Auren wata ukku by sameena - Chapter 19
Auren wata ukku by sameena Chapter 19: Auren wata ukku by sameena Chapter 19. Ummul ta katseta "Ni ban miki komai ba Anisa. Ke shaida ce keda k'awarki ku…
4,498 words
Ummul ta katseta "Ni ban miki komai ba Anisa. Ke shaida ce keda k'awarki ku kuka shirya abunku."
Ganin Anisar ta tsareta da ido Ya sanyata samun k'warin gwiwar ci gaba "Ni bana nemanki da fad'a. Kuma ki yarda dani har cikin zuciyata banji dad'in abinda Ya sameki ba."
"Oh please shut up! Spare me your false sympathy." Taci gaba da takowa gaban Ummul. Tana huci take nuna fuskarta. Muryarta ya soma rawa alamun kuka "Just look at my face.. Look at what you did to me. Kalli yanda fuskata ta lalace.. This is what you want right.? Farin ciki kike ko..? Na sani tun farkon zuwanki gidan nan baki sona.. Amma ban tab'a tunanin zaki min abinda kika min ba. Leenah ita ce ta zuba miki cream din ba ni ba. Meyasa kika zab'i b'ata nawa fuskar… It was Leenah's plan and not mine. Bansan ta shirya Miki haka ba amma ki zab'i cutar dani. Look duba kiga abinda kika min." Ta k'arashe cikin kuka.
Jikin Ummulkhairi yai sanyi. Ta soma girgiza kai "Anisa ki yarda Dani banji dad'in abinda ya samu fuskarki ba. Amma ki sani shi rayuwa abinda ka shuka fah shi ke dawo maka. Idan khairan khairan idan sharri sharri. Ya kamata ki d'auki darasi cikin abinda Ya faru."
"You are not in a position to dictate to me what I should do with my life. Idan kuma shawari ne ban nema ba. We are not even friends to begin with." Ta k'arashe tana juya ido.
Ummul ta kuma girgiza kai "Ni bance mu zama k'awaye ba. Amma ki sani bana neman abokin fad'a."
Anisa ta kafeta da ido sai kuma ta marairaice fuska ta k'arasa saman kujera ta zauna tana Shafa fuskarta. Ta d'ago tana duban Ummul da idonta masu zuban ruwa "You are right you know. Duk abinda ka shuka a duniyar nan shi yake dawo maka. At first I hate you Ummul.. Bazan b'oye Miki ba. Ina kishinki musamman ganin yanda daga zuwanki gidan nan hankalin Mommy da soyayyarta gaba d'aya ya koma kanki." Ta mik'e Tai tsaye gaban Ummul da idonta masu zuban ruwa "I'm not a bad person Ummulkhair. I'm so sorry for everything I did to you.. I don't want us to fight anymore.. Ko bamu zama kawaye ba I believe we can get along and live in peace.." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta. Ta mik'a ma Ummul d'in hannu murmushi saman fuskarta "Mu mance komai mu zauna lafiya."
Sosai Ummul tasha mamaki da sabon sauyin Anisar. Amma sai ta murmusa ta mik'a mata hannu sukai musabaha. Anisa Tai saurin hugging d'inta tana fad'in fad'a tsakaninsu Ya k'are tayi alkawari.
Ta dubi saman dining table yanda abinci suke nan a jere alamun tinda aka kawo ma Ummul d'in bata ko tab'a ba.
Ta murmusa ta dubi Ummul "Don't tell me you still haven't eaten. Koda yake zaman kad'aici Babu dad'i. Come zo muje. Barin tayaki cin abincin."
Ta janyo hannun Ummul suka nufi dining table. Anisa tace da Ummul ta zauna ita zatai serving d'insu. Ta zuba abinci ta shirya table.
