Auren wata ukku by sameena - Chapter 2
Auren wata ukku by sameena Chapter 2: Auren wata ukku by sameena Chapter 2. "A usual stuff.. Banyi daidai ba, Dikda bana tunanin Akan wann ne kawai.." Ya…
4,475 words
"A usual stuff.. Banyi daidai ba, Dikda bana tunanin Akan wann ne kawai.." Ya d'an daidaita tsayuwarsa kafin yaci gaba "Nafi zaton kece kika bashi shawarin yai mun wulak'ancin da ya mun.. A naki tunanin ta haka ne kawai zaisa ki fahimci mai kike son fahimta gameda D'anda kika dasa rashin yarda da daidaito a tsakaninku tun yana k'aramin yaro. Na sani ku biyun baku zama on the same page with each other unless wann abun will hurt me deeply. Ko ba haka bane Mommy.?" Ya k'arashe yana dubanta.
Furzar da huci tai had'ida girgiza Kai "It's for your own good Aliyu.. Dik Fad'i tashin da nake inayi ne domin ka zama mutumin K'warai sann rayuwarka ta inganta.. Bazai yuwu bayan tsayin dakan da nake Akan D'ah na na zuba ido rana daya komai ya rushe ba. Aliyu ka daina kwana a gida.. Ka tsiri wasu d'abi'u da ba naka ba.. Some strange behaviors wanda a baya bakayi. A baya baka tab'a maida mun magana kan duk abunda zan umarceka.. But now.. You've changed.. Completely Haidar.. Ina kake kai kudaden da kake fitarwa daga kampanin mahaifinka.. So kake ka hadani fada dashi..? A nashi tunanin nice nake daure maka gindi kake abinda ka so.. A nashi tunanin nasan duk halinda kake ciki.. What he was wrong about shine yanzu Aliyun da ya sani ya banbanta da Aliyu na wanda baya boye mun komai.. D'ah na mai biyayya a gareni koda na kasance mai tsauri akanshi.. Haidar din da baya mun musu koda munada banbancin ra'ayi.." Ta danyi fasali muryarta na rawa tana kuma matsowa kusansa "Aliyu nasan ba shaye shaye kake ba tunda bakayi ba a lokacin da tak'ura da tsanani zasusa kayi. Sann bana tunanin mata ne suka d'auki hankalinka tinda shima bakayi a baya ba lokacin da ya kamata ace kayi idan kai me yi d'in ne… Toh menene ya dauki hankalinka a duniyar nan.. Haidar please.."
D'aga mata hannu yai alamun dakatarwa "Kin rasa wann daman akan D'anki Mommy tuntuni..
Ya dan juyo yana dubanta kafin yaci gaba cikin rarrabewar kalmomi "What I do with my life is none of your Business… You said it right. Ni ba wann k'aramin yaron da kike kullewa a d'aki ki hana masa lokutansa na k'uruciya ki tilasta masa cinye takardu koda baya so.." Ya d'anyi fasali kafin yaci gaba "Kin mance ne na tuna Miki Mommy.? That unhappy little boy ya girma Mommy. Kuma zai yanda yake so da rayuwarsa ba yanda ke kike so ba.. After all, duk abinda kike yi kinayi ne sabida benefits d'inki.. Ba abu guda da kikeyi domin ci gaba na.. Kinayi ne kawai domin amfanin kanki.. Burinki shine ya mallaka min company sabida watak'ila akwai abinda kike tsoro ko kuma yake Miki barazana da rasa dukiyarsa wanda ni ban sani ba.. Shiyasa kike amfani Dani domin na zame miki makamin ki.. D'anki ba komai bane a wajenki face weapon. Yes, I am nothing to you face makaminki. Haka ne Mommy..?" Jinjina kansa yai jin bata amsa ba "Wace irin uwa ce take haka ma d'anta Mommy.? Ya k'arashe idanunsa cikin nata.
Dikda zuciyarta dake harbawa bata bari tsoro ya bayyana saman fuskarta ba. Saima girgiza Kai da take "Don't you dare question my motherhood.. You've no idea what it takes to be a parent..!" Ta k'arashe tana sakin huci.
