Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 31

Auren wata ukku by sameena - Chapter 31

Auren wata ukku by sameena Chapter 31: Auren wata ukku by sameena Chapter 31. Kafin yai wani magana ta dakatar dashi "K'warai na fitar da Tani tinda nasan…

4,472 words

Kafin yai wani magana ta dakatar dashi "K'warai na fitar da Tani tinda nasan burinka kenan ka fitar da ita ka burge Suwaiba. Sann abu na gaba nasan cewa kud'ad'en da ya baka na makaranta ka turasu ma Anisa. Kuma nasan ko mai zai maka bazaka tab'a cewa ma Anisa ka bayar ba. Abinda nake so kai a nan shine ba kai ba 'yar Suwaiba.! Ka nemi 'yar gidan ko waye ka aura amma ba 'yar Suwaiba ba.!"

Hilal ya girgiza Kai yana duban mahaifyarsa "Kinyi haka ne dan ki d'aureni Ammi..? Sabida haka kika zab'i taimaka masu.?"

"Burinka kenan ai ka fitar da Tani koh..? Toh na cika maka wann burin.. Saura nima ka cika min nawa burin ka fita daga hark'an Suwaiba da zuri'arta. Idan kuma ba haka ba yanda nasa kudi na fidda Tani sai na sa kud'i na kulle Suwaiba.! Idan auren kake so da gaske ka nemi 'yar gidan ko waye ni zan tsaya maka koda mahaifinka bai tsaya maka ba. Amma banda 'yar Suwaiba ehe.!"

Ya girgiza Kansa "Kiyi hak'uri Ammi.. You don't have to go this far.. Kimarki ya wuce haka a wajena.. Maganar aure kuma ki kwantar da hankalin ki na jinginesa , har sai na nemi na kaina kaman yanda Abba yace. Da yardar Allah.!" Yana ida fad'in haka yasa kai ya fice.

K'arshe dai Asshe ciwon k'arya ta kwanta gudun kar taje duba Haidar. **

Abuja..

Yau kwanan Haidar ak'alla biyar kenan a coma an doshi sati guda. Babu alamun farkawarsa. Duk wani masoyinsa Ya duk'ufa addu'a gareshi da rok'ar masa sauk'i wajen Ubangijin komai. Babu kaman Mommy da Ummul.. Mommy yini take asibiti yayinda Ummul ke kwana wajensa.

Yau suna zaune saman doguwar sofa dake fuskantar gadon da Haidar ke kwance bisa, na'urar nasara Sun masa k'awanya. Su duka biyun Sun saka shi gaba sun tsura masa ido.

Mommy taci gaba "A lokuta da dama mukan mance wasu ni'imomin da Allah yai mana na d'an lokaci ne ba mai tabbata ba… Allah yakan mana kyauta da samun wasu mutane cikin rayuwarmu. Kaman 'ya'ya, Iyaye, miji, mata da sauran makusanta. Wann kyautar ba mai tabbata ciki.. Ba Wanda yasan adadin kwanaki, watanni, a'a shekaru nawa zakuyi tare kafin Allah Ya amshe wann kyautar.. Shin kayi appreciating wann kyautar.? Shin ka sauk'e nauyin da aka d'aura maka na hakkoki..?" Ta juyo tana duban Ummul da idonta masu rauni "Ina rok'on Allah yasa da sauran rayuwar da zamuyi tareda Haidar a gaba.. Ina rok'on Allah Ya tashi kafad'unsa Ya raya mun shi cikin aminci Ya zamo majib'icin Al'amaransa.." Ta kamo hannayen Ummul cikin nata baya ta share hawayen da suka gangaro mata "Ina rok'on Allah Ya nuna mun zuri'ar Haidar kafin na bar wann duniyar Ummul.. He's all I have.. I can't lose him..!" Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.

Ummul ma hawaye ne suka ciko idonta. Ta shiga jinjina kai cikin k'ok'arin k'arfafa ma Mommy gwiwa, hawaye na gangaro mata "Mommy Haidar zai tashi cikin yardar Ubangiji.. Zakuyi rayuwa irinta D'ah da mahaifiya mai cikeda albarka da aminci.!"