Nan suka zauna suna facing juna itada Ummul d'in. Ganin Ummul ta matsar da table knife gefe yasa Anisa murmusawa tace "Ya kamata ki koyi cin abinci to our level. You must keep your table manners. And that includes the use of utensils. Kar ki mance ke sirkar gidan nan ce a yanzu. Hakan na nufin, your social status has changed. You should learn how to mingle with upper class people. Mijinki Haidar mutum ne da ya girma cikin wayayyu sann yake hulda da wayayyun mutane, so you must adopt our lifestyle." Anisa ta k'arashe tana gyara zamanta ta d'aura napkin saman laps d'inta. Sai faman kwarkwasa take.
Ta dubi Ummul tace tai irin zaman da Tai.
Murmushi Ummul Tai had'ida yin yanda Anisa tai.
Anisa tace "Good. Haka wayayyun mata ke zama bisa table especially in public. Yanzu ki d'auki fork and knife muga."
Ummul ta kuma murmusawa dan harga Allah dariya Anisa ke bata. Nan tai yanda Anisar tace. Anisa ta girgiza kai "No, fork should be in your left and knife in your right. Like this." Ta k'arashe tana nuna mata.
Murmushi Ummul ta kuma yi. Sai ta girgiza kai wann karon " Amma addininmu harma da al'adarmu basu koyar damu cin abinci da hannun hagu ba. Shed'an shi yake cin abinci da hannun hagu."
Anisa ta kauda fuskarta gefe tana juya ido. She had no other option than to put up da wann Bagidajiyar.
Sai ta juyo ta murmusa "Of course you are right. Kinyi gaskiya. Na gode da kika tunasar dani." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta. A haka sukaci abinci Har Ummul Tai mata rakiya sanda zata tafi.
Sai mamakin canzawar Anisar Ummul d'in take. Amma cikin ranta taji dad'i da suka shirya da Anisar dan harga Allah bata neman abokin fad'a.
Anisa tana shigowa ta tadda Mommy zaune a parlor alamun tana jiran shigowarta.
"Mai ya tsaidake can.? Shin kin bata turaren da na baki ki bata ko kin tsaya shashancinki ne." Mommy ta tambaya tana duban Anisar .
Murmushi Anisa tai "Na bata Mommy. Tace ta gode sosai. Taji dadin kyautar dan tin kafin na bar wajen ta shafa." Annurin fuskar Mommy ya k'aru jin tayi amfani da turaren. Anisa taci gaba "Na tsaya na tayata cin abinci ne Mommy. Sai kuma na mata hira.." Ta k'araso ta zauna kafin taci gaba "Da alama kad'aici na damunta. Dan ko abinci bata wani iya ci. Kar kiga yanda taci abinci sosai da muke tare.." Ta kuma muskutawa "Em Mommy nace why not gobe Ummul ta shigo muci abinci gaba d'aya tare. Zata d'an rage kewa kuma zata k'ara samun daman sakewa damu tinda har yau Haidar baizo ba.."
Mommy ta murmusa "Da alama ku biyun Kun fara sabo sosai. Sai ki samu ma'aikatan kitchen ku shirya komai."
Anisa ta murmusa "Okay Mommy.." Ta mik'e tana murmushi. Har ta soma tafiya ta juyo "Em.. Mommy nace, can I invite my friend over..?" Sanin ba ko wani shirgi Hajiya Kwaise ke bari a kawo mata cikin gida ba Shiyasa ma ta tambaya.
Mommy ta jinjina kai "Of course you can.." Tai maganar tana murmushi zuciyarta fari sol tinda Anisa ta sanar da ita Ummul tayi amfani da turaren da ta bata. burinta Ya kusa cika. Haidar d'inta zai dawo gareta.
**
Saida Anisa tai shirin kwanciya kafin ta d'aga waya ta kira Leenah. Tana tsaye gaban mirror tana cleansing soyayyan fuskarta da auduga taci gaba "I told you Leenah. Yarinyar nan sai tayi nadaman soyan fuska da tai. Zamanta a gidan nan yazo k'arshe. Kedai kizo da wuri ki sha kallo. Kar ki damu na karba Miki katin gayyata daga wajen Hajiya Kwaise Maitama dan kinsan da k'a'ida ake shigar mata gida. Matsalar kawai I need someone who can help me to carry out my plan ."
