Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 21

Auren wata ukku by sameena - Chapter 21

Auren wata ukku by sameena Chapter 21: Auren wata ukku by sameena Chapter 21. Bata Kai aya ba Hilal ya kaikaito yana dubanta cikeda takaicin kuskuren…

4,456 words

Bata Kai aya ba Hilal ya kaikaito yana dubanta cikeda takaicin kuskuren fahimtar da tai masa "Hey cut it out will you.!" Ya katseta da fad'in haka kafin yaci gaba "Seriously, is that what you think of me.?" Har lokacin da mamaki yake dubanta kafin yaci gaba "If that's what I wanted I'd have gone straight to a hotel or club, and not a hospital." Ya dan girgiza Kai "Look, ni ba irin wad'ann mutanen bane. And I'm not kidnapping you.. Idan na zo nan kawai nazo ne sabida mahaifiyarki dake zaune k'ofar gidanmu through out the day. Idan Ammi na ta fito ta taddata wajen it would be a disaster. Idan akwai girman mahaifiyarki da kike gani kike ji a cikin Zuciyar ki koda kad'an ne zaki taho tare Dani dan na tabbata ke zata iya sauraronki." Ya k'arashe yana bud'e motar.

Jikin Khulsum yai sanyi ta dubesa da mamaki "Umma ce take k'ofar gidanku.?"

Hilal ya zuba mata ido yana dubanta. Baice komai ba sai tada motar da yai "Zakije ne ko nai tafiyata.?"

Ta hareresa sai kuma tai still a wajen kaman mai tunani. Shin ta sanar da Inna Dije ne.? Toh amma idan ta sanar da Innah Dije wani wutan zata kunna tinda tasan Ummanta da Inna Dije basa jituwa. Sann Inna Dije zata iya hanata zuwa. Tana tsaka da tunanin taji sautin horn ya cika mata kunne alamun Hilal na jiran decision dinta. Harara ta b'alla masa kafin ta bud'e marfin motar ta shige.

Ya soma driving babu mai ce da kowa komai cikin su biyun har suka iso k'ofar gidansu Hilal. Can Khulsum ta hangi Umma rakub'e jikin gini tana lek'en gate din gidansu Hilal kaman wata mabaraciya. Sosai abin ya mata ciwo ganin mahaifiyarta a haka. Hilal na Ida parking ta fito ta nufi Umma.

"Umma.!" Khulsum tace daga nan yanda take tsaye kusan Umma.

Umma ta d'ago tana dubanta. Khulsum tai saurin k'arasowa ta duk'a gaban Umma "Umma Mai kike a nan. Dan Allah mai kike haka a nan.? Umma wann fah zubda mutunci ne. Dan Allah ki tashi ki bar k'ofar gidan nan. Duba fah kiga mutane masu shigewa suna kallonki.. Umma dan Allah ki tashi haka nan."

Hawaye Umma ta soma tana girgiza Kai "A'a Khulsum bani tafiya sai Hajiya Asshe ta sauraren."

Khulsum ta juya ta dubi Hilal dake can jikin motarsa yana tsaye. Shid'in ma su yake duba. Ko ba'a ce ba damuwan halinda Umma ke ciki ne saman fuskarsa dukda baya iya sauraron mai uwa da 'yar ke cewa.

Khulsum ta maidoda dubanta ga mahaifiyarta "Umma matar nan tareda ita ina nufin keda ita kuka k'ulla auren 'Yaruwata. Bansan dalilinta na juya Miki baya ba. Bansan meye ku biyun kuka bisne ba. Bansan meye a tsakaninku ba. Amma ke mahaifiyata ce kuma bazan so ki walak'anta ba. Dan Allah Umma ko mai kike nema wajen matar nan kiyi hak'uri ki bar k'ofar gidan nan."

Umma ta kuma girgiza Kai tana hawaye "Khulsum idan na tafi mai zanje nace da Tani. Na mata alk'awarin zan nemo kud'ad'en belinta. A nan ne kawai nake da yak'inin zan samu kud'in fiddo Tani Khulsum."