Jinjina mata kai yai "Eh bansan mene zama iyaye ba kuma bana so nai experiencing daidai da dak'ik'a guda. Kinsan dalili sabida ban taso naga misali mai kyau wajen mutanen da ya kamata na gani daga garesu ba.. " Ya d'an kuma matsowa had'ida sassauta murya "Kin gama sanin duk abinda ke faruwa cikin rayuwar D'anki.. Do you know why..?" Ya tsare mahaifiyar tasa da idanu kafin yaci gaba "Because I'm not that scary little cat da kikai traumatizing d'inshi da son zuciya irin naki. Bazaki sake amfani dani domin cimma burinki ba.!" Daga haka sa kai yai ya shige cikin huci.
Tabi bayansa da kalamansa na kuma dakan dodon kumnuwanta har zuwa tsakar kanta. Salati kawai take.. Meke faruwa da ita..? Meke faruwa da D'anta. Ko zamanin yarinta zamanin da take kulle Haidar cikin d'aki mai duhu bai mayar mata da maganganun irin haka. Hasalima duk abinda zata masa shiru yakeyi. Ya koma kaman mai tsoron mutane, dik yanda mutane suke baya zama baya kuma cewa um balle um um. Akwai lokacin da har sukai zaton ko ya kurmance ne har saida aka had'a masa da therapy kafin maganarsa ya dawo. Ita tsoro abun ya soma bata. Yafi kama da aikin asiri.
Yana tura k'ofan d'akinsa ya hangi Anisa 'yar k'anwar mahaifiyarsa dake aure garin Kano tsaye closet d'insa rungume da rigarsa ta lumshe idanu. Jin an turo k'ofa ya sanyata bud'e idanunta suka kuwa had'a idanu.
"What are you doing in here..? And can you explain why you are holding that..?" Yai mata nuni da rigarsa dake cikin hannunta da idanunsa.
Ta saki murmushin yak'e "Na shigo na gyara maka d'akin ne.. Mommy tace kwana biyu baka kwana a gida.. Nima d'in jiya da dare na shigo garin.."
Baiyi mamaki ba dan Mommy ta turo Anisa d'akinsa. Yasan kad'an ne da aikin Mommy ta turo Anisa tai mata binciken k'wak'waf cikin d'akinsa dukdai dan ta gane what's been going on cikin rayuwarsa.
"Get out.. I need to change.." Ya fad'i yana mai shigewa cikin d'akin lokaci guda yana k'ok'arin undressing Kansa. Suitcase ya ciro Anisa tana gani ya shiga ciro kayansa yana sakawa ciki.
Mamaki ya cika Anisa da ganin yanayinsa. Tasan bai iya fushi ba dukda kuwa ba kasafai kake gane normal days d'insa ba. Definitely dai wani abu na faruwa dashi. Ta girgiza kai kad'an. Sauri sauri ta fito ta nufi wajen da Mommy Ke tsaye tana tsaka da salallami. Anisa d'iyar k'anwar Mommy ce mai suna Asshe dake zaune a garin Kano. Daren jiya tazo gidan dama takan d'an zo tai masu kwanaki lokaci zuwa lokaci.
"Mommy wai lafiya.. Wai meke faruwa ne a gidan nan..?"
Har lokacin Mommy bata amsata ba ta kasa furta koda kalma. A haka Haidar ya k'araso ya shigesu ya barsu nan tsaye suna binsa da kallon mamaki.
"Aunty Kwaise.." Ta kira Mommy da sunanta kafin taci gaba "Wai meke faruwa ne.. Ina zaije shi da suitcase..?"
"Ban sani ba mana Anisa. amma hala Ke zaki iya sani.." Mommy tace a hasale.
Anisa da mamaki bai saketa ba tace "Mommy ta ya zan sani nida jiya jiya nazo gidan.."
Mommy ta shiga janyo hannunta cikin sauri tana fad'in "Binshi zakiyi ki gane mana yanda zaije… Maza maza kafin ya b'ace kinsan yanda car keys suke ai. D'au d'aya ki bi mana bayansa. Kar barshi ya b'ace ma ganinki Anisa.."