Leenah ta murmusa "Girl I've got your back. Just say the word kiga aiki da cikawa."
"Oh shut up Leenah! As if your tiny brain is capable of helping me out.. last time I checked stupidity dinki ne yasa fuskata ta soye."
Leenah ta murmusa "Haba Neesa trust me we re not going to repeat the same mistake.. You need me. After all, I'm the only one you can count on."
Shiru Anisa tai "Fine. But wait , if you screw up my plan Leenah. I swear I'm going to kill you myself."
Leenah ta murmusa "I'm on it girl. Kar ki damu zamu shirya komai ta yanda yarinyar zata bar gidan a gobe. I give you my word."
Jinjina kai Anisa take tana sakin murmushi lokaci guda tana duban fuskarta a mirror. A fili take furta "Tomorrow I am going to get rid of my problem. Goodbye to you. Ummul..!" Ta k'arashe tana mai fashewa da dariya had'ida duban kanta cikin mirror.
**
Bayan ta Ida shirin baccinta alwalwa ta d'auro ta soma jero nafilfili tana kai kokenta ga Rabbil Izza. Kama daga kan sabon rayuwar da ta tsinci kanta ciki zuwa ahalinta da ta baro Har dai izuwa kan wann k'addararren aure da Ubangijinta Ya jarabceta dashi. Auren da batada tabbaci akan makomarsa auren da har kawo wann rana bata san kalan mijin ba bata kuma da tabbacin mijin Ya san da ita. Dan dik kyautatawa da d'imbin alherin mahaifiyarsa gareta bata tab'a jin a ranta ta samu sukuni cikin fargaban abinda ka iya zuwa yazo cikin auren. Addu'a ta dingayi Allah ya shiga al'amarinta. Idan har akwai alheri a cikin auren. Idan har zamanta alheri ne a gidan Allah Ya kawo mata komai cikin sauk'i. Haka zalika idan Babu wani alheri Allah Ya sauk'ak'a mata ya kawo hanyar da zata bar gidan cikin sauk'i. Ta jima sosai tana kai kokenta wajen Ubangijin da Babu abinda yafi k'arfin buwayarsa. A nan kan sallayarta bacci yai gaba da ita.
**
Cuba..
Bacci yake yana jin Kansa na juya masa cikin baccin. Nan kuma ya soma mafarki da mahaifiyarsa. Mommy ya gani durk'ushe gabansa tana kuka hannunta rik'eda farin takarda. Tana fad'in mahaifinsa yayi canceling project d'insa. Saurin amsar takardan yai daga hannunta saidai yana ware takardan yaga sab'anin abinda Mommy tace. Domin kuwa takardan sakin mahaifiyarsa ya gani wai Daddy ya saki Mommy. Juyowa yai bayansa yana huci kaman zai shak'e Daddy yana fad'in maiyasa zai saki mahaifiyarsa. Daddy bai basa amsa ba saima nuni da yai masa da bayan wata mace tana tafe tana jan akwatinta. Jikin Haidar yai sanyi sanda Daddy ke fad'in 'Mahaifiyarka ita ta saka nata Auren cikin had'ari dan wanzuwar AUREN WATA UKU. Ka tuhumi kanka Aliyu.!'
Daga haka ya farka daga baccin duk ya had'a zufa. Nan yaga yamma ne sosai a agogon Cuba. Around karfe shida na yamma. Ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa yana mamakin baccinsa a daidai wann lokaci. Ba bacci bane yafi basa mamaki kaman mafarkin da ya tsinta kansa da yi cikin barcin. Meyasa hankalinsa ya tashi sanda yaga Mommy na kuka a cikin barcinsa. Baya son ganin hawaye. Baya so yaga ana kuka amma ya sani hawayen Mommy bai tab'a damunsa ba. Meyasa ya tsinci kansa yana mai damuwa da hawayenta cikin barcinsa. Meyasa zuciyarsa tai zafi da yaga mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa.? Wann shine abinda yake fata yake buri tsawon rayuwarsa ahalin ta ruguje ta lalace. Meyasa hankalinsa zai tashi bayan abinda yake buri ne Ya faru cikin barcin nasa. Ya furzar da huci a hankali yana kuma shafan fuskarsa. Can k'asan zuciyarsa ji yai yana son kiran Mommy amma wani b'angare na zuciyarsa na kuma tunzurasa gameda al'amarin iyayen nasa. Why would he even care. Toh su rabu mana for all he cares. Yai gajeren tsaki kafin ya mik'e yana neman Dareen yanda ya hangeta cikin pool tana waving d'insa tana fad'in he should join her.
