Auren wata ukku by sameena - Chapter 20
Auren wata ukku by sameena Chapter 20: Auren wata ukku by sameena Chapter 20. Da mugun mamaki Anisa da Leenah suke duban juna baki sake. Wai shin wane irin…
4,453 words
Da mugun mamaki Anisa da Leenah suke duban juna baki sake. Wai shin wane irin makahon so Mommy ke ma yarinyar nan Wanda hankali bazai d'auka ba. Wai Hajiya Kwaise ce ta zama very soft haka. Matar da sunyi imani irin sanin da suka mata yanda ta kama b'arawon nan sai Ya d'and'ani kudarsa. Matar da sam bata yarda da wani shit ba.
Ummul ta girgiza kai ba don bata d'auki maganganun Mommy da mahimmanci ba sai don bazata bari a mata shaidan sata ba. Amma ta ya zata wanke kanta. ta ina zata fara hakan.? D'agowa Tai tana dubansu gaba d'aya da idonta mai zuban ruwa. Sai ta dubi Mommy ta kuma girgiza kai "Ban d'auka ba. Kiyi hakuri Mommy ban raina k'ok'arin ki na kula dani da bani duk wani kariya ba. Amma hankalina zaifi kwanciya idan har aka tabbatar banida laifi."
Leenah da Anisa suka kuma duban juna suna mamakin ta Ya za'ai ta fidda gaskiyar.
Ummul Tai tsaye tana k'are ma gidan kallo. Cikin zuciyarta kaw addua take 'Ya Allah banida wani wayo sai abinda kayi dani. Ya Allah ina tawassili da azumin dake bakina Wanda nakeyi dan neman yardarka. Allah ka wanke baiwarka mai rauni daga wann sharri da aka k'ulla mata.'
Anisa ta katseta da fad'in "Ummul Mommy ta aminta dake inaga ya kamata ki bar zancen a haka. I think You don't need to prove your innocence."
Mommy ta girgiza kai "No, if she wants to prove her innocence bazan dakatar da ita ba. After all, I want to know who the real culprit is."
Zuciyar Anisa Ya kuma tsinkewa. Leenah ta dubeta a tsorace itama. Nan ta fara wak'an tafiya gida. Mommy tace babu mai tafiya sai gaskiya ya fito. Ta dubi Ummul tace suna sauraronta. Ta bayyana gaskiyarta.
Ummul ta jinjina kai a hankali kafin ta d'aga kai tana k'are ma gidan kallo.
Can k'ofan shigowa sashen ta hangi security camera.
Leenah ta rausayar da ido tace "Ummul bakida wani hujja please don't waste our precious time here. I really need to leave now. Is getting late already."
Juyowa Ummul tai ta dubi Leenah tana murmushi "A'a inada hujjar da zan kare kaina."
Leenah ta girgiza kai "So.. Where is your proof then.?"
Ummul ta girgiza kai "Kiyi hak'uri ban fahimci mai kike nufi ba."
Leenah tai murmushin rainin hankali tana duban Ummul a wulak'ance "Common English bakiji har kina tunanin kinada wani intelligence da zaki iya canza abinda idonmu ya gani.? Is this a joke or something."
Jinjina mata kai Ummul Tai "K'warai inada shi koda harshena bai iya furtawa ba." Ta d'aga hannu Tai mata nuni da cctv camera. Taci gaba "Na tabbata shi zai tantance na fita daga sashen Mommy ko ban fita ba. Haka ne.?" Leena tai Shiru sai muzurai dan batai zaton wann bagidajiyar zatai tunanin cameras ba. Batamayi zaton tasan da zaman cameras din ba. Ta juyo ta dubi Anisa cikeda tsoro. Sai Anisa ta kashe mata ido alamun ta kwantar da hankalinta she had everything under control.
Mommy ta jinjina kai "K'warai akwai cameras a wasu hanyoyi da zai sadaka da d'akuna cikin gidan nan. Shi zai tabbatar mana idan Ummul ta shiga d'akina ko bata shiga ba."
