Auren wata ukku by sameena - Chapter 22
Auren wata ukku by sameena Chapter 22: Auren wata ukku by sameena Chapter 22. Tin farar safiya take gidansu Leenah, ta kasa zaune ta kasa tsaye. Zuciyarta…
4,493 words
Tin farar safiya take gidansu Leenah, ta kasa zaune ta kasa tsaye. Zuciyarta ya cika da tsoron abinda ka iya zuwa ya zo. Yau kwanaki uku kenan da ta zuba poison din cikin turaren Ummul. Ta tabbata izuwa wann lokaci komai zai iya faruwa dan gaba d'ayan ranan ma bataji d'urin Ummul d'in ba. Ta dubi Leenah dake zaune hankalinta kwance tana kallon American movie ta k'araso ta zauna kusan Leenah zuciyarta sai tsinkewa yake "Hey.! What if she's dead by now.? Ko kuma ta shirya min wani makircin tinda kinsan makira ce ta gaske..!" Anisa tace duk a tsorace.
Murmushi Leenah tai tana jefa popcorn a bakinta "You know what Neesa, you should stop being paranoid idan ba haka ba a banza zaki sa ko wani Abu ya sameta a zargeki. And if that happens believe me I won't come to your aid. So ki kwantar da hankalinki ki tashi ki koma gidan ki tabbatar da abinda ya sameta." Ta k'arashe tana duban Anisa.
Jikin Anisa har lokacin a mace yake sanin ko wacece Ummul d'in tinda ta tsallake tuggunsu har guda biyu. Idan ta tsallake wann din ma ba abin mamaki bane. Babban abinda yafi bata tsoro shine wann ya k'unshi kisan kai ba kaman sauran ba. Bata kuma cewa komai ba sai zama da tai can gefe tana ci gaba da tunanin abin yi. Dan tsoronta d'aya ji take kaman idan ta koma gida Ummul zata kamata, reshe zai kuma juyewa da mujiya kaman ko yaushe. Da kyar ta iya tashi tai Sallama ma Leenah ta nufo gida duk jikinta a mace.
Daga can nesa tai tsaye tana hangen sashen Ummul amma bata shiga ba dan har lokacin zuciyarta bai daina bugawa ba. Sauri sauri ta nufi nata d'akin tana tambayan maids ko Ummul ta shigo. Nan wata maid ke sanar da ita bataga shigowarta ba. Da haka Anisa ta nufi d'aki duk a tsorace take. Tana shiga ma kwanciya tai saman gado ta sanar sa maid d'aya ko Mommy ta neme ta tace mata ta dan kwanta bata Jin dadi.
Kwanciyarta da kad'an ta hango mota bak'a k'irar Mercedes GWagon. Gabanta yai wani irin tsinkewa dan wann motar tasan ta Haidar ce. Yaushe Ya dawo.? Da gaske shine ciki.? Kodai idonta ne ke mata gizo.? Da gaske Haidar ne Ya dawo.? Take taji jirin gaske na neman kada ita sanda ta diro daga saman gado. Ta isa jikin window a guje dan tabbatar ma idonta.
Shid'in ne dai looking handsome as always a cewarta. Gani tai ma ya k'ara k'warjini da kyau. A hankali ta furta "Haidar… Mai ka dawo yi..? Meyasa bazaka jira ta cika ba.? Meyasa zaka dawo yanzu..?" Ji tai tana son sanin halinda Ummul ke ciki kafin Haidar Ya cimmata. Sauri sauri tai nufin fitowa daga d'akin sai kuma taja ta tsaya kaman wacce ta tuna wani abu zuciyarta na kuma bugawa. A hankali ta koma da baya ta zauna zuciyarta bai daina bugawa ba.
A b'angaren Haidar kaw tsaye ya hange mahaifiyarsa gaban tsohon hotonsu Wanda akai tun yana k'aramin yaro d'an shekara 10 Wanda bayan shi baya tunanin sunada wani family picture tare.
