Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 27

Auren wata ukku by sameena - Chapter 27

Auren wata ukku by sameena Chapter 27: Auren wata ukku by sameena Chapter 27. Ba shi ya dawo gidan ba sai yamma lis. Tana nan kwance k'asa zazzabi Ya gama…

4,143 words

Ba shi ya dawo gidan ba sai yamma lis. Tana nan kwance k'asa zazzabi Ya gama lullub'e ta. A hankali Haidar Ya tura k'ofan d'akin hannunsa rik'eda manyan ledodi. Hangota da yai kwance saman rug ya sanyashi saurin sakin ledojin Ya k'arasa gareta. Ya kai hannu ya tab'a goshinta ganin sai rawan d'ari take. Nan yaji jikin nata zafi k'au. A hankali ya furta "Oh no she's burning up. What do I do..?!" Ya furta yana dubanta gashi ya mance magungunanta a pharmacy din da ya saya. Wani tunani ne yazo masa yai saurin d'agota daga k'asa Ya daurata saman gado ya shiga janyo bargo yana rufa mata ganin sosai take rawan sanyi.. Ya soma rurrufe windows trying to keep her warm. dan dik shi a tunaninsa haka ne zai sauk'ar mata da zazzabin ta daina jin sanyi. Amma sai yaji kaman zafin jikin ya karu ga rawan sanyin da take ya karu.

Yai tsaye yana kallonta yana tunanin abunyi.. Ko room heater zai fita Ya nemo Yai warming dakin dashi..? Ya nufo waje sauri sauri yana tunanin nemo room heater. Cak kuma yaja Ya tsaya kaman Wanda aka dakatar dashi.

"Dr Faruk." Ya furta a hankali kafin ya soma jinjina kai "Yes I need to call him.." Ya k'arashe yana mai Ciro wayarsa daga aljihun jeans d'insa. Nan ya soma dialing layin Dr.

Dr yana dauka Haidar Ya soma sanar dashi cewa jikin Ummul yayi zafi sann Ya mance bai taho da maganin ba. Meye first aid da ya kamata ya soma bata.

Dr Faruk ya murmusa daga d'aya b'angaren. Soyayyar Haidar ga matarsa na kashesa "A cool shower will help.. And she should wear lighter and more breathable clothing."

Haidar ya jinjina kai yana nanatawa "A….. cool shower.. Ok, cool shower.."

Dr ya kuma amsawa yana mai fatan samun sauk'i ga matar Haidar d'in. Haidar yai masa godiya kafin yai hanging up.

Dawowa d'akin yai Ya ganta nan yanda ya barta saman gado tana rawar sanyi. Yai saurin k'arasawa Ya yaye bargon da ya rufa mata. Ya soma k'ok'arin rage mata tufafin jikinta amma sai ta takure jikinta waje guda tana fad'in Ya kyaleta dukda rawan sanyi da take.

Cikeda takaici Haidar yai jifa da hulan da ya zame daga saman kanta "Fine then, take the shower like this." Ya k'arashe yana mai dagota daga saman gadon Yayinda Ummul ke k'ok'arin tattaro sauran strength da ya rage mata tana janyewa daga jikinsa tana fad'in ina zai kaita ya kyaleta.

Bai tsaya amsata ba Ya nufi bathroom da ita cikin hannunsa. Taci gaba da k'ok'arin turasa Haidar na rik'eda da ita yana fadin "Stay here and take a shower. You are burning up." Ya k'arashe cikin k'ok'arin tsaida ita kan k'afafunta amma sai ta soma k'ok'arin zubewa a k'asa sakamakon rashin karfi. Bai bari takai kasa ba yai saurin k'arasowa ya rungumeta cikin jikinsa a daidai lokacin hannunsa ya tab'a switch na shower din ai kaw nan ruwan ya soma zubowa kawunansu su duka biyun. Sauk'an ruwan da taji saman jikinta a bazata ya sa ta sakin ajiyan zuciya Wanda yasa Haidar yai mata cover da arms d'insa kaman mai tsoron kar ruwan Ya cutar da ita. Ya shigar da ita sosai cikin k'irjinsa ruwan naci gaba da zubowa kansu. Yana jin yanda ruwan ke ratsa dumin jikinta zuwa nasa jikin. A hankali Haidar ke lumshe idanunsa yana jin harbawan da zukutansu keyi kaman a tare.