Anisa ta jinjina kai tace k'wari a duba footage.
Saidai koda aka duba cameras na cikin k'waryar gidan kawai aka duba kuma da alama duk Sun samu fault dan haka ba'a ga waye ya shiga d'akin ba.
Leenah ta rausayar da ido cikeda k'osawa tana fad'in Ummul batada sauran hujja.
Ummul ta girgiza kai tace "Na cikin k'waryar cikin gida kawai aka duba mai zai hana a duba na waje. Shi zai tabbatar ya kuma tantance waye ya kawo sark'ar b'angarenta.
Leenah ta dubi Anisa wacce izuwa lokacin ta gama razana dan zallan cameras na cikin gidan Tai tampering banda na haraban gidan tinda bata kawo abun zai kawo haka ba.
Mommy ta jinjina ma tunanin Ummul dan koda aka duba footage na haraban gidan Ya hasko wata maid din gidan sanye da uniform dinta ta nufi bangaren Ummul da sark'ar rike hannunta saima juyasa take tana waige waige.
Leenah ta rausayar da ido "See, this doesn't prove you innocent Ummul. It could be an alibi so that no one would suspect you. I'm sure this is pretty mandated. Bakinku d'aya kawai bata mana lokaci kike a nan."
Mommy ta daka mata tsawa da fad'in Tai masu shiru. Sai kuma ta juyo sosai tana duban Leenar dan ta kula zak'ewarta da k'ok'arin ganin ta d'aura laifin kan Ummul yayi yawa. Mommy ta girgiza kai kad'an tana kuma duban Leenah "Waye ya baki daman saka hancinki cikin al'amarin gidan nan.?"
Leenah ta sha jinin jikinta. Ta dan matsa gefe tana bama Mommy hakuri. Take Mommy tasa akai mata kiran maid din.
Ba'a jima ba Maid din ta bayyana gaban Mommy wacce ta tsareta sosai da ido. Sai rawa jikinta keyi dan tsoro.
Cikin murya mai tsoratarwa Mommy ke tambayarta waye ya bata umarni da ta kai sark'ar d'akin Ummul.
Maid din taci gaba da sunkuyar da kai tana girgiza kai. Ta d'ago tana dubansu a tsorace. Anisa ta Zare mata ido. Sai ta girgiza kai ta shiga nuna Ummul d'in tana fad'in ita ta bata umarni taje ta b'oye mata sark'ar a b'angarenta bayan ta d'auko. Cikin harshen turanci mai aikin tai maganar.
Leenah ta murmusa "My hunch was right, after all. Gashi Ummul Vicky ta bada shaida akanki. Bakinku d'aya. Shin har yanzu kinada sauran hujja.?"
Mommy ta kuma tambayar Vicky tabbata Ummul ce ta bata umarni. Vicky tace eh haka ne.
Girgiza kai Ummul take tana dubanta kafin ta k'araso gabanta "Kika ce ni na baki umarni.?"
Sai ta d'ago tana duban Ummul d'in dan bataji mai tace ba sabida ba hausa take ji ba. Ummul ta kula mai aikin bata jin hausa. Sai ta murmusa a hankali tana hamdala cikin zuciyarta dan da alama duk yanda mugun zaibi yaga Ya kulleta sai Allah ya bata k'ofan fita sabida batada hakki.
Taci gaba da duban Maid din tana mai ci gaba da furta "Amma baki jin yaren da nakeyi. Haka zalika nima bana jin yaren da naji kinyi magana dashi. Shin ta Ya akai har na k'ulla cinikayya dake.? Ta ya akai har kika iya d'aukan umarni daga bakin wacce baki jin mai take fad'i.?"
Shiru sai kallon Ummul da take cikin rashin fahimtar mai take cewa.
Mommy ta jinjina kai cikeda gamsuwa da yanda Ummul ke fayyace komai dalla dalla.
Mommy ta dubi Leenah tace "Yanzu kika mana proving a nan cewa Ummul bata jin turanci haka ne.?"