**
Washe gari ta kama Alhamis hakan yasa Ummul ta tashi da azumi dan dama azumin litinin da alhamis basa wuceta hasalima Sun zame mata jiki.
Anisa ce ta shigo Tai inviting b'angaren Mommy kaman yanda Mommyn ta buk'ata a Cewar Anisa. Ummul ta shirya tsaf kafin suka jera suka nufo b'angaren tareda Anisa.
SameenaAleeyou📚
*AUREN WATA UKU..!*
*28*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
A parlour suka tadda Mommy. Tana ganinsu ta fad'ad'a murmushinta. Ummul ta k'araso ta zauna daga can bakin carpet ta gaida Mommy. Bayan Sun gaisa Mommy ke ce da ita ta dinga shigowa b'angaren tana cin abinci tare dasu duk sanda take son hakan sabida zaman kad'aicin babu dad'i. Murmushi kurum Ummul tai dan harga Allah sosai take jin nauyin Mommy dukda k'ok'arin janta jiki da take. Nan take mata godiyan turaren da Anisa ta kai mata injita. Mommy ta murmusa tace Babu komai. Cikin zuciyarta kaw dad'i ne ya mamayeta. Daga k'arshe burinta yana gab da cika. Haidar ya gama gudunsa duk yanda zaije amma tanada yak'inin aikin Malaminsu zai tasiri akansa.
Anisa ce ta janyo hannun Ummul tace ta taso su duba ma'aikatan a kitchen. Aiko kaman wacce take kan k'aya ta mik'e tabi bayan Anisa.
A kitchen d'in ma saida ta janyo Anisa suka keb'e ta d'an mata nasiha kan wulak'anta d'an adam koda na k'ark'ashin ka ne. Musamman da taga yanda duk ta birkita ma'aikatan da tsiwa.
Anisa ta kauda fuska tana rausayar da ido. Cikin zuciyarta fad'i take ki gama duk wani kilibibinki bayan abinda na shirya Miki kin zama tarihi a gidan nan. Zuwan Leenah yasa Anisa barin kitchen d'in dan security personnel sun kira daga can gate sun sanar Anisa tanada bak'uwa. Hakan yasa bata bi takan Ummul ba ta fice.
Ummul na tsaye gefe ta hangi madara kan wuta yana gab da zuba. Cikin sauri ta isa ta d'auki abun motsawa tana juya dan hanasa zuba.
Chef d'in da bata jima da barin wajen ba ta k'araso da sauri tana bama Ummul hak'uri da fad'in urgent call ta samu daga gida Shiyasa ta tafi amsa kiran.
Ummul ta murmusa had'ida girgiza mata kai "Laa babu komai kar ki damu nima nayi kewan aikin ne. Ban Saba zama haka nan bana aiki ba. Duk sai ina jin ba dad'i." Ta k'arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta. Dan ta lura cikin ma'aikatan wann wacce ta d'an manyanta mai kula da sauran 'Yanmatan dake kitchen din ita kad'ai taji tana hausa sosai.
Matar ta d'an murmusa "I'm the chief chef here. I'm the one supervising and monitoring the kitchen staff. Kar ki damu munada yawa a nan.. Zamuyi komai kan lokaci in sha Allah."
Ummul ta murmusa kad'an "Amma zan d'an iya tsayuwa a nan na tayaku da wani abun..?"
