Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 4

Auren wata ukku by sameena - Chapter 4

Auren wata ukku by sameena Chapter 4: Auren wata ukku by sameena Chapter 4. Daddy ya soma k'ok'arin mik'ewa da zummar haurawa sama yana furta "This is a…

4,464 words

Daddy ya soma k'ok'arin mik'ewa da zummar haurawa sama yana furta "This is a complete waste of time Gimba. Ni zan shige ciki.."

Alhaji Gimba yai saurin dakatar dashi "A'a Abokina.. D'an Dakata, kalli nan..!" Yai masa nuni da screen yanda aka hasko Haidar yana k'arasowa cikin hall d'in. Yayi kyau cikin shiga irinta cikakkun 'yan kasuwa masu huld'a ciki da wajen k'asa. K'warjininsa ya cika wajen.

Bakin Alhaji Gimba ya gaza rufuwa sabida farin ciki.

Daddy ya jinjina Kai "I hope it doesn't turn out to be another scandal." Ya fad'i idanunsa akan Haidar da ake haskowa.

A can Company Hisham ya murmusa yana duban abokin nasa harda d'aga masa yatsa guda alamun jinjina. Wani duba Haidar ya aika masa kafin ya wuce yanda aka tanadar masa domin zama.

Yana k'arasawa mai gabatarwan ya mik'e had'ida mik'a masa hannu sukai misabiha kafin Haidar ya gyara zaman suit d'insa ya Zauna attentively.

Nan da nan aka soma gudanar da interview d'in. Yana jefo ma Haidar tambaya yana amsa sa daki daki cikeda k'warewa da sanin aikinsa nan ya jefa floor ma audiences wani ya d'aga hannu ya soma jefo ma Haidar nasa tambayar "Yallab'ai, munga wani hoto na yawo a kafafen sadarwa har wani gidan jarida ya wallafa wani labari cewa fad'a ya kaure tsakaninka da mahaifinka sabida gazawarka da kuma banbancin ra'ayi da kuke dashi. Shin menene gaskiyan al'amarin..?".

Haidar ya kafesa da idanu kafin yai clearing throat d'insa. "A ko wace ma'aikata I believe ana samun sauye sauye da banbancin ra'ayi tsakanin shugaba da ma'aikatansa. Which is what makes the company stand firm on its feet.."

Babu wanda zaice bai zama impressed da yanda Haidar ke amsa tambayoyin da ake masa with so much courage and determination.

Mutumin ya jinjina kai "So does that mean da gaske ne kenan kaida Mahaifinka baku samun jituwa har a wajen aiki..?"

Haidar yai masa k'uri dan ya gane turosa akai yai masa tambayoyin da zasu tunzurashi. Tafukan hannayensa ya d'an had'e waje guda "I'm not here to tell a story about my personal life. But Being the son of the president of this company doesn't make me different from others. If I don't receive any VIP treatment it's because that's the company's policy. And I believe this is why the company remains on track despite all the challenges."

Ya kuma jinjina kai. "One more question Engr. "Is it true that your company is going bankrupt.. And the economy is at the state of crisis.?"

Haidar ya d'an rage girman idanunsa kad'an yana duban mutumin, lokeci guda ya d'an gyara zaman suit d'insa "Let's call this a business perspective. Some times failures lead to future successes. I can assure you, MB (Maitama Builders) does not… and will never fear challenges.." Ya k'arashe yana mai mik'ewa lokaci guda mai gabatarwan ma ya mik'e yana mai mik'awa Haidar d'in hannu alamun musabiha "Mun gode da bamu lokacinka da kai Rankayadade.

Alhaji Gimba ya dubi Daddy "Look, duba kaga yanda yake amsa tambayoyin with so much focus and determination. He has all the potentials and skills to take this company to a greater heights. I'm super optimistic about him."

Daddy dai baice komai saima mik'ewa da yake k'ok'arinyi.

Alhaji Gimba ya rakashi da kallo yana mamakin Allah yai baiwa wa mutum da samun d'a irin Haidar Wanda yake d'aya tamkar ga dubu amma ya kasa gani ya kuma kasa appreciating. Sosai lamarin abokin nasa ke d'aure masa kai yanaji inama nasa d'an ya kasance kaman Haidar. **

Hisham ya kuma duban Haidar had'ida girgiza kai "Ban fahimceka ba Haidar."