Cikin sanyin jiki da daburcewa Leenah ke duban Mommy ganin table na k'ok'arin turning.
Mommy taci gaba da jinjina kai "Idan haka ne bana tsammanin zata iya dogon magana har su shirya wani plan da Vicky wacce sam ba hausa take ji ba."
Kowa ya shiga jinjina al'amarin yayinda zuciyar Ummul Ya cika da hamdala.
Anisa ta sake baki tana kallon ikon Allah yanda Bagidajiyar nan zata kamasu gidadancin da suka raina.
Leenah ta janyo Anisa gefe tana mata k'usk'us "Oh Girl, this is not happening.. What's she doing.? My goodness! Is she a detective now.? I never imagine zatai irin wann tunanin maiyasa kika bada aikin ma wann maid d'in da batajin hausa." Tai maganar tana satan duban Ummul. Kafin ta kuma kwantar da murya daidai kunnen Anisa "I thought you said you've everything under control.. looks like it's gonna backfire.. Hajiya Kwaise bazata yafe mana ba Neesa. Oh no.. I'm scared. Mai zai faru idan tasa 'yansandan su tafi damu.? This is all your fault Neesa. I shouldn't have involved myself in your plans."
Anisa ta furzar da huci Har lokacin k'usk'us suke yayinda Mommy ta tistiye Vicky tana tambayar sai ta sanar da ita waye ya bata order.
Leenah ta kuma tambayar Anisa "Girl what do we do now.? Your grand plan turned out to be brainless. Are you that stupid Neesa. Didn't it occur to you hakan zai iya faruwa.?"
"Oh shut up Leenah.! Banyi tunanin haka ba. You know why.? Because your stupidity is contagious.. Ke kika shafa mun shashancinki."
Ta k'arashe daidai lokacin da idon su Mommy gaba d'aya yayo kansu dan Vicky direction d'insu take duban sanda Mommy ta titsiyeta.
Mommy taci gaba idonta kan su Anisa "Tell me Vicky. If you don't want to go to jail alone. Who's your accomplice. Who ordered you to frame my daughter in-law.? Tell me now.!" Mommy ta k'arashe cikin tsawatarwa.
Ganin haka yasa Anisa yin alama ma Vicky da yatsarta tana nuna mata Leenah cewa tace Leena ce.
Hannu na rawa Vicky ta nuna Leenah "It's her.. She payed me to do a clean job. But believe me madam, I only accepted her offer because I desperately needed the money.. Please don't fire me. Have mercy on me.!" Ta k'arashe cikin kuka tana duk'awa gaban Mommy.
Leenah ta saki baki cikin tsananin shock jin yanda aka aza mata laifin komai tashi daya. Ta soma girgiza kai tana duban Vickey "Me.? Hey excuse me.! What crap are you talking about.? Why would I do such a thing.. What could be my motive. I have nothing against her..!" Tai maganar tana duban mutanen dake wajen cikin k'ok'arin kare kanta. Leenah ta tafi ta shiga jijjiga Vicky tana fad'in ta bud'e baki ta fad'i gaskiya cewa ba ita ta sakata ba.
Vickey ta nuna credit alert da Leenah tai mata dan dama da account d'in Leenah akai payment d'in sabida account din Anisa yak'i transfer kuma ba cash a hannunta. Leena tace akwai kud'i cikin account d'inta bari ta tura ma Vicky. Nan Anisa tace Tai payment d'in 100k zata bata daga baya. Hakan yasa da Vicky ta nuna kud'in da ya shiga account d'inta sunan Leenah ya fito. Vicky taci gaba da fad'in ta tura kud'in ne zuwaga mahaifiyarta dake jinya dan sayen magani. Shiyasa ta amsa tayin da Leenah Tai mata cewa taje ta aje sark'ar a d'akin Ummul.
Leenah ta saki baki ta juyo tana duban Anisa wacce Tai kaman batasan meke faruwa ba.
