Auren wata ukku by sameena - Chapter 26
Auren wata ukku by sameena Chapter 26: Auren wata ukku by sameena Chapter 26. Mommy ta kuma gyara zama "Uban Fannah labourer ne a kampanin Maitama.…
4,445 words
Mommy ta kuma gyara zama "Uban Fannah labourer ne a kampanin Maitama. Bincikena ya tabbatar min akwai wani lebura matashi kuma abokin aikin mahaifinta dake mutuwan sonta. Hasalima saurayinta ne kafin iftila'ain da ya samu mahaifinta ya samesa. Zuwa Kai ma mahaifinta abinci da take site a can Saurayin nata ya ganta ya fara sonta. Da uban ya Mutu mijina bai san da labarin tanada wani saurayi da suke soyayya ba Wanda shima yake aiki k'ark'ashin sa. danginta sukai wuf suka nuna masa batada kowa saidai ya aureta sabida tinanin zasu sami kudi. Ance sadaki suka yanka masa kaman dai mai biyan diya. Saida masa ita sukai. Fannah batada say ga danginta Wanda bayan rasa mahaifinta da tai ba rike ta zasuyi ba dole suka tilasta mata auren mijina dukda tanada Wanda take so. Dashi zanyi amfani na fitar da Fannah daga gidana dan ance har gobe yana mutuwan sonta."
Asshe ta sauk'e ajiyan zuciya "Toh ya abin zai kasance.?"
Mommy ta kuma murmusawa "Abin shine kece zaki taimaka min har komai ya kankama K'anwata."
Asshe ta girgiza Kai cikin rashin fahimta "Kaman ya kenan Anty Kwaise.? Ki sanar Dani wane irin taimako zanyi dan nafi kowa burin matar nan ta fice daga gidan nan."
Mommy ta jinjina Kai suka tsara yanda zasu aiwatar da komai cewa Asshe ta tafi ta samu wann Saurayin suyi ciniki dashi da Mommy yazo gidan a ranan da Engr Aliyu Maitama zai dawo gari ya kamasa a d'akin matarsa zai hau kan dik abinda ya gani ya zauna tinda su biyun tsaffin masoya ne." Ta k'arashe tana sakin murmushi.
Da taimakon Asshe Mommy ta tsara komai har shigowa gidan da Auwalu tsohon Saurayin Fannah yai ba tareda kowa ya gansa ba.
Fannah da fitowarta kenan daga band'aki tayi wanka cikin murnan mijinta na hanya zai dawo ya dubasu itada abin cikinta mai watanni uku a lokacin. Nan ta tadda Auwalu tsohon saurayinta kwance saman gadon ta daga shi sai singlet da gajeren wando. Jikinta ya d'auki kyarma ta soma salati tana karanto Innalillahi. Kafin tai wani aune Auwalu yai tsalle ya capkota had'ida toshe bakinta da k'arfin gaske. Fannah tana kuka tana k'ok'arin kururuwa amma inaa ya toshe bakinta.
Daddy ya dawo cikeda d'oki da murnan ganin matarsa mai juna biyu. Ko sashensa bai nufa ba ya fara nufan b'angaren ta d'aukeda tarin tsaraba irin Wanda mata masu juna biyu ke so. Nan ya tadda Kayan tashin hankali maras misaltuwa k'ato rungume da matarsa dake d'aure da towel ya toshe mata baki da hannunsa guda. Ga wani mummunar murmushi saman fuskarsa.
Daddy na huci yake duban mutumin Wanda ya saki Fannah bayan shigowan Daddyn. Ya duka jiki na kyarma yanda yake fad'in Engr ya masa sutura dole Yai ma Fannah bada amincewarta ba fyade yai mata.
Daddy ya shak'osa tamkar zai aikasa lahira ya kasa furta komai sai huci da kyarma da jikinsa keyi sabida b'acin rai. Da kyar Mommy ta janye Daddy. Ta isa ta yafa ma Fannah mayafi ta rufe mata jiki wacce towel ne kawai d'aure jikinta. Ta dawo ga Daddy tana fad'in "Engr kar ka biyesa kar Kai kisa. You are not like him. Ni dama tinda yake zuwa gidan nan ban yarda dashi ba."