"Meye baka fahimta ba..?" Haidar yace yana duban Hisham d'in.

D'an gyara tsayuwarsa Hisham yai "Kanaso kace min gadar zare yaso k'ulla maka da ya shirya wann interview d'in..? Kanaso kace min ya shirya hakan ne just for you to fall into his trap and create more scandals.? Kana so kace min shi kake zargi da yi ma Kampani zagon k'asa.?"

"He gave me all the reasons to suspect him."

Hisham ya kuma jinjina Kai "Amma zanji mamaki idan haka ya kasance duba da kusancin shi da mahaifinka.. So what are you planning now..?"

"Of course I'll play his little game. Shiyasa ma na halarci interview d'in." Ya k'arshe yana k'ok'arin mik'ewa.

Hisham ma ya mik'e suka soma takawa.

"If that's the case, I'll support you Haidar har gaskiya ta bayyana."

Ba tareda ya dubi Hisham ba yace "I'd rather do it alone. This is my battle and I'll fight it alone.. I'll make my Dad swallow all his words a lokacin da zan kamo wuyan mutumin da ya aminta dashi matsayin babban mak'iyinsa. Each and every insult da ya jefeni dashi sai na sashi ya cinye kalamansa. And hakan zai faru ne kawai idan ya d'aurani Akan project d'in nan. So I'll do whatever it takes to make sure ya mallaka min ragamar wann project din."

Hisham yai still yana duban Haidar d'in "Haidar kana magana kaman fansa kake so akan mahaifinka. Haidar.. Anya lafiya kake.. Mahaifi fah ya wuce wasa.?"

"Wani mahaifin kenan.. Amma wani suna ya tara..!" Yana ida fad'in haka ya bud'e motarsa ya shige.

Har ya bace ma ganin Hisham bai daina mamaki ba. Al'amarin Haidar da mahaifinsa ya soma zarce tunaninsa.

***

Kano.

Tinda Abba ya shigo gidan hannunsa na hagu ke dafe da b'angaren k'irjinsa. Ya kuma duban Umma dake zaune gefensa ta rapka uban tagumi tana masa sannu.

Ya amsa yana mai gyara zamansa bayan yasha maganin da ta kawo masa.

Saida ya daidaita zamansa sosai kafin Ya soma magana "Suwaiba" Ya kirawo sunanta.

"Na'am Abban Ummul." Ta amsa duk jiki a mace ganin yanayin Abban.

Abba yaci gaba "Magana nake so muyi amma ina so ki kwantar da hankalinki."

"Toh Abban Ummul.. In sha Allah zan kwantar da hankalina.. Nidai burina ka samu lafiya.."

Abba ya d'an b'ata lokaci kad'an kafin yace "Ai na sanar dake yanda mukai da manemin auren Ummulkhairy. Wato Alhaji Kamilu mak'ocina a kasuwa."

Umma ta jinjina kai "Eh kwarai anyi haka.."

Abba ya kuma jinjina kai "Wato Suwaiba bayan shi Alhaji Kamilu yazo yaga Ummul kwanaki uku da suka shige. Washe gari da safe kaman yanda kika sani sun taho har nan k'ofar gidana shi da wani abokinsa sun bada sadaki.. Alhaji Kamilu ya bada sadaki naira dubu d'ari a matsayin sadakin ita Ummulkhairy lakadan"

Umma kam tsaban farin ciki bata tsaya taji k'arshen zance ba ta shiga gud'a tana fad'in Ummul dinta tayi goshi 'yan bak'in ciki saidai su Mutu.

Abba ya lumshe idanunsa kad'an yana jin zafin k'irjinsa na k'aruwa. Daurewa yai ya d'an bud'e murya yai mata tsawa kad'an data saurare shi.

Umma ta kuma wahse baki tana gyara zama "Yi hakuri Abban Ummul.. Farin ciki na ne ya gaza b'uya. Ummul d'ina lokaci yayi. Ai ni dama tin a nan wajen ka kirawo yan uwanka a nan cikin gida suka zama shaidu aka d'aura."

"Suwaiba ki dubi girman Allah ki saurareni." Ya kuma fad'i cikin tsarewa.