Zata kuma magana Anisa ta dakatar da ita da fad'in "Oh shut up Leenah.! Bansan haka halinki yake ba. Bansan zaki k'ulla ma Ummul irin wann sharrin ba I shouldn't have invited you here in the first place."
Leenah ta saki baki tana duban ikon Allah jin yanda k'awarta Anisa Tai incriminating dinta ta kuma aza mata laifin komai tashi guda.
Leena baki na rawa take furta "But.. But wait.."
"Oh Leenah kowa yaga evidence da sunanki. Ke kika biyata Tai aikin without my knowledge. Amma nasan dalilin da yasa kikai haka k'awata. You did it out of your concern for me. A tunanin ki zaki rama min abinda Ummul ta mun a SPA ne Shiyasa kikai haka, right.?"
Leenah ta kasa cewa komai sai duban k'awarta Anisa da take da tsananin mamaki.
Anisa ta juyo ta dubi Mommy "Mommy dan Allah kiyi hak'uri. I know Leenah.. I know my friend is not a bad person. Misunderstanding aka samu." Tai briefing Mommy kan abinda Ya samu fuskarta duk akan Leenah ta d'aura laifin Har abinda ya faru a spa. Sam bata nuna ma Mommy tasan da plan d'in Leenah na k'ona fuskar Ummul ba Wanda ya juya nata fuskar.
Anisa taci gaba "Mommy Leenah thought she was doing it for me. Ta zaci hakan da Tai tamkar ta rama mun ne. Kinsan kishi irin na k'awaye. Kishi take da Ummul zata k'wace mata k'awancenmu. Musamman da yau da tazo taga yanda nake da Ummul d'in." Ta kuma duban Ummul "Ummulkhair please forgive my friend."
Muryar Mommy ta sinkayo tana fad'in "Dama nasan za'a rina. A yanda taketa k'ok'arin d'aura laifin ma Ummul. She's the real perpetrator. I dont care if she's your Friend. Criminals are not welcome in my house. And this won't go unpunished. She must pay for what she did to my daughter."
Ta dubi d'aya daga cikin ma'aikatan gidan tace ta kira mata 'yansanda. Matar ta jinin kai "Right away Madam."
Vicky sai kuka take tana fad'in a mata rai. Yayinda Leenah mamaki ya hanata katab'us.
Sai jan k'afafun Ummul Vicky take tana fad'in ta yafe mata.
Tsawa Mommy ta daka ma Vicky da fad'in "Shut your mouth and get up from there! You are leaving this house right this instant. I don't have room for criminals like you in my house." Ta kuma jaddada mata sai ta fara mik'asu ma hukuma daga ita Har Leenah.
Duk sai jikin Ummul yai sanyi. Yarinyar ta bata tausayi. Da alama cikin ma'aikatan tafi kowa k'arancin shekaru. Sann taji cewa da tai kud'in da ta amsa wajen Leenah ta aika wa mahaifiyarta dake jinya ne. Sai ta tuna nata mahaifin dake kwance yana jinya. Ta tuna mak'asudin zuwanta gidan itama yarda da auren da Tai sabida ta ceci mahaifinta dake jinya ne itama. Sann sadakinta shine kud'in jinyar mahaifinta. Tabbas kowa zai komai dan ya ceci iyayensa. Sai taji kaman batada wani maraba da Vicky.
Cikin sauri Ummul ta juyo ta dubi Mommy kaman zata fashe da kuka take fad'in Mommy tai hakuri ita ta yafe masu kar a kirawo 'yansanda.
Da kyar Mommy ta hak'ura da kiran 'yansandan sabida rok'on da Ummul Tai mata. Amma kam ba don Ummul d'in ba da daga Leenah Har Vicky sun kwana ofishin 'yansanda.
Mommy ta bada umarni ma babba cikin ma'aikatan gidan cewa a raka Vicky waje da kayanta ta koreta. Ita kuma Leenah ko me kamanta securities suka kuma bari ta shigo gidan a bakin aikinsu.
Harda Anisa akaima Leenah rakiya waje. Sai kallon mamakin cin amanar da Anisa Tai mata take ma Anisar.
