Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 3

Auren wata ukku by sameena - Chapter 3

Auren wata ukku by sameena Chapter 3: Auren wata ukku by sameena Chapter 3. Jin haka yasa Anisa komawa dan ta baiwa 'yan uwan waje su tattauna. Sosai…

4,492 words

Jin haka yasa Anisa komawa dan ta baiwa 'yan uwan waje su tattauna. Sosai hankalinta ya tashi da ganin yanayin Mommy dan tinda take bata tab'a ganin 'Yaruwar mahaifiyar nata cikin irin wann yanayi ba.

**

KANO

K'aton parlor ne mai d'aukeda kekunan d'inki kusan guda biyar. Yafi kama da wajen koyon d'inki.

Wata mata ce da ta d'an data a shekare tsaye cikin babban zauren tana duba kekunan.

Ummulkhairy ce ta soma halarta cikin d'aliban nata. Dama ita d'in da wuri take zuwa kafin lokaci yayi dan ta taimaka da share share da gyare gyare.

Sallama saman bakinta ta shigo.

Matar ta fad'ad'a murmushinta "Wa'slaikissalam uwar alkhairi. Dan haka take kiran Ummul d'in a akasarin lokuta.

Ummulkhairy ta risina ta gaidata. Ta amsa kaman ko yaushe da sakin fuska "Uwar alkhairi kece dai kullum akan gaba kina masu wayo kina kwashe ladan. Wataran bazaki huta ba.. Jiki da jini Ummul kink'i ayi maku roster da kowa tasan ranan nata aikin."

Ta murmusa "Hajja ai nafi son na tara ladan da albarkan ni kad'ai ne.."

Hajja Fannah ta murmusa "Ai kuwa da izinin Allah albarka na bibiye dake.. Kinci sunanki uwar alkhairi.."

Murmusawa ta d'anyi kad'an jikinta na kuma yin sanyi da kalaman Hajja sakamakon tuno tashin hankalin da ta baro a gida. Ta mik'e da sauri gudun kar Hajja ta fahimci yanayinta ta d'auko tsintsiya zata soma shara Hajja da tuni ta karanci yanayinta ta dakatar da ita.

"Zo nan Ummul, zo ki zauna magana zamuyi kafin sauran d'aliban su k'araso. Bar sharan nan." Tai mata nuni da gefenta saman tabarma.

Jiki a sanyaye Ummulkhairi ta isa ta zauna.

Hajja ta gyara zamanta "Fad'a mun me Ya faru.?" Hajja Fannah ta jefo mata tambayar dan dama tana sane da halinda Ummul d'in ke ciki. Gidanta na bayan layin su Ummul layin da ke babban kwalta. Hajja Fannah tanada shagon d'inki da yara maza masu d'inki a shagon ta dake gaban gidan nata yayinda take koyar da 'yanmata sana'ar d'inkin a cikin gidanta. Sunyi sabo mai tsafta da Ummul tin sanda ta soma koyon d'inki wajenta. Tana bata shawarwari had'ida kwantar mata da hankali hakan yasa Ummul ke samun sanyi wajenta, takan kai mata damuwarta su zauna su tattauna ta kuma bata shawarwari masu amfani a gareta had'ida nitsa zuciya.

Ummul ta d'an share hawayen da suka gangaro mata "Hajja wllhi na gaji.. Harga Allah na gaji.. Ita fah Umma ko wanne irin mutum so take na aura babu ruwan ta ko ina san wann mutumin ko bana so.. Ita burinta kawai nai aure da farin ciki ko babu. Ni kuma a halin yanzu wllhi batun auren nan ya fita kaina ni sana'ar nan da nake nafi samun kwamciyar hankali cikinsa fiyeda komai. Shin wai ita mace ba'a mata uzuri ne a rayuwar nan..? Hajja ba biye biyen maza nake ba.. Allah shine sbiadana ina k'ok'arin tsare mutuncina.. Sann azumin litinin da Alhamis duk basa wuceni ba wai dan na Gaza rik'e kaina ba sai dan sabida nasan shi azumi garkuwa ne Hajja.. Amma ita Umma duk fah bata ganin wann. Ita kawai damuwarta mutane da abinda suke Fad'i.. Shin Hajja menene laifin wacce Allah ya jarabceta da JINKIRIN aure..?" Ta k'arashe damuwa fal fuskarta hawaye na kuma gangaro mata.