Ta saka hannayenta biyu ta kame bakinta "Na tuba.. Nayi shiru Abban Ummul.. Ina sauraronka yaushe suka nema a saka lokacin biki..? Ni wllhi na ma basu wuk'a da nama su saka ko gobe ne."

Abba ya sauk'e ajiyan zuciya a hankali yana girgiza kai kafin yaci gaba "Toh kinsan kwanakin baya kasuwa ta d'an ja mun baya har na amso bashin hatsi a nan cikin kasuwa.."

Jikin Umma ya soma sanyi amma sai tace "Kasan mutane yanzu idan Sun bika bashi sunyita korortoto kenan kai kace duniya ka amsa wajensu.. Su kwantar da hankulansu lokacin biyansu yayi in sha Allah.."

"Ki saurare ni Suwaiba."

"Toh Ina sauraronka Abban Ummul.." Tace tana gyara zamanta.

Abba yaci gaba "Toh shekaran jiyan da suka kawo sadakin sai shi Wanda yake bina bashin hatsi Ya taho mun da buk'atan kudinsa. Lallai Lallai shima yana neman kudinsa zai amfani dasu. Kuma nima nasan yanda Kasuwa ta koma a halin yanzu. Wasu lokutan Har ka fita ka dawo ba'a zuwa saye. Godiyan Ubangiji ne kawai amma al'amarin k'asar sai addu'a. Hakan yasa na d'auka cikin sadakin Ummulkhairy na biya tinda gadarana sadakin 'yatace. Banida hanyan biya sai wann sadakin. Na cira ciki na biya.. Yau kwatsam da naje Kasuwa Alhaji Kamilu ya tareni da batu mai tada hankali."

Ai bai kai aya ba Umma ta soma girgiza kai tana fad'in "Dan Allah. Dan tsarkin mulkinsa da buwayarsa Abban Ummul ka rufa mun asiri ka mun sutura.. Kar kace min shima ya amshe sadakinsa.. Wayyo ni Suwaiba na shiga uku na Mutu na lalace.."

Abba ya kifa kansa yana girgizawa yana jin yanda Umma ke fad'in ta shiga uku ta Mutu ta lalace. Takaici da ya cika shi ganin tak'i sauraronsa sai kuka take tana jefa kanta a uku. Abba yace "Aima baki gama jefa kanki a uku ba Suwaiba sai kinji irin wulak'anci da kwance zanin da bawan Allahn nan ya mun a cikin kasuwa.!"

Umma ta d'ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansa hannayenta duka biyu dafe da k'irji yayinda Abba yaci gaba da fad'in "Tinda nake a rayuwata ba'a tab'a min irin tozarci da wulak'ancin da bawan Allahn nan ya min ba. Suwaiba, Alhaji Kamilu dai ya amshe sadakinsa ba yanda banyi ba ya bini bashin sauran kud'ad'ensa amma sai cewa yai bazai iya jira ba dan haka yasa yaran shagonsa suka kwaso kaya a nawa shagon darajan kud'ad'ensa makotanmu a kasuwa masu burin su ganmu a rana duk suna kallo. Wann wulak'anci da mai yai kama Suwaiba.."

Kukan Umma ya k'aru mik'ewa tai ta fice tana rera kuka tana fad'in Ummul zatayi ajalinta.

Daga Ummulkhairy har Khulsum a tsorace suka nufo waje jin Umma na ambaton zata fad'a rijiya.

SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU..!*

*08*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Yaran Umma suna kuka suna rok'onta ta sauk'o daga saman rijiya Mama na kuma ingizata "Suwaiba ko ki fad'a ko kar ki fad'a da alama dai bak'in cikin wann 'yar naki shi zai ajalinki.. Wayyo ni Tani zanyi kewarki Suwaiba. Ashe tafiya zakiyi ki barni.. Na yafeki duniya da lahira Suwaiba." Ta shiga rangad'a ma Badi'a da bata jima da zuwa gidan ba kira tana fad'in ta fito tayi bankwana da Suwaiba tafiya zatayi ta barsu.

Suwaiba ta dena kururwar da take tana duban Mama da mamaki "Yaya bazaki hanani fad'awa ba.. Rijiya fah zan fad'a.."

