Auren wata ukku by sameena - Chapter 17
Auren wata ukku by sameena Chapter 17: Auren wata ukku by sameena Chapter 17. Mommy da har lokacin ta gaza samun sukuni girgiza kai take "What if ya janye…
4,499 words
Mommy da har lokacin ta gaza samun sukuni girgiza kai take "What if ya janye fah Asshe.? What if wancan makirar ta kuma jifansa da wani mugun asirin fah..? Asshe what if Malaminta yafi namu..? Asshe I'm scared.. Tsoro nake kar duk efforts d'ina su tafi a banza."
Asshe ta kamo hannun Mommy ta zaunarta saman gado "A'a Aunty Kwaise ke uwa ce. Da izinin Allah k'ok'arin ki bazai tafi a banza ba. Haidar zai dawo gareki. D'anki zai dawo gareki. Munyi komai kaman yanda Malam yace. Inada yak'inin hak'armu zata cimma ruwa. Just relax, ki zama calm kuma ki tunk'ari Haidar a tsanake. Yanda kike ta rawar k'afa akan yarinyar zai k'ara tunzura Haidar ne. Kinsan halinsa hasalima kinfi kowa sani tinda ke kika haifesa. Ki bashi gobe zuwa jibi koma satin nan. A hankali sai ki tunk'aresa da batun."
Mommy ta girgiza kai "Sati Asshe..? Toh me zaman me yarinyar zatai a gidan nan idan Har babu wanda tazo domin shi.. Asshe no sati yayi yawa. Kema uwa ce ya kamata kifi kowa fahimtar mai nake ji."
Asshe ta jinjina kai "Na fahimceki Aunty Kwaise. Shiyasa nake k'ok'arin fahimtar dake abinda na hango."
Mommy ta jinjina kai a hankali tana duban Asshe wacce gaba d'aya batada wani kuzari "Asshe." Ta kirawo sunanta in a serious tune.
Zuciyar Asshe Ya tsinke. Kai da ganinta kaga maras gaskiya.
Mommy taci gaba "Akwai abinda ya kamata na sani ne..? Ina nufin, tinda kuka kawo yarinyar nan kin canza. Kaman akwai abinda ke damunki ba kaman lokacin da muka soma shirya auren nan ba. Tell me, is there something I should know.?"
Asshe tai Shiru zuciyarta naci gaba da yankewa sai tanajin tamkar 'yaruwar tata ta riga ta fahimci komai abinka da maras gaskiya.
"Asshe.!" Mommy ta kuma ambato sunanta su duka biyun suna duban juna.
Sai Asshe ta fashe da kuka tana girgiza kai.
Hakan yai mugun tada hankalin Mommy. Bata San sanda ta mik'e ta k'araso wajen 'Yaruwar tata ba. Ta dafata tana tambayarta meke faruwa.
Asshe na hawaye take bama Mommy hak'uri tana girgiza kai.
Cikin rashin Hajiya Kwaise ke girgiza kai "Asshe meyasa kike kuka irin haka. Kuma meyasa kike bani hak'uri.. Wani laifi ne kika min..?"
Cikin zuban hawaye Asshe taci gaba "Na miki laifi mai girma Aunty Kwaise.."
Mommy ta girgiza kai "Laifi.. Wane irin laifi..?"
Anisa da isowarta jikin k'ofan kenan nan tai tsaye ta kasa kunne tana sauraron wani laifi ne mahaifiyarta ta aikata ma Mommy. Cikin zuciyarta Addu'a take Allah yasa taji amsoshin duk tambayoyin da takewa mahaifiyarta gameda wann murd'add'en aure da sukai ma Haidar.
Muryar Amminta ta sinkayo tana fad'in "An sace komai Aunty Kwaise. Kayan lefe na gani na fad'a da kika sa akai ma yarinyar. A lokacin da kayan ya dawo gidana bayan an kai gidansu yarinyar.. A lokacin b'arayi suka biyo dare suka kwashe komai.. Maganar millions of Naira ake.. Shiyasa kikaga dik jikina yayi sanyi ko zarafin fad'a ma yarinyar ma ban samu ba balle danginta."