Daddy ya dubeta da mamaki "Dama ya Saba zuwa.?!"
Mommy ta jinjina Kai kaman gaske "Ai idan Baka nan yakan zo. Da abubuwa na kwadayi irin na masu ciki yakan ce Kai ka aiko shi zuwa wajen Fannah. Sabida abinda take so yake sayowa."
Asshe da fitowarta kenan sabida hayaniyar da taji ta dubi mutumin da Daddy dake duke yana kyarma tace "A'ah.. Wann mutumin ai mak'ocin su k'awata Baana ce. Kuma ta…" Sai tai shiru ta kasa ci gaba da magana.
Mommy tace "Kuma me Asshe.. Meye Baana ta sanar dake..?"
"Ta sanar dani shi d'in Saurayin Fannah ne Wanda mutuwan mahaifinta ya hana aurensu… Hasalima mahaifin Fannah kafin ya rasu ya masa alkawarin bashi ita..!"
Daddy ya dago jiki a sanyaye yana duban Fannah wacce kuka yaci k'arfin ta "Haka ne.? Wann D'an iskan saurayinki ne.?!" Ya tambaya yana dubanta.
Jin bata amsa shi ba ya sa ya kuma daka mata tsawa "Ki amsa min..! Haka ne..!"
Auwalu ne ya bama Daddy amsa da fad'in "Duk Wanda zaka tambaya Rankayadade haka ne. Fannah toshuwar budurwata tace da nake matuk'ar so. Kuma mahaifinta ya min alk'awarin bani ita.. Amma 'yanuwanta Sun karya wann alk'awarin sabida kwadayin abin hannunka. Saidai ni da Fannah bamu rabu ba.. Washe garin ranar da ta tare gidanka ma ba aiki na tafi ba gidanka na taho.. Kuma duk randa nazo mukan mu'amalanci juna da yarda da amincewarta. Amma yau din ba da son ranta na aikata mata ba fyade nai mata sabida ta sanar Dani akwai ciki jikinta Wanda batasan nawa bane ko naka..!" Bai Kai aya ba yaji saukar naushi a bakinsa. Duka Daddy yake Kai masa ta ko ina yana hawaye tamkar zai aikasa lahira A haka mai gadi ya shigo a guje yana sanar da Daddy window din section dinsa a fashe dik yanda akai b'arawo ya shigo gidan. Dan shi dawowarsa kenan daga masallaci ya tadda haka.
Daddy ya ci gaba da huci "Ga b'arawon a nan. Ya Saba shigowa Shayibu ba tareda kayi la'akari ba. Yau da dubunsa zai cika sai ya fasa window. Ya damk'a sa ma shayibu yana fad'in bari yaje ya duba section d'insa. Ai kaw nan Daddy ya tadda an fasa safe d'insa na cikin gidan an kwashe kud'ad'en ciki.
Koda aka mik'a Auwalu ma 'yansanda bai yi musun shi ya kwashe kud'ad'en ba. Ya ce da taimakon Fannah ya kwashe kud'ad'en dan su gudu su bar gari.
Daddy bai saurara daga b'angaren Fannah ba. Musamman da ya tabbatar da gaske Auwalu tsohon saurayinta ne kowa yayi wann shaidar.