Mama ta kamo bakin zani tana goge hawayen da babu su "Yo ko na hanaki ko ban hanaki ba wancan 'yar taki mai bak'in k'addara zatayi ajalinki Suwaiba. Ta shiga doka kiran Badi'a wacce bata jima da zuwa gidan ba.

"Badiatu.. Badiatu! Badiatu..!! fito kiyi sallama da Suwaiba.. Suwaiba dai lokaci yayi..!"

Badi'a ta d'age labule fuska a yatsine tana kuma turo kallabi gaban goshi "Toh Mama ki barta ta fad'a mana.. Idan bata fad'a ba ai bata tabbata shashasha ba.!"

Khulsum ta harzuk'a "Uwa bata fi uwa ba Anty Badi'a kar ki sake gangancin zagar min mahaifiya.."

Badi'a ta malamalo ashar had'ida zame d'aurin kanta tai d'amara dashi tayo kan Khulsum tana fad'in kafin uwarta Suwaiba ta fad'a rijiya sai ta fara jefata ciki taga uban da ya tsaya mata.

Ai sai Umma tai tsalle ta duro daga saman rijiya ta shiga janye Khulsum wacce Baid'ia Ke k'ok'arin janyota Mama na tayata. Abu sai ya koma kaman dambe Mama ta shige ma 'yarta Umma ma ta shige ma nata 'yar wacce taga haik'an rijiya za'a jefata.

Ummul kaw fashewa tai da wani irin kuka sosai ganin wann tashin hankalin dik sabida ita ake.

Tana tsaka da kuka tana rok'onsu suyi hak'uri su daina ta hangi Abba na rarrafowa daga d'akinsa hannunsa guda dafe da b'angaren k'irjinsa. Ta kirawo sunansa cikin kid'ima tana mai nufansa.

Hakan yaja hankulansu. Nan take suma sukai Kan Abba suna ambato sunansa. Tuni idanunsa sun kafe suna kallon sama baka iya ganin bak'in k'wayan idon.

Sai kuma suka koma kururuwa suna neman agaji.

Kaf mutanen gidan aka rasa mai kawo masu d'auki dan dik a nasu zaton wasan kwaiwayo ne da suka saba.

Sukai masa caa akai kowa yana ambato Sunansa suna rok'onsa ya tashi. Umma sai masa fifita take da bakin zani yayinda Mama ta kawo ruwa cikin kofi tana mik'awa Umman. Fad'i take "Suwaiba duba mana kiga yana numfashi."

Umma na kuka take fad'in "Haba Yaya kar kiyi tunani haka. Abban Ummul na numfashi.." Taci gaba da rera kuka tana rok'onsa ya tashi kar ya tafi ya barsu.

Kaf 'yanuwansa maza dake zama cikin gidan aka rasa mai zuwa ya dubasa balle a kaisa asibiti. Dama gidan Sun gaji gaba na 'yanubanci tin daga iyaye da kakanni. Yan wann d'akin babu ruwansu da yan wancan d'akin. Shi Abba kusan shine babba cikin mazan dake rayuwa a gidan sauran yeyyen nasu duk mata ne suna gidajensu. Shi a d'akin mahaifiyarsa shi kad'ai ne namiji. Hasalima su biyu mahaifiyar tasa ta haifesu. Daga shi sai kaw 'yaruwarsa k'anwarsa mai suna Inna Dije. Inna Dije da mijinta basu jima da komawa garin Dutse na jihar Jigawa ba yanda mijinta ke aiki. Hasalima mijin nata d'an asalin jihar Jigawa ne amma yayi zaman Kano yanda yaga Inna Dije k'anwa ga Abba ya aureta. Sun zauna tsawon lokaci a Kano kafin iftila'in rashin tilon d'ansu ya samesu. Tin bayan rasuwar D'ansu basu kuma zaman Kano ba hakan kuma yai daidai da canjin wajen aiki da mijin Inna Dije ya samu. Sann tin bayan wann lokacin Inna Dije bata kuma saka k'afarta a garin Kano ba.

Wasu dattawan unguwar masu ganin mutincin Abba su suka Kaisa wani k'aramin asibitin gwabnati mafi kusa. Mama da Umma sukai masu godiya.

