bama Inna Dije ma nata masauk'in nan cikin gidan da nufin washe gari idan Allah yakai rai zasu koma Kano itada abokiyar tafiyarta Asshe.

Ita kad'ai a d'aki sai sak'awa da warwarewa take. Ta d'au d'amarar kafin su bar gidan kafin su koma garin Kano sai tayi yanda tasan ta fahimci duk abubuwan dake wakana. Batai ma Ummul rakiya zuwa garin ba sai don su koma tare da Ummul d'in. Amma yanda taga Uwar mijin Ummul na kaffa kaffa da ita tana nan nan da ita bata tsammanin Auren zai Mutu a sauk'ak'e. Abu guda ne zai kashe auren nan shine kawai ta bud'e bakinta ta sanar da matar cewa ajalinta D'anta Asshe ta kawo mata cikin gida.

Ta mik'e da zummar fitowa nan taga Asshe tsaye gabanta.

Girgiza mata kai Asshe Tai tace "Koma ki zauna Tun muna mu biyu."

Inna Dije ta dubeta da mamaki. Sai kuma Tai 'yar bazawarar murmushi "Aw baki so mu kasance mu uku ne. Ina nufin ni da Ke da kuma 'yaruwarki wacce kikai mata rufa rufa ki aura ma D'anta ajalinsa. Kar ki tausareni da abun duniya dan yanzu na fahimci kema gaban 'yaruwar taki almajira ce. Sunan mijinki ne kawai kike tink'aho da tak'ama dashi amma da alama Babu abinda auren naki ke tsinana Miki. Da alama yayinki ya k'are wajen miji dole ki nemi hanyar neman kud'i kota halin k'ak'a."

A zuciye Asshe ta dakatar da ita "Kar ki kuskura ki bada shaida kan abinda bakida masaniya. Ina shawartanki kar kiyi gangancin shiga tsakanin 'yanuwa guda biyu. Ina nufin nida 'yaruwata." Ta k'arashe maganar nata tana sakin murmushi kamar ba itace ta sha mur ba.

Lokaci guda Asshe ta k'araso ta dafa kad'an Inna Dije guda tana sakin murmushi "Ki kwanta a saman gado irin Wanda baki tab'a mafarkinsa ba. Ki yada gajiya, kafin ki d'auki hanyar gida gobe dan ba Lallai ki sake karo da irin wann gadon ba. Kar ki mance 'yarku wata uku kacal zatai a gidan nan.!" Ta k'arashe tana k'irga uku da yatsunsa. Lokaci guda ta zaunar da Dije saman gado sai itama ta zauna a gefenta "Ya kamata mu tab'a hira ta k'awaye kafin safiya.. Baki tunani.?" Ta k'arashe tana kashe ma Dije ido. Daidai lokacin Anisa ta shigo da tea cups guda biyu.

Asshe ta fad'ad'a murmushinta "Yauwa 'yar albarka. Kin kawo mana shayin nida k'awata."

Anisa ta jinina kai tana mai ajewa gaba garesu.

Asshe ta d'auko ta mik'a ma Dije "Ga shayin gidan shugaban k'asa. Irin wann ganyen shayin a gidan shugaban k'asa kawai kike gani ki sha ki kafa tarihi ki goranta ma sirakanki ina nufin Tani da Suwaiba." Ta k'arashe tana kurb'an wanda ke d'aya hannun nata.

Ganin Dije ta k'ek'ashe ido tana dubanta Ya sanyata sakin murmushi "Aw na zaci k'awa kika d'aukeni. Kindai san k'awar arziki bazata baki guba ba. Ko dama k'arya kike da kika kirani k'awa.?" Ta murmusa tana kurban shayinta hankali "Ashe k'aryar gogewa kike Dije." TaI maganar tana kuma kurban shayin. Harda lumshe ido tana fad'in "Wani abu sai a fadan shugaban k'asa." Ta shanye nata tana k'ok'arin janyo na Inna Dije da niyyan shanyewa Inna Dije Tai saurin rik'e hannunta ta amshe tea d'in.

Inna Dije na murmushi tace "Yo Dije nake muricin kan Dutse . Idan baki sani ba ban fito ba saida na shirya. Ba wani barikinki da gogewarki da zai bani tsoro." Ta k'arashe tana kafa kai ta soma kurb'an shayi tana lumshe ido.