Shiru Mommy tai tana dubanta. Sai ta jinjina kai a hankali "Kan haka kika tada hankalinki.. Idan dan wann ne Babu wani matsala tinda kwalliya ta biya kud'in sabulu yarinyar ta riga ta shigo hannunmu. Akan auren nan har property na na d'aga na sayar a garin nan.. Kwabon Aliyu Maitama baiyi ciwon kai cikin yak'in neman auren nan ba. So ko nawa zan kashe akan yarinyar nan bazan Ji ciwo ba Asshe because it worth it. Gobe idan Allah Ya kaimu sai ita yarinyar su fita da Anisa ta tayata da shopping kafin mu shawo kan shi gogan. Kinga fitan nasu da Anisa ma zai d'an sa ta kuma sakin jiki sann Anisa ta koya mata wasu abubuwan yanda zamu samun daman shawo kan Haidar Ya amince ya zauna da yarinyar matsayin mata a sauk'ak'e.
Jin haka yasa Anisa sakin tsaki tana juya idanu cikeda takaici tasa kai ta shige dan batai tsammanin abinda za'a ce ba kenan. Ji yanda Mommy keta rawar k'afa kan wann yarinyar. Ita taji ta tafi taje ta k'are mata kallo taga me take dashi haka da Har Mommy ta kasa hangowa tattareda ita.
A b'angaren Asshe kuwa sauk'e ajiyan zuciya Tai dan dama kaya hayansu ta karb'o ta coge kud'ad'e. Dan a wann auren Ummul da Haidar da ta had'a ba k'aramin jari taja ba tinda a halin yanzu mijinta baya yayinta amaryarsa yarinyar Sa'ar Anisa ke cinye kud'in harta da yawon k'asashen waje ya daina yi da ita da amaryarsa yake. Abin sosai yake mata ciwo musamman idan ta tuna yanda tayi nata zamanin kafin ya auro yarinyar. Da alama bokan yarinyar da iyayenta yafi nata aiki ne inji Asshe. Hakan yasa ta buga business d'inta da auren d'an 'yar Uwar nata. Dan haka koda wasa bazata tab'a bari Kwaise tasan gaskiyan al'amari ba.
Sanda Anisa ta tafi sashen Haidar sai cika take tana batsewa ita kad'ai. Ji take tamkar cin fuska ake mata da matar Haidar. Ta ya ma za'a kawo wata kucakaa ajiye gidan da sunan matar Haidar. Gidan da ita da kanta ta shirya komai to her taste wanda takeda tabbacin Haidar d'inta zaiso. Bata hango Haidar tareda wata cikin gidan ba. Gida ne data shirya masu su biyu take kuma hangosu da kalolin soyayyar da zasu sha a cikin gidan harma da yaran da zasu haifa. Ta kuma rausayar da ido tana furzar da huci kad'an kafin ta nufi sama.
Ga mamakin Anisa zaune ta tadda Ummul a parlor har lokacin kanta rufe cikin mayafi. Ta saki baki tana kallon ikon Allah kafin ta girgiza kai had'ida juya ido "Seriously.! Da gaske kina nan kina k'unk'ume a wajen. Kina jiran miji yazo ya bud'e fuskarki.. Lallai kuwa zaki jima kina rufe kaman kwab'in cincin dan ba mijin da zai bud'e wann fuskar naki.!" Ta k'arashe tana fincike rufin fuskan Ummul.
Damm! Haka k'irjin Ummul ya buga sanda taji mai maganar ta finciki mayafin da Mommy ta rufa mata bayan sun kawota sashen.
SameenaAleeyou📚 .*AUREN WATA UKU.!*
*25*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Ya girgiza Kai kad'an disbelievingly "Hajjah.. Ban.. Ban fahimceki ba. Aure.? Ummul tayi aure..?" Ya kuma girgiza Kai "Ina nufin, wane irin aure kuma.?"
"Zauna." Ta fad'i tana nuna masa kujeran dake gefensa.
Jiki a matuk'ar sanyaye Hisham ya ja k'afafunsa ya isa ya zauna had'ida zuba ma mahaifiyarsa ido.