Anisa kaw tamkar wacce take jira gudu gudu tai yanda Mommy tace.
Tana tafe saman kwalta cikin k'ok'arin bin hanyar da taga Haidar yabi ganin bai b'ace mata ba kaman daga sama taji an daki bayan motarta da k'arfin gaske wanda hakan yai sanadiyar da motar Haidar ta b'ace mata.
A dole ta danna birki kanta ya daki jikin staring wheel. Kafin ta sami zarafin fitowa daga cikin motar mutumin da ya daki nata motar ya b'ace bashi a wajen. Mamaki ya cika Anisa ganin babu kowa bayanta da alama wanda ya mata wann aika aikan yayi gaba. Ta furzar da huci a hankali tana kuma duba bayan motar.
Bin bayan Haidar da batai ba kenan dole ta koma gida.
**
KANO
Yau d'in yaran Mama sunzo yini daga gidan mazajensu dan tini Mama ta kirasu a waya d'aya bayan d'aya ta sanar dasu abinda ya faru na amshe lefen Ummulkhairy da akai. Dan haka washe gari kaf suka hallara. Sukai bak'e bak'e tsakar gidan suna watsa habaice habaice. Idan an Fad'i abinda ya basu dariya kaji Sun saki shewa harda gud'a.
Umma kaw ta kasa ko fita tsakar gida sabida habaice habaicensu. Ko abincin rana Sun kasa fita suci kasancewar girkin Maman ne. Ta kuma hana Ummul da Khulsum fita ko k'ofa.
Khulsum ta dubi agogo k'arfe d'aya saura na rana. Ta dubi Umma dake zaune ta rapka uban tagumi tana sauraron habaice habaicen Mama dasu Salima.
"Umma lokacin sallan azahar yayi zan fita nai alwala.." Ta Fad'i tana k'ok'arin mik'ewa.
Saurin janyota Umma tai tana aika mata mugun kallo "A haka ne zaki fita su cinyeki da habaice habaice.. Nemi waje ki zauna akwai sauran lokaci." Ta k'arashe tana zaunar da Khulsum da k'arfin gaske.
Khulsum ta dubi mahaifiyarta da tsanin mamaki "Haba Umma dan Allah shikenan har ibada ma kar muyi sabida muna tsoron maganan mutane.. Umma shikenan yau a d'aki zamu yini sabida maganganun mutane.. Umma dan Allah ina kika tab'a Jin mutane Sun fasa magana.. Kuma waye magana ya taba kashewa.? Umma komai mukai wllhi sai anyi magana gara ma ki bari mu fita muyi ibada mu rok'i Allah mafita da zaman tagumin da muke uwar d'aki.. Umma zaman mu a d'aki fah bazai sa su fasa maganganunsu ba.."
Kuka Umma ta kece dashi tana fad'in "Dik ba kece kika jawo ba.. Kin tsaya kina dambe bakin kwalta.. Yo ba da dole Zubairu da yaga haka yak'i dawowa ba.. Nayi imani ba don ya hanngi Ummul na rabon fad'a ba da ya taho ya nemi afuwa ya kuma sa an maido da lefen nan dan Zubairu yaron kirki ne.. Amma jarabar fad'anki ya jawo Zubair ya kufce ma 'yaruwarki.. Dole ma kice kar mu damu da maganganun mutane sabida ba lefenki aka amshe ba.. Wayyo ni Suwaiba wani laifi nai nake fuskantar irin wann iftil'ai..!" Ta kuma d'aura hannayenta aka tana kuka.
Su Mama dake mak'ale bakin k'ofa komai a kunnuwansu. Badia ta janye labule ta lek'o tana fad'in "Gaskiya Khulsum bakida mutunci wann ai zubar mana da mutuncin gida ne dambe da k'artai a bakin layi..!"
Mama tai karaf tace "Ah toh hassada take maku ku da kuka samu Allah ya rufa maku asiri kuke d'akin mazajenku bari tai abinda zai Shafa maku bak'in fenti wajen dangin mazajenku.. Yo sukaji 'yaruwarku guda an kuma amshe lefe da sadakinta d'aya kuma tana dambe da k'artai a bakin layi ai cewa zasuyi duk zuri'arku haka kuke ke Salima me kishiya ta samu abun goranta Miki.."