Baki sake Khulsum ke dubanta. Da mamaki tace "Umma wai dama kan kud'ad'en belin Mama kike nan.?"

Umma ta jinjina mata Kai alamun eh.

Shiru Khulsum tai na d'an lokaci kafin ta dubi mahaifiyar tata tace "Umma kece zakiyi belin Mama. Wai Mama Tani dai da ta saida shagon Abba.?"

Umma ta kuma jinjina mata Kai "Dukkanmu masu kuskure ne Khulsum. Tani ta salwantar da dukiyar Malam ni kuma na salwantar da rayuwar 'yarsa. Cikin mu biyun idan akwai Wanda tafi girman laifi toh ni ce Khulsum. Ni yafi cancanta na tafi gidan kasu ba Tani ba. Idan har zan zuba ido ni ina shak'an iskan 'yanci yayinda Tani ke gark'ame kurkuku bana tsammanin nayi ma kaina adalci. Sann bana jin 'yancin iskan da nake shak'a a mak'oshi na. Tani ta tuba Khulsum. Dukanmu mun gane kurakurenmu. A halin yanzu bamuda wani buri da ya wuce mu koma ga mijinmu mu kula dashi mu masa jinya mu samu aljannarmu." Ta k'arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.

Jikin Khulsum yai sanyi. Tasan mahaifiyarta tanada zuciya mai kyau Wanda da yawan mutane suna amfani da wann damar su shashashantar da ita. Kaman dai yanda takeda kokonto Akan tuban Mama Tani. Dan tasan kad'anda aikin Mama ne ta shashantar da mahaifiyarta ta samu ta fito daga prison.

Muryar Umma ta kuma sinkayo sanda ta tallafo fuskar Khulsum d'in cikin zuban hawaye take fad'in "Nayi kewarku Khulsum daga ke har 'yaruwarki. Ina zaman kad'aici a gidan.. Babu ke.. Babu Ummulkhair.. Babu mahaifinku.. Tani ma bata nan." Tai shiru tana tinanin daga ita sai su Azeema Wanda suka maidata wofi cikin gidan barikinsu kawai suke bugawa. Su fita sanda suka so su dawo sanda suka so. Idan tai masu abincin da bai musu ba su mata tatas. Har wankin kaya Badia ke sakata. A cewarsu idan batai ba zata fice ta bar masu gidan uba tinda gidan na ubansu ne.

Ganin tayi shiru ta tsunduma tunani yasa Khulsum kamo hannayenta "Umma." Ta kirawo sunan Umman a hankali.

Umma ta d'ago tana duban Khulsum.

"Zaman kad'aici yasa kike so ki fiddo Mama Tani.?"

Shiru Umma bata ce komai ba sai hawaye dake kuma gangaro mata.

Khulsum ta janyo mahaifiyarta ta rungume sai dukansu biyun suka fashe da kuka.

Cikin muryar kuka Khulsum ke fad'in "Umma kiyi hak'uri ki koma ki zauna. Nayi ma Abba alk'awari bazan sake barin kusansa ba bayan abinda ya faru." Cikin rawar murya taci gaba da fad'in "Umma ba zama da Inna Dije na zab'a ba. A'a zama da Abba na na zab'a. Inna Dije bazata kuma barinki kije kusan mahaifina ba Umma. Zanfi kowa so naga ahalinmu ya kuma cika amma a halin yanzu Abu ne mai matuk'ar wuya Umma. Ki koma kici gaba da addua ma Abba har Allah ya bashi lafiya iyakacin soyayyar da zaki nuna masa kenan a halin yanzu. Da sannu Allah zai duba Zuciyar Wanda yai tuba na gaskiya ya yaye masa matsalarsa kinji Umma na." Ta k'arashe cikin rawar murya.

Umma ta shiga jinjina mata Kai a hankali har lokacin tana hawaye. Cikin zuciyarta kaw cewa take ita kanta bazata so ta bar Malam k'ark'ashin kulawar Dije kawai ba. Gwara ace Khulsum d'in na tare dasu. Zatai hak'uri kuma zataci gaba da addua kaman yanda 'yar nata ta shawarceta.