Sosai take kuka duk'e gabansa tana girgiza Kai tama kasa cewa komai. Mai ma zata ce bayan an kulleta ta ko ina. Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta "Ki sani wann shegen da yake cikinki ba nawa bane. Kuma har Abada kar ki taba danganta ni dashi. Kije can keda wancan Daniskan ku rainesa a gidan Yari." Yana ida fad'in haka ya mik'e yana hawaye sosai. Bai wata wata ba ya tura su duka biyun gidan Yari. 'Yanuwan Fannah suka barranta da ita cewa basu ba ita. Ta tona ma kanta asiri ta cuci kanta. A prison Fannah ta raini abinda ke cikinta har ta haifesa. Bayan faruwan haka da wasu watanni Mommy ta fara nuna alamu na masu ciki. Batai gaggawan sanar da mijinta ba Wanda tsawon shekarun da suka diba tare suna jiran wann batu mai dad'in ji tin kafin shigowar Fannah cikin rayuwarsu. Yau gashi ta samu juna. Tasan Engr zai farin ciki fiyeda lokacin da Fannah ta samu. Tai shiru tana tinanin da Fannah tana nan k'ila da an fara k'irga ma abinda ta haifa watanni.
Suna hira itada Asshe wani rana, nan Mommy ke zayyano ribar da taci bayan ta k'ulla ma Fannah Makirci gashi ta fice cikin rayuwarta cikin ruwan sanyi. Tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu.
Sam bata San Daddy ya shigo ba take b'arin zance.
Daddy ya dubeta da mamaki "Kwaise.. Sharri kikai ma Fannah.?!"
Sai Mommy ta mik'e tana girgiza Kai "A'a Engr dan Allah ka saurareni."
"Mai zan saurara bayan abinda naji da kunnuwa na.. Ki bud'e baki ki sanar Dani.. Sharri kikai ma mata..? Kece kika shirya komai..?!"
Cikin kuka Mommy ke jinjina Kai "Wllhi Allah shine shaida na Engr sharri kawai nace yai mata.. Wllhi ban ban bashi umarnin wani abu bayan haka ba.."
Gijif ya zauna cikin kujera yana jin duniyar na juya masa yayinda Mommy ta rarrafo zuwa gabansa tana Neman afuwa.
Mik'ewa yai ya fice ba tareda ya dubeta ba. Kai tsaye prison yaje amma koda yaje ta gama sentences d'inta an kuma sallameta bayan ta haihu sann babu Wanda yasan yanda ta tafi. Shima Auwalu babu Wanda yasan yanda yake bayan Sallamansa daga prison da akai. Haka Daddy ya zauna yana kuka sharshar da hawaye tareda nadaman hukuncin da ya zatar ba tareda yayi bincike ko ya saurara daga Fannah ba. Gaba d'aya Mommy ta rasa gane kansa tin daga wann lokacin. Baya mata magana baya kulata baya shiga sabgarta. Kasuwancinsa ta soma girgiza bayan hab'akar da tai sabida halin k'unci da damuwa da ya tsinci kansa ciki. Daddy ya koma tamkar baya rayuwa cikin wann duniyar. Ya daina fita ya daina magana ya daina mu'amala da kowa da komai. A haka Mommy ke rainon cikinta cikin damuwa da k'unci hopping idan ta haihu zuwan D'an cikin rayuwarsu zai canza komai. Har zuwa lokacin da ta haihu Daddy bai dawo normal ba. Yana nan jiya iyau ba um ba um um. Bayan Mommy ta haihu ta shigo da jaririn cikin hannunta tana hawaye take nuna masa "See burinka ya cika Engr ka samu Magaji and I named him after you. Aliyu Aliyu Maitama.. Zai girma ya zama Engr kaman Kai. Zai girma ya zama d'an da zakai alfahari dashi."
Tin bayan abinda ya faru bai kuma duban cikin idonta ba sai wann lokacin.
