Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 18

Auren wata ukku by sameena - Chapter 18

Auren wata ukku by sameena Chapter 18: Auren wata ukku by sameena Chapter 18. Juyowa Anisa tai tana dubanta da toyayyan fuskarta "You know what Leenah, I…

4,490 words

Juyowa Anisa tai tana dubanta da toyayyan fuskarta "You know what Leenah, I don't want to listen to you. Just get in the car and let's get out of this place..!" Ta k'arashe tana furzar da huci had'ida rausayar da ido.

Saurin rik'ota tai ta dawo da ita baya "Hey hey easy.. Wai mai ya faru ne.. For as far as I know ba ma Ke na zuba cream din ba. How did it end up on your face..?"

Anisa ta rausayar da ido "Because She outsmarted you Leenah.. Isn't it obvious..? You are so useless.!" Ta k'arashe cikin huci tana juya ido.

"Hey easy don't take it out on me. She's the culprit. She switched the bowls." Cewar Leenah tana nuni da Ummul dake zaune cikin mota.

Anisa ta rausayar da ido "That's because you are stupid. You know what Leenah, I feel like punching your ugly face."

Leenah ta shafa fuskarta "Hey don't be mean. I spent so much on this beauty.." Ta k'arashe tana Shafa fuskarta da murmushi.

Rausayar da ido Anisa tai tana sakin huci. Zata shige Leenah tai saurin kamo hannunta. "Girl, if she can do something terrible like this, with that innocent looking face. Then believe me she's dangerous.. She's a wolf in sheep's clothing. You need to eliminate her out of the picture.. As soon.. As possible..!" Ta k'arashe tana firfito da ido waje.

Tururi kurum Anisa take "Believe me Leenah. I won't play fairly this time around..She wants battle? then I'll give her war..Just watch and be amazed.!" Ta k'arashe tana sakin huci.

Leenah ta girgiza kai "You need to change your ways Neesa. Ki fito mata a musulma. Make sure you win her trust first before you make your move."

Anisa ta rausayar da ido "I don't think I have that kind of patience. I can't stand her one bit."

"You have to Neesa. You must put up with her. That is idan har kina so ki kawar da ita cikin sauk'i."

Anisa tai Shiru without saying a word.

Murmushi Leenah ma ta saki amma sai murmushin ya rikid'a Ya koma dariya dan sosai fuskar Aminiyar nata ya bata dariya yanda ya sauya halitta lokaci guda.

"What's got you laughing..?" Anisa ta tambaya a hasale.

Leenah ta soma k'unshe baki tana nuni da fuskar Anisa "Seriously Girlfriend you look like a monster." Ta dubi Ummul da ko kallon yanda suke batayi tace "Ita kuma makirar tayi kyau jibi yanda take glowing.. Awwn I'm jealous of her skin.." Ta k'arashe tana dafe fuska.

Tsawa Anisa ta darara mata tana fad'in ta shige mota su tafi ko ta tafi ta barta nan wajen.

"Oh hey. Easy girl, I'm just joking.. You are still more beautiful than her." Leenah ta fad'i tana take ma k'awarta baya.

Haka suke tafe Mota Leenah na kuma tunzurata da surutanta har dai aka sauk'e Leenah a destination dinta shak'e da kayyayakinta da sukai shopping.

Mota ya rage saura Ummul da Anisa. Ba mai ce da kowa komai har suka iso gida.

Ummul ta dubi Anisa Tai mata godiya wann murmushin Wanda sam Anisa bata k'aunar gani saman fuskarta.

Suna shigowa cikin gidan suka tadda Mommy zaune da wasu mata masu sanye da rigar kampani na tailoring a first parlor.

Ma'aikatan gidan da kusan ko yaushe suke cikin shiga ta uniform suka soma amsan kayyakin hannunsu suna masu sannu da zuwa cikeda girmamawa had'ida ladabi.