Hannunta Khulsum ta kamo suka nufo Motan Hilal. Hilal na ganin su ya isa ya bud'e back seat Khulsum suka shige tareda Umma hannayensu rik'e cikin na juna suna Jin d'umin juna da suka jima basu samu hakan ba.

Ta mirror Hilal yake dubansu yanda suka shige jikin juna. Kan Khulsum na kwance gefen kafad'an mahaifiyarta yayinda Umma ta rik'e hannun Khulsum d'in k'am cikin nata tamkar kar wani Abu ya rabasu. Murmushi ne yaji out of nowhere na zuwa fuskarsa. Shi a duniyar sa duk yanda yaga shak'uwa da soyayya mai tsafta tsakanin iyaye da 'ya'yansu ba kowa yake hasashowa ba face D'an Uwansa Haidar. A kullum addu'arsa kenan yaga irin wann bond d'in tsakanin Haidar da iyayensa.

Har gida Hilal ya kawo Umma. Khulsum ta fito taima Umma rakiya zuwa cikin gida ta kuma tausarta had'ida kwantar mata da hankali amma fah dukda haka bata ji cikin zuciyarta zata iya baro Abba ta dawo ta zauna da Umma musamman idan ta tuna abinda matan Abban nata suka masa.

Tana fitowa ga mamakinta ta tadda Hilal na nan na jiranta.

Daga can yanda take tsaye ya zuba mata "Rankidad'e jirana ake gida muje mana."

Ta had'e fuska sosai "Toh ce maka nai ka jirani. Kai tafiyarka mana." Tace tana canza hanya.

Furzar da huci yai kad'an ga wayarsa da ta kasa shiru sakamakon kira da Mahaifiyarsa ke jero masa. Yasan bazai wuce Abbansa ne ya iso ba. Baisan mai zaice mata ba dan shi dai bai iya k'arya ba amma muddin ya sanar da ita Umma ya kawo gida ya taro match ne tsakaninsa da Ammi.

Ya k'arasa da mota gaban Khulsum yai rolling glass "Zaki shiga ne ko sai na fito na shigar dake da k'arfi.? Be thankful, albarkacin Umma kikace idan na maidake.alk'awari na daukar mata zan maidaki yanda na d'aukoki." Yace a mugun tsare.

Khulsum ta dubesa dan yanzu gadararsa da k'arfin halinsa ya daina bata mamaki. Bata son dogon hira dashi dan kaf zuri'arsu haushi suke bata. Sann ga magarib ya k'arato hasalima batasan yanda za'ai ta koma ba tinda ba kud'in abun hawa wajenta. Ta kauda fuska gefe cikeda takaici zata bude backseat ya saka motar a lock.

Fitowa yai daga mazauninsa yana fadin "You must be kidding. D'azunma albarkacin Umma kikaci na barki kika zauna baya." Ya bud'e mata front seat "Shige muje."

Ta hararesa kafin ta shige.

Tana shiga ya sakar mata murmushi had'Ida kashe mata ido kafin ya zaga ya shige. Takaici ya kuma cika Khulsum.

Suna tafe babu mai cewa komai. Khulsum ta saci kallonsa. Yanzu wai godiya ya kamata ta masa ko hakurin kuskuren fahimtar da tai masa zata basa.? Kai ina ita dai bazata basa hakuri ba dan bataga laifin da tai masa ba. Ta saci kallonsa suka had'a ido.

Sai ta wayance dan bata so ya fahimci tana dubansa. tai kaman bata kalli b'angaren da yake ba. Saida tai gyaran murya da kyar kafin tace "Idan kana jira na baka hak'uri ne kan abinda ya faru ni dai bazan baka ba. Abinda Kai kuma shima Kai ka saka kanka shima bazan maka godiya ba." Ta k'arashe tana kauda fuska.

Hilal ya murmusa "Guilty conscience.? Kar ki damu na yafe miki." Yace idonsa naga kwalta.