Sun d'auke minutes a haka kafin yaji temperature dinta na sauka a hankali. A haka Ya fito da ita daga bathroom din su duka biyu jikkunansu a jik'e. Cikin kayan da ya shigo dasu Ya Ciro towel sabo Ya rufa mata. Ya d'auki hand towel din yana tsane sumarsa. Lokaci guda yake furta "Change those clothes before you catch cold." Yana ida fad'in haka yasa zai fice yayinda Ummul ta mak'ale sosai cikin towel din da ya rufa mata. Tabbas zazzabin da takeji ya dan sauka. Sanda taga haikan zai kuma ficewa ya kulleta a wann dakin tai saurin bud'e murya tace "Dan Allah ka dakata."

Haidar Ya tsaya Cak sanda yaji muryarta.

Ganin Ya tsaya yasa Ummul ci gaba "Meyasa ka kawoni nan ka kulleni..? Dan.. Dan Allah.. Ka fitar Dani daga kurkukun nan." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya.

Juyowa yai yana dubanta sai ya dawo da baya. Yai tsaye kanta hannayensa hard'e yayinda Ummul ta soma k'ok'arin jada baya. Sai taji ya soma fad'in "Who are you.? Meyasa kika yarda da auren mutumin da baki taba sani ba. Is that even possible.?"

Shiru tai ba tareda ta iya amsa masa tambayarsa ba sai bugun zuciyarta dake karuwa.

"Did Mommy buy you with money.? Nawa ta biya ta sayeki dan kawai kizo cikin rayuwana.?!" Ya k'arashe cikin d'aga murya.

Ta soma girgiza kai tana hawaye. Abinda baison gani a rayuwarsa. Yai gajeren tsaki yana kauda fuska gefe jin bata amsa shi ba sai hawayen dake gangaro mata.

"Fine.. Since you don't want to talk. Enjoy your stay here. Dan bakida ranan fita a nan.!" Ya k'arashe yana mai jifa da hand towel din da ya gama tsane sumarsa dashi zuwa gefenta Wanda saida ya dan firgitata.

Da taga haik'an da gaske zai kuma ficewa ya sanyata saurin fad'in "Nayi ne sabida Iyayena.!" Tai maganar cikin rawar murya irinta mai kuka.

Haidar Ya kaikaito yana dubanta. Ya tako zuwa gabanta "Kin amince da auren mutumin da baki tab'a sani ba sabida iyayenki .? Are you that desperate.?!"

Ta girgiza masa kai tana hawaye "Kud'in aure na.. Shi…. Shine kudin jinyar Abba na… Sann mahaifiyata…" Ta kasa ci gaba da magana sakamakon rawa da muryarta keyi.

Haidar ya kafeta sosai da ido. Ya dan d'ibi dak'ik'ai a haka kafin yace "So I was right. Mommy sayenki tayi da kudi.. Nawa ta sayeki dashi.?!" Ya k'arashe maganar zuciyarsa na masa zafi.

Ta rintse idanunta sosai hawaye na zubo mata. Ba yanda ta iya dole ta fad'a ma Haidar mak'asudin aurensa koda zai kawo karshen zamansu. Ita dai burinta taje ta fidda Mommy daga kurkukun da ake k'ok'arin kaita. Zatai komai dan ta kub'utar da Mommy matar da tun shigowarta gidan bata nuna mata komai ba face zallan k'auna.

Muryar Haidar ta kuma ji cikin tsananin huci yana fad'in "You sold yourself to her.. You don't deserve to go free.!" Yana maganar yana jinjina Kansa. Lokaci guda yasa kai ya fice rai bace. Kallo d'aya zaka masa ka fahimci abun ya masa zafi sosai.

Ummul ta kuma runtse idonta wasu hawayen na gangaro mata.

Can dare ta kuma jin shigowarsa dan har tayi zaton bazai kuma dawowa ba. Wann karon bai ko kalli yanda take tak'ure ba ya aje mata wasu ledodi. D'aya na abinci d'aya na magani.

Baice da ita komai ba ya nufi k'ofa. Yana k'ok'arin fita ta rarrafo garesa tana rok'onsa "Dan Allah ka fitar Dani daga gidan nan.. Wllhi tsoro nakeji.. Dan Allah kar ka barni a nan..!" Ta k'arashe tana had'e hannu alamun rok'o.