"Hisham, ba wann karon bane ka fara Neman aure baka samu ba. Ka kai sadaki, har an saka rana a wasu lokutan amma daga k'arshe an hanaka. Toh ina so ka saka ma ranka wann bazai zama na k'arshe ba. Kuma shi aure da kake gani nufi ne na Allah. Matar mutum kuma bazata wuce shi ba. A kullum hud'ubar da nake maka kenan. Kar ka saka damuwan rejecting d'inka da akeyi cikin zuciyarka. Lokaci ne kawai baiyi ba amma idan lokaci yayi zakayi Aure. Abinda yasa na maka sha'awan Unmulkhair ba komai bane face aminta da nayi da hankalinta, tarbiyarta da kuma addininta. Kaman yanda yazo cikin hadisin Abu Hurayrah Wanda bukhari ya rawaito 'Manzon Allah (SAW) yace ana auren mace sabida abubuwa guda hudu, sabida dukiyarta, sabida nasabarta, sabida kyaunta ko sabida Addininta. Sai Manzon Allah SAW yace Na horeku da ma'abociya addini hannunka zai samu riba.' Wann yasa nai maka sha'awar Ummulkhair." Ta kuma daidaita zamanta cikin kujeran kafin taci gaba "Bugu da k'ari kaida Ummul kunada k'addara mai kamanceceniya. Dukanku Kun fuskanci k'alubale na lalacewar neman aure kafin akaiga auren. Toh amma a ko yaushe shi mutum ya zama mai d'aukan k'addara da hak'uri da jarabawar Ubangiji a yanda tazo masa. Duk iyaye burinsu kenan. Farin cikinsu kenan suga 'yarsu ta natsu a gidan aure. Haka zalika idan namiji ne suga yayi archiving a rayuwa sann ya zama mutum mai cikan kamala yayi aure. Shi aure abun so ne ba abun gudu bane ba abun k'i bane. Hasalima ya inganta a hadisin Anas dan Malik wanda Bukhari da Muslim sukai ittifak'i akai. Cikin hadisin Manzo SAW ya tabbatar Aure sunnarsa ce kuma wanda ya k'yamaci sunnarsa baya tare dashi. Toh kaga kuwa aure sunnah ce mai girma kuma koyi ne da Manzo SAW. Yayi umarni ma samari da suyi aure ga Wanda Allah ya bama ikon yi. Domin shi aure yana tsare gani da kuma kamewa. Ga Wanda baida hali kuma yayi azumi domin shi azumi garkuwa ne. Hadisin Abdullahi bn Umar wanda Bukhari da Muslim suka rawaito shi." Ta d'an numfasa "Toh kaga duk wad'ann hadisan suna nuni da aure ba abun k'i bane aure ginshik'i ne na ko wani Al'umma. But you can't force it. Kuma ka nemi zab'in Allah cikin duk abinda ka sa gaba. Kana so kana buri kana kuma fatan kayi. Cikin aure akwai tarin albarka kuma ibada ne. Allah ya halicci 'yan Adam jinsu biyu domin su samu natsuwa da juna. Kaga wann natsuwar sai ta hanyar aure za'a samu. Kai hak'uri d'ana, Kai hakuri da jarabawarka. Kai hak'uri da Ummulkhair. Ka cireta a zuciyarka ka nemi wata daban. Allah yasa haka shi yafi zama maka alkhairi da mu baki d'aya."
Sauk'e ajiyan zuciya Hisham yai yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa. Sai ya kifa Kansa na d'an lokaci. Ya d'ago yana duban mahaifiyarsa broken "Hajjah.. Hajjah wanene Ummul ta aura.?"
Tambayar da ya haifar mata da fad'uwan gaba. Ta girgiza Kai kad'an "Shin baka d'auki k'addara bane.? Are you having doubts kan abubuwan da na sanar dakai.?"
Girgiza mata Kai yai a hankali ba tareda da ita cewa komai ba.
Hajjah Fannah ta jinjina Kai "Sanin waye Ummul ta aura baida wani alfanu wajenka. She's someone's wife now. Ka cireta gaba d'aya a ranka kuma kar ka waiwayi baya.. Ka min wann alk'awarin D'ana."