Matar ta kuma murmusawa "I'm afraid you can't. Idan Madam tazo taga mun baki aiki zai iya shafan namu aikin musamman ni.. Kar ki damu zamu kula da komai a nan.. Kije kawai."
Ba don Ummul taso ba ta jinjina kai ta nufi k'ofa matar sai sakar mata murmushi take.
Tafiya take a katafaren gidan tana waige waige. Tabbas batada tabbaci idan bata b'ace hanya ba. Tana tafe tana tinanin ta ina zata bi nan ta hangi wani k'ofa tabi k'ofar. Wata ma'aikaciyar gidan mai sanye da uniform ta gani.
Budurwar ta tambayi Ummul "Ma'am, are you looking for someone.. Do you need something..?"
Ummul ta dubeta sai tace "Hanya nake nema dan Allah."
Budurwar ta murmusa "Oh that's the way to the main house Ma'am." Ta k'arashe tana nuna ma Ummul b'angaren dama.
Ummul ta jinina kai a hankali kafin Tai mata godiya tabi hanyar da budurwar ta nuna mata. Tana tafe taga wani k'aton hoto manne a wani madaidaicin parlorn mai kaman waiting. Ta gane Mommy a hoton dukda k'uruciya da ya nuna a fuskar Mommyn. Gefe da Mommy wani mutumi ne mai Kamala da bata tantance ba amma tanada tabbacin shine mai gidan kenan. Tsakiya dasu wani yaro ne Wanda duka duka bazai gaza shekaru 10 ba. Kansa an tara masa suma irin mai laushin nan da cika. Ga kamannin iyayensa d'auke a fuskarsa. Yanda yaron ya b'ata rai cikin hoton ga fuskarsa da Ya buya cikin sumar kansa sosai abun yaso bata dariya musamman da taga kaman ita yake harara. Kai da gani kasan camera yasha harara kaman dai Wanda aka masa dole.
Muryar su Anisa da ta soma jiyowa ne Ya janyo hankalinta. Ta nufi hanyar da take sinkayo muryoyin. Nan ta kuma cin karo da wani hoton a wani dogon corridor. Saidai wann hoton matashi ta gani tsaye gaban wani k'atoton zanen gine gine hannunsa rik'eda wani k'aramin abu kaman kara yana nuna ma mutanen dake zaune saman kujeru bayansa zanen dake gabanshi. Ko ba'ace ba zaka fahimci ma'aikata ne. Matashin yana sanye da suit saidai fuskarsa bai bayyana cikin hoton ba sakamakon Ya bada baya alamun yana bayani gameda hoton dake gaba gareshi. Bata san dalili ba amma kallo guda Tai ma mutumin dake cikin hoton zuciyarta ya yanke. Ta tsinci kanta da fad'uwan gaba dukda ba wai ganin fuskarsa tai ba.
A haka tana nan tsaye su Anisa suka k'araso suka taddata. Anisa da Leenah suka dubi juna kafin Anisa ta k'araso murmushi saman fuskarta. Tai tsaye gefen Ummul dake duban hoton.
"Aliyu Haidar Maitama. D'a d'aya tilo ga Engr Aliyu Maitama da kuma Hajiya Kwaise Maitama." Abinda Anisa kenan tace Wanda ya kuma haifar ma Ummul fad'uwan gaba. Kenan wann shine Aliyu.. mijinta.? Sai ta kuma jin zuciyarta na bugawa da sauri. Musamman da Zuciyar nata ta ambacesa da mijinta wanda ko shakka babu da kokonta zuciyar nata ta raya mata.
Anisa ta murmusa tana ci gaba da kallon hoton "Mutumin da manyan mujallu ke rubibin hasko fuskarsa yana guje masu. Da matuk'ar wahala kiga hotonsa koda cikin mutane saidai a bazata." Ta kuma murmusawa "But If you read papers definitely zaka iya sanin fuskarsa. Dan bana tunanin wann d'anuwan nawa has any social media account." Ta kuma murmusawa tana girgiza kai "I guess my cousin is allergic to camera. He is the weirdest person with high standards I've ever known." Ta juyo ta dubi Ummul "Shall we.. Abinci is ready ke muke jira ranki dad'e."