Ta d'ago tana duban Ummul wacce itama d'in Mommyn take duba hawaye fal idonta.

Ta kuma kamo hannayen Ummul cikin nata "Na fad'a zan k'ara fad'a, kin amsa sunanki Uwar alkhairi.. Kinzo da d'imbin alkhairi cikin ahalinmu.. Ummulkhair.!" Ta ambaci sunanta cikin wane irin siga mai nuni da yarda da aminci. Ummul ta d'ago ta dubi Mommy a sanyaye jin yanda ta ambaci sunanta. Mommy taci gaba "I entrust my son to you.. Please take care of him.. Be patient with him.. Don't let go of his hand.. Help him find his way.. Nasan zaki iya.. Allah ya zama maku jagora Ya albarkaceku rayuwarku da zuri'a ta gari."

Sai Ummul ta sadda idonta k'asa cikin jin nauyin Mommy.

Mommy ta murmusa kad'an tana dubanta kafin tace "Tashi ki shiga alwalanki.. Ni zanje na samu Daddynku naga sak'on sa yana jirana a reception."

Ummul ta jinjina kai a hankali tana mai amsawa kafin ta mik'e ta nufi bathroom.

Koda Mommy ta mik'e sai ta nufi jikin gadon Haidar.. Ta dafa goshinsa tana dubansa. A hankali ta furta "My handsome Boy. Allah ya baka lafiya." karanto masa addu'o'i samun sauk'i tai. Ta sumbaci goshin nasa cikeda so da k'auna kafin ta fice.

Tana ficewa hawaye suka gangaro daga lumsassun idon Haidar.

A hankali yatsarsa guda ke motsi.. Ya soma k'ok'arin bud'e idonsa da suka masa nauyi. A haka Har ya bud'esu tar yana kallon sama.. Komai ya soma dawo masa gameda had'arin da sukai.

Ya tuna sanda motar ta sauk'a saman shoulder.. Ya tuna tsallen da yai ya rufe Ummulkhair gudun kar wani abu ya sameta. A hankali ya kai hannunsa ya zame na'urar dake hancinsa lokaci guda ya furta "KHAIRY.!"

A daidai lokacin Ummul ta fito daga bathroom.

Haidar na jin an tab'a k'ofa ya kuma lumshe idonsa kif.

Ummul takai dubanta garesa. Batasan ko idonta bane amma sai taga kaman ya motsa daga kwancen.

Ta nufi jikin gadon nasa Tai zaune saman kujeran da take kusan yini akai tana dubansa dake nan jikin gadon. A 'yan kwanakin da sukai asibitin..

Tagumi tai da hannayenta biyu had'ida tsura masa ido daga nan yanda yake kwance. Ta shiga tuno kalaman Mommy a gareta wanda tamkar amanar Haidar d'in ta damk'a hannunta. Sai ta tsinci kanta da shakku da kokonto musamman da ta tuna kafin had'arin ya faru ya furta mata cewa he'd set her free.. Zai sawak'a mata. A b'angaren guda ga Mommy tace don't let go of his hand..! Mai zai faru idan k'addara bai bata daman sauk'e alk'awarin da ta d'aukar ma Mommy ba.? A wani b'angare na zuciyarta tana tunanin aurenta ya k'are a daidai wann gab'ar bayan ta d'aukar wa mahaifiyarta alk'awarin bazata waiwayi gida ba har sai ta cika watanni uku da aure. Wani k'alubale zata fuskanta bayan ta koma gida.? Shin ta Ya zata fuskanci Umma da sauran ahalin gidansu idan har aurenta Ya Mutu. Auren da ga yanda Ya kasance Tun farko.. Tabbas batasan yanda zata fuskanci Umma ba muddin aurenta Ya k'are kafin aje ko ina.. Ita duk ba wann ba. Ko kiran waya Umma ta haramta mata mai zai faru idan ta koma da sunan auren ta Mutu.? Ta lumshe idonta a hankali tana furtawa cikin zuciyarta 'Allah duk yanda kayi daidai ne.! Ka shiga al'amari na ka zamto majib'icin lamrana.!'

Ta bud'e lumsassun idonta ta zuba su tsaf akan Haidar dake kwance.