Anisa ta dubeta bayan Sun rage saura su biyu "Let me call you a cab for you.."
D'aga mata hannu Leenah tai alamun dakatarwa "Ki barshi bana buk'ata. You know what Neesa ban tab'a zaton zaki ci amanata irin haka ba. Ta ya zaki d'aura min laifin da banyi ba. You planned the whole thing. Sann kin d'aura min laifi kaman wata sakarai. You know what? I think you're right. I'm stupid and that's why I remain loyal to you." Tana gama fad'in haka tasa kai ta shige kaman zata tashi sama ba tareda ta kuma bi takan Anisa ba.
Juya ido Anisa Tai had'ida furzar da huci kafin ta koma cikin gida.
Nan ta tadda Mommy ta had'a kaf ma'aikatan gidan tana kafa masu warning. Ta dafa kafad'an Ummul tace "She's my Son's wife. I expect each and everyone of you to treat her with absolute respect, Including you Anisa." Tai maganar tana duban Anisa da shigowarta kenan kafin taci gaba "The same respect da zaku bama D'ana Haidar. Bana so makamancin abinda ya faru yau Ya kuma faruwa. Do I make myself clear.?"
Gaba d'aya suka jinjina mata kai hadida amsawa cikeda risinawa
** Bayan Ummul ta koma sashenta tana zaune saman darduma Ida sallarta kenan Anisa ta shigo da murmushi saman fuskarta.
Ummul bata nuna mata komai ba dan itama wann sassanyar murmushin wanda a baya Anisa ta d'aukesa shashanci da gidadanci a halin yanzu shakkar wann murmushin take shine dai saman fuskar Ummul.
Ta zauna tana tambayarta an sha ruwa lafiya.
Ummul ta amsa mata da sakin fuska. Nan Anisa ta soma bata hakurin abinda Leenah Tai tana mai kuma tabbatar mata Lallai Babu hannunta cikin abinda Leenah da Vicky suka k'ulla mata.
Murmushi Ummul ta kuma yi "Babu komai Anisa kar ki damu. Suma ban k'ullacesu ba. Daga k'arshe Allah Ya bayyana gaskiya. Ba wayona bane ba kuma dabarata bace. Allah ne Ya dube ni da rahamarsa Ya wanke ni daga k'agen da aka so min. Na kuma gode masa da Ya wanke sunana daga k'agen sata. Ina kuma fata ya shiryi duk masu tunani irin nasu damu baki d'aya."
Anisa ta jinina kai "You are a good person Ummul. You have a clean heart that's willing to forgive and forget. Yanda kika wanke kanki cikin hikima ya burgeni. I wish zan zama kaman ke."
Ummul ta murmusa "Duk wanda ya dogara ga Allah Allah ya isar masa. Kuma duk wanda yaji tsoron Allah Allah zai samar masa mafita. Ba yin kaina bane Allah yakan wanke bayinsa da akai masu k'age ba tareda sun aikata laifin ba. Kaman yanda Ya wanke Ummuna Aisha (RA) daga k'agen da azzalumai suka mata. Kaman yanda Ya wanke Annabi Yusuf (AS) daga k'agen da aka masa. Kaman yanda Ya wanke bayinsa muminai da dama daga k'agen da aka masu. Kaman haka yanke wanke bayinsa da basuda hakki. Na gode masa da ya wanke ni daga k'agen da aka min ba tareda hakki ba. Amma ni Ummulkhair banida wani wayo. Saidai Inaso mutane irinki da Leenah su fahimci English is just a language and not a means to measure one's intelligence or education. Snn duk wani wayewar da yai karo da koyarwar addininmu da d'abi'u da kyawawan al'adunmu ba sunansa wayewa ba." Tai maganar murmushi saman fuskarta.
Baki sake Anisa ke kallonta "So you can speak English.?"
Ummul ta murmusa "Ba sosai ba abinki da Wanda taje makaranta na gwabnati."