Ita dai Ummul duk ba wai ta Saba da irin wad'ann abubuwan bane. Musamman idan taga manyan mutane suna girmamata suna gaisheta koda kuwa masu aiki ne. Sam batajin dadin irin abun. Sosai abun ya bata mamaki da safe kafin su fita yanda Anisa ta dinga masifa ma babban mata dake kitchen wai dan kawai bata kawo mata abinda ta buk'ata kan lokaci ba. Tana jin wacce ta amsa Kayan hannunta tana tambayarta "Ma'am, should I take these to your section..?" Kasancewar akasarin ma'aikatan gidan hiring d'insu akai daga registered company na masu aikace aikacen gida da Office ba hausawa bane ba sosai suke hausa ba.

Sai Ummul tai sakare tana dubanta. Ba wai dan bataji mai tace bane, kawai sabo ne da irin rayuwar da Sam batai ba. Rayuwar da gaba d'aya ya banbanta daga irin rayuwar da ta girma ciki tai wayo ciki.

Mommy ce ta bata amsa da fad'in ta kai mata su side dinta. Wato b'angaren Haidar.

Maid din ta amsa da "Yes Ma." Cikeda risinawa.

Mommy ta k'araso ga Ummul wacce tuni ta risina tana gaisheta.

Bata amsa gaisuwar ba sai kamo hannunta da Tai tana fad'in suje ga masu d'inki zasu gwadata su d'auki measurement dinta. zasu d'inka mata atamfofi da laces daidai size d'inta.

Anisa ta saki baki tana kallon ikon Allah musamman da ta ga babban tailoring company da Mommy ta kira Wanda a garin ma ba ma kowa suke d'inki ba sai ka cika elite. Ko ita kanta Anisa basu tab'a mata d'inki ba sai gashi wai zasuyi ma wann kucakar. Zuciyar Anisa ta kuma tunzura. Tsanar Ummul ya kuma cika mata zuciya. Ko ta kanta fah Mommy bata bi ba balle taga abinda ya samu fuskarta. Cikin k'unan rai ta nufi d'aki tana tuanin sabon hanyar da zata bi ta b'ullo ma Ummul dan bata tunanin zata iya hak'uri da Ummul d'in kaman yanda Leenah ta bata shawari.

**

Kano…

Da kyar Mama ta amince ta fito wajen ganawa da mutane yanda Umma ke jiranta a nan police station da akai detaining dinta.

Umma ta zuba tagumi tana duban Mama yanda ta jeme ta rame duk tsawo da jiki irin na Tani duk ta lalace cikin k'ank'anin lokaci ta zama abun tausayi.

Banda Uwar harara Mama bata aika mata komai.

"Kinzo ne kimin dariya Suwaiba.? Kinzo ne dan kiji dadin ganina a k'ask'ance..?" Muryar Mama ya soma rawa "Ki amsa min Suwaiba. Kinzo ne dan ki min dariyar abubuwan dake faruwa dani..? Ina nufin 'Ya'yana Sun jirge gida. Badia miji ya gudu Ya barta ita kuma Azeema miji ya koreta.. Ni kuma gani a nan cikin k'ask'anci da tozarci.. A yayinda ke Allah ya cika miki burinki. Ummul d'inki tayi aure.. Aure na gani a fad'a irin Wanda nawa 'ya'yan basu samu ba.. Mutanen unguwa sun bar nunaki da baki sun koma nuna ni nida nawa 'ya'yan.. Mijinmu kuma yanzu na k'ark'ashin kulawarki.. Ya zama naki ke kad'ai.. Haka ne Suwaiba..?" Ta k'arashe kuka na b'alle mata yayinda Umma ma kukan take. Cikin zuciyarta cewa take Allah sarki Yaya baki san tashin hankalin da kike ciki mai sauk'i ne gaban Wanda nake ciki. Baki san wani irin aure Ummul Tai ba. Baki san cewa Aure ne mai k'ayyadadden wa'adi ba. Baki san Aure ne da aka k'ullasa bisa yarjejeniya na tsawon watanni uku.. Aure mai gib'i auren da zan jima ina d'an dana sanin yi ma Ummul irin wann auren Har tsawon rayuwata. Sann Mijinmu banida ikon taka yanda yake.

Muryar Tani ya kuma katseta cikin karaji sanda ta soma janyo Umma tana fad'in "Tashi ki tafi Suwaiba. Ki tashi nace ki tafi kuma kar ki sake takowa yanda nake.!"