Sosai k'irjinta ke bugu sanda Takai hannunta dake tsananin rawa mai d'aukeda damshin ruwan alwala tana shafa goshinsa zuwa sumarsa a hankali. Abunda tasan ko bindiga za'a saka mata idan idonsa biyu ne bazata tab'a iya yin hakan ba.

Tamkar electric shock haka Haidar yaji sauk'ar hannun nata saman goshinsa. Har lokacin bai nuna alamun farkawa ba.

A hankali taji tana samun natsuwa, bugun zuciyarta na daidaita bata daina abinda take ba.

Ta tsinci kanta tana mai sakin Murmushi a yayinda take dubansa. Har lokacin bata daina shafa goshinsa zuwa sumarsa ba "Kasan mai..!" Ta furta a hankali had'ida gyara zamanta. Ta d'aura hannunta saman yatsunsa a hankali "Kanada sa'a. Kai d'an gata ne.. Ina nufin kanada mahaifya da take matuk'ar k'aunarka..!" Ta k'arashe maganar cikin sanyin jiki tunowa da nata mahaifiyar da tai da kuma irin rabuwar da sukai bayan tayi aure. Ta jinjina kai a hankali tana share hawayen da suka gangaro mata. Sai ta d'an tsura masa ido kad'an "Kanaga zan iya sauk'e nauyin alk'awarin da na d'aukar ma Mommy.?"

Sai ta d'an girgiza kai "Na tabbata da idonka biyu zaka ce.. Ke! Get out of my face.! You don't want to have a monster for a husband.!" Tai maganar cikin tsarewa ita a dole tana kwaikwayonsa.

Sai kuma ta bama kanta dariya. Ta murmusa kad'an tana mai tsura masa ido tsananin tausayinsa kwance cikin k'irjinta. Tai raurau da ido Kaman mai shirin kuka tace "Watak'ila You are a bit of a Monster, but you are also sweet.. So sweet…. Sweet Monster.!" Taci gaba da sakin sassanyar murmushi tana dubansa "Na gode da ka ceci rayuwata.! Na gode da rayuwata ta kasance mai mahimmanci a wajenka. Allah ya baka lafiya.!" Ta k'arashe tana k'ok'arin mik'ewa. K'ok'arin zame hannunta daga nashi take amma mai .? Sai ji tai gam Haidar ya tamke hannunta cikin nasa.

K'irjinta yai wani irin bugawa. Ta zaro ido waje tana jin bugun zuciyarta na k'aruwa. Ta kasa juyowa ta dubesa sai rawa da jikinta yake.

SameenAleeyou📚 *AUREN WATA UKU..!*

*41*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Duk sai ta daburce ta rasa mai zatai. Ta kasa furta komai sai duban juna da suke su duka biyun… A haka aka turo k'ofan d'akin.. Ba kowa bace face Mommy. Ganinsu a haka yasa Mommy saurin k'arasowa murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta. Farin cikinta ya gaza b'uya.

"Haidar. My son.! Alhamdulillah.. Haidar ka tashi..!" Sai kuka ya b'alle ma Mommy. Ta d'aga hannayenta sama tana fad'in "Alhamdulillah.! Allah na gode maka da ka tashi D'ah na. Allah na gode maka..!" Hawaye na gangaro mata tafukan hannayenta tallafe da fuskan Haidar din duka b'angare biyu taci gaba "I can't believe you are finally here with us again son.. You know, I don't mind losing everything.. But.. Amma bazan iya rasaka ba Aliyu… Bazan iya jure rashin ka ba..!" Ta daga hannayenta guda biyu sama "Allah na gode maka daka tayar min da D'ahna… Allah na gode maka for giving me such a blessed opportunity to be with my son again..!" Ta k'arashe tana mai rungumo kansa daga nan yanda yake a kwance. Dole duk Wanda ke duban Haidar da mahaifiyarsa su basa tausayi.

Ummul ta share kwallan da suka zubo mata. Ta janye jikinta ta matsa gefe kad'an cikeda farin ciki musamman yanda taga farin ciki Ya mamaye Mommy.