A hankali Anisa ke jinjina kai "Na yarda da duk abubuwan da kika ce. A yau kin kuma tabbatar min da haka. " Ta kamo hannayen Ummul "Mommy tayi zaton ni zan koya miki abubuwa musamman zamantakewan rayuwar civilized world. But it turned out ni ce wacce ke koyo wajenki. Yau na raina duk wani exposure na Ummul."
Ummul ta girgiza kai "A kullum ko wani shafi na rayuwar mu darasi yakan bude mana dan mu koya. Kullum cikin koyo muke a duniyar nan. Kaman yanda muke had'uwa da mutane iri daban daban." Ta d'an murmusa "Nima ina koyo daga gareki Anisa."
Shiru Anisa Tai sai kuma ta saki murmushi da yafi kama da yak'e.
Tin daga wann rana Ummul ta samu sanyin abubuwan da Anisa ke mata. Sai ta koma kaman tana shakkan Ummul d'in koda bata nuna a fili ba. A kwanakin da alama Anisa ta maida makaman yak'inta.
**
Kano…
Batai k'asa a gwiwa ba dukda fargabn abinda ka iya zuwa yazo ta nufi gidan Hajiya Asshe. Juyin duniya Umma tayi amma masu gadi sun hanata shiga sabida dokan da Asshen ta basu tin kwanakin baya.
Asshe na kitchen tana had'a ma maigidanta abinci kasancewar ranar yake dawowa daga tafiya kuma gidanta yake. Mai gadi yai Sallama ya sanar da zuwan Umma wacce babu yanda basuyi ba amma tak'i barin bakin gate din tace sai ta gana da Hajiyar.
Zuciyar Asshe ya tsinke yanzu idan matar nan ta tada mata hargitsi a k'ofan gida har mijinta ya iso ya tadda wann al'amari mai zata ce masa. Oh! Ita kam dai ta d'ebo ruwan dafa kanta. Wann wasu irin ahali ta kwaso masu ne wai ita Asshe. Bata gama da fitinan Dije ba ga Suwaiba da tai tunanin ta ajeta yanda ya kamaceta yanzu ta dawo. Toh uban mai ta dawo zata mata.?
Fuuu ta nufo gate tana huci dan wllhi bazata bari d'aya daga cikin watsatsun matan nan su mata sanadin aurenta da take lallab'awa ba.
Tana fitowa ta shiga janyo Umma tana fad'in yau hukuma ce zasu mata iyaka da ita muddin bata bar mata k'ofan gida ba.
Umma bata tafi ba bata fasa rok'on Asshe tana fad'in ta dubi girman Allah ta saurareta.
Hilal daga sashensa yake jiyo haniya yak'i k'arewa daga gate. Babu shiri ya bar abinda yake ya nufo gate d'in.
SameenaAleeyou📚.. *AUREN WATA UKU..!*
*29*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Asshe taci gaba da janyo Umma tana fad'in kodai ta bar mata k'ofar gida ta mik'a mata ma 'yansandan dan ta gaji da fitinan fitinannun mata Irinsu. Wanda tin had'uwar ta dasu Masifan yau daban na gobe daban.
Umma taci gaba da girgiza kai "Idan kina ma Allah ki tsaya ki saurareni Hajiya Asshe."
"Na saurareki na saurari mi inyi.? 'Yarki ce nace Miki akwai wa'adin da na d'ibar Wanda zan dawo da ita gareki. Amma a halin yanzu ni Asshe banida wani sauran alak'a dake da sauran zuri'arku. Na gode ma Allah da yasa auren Ummul ba mai d'orewa bane. Mi za'ayi da zuri'arku dangin masifa dangin mayu dangin matsafa.. Zo ki wuce.. Idan kika kara minti d'aya k'ofar gidan nan ki kwana ofishin 'yansandan" Ta k'arashe tana hankad'a Umma da iyaka k'arfinta Wanda saida ta kaita k'asa.
Daidai nan Hilal Ya fito ya taddasu. Ya isa da sauri yana ma Umma sannu had'ida tambayar bataji ciwo ba.
Umma ta d'ago tana girgiza masa kai alamun a'a.