Wani kallo ya watsa mata kafin yasa kai ya fice yana mai rufe d'akin.

Ummul tai lamo a wajen tana mai lumshe idonta Wanda kuka ya zame masu jiki. Ga dare ga jeji. Bata jin komai sai kukan tsuntsaye. Addu'a kawai take tana kai kukanta ga Rabbil Izza da Ya jibinci lamuranta.

**

Washe gari Haidar bashi yazo gidan ba sai wajajen azahar. Ta Ida sallah kenan taji tsayuwar motarsa. Ga yunwa da ya azalzaleta. Tin bayan abincin da ya kawo mata bata kuma saka komai cikinta ba.

Tai saurin mik'ewa ta Lek'a window dan tabbatar ma idonta ko shi d'in ne. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa sakamakon tuno abinda ya faru jiya. Tai saurin komawa da baya tana jin bugun zuciyarta na k'aruwa.

Sanda Haidar ya turo k'ofan kanta a k'asa. Ya dan d'auki lokaci tsaye daga k'ofan yana dubanta.

Janye idonsa yai daga barin dubanta yana k'ok'arin shigowa d'akin dan shima a b'angarensa yana shigowa Ya soma tuna kasancewar da sukai tare k'asan shower a jiya. Yai gajeren tsaki yana mai shigowa dakin.

"Have you taken your meds.?" Ya fad'i kaman baya so. Daga nan yanda yake tsaye.

Jin bata amsashi ba yasa shi yin gajeren tsaki ya isa ya janyo ledan maganin yana d'aga ko wani maganan Wanda a rubuta dose jikin ko wanne. Nan yaga dai tasha duka. Cikin ko inkula Ya aje mata ledan abinci kafin ya tako zuwa gabanta "Ke.!" Ya fad'i yana dubanta.

"Sunana Ummulkhairi." Ta basa amsa daga nan yanda kanta ke kife.

Bai ambaci sunan nata a fili ba dukda zuciyarsa ya maimaita the moment she closed her lips.

Takarda ya mik'a mata "Sign these papers." Ya fad'i cikeda umarni.

Ta dubeshi ta dubi takardun da yake mik'a mata. Sai ta girgiza kai kad'an "Na menene..?"

"You want be free. Then sign these..!" Ya kuma fad'i yana mik'a mata.

A hankali tasa hannu ta karbi takardun tana dubawa. Dukda ba wai ta fahimci bayanan da suke kan takardun sosai bane. Ta gane takardu ne daga Kotu Wanda idan ta saka hannu tamkar tayi k'arar Mommy ne kai tsaye. Bata San meyasa Haidar ke fad'a da mahaifyarsa irin haka ba. Mahaifiyarsa fah yake yunk'urin kaiwa prison. Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un. Anya yasan k'ima da darajan mahaifiya.? Waye yake fad'a da iyayensa sai tab'ebb'e.

Ta d'ago a d'an tsorace tana dubansa "Bazan iya ba.. Bazan iya kai Mommy gidan Yari ba.!"

Ya duk'o da fuskarsa kusan nata "Why.? Are you even related to her.?!" Yanda yake maganar tamkar fuskokinsu zasu hade waje guda. Ummul na iya jin huci da tururin numfashinsa saman fuskarta mai cikeda tsoro.

Ya damk'o hannunta da iyaka k'arfinsa yana fad'in she should sign the papers.

Batajin tana da k'arfin da zatayi kokawa dashi amma abu guda da ta sani shine har abada bazata kai Mommy prison ba. Wani dabara Ya fad'o mata kawai sai ta fashe da kuka tana k'ok'arin rik'e b'angaren da akai mata aiki alamun na mata ciwo. Haidar yai saurin sakinta yana kallon yanda take kuka tana kama wajen. A d'an daburce Ya soma fad'in "I.. I didn't mean to hurt you… This is your fault you know. Da ace kinyi abinda nace it wouldn't have to be this way. Wait let me see.." Ya soma k'ok'arin janye rigarta ai sai ta zaro ido da gaske ganin zai dage mata riga. Ta soma turasa cikin tsananin k'idimewa tana fad'in "Ai Ya.. Ya ya daina.. k'alau nake yanzu ka gani..!" Ta mik'e tsaye kan k'afafunta kaman wacce aka razaneta cikin k'ok'arin nuna masa lafiya take ba ciwon dake damunta.