Girgiza kai kad'an Hajja Fanna tai, cikeda tausayi. Ta kuma gyara zama tana duban Ummulkhairy "Ummul, shi fah d'an Adam a koda yaushe bai rasa abin Fad'i.. Sann har abada bazaka tab'a Iyar masa ba.. Mutum sai Allah.." Ta kuma gyara zamanta "Wato muna cikin wani irin Al'umma ne da k'addararka take iya zama zunubi a gareka.. Mai nake nufi da k'addararka tana zama zunubi a gareka? Macece Allah zai jarabceta da JINKIRIN aure sai kiji mutane suna cecekucen cewa ta zauna a gida tak'i aure. Idan wacce take karatu ne sai kiji ance ta rungumi boko tak'i aure.. Idan ma Sana'a take dan ta rufa ma kanta asiri sai kiji ana cewa maza ke bata kud'i ta Kama Sana'a ne dan ya zame mata garkuwa kar a zargeta.. Ita dai mace wai bazata rayu ba saida tallafin namiji. Mace ce Allah zai jarabceta da mutuwar aure sai kiji ana cewa ta kashe aurenta ta dawo gida bazaki tab'a Jin ance miji ya kashe mata aure ba sai k'alilan a'a itace dai Sarkin laifi. Kuma babban abin takaicin mutanen da tafi kusanci dasu Sune mutanen da take soma fuskantar k'alubale daga wajensu. Kowa sai ya tsangwameta a cikin gidan baga iyayenta ba baga 'yanuwanta ba a wasu lokutan. Kinga a nan k'addararta ya zama kuskurenta." Ta d'an numfasa kafin taci gaba "Ummul ba ina fad'a Miki haka bane dan kiga laifin iyayenki ko wani abu mai Kama da haka. A'a ko d'aya, burin ko wasu iyaye shine da zaran 'yarsu ta isa aure su ganta a d'akin mijinta. Kuma babu iyayen da zasu so suga auren 'yarsu ya Mutu. Toh amma idan jarabawan Ubangiji ya shigo ciki sai ayi hak'uri a fawwala masa lamuran. Ka tsara rayuwarka yanda kake burin Ubangiji ya tafiyar maka da ita tareda fatan mafarkan ka su cika ba laifi bane hasalima Wanda baya planning rayuwarsa baisan ina ya dosa a rayuwar ba. Toh amma wasu lokutan yanda muka tsara ba haka rayuwar take zuwa mana ba. Dalili kuwa shine ba muke da hakkin tsara rayuwar ba iyakacin namu mafarkai da burika had'ida fata na gari. Ubangijin duka shike tsara mana rayuwar yanda yaso. Kuma tsarinsa a koda Yaushe shine daidai. Idan ya amsa mana addu'anmu ya tabbatar mana da burinmu da fatanmu sai muyi farin ciki mu kuma gode masa. Sann idan ya jarabcemu ya janye wann fata daga garemu bamu samu abinda muke mafarki da buri ba shima sai mu masa godiya sabida shi yasan abinda yasa ya hana mu kodai abin mai cutarwa ne a garemu. Ko kuma ya mana tanadin Wanda yafi wann." Ta kamo hannun Ummulkhairy cikin nata "In every delay, I believe there's khayr.. Just like your name Uwar alkhairi. In sha Allahu JINKIRINki zai zamto cikeda d'imbin alkhairi.. Babban abinda zan Miki wasiya dashi shine biyayya ma iyaye. Kar ki kuskura koda wasa ki fasa musu biyayya matuk'a bazasu ce ki sab'i mahaliccinki ba.. Idan kika rik'e biyayyan iyaye alkawarin Allah ne rayuwarki zai cika da d'imbin alkhairi kinji ko.."