Da tsananin mamaki yake duban mahaifiyarsa "Ammi what's the meaning of this.? Kan wani dalili zaki aikata abu makamancin haka..? Mai yayi zafi..? Wai meke faruwa ne ma.?"Ya k'arashe damuwa saman fuskarsa.
Asshe na huci take furta "Babu ruwanka Hilal. Ba abinda ya had'aka da Matar nan zo ka shige gida."
Hilal ya girgiza kai "Ammi matar nan sirkar Haidar ce.. 'Yarta Haidar ke aure.. We are practically family now."
Bai kai aya ba Asshe ta k'araso a guje ta toshe bakinsa "Allah tsari gatari da saran shuka. Allah mana tsari da had'a iri da wann zuri'a.. Shige gida kar na sake jin bakinka." Ta k'arshe tana nuna masa k'ofa.
Girgiza kai Hilal Ya kumayi "Ammi I'm sorry. Bazan iya barin Umma a nan ba har sai na san abinda ke faruwa."
Baki sake Asshe ke dubansa "Umma.?" Ta nanata a fili. "Umma ka kirata.? Toh sunanta Suwaiba. Kanwar uwarka ko na ubansa da zaka kirata da Umma.?. Ka sake kiran mahaukaciyar nan Umma sai naci maka. Zo ka shige kafin Abbanka Ya k'araso." Ta k'arashe tana janyo Hilal yana tirjewa haka Har ta shigar dashi cikin gidan ta janyo k'ofa tana fad'in masu gadi kar su bari Suwaiba ta zo koda kusan gate din ne.
Mamaki Ya cika Hilal. Shi Ya kasa gane wann irin al'amari ne wann da kuma abindake tsakanin mahaifiyarsa da da Umma.
After some hrs da faruwan hakan. Tsaye yai bayan mahaifiyar tasa sanda take lek'e daga window ko zata hango Umma. Cikin zuciyarta tana addu'an Allah yasa mayyar ta tafi dan bata fata mijinta ya dawo ya tadda Suwaiba kofan gidan balle asirinta ya tonu.
Ya girgiza kai kad'an yana kuma takowa kusan mahaifiyarsa. Aiko a firgice ta juyo tamkar maras gaskiya. Ta dafe k'irjinta tana fad'in "Haba Hilal, halin Anisa na lab'e ka koya kaima. K'iris zuciyata bata buga ba." Ta k'arashe har lokacin hannunta dafe da k'irji. Sai kuma ta canza maganan da fad'in "Lek'e nake naga ko Abban naka Ya iso.. Gashi dai da alama har yanzu bai iso ba.. Lallai da alama zai dare." Ta kuma duban Hilal tana tsimewa "Waima mai ya shigo da Kai nan ne. Mai kake nema.?"
"Dama na shigo ne na fad'a Miki zan d'an kwanta kafin la'asar tinda naga har yanzu Abban bai iso ba."
Ta jinjina Kai tana dubansa "Idan ya iso zan tada Kai." Ta fad'i tana nufan k'ofa yayinda Hilal ya take mata baya.
*
Fitowan Hilal sallar la'asar bayan an Ida sallah a masallaci a hanyar sa ta dawowa gida ya hangi Umma tana sallah jikin wani gini dake manne da karantar gidansu. Kasancewar akwai interlocks wajen. Mamaki ya cika Hilal. Ikon Allah yanzu dama ashe matar nan bata tafi ba. Lallai ba k'aramin Abu ya zaunar da ita ba.
Ya k'araso gefenta daga can ya tsuguna kan k'afafunsa har ta Ida addu'arta. Hilal ya tayata shafawa.
"Umma." Ya ambaci sunanta daga nan yanda yake tsugune kaman dai yanda yaji Khulsum na kiranta.
Umma ta d'ago ta dubesa sai ta sakar masa murmushi "Hilal d'an albarka." Ta fad'i tana dubansa dan bazata tab'a mance alkhairan yaron ba koda kuwa ita mahaifiyarsa suna buga dabi. Kaman yanda nata yaran basuyi halinta ba haka zalika Hilal baiyi halin mahaifiyarsa ba a cewarta.