Jigum jigum sukai gaba d'aya suna jiran ba'asi daga wajen likitoci.

Daga yanda suke zaune Mama ta kafe Umma da yaranta dake zaune daga d'aya b'angaren suna hawaye. Sai cika take tana huci dan wann dik dalilin Suwaiba da 'yarta ke faruwa. Ta sauk'e idanunta kan Ummul wacce ta kasa daina kuka maras sauti. Kaman wacce aka sinkara ta soma furta "Wann duk laifinki ne Ummul.. Idan Abbanku ya rasa ransa ki sani alhakin mutuwarsa zai ratayu ne a wuyanki.. Kece nan kikai silan mutuwar mahaifinku..!"

Umma ta d'ago tana duban Mama shaye da mamaki "Yaya ya zaki ce haka.? Ta ina Ummul ta zama Sila..?"

"K'warai kuwa ita ce Sila dan bak'in cikinta da abunda ke faruwa da ita su suka taru suka haddasawa mijin mu ciwo ehe.!"

Badia dake koke Koke tana ambato sunan mahaifinta ta k'arasa a guje ta shiga janyo Ummulkhairy tana fad'in shegiya mai bak'in k'addara kafin ki kashe mana uba sai and fara kasheki kowa ya huta. Daidai lokacin su Azeema da Salima sauran yaran Mama dake gidajen aurensu suka iso ai nan suma suka aukawa su Khulsum. Fad'a dai yaci gaba a asibiti. Har saida ma'aikatan asibitin suka tasamma koransu.

Da kyar dai aka raba bangarorin guda biyu fada. Kowa suka koma gefe suna aika ma juna mugun kallo.

Can da jimawa wani Likita ya fito. Suka mik'e gaba d'aya suka nufesa. Sukai ma likitan caaa da tambayoyi kowa naso a soma amsa nasa. Mama da yaranta su Salima na yi Umma da Khulsum na yi. Ita dai Ummul ita kad'ai ce baka Jin bakinta.

Likita ya zuba ma sarautar Allah idanu yana duban wann ahali Wanda majinyacin da suka kawo baya buk'atan irin wann hayaniya da tashin hankali nasu. Ya d'an girgiza kai yana k'ok'arin kwantar masu da hankali amma sai yaga kaman basa gane wann yaren. Tsawa ya daka masu yace duk suyi shiru ko su fice su bar masu asibiti.

Bayan Likitan ya kebe da Mama da Umma Ya dubesu yace "Ku sani yanzu ba lokacin tashin hankali bane. Lokaci ne da mijinku ke tsananin buk'atar kwanciyar hankali. Ko kunsan mijinku na d'aukeda matsanancin ciwon zuciya mai haifar da Kumburin zuciya.!"

Ai sai suka rikice Umma kuka Mama kaw mik'ewa tai dafe da k'irji "Likita kumburin zuciya fah kace.?!"

Likita ya jinjina mata Kai "K'warai Hajiya.. Kuma ciwonsa ya wuce matakin farko.. Hasalima zamuyi k'ok'ari ne mu turasa can babban asibitin koyarwa dan a can ne zaifi samun kula sunada k'wararrun likitoci da ya shafi ciwon zuciya.."

Umma ta share hawayen da suka zubo mata tana tuna ranan da mijin nasu yai masu wasiya da hak'uri da zaman lafiya "Likita yanzu mai zai faru da mijinmu..?" Tai maganar cikin tsananin rawar murya mai cikeda rauni.

Sauk'e ajiyan zuciya yai yace "Kwararrun Likitocin da suka shafi b'angaren ciwon zuciya ne kad'ai zasu iya sanar daku abinda zai faru.. A halin yanzu bazan iya ce da ku komai ba.. Zuwa gobe da yardar Allah zaa tafi dashi can asibitin koyawar sai Likitocin zuciya su dubasa. Amma ku kwantar da hankulanku ba wani abin tashin hankali ana warkewa cikin k'udarar Ubangiji. Kuyi hak'uri na fad'a maku gatsau sabida Kun Kai hak'urina bango ne shiyasa. Ku kwantar da hankulanku ku had'e kan ahalinku ko dan samun lafiyan mijinku.. Please do this for your husband." Ya k'arashe yana dubansu su duka biyu.