Hawaye take tana Shafa hoton, at same time tana ci gaba da furta "I want nothing but the best for you.. I know I've never been a good mother to you.. But please give me a chance Haidar.. Ka bani dama na gyara kurakuran da nai a baya. Just this once.." Kuka ya hanata ci gaba da magana.
D'an kauda fuskarsa yai cikeda k'osawa dan yasan hakan bazai wuce d'aya daga cikin acting d'inta ba. Yasan bazai wuce ta hangi motarsa ne ko taji shigowarsa shine tazo gaban picture d'insu take wann wasan kwaikwayon nata in order to gain his sympathy.
"Nice performance Mommy.! I'm here already. I guess the show is over." Yace yana k'arasa shigowa parlorn.
Mommy ta juyo cikeda mamaki tana dubansa. Ta kuma mutsuka idonta. Sai taji murmushi na zuwa saman fuskarta.
"Haidar.. My Son..!" Ta furta cikin rawar murya hawaye basu daina ambaliya a fuskarta ba.
Sai Ta isa da sauri ta rungume shi kukanta na k'aruwa. Tsam ta rik'e sa cikin jikinta. Tana hawaye take furta "I knew it.. I knew You'd come back to me.. To your family. Nasan zaka dawo garemu Haidar.. Nasan bazaka bani kunya ba. Sabida kai d'in D'ana ne.."
Duk sunbatun nan da take ji yake ta cika masa kunne. Yai k'ok'arin cireta daga jikinsa da k'arfin gaske.
"Don't get it wrong Mommy. Idan na dawo na dawo ne kawai sabida project d'in amma ba sabida ke da k'udirinki ba." Yace yana duban mahaifiyar tasa dake tsaye gabansa tana kuka cikin sanyin jiki.
Mommy ta jinjina kai "Even so Haidar. I'm glad ka dawo sabida project d'in. Nafi kowa farin cikin dawowarka. Your wife is waiting for you Aliyu.. She's been waiting for you for the past two weeks.."
Bata kai aya ba suka soma sinkayo hayaniyar wata 'yar aikin gidan tana ihu tana kiran Mommy.
Gaba d'aya Haidar da Mommy suka juyo a tare sanda maid din ta shigo tana haki.
Anisa da hayaniyar ya sanyata fitowa ba shiri ita ta tari maid din da tambayar meke faruwa ta shigo haka tana ihu.
Cikin haki take sanar dasu ta shiga kai abinci section d'in Ummulkhair amma ta tararta a kwance lifeless.
Mommy da taji batun bagatatan saurin k'arasowa tai tana jijjiga mai aikin tana tambayarta mai take cewa. Mai aikin ta kuma nanata binda tace.
Babu shiri Mommy ta fice ba tareda ta bi takan kowa cikinsu ba ta nufi sashen Haidar.
Yayinda Anisa taji kama an yaye mata duka damuwarta. Daga k'arshe dai burinta Ya cika.
Yanda Mommy taga Ummul kwance k'asa tamkar maras numfashi sai ya kuma gigitata. Ta shiga jijjigata tana ambaton sunanta.
Mik'ewa tai cikin kuka tana fad'in ma'aikatan gidan su kira ambulance amma kafin tai wani aune sai ganin Haidar tai ya ciccib'i Ummul d'in Ya nufi motarsa da ita yana Anisa ta isa ta bud'e mata bayan motar.
Mommy ta biyo bayansu cikin sauri Har lokacin hawaye take.
Anisa jikinta duk a mace ganin Haidar ya d'auki kucakar nan ya sakata motarsa harma cewa yake ta bud'e masa motar. 'Kan uba toh wllhi ka d'auki wofi domin kuwa fanko ce wajen gawa ce Babu rai.' Ta fad'i haka cikin zuciyarta.
Mommy ce ta shiga bayan motar ta d'aura kan Ummul saman cinyarta yayinda Anisa tai maza ta shige gaban Motar Haidar ke driving.
Yanda hankalin Mommy ya tashi dole ta baka tausayi. Dan kuka take da gaske tana fad'in Ummul ta tashi kar ta tafi ta barsu ga mijinta Ya dawo gareta.