Mommy ta dubi Anisa da shigowarta kenan tace maza ta kirawo Likita. Cikin sauri Anisa wacce itama farin cikinta had'ida mamaki Sun gaza b'uya ta shiga jinjina akai tana fad'in "Sure Mommy. Right away.!"

Koda Likita ya shigo tambayoyi ya soma masa yanda ya fara da tambayarsa meye sunansa.

Shiru Haidar baice komai ba sai kallon da yake binsu dashi d'aya bayan d'aya. Zuciyar Mommy yai wani irin yankewa ganin irin duban da Haidar ke masu tamkar Wanda bai tab'a saninsu a rayuwarsa ba. Duba irinta rashin sani.

Mommy ta soma girgiza Kai tana duban Haidar tana duban Likita "Dr.. Meke faruwa da D'anah..? Why can't he say anything..?"

Dr yai k'ok'arin calming Mommy kafin ya dan soma 'yan dube dube dangin su ido da k'irji ma Haidar dake nan kwance yana musu kallon rashin sani musamman Mommy.

Mommy ta dubi Haidar ta kuma dubi Dr "Likita sanar Dani meke damun D'ana.?"

Dr ya girgiza Kai kad'an had'ida furzar da huci kafin ya maida dubansa ga Mommy "I'm not sure if he's having a temporary memory loss.. But there are some testes he has to undergo ta haka zamu iya fahimta matuk'a baiyi magana ba har na tsawon dak'ik'ai."

Mommy ta lumshe idonta hawaye suka gangaro mata. Taci gaba da duban Haidar tana hawaye take girgiza Kai.. Ta rungume kan Haidar cikin k'irjinta hawaye naci gaba da gangaro mata. Mai zai faru idan Haidar ya mance ta.? Mai zai faru idan D'anta bai kuma tuno ko wacece ita ba. Just when she thought rayuwa ta basu daman kasancewa tare a karo na biyu kwatsam wann tashin hankalin ya Kunno Kai.. Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un.!

Cikeda tsananin tausayi Ummul ke duban Mommy da Haidar hawaye na gangaro mata. Allah sarki Mommy ta jira farkawan D'anta ta sanar dashi how much she loves him sai gashi ya farka amma ba Lallai ya kuma sanin ko wacece ita ba.. Kai Lallai rayuwa abar tsoro ce.

Anisa ce ta kamo hannun Ummul itama guntun hawaye ne cikin idonta "Let's go Ummul. Let's wait outside.. Mommy needs some time with her Son alone."

Ummul duban Anisa kawai take tana Jin zuciyarta na wani irin yankewa.. Tamkar rak'umi da akala haka tabi Anisa suka fice daga d'akin.

Kan Mommy na kife gefensa tana hawaye taji hannun Haidar saman nata.

"Mommy.!" Taji ya furta a hankali cikin murya irinta majinyata.

Ta d'ago tana dubansa yayinda Idanun Haidar ke kallon sama.

"Aliyu..!" Ta furta a hankali tana dubansa "Ka.. Kana iya magana..? Ka gane ni..? Ka.. Ka ambaci Mommyn ka.!"

Still idanunsa na duban sama yake fad'in "Even back then.. Lokutan da kike hukunta ni bisa laifin da ba nawa ba ban tab'a mance ki ba Mommy.. And do you know why.?!" Ya k'arashe yana mai karkato da fuskarsa suna fuskantar juna shida ita. K'walla ne tab cikin idonsa yayinda hawaye suka ci gaba da gangaro ma Mommy.

Haidar yaci gaba "Because you are my mother.! Ban tab'a tunanin rejecting d'inki matsayin mahaifiya ba. Haka ne.?"

Mommy taci gaba da hawaye yayinda Haidar yaci gaba da jinjina Kai siririn hawaye na gangaro masa "Koda ace wann D'an talikin yaron babu abinda yake mafarki da buri sama da soyayyar ki da kulawarki.. Not once have I ever looked down on you..!" Ya lumshe idonsa siririn hawaye ya gangaro masa.

Mommy ta lumshe idonta hawaye suka gangaro mata. Tana tuna rayuwar k'unci da ta ba ma d'anta ba tareda tayi la'akari ba.