Kuka Umma take tana girgiza kai "A'a Yaya.. Dan Allah ki saurareni.. Wllhi ko d'aya banzo nan dan abubuwan da kika zayyano ba.. Yaya ki saurareni.." Sai Umma ta rungume Tani tana kuka.. Su duka biyun kuka suke Wanda yafi kama da kukan nadaman rayuwa.

Mama ta fincike jikinta daga rik'on da Umma tai mata. Zata sa kai ta shige Umma ta kuma rik'o hannunta "Yaya dan Allah ki saurareni.. A halin yanzu bamuda kowa sai mu biyun.."

Mama Tani ta goge hawaye da bakin zaninta Wanda yai duk'un duk'un "Yayane Suwaiba..? Ki sanar Dani yayane..?"

Umma ta goge hawayenta da bakin mayafi "Yaya yanzu ba lokaci bane da zamu rik'e juna abokan gaba. Lokaci ne da zamu fahimci dukkanmu masu kuskure ne.. Kuma Allah yana sonmu da ya nuna mana kura kurenmu tun a nan gidan duniya.. Saura ya rage namu mu d'auki darasi ko mu bijire."

Jikin Tani ya kuma yin sanyi wasu hawayen na zubo mata yayinda Umma taci gaba "Yaya babban abinda ya jefa mu cikin halinda muka tsinci kanmu shine son kanmu, rashin tawakkali da yin abu dan mu burge mutane Wanda Har yasa mun mance su waye mu. Mun mance auren mu, mun mance 'ya'yanmu da Allah ya dank'a mana amanarsu. Mun mance mijinmu da yakeda girman hakki akanmu.. Sabida son zuciya irin namu.. Mun mance mu masu kiwo ne kuma za'a tambayemu bisa abinda aka bamu kiwo.. Yaya duk mun mance wad'ann mun saka son zuciya a farko.. Wanda shi ya kai mu ga halinda muka tsinci kawunanmu." Ta kuma jinjina kai tana hawaye "Watak'ila Ummul tayi aure.. Amma ba irin auren da naci mata buri ba.. Dije ta rabani da Khulsum kaman yanda ta rabani da mijinmu.. Nida ke bamuda wani maraba Yaya. Yanda kike rufe a nan babu walwala nima a b'angare na haka take.. Kullum ina kulle ne cikin d'aki Babu walwala." Ta kuma share hawayenta yayinda Tani ta katseta "Wani irin aure ne Ummul Tai Wanda baki ci mata buri ba Suwiaba.?"

Tambayar da ya haifar ma Umma fad'uwan gaba. Koda Ummul AUREN WATA UKU Tai bazata so ta sanar da Tani ga irin auren ba. Hasalima bazata iya ba. Batada wann k'warin gwiwar.

Girgiza mata kai tai "Ki yarda dani Yaya na tapka babban kuskure.." Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.

Mama ta jinjina kai "Na yarda da duka abubuwan da kika fad'a Suwaiba.. Mun tapka kuskure.. Kuma idan bamu had'e kawunanmu yanzu ba bazamu tab'a k'wato mijinmu daga hannun Dije ba. Tazo Har nan ta min d'iban albarka ta kuma jaddada min tinda naci amanar d'anuwanta dake kwance nida fita a gidan yari sai Randa jakin Baba yayi k'aho. Zata tabbata ban samu wani k'ofa da zan tsira ba. Sann yarana sun guje ni. Salima ce kawai ke zuwa nan ta dubani. Amma Azeema da Badia Wanda nake gark'ame nan sabida su sun wofantar dani Suwaiba.." Ta kamo hannayen Umma "Suwaiba dan girman Allah ki taimaka min kafin a tafi Kotu. Sunce cikin satin nan za'a shiga Kotu da mutumin k'auye mai kudi. Dan girman Allah Suwaiba ki taimaka ki nemo kud'd'en nan a fitar dani.. Naga Sirakan Ummul masu hannu da shuni ne. Ki taimaka min Suwiaba ko wajensu kije ki nemo kud'ad'en nan ki fitar Dani a nan.." Ta k'arshe tana tsare Umma da ido. Zuciyarta na tabbatar mata hanyar da zata bi kenan ta samu ta fita daga wann tuggun. Ta nuna ma Suwaiba nadamarta a fili Har dai Suwaiban Tai mata hanyar fita..