Ummulkhairy ta jinjina mata Kai a hankali kyakkyawan murmushi saman kyakkyawan fuskarta. Hak'ik'a tana samun relief da kalaman Hajja Fannah. Inama Ummanta zata kasance mai fahimta kamar haka. Sallaman wasu daga cikin d'aliban yasata k'ok'arin saita kanta Hajjah Fannah na fad'in ta kwantar da hankalinta komai zai shige ya zama tarihi da izinin Allah. Ta mik'e tana amsa gaisuwan 'Yanmatan da suka shigo tana fad'in yau dai Ummul d'inta zata huta Sune zasuyi shara su gyara waje.

Daga can bakin Layi Alhaji Kamilu Ya aje motarsa Mama na biye dashi tana fad'in "Kai dai muje ka bama idonka abinci Alhaji."

SameenaAleeyou📚

*AUREN WATA UKU..!*

*06*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

K'ofan gidan Hajja Fannah Mama ke nuna masa "Yauwa Alhaji. Nasan Kai mutumin kirki ne. Ance matanka ma ko fita unguwa basayi tsaban yanda kake kaffa kaffa da iyalanka. Toh kaga can yanda kaga mata da maza suna safa da marwa."

Alhaji Kamilu ya kuma duba k'ofan gidan wanda shaguna suka saka a tsakiya ga samari sai kai komo suke tsakanin shagunan can gefe harda shagon aski ga 'yanmata masu sana'an koyon d'inki suna Kutsawa suna shiga gidan Hajja Fannah.

Mama taci gaba "Toh wann gida dai dake gani Ummul tana ciki da ita ake wann kai komo tsakanin wad'ancan samari marassa tarbiya masu aski irin na shed'an." Idanun Alhaji Kamilu ya sauk'a samarin da Mama Ke nuni dasu wanda suka fito shagon Aski gana ganinsu kaga samari marassa tarbiya ga wani aski da aka musu an kwashe gefe d'aya an bar d'aya. D'aya saurayin ma harda sark'a a wuyansa.

Alhaji Kamilu yai Shiru kaman mai nazari. Sai kuma yace "Da zaran na aureta ta dena fita ko k'ofa dan mata na ko taron biki da suna basa zuwa babu yanda suke zuwa sai asibiti da ya zama dole."

Mama tai 'yar bazaurar murmushi "Toh ai Alhaji ba a nan gizo Ke sak'an ba." Ta kuma gyara tsayuwarta "Kaga wann gida da Ummul Ke zuwa da sunan koyon Sana'a. Matar gidan ba kowa bace face gasunk'umar kawaliya. Wllhi nake fad'a maka Alhaji ta addabi kowa ta fitini kowa a unguwar nan. Mata take tarawa cikin gidanta maza kuma suna daga waje a shago. Maza take had'awa waje mata kuma cikin gidan ayita aikata masha'a ana aikata alfasha. Kuma ba zallan 'yanmata harda matan aure a wann bad'ala da take had'awa. Na tabbata bazaka so ka auri yarinyar da ta gama watsewa wajen wann hatsabibiyar Matar wacce ko aure bata dashi zaman kanta take zaman daduro.. Wann shago da koyar da sana'a da take cikin gidanta ba komai bane face rufa rufa gudun idon mutane. Amma mu da mukaga jiya mukaga yau a unguwar kowa ya kwana da sanin Kawaliya ce. Amma idan baka aminta da abinda nake fad'a maka ba zaka iya tare mutanen unguwar nan ka tambaya Kaji idan ba zaman kanta take ba. Ko aure bata dashi babbar Magajiyar karuwaice. Kaf 'yanmata da matan aure dake zuwa wajenta da sunan koyon sana'a, karuwanci suke fitowa su fake da san'a. Meyasa Ummul tak'i aure..? Kai bakai ma kanka wann tambayar ba. Mace har mace kyakkyawa irin Ummulkhairy ta gaza samun mijin da zai aureta.. Ai kaima kasan da walakin wai goro a miya."