Haidar yaci gaba da jinjina Kai yana duban mahaifiyarsa "Dukda duka wad'ancan abubuwan da kika mun.. Dai dai da rana d'aya Mommy ban tab'a danasaninki matsayin mahaifiya ba.. Ban tab'a hanaki yanke wani hukunci na rayuwata ba.! You dictated my whole life.. Karatuna..! Aikina.! Daga k'arshe har aure na Mommy… Kece kika zabo matar kika kuma yi a lokacin da kike so koda auren ya kasance k'ark'ashin yarjejeniya.! Koda ban kasance wann D'an da kike so mahaifinsa yayi alfahari dashi ba. Ban tab'a taka wani dokanki ba sabida ina ganinki matsayin mahaifiya.!" Suka ci gaba da duban juna hawayen Mommy na k'aruwa.

Haidar ya maida dubansa ga duban sama "Amma daga lokacin da na dubeki da kallo na k'ask'anci.. Na Miki kallon tir da zama mahaifiyata. Na kulle ki a kurkuku Mommy.. Na fad'a Miki kalamai masu tsanani Wanda duk rayuwar da mukai lokutan baya ban tab'a fad'a Miki irinsu ba.!" Sai ya d'an girgiza Kai kad'an "Ummulkhair..!" Ya furta a hankali kafin yaci gaba "Thanks to her na fahimci ke d'in Mahaifiyata ce. Kuma ba'a tab'a iyaye irin haka a zauna lafiya.!" Ya Kuma duba Mommy kafin yaci gaba "Na fad'a Miki kalaman ne cikin b'acin rai bayan kin sanar Dani labarin yanda kika salwantar da ahalin mahaifina... D'anuwana ko 'yaruwata dake ciki bai zo duniya ba da kuma matar mahaifina da batada hakkin komai..!" Yaci gaba "Na mance cewa dukanmu 'yanadam ne.. And we all have our shortcomings. Na mance cewa we all make mistakes and We are far from being perfect…!" Yaci gaba da duban Mommy daga nan yanda Yake kwance "Watak'ila na shiga hurumin da ba nawa ba..! She was right Mommy… Khairy was right, I shouldn't have looked down on you.! I shouldn't have locked you up in jail..! I shouldn't have said all those horrible words to you." Ya d'an karkato sosai yana duban mahaifiyarsa. Hannunsa na matuk'ar rawa ya d'aura saman na Mommy. Mommy ta dago da idonta masu zuban ruwa tana duban Haidar da kuma yanda ya d'aura hannunsa saman nata.

"Please forgive me Mommy..!" Ya k'arashe muryarsa na shaking sosai. The sincerity in his voice was clear.

Sai Mommy ta rungumosa daga nan yanda yake kwance saman gadonsa. Cikin kuka take girgiza Kai tana fad'in "Baka mun komai ba Aliyu.! Tun tasowarka ni ce na cuzguna maka na bak'anta maka rayuwa sabida son zuciya....! Tabbas abinda mutum ya shuka shi yake girbewa. Na cutar da Fannah da abinda ke cikinta dan na samu dawamammen farin ciki a cikin gidana. Shi kuma alhaki kwikuyo ne. Sai na samu akasin haka tsawon shekarun nan. Ban samu wann farin cikin ba. Bakada laifi ta ko wace fuska Haidar kuma banji ciwon abinda ka mun ba sai ciwon abinda ni na jima ina maka. Na aza maka nauyin zunubaina bisa kafad'unka ba tareda hakki ba." Ta numfasa hawaye na kuma gangaro mata "Aliyu D'anah ina matuk'ar k'aunar ka.. Ina rok'on Allah ya bud'e Zuciyar D'ah na ya mun kwatankwacin kaunar da nake masa.!" Ta k'arashe hawaye da murmushi saman fuskarta.

Ya rik'e hannun Mommy cikin nasa sosai "I would pick my mother to be my mother again in any and every life time..

Farin ciki ya gaza b'uya a fuskar Mommy cewa da Haidar yai zai zabe ta matsayin mahaifiya a kowace rayuwa ya yaye mata wani burden da take kwana ta tashi dashi.