Ya tsareta sosai da ido. Wato kukan da take acting ne kawai ba ciwon da take ji. Da taga da gaske zai d'age rigarta ta daina acting d'in. Women are so good in acting kaman dai mahaifiyarsa.

Sai shima ya mik'e tsaye yana binta da kallo daga sama Har k'asa. Ya kula har lokacin kaman rawa jikinta yake. Ai kuwa idan Har haka ne Ya gano lagonta. Zaisa tai signing papers din cikin sauk'i. Ya soma takowa gareta tana k'ok'arin jada baya.

"Kodai ki saka hannu a takardun nan a dad'in rai… Ko kuma…" Yana maganar yana k'ok'arin balle botiran rigarsa. Bai kuma fasa nufota ba.

Ta soma girgiza kai hawayen gaske na zubo mata "A'a dan Allah..!" Cikin rawar murya take maganar har saida Haidar Ya cimmata.

Zuciyarta bai daina tsinkewa ba ganin ya mata rumfa "Zaki saka ne ko na sakaki kisa da k'arfi..!" Ya fad'i fuskarsa dab nata.

Dukda zuciyarta dake tsananin bugu bata fasa girgiza masa kai tana fad'in "K'ima da darajan mahaifiya Ya wuce ai fad'a da ita balle a kaita kurkuku duk girman laifinta.!"

Bakinta dake fitar da kalaman yaketa kalla zuciyarsa na kuma masa zafi da kiran Mommy mahaifiya da take dan shi a idonsa Mommy bata canci a kirata mahaifiya ba.

Jinjina kai yake yana huci "You think I'm playing here right.?!" Batai aune ba taji ya rufe bakinsa da nata.

Hankalin Ummul yakai k'ololuwa wajen tashi. Al'amarin da ko a mafarki bata tab'a hasasho kanta ciki ba sai gashi na k'ok'arin faruwa da ita.

Numfashinta ne Ya soma fita sama sama… Take taja wani irin numfashi ta zube masa a wajen.

Ya duk'a yana jijjigata yana fad'in ta tashi ta daina wann wasan kwaikwayon.

Shiru bata tashi ba har dai Haidar Ya soma tunanin ko sumar gaske ne tai.

Ya tashi ya fice cikin k'ok'arin kawo ruwa ya yayyafa mata aiko yana ficewa Ummul ta mik'e a guje dikda rawa da jikinta keyi ta isa ta rufe k'ofan dan dama ya bar key d'in jiki.

Da mamaki ya juyo yana duban k'ofan. Ta dai k'ara shashantar dashi a karo na biyu. Ya girgiza Kansa k'adan yana mamakin yanda Ya fad'a tarkon yarinyar Har sau biyu dikda matsalan saurin yarda da yake dashi gashi har sau biyu ya yarda da acting da Ummul tayi. Lallai da alama wann yarinyar zata basa matuk'ar wahala kafin ya samu ya cimma burinsa na tura Mommy prison. Sai kuma yaji gaba d'aya jikinsa ya sake kaman baida sauran kuazari. Ya isa saman kujera ya zauna gijif had'ida kishingid'a. Ya lumshe idanunsa bugun zuciyarsa na k'ok'arin daidaita.

** Police headquarters.

Barr ya dubi Daddy da Mommy ya dan girgiza Kai "Zamu iya making abun Ya zama kaman illegal detention tinda Haidar ya b'oye matarsa babu Wanda yasan yanda take."

Daddy yace "So does that mean they would let her off the hook.?"

Kafin Barr yakai ga bada amsa Mommy ta katsesu "No.. I don't want money or power to speak for me.. Iyakacin abinda nake so shine D'a na ya dawo gareni.. I'll plead guilty, if that's what it takes… Zan amsa laifin gaban Alk'alai zan tafi prison for Haidar to forgive me."

Daddy ya dubi Barr yace ya dan basu waje.

Bayan Barr ya fice ya tsare Mommy sosai da ido kafin ya soma girgiza kai cikin rashin yarda "You don't know what you are talking about Kwaise. Do you really want to get convicted.? That ungrateful Son of yours doesn't even care about you..!"