Dum!! Haka k'irjin Umma ya buga dan ita kanta bata isa tace ga kalan sirakan Ummul ba. Uwa uba rabuwar da sukai da Asshe Wanda Asshe tai mata iyaka da gidanta.

Tani ta tsare Umma da ido. Cikin zuciyarta take ayyana tinda na sauko da kaina Suwaiba dole kimin abinda nake so. Ta haka ne kawai zan samu na fito har na fahimci mai kike b'oye min gameda auren Ummul.

"Ke nake sauraro Suwaiba, zaki min wann alfarmar.?" Mama tace tana tsareta da ido.

Zuciyar Umma ya kuma tsinkewa. Ta d'ago tana duban Mama cikin sanyin jiki…

SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU..!*

*27*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Umma ta girgiza kai a hankali "Kiyi hak'uri Yaya.. Bazan iya Miki alk'awarin komai ba a halin yanzu." Tai maganar ba tareda ta iya duban fuskar Mama Tani ba.

A dak'ile Mama ke dubanta "Suwaiba.. Kina nufin bazaki taimake ni ba..? Kenan kema kin zab'i a tura ni kurkuku kaman Dije.?"

Umma tai saurin d'ago kai tana girgizawa alamun a'a.

Tani ta gyara zama "Toh idan ba haka ba yaya ne.? Bakida wani maraba da Dije Suwaiba.. Banyi zaton haka daga wajenki ba Suwaiba.." Sai ta fara hawaye "Bayan ke banida kowa Suwaiba.. 'Ya'ya na Sun guje ni.. Mijina na kwance jinya ta cinyesa.. Ke da nake zaton zamu taru mu rufa asirin juna kema kin juya mun baya Suwaiba.?" Sai ta fashe da kuka tana fad'in bata zaci haka daga Umma ba.

Lokaci guda Mama ta mik'e tana huci "Tinda haka kika ce Suwaiba.. Shikenan kije abinki.. Kije kici arzikin sirakanki ke kad'ai. Ni kuma in sha Allahu babu ni babu Ke Suwaiba. Kar ki sake tako inda nake idan har ba taimako na zakiyi ba." Tasa kai zata shige Umma tai saurin mik'ewa ta tareta "A'a Yaya. Dan Allah kar kice haka.. Ni ahalin yanzu banida kowa nima sai ke. Bamuda kowa sai mu biyun.. Amma.."

Katseta Tani tai "Amma me Suwaiba.?" Tai maganar tana tsare Umma da ido.

Gaba d'aya Umma ta daburce bata San mai zata sanar da Mama Tani ba. Bata san ta yanda za'ayi ta sanar da ita cewa itama ta riga ta k'are mata ba. Tai saurin jinjina kai "Toh. Toh.. Yaya.. In sha Allah zan nemo hanyar da zaki fita.."

Mama ta jinjina kai "Yanzu naji batu Suwaiba. Kar ki mance fitowa zanyi muyi yak'in k'wato mijinmu daga hannun azzalumar 'yar uwarsa wacce babu komai cikin zuciyarta face burin fansa dan nayi imani ba tsakani da Allah Dije ke ma Isubu jinya ba. Shi kansa yasan halin Dije Shiyasa tun yanada lafiya ya mata iyaka da yanda yake. Ko dan wann Suwaiba bazamu bari Dije ta rab'esa ba. Ki nemo kud'ad'en bak'auye a biyasa na fito mu k'wato mijinmu uban 'ya'yanmu. Ta haka ne kawai ahalinmu zai kuma samun daidaito. Kin fahimta."

Umma tai Shiru kaman mai nazari sai kuma ta shiga jinjina kai "Na fahimta Yaya. Nima zanso muyi jinyar mijinmu mu samu ladansa. Kuma kuskure ne mun riga Munyi amma munyi nadama. Kuma Allah mai afuwa ne mai yawan gafara."