Daga Anisa Har Haidar d'in sumbatun Mommy ya cika masu kunnuwa cikin motar. Allah Allah suke a isa asibiti ko sun huta da sunbatun Mommy.
Suna isa Ya kuma d'aukanta suka nufi cikin asibitin da ita. Take Likitoci suka amsheta aka nufi ER da ita.
Nan suka zauna suna jiran ba'asi daga Drs. Har lokacin Mommy kuka take yayinda Anisa ke addu'an Allah yasa a fito da sakamako mai dad'in sauraro a kunnuwarta ma'ana ta mutu.
Ganin Mommy bazata daina kuka ba yasa Haidar mik'ewa Ya zira hannayensa cikin aljihun wandonsa. Kukan da Mommy take irritates him musamman idan yaji tana ambaton yarinyar ta tashi mijinta ya dawo gareta. Gaba d'aya ji yake zuciyarsa a cunk'ushe. Meyasa ma bazai tafi ba.? Zaman me yake a asibitin.? He did what he had to do sanda yaga yarinyar kwance lifeless. Ya kawota asibiti. Toh zaman mai zaici gaba da yi.? Yai gajeren tsaki sanda ya kuma duban Mommy dake ci gaba da matsan hawaye. Wani b'angare na zuciyarsa na sanar dashi ka zauna ko dan mahaifiyarka. Ya kuma yin tsaki wai shi Haidar ke yin abu dan mahaifiyarsa matar da bata da wani buri bayan taga ta k'untata masa. Ya kuma yin gajeren tsaki yana mai duban k'ofan ER din.
Can gefe ya matsa dan baya son sauraron kukan da Mommy take.
Anisa sai satan kallonsa take da duk wani motsinsa.
Wayarsa ce ta soma ruri Ya fito da ita daga aljihu nan yaga Dareen ke kiransa. Bai amsa ba sai Ya maida wayar aljihu Har ta k'arashi ringing d'inta.
Hankalin Anisa sosai ya kuma tashi ganin Haidar baibi takan wayarsa ba sann ga damuwa k'arara Ya nuna saman fuskarsa. Mai hakan yake nufi .? Ba dai Haidar damuwa yai da wann kucakar ba Wanda ko wayarsa Ya kasa amsawa. Dan ita duk a nata tunanin damuwar halinda Ummul ke ciki ne ke d'awainiya da Haidar d'in tsaban abinda ta raya ma ranta kenan. Zuciyarta sai wani irin k'una yake mata tana ci gaba da addu'an Allah yasa a fito masu da gawan Ummul kowa ya huta.
A can gidan Haidar d'in kuwa hankalin Dareen yayi dubu Ya tashi. Haidar d'inta ne ke ignoring calls dinta yau. Mutumin da ko important meeting yake zai excusing kansa ya d'aga kiranta musamamn da taga an d'auki lokaci bai returning call din ba. Ita kad'ai sai safa da Marwa take tana jin zuciyarta na mata d'aci. Tana a haka taga wayan Shadow na shigo mata.
SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU..!*
*31*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Tana d'aga kiran ta sinkayo muryarsa daga d'aya b'angaren "I heard that you're back in the country.. Ya akai banji hakan daga bakinki ba..?"
Shiru batace dashi komai ba sai hucin da take dan gaba d'aya zuciyarta a cunkushe take tinda ta kasa samun Haidar a waya. Muryar Shadow ya kuma dakan dodon kunnenta "Dareen are you sure you are not hiding something from me.?"
"Toh mai zan b'oye maka. Yes mun dawo amma ban samu chance na sanar dakai hakan ba. After all, jiya ne kawai muka dawo k'asar. Is not as if na shafe kwanaki ne da dawowa bakaji daga gareni ba."
Katseta yai "Don't you dare take me for a fool. I know you so well. Na sani idan kina shirya wani abun.. Let me warn you Dareen. Idan kika shirya wani abu a bayan ido na believe me zaki d'and'ani kud'arki."
Tai murmushin takaici "Is that a threat.?"