D'agowa ya kumayi ya dubeta. Sai yai murmushi mai ciwo "Kamar yanda kika ce Hajjah.. Zanyi kaman yanda kikace.." Ya mik'e yana kuma shafa fuksarsa "Inaga zan koma bakin aiki ko zuwa… Gobe idan Allah ya kaimu. If that's with you." Ya k'arashe jiki a mace.
Sosai tausayin shi ya cikata. A hankali ta jinina masa Kai "Hakan yayi D'ana.. Allah ya tsareta da tsarewarsa ya baka dukkan kariya. Ya saka maka albarka cikin duk abinda ka sa gabanka."
Ya k'ak'aro murmushi ya sakar mata kafin yasa kai ya shige.
Sauk'e ajiyan zuciya tai tana jin ciwon da D'an nata ke ji har cikin zuciyarta. Shin har yaushe zata ci gaba da b'oye masa.? Shin sai yaushe zata sanar dashi gaskiyan lamari gameda mahaifinsa.? Shin rufe masa da tai tayi daidai..? Shin yaushe zata sanar dashi gameda Ahalinsa.? Shin Anya wann ba alama bace a gareta na cewa ya kamata ta fayyace ma D'anta komai. Musamman da yanzu d'an uwansa ya auri Ummul.? Anya ba baya bane yake hunting d'inta..? Bayan ta datse duk wani alak'ar da take da tabbacin zaisa su waiwaya.. Meyasa kwatsam abubuwa ke neman sauyawa..? Shin Ummul zata iya kasancewa dalilin da zaisa su waiwayi baya.? Ta kuma girgiza kai cikin sauri. A fili take furta "Bana fatan hakan. Allah ya gani tsakani da Allah naso Ummul tamkar 'yarda na haifa a cikina. Watak'ila iyaka lokacin da zamuyi kenan a tare. Tabbas ya zama dole na datse alak'a da Ummul da duk wani abinda zai had'a d'ana da Aliyu Maitama."
**
Abuja…
Tsaf suka fito cikin shirin fita. Doguwar rigar abaya Anisa ta bata ta saka. Da shike kaf dogayen rigunan Anisa ta rage fad'insu hakan yasa ya kama Ummul sosai sai yafi kyau a jikin Ummul d'in saidai tsawo da ya d'an mata yawa sakamakon Anisar ta fita tsawo.
Sai faman yatsina fuska Anisa take tana mata kallon wulak'anci.
Mommy kaw suna fitowa ta mik'e ta isa ga Ummul wacce tuni ta sadda kanta k'asa.
Murmushi saman fuskar Mommy take fad'in "Ki saki jikinki 'Yata. Ki zabi duk abinda kike so. Ko menene." Ta dubi Anisa "Ki tayata ta zab'i kaya masu kyau Wanda zasu k'ara fito da kyaunta. And make sure you take good care of her."
Anisa ta kauda Kai gefe tana rolling ido. Kuji Mommy fah wani wai ta kula da ita saikace watchdog d'inta or something.?
"I'm talking to you Anisa kina kallon wani wajen. Kinsan bana san shashancin nan naki.." Mommy tace ba walwala.
Anisa ta juyo fake smile saman fuskarta "Ok Mommy. Kaman yanda kikace .. I'll take good care of your daughter in-law for you. I promise."
Mommy tace "She's my daughter, not daughter in-law.."
Anisa ta kuma kauda Kai tana fuzar da huci. Sai yanzu ta yarda da kalaman Haidar idan ya kira Mommy good actress. Tayi imani ba a banza take ma wann kucakar makahon so irin haka ba. Yarinyar da gaba d'aya duniyarsu ya banbanta. Su d'in gaba d'aya ma ba d'aya bane. Wai Hajiya Kwaise Maitama ke treating 'Yar talaka haka. Wllhi idan za'a Mutu bazata tab'a yarda auren nan na Allah da Annabi akayi ba. Kuma ko menene ke rufe cikin auren she vowed to find out about it. Sai ta binciko to the core.