Ganin Alhaji Kamilu ya kifa kansa had'ida maida hannayensa baya irin yanda manya suke idan suna tunani yasa Mama ci gaba "Ni wllhi ganin mutuncinka ne kuma ganin Malam zai yaudareka ya lik'a maka 'yarsa da ta gama yawon ta zubar a kororo yasa nai wann shahadar nace bari dai na sanar dakai gaskiya ka gane dalilin da Ke sa ko wani namiji mai kamala da mutunci Ke guje ma aurenta. Malam bai dubi amanar dake tsakaninku ba. Ba kalan suturan da baka masa ba amma ya zab'i ya maka lumbu lumbu dan dai kawai shima ya rabu da alk'ak'ai.. Yo shima ya gaji da ita."

Birki tai da kalamanta ganin Hajja Fannah ta fito biyeda ita Ummulkhairi ce rik'e da kayan d'inki suka shige shagon d'inki ga wani matashi ya fito daga cikin shagon ya gifta ta gefen Ummulkhairi.

Mama tai kabbara tana hamdala "Ka gani ko.. Ka tabbata ba sharri nake ba. Wai ance gani ya kori ji.. Kana nan kanata rawar k'afa zaka angwance toh aikin banza kake wai rufin d'aki da b'arawo dan k'artai bila adadi sun rigaka.." Ta numfasa had'ida gyaran murya "Toh Alhaji ni na gama nawa, Allah ya gani na fita na sanar dakai. Kuma ka gani ma idanunka. Ya rage maka ka amince ka sai ma kanka da iyalanka tikitin mutuwa dan k'anjamau ne zai maku sallama. Ka taimaki kanka kaman yanda saura suka taimaki kawunansu. Ni na Barka lafiya Alhaji.."

Tana ida fad'in haka tasa kai ta shige zuciyarta fari tas.

Alhaji Kamilu kuwa sai kallon k'ofan shagon yake yana jira yaga ko Ummulkhairi zata fito amma shiru. Zuciyarsa sai tafarfasa take haka yaja k'afafunsa yana sab'a babbar rigarsa da take 'yar duk'unaso ya nufi motarsa. **

Mama tana shigowa gidan ta cire mayafi ta soma zuba ruwan bala'i

"Iyi.. Kan wani dalili za'a tare ni a hanya ana mun cin mutunci kan laifin da banji ba ban gani ba.. Babu wanda ya huta a gidan nan duk akan rai guda.. Baga yarana dake gidan mazajensu ba yanzu abun har ya tsallako kaina… Toh wllhi bazan d'auki cin mutunci daga kowa ba kan 'yar da ban haifa ba..!"

Umma ta fito daga kitchen afujajan tana goge idanunta da hayak'i ya sanya mata su hawaye "Yaya lafiya.. Meke faruwa..? Wani abu ne aka miki..?"

Mama taci gaba da tururi "Yo uban meye ma ba'a mun ba.. Gashi can Alhaji Kamilu yake ko ya tareni a hanya ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba saikace alhakin tarbiyan Ummul a hannuna yake.!"

Cikin Umma ya bada wani irin sauti k'uuuu "Wani abu ne Ummul d'in tayi Yaya.?"

"Meye kuwa batayi ba bayan ganinta a gidan Matar nan da yayi wacce kowa ya kwana da sanin Gasunk'umar magajiyar karuwai ce.. Ai bansan shashashancinki ya kai har haka ba Suwaiba.. Ni na zata da kika samu wanda zai rufa ma Ummul asiri ya aureta kinyi mata iyaka da gidan wann Kawaliyar mai zaman kanta ashe saketa kikai kamar tinkiya tana ci gaba da zuwa.. Yo a haka ne kike buri da fata ta samu mijin aure bayan kowa ya kwana da sanin ga hark'ar da Matar take d'aura 'yanmata. Ai gashi can Alhaji Kamilu dik yanda akai yaji daga bakin mutane. ya tareni yana sanar dani dama munsan 'yar mu yawon ta zubar take waye ya mutu waye tashi.." Ta kafe Umma da tuni duniya ya shiga juya mata kafin taci gaba " Bari kiji Suwaiba nidai ban haifi Karuwa ba Allah ya gani ehe..!" Ta k'arashe tana mai shigewa fuuu.