Mommy na hawaye take jinjina kai "Yes.. Zanyi idan hakan zai kawo maslaha cikin rayuwar Haidar. Na rasa shi a farko.. I can't lose him again."

Daddy yaci gaba da girgiza kai "You know you can't appear in court da aurena akanki, bearing my name… Mai kike tunanin sunana zai zama a duniyar Kasuwanci.?!"

Mommy na kallon Daddy take girgiza kai "Then end it Engr.!"

Da tsananin mamaki Daddy ke kallonta. Duk juran zaman da tai a gidansa dukda rikon ko inkula da yake masu daga ita Har Dan nata bata tab'a zab'an rabuwa dashi ba daidai da rana guda sai gashi yau tana fad'in haka kai tsaye.

"It has always been… an empty marriage that's hanging by threads… Watak'ila sabida Haidar ka barni na zauna. Saidai a bangarena na zama lost between zama Mata ko Uwa.. Watak'ila na zab'i na zauna ne Thinking one day komai zai wuce ahalin Ya daidaita… Na Had'iye komai sabida D'ah na da mijina. I even named him after you… I turned myself into a monster a k'wayar idonsa ba tareda nayi la'akari ba. Na tilasta masa ya zamo abinda nake so thinking watarana zaka k'aunacesa zakai alfahari dashi kaman yanda ko wani uba yake… Ya kai matsayin da Har na mance cewa ni Uwa ce dik cikin k'ok'arin ganin burina na had'e kan ahalin Ya cika. But then I realise wann burin nawa bazai tab'a cika ba… Dik abinda naso ma nawa D'an na hana ma D'an wata ya samu.. Na rabaka da D'anka da matarka… Ta Ya zanyi zaton zan samu wann farin cikin da nake fad'i tashi akai tsawon rayuwata..? I am so selfish." Kuka ya hanata ci gaba da magana yayinda jikin Daddy yai matuk'ar yin sanyi.

Mommy ta share hawayen da suka zubo mata kafin taci gaba "Na gode da hakurin da kai Dani tsawon shekarun nan. For letting me stay koda sabida D'anmu. Na gode da ahalin da ka bamu koda bai zamto kaman ko wani ahali ba. Koda cike yake da tarin k'alubali." Taci gaba da jinjina Kai "I give up Engr.. I'm tired.. Na gaji.. Iyakacin abinda nake so a yanzu shine D'ana Ya dawo gareni. The wealth, the name.. Duka na hakura dasu. Na zab'i D'ah na.. Na rasashi daga farko bazan kuma sake rasashi a karo na biyu ba.!" Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya hawaye na gangaro mata.

Daddy ya kauda fuskarsa gefe yana k'ok'arin maida hawayen dake yunk'urin ciko idonsa. Bai kuma cewa komai ba sai mik'ewa da yai ta fice cikin sauri.

Mommy ta kuma rintse idonta wasu hawayen na gangaro mata. A halin yanzu ta gama aminta bokan da suka je wajensa itada Asshe mashahurin makaryaci ne. Tinda gashi turaren da Ya bata ta bama Ummul yasa ta fad'a uku. Dama ita bata tab'a yarda da aikin boka ba ko can baya Asshe ce ta ingizata sukaje. Sann she was desperate ta dawo da D'anta gareta. Bazata gushe ba zataci gaba da rok'on Allah Ya yafe mata kaucewa da tayi dan Tabbas taga aya. Zuciyarta na cikin natsuwa da aminci matuk'a Haidar d'inta na tareda Ummul. Ta aminta da hankali da natsuwar Ummul. Tanada yak'inin D'anta bazai tab'e ba cikin ikon Allah matuk'a na tareda Ummul. Da wann tunani Zuciyar Mommy ya dan samu natsuwa.

SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU..!*

*37*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Bayan shud'ewan awanni ta mik'e da kyar dan a tunaninta ya tafi musamman da taji sam babu d'uriyarsa. Window ta lek'a a hankali kaman mai tsoron kar a ganta. Ga mamakinta shi ta hango zaune k'asar wata bishiya Ya bada baya ma yanda take tsaye daga cikin d'akin. Tsuntsayi ta gani kaman dangin tattabarai Sun taru gabansa sai watsa masu abinci yake suna ci. Wasu Har kaman zasu d'ale saman hannunsa. Kai da gani zaka fahimci yana cikin annashuwa da jin dad'in abinda yake. Juyowa yai yana watsa ma sauran abincin nan ta hango kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Abinda bata tab'a gani ba. Zuciyarta yai wani irin yankewa tai sauri ta koma da baya had'ida jingina jikin gini.