Mommy tana hawaye take dubansa cikeda Jin dadin yau yau ya kalleta. Amma sai taga ko kallon jaririn dake rik'e cikin hannunta baiba balle ya karb'e sa. Sai ma mik'ewa da yai a ranan ya koma aikinsa gadan gadan. Baya shiga sabganta balle na D'anta sai hidiman bunk'asa Kasuwancinsa da yake. K'unci da damuwa suka taru sukai ma Mommy yawa tinda taga wann lokacin Mommy ta shiga damuwa kullum cikin kuka da tashin hankali take bata kula jaririnta Wanda tinda taga mahaifinsa bai amshesa ba. A nata zaton zai zamto makamin da zatai amfani dashi ta kuma janyo hankalin mijinta gareta. Asshe ita ke rainon Haidar. Hasalima ita take kiransa Haidar bayan mahaifiyarsa ta sanya masa suna Aliyu har Haidar ya bisa. Asshe ita ke kula da Haidar tamkar itace ta haifesa. Madararsa d'awainiyarsa komai itace. Mommy kullum cikin kuka da damuwan wofantar dasu da ita da D'anta da Daddy yai take. Ta duk'ufa Neman Fannah dan ta nemi yafiyarta amma Fannah was no where to be found. Sanda Asshe tazo aure ji tai kaman ta tafi da Haidar sabida son yaron da take da tsoron barin sa tsakanin iyayen da babu shi a gabansu. Damuwar gabansu kawai suke. Burin Mommy shine Uban ya kalli d'an matsayin D'a da ko wani Uba ke alfahari dashi yayinda Daddy ya ta'allak'a ga bunk'asa Kasuwancinsa. Wann dalili yasa kasuwancin Aliyu Maitama ya fiye masa ahalinsa dan wann Kasuwanci shi yai keeping dinsa going a tunaninsa bayan abinda ya faru dashi. Shi ya zame masa tamkar therapy. A haka rayuwa take tafiya ma wad'ann bayin Allah. A haka Haidar ya taso ya tsinci Kansa tsakanin iyaye biyu Wanda baisan wani Abu mai suna soyayya tsakaninsa dasu ba. Koda ya soma girma Mommy kullum cikin tilasta masa yake yai abinda zai birge uban ko zai alfahari dashi yayinda Daddy bai tab'a ganin k'ok'arin Haidar ba har kawo girman sa.
Wann kenan.
(Kar mai karatu ya mance kacaukam labarin nan an Ginasa ne kan 'ya'ya da Allah kan jarabcesu da iyayensu da kuma iyaye da Allah ke jarabtansu da 'ya'yansu. Wasu mutanen ana sanyasu ne cikin rayuwar sashe matsayin jarabawa).
* Ci gaban labari..
Haidar ya share hawayen da suka zubo masa "So that's the reason why he hates me.!" Ya fad'i haka Kansa a kife.
Mommy tai saurin girgiza Kai hawaye naci gaba da gangaro mata "No Haidar.. Your Dad doesn't hate you.. He loves you.. In fact inada tabbacin bayan abinda na masa albarkacinka naci bai koreni ba.. That's just.. his way of punishing me.!"
"Well I don't care.!" Ya fad'i haka yana mai buga teburin gabansa da k'arfin gaske. Ga wane irin huci da yake fiddawa. Yaci gaba da jinjina Kai yana ci gaba da fad'in "I wish you let me die as a child. I hate you. I hate you.!" Yai maganar a hankali har lokacin girgiza Kansa yake.
Mommy na kuka sosai take girgiza masa Kai "I'm sorry my Son.. I'm sorry.. Ba garin Allah da zai waye banyi nadaman abubuwan da na aikata ba da yanda yai affecting rayuwarka.. Haidar ka yafe mun..!"
Kauda fuska yai dan baya fatan ya kuma d'agowa ya dubi fuskar mahaifiyarsa.
Ya saka tafukan hannayensa ya goge fuskarsa da ya koma jazir. Cikin wane irin tune yake furta "Serving jail sentences won't be enough punishment for you Mommy. Amma dikda haka nan shine yanda ya kamaci criminal irinki. Now more than ever, I won't rest until I see you locked up in jail.. Koda zaki k'arar da duka resources dinki sai na tabbata you rot in jail. I don't want to see your face ever again.!" Ya k'arashe cikin tsananin huci hawayen zafin rai na fita daga idonsa. Lokaci guda ya mik'e ya nufi k'ofa kaman zai kifa Mommy na kuka na kiransa amma inaaa tuni ya finciki k'ofa ya fice cikin tsananin huci..
SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU..!*
*36*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
A tsorace ta d'ago tana dubansa.
"Can you walk.?" Ya tambaya yana dubanta itama shi take duba. Ganin bata ce masa komai ba sai ma rawa da jikinta keyi alamun dai batada strength har lokacin yasa bai kuma yin wata wata ba ya fiddota daga cikin motar.
Ganin haka yasa ta soma girgiza masa kai tana fad'i cikin rawar murya "A'a dan Allah.. Ina ne nan… Ina ka kawo ni..?!" Cikin muryarta da bai fita sosai take maganar.
"Shut up. Just shut up.!" Ya fad'i still tana cikin hannunsa. A haka ya tura k'ofan parlorn suka shige. Ko ina an rufe da farin kyalle alamun dai babu mai zama cikin gidan. Wani d'aki ya bud'e ya ajeta saman gado.
Ta d'ago a tsorace tana dubansa had'ida girgiza Kai ganin na k'ok'arin ficewa. Da tangadi ta nufo k'ofa tana fad'in "Dan Allah.. Kar ka barni a nan.. Ka Kaini wajen Mommy dan Allah ina buk'atan ganinta."
Haidar ya d'auki lokaci yana dubanta kafin ya tako zuwa gabanta "Look, I don't intend to keep you here for good. If you cooperate with me.. Bazaki jima a nan ba zaki tafi.!" Yana ida fad'in haka ya janyo k'ofan ya rufe kirif.
Ummul ta duka a wajen tana dukan k'ofan da d'an sauran strength dinta tana fad'in dan Allah ya bud'e ta ya barta ta fita.
Shiru babu agaji ba taimako, Haidar bai bud'e ta ba sai sautin tashin motarsa da taji. Ta rarrafa da kyar ta isa jikin window nan ta hangi hancin motarsa na barin wajen. Wani irin kuka ta fashe dashi tana Jin zazzabi mai zafi na sauko mata.
**
Anisa ta dubi Dr "Dr wann ai kidnapping ne. We need to see your security footage."
Dr ya murmusa "How is that a kidnap.? Haidar shi ya d'auke matarsa.. He's her legal Husband.. So wann ba kidnapping bane." Ya k'arashe murmushi saman fuskarsa.
Anisa ta furzar da huci "But still you are her Dr. And it's your duty to call him and tell him exactly the consequences of what he's done.. I mean, she's still recovering.. She needs to stay here at the hospital."
Dr ya dubeta still murmushi saman fuskarsa "If you excuse me Miss. I have some patients to attend to." Ya k'arashe yana mai shigewa.
Anisa taci gaba da huci "Ahhhg! Imbecile.!" Ta fad'i tana sakin huci. Wayarta ne ya soma ringing. Ta duba taga Leenah ce. Gajeren tsaki tai had'ida kin d'agawa. Leenah ta kira har kusan sau uku Anisa bata daga ba sai ta turo mata SMS.
_Remember you only have 2 days_
Tsaki Anisa tai tana sakin huci. Yanzu ya zatai ga wann D'an zafin Kan ya d'auke Ummul wacce take tunanin itace last alternative d'inta. Kodai Hilal ne zata kira.? Ta d'anyi gajeren tsaki kafin ta soma Neman layin Hilal.
Bugu biyu Hilal ya d'aga "How's my fish brain sister doing.?"
"Zanci k'aniyarka Hilal." Anisa tace a hasale Jin ya kirata da sunar tsokanar da ya saba kiranta tin yarinta fish brain.
Hilal ya dara "Hey easy. Nayi kewar tsokanarki ne. How have you been.. Bazaki zo bane sai na tafi.?"
Ta dan rausayar da ido had'ida furzar da huci "Yaushe zaka koma school din.?"
"Nayi postponing akwai abinda nake a nan." Ya bata amsa Kai tsaye.
Anisa ta dan zaro ido "Kuma Abba na sane da haka.?"
Hilal ya dara kad'an "He doesn't need to know.. Wani Abu kawai zan k'arasa sai na tafi."