Umma ta soma girgiza kai tana dafe kai ta shiga bin bayan mama tana "Na shiga uku ni Suwaiba..! Yaya kar kiga laifina.. Wllhi laifin Malam ne na mata iyaka da wann koyon san'a amma shi ya k'yaleta yace dole ya koyi san'a tinda ba karatun take ba.. Amma anyi na farko anyi na k'arshe bazan bari Ummul ta kuma jaza mun ba..!" Ta k'arashe tana zaran mayafinta. Ta nufi waje a fujajan.

Mama ta bud'e murya tana fad'in "Miyar tuwonki fah.. zai k'one.."

"Yaya ki rik'e min ni nayi nan..!" Ta fad'i takalma a hannu ta nufi waje kaman zata tashi sama.

Tana ficewa Mama ta kece da wata irin muguwar dariya. Har ga Allah shashancin Suwaiba na saka ta nishad'i. Wai Malam ya rasa da wa zai had'ata su goga a kishi saida wann shashasha ballagaza lamba d'aya wacce sam wayau da hankali basu isheta ba. Indai kishiya irin Suwaiba ne a kawo mata gomansu ma. Ta kuma kecewa da dariya tana kwaikwayon gudun Umma takalma a hannu. Ta bud'e murya tana fad'in "Kiyi a hankali dai kar ki fad'i ayi haihuwar guzuma uwa kwance 'ya kwance."

**

Abuja.

Hisham ya kuma girgiza kansa a karo na biyu yana duban Haidar dake zaune calmly kaman babu abinda Ke faruwa saima d'an tapping table din dake gaba garesu da yake da yatsarsa guda fuskarsa na duban wani b'angaren.

"Haidar kamata yai muyi suing news outlet da sukai publishing labarin nan for defamation of name.."

Kaikaitowa yai yana duban Hisham, ya d'anyi still kafin ya girgiza kai "Seriously Hisham..Are we going to waste our time going against the media..?" Ya d'an girgiza kai "Don't you think we should focus on finding the traitor that leaked the video..?"

Hisham ya d'anyi Shiru kaman mai nazari. Sai kuma ya jinina kai "Yeah you are right.. Gaskiyanka ne fad'a da media ba riba.. Wann b'eran na cikin company zamu kama sai ya sanar damu wanene uban gidansa. And I'm pretty sure shine wanda ya fitar mana da bayanan sirri na company." Rufe bakin Hisham keda wuya wayarsa ta soma ruri. Daga Company ake kiransa.

Hisham ya d'aga suna gaisa nan ya fahimci aminin mahaifin Haidar ne Alhaji Gimba mai kiran. Bayan sun gaisa ya tambayesa ko suna tareda Haidar.

Saida ya dubi Haidar d'in wanda hankalinsa ya koma kan wayar salular salulansa kafin ya d'an matsa gefe ya sanar dashi eh suna tare. Magana suka d'anyi na lokaci kafin daga bisani sukai sallama.

Hisham ya dawo wajen zamansa ya zauna yana tunanin ta yanda zai soma sanar da Haidar abinda Alhaji Gimba ya sanar dashi.

"That was Alhaji Gimba. One of the board of directors.. Aminin Dad.."

Haidar ya murmusa da gefen bakinsa kad'an jin yanda Hisham Ke masa bayanin mutumin da ya masa farin sani "What's with the introduction..?" Yai maganar yana tsare Hisham da idanu.

Hisham ya gyara zamansa cikin kujeran "He called to say ya shirya maka interview with the media tomorrow by 10am at the company."

Haidar ya kuma murmursawa da gefen bakinsa irin na Wanda takaici ya gama cikasa yana mai girgiza kai "Unbelievable.!" Ya furta a hankali. Yanzu ba Daddy kawai ba even his friends suna intruding cikin rayuwarsa.

"Kan wani dalili zai shirya mun interview ba da sani ba..?"

Ya mik'e tsaye yana nuna Hisham d'in "Look, you call that man right this instant and tell him I'm not attending.!"

Hisham ya girgiza kai had'ida furzar da huci kad'an yasan halin abokin nasa yasan kayansa hakan dama zai kasance. Shima d'in mik'ewa tsaye yai "Of course you are attending.."

Haida ya dubesa da mamaki "Amma kaji yanda kake min magana..?"

Hisham ya kuma furzar da huci "Haidar he's only trying to help here."