Bata amsa shi ba sai kuma tace "Toh mai za'a tsammata daga wanda yake sallah babu alwala.?"

Ya kuma murmusawa "Allah yasa dai ba kece mai karb'an tuba ba balle ki k'i karb'an nawa tuban."

Ta kuma hararsa "Ka fad'a ma wann D'anuwan naka mai sallah babu alwala 'Yaruwata musulma ce bazata zauna dashi ba. Ni Khulsum sai na datse wann auren."

Hilal ya jinjina Kai "Why not ask your sister to tell him. After all su biyun sunfi kusa a halin yanzu."

Ya d'an dubeta a kaikaice kafin ya k'ara "And remember they say, Wanda ya shiga tsakanin mata da miji shi zaiji kunya."

Ta hareresa musamman da taga murmushin dake bisa fuskarsa.

Yana ida parking tasa hannu ta bude marfin motar a fizge ta fice. Ko kallon yanda yake bataiba balle tai masa sallama balle ya samu arzikin godiya.

Bayanta yabi da kallo yana murmushi. Cikin zuciyarsa yake jin yanzu yanada k'wakk'waran dalilin da zaisa ya k'ara delaying lokacin komawarsa makaranta koda hutunsa ya k'are. Bazai tafi ba har sai ya tabbata baida wani pending matters. Saida ta b'ace ma ganinsa kafin yaja motarsa ya bar wajen.

**

Cuba…

Waya manne b'angaren kunnensa na dama. Dareen na hankalce dashi tinda ya soma wayar.

Daga d'aya b'angaren Hisham yaci gaba "You know I still can't get over her. I don't know why.. But I find it difficult to forget about her. Dukda cewa mun hadu ne na d'an wani lokaci. Nayi tunanin zan cireta a zuciyata cikin sauk'i kaman yanda na cire sauran. But then I realise she's different. So different." Ya d'anyi fasali "Haidar na kasa hana zuciyata tunanin matar wani. I dream about her every night. And worse part d'in shine zuciyata tak'i ta karbi k'addaran. Haidar ji nake zata dawo gareni.. Astagfirullah." Ya k'arashe jikinsa duk a mace.

Sosai Haidar yaji tausayin abokin nasa. Shi ire iren abun nan ba layinsa bane. Hasalima bai tab'a soyayya ba. Dareen ma bazaice ga yanda akai har ya fara sonta ya aureta ba. So baisan wani shawari zai ba ma abokin nasa ba. Ya d'an numfasa kafin yace "Just.. Just try to distract yourself.. Engage in activities that require your full attention… Like work.. Zaka gani in no time zaka mance da ita. And you'll find someone better than her."

Hisham ya d'an furzar da huci "What if my mind gets stuck here Haidar.? What if I couldn't move on.? What if banida wani future dangane da abinda ya shafi Aure.? What if this is my destiny.?"

Haidar yai shiru cikin sanyin jiki ba tareda ya iya cewa komai ba.

Hisham yai murmushi mai ciwo "Sorry I shouldn't be telling you all this. Kayi tafiya ne dan ka rage damuwar dake kanka bai kamata na k'ara maka da nawa ba. Anyways, I guess this is life for us. Ba ko yaushe muke samun abunda muke so ba." Ya d'an murmusa kafin yace "Let's talk business maybe this will keep me busy." Yai maganar da gajeren murmushi kafin yaci gaba "Ya kamata ka dawo haka work is getting hampered because you are not here. Komai so yake ya tsaya. And kasan lokaci baya jiranmu."

Ya d'anyi gajeren tsaki "I'm still on my vocation. Zanje Pennsylvania daga nan."

Daga d'aya b'angaren Hisham Ya girgiza kai "Wai kana nufin hutun naka bai k'are ba.. Ko wani business d'in kakeda a can US d'in.?"

Gajeren tsaki ya kuma yi "Ka kira ne dan ka bani haushi.? What business kuma.?"