Anisa ta jinjina Kai "Hey Hilal, brother… Alfarma nake nema."
Hilal ya kuma d'an darawa tinda yaji ta fara kashe murya tana kiransa brother yasan abu take nema wajensa "Fad'a kawai meye kike nema wajena.?"
Anisa ta furzar da huci "Money Hilal. Kudi nake nema wajenka."
Hilal ya kuma darawa teasingly yake fad'in "Kuda kuke Abuja gaki ga shugaban k'asa ina zan samo kudi a state na baki."
"Hilal I'm being serious here. Da gaske kudi nake nema. And it's urgent."
"Ok fine. Nawa kike nema.?"
"1M..!" Ta fad'i kaman mai tsoro.
Dariyar rainin hankali Hilal yai "What.! Are you kidding me Neesa.. 1 million a wajen D'an makaranta irina..? You've got to be kidding me. Why not ask Abba. shine D'an kasuwan bani ba. And hey I'm not his manager."
Anisa tace "Haba Hilal. Nasan kanada hanya Shiyasa na kiraka.. Wllhi ina tsananin buk'atar kudin nan. Look zan biyaka da zaran na samu."
Hilal ya d'anyi Jim Jin tayi sounding serious. Shima sai ya daina wasa "Wait Anisa. Be honest with me.. What have you got yourself into..? Gambling kika fara..? Dan nasan dai ba business din da kike. Kodai kinje kin hadu da wasu scammers ne.?"
Anisa ta rausayar da ido "Hilal dan Allah ka taimaken mana nasan Abba naji dakai wllhi na rantse maka da Allah matsala nake ciki. Haba Hilal meye amfanin 'yanuwa ma junansu idan bazasu rufa asirin juna ba. Nasan Mommy zata bani idan tasan ina nema amma bana so ta sani. Kasan masu kudin nan the moment suka gane abun hannunsu ya rufe maka ido akwai matsala."
Hilal ya d'anyi jim "Anisa ni fah kudin dake account dina pocket money na ne. Kuma idan har na baki su yanzu za'azo a shiga tsakiyan semester ne ina nema. And kinsan Abba komai da lissafi yake bazan zo masa da labarin rashin kudi ba tinda yasan ya sallameni. Cewa zai wasa nake da kudi sai naje nai ko aikin k'arfi ne a can na ci da Kaina."
Anisa tace "But you are his favourite."
"Even so Neesa. Kinsan yanda mahaifinmu yake idan aka zo maganar kudi."
Zata kuma magiya Hilal yace "Fine… Zan tura miki.. Amma ko da wasa kar ki bari ko Ammi tasan na baki banso na hadasu fad'a da Abba."
Anisa tai alaman zipping bakinta da yatsa kaman Hilala na kallon ta "An gama my dear Brother. That's why I so much love you."
Da haka Anisa taita gwada Hilal tana fad'in irin son da take ma tilon dan uwan nata.
Gama wayar da zatai ta waigo gabanta yai wani irin fad'uwa samakon ganin mutum da tai tsaye bayanta. Taci gaba da yatsina fuska tana dubansa "Malam lafiya.? Wanene kai.?"
Huci kurum Hisham yake yana dubanta kaman zai shak'ota. Yaci gaba da jinjina Kai yana fad'in "Nasan kece.! Kece kika tassama kashe Ummul.!"
Anisa ta zaro ido waje ganin stranger da ko saninsa batai ba yana fad'in laifin da ita da Laila suka binne. Ta soma girgiza kai tana fad'in "No.. I don't know what you are talking about Malam. Meyasa zanyi yunk'urin kashe Ummu. What could be my motive.? Wait why am I even explaining myself. I don't even know you. Excuse me." Tasa kai zata shige.
"You are the only person with the motive to kill her.. Because you love Haidar.. Haka ne.?" Ya k'arashe yana tsareta da ido.