"Did I ask for his help..?!" Ya katse Hisham a fusace.

"But.."

"Bana buk'atar taimakon kowa.. And Much less from him.!" Ya k'arashe yana mai buga table d'in da hannunsa. Lokaci guda yasa kai zai shige.

Hisham yai saurin dakatar dashi "Haidar this is the only way to save…"

"The Company's image, right.?" Haidar ya katsesa da fad'in haka.

"No.. I mean to fix this.. Ina nufin ya shafi sunan mahaifinka Haidar.. Harma da ahalinka."

"Oh c'mon.! What family.. Wani ahali kake magana..? Kafi kowa sanin banida wani ahali."

Hisham ya d'anyi still "Haidar kullum ina fad'a maka ba'a fad'a da iyaye a zauna lafiya.."

"Oh shut up.!" Ya fad'i yana mai nufan motarsa.

Hisham ya furzar da huci kad'an yana mai take masa baya yake ci gaba da fad'in "Haidar kai kad'ai kafi cancanta ka jagoranci project d'in nan.. You work so hard to get to where you are now.. Bazaka bari all your efforts and hardworking su tafi a banza ba.. I know you so well, you don't surrender. You just need a minute to cool off.."

Kaman dai badashi yake maganar ba haka yaba ma banza ajiyarsa ya isa ga motarsa cikin sassarfa.

Daidai sanda Haidar ke tada motar Hisham ya bud'e murya yana fad'in "10am tomorrow at the company." Yai maganar cikin d'aga murya dan tuni Haidar yaja motarsa ya bar wajen.

Hisham ya girgiza kai kad'an dafe da kunkuminsa yabi bayan motar Haidar d'in da kallo. Yasan ba lallai Haidar ya halarci wann interview d'in sanin wanene abokin nasa.

Yana tafe cikin mota yana kuma nazarin abun. Wai Alhaji Gimba ya shirya masa tattaunawa da 'Yan jarida. How could he..! Ta yaya zai yanke babban hukunci haka ba tareda ya tuntub'e shi ba. Akan me za'a sakashi magana da media ba tareda amincewa da yardarsa ba. Duk ma ba wann ba since day one bai k'aunar mutumin sabida k'ok'arin shiga rayuwarsa musamman tsakaninsa da mahaifinsa da yake. Ya tsani a shiga rayuwarsa without an invitation. Idan bai gayyaceka cikin rayuwarsa ba kawai kar ka shiga. Ya furzar da huci a hankali yana so ya gano wani abun. ** Kano.

Banda sautin keken d'inki dake tashi cikin zauren baka iya sauraron komai. Ko wacce ta bada hankali da himma wajen ganin ta zama k'wararriya a sana'ar da suke koyo. Kaman daga sama suka soma jiyo kururuwa na nufosu.

Gaban Ummulkhairi ya yanke ya fad'i. Cak ta dakata da abinda take tana mai furtawa a hankali "Umma..!"

SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU..!*

*07*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba "Sai kinyi ajalina da bak'in ciki kiji dad'i. A sau nawa zan miki iyaka da wann gidan amma kin rantse sai kin tona min asiri Ummul. Me kike nema ki zama ne wai.!" Ta karashe tana fashewa da kuka.

Hajja Fannah wacce tun shigowar Umma ta sallami sauran 'yan ajinta dakatar da Umma tai fad'in "Haba Umman Ummul ya kike kausasa harahenki akan 'yarki. Shin baki san fushinki mai tasiri ne akanta koda baki nuna ba. Ke fah uwa ce kuma za'a tsai dake a tambayeki gameda kiwon da aka baki. Kaman yanda kikeda hakki akan yaranki haka suma sukeda hakki akanki.. Addini bai barmu kara zube ba face saida ya tsara mana yanda zamu tafiyar da rayuwarmu.. Yanzu islamiya har na matan aure sun yawaita.. Duk wanda kikaga ya zauna da duhun kai shi yaso."