Haba nan fah Salima ta kuma harzuk'a ta fad'a d'akin tana kokawan janyo Khulsum tana fad'in wllhi bata isa ta kashe mata aure ba.
Umma na kuka take rok'on Mama da yaranta da sukai ma Khulsum taron dangi suyi hak'uri su fice. Itakam Ummulkhairy kuka ma ya hanata katab'us yayinda Mama ke kuma ingizasu. Kan kace me ayarin yan cikin gidan Sun cika a k'ofan sashen su Ummulkhairy suna bama idanu abinci. Tuni masu jin haushin Khulsum suka goyi bayan Mama da yaranta cewa Khulsum zata b'ata masu sunan ahali bayan fentin da Ummulkhairy ke Neman shafa masu suma ak'i Neman auren yaransu.
Ana wann kacaniyar mahaifinsu ya dawo daga Kasuwa. Ganin iyalansa haka yasa shi Jin kaman wani abu ya sokesa a k'ahon zuciya. A hankali ya dafe k'orjinsa yana k'ok'arin silalewa.
SameenaAleeyou…📚 *AUREN WATA UKU.!*
*05*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
K'ara Badia ta saki sakamakon hango mahaifinsu da tai yana k'ok'arin kaiwa k'asa. Nan kuma hankula suka koma kansa. Mama ta k'araso da sauri ta tallafesa tana fad'in "Malam dan Allah ka rufa mana asiri kar bak'in cikin Ummulkhairy yai ajalinka.. Wayyo ni Tani.. Sannu Abban Salima.." A haka ta k'arasa dashi madaidacin parlonsa tai masa masauk'i saman d'aya daga cikin lamusassun kujerun dake a cikin parlorn. Sai jero masa sannu take tana bangaje Umma daga kusansa. Badia ta kawo mafifici Mama ta amshe tana masa fifita tana fad'in maza ta kawo ruwa.
Bayan shud'ewan wasu mintoci Abba ya soma dawowa hayyacinsa.
Gaba d'aya ya had'e matan nasa guda biyu. Ya d'an kishingid'a yana dubansu. Lokaci guda yake furta "Tani, Suwaiba.."
Kowaccesu ta amsa jiki a sanyaye.
Abba yaci gaba "Bazai yuwu ku maida min gida kaman gidan kallon kwallo ba.. Ke Tani kin gayyato yaranki Sunzo kuna murnan abinda ya samu 'yaruwarsu.. Ke kuma Suwaiba kin saka ma ranki damuwan abinda Allah bai saka Miki ba.. Ita rayuwar nan wai duka kwana nawa ne za'ayi.. Kun raba mun kan ahali kun maida min gida kaman gidan maguzawan farko.. Idan kaji hayaniya na tashi a gidan nan toh wann k'ofan ne.. Akan wani dalili..?" Ya d'anyi fasali yana dubansu kafin yaci gaba "Toh ku kula.. Ku kuma tuna cewa duk abinda Kai a wann rayuwar shi zakaje ka cimma a cen.. Bazan gushe ba ina maku nasihan kubi duniya a sannu rayuwar duka ba yawa ne da ita ba.. Bazan bari ku saka mun ciwon da bani da shi ba.."
Murya a sanyaye Umma tace "Kai hak'uri Abban Ummul in sha Allah zamu gyara.. Ko Yaya..?" Tai maganar tana duban Mama.
Mama ta saci idanun mijin nasu kafin ta aikama Umma harara sama da k'asa sai kuma ta juyo da duban nata ga Abba. Tai murmushi Wanda yafi Kama da yak'e "Eh in sha Allah zamu gyara mun tuba Kaji Malam..Allah ya baka lafiya."
Jinjina Kai yai yace "Alhamdulillah.. Allah ya ganar damu baki d'aya ya kuma had'e mana kan ahalinmu ya shirya mana zuri'armu."
Gaba d'aya suka amsa da Ameen. Abba yai masu izinin tafiya sai kuma ya dakatar da Umma yace ita ta tsaya.