Mama tace "Sunan maganin ka fad'a Likita.?"

Ya d'an murmusa kad'an had'ida girgiza Kai "Cewa nai kuyi hakan domin mijinku."

Suka jinjina Kai a tare Likitan ya k'arada "Kar ku damu babu abinda zaku biya mutanen da suka kawo sa nan sun biya komai. Saidai idan an kaisa can babban asibitin koyarwa dole zaa bukaci kud'i ko nace kudade masu yawa."

Daga haka Sallama likitan yai masu suka fito jikkunansu duk a sanyaye.

**

Abuja.

Hisham ya dubi Haidar wanda ya bada hankalinsa sosai ga laptop d'in dake gabansa wanda da gani ko ba'ace kasan aiki tuk'uri yake domin achieving goals dinsa. Ya d'an Sauke ajiyan zuciya "I hope he approves the new proposal."

Shiru Haidar yai idanunsa kan computer din har lokacin. Yeci gaba da juya pen d'in dake mak'ale cikin yatsunsa guda biyu "I know my Dad, he's so meticulous… So everything should be done carefully.."

Hisham ya jinina kai yana mai mik'ewa "Alright, with your permission Sir, zan koma bakin aiki na."

"Dama ban rik'eka ba." Haidar yace yana d'an juyi cikin kujeran da yake.

Kafin Hisham yakaiga ficewa wayarsa tai ruri. Mahaifiyarsa ce mai kira. Ya fad'ad'a murmushinsa yana mai d'aga kiran.

Sosai yake hira da ita cikeda so da k'auna da alamun kewan juna daga duka b'angarorin nasu. Haidar na iya sinkayo muryar mahaifiyar Hisham yanda take ta binsa da addu'o'i nagartattu yana amsa mata da ameen. Baya kasa kunne ya saurari abinda bai shafesa ba amma sai ya tsinta kansa da sauraron wayan Hisham da mahaifiyarsa. Har dai Hisham d'in suka ida waya da mahaifiyarsa Hisham na sanar da ita bazai jesa Kano anytime soon ba she shouldn't expect him bayan bai jima da sanar da Haidar yana son daukan hutu yaje ya duba gida cikin kwanakin.

Haidar ya d'an dubesa. Sai Hisham ya murmursa "Ban sanar da ita ina tafe soon ba. I want it to be a surprise."

Gajeren murmushi Haidar yai "Idan bazatan zai sanayata farin ciki."

Hisham ya jinjina kai "I hope so.. Nayi kewar Hajjata.. She's my everything Haidar.. Ina mata son da bayada iyaka.. Na girma matsayin maraya amma bansan maraici ba sabida ita.. She's my two in one.. Zatayi komai domin farin cikina.."

Haidar ya jinjina kansa a hankali yana jin rayuwar abokin nasa total opposite da nasa rayuwar. Amma sabida k'arfin hali irin nasa sai ya kauda tunanin yana mai ci gaba da abinda yake. Saidai da alama tunanin yak'i barinsa, Ya kasa yakicewa daga zuciyarsa. Sosai Hisham da mahaifiyarsa suka birgesa. Inama shine yakeda kusanci irin haka da nasa mahaifiyar. Ba abunda ya nema ya rasa a rayuwarsa ta duniya face soyayyar iyayensa guda biyu. Da ace dukiya shine farin cikin rayuwar duniya tabbas da ahalinsu ya cika da farin ciki. Saidai kash sab'anin haka ne cikin ahalinsu. Da ace za'a karb'e duk abinda suka mallaka na duniya a azurtasu da farin ciki kwanciyar hankali da soyayyar junarsu tabbas da sai yafi masa duk wann k'yale k'yale na duniya da suketa bautuwa akai. Ya d'an limshe idanunsa yana mai canza direction d'in tuk'insa. Can k'asan zuciyarsa yana jin akwai gibi babba cikin rayuwarsa. Har ya iso k'ofar gidan mahaifinsa yana tunanin shiga ya duba Mommy wacce sukai kwanaki basuyi koda magana ta waya ba kaman dai ba d'ah da mahaifiya ba. Ringing d'in da wayarsa tai ya dakatar dashi.