Hisham Ya murmusa kad'an "Alright fine. Yanzu dai Ya kamata ka dawo. Kaga we need to meet up. Ina nufin our team members. We've got a lot of things to discuss."

Tsakin ya kuma yi dan ya kula da gangan Hisham ke son tunzirashi "Maiyasa zan dawo. Mai zan dawo na maka when you can schedule a zoom meeting. I just hope ba shirme da shiririta bane cikin meeting d'in ba. Because you know my time is precious."

Hisham ya murmusa kad'an "Look Haidar, you and I both know dawowarka nada mahimmanci. Magana muke kan project d'in da bamu tab'a handling babba kaman shi ba. Kuma a matsayinka na Wanda ragamar kula da aikin ke k'ark'ashin ka ya kamata ace by now ka ziyarci site not just once or twice. Cikin k'ank'anin lokaci zamu fara. Sann any moment any time Dad dinka zai iya dawowa k'asar nan. Mai kake tunani idan ya dawo Ya tadda baka nan.? The story will definitely change. And all our hard workings will go to waste.. Haidar you need to forget about your tour to America and come back as soon as possible."

"I don't take orders from you Hisham. Let Aliyu Maitama do his worse. I do not give a damn.!" Yana ida fad'in haka ya katse kiran kafin yasa kai ya fice cikin huci saikace Hisham d'in na ganinsa. Zuciyarsa na masa zafi dik sanda aka ambata masa mahaifinsa. Sunan da dik sanda aka ambata sai yaji k'una cikin zuciyarsa at the same time babu yanda ya iya wann sunan dai yake amsawa. Babban kuskuren da mahaifiyarsa Tai shine saka masa sunan wann mutumi da Tai Wanda duk duniya babu Wanda Ya tsana sama dashi.

Dareen ta fito daga mab'oyarta tana bin bayansa da kallo Har ya b'ace ma ganinta. Zama tai tana k'ok'arin figuring out maganganun da taji ya tattauna cikin waya.

A b'anegarn Haidar kuwa can bakin beach yaje ya zauna tunanin duniya na damunsa. K'iyayyan mahaifinsa ne zalla cikin zuciyarsa. Lokaci guda maganganun Hisham na yawo a kwanyarsa. If he wants to take his Dad down dole yaje yayi aikin koda baya son komawa. Rashin komawarsa na nufin zai iya rasa chance d'insa na k'arshe akan mahaifinsa. Dan kaman yanda Hisham yace ne idan har Dad d'insa ya rigashi komawa Nigeria toh fah zaiyi replacing d'insa da wani ne. He promised to make his Dad swallow all his words sann baya jin zai janye wann k'udirin nasa.

Gajeren tsaki yai yana tunanin abun yi. Mommy ce ta fad'o ransa. Yai scrolling kan sunanta. Kaman mai tunanin wani abu ya jima sosai kan lambarta had'ida k'ura ma sunanta ido. Saida ya furzar da huci kad'an dan baida wani option kafin yai dialing layin.

Sunanta Ya fara ambata tana d'aga wayan in the way he does sanda yake k'arami. Sai Mommy taji hawaye ya ciko idonta. Idan Ya kirata da wann sigan lokacin k'uruciyarsa ta kullesa ne a d'aki taurin zuciyarsa bazai bari Ya rok'eta ta bud'e sa ba sai ya ambaci sunanta da wann sigan. Tai k'ok'ari Tai ta maza ta share hawayen da suka gangaro mata "Haidar ina ka shiga tsawon sati biyu.? Mai kake nufi Dani Haidar..? Mai kake nufi da Amaryarka dake zaman jiranka tsawon sati biyu. Shin ka cika alk'awarin da ka d'aukar min.?"

Da ta ambaci amaryarsa sai yaji abun Ya masa wani banbarak'wai. Girgiza kai yai kad'an "Alk'awari d'aya na d'aukar miki Mommy shine bazan saketa ba sai ta cika wata uku kaman yanda yake a Yarjejeniyar. Amma ban miki alk'awarin zama da ita cikin watanni ukun ba."