"Malama dalla ki min shiru ba wa'azi nazo kimin ba… Yo idan ma zan d'auki wa'azi sai na d'auka daga bakin ballagazar mace irinki mai zaman kanta wacce ta kasa zaman aure. Sann da kike maganar a koma makaranta yanzu kai waye kije garinmu kaf ki tambaya waye mahaifina.. D'iyar malamai nike jikan sha rubutu. Ubana Malami ne mai tak'ama da Zauren karatu, na girma ina kwankwad'an ruwan alk'alami da tawada.. Ni har an isa amin gorin ilimi nida na gajeta. Sauk'a uku nayi da k'ananan shekaru kafin a rufani akaini d'akin miji..!" Taci gaba da jijjiga tana nuna Hajja Fannah "Kuma bari kiji na fad'a miki idan ma kece kike ziga Ummul kike burin ki hanata aure kaman yanda ke kika kasa zaman aure toh Allah bazai baki nasara ba. Ummul tun tana ciki aka nema mata tsari da shed'anu irinku. Ko ana ha maza ko ana ha mata Ummul d'ina zatayi aure kaman yanda ko wacce mace mai mutunci keyi ehe..! Ke kuma shige muje kafin na kwashe miki albarka..!" Ta k'arashe tana tasa k'eyar Ummulkhairi wacce da alama ta gama saduda da sha'anin Umma.

Mamaki bai saki Hajja Fannah har suka fice. Gaba d'aya ta gaza katab'us. Ita a halin yanzu ta fara tantama idan Mahaifiyar Ummul na cikin hayyacinta. Girgiza kai tai cikeda tausayin Ummul tana mai ayyanawa lallai tana cikin jarabawa.

**

Khulsum da dawowarta kenan daga makaranta taji k'urin miya na k'una kan wuta duk ya cika gidan. Ga hayak'i na fitowa daga kitchen. Da sauri sauri ta shigo a tunaninta babu kowa ne amma sai ta hangi Mama zaune tsakar gidan tana gyaran k'umbarta.

Bata ce komai tasa kai zata shige muryar Mama ya dakatar da ita "Toh shafaffiya maras kunya. Kin shigo kina kallo na dan rashin mutunci ko sannun fatar baki ta gagareki. Toh ai sai ki shige ki aje jakarki kije ki gaida tukunyar miyan dake k'auri kan wuta idan ba haka ba tuwon dare ya haramceku. Ahtoh dan a banza azumin da ba lada zai hau kanku daga ku har uwarku dan nikam raina guda inada gidajen 'ya'ya 'yan albarka da suke kame gidan mazajensu da zasu bani tuwo. Saima gidan da na zab'a naci. Banda asara har yaushe za'a ce manyan budare da suka rik'a suka rik'e a gida ana saka masu kwanon tuwo gidan mahaifinsu. Yo sadaka kuke ci sa'anninku masu mutunci dai suna d'aunansu suna aikin lada suna girka ma mazajensu tuwo." Ta mik'e tana buge zaninta "Idan Kinga dama kar ki duba miyan girkin uwarki Suwaiba ne dan nikam na gama girka ma k'artai irinku tuwo a gidan nan. Dan dai cikina d'aya da Malam bazai gagara ba. Amma bazai yuwu da girmana a ganni ina zama bakin murhu ina girka ma gandama gandaman 'yanmata irinku tuwo ba. Daga me yawo da sunan karatu sai mai yawo da sunan koyon san'a.." Tasa kai ta nufi d'aki "Tani ta daina girka ma k'artai tuwo wacce duk tai zuciya cikinku ta tafi nata d'akin mijin ta girka." Ta k'arashe tana rangad'a gud'a da shewa.

Khulsum ta girgiza kai kurum kafin ta aje jakar makarantarta nan tsakar gidan ta cire hijab ta nufi kitchen d'in. Shigarta keda wuya ta soma jiyo muryar Umma ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba.

"Ko labari na sakeji kinje gidan matar can da sunan koyon San'a Ummul saidai ki nemi wata mahaifiyar amma bani Suwaiba ba. Banda salo da fitina ke da ake gab da saka miki rana yo wacce sana'a zaki koya ya wuce zaman aure dake gabanki."