Wani birki Mama taja kaman zata dungura ta juyo tana duban Abba da yace Umma ta tsaya bayan yau girkinta ne.
"Malam ban gane Suwaiba ta tsaya ba.. Ni ce da alhakin abincika yau fah ko ka mance ne..?" Tai maganar tana tururi kai kace ba itace yanzu ta gama ce ta tuba ba.
Abba ya murmusa yana ayyanawa cikin zuciyarsa Mata sai a barsu wajen kishi. So tari yakan yi ma Mama uzuri dan kishi Tabbas akwai ciwo. Wani abun yasan zafin kishi ne kawai yake sanyata yi amma Tani d'insa tanada halin k'warai.
"Magan zamuyi Tani ba wani abu ba.." Abba yace cikin sigan lallama.
Mama ta kad'a Kai "Aiho.. Kardai garin dad'in zance a zarce a shiga hakki ehe..!"
Murmusawa kurum Abba yai ba tareda yace komai ba.
Saida Mama ta fice ya dawo da dubansa ga Umma.
"Suwaiba.." Ya kirawo sunanta
"Na'am Abban Ummul."
"D'azu a kasuwa mak'ocin shago na ke jajanta mun al'amarin auren Ummulkhairy."
Umma ta jinjina Kai alamun tana sauraro.
Abba yaci gaba "Bansan ko kin gane shi ba mai babban kanti na kayan masarufi da yake jikin nawa kantin.. Wasu lokutan har rancen kaya yake bani idan na saida na mayar masa uwar kud'i hardai jarin nawa ya d'an ja baya. Mutumin kirki ne Alhaji Kamilu.."
Umma ta jinjina Kai tace "Allah sarki.."
Abba yaci gaba "Toh nan dai nake labarta masa al'amarin ita wann yarinya nawa Ummulkhairy.. Toh kwatsam sai ya sanar Dani yana so na bashi auren ita Ummulkhairin idan babu wani matsala.. Toooh wato gaskiya banyi garajen amsa masa ba duba da irin abubuwan dake faruwa. Ak'alla aure nawa ake sakawa na Ummulkhairy abu baya yuwa.. Sann ko sati ba'ayi ba da abinda ya kuma faruwa na amshe lefen shi yaron nan Zubairu. Amma dukda haka bazaka yanke tsammani daga rahamar Ubangiji ba. Ba wann dalilin ne yasa nace ya dakata ba.. Babban dalilina shine sai naji daga bakin 'yata idan tana sonsa.. Idan har bata sonsa JINKIRIN aurenta bazai sa na aura mata mutumin da bata so ba.. Sabida shi Alhaji Kamilun lallai lallai ya nuna mun yana son na basa dama kuma Kinga akwai 'yar kunya a tsakaninmu… Tooooh dai gaba d'aya kaman ya d'aure ni ne.. Dan a gaskiya.." Sai ya d'anyi Shiru kuma kaman mai nazari "Bana so Ummul taga kaman na tak'ura mata da batun aure ne tinda dudu ba'a jima da fasa.."
Bai kai aya ba Umma ta katsesa "Haba Abban Ummul.. Ta ya ma zakace haka.. Yo har wani lokaci zaa d'ibar mata.. Shifa lokaci baya jira. Ka duba sa'anninta duk suna d'aki daga masu yara uku hudu kai har masu shida akwai sa'anninta… Yo ai ko ta gansa ko bata gansa ba tinda har zai rufa mana asiri ya aureta ai shikenan.."
Katseta yai da fad'in "A'a Suwaiba, JINKIRIN Ummulkhairy ba zaisa na tilasta mata kasancewa da Wanda bata so ba.. Kece mahaifiyarta, ki kirata a d'aki a natse ki sanar da ita. Idan tayi na'am falillahil hamdu yau da dare sai na d'aga waya na kirasa gobe idan Allah ya kaimu sai yazo su fahimci juna.. Alhaji Kamilu mutumin kirki ne kuma yanada matan aure biyu da yara da d'an dama.. Ki kira ita Ummulkhairy ki sanar da ita a natse. Idan Sun daidaita kansu shikenan sai ai maganan aure tinda babban mutum ne ba wani Jan lokaci za'ayi ba. Hasalima Jan lokacin baida wani alfanu.."