Mommy ta zaro ido waje kaman yana ganinta. Idan baizo ba ai Babu amfanin auren. Ya zama wofi kenan.

Katse shirun Tai da fad'in "A'a Haidar kar mu fara wann wasan dakai. I mean what about the project.? Muddin mahaifinka ya rigaka saka k'afa cikin gidan nan kasan sauran Haidar. All our efforts and sacrifices zasu tafi ne a banza . Haidar ka tuna na k'ulla auren nan ne dan mahaifinka ya amince ya baka project din nan."

Katseta yai da fad'in "To hell with everything Mommy."

Mommy ta mik'e tsaye tana jin zufa na keto mata. Sai muryarta Ya soma rawa "A'a Haidar.. Haidar kar kace haka."

"You know what Mommy, you are too demanding. Yes na yarda zan auri yarinyar chan or whatsoever da kika kawo kika ce na aura because I wanted to manage the project. But zama tareda ita under same roof ban miki wann alk'awarin ba. It's suffocating already da na amince da auren."

Mommy taci gaba da girgiza kai jin duk sadaukarwan da tai da duk wasu k'ok'arin ta zasu tashi a banza. Sai ta soma hawaye "Yanzu da gaske ka hakura da aikin Aliyu.? Mai zai faru Dani Haidar.? Mai zai faru da nawa auren.? Yanzu bazaka amince da AUREN WATA UKU dan ceto auren naka mahaifiyar ba."

Cikeda k'osawa yake tattare naman goshinsa "Quit the act Mommy. Your victim card won't work on me. You brought this to yourself. You should blame yourself."

Cikin kuka Mommy ke fad'in "Haidar cikin satin nan Mahaifinka zai dawo k'asar nan. Na tabbata idan Har ya rigaka dawowa zaka dawo ka tadda bana nan. Idan har ni na haifeka zaka dawo Aliyu.. Zaka dawo ka ceci Aurena kafin mahaifinka ya sauk'a k'asar nan.." Tana ida fad'in haka ta katse kiran ba tareda ta jira cewarsa ba.

Ya lumshe idonsa kad'an yana tuna mafarkin da yai tareda iyayen nasa a kwanakin baya.. Yai gajeren tsaki wani b'angare na zuciyarsa na fad'a masa mafarki is the opposite of reality. Ya kuma yin gajeren tsaki zuciyarsa na kuma tunzura shi gameda al'amarin iyayen nasa. Meyasa yakeji gaba d'aya shidai baida wani alk'ibla a rayuwarsa. Like his life's a complete messed up. Baisan mai yake son yai ba. Baisan mai yake ji ba. A haka ya mik'e yana tafiya baisan wani direction zaibi ba.

**

Abuja..

Mommy yau din mafarki tai Haidar ya dawo suna zaune parlor Kansa kwance saman cinyarta suna hira na d'a da uwa da basu tab'a irinsa ba. Tinda tai wann mafarki ta tashi da farin ciki ga dukkan alamu shirinta mai tasiri ne Akan Haidar din. A b'angare guda ga Daddy ya mata waya ya sanar da ita nan da kwanaki biyu zuwa uku zai dawo da izinin Allah. Gaba d'aya sai tana ji kaman lokacin dunk'ulewar ahalinta ne yazo. Burinta yana gab da cika. Tuni tasa akai mata kiran Ummul ta sanar da ita Mijinta na nan tafe. Yacce kasan wacce takeda tabbacin dawowar Haidar d'in ta dauko mai gyara na musamman irin nasu na shuwa aka soma yi ma Ummul sabon gyara. Wani sabon kula na musamman Mommy ke bawa Ummul.

Hankalin Anisa idan yayi dubu ya tashi. Babu shiri ta fita ta nufi gidansu Leenah dan bazata iya kallon wann kayan tashin hankali ba. Bazata bari Haidar ya dawo gidan ya cimma Ummul ba.

Leenah ta dubeta a dak'ile "So da kika taso kika zo nan mai kike so na miki.?"