Dareen ce mai kiransa hakan yasa ya fasa shiga gidan ya juya Kan motar.

**

A can Kano kuwa Tuni an tura Abba babban asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano. Ana kan basa kula na gaggawa had'ida da masa gwaje gwaje da yake bukata.

Mama tai saurin funcuke takardan da likita ke mik'a masu tin kafin Umma ta mik'a hannu. Sai ka ranste tasan mai aka rubuta cikin takardan ne. Ta shiga juya takardan tana dubawa "Babu damuwa Likita za'a sayo maganin Allah sa babu tsada.."

Dr dai bai tsaya sauraronsu ba yasa kai ya shige.

Mama ta kuma yatsina baki tana juya takardan " Toh ma Wai Ina yaga kud'ad'en da zaa masa jinya ne wai.. Wllhi Suwaiba keda d'iyarki dai anyi annoba.. Ummul ta haddasa masa wann ciwo.." Jiki a matuk'ar sanyaye Umma tace "Kar kice haka Yaya.."

Ta watsa mata harara had'ida jan tsuka kafin tai saurin tare wata nurse da tazo shigewa "Yauwa 'yar nan dan Allah nace ba ko zaki iya duba mun mai aka rubuta takardan nan.."

Nurse d'in ta amshi takardan tana dubawa "Sunayen magani ne da allurai.."

Mama tace "Tooh inji dai basuda kud'i..?"

Nurse d'in ta d'an kuma duban Mama " Magunguna ne da allurai masu kud'i dan allura guda a nan yakai dubu goma.. Kije pharmacy zasu Miki bayani.." Bata kuma tsyawa sauraron Mama ba tasa Kai ta wuce.

Mama ta waro idanu "Tirk'ashi toh idan jinyar Malam da tsada haka ai akwai matsala dan irin wann babban jinya kankataraf sai ya cinye d'an abinda zai bari ma yaran nasa bayan babu shi.." Ta juyo sosai tana duban Umma "Wann duk laifinki ne Suwaiba.. Ke da 'yarki ku kuka kashe Malam a tsaye dan haka sai Kuje ku nemo kud'ad'en da zaa masa Jinya."

Cikin rawar murya Umma ke furta "Haba Yaya ki dubi yanda muke fah.. Asibiti fah muke.. Sann meyasa zaki d'aura alhakin ciwon mijinmu kaina nida 'Yata.. Kinsan bazamu tab'a so haka ya same shi ba.."

"Ke dalla rufe mun baki munafukar banza da wofi idan ba takaicin Ummul da hayagaganki ba me ya janyowa mijinmu ciwon zuciya.. Kinji na rantse Miki da Allah kije ki nemo kud'ad'en masa jinya.. Ina zaki samu bai dameni ba kawai abinda na sani shine alhakin ciwonsa na wuyanku keda Ummul.!"

Jin hayaniya yasa wasu nurses k'arasowa suna masu fad'an asibiti suke ba dandali ko kasuwa ba idan hayaniya zasuyi zasu koresu.

Mama tai saurin nuna Umma "Kun ganta nan ita zaku kora itace silan ciwon mijina gashi zata k'ara masa. Tinda mijina ya aureta tsiya ke bibiyarsa, Kayan kantinsa ya daina bunk'asa ta kuma haifo masa annoba wacce kowa ke gudu."

Nurse guda tace "Malama wann ba matsalar mu bace zan kira security yai waje dake idan bazaki mana shiru ba."

D'ayar tace "Visiting hours ya shige mutum d'aya ne zata iya zama, ki gode ma Allah mijinku ya samu d'aki mai d'aukan mutum guda godiya ga sabuwar gwabnatinmu dake k'ok'arin inganta hark'an kiwon lafiya da yanzu dole ku nemo namiji da zai zauna.. Yanzu mace d'aya cikinku zata tafi.."

Ai bata Kai aya ba Mama ta nuna Umma "Itace zata tafi dan bamu San idan ya farka ya ganta mai zai faru ba tinda ita da d'iyarta ne silan ciwon.. Na tabbata zuciyarsa bugawa zai idan ya ganta."

Umma ta girgiza Kai tana duban Mama "Kiji tsoron Allah Yaya."

"Da tsoronki zanji Suwaiba.!"