Credit card Mommy ta mik'a ma Anisa bayan ta tambayeta zatai driving ko driver ya kaisu. Anisa tace no zata tuk'asu.
Murmushi Anisa ta sakar ma Ummul harda bud'e mata front Seat gaban Mommy. Dan Mommy ta tabbata zata kula mata da sirkarta. Cikin zuciyarta kaw cewa take 'I'll play your little game Mommy har na gano bakin zaren komai.'
A haka suka d'auki hanya.
Suna tafe Anisa ta d'aga waya ta k'ara a kunne "Hello Girlfriend kina ina..?" Ta murmusa "Toh ki bar duk abinda kike let's go shopping." Ta kuma darawa "Ok just wait there yanzu zaki ganni." Tana Ida fad'in haka ta katse kiran.
Tai parking ta dubi Ummul "Ke koma baya zan d'auki k'awata"
Ummul ta dubeta sai ta murmusa. Kaman zata fita sai kuma ta fasa. Ta juyo ta dubi Anisa "Amma ba a gidan baya Mommy tace na zauna ba. Kiyi hak'uri bazan iya sab'a umarninta ba." Ta k'arashe murmushi mai k'untata ma Anisa saman fuskarta.
Hararta Anisa tai kafin taja motar. A haka suka k'arasa kusan wani k'aton gini mai gidaje iri guda a jere.
Can wata budurwa ta fito cikin shigar Wando sai top bajajje wanda bai matseta ba sai d'ankwali d'aure kanta.
Tana k'arasowa Anisa ta bud'e motar ta fito suka tafi a guje suka rungume juna suna kiran juna Girlfriend.
Da mamaki budurwar ta tsaya tana kallon wacce ke zaune gaban motar.
Ta juyo ta dubi Anisa "Neesa wacece kuma wann..?"
Anisa ta rausayar da ido "Kinsan a duniya ba abinda ke burge bakauye irin zaman gaban mota. Kedai shige muje Leenah we gonna shop the entire city.." Ta k'arashe tana d'aga mata card d'in mommy dake hannunta.
Leenah ta shige backseat sai labari suke itada k'awarta Anisa. Tanata k'are ma Ummul kallo wacce batabi ta kansu ba.
Can Leenah Ta bangaji Ummul ta mik'a hannunta jikin radio na motar ta k'ure kid'a. Har lokaci Ummul batabi ta kansu ba. K'arshe hannu tasa ta cikin mayafi ta toshe kumnuwarta dan ita dama ba mai sauraron irin wad'an wak'ok'in na turawa bane.
Sanda suka isa ma gaba sukai suka barota baya. Har sun d'an yi nisa kafin Anisa ta rausayar da ido ta juyo ta dubeta. Nan ta hange Ummul na kokawan d'alewa escalator. Sai kuma ta dubi Leenah "I can't believe this is happening to me. I can't believe we are hanging out da bagidajiya irinta. Dubi abinda take neman wani ya mana video yace tare muke. Anjima mu ganmu ana tagging d'inmu. Nidai yau Mommy ta kashe ni. Wann da kyar idan ba daga kauye aka d'aukota ba dan ba dai cikin birnin Kano ba." Ta k'arashe tana furzar da huci. Daidai sanda Ummul ta k'araso "Kuyi hakuri takalmin ne nakeji kaman zai kadani."
Leenah da Anisa suka dubi juna suka dara a tare. Kafin Anisa tace "Malama karkiji Mommy ta ce na kula dake. If you go missing babu wanda zai b'ata lokaci wajen nemanki dan da alama this is your first time in a place like this."
Leenah ta tab'e baki sai kuma ta nufi wani wajen cikin sauri tana ambaton sunayen designers.
Anisa ta rausayar da ido tana duban Ummul da Leenah ta barsu nan tsaye tare "Baiwar Allah. We are here already. Select what you want.. Ko shima sai na tayaki.?" Ta k'arashe tana kuma rausayar da ido had'ida furzar huci.
Tuni Anisa ta tafi wajen k'awarta Leenah. Suka kyale Ummul ita kad'ai.
Saida suka jida kaya nik'i nik'i suka tadda Ummul tsaye da wasu dogayen riguna da basu wuce uku ba.