"Yauwa dai Suwaiba ko ke fah. Nasan kinada fahimta Shiyasa munafukai basu tab'a samun nasaran shiga tsakaninmu ba. Ni 'yaruwa na d'auke ki Suwaiba ba kishiya ba. Kuma 'yan sa'insa da sab'ani da muke samu a baya zama ne Ya kawo haka. Dama shi kansa rayuwar zo mu zauna ne zo mu sab'a. Harshe da hakori ma suna samun sab'ani ballantana mu 'yan adam."

Umma ta jinjina kai "Haka ne Yaya. Zanyi iyaka kokari na in sha Allahu. Allah ya mana jagora."

Mama ta murmusa had'ida amsawa da "Yauwa yanzu naji batu Suwaiba. Ina nan ina saka tsammani. Na d'aura duka yardana akanki Suwaiba." Ta k'arashe cikin yanayi na tausayawa.

A hankali Umma ta jinjina kai duk jikinta a mace haka sukai Sallama da Tani. Tana ficewa Tani ta kece da dariya. A fili take furta "Saidai ba Suwaiba matar Malam Isubu ba. Muje zuwa, da kanki zaki fiddani ni kuma na fidda 'yar naki a gidan auren nata. Tinda 'ya'yana basu zauna d'akin miji ba naki 'yarma bazata zauna ba. Abun yazo gidan sauki dan da alama akwai abinda kike b'oyewa gameda auren. Bazan yi k'asa a gwiwa ba har sai na shak'a iskar 'yanci dan na cimma burina." Ta kuma murmusawa daidai sanda wata 'yar sanda tazo maidata cell dinta.

Umma tana tafe tana lazimi da tinanin ta yanda zata b'ullo ma al'amarin Tani. Zatai iyaka yinta dan ta taimaki Tani tinda ta tabbata idan yau mijinta ya farka Ya gansu sun had'e kawunansu kuma sunyi nadaman duk abubuwan da suka aikata a baya zaifi kowa farin ciki kuma Watak'ila fushin da yake dasu ya gushe. Watak'ila hakan ya zama silan yafe masu duk wasu kurakuren da sukai sanda yake kwance. Toh amma ina ta nufa..? Ina zataje .? Wajen waye zata je ta samo kud'ad'en da za'a fidda Tani.? Asshe kawai ta fad'o ranta. Dan idan ba Asshen ba bata kuma san wajen waye zataje ba. Toh amma sanin irin rabuwar da sukai da Asshe sai ya kuma haifar mata da sanyin jiki. Asshe ta bada umarni ma masu tsaron gidanta cewa ko mai kamanninta suka gani kar su bari ta shiga. Uwa uba had'e kan da Dije da Asshen sukai mata kafin a tafi da Ummul. Ta tabbata idan Har Dije ta k'ulla aminta da Asshe zuwa wajen Asshe had'ari ne. Dan idan har Dije ta fahimci Matan Isubu Sun had'e kai. Wato ita Suwaibar da Tani wani sabon wuta zata kunna masu. Snn abinda take k'ok'arin b'oye ma Tani gameda auren Ummul kuma shikenan ya tashi daga sirri. Dan tayi imani Dije bazata so taga wann had'in kan ba Wanda yake nufin rugujewar shirin duk wani fansarta akansu. Dole tai taka tsantsan. Dole tabi komai a tsanake idan har tana so ta taimaki abokiyar zamanta Tani ta fita daga kurkuku. Da wann tunanin ta sallami mai adaidaita ta shigo gida. Saidai tana shigowa abinda Tai karo dashi ne Ya mugun bata mamaki. Dije ta gani tsaye tsakar gidan ga kayan abinci da kwanaki Suwaibar ta kawo lokacin sunayi da Asshe lokacin yak'in auren Ummul jirge gaban Dije ta kirawo yara tana fad'in maza su fidda mata kayayyakin su kai mata cikin adaidaita dake jiranta k'ofar gidan.

Umma ta saki baki tana kallon ikon Allah "Dije.. Lafiya mai nake gani haka..? Ina zaki kai mana kayan abincin.?"