Murmushin shima yai "You know me so well. I don't keep people around with threats. Idan har zanyi abu lokaci d'aya nakeyi ke kinfi kowa sanin hakan."
Yai gyaran murya kafin yaci gaba "Ina Haidar..?"
Ta kuma furzar da huci "How would I know.? Ya fita bai sanar Dani ba."
"You should know Dareen. Because that's what you are there for. Ban ajiyeki tareda dashi ba just for you to have fun with him kin fahimta."
"Oh excuse me! You don't own me.. And you are not the one calling the shots here. Ni ce nake rayuwa da Haidar a halin yanzu… Barazana kawai kake da kake cewa tulun da aka d'aure kurwar Haidar aka shata layin k'iyayya tsakaninsa da iyayensa na wajenka.. Kuma bari kaji from now henceforth bazan bari ka cutar da Haidar ba. Babban kuskuren da ka tapka shine da ka min sanadin shiga rayuwarsa. A halin yanzu Haidar dani are one.. He's my husband da nake sonsa da duka zuciyata.. Bazan bari kai ko wani ya cutar dashi ba. So if I were you zan maida makaman yak'ina."
Murmushi yai daga d'aya b'angaren "Haka kika ce.?!"
Bata bashi amsa ba sai sakin huci da take.
Ya kuma murmusawa "Fine. Zamu gani tsakanin mu biyun Who owns Haidar..!" Yana Ida fad'in haka ya katse kiran.
Dareen taci gaba da kallon wayar tana sakin huci.
**
A can asibiti kaw suna nan zaune jiran tsammani Mommy ta dubi Anisa wacce dama saura su biyu ne zaune wajen "Idan likitocin Sun fito kimin magana."
Jinjina mata kai Anisa tai had'ida amsawa. Tabi bayan Mommy da kallo wacce hankalinta ke ga wayar salularta. Mommy tana ficewa wani corridor d'in ta soma waya da 'yaruwarta Asshe. Nan take sanar da Asshe abinda ke faruwa.
Baki har na rawa Asshe ke tambayarta "Haidar..? Haidar fah..? Ina Haidar Haidar yana lafiya.?" Dan ita duk a tunaninta aikin gama ne Ya riga Ya gama tsakanin Haidar da Ummul.
Mommy ta girgiza Kai kad'an "Asshe Haidar lafiya yake. Hasalima shi yai driving namu to hospital. Amma meyasa kike tambayar lafiyar sa.?"
Sauk'e ajiyan zuciya Asshe tai tana jin gumi da ya tsartsafo mata na bin jikinta yana sauk'a. Lokaci guda tai k'ok'arin saita kanta "Toh amma Aunty Kwaise is possible asirin ne yai aiki. Is possibile amfanin yarinyar ya kare ne. Tinda ita d'in makarin asiri ce."
Kaman Asshe na ganinta haka Mommy ta girgiza kai "Ta ya hakan zai kasance bayan Haidar shigowarsa gidan kenan. Babu wata alak'a data shiga tsakaninsa da yarinyar. Ko kin mance mai Malam Ya sanar damu. Har sai wata alak'a ta auratayya ta gifta tsakaninsu kafin ta karya asirin."
Daga d'aya b'angaren Zuciyar Asshe yaci gaba da tsinkewa. Toh ko dai Anisa tayi shashashancinta ne ta bama yarinyar turaren bata zubar ba kaman yanda ta umarceta. Kodai har mai aukuwa ya auku ne ba tareda Kwaise tayi la'akari ba. Wann abu da d'aure kai yake. Toh amma idan Har illan dake jikin yarinyar bai shafi Haidar ba kaman yanda Dije ta sanar da ita. Ta iya yuwa da gaskiyar Suwaiba Dije fansarta kawai take son d'auka kan yarinyar da uwarta tinda gashi yarinyar ce ke kan gargarar mutuwa kaman yanda bokansu Ya sanar dasu ba Haidar ba. Idan Har hakan ta kasance zatafi kowa farin ciki.