Umma tai karaf tace "Ai ko gobe ma sai a d'aura kawai nidai ta tafi d'akinta.." Ta d'aga hannu sama tana fad'in "Oh Allah na gode maka ni Suwaiba.. Allah maji kukan bawansa mai maida asara da alkhairi.."
Girgiza kai kurum Abba yai yana dubanta. Zaman Ummu a gabansa bai d'aga masa hankali ba kaman fitinar mahaifiyarta matarsa Suwaiba . Fatansa Allah ya had'a Ummul d'insa da miji na gari wanda zai kular masa da ita ya kaunaceta tsakani da Allah dama sauran yaransa gaba d'aya.
Cikeda farin ciki tamkar wacce aka yaye mata kaf damuwarta na gidan duniya haka Umma ta fito tana k'wlla kiran Ummulkhairy.
A daidai bakin farandar d'akin Abba ta riski Mama rik'eda farantin abincin Abban. Umma tana ganinta ta tsuke Baki tana zancen zuci Wanda sam bata san ya fito fili ba tsaban farin cikin da ta tsunduma ciki "A sirrace nema a bayyana samu."
Rangaji Mama take tana dubanta daga sama zuwa k'asa. Kafin tai murmushi mai sauti tace "Ayi dai mai mu gani wai gurguwa da auren nesa." Ta k'arashe kaman zata bangaje Umman ta nufi parlorn Abba.
Umma ta tab'e Baki ta nufi d'akinta cikeda farin cikin abin alkhairin da ya sameta dan yau d'in Ji take burinta na gidan duniya ya gama cika.
**
Abuja.
Cikin bacci yake Jin vibrating d'in wayarsa na kuma k'aruwa alamun wayar ta gaza yin Shiru. Yai k'ok'arin mik'ewa had'ida janye Dareen dake kwance saman k'irjinsa. Hannu yasa ya d'auki wayar dake aje gefen bedside yana ganin lokaci quart after six na safiya. Lokaci guda ya d'anyi relaxing jikin pillow yana k'ara wayar a kunnensa yana rage girman idanunsa masu cikeda bacci wanda hasken hantsi da ya soma bayyana ya tilasta masa yin hakan.
"What Hisham." Ya Fad'i yana gyara zaman wayar a kunnensa.
Daga d'aya b'angaren Hisham Yace "Haidar, Kana Ina ne.. me kakeyi..?"
Da mamaki Haidar yace "What kind of question is that..? What could I been possibly doing at this time..? Bacci nake obviously kafin ka tadani."
Hisham ya katsesa "Have you seen the news..?"
"What news..?" Haidar yace cikin muryarsa mai cikeda bacci.
Hisham ya furzar da huci "Lallai na yarda kana bacci.. Check your phone ka karanta labarun kasuwanci kaga abinda muka tashi dashi." Daga haka katse kiran yai yayinda Haidar ya shiga shafa wayarsa. Tin daga saman fuskar wayan yake karo da notifications.
Notification guda d'aya ne ya d'auki hankalinsa. THE BUSINESS PRESS. Yanda aka rubuta *Top Business Scandal.* Saurin clicking yai ya shiga kan labarin. Abinda ya soma karo dashi a labarin shine hotonsa da mahaifinsa lokacin da ya cakumosa a cikin Kampaninsu yana jijjigasa yana fad'in yayi disappointing d'insa, daidai wajen akai cutting a video d'in Wanda aka fitar da hoton sosai yanda ya rik'e kwalan Haidar d'in ga jini gefen bakin Haidar. K'asan hoton kad'an an rubuta kamar haka *Owner of Maitama Builders Engr Aliyu Maitama gets into a physical fight with Son over augment.*
"Damn it..! This is not happening." Ya furta a hankali. Sauri sauri ya mik'e ya shige bathroom dan shiryawa.
Dareen dake baccinta peacefully ta soma bud'e idanunta masu cikeda bacci wanda ko shakka babu shirin da Haidar d'in keyi ne ya katse mata baccin.