Kallonta Inna Dije Tai daga sama zuwa k'asa "Makauniya ce ke.? Bayan shahshanci kuma idonki Ya rufe ne Suwaiba.? Tafiya dasu zanyi. Tinda na tabbata da kud'ad'en da kika saida d'iyar D'anuwana kika sayi kayan abincin nan. Ko ma ince su suka baki. Kaman yanda kika sani da zaran an sallamesa daga asibiti ko gidan nan bazai taka ba balle yayi karo da wani tashin hankalin da tsautsayi. Dutse zan wuce dashi ya samu hutu da jinya a can. Kayan abinci kuma zamu buk'ata." Ta k'arashe tana d'aura ma yaro guda kwalin taliya akai.

Umma ta girgiza kai "Amma Dije mai zamuci.? Kar ki mance ba ni kad'ai ce a gidan nan ba. Akwai Badi'a sann akwai Azeema. Idan kika kwashe komai mai zaki barmu dashi.?"

Dariya Inna Dije tai harda shewa kafin tace "Lallai Suwaiba. Yau kece mai fafutakan abinda yaran Tani zasu ci.? Saikace ba kece Tani ke hana naki yaran abincin da ubansu Ya kawo ba. A cewarta bazata girka ma k'artan banza Wanda suka ki aure abinci ba.? Ikon Allah sai gashi yau ke Suwaiba kece kika nemo abinci kika ba ma yaran Tani da suka k'i zaman aure harma girka masu kike. Yaran da ko ganin mutuncinki basayi. Lallai na yarda kin tabbata shashasha Suwaiba."

Umma ta girgiza kai "Dije rayuwar duka nawa take. Ciyar da rai lada ne dashi balle 'ya'yan mijina Wanda jarabawar rayuwa ya fad'a kansu suka baro gidan mazajensu. Babu mahaifinsu a gidan Babu mahaifiyarsu. Gatansu Allah sai ni kad'ai da na rage masu cikin gidan kuma in sha Allahu bazan wofantar dasu ba. Idan Allah ya bani dama da iko na zama mahaifiya a garesu zan zama. Idan ban samu daman gyara kura kuran da nai a baya kan nawa 'ya'yan Ummulkhairi da UmmuKhulsum ba zan kwatanta gyara akan Azeema da Badia cikin yardar Ubangiji Dije. Ki kirani da duk sunan da kikaga dama amma in sha Allahu ni Suwaiba bazan sake maimaita kura kuren da nai a baya ba."

Inna Dije ta murmusa ta matso kusan Umma sosai "Idan dai Tani da iyalanta ne gaki gasu. Sai ki fita ki nemo ki dafa ki basu. Idan ma aikatau zakiyi ki nemo masu wann ke ta shafa. Amma kinga wann abincin Ya haramceku daga ke Har su." Ta k'arashe tana sunkuman kwalin taliya. Kaman daga sama taga Azeema da Badia kanta ko wacce tana sakin huci. Shigowarsu gidan kenan.

Azeema ta nuna mata kwalin taliyar "Ajiye." Ta fad'i cikeda gargadi.

Inna Dije ta dubeta da mamaki "Ke Azeema ni zaki ma rashin kunya."

"Zaki ajiye ne ko zaki jira na tayaki ajewa." Cewar Badia tana shan d'amara.

Inna Dije ta saki baki da mamaki "Ke Badi'a.. Ni zaku ma d'iban albarka ina kanwar Ubanku.?"

"Allah yasa k'anwar uban kikace ba uban ba. Rashin kunya kuma ai mai sauk'i ne wann. Billahillazi akan abincin nan sai mu tara Miki na jaki a nan mu bama idon mak'ota abinci dan kinsan dai wann ba bak'on abu bane a wann k'ofar." Azeema tace tana kuma shan d'amara.

Har lokacin mamaki take baki bud'e "Ni Dije zaku daka ke Azeema.! Eh Lallai! Ai idan bakuyi ba baku cika jinin Tani ba. Ba laifinku bane Kunsha a nono."