Muryar Mommy ya kuma katseta "Kaina Ya k'ulle gaba d'aya Asshe. Shin idan yarinyar nan ta mutu a haka wann na nufin asirin dake jikin D'ana Ya karye ne kokuwa dai Har yanzu da asirin jikinsa.?"
Asshe ta sauk'e ajiyan zuciya tace "Aunty Kwaise bakida tabbacin idan Haidar bai shiga b'angaren yarinyar nan ba a tsakanin shigowarsa gidan. Kinsan abu ne da aka had'a da asiri kuma wann turaren da Malam Ya bamu ya tabbatar mana shi d'in tamkar magnet ne Wanda zai janyo Haidar zuwa gareta.."
Mommy tai Shiru kaman mai nazari sai kuma ta girgiza kai "Asshe al'amarin nada rikitarwa amma inada tabbacin a lokacin da muka tsinceta kwance k'asa kaman gawa a wann lokacin Haidar ya soma sanyata a idonsa.. Tabbas tayi amfani da turaren inada tabbacin hakan amma bana tunanin amfani da turaren kawai zaisa ta Mutu kafin Haidar ya samu kusanci da ita."
Haidar da isowarsa wajen kenan yai tsaye Cak yana sauraren kalaman Mommy na k'arshe. 'Turare.? Mutuwa kafin shi Haidar ya samu kusanci da yarinyar.?' Ya nanata kalaman da yaji Mommy tace cikin zuciyarsa.?
A razane Mommy ta juyo tana dubansa duk a birkice. Kana ganinta kaga maras gaskiya. Tai saurin canza maganar da take cikin wayar tana mai katse kiran. Ta k'ak'aro murmushin da yafi kama da yak'e ta sakar masa "Em.. Em.. Haidar ashe kana nan baka tafi ba..? Na zata ai ka tafi..?"
Ya girgiza mata kai kad'an alamun a'a "Ina nan Mommy.. Naje sallah ne. Why.? Is there something I should know.?" Yai tambayar yana tsareta da idonsa.
Tai saurin girgiza masa kai alamun a'a.
Ya jinjina Kansa a hankali ba tareda ya nuna mata yaji koda word d'aya daga wayan da ta gama ba. Ya d'an ci gaba da takowa kusanta har lokacin Mommy a tsarge take. Haidar na hankalce da ita.
"Any news about the girl's condition.?" Ya tambaya yana tsare Mommy da ido.
Zuciyarta Ya kuma tsinkewa tana tuhumar kanta mai hakan yake nufi.? Kenan Haidar Ya damu ne da Ummul.?
Bata kai ga samo amsa ba suka hango wani Dr ya fito daga ER d'in. Mommy ce ta nufe shi cikin sauri tana tambayarsa Ya jikin Ummul. Yayinda Anisa ma ta taso daga yanda take zaune ta nufo su.
Haidar kaw daga can yanda yake tsaye yana karantar yanayin Mommy. Meyasa take nuna damuwa gameda yarinyar bayan ga abinda yaji a waya kaman mutuwa take nema ma yarinyar.? Meye nufin Mommy akan yarinyar.? Mecece manufarta na aura masa yarinyar.? Tunani daban daban cikin zucjuarsa. Muryar Dr ya sinkayo yana fad'in "She's still not out of danger. A halin yanzu bazamu iya bada shaida akan komai ba. Anything can happen." Ya numfasa kafin ya dubi Mommy "Is she your Daughter.?"
Kafin Mommy ta bada amsa Anisa tai tsulum ta bud'i baki tace "No she's not her daughter."
Mommy ta k'ara da "She's my Son's wife.. Dr meke faruwa da ita ne.?"
Dr ya d'anyi Jim sai yace "Where's her husband then.? I'd like to speak with him."
Mommy ta juyo a d'arare tana duban direction din da Haidar yake. Anisa ma shi take duba tana jira taji yayi rejecting hakan amma sai taji akasin hakan. Abun mamaki muryar Haidar suka sinkaya yana fad'in "I'm here. I am her husband."