Ta girgiza Kai kurum tasa Kai ta fice tamkar kazar da k'wai ya fashe ma a ciki.

A haka Umma ta dawo gida cikin jimami.

Aiko tin daga bakin k'ofa take sinkayo sautin yaran Mama Salima Badia da kuma Azeema Sun saka Ummul gaba sai kwashe mata albarka suke suna fad'in ta kashe auren Azeema bai isheta ba zata kashe masu mahaifi toh wllhi idan mahaifinsu ya Mutu ta dalilin bak'in cikinta sai Sun d'auki fansa akanta. Duk fad'a irin na Khulsumu da k'ok'arin karb'ar ma 'yaruwar tata 'yanci yau sai ta gaza tab'uka komai sakamakon tuno halin da mahaifinsu ke ciki Wanda yake tsakanin rayuwa da mutuwa.

Umma ta k'araso da sauri ta rungume Ummul. Umma kuka Ummulkhairy kuka.

Kaman an jefo Mama haka ta shigo gidan tagajan magajan. Ashe koda Umma ta fice ta biyo bayanta. Nan ta tadda yaranta na d'iban albarka wa Ummul da mahaifiyarta.

Mama ta cab'i zancen daga sama "Shisa nace bazan bari Suwaiba ta kwana wajen mijinmu ba. Kuma sun gama rab'ansa har Allah ya tashi kafad'unsa daga ita har 'yar tata. Zuriyan annoba."

Azeema tace "Kinyi daidai Mama dan wllhi ko ni nan ko kan gawan mahaifina bazan bari Ummul taje ba.!"

"Ya naji ana zancen gawa.. Abban ya cika ne..?" Badia tace tana dubansu.

Mama tace " Baidai cika ba amma yana hanya. Dan idan ba'a samu kud'ad'en da zaa masa jinya dasu ba nan da kwanaki k'alilan toh fah mahaifinku zai zama gawa silan wad'ann..!" Ta k'arashe tana nuni dasu Umma.

Sai sann da abun ya ishe Khulsum ta mik'e idanunta na zubda hawaye take dubansu gaba d'aya "Tir da hali irin naku.. Tir da ahali irinku.. Abba na gadon asibiti kuke maganganun marassa kan gado irin haka.. Idan burinku ya Mutu ne domin ku tozarta 'Yaruwata da mahaifiyata in sha Allahu babu d'aya daga cikin burinku da zai cika.. Allah zai tashi Abba zai basa lafiya sann rayuwar mahaifiyata harma da ta 'Yaruwata zai inganta."

"Ke rufe mana baki k'aramar maras kunya.!" Mama tace tana huci.

Badia da Azeema suka soma k'ok'arin kwance d'ankwali zasu yi d'amara.

Badia na dukan k'irji take fad'in Mama ta k'yaleta ta gurji bakin Khulsum yayinda Umma ta mik'e da sauri ta tare yaranta guda biyu hawaye bai daina ambaliya a fuskarta take fad'in "Yaya dan Allah kuyi hak'uri." Ta dubi su Salima kafin taci gaba "Ku tuna halinda mahaifinku ke ciki.. Yanzu ba lokaci ne na tada rikici ko nuna yatsa ba. Yanzu lokaci ne da ya kamata mu had'e matsayin ahali ko dan samun lafiyan mahaifinku.. Kunfi kowa sanin yanayin gidan nan yanda 'yanubanci ya raba kan ahalin tin kan iyaye da kakkanni.. Idan bamu had'e kawunanmu ba kunfi kowa sanin babu mai yiwa mahaifinku kaf gidan nan. Dan Allah muyi hakuri duka mu nemawa Malam lafiya koda da abinda ya mallaka ne."

Mama tai saurin katseta "Ban gane koda da abinda ya mallaka ba.. Yo me ma ya mallaka da zaa masa jinya dashi.?"

Umma ta jinjina kai "K'warai ya mallaki kanti. Ko Kayan ciki aka sayar da gaba d'aya kantin na tabbata zaa iya rage wani abin saura sai a nema wajen bayin Allah tinda ga yanayin ciwon nasa ciwo ne da za'a buk'aci kudade ga yanda komai ya koma a k'asar."

Readers Also Read