Da mugun mamaki Khulsum ke duban mahaifiyarsu "Umma.. Yanzu d'an koyon sana'ar ma hanata kikayi. Umma itafa sana'a dogaro da kai ne…"

"Ki rufe mun baki Khulsum, aure shine babban sana'ar dake gaba gareta.. Shine daraja da cikan mutuncin 'ya mace."

Khulsum ta saki baki da mamaki " Umma a wann zamanin da akasarin wasu mazan basu sauk'e nauyin d'awainiyar matansu da Allah ya hukunta masu wann san'ar ba ita zata rufa masu asiri ba. Umma ko za'a baka Shi fah abu naka dad'i ne dashi."

"Idan bakiyi shiru ba Khulsum zanzo wajen naci miki mutunci.. Hanshak'iya ana fad'a kina fad'a."

Muryar Mama da fitowarta daga d'aki waya manne kunnenta ya katse Umma. Cikin d'aga murya Mama Ke ci gaba da fad'in "Hellaww ina jinki Badidi na Badi'atu 'yar albarka.. Wai shi Tasi'un ya kawo miki Kaji kika soye mun.. Kaji D'an albark. lallai Tasi'u ya cika Surki na k'warai.. Allah dai ya maku albarka ya k'ara zaunar daku lafiya a gidajenku ya rabamu da sharrin mahassada masu san ganinmu a rana."

Kuka ya kuma zuwa ma Umma bata iya sauraron wayar da Mama keyi ba ta shige d'aki.

Ita kuwa Mama tana ganin Umma da yaranta sun shige d'aki ta sauk'e nannauyan ajiyan Zuciya tana datse wayan Badi'a wacce ita kanta Badi'an ta rasa gane wasu surkulle mahaifiyarta Ke mata cikin waya. Ita da take sana'ar da ita irin uk'ubar da Tasi'u Ke bata a 'yan kwanakin wanda ta gaza jurewa tana ce mata ita ta gaji da auren gida zata dawo sai taji tana mata wasu sunbatu wai Tasi'u ya kawo Kaji a gyare mata.

Mama ta koma d'aki ta kuma danna kiran Badi'a. Kaman jira Badi'a take ta d'aga kiran "Mama wani irin abu ne inace miki Tasi'u ya dawo da hallayansa na baya yau bugun tsiya ya min saida mak'ota suka k'waceni kina kira mun wasu kaji."

Mama ta yarfe gumi "Ke Badi'a saurareni. Idan Tasi'u tsire naman jikinki yake haka zakiyi hak'uri ki zauna.. Zanzo gidan na sameki nasan yanda zamu b'ullo masa amma koda wasa kar kiyi tunanin dawowa gida." Daga haka bata kuma tsayawa sauraron Badi'a da tuni ta fashe mata da kuka tana fad'in ita dai ta gaji.

Mama kaw ta mik'e tana tunanin yanda zasu b'ullowa al'amarin Tasu'u mijin Badi'a.

**

Abuja.

Maitama Builders (MB).

Zauren tattaunawar ta cika da 'yan jarida abinda ya shafi b'angaren kasuwanci. Kowa shirye yake da tambayoyin da zai Engr AA. Maitama yake. Hisham ya shafi goshinsa dan interview d'in zai kasance live ne sakamakon yanda kowa ya k'agu yaji gaskiyar al'amarin bayan video da yai trending a manyan shafuka musamman shafukan watsa labarai na kasuwanci.

Hisham sai kai komo yake yana duba lokaci yana add'uan Allah sa kar Haidar ya badasu. Wann shine kad'ai damarsu ta k'arshe da zata d'aga darajan Kampanin ta kuma wanketa daga daud'an da aka shafa masu.

Masu gabatar da interview sun cire rai da zuwan Haidar. Sun mik'e da zummar tafiya Hisham yai saurin dakatar dasu yana sanar dasu Lallai Haidar zai zo shi.

A can gidan Daddy kuwa suna zaune shida Alhaji Gimba a parlor suna duban live event d'in yanda Daddy Ke girgiza kai. Ko janye idanunsa daga screen bayayi "I told you he's not capable of anything good.."

Alhaji Gimba ya girgiza kai "Inada yak'ini akanshi, Zai bayyana, kuma zai abinda ya dace.. Na tabbata bazai bamu kunya ba."

Readers Also Read