Daga Anisa Har Mommy cikin tsananin shock suke duban Haidar Wanda tuni ya soma takowa kusansu.
Dr yace "May I have a word with you.?"
Haidar ya jinjina masa kai alamun eh "Sure.. After you." Ya k'arashe yana alama ma likitan da hannu.
Dr ya jinjina masa kai kafin yasa kai ya nufi ofishinsa Haidar na take masa baya. Daga Mommy har Anisa mamaki ya hanasu rufe baki. Babu Wanda ya tasammaci haka daga Haidar. Ko ita kanta Mommy da takeda yak'inin maganin bokansu ka iya tasiri akan Haidar tinda ya sanar dasu turaren da suka ba ma Ummul ta dinga amfani dashi zai janyo Haidar gareta batai zaton abun zaizo da sauk'i haka ba. Kenan Watak'ila d'aukanta da yai cikin hannunta har ya shak'i turaren.? Gaba d'aya kan Mommy ya k'ulle ta rasa fahimtar tunanin da take. Gaba d'aya duk abubuwan dake wakana Sun k'ulle mata kai.
Anisa ta sauk'e ajiyan zuciya a hankali tana tinanin kiran k'awarta Leenah dan sanar da ita halinda ake ciki.
**
Dr ya dubi Haidar kafin yace "Amma kana ina har ake barazanar d'aukar rayuwar matarka..?"
Haidar ya jinjina kai lamun nuna rashin fahimta "Ban fahimceka ba Dr. Barazanar d'aukar rayuwarta kaman yaya.?"
Dr ya jinjina kai yace "Sakamakon gwaje gwajen da mukai mata na gaggawa ya tabbatar cewa she's being poisoned… Guba ne da ta shak'esa ta numfashi Wanda ya harba huhunta. Most likely cikin turare aka saka guban."
Haidar yai shiru yana had'a maganganun Likitan da wayan da yaji Mommy nayi. Sai girgiza kai kad'an yace "Turare.?"
Dr ya jinjina kai alamun eh kafin yaci gaba "Irin wann guban akan sanya shi ne cikin wani scent da mutum ke amfani dashi slowly yake lalata lungs d'in mutum ba tareda an ankara ba. Shi irin wann guban anfi amfani dashi ne idan ana so mutum ya samu slow and painful death. Fortunately guban baiyi wani tasiri jikin matarka ba. But we can't say she's completely out of danger har sai mun mata minor aiki a lungs d'insa munyi flushing sauran wann guban to prevent it from spreading. Muna buk'atan saka hannunka Shiyasa na buk'aci ganinka a sirrance. Sann abu ne da Ya danganci criminal act kaga dole ai taka tsantsan tinda ba'a tantance waye perpetrator din ba. Koda tana k'ark'ashin kulawarmu a asibiti rayuwarta na cikin had'ari Har sai an kama mutumin dake k'ok'arin ganin bayan rayuwarta."
Shiru Haidar yai Zuciyarsa Ya kasa aminta da abinda Likitan nan ke fad'i da maganar da yaji Mommy tayi cikin waya. Idan ya had'a maganan Mommy da maganan Likitan nan. The whole thing yanada alak'a da turare kaman yanda yaji Mommy tace sann ta ambaci mutuwa a ciki. Ga turare ga mutuwa. Ga kuma abinda Dr ya sanar dashi cewa anyi poisoning yarinyar ne ta cikin turare. Toh idan Har Mommy kashen yarinyar takeda niyya meyasa ta aura masa ita.? Meyasa zatai poisoning d'inta.? Shin kodai Mommy shi take so tai poisoning shine ta b'ullo ta wann hanyar ta aura masa wann yarinyar ta saka poison din cikin turarenta dan shima ya shak'a su hadu su Mutu gaba d'aya tinda gashi ta matsa sai yazo ya zauna da yarinyar. Shin wann shine shirin Mommy na k'arshe akan shi ta kashe shi ba tareda kowa ya zargeta ba.? Shin har haka Mommy ke masa k'iyayya.? Shin Anya Mommy ita ta haifeshi.? Anya shi d'aya ne daga cikin wann ahalin.? Muryar Likitan ne Ya dawo dashi daga duniyar tunanin da Ya tafi yanda Likitan Ya d'an murmusa dan dik shi a tunaninsa Haidar tunanin aikin da za'ai ma matarsa a lungs yake kar aje a tab'a mata lungs dinta sabida sanin Had'arin irin aiki da Ya danganci organs.