Ummul ta murmusa kad'an "Saidai ni Ina azumi yau d'in.."
Anisa da Leenah suka dubi juna. Anisa tace "Azumi ba cikin watan azumi ba."
Ummul ta kuma murmusawa "Yau d'in alhamis ne akwai falala cikin yin azumi a wann ranar."
Leenah ta kauda fuska gefe tana rausayar da ido cikeda k'osawa yayinda Anisa ta murmusa "Wow. A gaskiya kin burgeni Ummul. Zan so na koya daga wajenki."
Batace da Anisa komai ba sai murmushi da tai. Anisar ta janyo hannunta tana fad'in suje she can wait in her room idan bazata zauna a table din ba. Nan d'akin Anisa suka baro Ummul d'in yanda Anisar da Leenah suka nufo teburin cin abinci.
Mommy ke tambayarsu ina Ummul d'in.
Anisa ta waiga kaman wacce take nemanta "Oh mun fito tare daga d'akina.. But where has she gone.?" Tai maganar fuskarta d'aukeda alamun tambaya.
Leenah tace "I think naga komawarta cikin d'akin. Maybe ta mance wani abun.. Or she's Probably using the bathroom."
Mommy bata ce komai ba taci gaba da cin abincinta. Can wayarta yai ruri ta tashi daga table din tabi wani k'ofan tana amsa kiran.
Leenah da Anisa suka dubi juna suna murmushi daidai lokacin Ummul ta fito. Su biyu ta tadda a table d'in.
Anisa ta fad'ad'a murmushi sanda taga fitowarta "Har kin fito. Sorry we left you alone. Gashi na mance ban kunna miki Kayan kallo ba. You must be bored."
Ummul ta girgiza kai "A'a kar ki damu babu komai. Ina so na koma ne naga garin da hadari na bar wasu Windows a bud'e."
Leenah ta girgiza kai "Haba Ummulkhair kan wann zaki wahalar da kanki. Umarni kawai zaki bawa ma'aikata su miki.. Wai ko Har yanzu baki gane matsayinki bane a gidan nan.? Kinga koma abinki kiyi zamanki yanzu zamu shigo nasan kunya kikeji. Bazaki iya zama ki saka surkarki gaba tana cin abinci ba dikda ita Mommy normal ne wajenta abinki da civilized woman." Ta karkato sosai tana duban Ummul "Kinada babban sa'a Ummul. Mata da yawa suna burin ina ma ace sune a matsayinki. Wayayyun mata Wanda suka had'a komai na rayuwar duniya. If I were you, bazanyi wasa da wann damar ba." Ta kuma murmusawa "Kar ki damu a hankali zaki koyi irin rayuwar." Ta k'arashe tana sakar mata murmushi kafin Ta mik'e tana fad'in "I'll ask one of the maids ta rufe windows din." Bata jira Cewar Ummul d'in ba ta wuce b'angaren ma'aikatan cikin sauri Kai kace itace 'yar gidan. Anisa ta dubi Ummul d'in da murmushi.
Ummul Tai tsaye kaman mai tunanin wani abu. Magaganun Leenah take kuma nanatawa cikin kanta. Sai tanaji tamkar wani sak'o Leenar ke son bata a dunk'ule. Allah sarki da ace Leenah tasan ita wann auren ba da son ranta akai ba. sadaukarwa ne kawai ga ahalinta da bata fad'i abinda ta fad'i ba.. Ta d'anyi still a wajen sai kuma ta juya ta koma d'akin Anisar dan gabatar da sallar la'asar da aka soma kira.
Bayan Sun gama cin abinci suna zaune suna hira nan d'akin Anisa gaba d'ayan su ukun. Da alama harta Leenah ta saki jiki da Ummul. Har kana iya jiyo shewan Leenah da Anisa alamun hira ta masu dad'i. Ita dai Ummul saidai tai murmushi idan an fad'i wani abun bakajin muryarta.