Anisa taja Birki tana dubansa shaye da mamaki. Sai ta soma girgiza kai kad'an ganin dai guy d'in nan da gaske ya sansu "Mai kake nufi..? Wanene Kai.?"
"Na tuna miki ne. Kwanakin baya lokacin da motar ki tabi bayan motar Haidar. Cikin k'ok'arin bin bayansa da kike dan ki gano yanda yake zuwa. Someone hit your car and stopped you from following him.. That someone.. Was me.. Ni ne na bigi bayan motar ki na hanaki bin bayan Haidar."
Anisa ta soma tuno kwanakin baya Mommy tasa ta bi bayan motar Haidar dan gano yanda yake zuwa amma sai tai accident a hanyar ta wata mota da bata tantance ba ta bugi bayan motar ta Wanda hakan Ya hanata bin bayan Haidar.. Kenan wann mutumin ne Ya bigi bayan motarta. Ta d'ago a d'an firgice tana dubansa "Wait.. Kaman nasan fuskarka.. Wait… Aren't you friends with Haidar.?" Ta dan murmusa tana girgiza kai "Oh now I understand.. Are you his watchdog.? Trying to play best friend of the year.? Wow you try.." Ta d'anyi shiru tana dubansa "Don't you think… you are over reacting.. I mean, matar abokinka kake karewa irin haka."
Hisham Ya fahimci Anisa shashasha ce kuma zata zamto makami mai k'arfi da zai amfani da ita wajen k'watan Ummul daga wajen mortal enemy d'insa Haidar.
Anisa ta murmusa tana dubansa "Or maybe it's the other way around.. Mai kake tunanin Haidar zai yi.? if he finds out that his coworker or should I put it this way… His friend is in love with his wife… Kodai ku masoya ne dama tintinin.?" Ta k'arashe tana tsaresa da ido.
"Think whatever you want to think.!" Ya k'arashe yana matsowa kusanta kaman zai shak'ota tana k'ok'arin matsawa baya.
Anisa taci gaba da Zare ido "Malam idan baka k'yaleni ba zan maka ihun b'arawo.!"
Yaci gaba da jinjina Kai "Go ahead and shout! Let see waye yakeda abun fad'i ma 'yansanda."
Sai kuma tai shiru tana ci gaba da Zare ido. Hisham yaci gaba "If you dare think of hurting Ummul.. Believe me I'll deal with you myself.!"
Cikeda tsoro had'ida mamaki Anisa ke dubansa. Sai kuma ta girgiza Kai tace "And… who are you to Ummul.? Dan ban yarda kana son kareta ne kawai dan kana abokin Haidar ba."
Kallon shashasha yaci gaba da yima Anisa dan da tasan lokacin da ya bugi bayan motarta Ya hanata bin bayan Haidar ba don Ya kare Haidar yai ba sai dan ya hanata gano Matar Haidar da Ahalin Haidar d'in basu san da ita ba wato Dareen da wann doluwar bata tsaya tana bata bakinta ba.
"Idan kika sake yunk'urin cutar da ita .. Sann ne zaki san ko ni waye."
Anisa ta murmusa tana dubansa "Ta Ya zan cutar da ita balle Har ka bata kariya bayan an riga an d'auketa."
Hisham Ya dubeta ya kuma girgiza kai da mamaki "Kina so kice mun Ummul bata asibitin nan.?! Is she kidnapped or something.? Waye ya saceta.?"
Anisa ta kuma murmusawa "One question at a time. Wanda ya fimu kusanci da ita daga ni har kai shi ya saceta.. Ina nufin mijinta..!" Ta k'arashe da murmushi saman fuskarta. Zuciyarta na tabbatar mata abokin Haidar son Ummul yake ba tareda sanin Haidar d'in ba. Amma ita idan har haka Ya tabbata ribanta ne dan zasu had'a team mai k'arfi wajen ruguza tsakanin Ummul da Haidar.
"Ina Haidar Ya kaita.?" Ya tambaya yana duban Anisa.