"Look Engr. It's just a minor surgery. We call it Minimally invasive thoracic surgery." Ya d'an numfasa kafin yaci gaba "Is a way of performing surgery in the chest through small incisions, without making large cuts in the body, and it does not require spreading apart of the ribs. We use camera and instruments to get to the lung through small incisions in between the ribs. Kaman ma ba'ayi wani aiki ba haka jikin matarka zai zauna. But it's necessary a dakatar da guban daga yad'uwa cikin jikinta." Ya k'arashe yana mik'a ma Haidar pen da form.
Haidar ya jinjina kai a hankali kafin ya karba yai signing a yanda aka buk'aci Ya saka hannu. Har lokacin ya kasa yarda da abinda ke faruwa. Ya dubi Dr yace "Dr I want this to stay between us please. Ban jima da dawowa k'asar ba so bansan waye ke farautar rayuwar matata ba da kuma dalilinsa. I need to investigate first."
Dr ya jinjina masa kai "Bakada matsala Engr. If you excuse me. Zan koma bakin aiki."
Haidar ya jinjina masa kai kafin suka mik'e a tare suna masabaha cikin mutunta juna.
Sanda Haidar Ya fito ya iske Mommy da Anisa duk sunyi tsuru tsuru alamun suna jiran ba'asi. Babu ya Mommy. Kallo d'aya zaka mata ka fahimci a hargitse take. Ta k'araso da sauri tana tambayarsa Ya jikin Ummul mai Drs suka ce.?
Haidar bai kaiga bata amsa ba dan har lokacin mamakin matar yake Wanda Ya girma ya sani matsayin mahaifiyarsa.
Wayar Mommy ne yai ruri Daddy ke kiranta nan ta matsa gefe tana amsawa dan ita Har ta mance ranan Daddy ke dawowa Nigeria.
Bayan ta Ida wayar ta dawo garesu tana duban Haidar Wanda ya tsareta sosai da ido kaman mai tuhumar ta.
A d'an daburce tace "That was your Dad. Gaba d'aya na mance yana hanya sabida tashin hankalin nan da muka tsinci kanmu ciki. Driver yana hanya zaizo Ya tafi dani.. Yanzu yarinyar ce bansan da waye zamu barta ba."
Anisa tai karaf tace "I'll stay here with her."
Ga mamakinsu muryar Haidar suka sinkayo "No, I'll stay with her. Kuna iya tafiya Mommy. After all, abinda kike so kenan na dawo na zauna da ita. Right.?" Ya k'arashe yana tsare Mommy da ido.
K'ak'aro murmushi Mommy tai tana jinjina masa kai alamun eh. Yayinda Anisa tai mutuwar tsaye tana kallon abun mamaki wai Haidar zai zauna a asibiti da wann bagidajiyar.? Ikon Allah. Wai meke shirin faruwa ne.? Anya Haidar bai kamu da son bagidajiyar nan a kallon farko ba.? Sai tai saurin girgiza kai alamun a'a tana mai kwaban zuciyarta da irin wann tunani maras kan gado. Abu ne da bazai tab'a faruwa ba ko a mafarki. Haidar would never ever fall for someone like her. Muryar Mommy taji tana fad'in suje driver yana close Daddy na gida na jira. Anisa tabi Mommy jiki duk a mace sai waigowa take tana duban Haidar da Ya tsaya kaida fata wai shi zai zauna wajen Ummul. Gaba d'aya mamaki ya kasa sakin Anisa.