Kan kace me Inna Dije ta zube kan gado bacci yayi awon gaba da ita. Asshe ta kece dariya tana jinjina k'ok'arin 'yarta Anisa da ta kawo wann plan d'in. Lokaci guda ta gyara ma Inne Dije kwanciyarta tana furta "K'awata ki sha bacci lafiya. Keda bud'e ido kuma sai gobe da safe in sha Allahu." Ta k'arashe tana kuma kecewa da dariya.

A haka Anisa ta kuma shigowa ta tadda Amminta "Gobe da safe jirgin Daddy zai tashi. Mommy zata masa rakiya zuwa airport. Sai kiyi amfani da wann dama Ammi ki fitar da matar nan daga gidan nan da zaran Mommy ta fice. Kinga hakan na nufin bazata samu zarafin sanar da Mommy abinda kike tsoro ba wanda kika kasa sanar dani." Ta k'arashe tana tab'e baki had'ida rausayar da ido Wanda d'abi'anta ne.

Bakin Asshe Ya gaza rufuwa dan farin ciki bata tab'a tsammanin zata samu solution na yanda zatai da matar nan cikin sauk'i ba. Ta dubi Anisa tace "Ni yau kin gama min komai. Ina Miki kallon marar wayau ashe zaki iya had'a plan irin wann. Lallai na yarda banyi ganganci ba da nace You'd become my eyes here."

Anisa ta murmusa "I'm your daughter after all, Ammi."

Asshe ta jinina kai "K'warai yau kin gama tabbatar min. Kuma na yarda zakiyi kaman yanda nace. Koda wasa kar ki bari D'anuwanki Haidar Ya samu kusanci da yarinyar nan. Kiyi duk irin makircin da kikaga Ya dace ki tabbata basu samu kusanci ba a tsakanin watanni uku."

Anisa ta girgiza kai kad'an "Amma Ammi meyasa kika canza ra'ayinki akan yarinyar bayan da kince mun na zama mabudin k'ulla shak'uwa tsakaninsu da Haidar.. Ammi what's with all the mystery behind this marriage.. Ke yanzu kin nuna baki so amma a b'oye ba tareda kin bari Aunty Kwaise ta fahimci haka ba. Ita Aunty Kwaise tana son auren tana son yarinyar da duka zuciyarta. And at the same time baki so wann matar tayi magana da Aunty Kwaise.." Ta k'arashe tana nuna Inna Dije dake zube saman gado tana bacci. Ta kuma girgiza kai "Ammi wai menene b'oyeyyen al'amarin gameda Auren Haidar.?"

Asshe ta sauk'e ajiyan zuciya ta kamo hannayen Anisa "Ki yarda dani Anisa. Zan fayyace miki komai amma ba a daidai wann lokacin ba. Akwai lokacin da zaki fahimci duk abubuwan da nayi. Iyakacin abinda zan fad'a Miki a k'arshe shine zaki mallaki Haidar da izinin Allah. Amma fah sai kinyi aiki tuk'uru Anisa. Kar ki bari Ya kusanci yarinyar nan. Daga k'arshe zamu nemo mafita."

Anisa ta sauk'e ajiyan zuciya "Shikenan Ammi zanyi yanda kikace. After all, bana son auren tin daga farko. Yanzu zan d'auko makaman yak'i na da kika sa nai watsi dasu daga farko." Ta kuma murmusawa kafin tace "Tinda inada ke Ammi, I know I'm not fighting a losing battle."

Suka sakar ma juna murmushi a tare kafin Anisa tasa kai ta fice zuciyarta na mata sanyi. Zatai whatsoever it takes dan ta tabbata yarinyar nan ta fita daga rayuwar Haidar duk tsananin son da Mommy ke mata kuwa. Ta kuma rausayar da ido kafin ta shige.

Asshe ta janyo ma Inne Dije k'ofa kafin ta fito daga b'angaren bak'in ta nufi wajen 'yaruwarta daketa faman neman layin Haidar bata samu.

Zama tai gefenta ganin damuwa ya nuna k'arara saman fuskar Mommy.

"Aunty Kwaise, ya na ganki haka. Allah sa dai lafiya.?"

Mommy ta furzar da huci kad'an "Na gaza samun layin Haidar Har yanzu. Ga amaryarsa ta iso."

Asshe ta jinina kai kad'an "Relax Aunty Kwaise. Ki kwantar da hankalinki.. Yarinyar nan tana nan a gidan nan har tsawon watanni uku. Ki basa space kar ki tak'ura masa da batun a yanzu. Tinda an samu Ya amince kuma yarjejeniya akai dashi so I believe zai zo Har nan kan k'afafunsa."

Readers Also Read