Suna tsaka da hiran suka soma sinkayo muryar Mommy tana doka kira ma ma'aikatan gidan.
Anisa Tai shiru tana fad'in "Kai ku saurara kuji.. Meke faruwa.? Kaman muryar Mommy nakeji cikin fad'a."
Gaba d'aya suka saurara aiko nan suka sinkayo muryar Mommy tana fad'in kaf ma'aikatan su hauro parlornta.
Anisa tace maza su tashi suje suji abinda ke faruwa.
Suka mik'e gaba d'ayansu suka nufo parlorn Mommy yanda suka tadda ta had'a assembly ma gaba d'aya ma'aikata tana tambayar waye ya shigar mata d'aki cikinsu.
Wann ya dubi wancan wancan Ya dubi wann. Kowa yace bai shiga ba tin gyaran safe.
Mommy ta d'ago wani d'an box hannunta. Cikin tsimewa taci gaba da fad'in ta tadda jewelry drawers d'inta a bud'e kuma an d'auki sark'ar dake cikin box d'in hannunta. Waye ya d'auka.?
Anisa ta zaro ido waje "Mommy sata cikin gidan nan..? This is something unusual.. Abu ne da bai tab'a faruwa ba."
Mommy taci gaba da jinjina Kai "If there's one thing I hate shine rashin gaskiya. Abu ne da akayi shi a cikin gida. And that's why dole a fito da koma waye yayi satan. If it takes ayi searching every angle na cikin gidan nan ne za'ayi. Kayan kowa cikinku kaf sai an bincika." Ta k'arashe tana duban ma'aikatan.
Anisa ta jinjina kai "K'warai Mommy a duba ko ina cikin gidan nan. I'll search the employees section myself." Mommy ta dubi babba cikin ma'aikatan wacce tafi aminta da ita Tai assigning d'inta da suje su duba su caje kaf b'angaren ma'aikatan. Daga b'angaren ma'aikata Anisa tace su nufi b'angaren Ummul tinda Mommy kaf gidan tace a duba.
Su Mommy da Ummul suna tsaye tareda sauran ma'aikatan a parlor wayan Mommy yai ringing. Anisa ce mai kira duk jikinta a sanyaye.
Mommy tace "Ehen I'm listening to you. Kun samu sark'ar.?"
Anisa ta jinjina kai a hankali kaman Mommy na kallonta "Eh mommy mun samu.."
Mommy taci gaba da jinina kai "Cikin kayan waye kuka samu tsakanin maids d'in. Ki sanar da security guda d'aya a kira 'yansanda. Wacce duk tai satan must be punished kuma zata bar gidan nan a yau."
Anisa ta kuma fad'i a sanyaye "Mommy you need to come see it yourself.. Ban san yanda zan sanar dake ba.. Amma Ya kamata ki gani da idonki.. I'm still in shock.."
Mommy ta girgiza kai kad'an "Anisa.. Ban fahimceki ba.. Mai kike nufi.?"
Shiru ne Ya biyo baya alamun Anisa na sanar da ita abinda ke faruwa.
Ta juyo ta dubi Ummul wacce damuwar abuja ke faruwa Ya nuna a fuskarta "Kin tabbata da abinda kike fad'a Anisa.?"
Jinjina kai Mommy tai a hankali kafin ta nufo k'asa.
Sosai taji mamakin ganin sark'ar cikin d'akin Ummul. Toh amma Ya hakan ta kasance.?
Ma'aikaciyar ta girgiza kai "Hajiya gaskiyar kenan. Nima naji mamaki sosai da abinda muka gani."
Mommy ta girgiza kai "Ummulkhair bata jima da zuwa gidan nan ba. Amma inada tabbacin bazatayi abu makamancin wann ba."
Anisa Tai Shiru kaman mai tunani "Nima dai Mommy ban zaci haka daga wajenta ba. Dukda yau ce rana ta farko da ta jima b'angarenki.."
Shiru Mommy tai tana juya maganganun Anisa. Tabbas yau ne rana na farko da Ummul ta jima irin haka a b'angaren ta. Sann lokacin da suke cin abinci batazo teburin cin abinci ta zauna tareda su ba.