Duban juna suka kuma yi kafin Anisa tasa hannu ta finciki Kayan dake hannun Ummul. Ta d'aga kayan sama ta Ware tana gani Leenah na tayata "What.! Are you kidding me..? Wann shine iyakacin abinda kika iya zab'a tuntuni.?" Ta girgiza Kai tana kuma duban Kayan.
Leenah tace "Wai zallan jallabiya ta zab'a. Ina zata dasu.. Ba azumi ake ba balle nace ittik'afi zata shiga."
Anisa ta girgiza Kai tana duban Ummul take d'aga rigunan "Baiwar Allah. We are shopping with Hajiya Kwaise Maitama's card, we can buy the whole mall if we want.. And hello! You are married to Haidar Maitama. So get used to spending a lot."
Leenah baki sake take duban Anisa Jin ta kira budurwar da suke tare matar Haidar. Saurin janyota tai suka matsa daga kusan Ummul.
Leenah ta dubi Anisa "Wait, did I hear that right..? Wann d'in matar Haidar.. Haidar Maitama da na sani. Our long time crush..?"
Anisa ta juya ido "You heard it right. Wai wann d'in matarsa ce. Amma bana tunanin auren mai d'orewa ne dan dai tin jiya da aka kawo masa ita gidan he didn't show up. Mommy ce kawai mai son Auren Amm Wanda akai domin shi baisan anayi ba da alama."
Leenah ta jinina Kai "No wonder. Dan dai wann hanyar da Haidar yabi ma bata isa bi ba." Sai ta kuma gyara tsayuwarta tana duban Anisa "But what about you girlfriend. I know you love your cousin so much. Does that mean.. You give up.."
"Giving up is not in my vocabulary Leenah. You should know better. Kawai lokaci na d'ibar masu. I have to study my target well before I strike.! But trust me sweetheart hakan zai faru ne kafin ta samu kusanci da Haidar." Ta k'arashe makirin murmushi saman fuskarta.
Leenah ta murmusa "Then do it fast sweetheart. Kinga irin wadnn makiran babu wuya sun saye Zuciyar namiji."
Dubanta Anisa take fuska a yatsune. Tai nuni da Ummul wacce mata me kula da kantin keta faman nuna mata wasu kalolin designs din. Anisa ta murmusa ta kuma duban Leenah "Haidar Maitama ya fada soyayya da wann bagidajiyar. You know what Leenah. I hate to burst your balloon but what you're imagining is never ever going to happen." Ta k'arashe tana kuma rausayar da ido.
Leenah ta murmusa "Lallai Neesa toh barikiji na fad'a miki. You'll remember this moment idan baki tashi tsaye tun yanzu kin kawar da ita ba. Ina nufin tun kafin Haidar ya zame Miki k'alubale wajen kauda ita."
Shiru Anisa tai sai kuma tace "I don't want things to reach the point where I have to stain my hands."
Leenah ta murmusa "Then hire someone to do the job for you.. I can't wait to get my hands dirty.." Ta k'arshe tana kashe mata ido.
Juyawa tai ta kalli wani cream yanda aka rubuta do not apply on face. It contains strong fragrances that might irritate your facial skin. Ta murmusa ta kuma duban Anisa "Hey Girlfriend. Daga nan ya kamata mu ziyarci beauty Spa." Tai maganar tana d'auko cream d'in ta nuna ma Anisa. A tare suka dara kafin suka k'arasa wajen Ummul suka ci gaba da tayata shopping kaman babu abinda ke faruwa. Har cewa Anisa take ita tasan taste d'in Haidar so zata zab'a ma Ummul kaya to taste d'insa. Ita dai Ummul bata tankasu ba amma jikinta ya bata wani abun suke shiryawa.
Daga nan Beauty Spa suka tsaya. Ummul ta dubi Anisa "Mai zamuyi a nan."
"Face treatment sweetheart." Ta bata amsa tana unbelting kanta daga cikin kujeran.
"Amma ba abinda ya samu fuskata ni.." Ummul ta bata amsa.