Anisa ta murmusa "Why not ask him.. After all, abokin ka ne… Kasan me.? Although Haidar never introduce his friends to his family na rasa gane ya akai nasan fuskarka matsayin abokinsa… Koda yake wann Dan uwan nawa bamuyi zaton ma nada abokai ba.. Maybe kaima d'in dan wajen aikinku d'aya ne Shiyasa.. Im sure na tab'a ganinka ka kawo masa wasu takardu da Ya danganci aikin company gida."
"Shut up." Hisham ya katseta jin tana sunbatun da babu Wanda Ya tambayeta. Yaci gaba da dubanta "Kina jina.. Yes ina son Ummul. With every fibre of my being. Hasalima ni na fara sonta kafin ta zama matar Haidar.. You and I are going to help each other out. Ina so ki tabbatar min cewa my secret is safe with you kaman yanda naki ya zama safe dani. That is idan kina so mu raba su biyun.. Ki mallaki Haidar na mallaki Ummul.. Zan iya tabbatar Miki with my help.. Haidar will be yours forever.."
Anisa ta zaro ido waje "Da gaske kake.. Let's team up then.. Zanyi komai.. In fact kokari kullum nake dan burina Ya cika."
"Your wish has been granted.." Ya fad'i yana jinina kai.
Take sukai exchanging phone number cikin k'ok'arin yanda zasu fara zartar da plan dinsu na k'ok'arin raba Haidar da Ummul.
Tsaye Hisham yai a dakinsa na sirri Wanda hotunan Daddy Mommy harma da Haidar sune kawai a cikin d'akin an mammannasu jikin wall. Had'ida dangin magazines masu d'auke da labarun Maitama Builders. Da duk wani article da ya k'unshi scandals wanda sukai popping a labarun kasuwanci wad'anda suka danganci Kampanin Maitama da ahalinsa. kaf shi yake fitar da scandals d'in. Yai tsaye gaban hotunansu yana kallo lokaci guda yake furta "Why Ummul.? Why her..? Menene dalilinku na kawo Ummul cikin wann messed family din naku.!" Yakai dubansa kan hoton Mommy, lokaci guda yaci gaba "Kwaise Maitama ya kikaji zaman kurkuku.? you are the one who instigated everything.! You should suffer the consequences.. All the hardships nida mahaifyata had to experienced. Kece kika jawo.!" Yaci gaba da jinjina Kai "It is your fault that I had to search for people who would accept me all my life..?!" Ya k'arashe hawaye na gangaro masa. Yaci gaba da jinjina kai "You are now in Jail… Ke d'in yanzu kina tsare a kurkuku.. Abin takaicin kuma D'anki ne Ya kaiki. Did you know that… I was born in a prison..? Did you know that I grow up thinking ni ba kowa bane but a son of a criminal..?! Yai maganar cikin tsananin sakin huci kafin yaci gaba "This is the perfect time for me to ruin your life completely kaman yanda kika lalata nawa. Yanzu ne lokacin da ta kamata na fitar da labari akanki. Kinyi yunkurin kashe matar D'anki. Ya kika ji labarin Kwaise.? Abun zai matuk'ar k'ayatarwa musamman a shafukan labarun kasuwanci. Dan na tabbata Aliyu Maitama ba korar wulakanci kawai zai Miki ba muddin kika bata masa suna irin haka a duniyar kasuwanci. Zai tabbata dake da D'anki da kika koreni sabida shi naku rayuwar ya daidaice fiyeda yanda nawa rayuwar da na mahaifiyata ya daidaice. Saidai kashh.! Ummul ta shiga cikin wann ahalin naku. She shouldn't get involved..! She shouldn't.!" Yaci gaba da jinjina Kai yana sakin huci "Kaman yanda nai alk'awarin tarwatsaku haka nai alk'awarin fitar da Ummul daga wann ahalin naku. Sai na rabaka da Ummul Haidar domin kuwa ita d'in tawa ce.!" Ya k'arashe yana duban hoton Haidar da idanunsa da suka gama rinewa zuwa ja.
**