Anisa ta kuma duban Mommy kafin tace "Mommy bazanso hakan ta kasance ba.. Yarinyar nan ba saninta mukai ba. Ammi ce kawai ta Santa da background d'inta.. I'm sorry to say kinsan talakawan nan gold diggers ne. Ammi used to tell me this." Ta kuma duban Mommy sosai "What if Ammi batai bincike mai zurfi kan ahalin Ummul ba.. Kuma d'azu da naje zan shigo da Leenah na ganta ta fito ta hanyar parlorn ki na sama. I thought kece kika aiketa wajen or something. Kuma one of the maid ta sanar damu taga Ummul wandering around the house."
Shiru Mommy tai tana juya maganganun. Sai kuma ta girgiza kai "I still find it hard to believe Ummulkhair zata iya aikata abu makamancin wann. But koma menene we'll find out about it. Je ki kira Ummulkhair da ita da maid din da tace miki ta ganta tana zagaya gidan."
Anisa ta jinjina kai "Yes Mommy." Lokaci guda tasa kai ta fice tana sakin muguwan murmushi zuciyarta fal nishad'i.
Ba'a jima ba Ummul da maid d'in da Tai mata kwatancen hanya harma da Leenah suka k'araso. Anisa na tafe gaba garesu.
Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa ba don tsoro ba sabida tasan akan gaskiya take ba abinda zai bata tsoro saidai a duniyarta ba abinda ta tsana irin a danganta ta da sata. Sata abu ne mai ciwo ace an danganta ka dashi. Koda ace ta fito gidan da basuda arziki Allah ya masu arziki da wadatan zuci wanda shine babban arziki. tayi imani basuda abinda zata sata. Sanda Mommy ta d'ago sark'ar tana nuna mata sai taji kuka yazo mata.
Mommy ta k'araso ta dafata "Bance kin d'auka ba Ummul. So nake kawai ki amsa min tambayata dan haka ne zai wanke ki. An samu sark'ar a cikin d'akinki.. Ta Ya haka ya kasance.?"
Ummul ta girgiza kai "Ki yarda Dani Mommy. Ni ba b'arauniya bace. Ban kuma d'auka ba. Sann bansan Ya akai ya zo d'akina ba. Gaba d'aya ranar ina zaune cikin gida ban ma shigo b'angarena ba."
Leenah tai kaf tace "But wait kince zaki zo ki rufe Windows d'inki sabida hadari da kika gani gudun kar ruwa ya shiga miki.. Kodai lokacin ne kika fito kika kawo sark'ar kika ajiye a d'akin ki."
Ummul ta dubi Leenah cikeda mamaki dan ta ma kasa cewa komai yayinda Anisa Tai karaf tace "A'a Leenah. Ai Ummul bata zo ta rufe Windows d'in ba.. D'aya daga cikin ma'aikata ne tazo ta rufe Windows d'in."
Leenah ta tab'e baki "But samun sark'ar a nan proves otherwise."
Ummul taci gaba da girgiza kai tana hawaye take fad'in ita ba b'arauniya bace.
Leenah tace "Prove it then.. So kike a d'aura ma wani sharri bayan ga abinda aka gani."
Mommy ta aika ma leenah wani kallo ganin irin kukan da Ummul keyi.
Hannayen Ummul Mommy ta kamo tace "Idan kina son sark'ar Ummul zan baki ita kyauta. Kar wann yasa ki d'aga hankalinki. Ni ban kawo a raina zaki min sata ba. Duk abinda kika d'auka nawa tamkar naki ne. Ke matar Haidar ce idan har zance kin min sata kaman nace Haidar ya mun sata ne. Duk abinda kika d'auka gidan nan ba sunansa sata ba. Case closed." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta tana goge ma Ummul d'in hawayen dake gangaro mata. Cikin zuciyarta cewa take ke d'in makarin asirin d'ana ne ko mai zaki min zan shanye har na samu Haidar ya dawo gareni.