Gajeren tsaki Anisa tai "Beauty treatment ake magana ba sai kinji rauni ba. Dan Allah bani son stinginess naku na talakawa. Mommy card ta bayar mu k'arar dashi akanmu idan munso."
Ummul ta murmusa had'ida girgiza Kai ganin Anisa ta fice zata rufeta a mota.
Koda suka shiga Ummul na hankalce dasu. Anisa da Ummul ake ma gyaran fuskar yayinda Leenah ke tsakani tana jira ta cika aiki kaman yanda suka tsara itada k'awarta Anisa. Ana fara face massage cikin dabara Leenah ta dauko wann cream din ta zuba cikin bowl din da aka kwaba kayan gyaran fuska na Ummul. Tana gama zubawa ta fice dama idon Anisa a lumshe suke sakamakon abinda aka daura mata saman idon.
Ummul ta murmusa a hankali dan taga sanda Leenah ta matse tube din ciki. Aiko nan Ummul ta soma kokawan mik'ewa a birkice jin ana juyata mata fuska alamun bata saba ba. Aiko nan bowls d'in suka fado k'asa saidai basu zube ba. Ummul tai saurin d'aukan na Anisa wacce idonta ke lumshe sai faman tsaki take Bagidajiyar nan na bada ita. Ummul ta mik'a ma mai mata gyaran fuskar robar gyaran fuskan Anisa yayinda mai gyaran fuskar Anisa ta Sunkuya ta d'auki na Ummul dake k'asa tana ce da ita ba komai ta daina basu hakuri.
Anisa ta rausayar da kwayar idonta dake rufe. Takaicin Ummul fal zuciyarta wani b'angare na zuciyarta kuma cikeda farin ciki zata toya ma Bagidajiyar Amaryar Haidar fuska tun kafin ya ganta.
Bata Ida tunanin ba taji wani k'aik'ayi mai gauraye da k'una saman fuskarta. Aiko nan Anisa ta saki k'ara tana tsalle tana ihu tana tambayarsa mai suka saka mata a fuska.
**
Royalton Cayo Santa Maria resort. Cuba…
Tana kwance tana facing view na ruwa. Zuciyarta na mata sanyi. Rayuwar Jin dadi da bata fata wani abu ya katse mata shi. Nan ta bud'e WhatsApp dinta da ta kwana biyu bata waiwaya ba. Sak'onni ne sukaita shigo mata daga wani number da tai saving da . *Shadow.* Kaman jira yake ta kunna nan k'ira ya soma shigowa. Dareen taja garen tsaki. Tasan babu abinda zai tambayarta face mai suke Cuba a daidai wann lokacin bayan kwana biyu bata basa wani update kan Haidar d'in ba. Ganin bazai daina kiraba yasa ta d'aga ba don taso ba.
Tana d'agawa ta fara da "Shadow shadow. Looks like kana biye damu dik yanda muka je. Just like your name.. Before you ask. We are here on our third honeymoon. Oh! I forgot to put my cellphone on DND mode."
Muryar Haidar ta sinkayo daga bayanta "Who is Shadow.?!"
Zuciyar Dareen yai wani irin tsinkewa tamkar statue haka ta kafe ko motsawa ta kasa.
SameenaAleeyou📚
*AUREN WATA UKU..!*
*26*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Ko motsawa ta kasa. 'Yan hanjin cikinta tuni Sun kad'a. A hankali ta zame wayar daga kunnenta bayan ta katse kiran. Muryarsa ta kuma sinkayowa Ya daki dodon kunnwanta a karo na biyu.
"I think I ask you a question. Who were you talking to on the phone. Who the hell is Shadow.?!"
Juyowa tai tana dubansa yanda ya tsareta da rikitattun idanunsa. Alamun yana jiran amsarta.
Abinka da gogaggiya sai tai murmushi "Shadow.. Inuwa.. Asalin sunansa Inuwa.. He's.. He's my cousin.. My cousin that I told you about lokacin auren mu.. Ka tuna..?" Ta k'arashe tana tsaresa da ido.