Ta d'auki lokaci a haka. Kafin ta kuma rintse idonta sakamakon tunowa da tai da yanayin da suka kasance ciki bada jimawa ba. Bata San dalili ba amma sai taji hawaye Sun ziraro mata. Ta jima nan a haka kafin ta bud'e lumsassun idonta da suka jike da hawaye. Ta kuma leka window amma sai taga bata gansa ba wann karon. Babu tsintsayen shima baya nan. Babu ko alamunsa. Ta sauk'e ajiyan zuciya a hankali kafin tai k'ok'arin saita kanta. Bata San ya za'ai tai escaping kurkukun da Haidar ya boyeta ciki ba. Bata san hanya ba bata kuma san idan zata iya isaga Mommy ba. Saidai abinda take da tabbaci akai shine zata fice tinda tai saa makulin na tareda ita. Zata fice kodan taje ta ceci Mommy. Har abada bazata bari Mommy ta tafi prison saboda ita ba.

Sauri sauri ta isa k'ofa ta murda makullin ta soma k'ok'arin fitowa a hankali cikin sand'a. Tana tafe tana waige waige ga tsoro da Ya cikata. Saidai tana zuwa k'ofan da zai fitar da ita waje taji gam an rik'e hannunta. K'iris Ya rage bata saki k'ara ba amma sai taji an toshe bakinta. Ta d'ago idonta masu cikeda tsoro tana duban Haidar dake huci yana dubanta.

A matuk'ar tsare yace "Are you trying to escape.? Where do you think you are going.? Answer me.! Guduwa kike so kiyi..?"

Girgiza kai take hawaye naci gaba da gangaro mata. Haidar yaci gaba da janyota yana fad'in bazata bar wann gidan ba Har sai tayi abinda ya umarceta. Da k'arfin gaske Ya tura k'ofan d'akin Ya jefata ciki.

Cikin rawar jiki Ummul ra soma k'ok'arin rarrafowa tana fad'in "Dan Allah kar ka sake rufeni.. Dan Allah Kaji tausayi na ka kyaleni na tafi.. Na maka alk'awari bazan zauna cikin rayuwarka ba.. Dan..!"

"Shiiii..!" Ya mata alama da yatsarsa saman labb'ansa. Ya duk'a gabanta yanda take nan duke tana hawaye cikin rawar jiki. Sai ta soma k'ok'arin matsawa baya ganin Ya duk'o gabanta suna fuskantar juna. Ga zuciyarta da bai daina tsinkewa ba.

Haidar ya dan d'auki lokaci yana dubanta kafin ya kauda kansa gefe. Hannu yasa ya kamo hannunta cikin k'ok'arin hanata ci gaba da matsawa. Tsoro Ya hango sosai saman fuskarta. Sai ya soma sassauta rikon da yai mata a hankali. D'ankwalinta da ya fad'i gefe ya d'auko. Ummul taga Ya kuma nufota taci gaba da k'ok'arin matsawa Har saida ta isa jikin gado. Ga mamakinta bai mata komai ba sai rufa mata D'ankwalin da yai. Ya kuma duk'awa gabanta suna fuskantar juna.

Ta sadda kanta kasa tsoron dake fuskarta bai gushe ba.

A hankali ya soma fad'in "Look, you can call me a monster, but I don't hate you… And..that doesn't mean I like you either.. Kuma idan har kikayi abinda na sakaki.. Believe me, I'll let you go.."

Ta dago raunannun idanunta tana dubansa. Sai Ya jinjina mata kai a hankali alamun tabbatarwa.