Daddy dake daga k'ofa Akan idonsa komai ta faru.. Murmushi out of nowhere ya subce masa ganin ahalinsa cikin yanayi mai ban sha'awa da bai tab'a gani ba. Kasa shiga d'akin yai sai ya juya ya fice yana jin zuciyarsa na masa wasai.. Koda ace baida k'warin gwiwan tunk'aran ahalin nasa a yanzu. Ganinsu haka cikin farin ciki Ya wadatar masa. Yana Jin wani annashuwa da sakinah da ya jima bai tsinci kansa ciki ba tsawon shekarun.

Koda ya isa company ma Alhaji Gimba ya fuskanci relief da farin ciki da abokin nasa ke ciki.

Alhaji Gimba ya murmusa yana duban Daddy alamun da magana a bakinsa.

Kafin yakai ga furtawa Daddy ya katsesa "A fad'a maka Haidar ya farka..?" Yai maganar har lokacin dai murmushi ne saman fuskarsa.

Alhaji Gimba ya kuma murmusawa "Ka fad'a mun wann the moment labarin ya same ka. Har ka mance.?"

Daddy ya d'an shafi goshinsa "Aff haka fah.."

"Ya baka zauna can ba.! Ai da kayi zamanka.. I have everything under control here."

"Kwaise tana can." Ya fad'i jikinsa a dan sanyaye wann karon. Dan har kawo wann lokacin Mommy bata daina sha masa k'amshin da ta tsira ba. Kallo guda zaka masa ka gane duk baya wani hayyacinsa.

Shiru Alhaji Gimba ya d'an yi kafin ya numfasa yace "Ka k'ara mata lokaci abokina.. Ita mace fah duk girmanta sunanta mace. Kuma su mata rauni ne dasu… Ba wuya an janye wayonsu da kalamai da kyautatawa.. Nan da nan sai kaga Sun sauk'a daga dokin fushi.. Amma fah idan aka kaisu mak'ura kalamai da lallama basa aiki nan take.. Toh fah wann karon kaine zakayi hakurin da ita."

Daddy ya dan dubesa sai ya furzar da huci a hankali.. Ya kishingida cikin kujera yana mai lumshe idonsa.

**

A can asibiti kuwa Hisham ne yaje duba Haidar.

Yana zaune gaban gadonsa ya k'ura masa ido fuskarsa fal damuwa.

Haidar yai gajeren tsaki "Kasan dai bana so ayita kallo na.. It irritates me.."

Hisham ya Kai masa punch a damtsensa maras ciwo. Haidar ya dan saki k'ara yana fadin "You are such a jerk you know.!"

Hisham ya girgiza Kai "You are the real jerk here Haidar.! This isn't a joke.. I mean, You almost killed yourself in that accident.. I know you so well.. Idan ranka ya baci tuk'i kake ba tareda kana sanin ina kake zuwa ba.!"

"Kana tunanin akwai b'acin ran da zaiza nai yunk'urin kashe kaina..? Hisham akwai wata cikin motar nan. And she happens to be my wife.!"

Saida Hisham ya dago ya kallesa jin ya ambaci Ummul da matarsa.

Haidar yaci gaba "You know me.. I wouldn't put someone in harms way.. Koda ace ni mutum ne da ya yak'i ahalinsa tsawon rayuwarsa…" Yana jinjina Kai yake fad'in haka kafin yaci gaba "Abinda nake tunani shine… the accident was planned. Someone planned it.!"

Gaban Hisham ya yanke ya fad'i amma sai ya dake . Ya dan girgiza Kai kad'an yana karantar Haidar d'in "What do you mean.? Kana so kace kana zargin wani da shirya maka had'arin.? Kamar ya kenan Haidar.?"

Ya dan rage girman idona still yana duban Haidar d'in "Wait don't tell me har yanzu zargin ahalinka kake da yunk'urin kasheka.. My goodness Haidar.. Wai har yaushe zaka watsar da wann tunanin ne..? Sai yaushe zaka watsar da makaman fad'anka Akan ahalinka. Until when Haidar.?!" Ya k'arashe cikeda nuna kulawa kaman dai ko Yaushe.

Haidar ya tsaresa sosai da ido "Someone tampered with my brakes.!"