Kansa ya soma juyawa. Sai yaji ya soma wani tunani wanda bazai iya cewa ga specific abinda yake son tunowa ba. Sai ya zama lost and confused. Dan shi bazai iya cewa ga abinda ya faru lokacin auren nasu ba. Iyakacin abinda yakeda tabbaci akai shine sunyi aure. But baya iya tuna komai in detail.
Dareen taci gaba "Cousin dina da na baka labari. Wanda yake so na ni bana sonsa. Because my heart belongs to you tun kafin mu had'u." Ta kuma murmusawa "Yaron Uncle dina. Shine ya kira wai mu gaisa har kaji ina kiransa Shadow ina kuma ce masa ya daina damuna because ina tareda lovely husband d'ina, enjoying our third honeymoon." Ta k'arashe tana d'aura duka hannayenta saman kafad'unsa makirin murmushi saman fuskarta.
Kansa ne Ya kuma Ji ya cunk'ushe sai ya rasa wane tunani yake guda d'aya. Wani abu yake son tunawa amma bai sani ba. Ya kuma kasa tuna komai. Tinda Dareen ta d'aura hannayenta saman kafadunsa sai ya kuma Ji ya zama confused. Sai ya zama baya tunanin komai cikin kwakwalwarsa baya kallon kowa cikin k'wayar idonsa sai ita.
Dareen ta karkatar da kai tana dubansa har lokacin murmushin ne saman fuskarta "Shall we go now.?"
Girgiza mata kai yai cikin rashin fahimta "To Where.?"
Ta kuma murmusawa tana mai tallafo fuskarsa da tafukan hannayenta "You seem to forget things easily nowadays My love.. Har ka mance. Jiranka nake ka fito mu tafi Spa and fitness.. I thought kace zaka gym."
Shiru yai kaman mai nazari sai Ya karisa saman drawer ya d'auki wayarsa had'ida jefata cikin aljihun wandon three quarter dake jikinsa.
Har ya soma takawa ya juyo ta dubeta "Don't answer his calls again." Ya fad'i cikeda gargad'i.
Saurin jinjina masa kai tai "I'm blocking his number right this instant."
Baice da ita komai ba yasa kai ya shige ba wai dan ya aminta da labaran da ta basa ba sai don Ya k'asa tuna komai.
Bayansa tabi da kallo murmushin saman fuskarta 'Bazaka tab'a sanin waye Shadow ba Haidar.. Shadow has been shadowing you for a long time now.. Maybe tun kafin na shigo rayuwarka. But one thing I'm sure of shine Shadow made a huge mistake da har ya bari na shiga rayuwarka. Because I'll protect you from him. Kuma bazan tab'a bari ya cutar dakai ba for as long as we are together..' Ta k'arashe zancen zucin nata tana take masa baya dan tuni Haidar ya fice.
Motsa jiki yake da iyaka kuzarinsa da k'arfin sa ko zai iya tuna wani abu amma ya kasa. Why couldn't he remember a thing.? Meyasa yake ji kaman brain d'insa na barazanar tarwatsewa.? Meyasa yakeji kaman chest d'insa ya masa nauyi. Meyasa yakeji like he's lost in his own world. Rintse idanunsa yai yana kuma tuk'a keken motsa jikin da iyaka k'arfin sa.
**
Abuja..
Suna fitowa Leenah ta mik'e a birkice tana duban fuskar k'awarta da ya koma jazir abinka da farar fata. Fuskar tayi rod'i rod'i duk tayi jazir kaman k'osan da ya sha wuta cikin mai.
"OMG.! Girl.. What happened to your face…?" Leenah tace tana zaro ido waje.
"Just shut up Leenah..! This is all your fault.." Anisa tace tana sakin huci. Lokaci guda tasa kai ta nufi mota.
Daidai lokacin Ummul ta fito fuskarta ta k'ara kyau sai wani shek'i na musamman da fuskar nata keyi. Sosai gyaran ya amsa fuskarta.
Leenah ta saki baki tana duban Ummulkhairi.
"But..But.. Wait.. How's this possible..?" Leenah tace cikin rashin fahimta.
Murmushi Ummul ta sakar mata kafin tasa kai ta shige ta nufi mota.
Leenah tabi bayan k'awarta Anisa cikin sauri tana tambayarta me Ya faru.