Dubansa take shima ita yake duba. Sai ta sadda nata idon a hankali tana mai girgiza masa kai alamun a'a. Cikin sanyin murya mai gauraye da rauni take furta "Ubangijina Ya bani umarni da nai maka biyayya cikin abinda bai sab'a masa ba. An shar'anta wa mace neman al'jannah a k'ark'ashin mijinta. Kaman yanda shima namiji nashi aljannar yana k'ark'ashin mahaifiyarsa. Ka sani Mommy da kake k'ok'arin turawa kurkuku naka aljannan ta wajenta aka ce ka nema.?" Shiru baice komai ba. Ummul ta goge hawayen da suka gangaro mata kafin taci gaba "Shin akwai D'an Adam din da zai wasa da aljannarsa.?" Cikin k'arfin hali Tai maganar dukda zuciyarta dake bugawa.

Katseta Haidar yai da fad'in "Shut up.!" Ya katseta yana mai nunata da yatsa kafin yaci gaba "Who do you think you are.?" Ya kuma girgiza Kai yana rage muryarsa cikeda gargad'i "You don't have the right to speak to me that way.?"

Sai ta tsinci zuciyarta da ba ma Haidar amsa da fad'in 'Ni matarka ce.!'

Kaman Wanda yaji amsar da Zuciyar nata ta bayar sai yaci gaba da jinjina Kai had'ida furta "Kiyi gaggawan yin abinda na umarceki for your own freedom. You don't want to live with a monster as a husband.!" Ya k'arashe yana tsareta da ido.

Girgiza masa kai tai "Kai ba mugu bane. Kana kuma da zuciya mai kyau.. Wanda har zaiji tausayin dabba Ya bata abinci bana jin zaik'i jin tausayin mahaifiyarsa wacce tai sanadiyar zuwansa wann duniyar, ta rainesa har kawo girma.."

Katseta yai da fad'in "Enough.! Ya isheki haka.. You don't know anything..! Ke baki san komai ba gameda wann matar.!"

Sosai Ummul ta razana da yanayinsa.

Haidar yaci gaba cikin tsananin huci "Yes you might be right.! Watak'ila tayi sanadiyan zuwana wann duniyar. Amma naso ace ta barni na Mutu ina yaro da rayuwar k'unci da ta bani.! Yes. Watak'ila ta raine ni kaman yanda kikace. But I was sacred the whole time!" Yaci gaba da jinina Kai yana duban Ummul da idanunsa da suka kad'a sukai jazir "She raised me while degrading me.. While insulting me.. She raised me locking me up in a dark room. Forcing me to eat papers. She raised me punishing me for her sins.!" Yaci gaba "Because of her.. I grew up feeling low self esteem, feeling insignificant… I had a hard time living in myself..!" Yaci gaba da huci yana jinjina akai "And for years… It took me years to overcome the fear and the trauma..!" Ya matso da fuskarsa kusan nata "Did you know na girma ina shakku da kokonto if she's really my real mother.? Do you know how it feels ka girma cikin shakku da kokonton sanin wanene kai.?!"

Suka dauki lokaci a haka suna duban juna hawaye na gangaro ma Ummul. Haidar ya matso kusanta had'ida sassauta murya "So don't act like you know everything.!" Yana ida fad'in haka yasa kai ya fice ba tareda ya kuma yunk'urin rufeta ba.

Tana jin sautin tashin motarsa. Tai saurin Lek'awa nan taga Ya fuzgi motar ya bar wajen a guje. Tabi bayan motar da kallo Har ya b'ace ma ganinta. Sai ta tsinci kanta da masa addu'an kasancewa cikin aminci.

Jiki a sanyaye ta dawo da baya ta zauna saman gado had'ida rapka tagumi. Ta rasa mai zuciyarta ke ji gameda al'amarin Haidar. Idan ta fahimcesa kaman dai ya amo da abinda ke masa ciwo a zuciya ne. Har k'asan zuciyarta bata jin shid'in mugu ne. Sai ta stinci zuciyarta da tausaya ma rayuwar Haidar d'in. Dan bayan abinda ya gama amo mata ta fahimci alak'arsa da mahaifyarsa ya samo nakasu ne tun yarintarsa. Sosai taji tana son sanin asalin wanene Haidar. A wata fuskar sai tana ganin kaman shida ita sunada k'addara mai kamanceceniya musamman a b'angaren abinda ya shafi alak'arsu da iyayensu. Tunanin Umma da irin rabuwar da sukai ya fad'o mata.. A hankali ta lumshe idonta hawaye na gangaro mata.

Ranan har dare bata kuma saka shi a idonta ba.

**

Readers Also Read