Suna isa gida ta shige d'aki tana faman safa da marwa tana tunanin kiran Leenah dan ta sanar da ita halinda ake ciki. Bata Ida tunanin ba taga wayar Haidar na shigo mata. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa sai tana ganin kaman Haidar Ya fahimci cewa ita tai poisoning Ummul. Da kyar ta iya d'aga kiran zuciyarta sai harbawa yake dan tsoro.
Daga d'aya b'angaren Haidar yace "Kina jina. Kije d'akin yarinyar nan ki tattaro mun duk wani perfume dake d'akin ki kawo mun shi asibitin right this instant. Ina jiranki.." Ya k'arada Kar ki bari Mommy ta ganki ko ta fahimci wani abu. Understood.?"
Anisa da zuciyarta bai daina tsinkewa ba a d'an daburce take jinjina kai "Oh ok.. Zanyi yanda kace."
Jinjina kansa yai kaman tana ganinsa kafin ya k'ara tabbatar mata da yana jiranta yanzu yanzu. Daga haka katse kiran yai Anisa kaw gijif ta zauna cikin kujera shikenan asirinta Ya tonu Dr ya sanar da Haidar guba aka saka ma Ummul cikin turare. Yanzu mai zatai..? Taje ta fasa turaren ne ko ta kai masa ne.? Amma idan ta kai masa ta kama kanta ne.. A fili ta furta "Oh no Neesa.. This is not happening. You screwed up again.!" Ta kuma rintse idonta tana tunanin abin yi. Cikin sauri ta d'ago wayarta . Jikinta har na wani irin kyarma ta shiga neman layin Leenah dan samun mafita.
Leenah tana zaune taga kiran Anisa na shigo mata. Ta saki murmushi a hankali kafin ta furta "My stupid friend is calling again." Ta kuma sakin murmushi kafin ta d'aga wayar.
A birkice Anisa ta soma fad'in "Leenah komai Ya lalace.. Our plan didn't succeed.. I'm afraid I messed up everything again..!"
"Girl calm down..! Just… What are you trying to tell me..?" Leenah tace cikin dakatar da Anisa.
A tak'aice Anisa ta bama Leenah labarin duk abinda ke faruwa Har kawo yanzu da Haidar Ya bata tax na kawo masa duka turaren da suke d'akin Ummul. Anisa ta k'arada "Leenah what if he he suspects me.. What if he finds out about the truth cewa ni ce nan na zuba poison din..?"
Leenah ta rausayar da idonta "Here you are being paranoid again Neesa. Ta ya zai zargeki idan ba kece kika basa k'ofa ba. Base on abinda kika ce. Idan har Haidar ya baki tax na kai masa turaren hakan na nufin Ya yarda dake ne."
Anisa ta katseta "Nifa Leenah mafita na kiraki ki bani ba wai kimin narrating abinda na gama baki labari ba. What if I destroy the perfume..?"
Murmushi Leenah tai "Idan kikai destroying turaren shine kin basa room na suspecting d'inki… You know what Neesa, You always call me a moron. But you are the one acting foolish here. Idan har kika lalata turaren nan no doubt Haidar zai zargeki. Idan kuma ya zargeki ki tabbata sunana bai fito ba. Sabida nida kike gani inada burin aure da samun family of my own bana mafarkin karasa rayuwata a jail." Ta numfasa "But wait.. A yanda kika bani labari Haidar yace kar ki bari mahaifiyarsa yasan kin kai masa turaren."
Anisa ta jinina kai alamun eh kaman Leenah na ganinta kafin Leenah taci gaba "Then let him suspect his mother.. Incriminate her. After all, kin sanar dani turaren da kika zuba poison din ma Ummul ciki turaren da Mommy ta baki ki bata ne kika canza da wani. Ya zo gidan sauk'I Anisa. Mahaifiyarsa itace ta bada wann turaren mai guba aka zuba ma matarsa ciki.!"
Dummm.! Haka k'irjin Anisa ya buga. Leenah fah cewa take tai incriminating Mommy. Mahaifiyar Haidar..?
A hankali Anisa ta soma girgiza kai…
SameenaAleeyou📚
*AUREN WATA UKU..!*
*32*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*