Hisham ya dan girgiza Kai "But.. who could have done that.? I mean all your life you thought ahalinka sune mak'iyanka.. Dukda cewa kanada b'oyayyun mak'iya masu son ganin bayan ahalinka da family business dinku.. Ina nufin masu kai maka suka a company da media.. But basu tab'a yunk'urin kasheka ba.. "

Katsesa Haidar yai da fad'in "What if I have a new enemy..? What if someone's holding a grudge against me..? What if someone wants to take their revenge on me.!?"

Cikin sakanni Zuciyar Hisham ke bugawa dan gani yake Haidar Ya gama ganosa ne.

Daidai lokacin akai knocking a k'ofa.. Mommy ce ta shigo fuskarta d'aukeda murmushi.

Hisham ya mik'e cikin k'ok'arin bama Mommy da Haidar waje. Ya gaida Mommy had'ida mata sannu da jikin Haidar kafin ya maida dubansa ga Haidar. Sallama Yai masa tareda fatan samun lafiya had'ida k'arawa da zasuyi magana.

Mommy tabi bayansa da kallo fuskarta d'aukeda murmushi. Shi d'aya ne abokin da zata iya cewa ta sani na Haidar.. Dukda ba wani saninsa tai sosai ba tasan wajen aikinsu d'aya kuma he's very fond of her son.. Tasan duk Wanda zai hak'uri da halayyan Haidar Ya zauna dashi irin haka sai Wanda yake masa soyayya na gaskiya tsakani da Allah. Tana ji Har cikin ranta he's a good influence for her son.

Farin cikin Mommy gaba d'aya ya gaza b'uya. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tamkar k'wai hannun jariri haka take ririta Haidar. Gaba d'aya jinsa yake Awkward dan shi tun tasowarsa zai iya cewa babu wata alak'a mai kamanceceniya da wann tsakaninsa da mahaifiyarsa.

Ya d'an soma yunk'urin mik'ewa Mommy ta k'araso da sauri tana k'ok'arin taimaka masa take tambayarsa mai yake so.

A hankali yake furta "Is ok Mommy.. I can manage.."

Mommy ta gyara masa pillow ya kishingid'a sosai. Tana dubansa tana sakin murmushi…

Gani tai sai kalle kalle yake kaman yana neman wani abin ko yana so ya tambayeta wani abu.

Ta matso ta dafa hannunsa kad'an "Akwai abinda kake so ne Son.. Should I call the Dr for you..? Kana jin wani ciwo ne..?"

Ya d'an girgiza kai kad'an "Where is she..? Why isn't she here..?!" Magana yai a hankali amma bai san Ya fito fili ba.

Mommy ta girgiza Kai kad'an tace "Wace kenan..?"

Ya dan dubi Mommy kaman bazai ce komai ba sai Ya tsinci bakinsa kai tsaye da furta "Khairy..!"

Farin cikin Mommy ya k'aru. Sai tace "Oh.. Ai Sun tafi tareda Anisa ta kaita gida. Nace ko zata d'ebo maka wasu kayyakin da zaka buk'ata. Amma nasan Watak'ila ma suna hanyar dawowa."

Baice komai ba sai Ya d'an kuma yunk'urin mik'ewa alamun yana son sauk'owa daga saman gadon.

Mommy tai saurin tallafosa tana tambayarsa mai yake so.

Ya d'an dafa gadon yana fad'in "I need to use the bathroom.."

Mommy ta soma k'ok'arin dafa masa tana fad'in bari ta taimaka masa.

Ya girgiza Kai cikeda kokari mai nuni da jarumta "You don't have to worry Mommy.. I can manage.."

Ta girgiza kai a'a Haidar Bakada wani k'arfi fah.. Duba ka gani.."

Daidai lokacin su Ummul da Anisa sukai sallama.

Mommy tai hamdala tana fad'in "Gwara da Allah Ya kawo ku. Maza k'araso Ummul ki taimaka ma mijinki.."

Haidar yai saurin katseta "I said I can manage, Mommy.."

Girgiza Kai Mommy tai "So kake ka fad'i ka kuma jin wani ciwon…?" Ta k'arasa ta kamo hannun Ummul da tai sororo ga zuciyarta da bai daina tsinkewa ba. Ta dank'a mata hannun Haidar cikin nata "Assist your husband."