"Wllhi Inna Dije zakici bugu a banza dan kin fad'a da bakinki nida kunya dama munyi hannun riga. Ke d'in banza tinda na tafi na tari fad'a da budurwar Habibu mai tak'ama da uniform da bakin bindiga banga uban da bazan taresa ba. Ke mu fah fad'a ma rancenta muke ko ya kikace Badia.?"

Badia ta dubi Inna Dije da bakinta ya gaza rufuwa sabida mamaki "Inna billahillazi idan baki kira yaran nan sun maido da abincin da suka fitar ba wllhi Kinji na ranste Miki kaf takaicin duniya da Tasi'u Ya juye mun zan juyesu akanki. Dan wllhi yanzu a haka hannayena k'aik'ayi suke.!"

Inna Dije ta jinjina kai "Eh na yarda dole ku kasa zaman gidan aure dan babu Wanda zai zauna da shed'anu Irinku. Me za'a tsammata daga wajen yaran da uwarsu ke tsare a gidan gyaran hali."

"Saki nawa aka Miki.? Yaji sau nawa kikayi da wayonmu kafin ki zauna gidan auren.?da wayonmu muna rakaki kome. Naga gado mukai wajenki" Badia tace tana fincikan kwalin taliya dake hannun Inna Dije.

Inna Dije ta jinjina kai tana duban Umma da ta zuba ma sarautar Allah ido. K'wafa tai tasa kai zata wuce Badia da Azeema suka shiga janyota suka nufo waje suna fad'in saita maido kayan abincin da ta sace ta saka a keke napep.

Haka Azeema da Badia suka tirsasa ma Inna Dije ta dawo masu da kayan abinci.

Suka k'araso da kayan suka jirge gaban Umma. Har lokacin ko waccensu da d'amara a kunkuminta. Azeema taci gaba da nuna ma Umma kayan abincin "Kema kiji da kyau bamu k'wata abincin nan sabida Ke ba sai don yunwar cikinmu. Kici gaba da girkawa kina bamu."

Umma bata ce komai ba har suka gama maganganun da zasuyi. Dan tun bayan abubuwan dake faruwa kaman abun nasu k'aruwa yai. Cikin Zuciyarta tabi su da addu'ar shiriya. Ta d'au alwashin zatai hak'uri dasu kuma bazata fasa masu nasiha ba har lokacin da abubuwa zasu daidaita da taimakon Allah.

**

Abuja…

Anisa taci gaba da juya kwalaben turare da Mommy ta bata tace ta kaisu ma Ummul.

Waya ta d'aga ta kira Amminta. Asshe na ganin wayar Anisa Tai saurin d'agawa "Ina sauraronki Anisa meke faruwa.? Shin Haidar yazo gidan.?"

Anisa ta rausayar da ido "No Ammi he hasn't shown up until now. And I don't think zaizo gidan anytime soon."

Asshe ta jinina kai "Toh ina sauraronki, wani abun ne Ya faru.?"

Anisa taci gaba da juya kwalban turaren "Ammi Kince duk abinda ake ciki na dinga sanar dake."

Asshe tace "Eh K'warai. Remember you are my eyes there."

Anisa taci gaba "Ammi Mommy ta bani wasu kwalaben turare guda biyu.. Kaman turaren black khumra amma banaji suna k'amshin khumra.. Tace na bama Ummulkhair.. Lallai Lallai na bata na kuma sanar da ita had'in khumra ne na musamman Mommyn Tai mata kyautar su."

Ai Asshe bata San sanda ta mik'e daga zaunen da take ba. Ta soma tuna lokacin zuwansu wajen boka sanda za'a masu aiki akan makarin asirin Haidar. Boka Ya basu wani turare mai launin bak'i ya kuma ce lallai lallai duk matar da za'a karya asirin jikin Haidar da ita sai ta zamto tana amfani da wann turaren domin kuwa turaren tamkar shine kuran k'arfe da zai janyosa zuwa gareta Har dai sihirin Ya lalace. Idan kuwa haka ne bazata bari Ummulkhairi Tai amfani da turaren ba tinda ita d'in barazana ce ga rayuwarsa.