Anisa tace "Leenah let's forget about everything. Nasan ban kyauta ba amma dole ce ta saka ni d'aura miki laifin. Da ace na d'auki laifin da yanzu bana gidan. Leenah I have no one to turn to but you. You just can't abandon me you know." Ta k'arashe tana duban kawar tata kaman zatai kuka.

Shiru Leenah tai na d'an lokaci kafin tace "Neesa I'm not doing this. I won't allow myself to fall into your trap again. I'm not that stupid."

Anisa ta kamo hannayen Leenah "Girlfriend please mana. Zamu bari wann low class d'in ta shiga tsakanin abotanmu ne.? Tayi mana guda biyu bazamu bari tayi na uku ba. Think, yanzu idan muka kyaleta ji zatai tayi nasara akanmu. And remember, we never back off for a fight."

Shiru Leenah tai kafin tace "This is your battle Anisa. You should fight it alone.. Kin gane."

Sai kuma ta faurzar da huci kad'an ganin Anisa ta tsareta da ido "Fine, naji.. What do I get in return dan wann karon shiri babba zamuyi wanda bazata iya tsallakewa ba."

Anisa ta jinjina Kai tana murmushi "Idan har kika taimaka min na zama matar Haidar komai mai sauk'i ne Leenah. I promise not to let you end your life Washing clothes with bleach just to keep them white."

Leenah ta jinjina Kai tana murmushi "Lokaci yayi da zakiyi abinda kike tsoro Anisa."

Anisa ta dubeta cikin rashin fahimta "Kaman yaya..?"

Leenah tace "Your ultimate goal is to get rid of her for good. Right.?"

Anisa ta jinjina Kai "K'warai kuwa."

Leenah ma ta jinjina Kai "Good..! Then make her disappear for good.."

Anisa ta kuma girgiza Kai "But how.?"

"Kill her Neesa.! Poison her once and for all."

Anisa ta zaro ido waje "A'a Leenah.. What what if our plan fails again..? Kaman dai sauran..?"

Leena ta dubeta "Anya da gaske kin shirya Anisa..?"

Anisa ta dubeta a d'an tsorace "Mai a zai faru idan bataci poison din ba.?"

Leenah ta murmusa "Ba ko wani poison bane ake ci Anisa. Wani shak'ansa ake a iska. A hankali yake lalata lungs kafin a ank'ara sai gawan mutum. Kinga irin wann babu wanda zai zargeki." Ta k'arashe da murmushi saman fuskarta.

Anisa ta murmusa "Yayi. Yanzu ya za'ayi mu samu.?"

Leenah ta murmusa "Wann mai sauk'i ne ki bar min komai a hannuna. Nasan kudi bazai zame miki matsala ba."

Anisa taita murna tana mata godiya. Akan haka suka rabu washe gari suka had'u a mahad'a.

Leenah ta ciro wani mistitsin kwalba cikin jakanta ta mik'a ma Anisa. Anisa hannu na rawa ta amsa dan kwalban da wani ruwa mai kaman acid ciki.

Anisa na juya kwalban Leenah ke mata bayanin yanda zatai amfani dashi.

"Cikin turaren da take yawan amfani dashi zaki zuba kad'an. Muddin tana shak'an wann turaren bazata wuce kwanaki uku tana numfashi ba."

Murmushi Anisa tai. Cikin zuciyarta take fad'in Yazo gidan sauk'i dan ta kula Ummul tana yawan shafa turaren humra da ta kai mata a kwanakin baya Wanda ta sauya turaren da Mommy ta bata dashi. Tabbas zata zuba mata a ciki.

Leenah ta dubi Anisa had'ida gyara zamanta "A baya nayi zaton Hajiya Kwaise bazata tab'a bari D'anta ya auro d'iyar talakawa ba. Nafi tunanin iyayen Haidar zasu nema masa aure ne daga babban ahali. A well known and influential family. Like business partners d'insu ko d'iyar manyan 'yan siyasa kodai d'iyar masu mulki. Amma na sha mamaki yanda ta auro ma d'anta wann yarinyar."