Bata tsaya sauraron komai ba ta janye Anisa da tai mutuwan tsaye nan wajen tana kallon yanda Mommy ta saka hannun Ummul cikin na Haidar.. Bata ankara ba sai ji tai Mommy tana janyota tana fad'in ta shige su basu waje.

D'akin ya rage saura Ummul da Haidar. Ya kuwa tsareta da ido fuskan nan a murtuk'e kaman ba shine ya gama jajenta ba.

Ta had'iyi abinda ya tsaya mata da k'yar dan tinda yai regaining consciousness bayan gaisuwa da tai masa basuyi wani magana ta fatan baki ba.

Takai idonta kan hannunta yanda Mommy ta had'e da na Haidar waje guda. A hankali ta soma k'ok'arin zame hannun amma sai taji ya matse hannun ya hanata abinda take k'ok'arin yi. Ta d'ago ta dubesa ita d'in yake duba har lokacin babu wani walwala saman fuskarsa.

Hannunta taji ya janyo ya zagaye bayansa dashi ya d'aura saman waist d'insa.. Ta kuma dubansa cikin fad'uwan gaba. Har lokacin bai janye ido daga barin dubanta ba.. Bata kuma ankarewa ba saiji tai ya d'aura hannunsa guda saman kafad'arta yayinda hannunta guda ke saman waist d'insa irin dai yanda ake taimaka ma maras lafiya idan zai tafiya..

Maimakon ta soma takawa sai shine dai yai yunk'urin tafiyar Kai kace itace maras lafiyan.

Muryarsa ta sinkayo yana fad'in "Don't look at me like you've seen a ghost… They say monsters don't die early.!"

Yai maganar kaman ba shi ba saida ta dan dago ta dubeshi tana mamakin kar dai yaji kiransa monster da ta dingayi sanda yake kwance unconscious. Sai ta tsinci kanta da Jin kunya ta sadda kanta k'asa.

A haka suka ci gaba da takawa Zuciyarta bai daina yankewa ba. Addu'a kawai take cikin zuciyarta Allah ya bata k'warin gwiwa..

Aiko suna shigewa bathroom din ta soma k'ok'arin janye jiki daga nasa..

Cikin in ina take furta "Zan.. Zan jiraka a k'ofa.." Juyawan da zatai ta kunna musu shower akansu.. Haidar ya janyota jikinsa gaba d'aya "What if I fall..?" Ya fad'i yana mai manne goshinsu waje guda su duka biyun idonsu a lumshe. Sosai Ummul ta rintse idonta tana Jin yanda karan hancin Haidar ke gogan nata ga ruwa dake zubo musu.

"Amma.. Amma.. Naji kaman kace ma Mommy zaka iya.." Ta fad'i da kyar cikin k'ok'arin ganin ya k'yaleta ta fice. Amma sai taji ya kuma had'e fuskokinsu waje guda.

Murya na rawa ga ruwa dake jik'asu tace "Mai.. Kake aikatawa..?"

"I'm rebuilding my life..!" Ya furta a hankali saitin kunnenta kafin yaci gaba "Isn't this what you want..?"

Tai saurin ware idonta tana dubansa zuciyarta naci gaba da bugawa.

Haidar yaci gaba "Isn't this what you promised Mommy… That you'd help her son…rebuild his life… Are you scared now..?" Yai maganar yana mai kuma rungumeta cikin jikinsa. Cikin sigan rad'a yaci gaba "Are you sure you are ready to invade my sick world..? Don't you think you are taking too much of a risk..? Are you not scared of a monster..?"

"But you are not a monster…!" Ta furta cikin rawar murya.

"What makes you believe… That… I'm sweet…?" Yai maganar d'umin numfashinsu na gaurayuwa da juna. Kaman zai sumbaceta. Har lokacin idanun Ummul suna lumshe. Ga heartbeat dinta dake k'aruwa.

Ta kasa furta komai sai k'ok'arin cire jikinta daga nasa da tai dan ta gama amincewa yanzu kam duk wasu maganganun da tai sanda yake kwance yaji komai.

Readers Also Read