Ta zuba masa idanu tana duban yanda yake komai a gaggauce. Ta saki murmushi zallan k'aunarsa cikin zuciyarta. A hankali ta sakalo k'afafunta ta sauk'o daga saman gadon.
Yana tsaye gaban full length mirror yana k'arisa shiri yaji ta rungumosa ta baya had'ida matsesa sosai cikin jikinta.
"Good morning.." Ta furta tana mai d'aura hannayenta saman nasa ta amshe agogon da yake k'ok'arin d'aurawa taci gaba da d'aura masa "Are you leaving this early..?" Tace sanda take kaikaitowa ta dawo ta gabansa.
"I have to.. I need to take care of something.. I'll see you later.." Yace a tak'aice yana d'aukan wayarsa da mabud'in mota
Ta take masa baya ganin zai fice cikin sauri. Ta kamo hannunsa guda "What about breakfast..? Your cool tea is in the fridge.. Tun asuba na had'a maka.. The way you like it.. Should I serve you..?"
D'an dubanta yai kafin ta girgiza kai "Kar ki damu, I'll be fine.."
Ta kuma rik'e hannunsa "Does that mean ka amince da k'orafina ka fasa aje aikinka a Kampanin Daddynka.?" Tai maganar idanunta tar akansa.
Ya d'anyi still yana dubanta "I don't know… I'm not sure.. I.. must go now.. Take care.." Ya k'arashe yana shafan b'angaren fuskarta guda da tafin hannunsa.
Ta janyo hannunsa ta sumbaci tafin hannun kafin ta sakar masa murmushi tana masa fatan nasara har saida taga tashin motarsa. A hankali ta lumshe idanunta had'Ida sauk'e ajiyan zuciya kafin ta koma cikin gidan.."
ya d'auki car keys d'insa da wayarsa ya fice a gaggauce.
Yana tafe saman kwalta wayar Hisham amininsa kuma abokinsa a wajen aiki ya kuma shigowa.
"Haidar this is bad.. Very bad.!" Abinda Hisham yace kenan koda Haidar ya d'aga kiran.
Jinjina Kai Haidar yai "Yanzu zaka yarda da magana na.. Someone is sabotaging the company.. And trust me, I know exactly how to catch that rat." Shiru yai alamun yana sauraro daga b'angaren Hisham.
Hisham yace "Kuma ba yanda za'ai ka kamo wann b'eran har sai kana aiki da Kampanin. Now more than ever you can't quit your job.. You need to fix this Haidar.. You need to clear your Dad's name.. Bazaka bari sunan Kampanin ya b'aci ba..!"
"Oh Shut up Hisham..!" Ya fad'i yana mai katse kiran lokaci guda yana mai k'ara gudun motar.
A can gidan mahaifinsa kaw ya tsare mahaifiyarsa ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Ga 'yan jarida sunyi chaa a bakin gate suna jiran fitowarsa.
Yaci gaba da nuna Mommy da yatsa "Call that pathetic son of yours and tell him to fix this mess immediately.. Bayan asaran da zamu tapka sabida shashashancinsa, I won't allow him to ruin my company's image.!" Ya k'arashe cikin tsananin huci yana mai ci gaba da zagaye katafaren parlorn nasa.
Furzar da huci Hajiya Kwaise tai, tana mai kuma dialing layin Haidar amma shiru bai d'agawa.
Dad ya kuma dubanta "He's not answering right..?"
D'an lumshe idanu tai had'ida mik'ewa tsaye "Engr please calm down."
Ya kuma katseta "Seriously Kwaise..? Are you asking me to calm down.? Ko bakiga babban abun kunyan da wann shashashan d'an naki yai bane.. Kwaise, I'm a highly respected person. A well known businessman. I have a reputation to protect.. Bazan bari wann d'an naki ya ruining d'ina ba."
Izuwa lokacin cikin ta tunzura itama "Aw laifin Haidar kake gani..? Kai bakaga laifinka ba.. Kan wani dalili zaka cakume kwalan d'anka a bainar mutane.. Cameras all over ba dole masu Neman ganin bayanmu suyi amfani da wann damar ba.. Yanzu sai ka yarda da maganan Haidar da yace maka akwai mai maka zagon k'asa cikin mutanen da ka aminta dasu.."