Hilal ya gaisheta kafin ya k'arada "Umma mai kikeyi a nan.? Mai ya zaunar dake nan.?" Ya dan numfasa kiyi hak'uri da tambayar da zan Miki "Shin akwai wani matsala ne tsakaninki da mahaifiyata.? Meke faruwa tsakanin ku biyun.?"
Umma ta girgiza Kai kad'an "Babu komai Hilal. Amma Kai hakuri bazan bar k'ofar gidan nan ba har sai mahaifiyarka ta saurareni."
Hilal ya zuba ma sarautar Allah ido yana tuno yanda sukai da Amminsa. Ya d'an kuma girgiza Kai "Amma.. Kiyi hak'uri da tambayarta da zan Miki.. Wani abu ne kike nema wajen mahaifiyata.? Ki sanar dani dan Allah idan wani Abu ne da zan iya taimakawa."
Umma ta kuma murmusawa "A'a Hilal. K'arshen abinda zanyi shine na saka ka cikin matsalolinmu. Kai d'in kanada zuciya mai kyau. Ina rok'on Allah yasa D'anuwanka dake auren Ummul d'ina ya zama mai kyaun hali da d'abi'u irin naka.." Ta k'arashe cikin rawar murya irin na mai kuka hawaye na gangaro mata dan a koda yaushe cikin tunanin Ummul d'inta take da halinda zata iya kasancewa ciki. A gaggauce tai k'ok'arin goge fuskarta kafin ta kuma duban Hilal tace "Mahaifiyarka nake son magana da, sabida wajenta nazo. Domin dani da mahaifiyarka munada alak'a mai kyau." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta.
Mamaki ya kuma cika Hilal. Kansa ya kuma k'ullewa. Tabbas wad'ann mata wato Amminsa da Umma al'amarinsu abin dubawa ne sann yanada rikitarwa. A b'angare guda mahaifiyarsa tana ikirarin datse alak'a da Umma da ahalinta. A b'angaren Umma tana fad'in itada mahaifiyarsa sunada alak'a mai kyau. Shin na waye zai d'auka cikin su biyun.?
Juyin duniya Hilal yayi Umma ta hakura ta koma gida amma fir fir tak'i ta kafe lallai lallai sai Asshe ta saurareta. Ganin yamma nayi yasa Hilal d'aukan mota ya fice daga gidan. Dan yasan watak'ila maganarta kawai Umma zata saurara ta amince ta bar k'ofar gidansu.
A bakin ward din ya hangeta tana k'ok'arin shiga. Sauri sauri ya k'arasa ya cimmata.
Kaman Wanda aka jefo shi haka Khulsum taga Hilal gabanta.
Da mamaki take dubansa.
"It's a good thing that I found you here. You need to come with me." Abinda kawai Hilal yace kenan.
Khulsum ta girgiza Kai cikeda mamaki "Malam lafiya.?"
Yai gajeren tsaki "Wai ke ko yaushe haka kike ne. Abun fad'a baya Miki kad'an ne.?" Ya kuma girgiza Kai "I need you to come with me right away. And please you alone. You don't need to inform that aunt of yours… She might stop you." Dan bai mance ba kwanakin can da suka shige ita ce ta hana Khulsum bin Umma Akan idonsa. Daga haka sa Kai yai ya soma tafiya yana fad'in tai sauri ba lokaci.
Takaici ya cika Khulsum, mai wann D'an rainin hankalin ya d'auketa da zaice tazo ta bisa. Ina ma zata bisa.? Mai ya maidata.?
Ganin ya soma tafiya ya nufi mota yasata bin bayansa da sauri tana fad'in "Kai Malam.. D'an dakata.? Kana tunanin kai waye.? Mai ka d'auke ni.. Mai ka maidani da zaka tako har yanda nake kace nazo na bika kuma kar na sanar da Innata.. Ce maka akai.."