Baki na rawa Asshe tace "Turaren humra.? Kar ki bata su Anisa..!"

Anisa tace "Meyasa Ammi.?"

"Na fad'a Miki no asking questions Anisa. Just do as I say. Ki zubar ki zuba turaren Khumra cikin kwalban ki bata. But koda wasa kar ki bata wann turaren idan har kina son ki mallaki Haidar."

Anisa ta kuma juya ido "But Ammi what if Mommy ta ba ma Bagidajiyar nan turaren da zata mallaki Haidar ne since she wants her for her son. What if I use it instead.. Kinga sai ya soni bai sota ba.."

K'iris Ya rage Asshe bata kurma kururuwa cikin waya ba jin nata 'yar zata zama makarin asiri "Ke Anisa. Zan tsine miki albarka idan kikai amfani da turaren nan.. Wai ke wace irin shashasha ce. Nace duk abinda nace kiyi kawai kiyi zan miki bayanin komai daga baya.. Just dispose it and replace with natural Khumra. Kin fahimceni.?" Ta k'arashe cikeda gargadi.

Anisa ta furzar da huci dan ta gaji da wann mysteries d'in "Ok fine Ammi. As you wish." Ta k'arshe tana katse kiran.

Taci gaba da juya turaren kafin ta nufi d'aki ta nemo wani kwalban ta juye turaren ciki ta wanke kwalban kafin tai yanda Amminta tace. Can k'asan kayanta ta b'oye turaren da Mommy ta bata Wanda zuciyarta ke raya mata turaren da zaisa Haidar yaso Ummul Mommy ta bayar a kai ma Ummul d'in tinda tana mata makahon so. Idan kuwa Har hunch dinta ya zama gaskiya ita ce wacce zatai amfani da wann turaren dan Haidar ya so ta.

** Gaba d'aya Ji take bata kyauta ba tin bayan abinda Ya faru tsakaninsu da Anisa. Musamman da taga yanda fuskar Anisar Ya b'aci. Ita a halin yanzu ba abokin fad'a take nema ba. Hasalima Tun farko batada abokin fad'a dukda kuwa masu nemanta da fad'an sunada yawa kama daga cikin gidansu har izuwa mutanen unguwa. Khulsum ce ta fad'o ranta wacce a ko yaushe idan an taresu da fad'a ita ke d'aukan fad'an. Tayi nata Tai na Ummul d'in. Ta murmusa a hankali. A fili ta furta "Nayi kewar ki fitananniyar 'Yaruwarta." Ta share hawayen da Ya gangaro mata. tunanin mahaifinta ne Ya fad'o mata sai ta tuna alk'awarin Inna Dije gareta a lokacin da suka kawota cewa kar ta saka damuwan mahaifinta a ranta domin kuwa zata kula dashi cikin yardar Ubangiji. Umma ta fad'o ranta. Sai ta lumshe ido a hankali tanajin kuka na zuwa mata. Kalaman Umma na k'arshe a gareta su take tunawa cewa kar ta nemeta kar ta nemi kowa cikin danginta Har na tsawon watanni uku koda kuwa a wayan salula ne. Meyasa Umma zata yanke mata hukunci mai tsauri irin wann. Shin ko haka take a al'adarsu idan anyi aure sai bayan watanni uku kai magana da ahalinka.? Bata jin hakan ne. Ta lumshe idonta wasu hawayen suka kuma gangaro mata.

Tana a haka taji ana knocking a b'angaren ta. Ta mik'e Tai k'ok'arin kintsa kanta kafin ta nufi k'ofa.

Ga mamakinta Anisa ta gani tsaye tana sakin huci.

Ummul ta sakar mata sassanyar murmushi had'ida bata hanya "Bismillah shigo."

Anisa ta watsa mata harara kafin tasa kai ta shigo. Sai faman yatsina yank'wanannen fuskarta da bai Ida warkewa ba take.

"Ba zama nazo yi ba. Ban kuma zo dan na rama abinda kika min ba dan naga kin sha jinin jikinki. Sak'o Mommy ta bayar a kawo miki." Tai maganar tana mai aje turaren saman centre table.

Readers Also Read