Anisa ta jinjina Kai "Ba ke kad'ai kike mamaki ba Leenah. Shiyasa zuciyata ke tabbatar min akwai wani Abu a k'asa k'ark'ashin wann auren. Massive love d'in da Mommy ke nuna ma yarinyar yafi komai d'aure min kai. Ko ni nan da nake tamkar 'yarta sann mahaifina is a successful businessman banyi zaton zata bari d'anta ya kawo mata ni matsayin sirka ba sanin ko wacece ita. Nafi zaton zata tafi da nisa sai gashi ta k'are a 'yar talaka. Ke da ganin wann al'amari kinsan akwai lauje cikin nad'i. And believe me I vow to find out whatsoever she's hiding."

Leenah ta jinjina Kai "Ta haka ne kawai zaki fahimci komai Neesa. Idan kika kashe yarinyar."

Anisa ta jinjina Kai tana tabbatar da kalaman Leenar.

Daga bisani godiya tai ma k'awarta Leenah sukai sallama Leenah na fad'in sai taji result.

Koda Anisa ta koma gida cikin hikima da dabara ta zuba wann ruwan lungs poison da Leenah ta bata cikin turaren Ummul.

Ta dawo d'aki tai relaxing tana sakin murmushin nishad'i. Nan da kwanaki biyu zuwa uku mataalarta zai kaw. Saidai a fidda gawan Ummul daga gidan. Dan ta tabbata wann karon Ummul bazata haye tuggunta ba.

A fili take furta "Mommy ki gama duk wani shirin da zaki mata. Haidar gawar Amaryarsa zai dawo ya tadda." Tana Ida fad'in haka ta fashe da dariya.

SameenaAleeyou📚

*AUREN WATA UKU..!*

*30*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Tinda jirginsu tai landing a Nigeria Dareen ta rasa sukuni. Ta kula akwai mihimmin abinda yasa suka yanke hutun nasu suka dawo gida Nigeria. Toh amma rashin sanin mak'asudin dawowar tasu shi yafi komai d'aure mata kai. Da fari tayi zaton project d'insa yasa ya dawo amma daga bisani ta kula kaman dai abun nada alak'a da ahalinsa ne musamman ma mahaifiyarsa. Meyasa duk irin aikin da suka tabbata anyi kan Haidar d'in da iyayensa kaman bai wani tasiri tsakaninsa da mahaifiyarsa ba. Kaman dai Har yanzu shid'in koda bai nuna ba can k'asar zuciyarsa yana kwad'ayin Ya mata biyayya. Dan taga call history nasu a wayarsa shida mahaifiyarsa. Kuma tinda sukai wann wayar ya yanke decision d'in dawowa gida. Tabbas ya zama dole ta koma wajen Dodon kobuku ta sanar dashi halinda ake ciki. Tana so aimata aiki na musamman akan mahaifiyar Haidar wacce take ji a jikinta ita d'in nema take ta zame mata barazana. Sann wann zuwan da zatai bazata bari Shadow ya sani ba. Aiki ne da za'a mata ita kad'ai. Ya kamata ta saka rana ta tafi gida Ilorin dan ta gana da Dodo Kobuku. Ta k'arashe tunanin tana kallon fuskar Haidar dake kwance yana baccin gajiyan hanya. Fuskar tasa tayi fayau tamkar Wanda baida wata damuwa. Ta murmusa zallan k'aunarsa takeji na bin duk wani vein na jikinta. Ta Shafa fuskarsa a hankali. Can k'asar zuciyarta take furta 'You are mine Haidar Maitama. Ni kad'ai na. I won't allow anybody to come between us. Not Shadow, not even your own parents. Idan shiga tsakaninku is not enough zan b'ullo maku ta wani hanyar. Idan ta kama na kashe rai ne akan ka zan kashe. Koda mahaifiyarka ce dan na kasance dakai zanyi Haidar. Kaid'in nawa ne. Ni kad'ai.!' Ta k'arashe tana tsura masa ido.

**

Readers Also Read