Katseta yai cikin b'acin rai "This is natural in a business world. We've business rivals and competitors. So ba abin mamaki bane idan sunada spy cikin Kampaninmu.. Amma babban abun takaicin shine yanda muka gaza handling such situations.. And this is all your Son's fault.. He's weak, idiot.. A pathetic loser.. Yana can ya saka mata a ransa.. What do you expect..?"
Ya kuma jinjina Kai yana sakin huci sai yarfe gumi yake kai kace ba sanyin AC ne ke circulating cikin parlorn ba.
Isowar Haidar k'ofan gidan mahaifin nasa yai tozali da dandatson 'yan jarida. Ai kuwa kaman jira suke suka nufosa suna jefo masa tambayoyi ta ko ina. "Yallab'ai Aliyu. Da gaske ne mahaifinka ya tareka da fad'a bayan cecekuce da ya kaure tsakaninku cikin Kampanin mahaifin naka..? Engr Maitama ka amsa mana.."
Da kyar ya samu ya kutsa cikin gidan sabida tambayoyi da kalaman da manema labaren keta jefo masa.
Yana dosowa parlorn Daddy ya nufesa a zafafe kaman zai shak'o sa Mommy tai saurin shiga tsakani cikin k'ok'arin dannar mijinta.
Sosai yake huci kaman zai kifa k'asa yana nuni da Haidar hannunsa har rawa yake.
"You.. You and your entire existence is a disappointment..! Kai kayi kad'an ka lalata mun suna da sunan Company.. You better find a way to fix this mess kafin business rivals d'inmu su samu abun yawo damu kaji na fad'a maka.. Bazan tab'a bari bak'in cikinka yayi ajalina ba.. I will make sure to cut you off kafin hakan ta kasance.." Yatsanshi na rawa yaci gaba da nuna Haidar "So Kar ka sake kayi abinda zaisa na haramta maka amfani da sunana..!" Daga haka sa Kai yai ya haura sama dan a halin yau fita ma bai ganshi ba 'Yan jaridu ta ko ina. Dan yasan K'iris abokan adawansu na kasuwanci Ke jira. Har yayi step biyu ya kuma juyo ya dubi Haidar da idanunsa suka kad'a sukai jazir "Kaje ka sallami mutanen can da ka tara mun kof'ar gida.!" Yasa kai yaci gaba da haurawa.
Furzar da huci Haidar yai yasa kai zai shige. Dan yasan mahaifinsa bazai tab'a sauraransa ba. Momy ta dakatar dashi
"Mom please not now.!" Ya katseta da fad'in haka.
Cikin rawar murya take furta "What's wrong with you Haidar.. Why are you doing this to us to yourself.. Meyasa ka maida iyayenka Abokan gabanka.. Why can't you open your eyes and see my son.. Your Dad is only trying and struggling to make a proper man out of you.."
"Oh really Mom.! Is he really trying to make me become a better person by pressuring me to meet all his expectations..?" Muryarsa ya soma rawa sanda yake furta "Na gaji.. Na gaji.. I'm fed up with everything around here..!" Bai kuma tsayawa sauraronta ba yasa kai ya fice yana haki da huci ga wayarsa da ta gaza yin Shiru. Kira ne keta shigo masa.
Saiga Mommy ta koma gefe tana hawaye. Meke faruwa da rayuwar ahalinta.. Meke damun Haidar.. Dik yanda akai something is wrong a wani wajen.. Zama bai ganta ya zama dole ta tashi tsaye. Da wann tunanin ta nufi nata b'angaren duk jikinta a mace kaman dai ba Mommy ba. Mace mai zafi da jajircewa.
Jiki a sanyaye Anisa ta k'araso rik'eda waya ta mik'a ma Mommyn tana fad'in "Ammi Ke son magana dake tana ta kiran wayarki bata samu."
Mommy tana amsar wayar ya fashe da kuka tana fad'in "Asshe ba lafiya.. Asshe gidana a hargitse yake.."