Auren wata ukku by sameena - Chapter 32
Auren wata ukku by sameena Chapter 32: Auren wata ukku by sameena Chapter 32. "Zan… zan jiraka a k'ofa ta fad'i tana mai tamke tufafin dake jikinta cikin…
1,264 words
"Zan… zan jiraka a k'ofa ta fad'i tana mai tamke tufafin dake jikinta cikin tsananin rawar murya. Kaman zata kifa haka ta fice tana had'e hanya. Haidar yabi bayanta da kallo murmushin da ba lallai ka fahimta ba saman fuskarsa.
Ummul kaw tana ficewa ta jingine jikin k'ofa tana maida numfashi.
A b'angaren su Mommy kuwa Asshe ta iso gari dan haka Kai tsaye ta taho asibitin yanda ta tadda 'Yaruwar tata.
Suna zaune saman wani kujera a wani hanya da zai sadaka da hanyar dakin Haidar d'in.
Asshe taci gaba "Aunty Kwaise yarinyar nan annoba ce.. Tsautsayi ke bibiyarta.. Ya kamata ayi gaggawan datse aurenta da Haidar… Allah na tuba bamusan dalilin da yasa boka yace mu aura masa mace irinta ba.."
Anisa da karyo kwananta kenan zata nufi d'akin Haidar ta sinkayi tattaunawar iyayen nata. Ta zaro ido waje tana dafe k'irji "Boka.!" Ta furta a hankali. Lokaci guda ta gyara tsayuwarta ta lab'e sosai.
Mommy ta girgiza Kai tana duban Asshe "A'a Asshe na yada batun boka tuntuni kuma na k'aryatasa kaman yanda Ayoyin Alk'ur'ani mai tsarki ya k'aryatasa a wajaje da dama. Asshe ba shakka munyi kuskure a yanda muka faro Auren Haidar da Ummul.. Amma na gode ma Allah da ya nufeni da tuba ya kuma bud'e min ido na na gane gaskiya dalilin shigowar Ummul cikin rayuwarmu. Sann inada yak'inin Auren Haidar da Ummul Alkhairi ne Asshe. Domin shigowar Ummul cikin ahalinmu shi ya fargar damu gaba d'aya.. Ita d'in ta zamto tamkar wani igiya mai k'arfi da ta had'e ahalinmu waje guda ta d'aure Asshe. She's an Element of Union.. Na shafe skaru sama da talatin ina fad'i tashi da ganin na had'e kan ahalina sai gashi cikin watanni biyu na zaman Ummul tareda mu Allah ya jefa wann had'uwan ahalin da soyayyar d'ana da mijina da nake buri. Kuma in sha Allah Ummul ko Haidar cikin su babu Wanda zai San ga Manufar aurensu daga farko. An Gina auren ne bisa sharad'in boka domin a raba Haidar da wancan Hatsabibiyar da tai masa sihiri Wanda a halin yanzu ma bana tunanin suna tare."
Anisa ta zaro ido waje tana Jin sirrin Auren Ummul da Haidar Wanda ba yanda batai ba Mahaifiyarta ta sanar da ita. Dama wann shine dalilin da yasa Kwaise Maitama ta auro ma D'anta D'iyar talakawa da taita mamaki daga farko.? Dama wann shine dalilin da yasa Mommy hak'uri da Ummul da nuna mata unconditional love.? Tirk'ashi Lallai yau akeyinta.
Mommy taci gaba "Asshe kimin alk'awari babu Wanda zai San wancan manufar tamu na farko domin na riga na bisne wancan manufar na lullubesa da tuba na gaskiya. Ummul da Haidar zasu rayu a k'ark'ashin inuwar aure tsawon rayuwarsu cikin yarda Ubangiji aure mai cikeda d'imbin albarka ba AUREN WATA UKU mai k'ayyadadden lokaci Wanda Boka mak'aryaci yaima Ummulkhair alk'awarin mutuwa ciki ba.!"
Anisa sai ta sake baki tana fito da ido waje.! Mutuwa..? Shiru tai tana sauraron yanda Mommy ke zayyano sharud'an boka gameda auren cikeda nadama. Anisa ta kasa rufe baki dan mamaki. Kenan An auro Ummul ne dan ta zamto makarin asirin da akai ma Haidar. Sai yanzu ta gane manufar turaren da Mommy ta bata ta bama Ummul. Sai wann lokacin take fahimtar komai.. So Mommy isn't as innocent as she thought.. So duk wann soyayyar da Mommy take ma Ummul na k'arya ne tana mata so ne out of guilt tinda ta kawo ta cikin rayuwar D'anta ne dan ta kasheta ta kuma ceci nata D'an. Muryar Mommy ya kuma dawo da Anisa daga duniyar tunanin da ta tafi.
Mommy ta kuma kamo hannayen Asshe "Asshe Alhamdulillah ahalina Ya fara daidaita cikin ikon Allah. Bazan kuma yin wani abu da zai tarwatsa min wann farin ciki da na jima ina fatan samu ba. Haidar da Ummul harma da Engr bazasu San ga manufar auren ba… Asshe idan suka sani ahalina zai kuma tarwatsewa Watak'ila yai rushewar da baiyi ba a baya… Kimin alk'awari kaman yanda muka shirya komai daga farko tare zamu bisne wann magana kuma bazamu sake d'agota ba har abada." Ta k'arashe tana duban Asshe.
Asshe Tai shiru tana duban 'yaruwar tata dan dik yanda Anisa ke sanar da ita irin makancewar da Mommy wajen nuna ma Ummul so bata kuma gaskatawa ba sai yanzu "Amma… Aunty Kwaise.."
"Babu amma Asshe. Inada yak'inin kafin a sallami Haidar daga asibitin nan shida Ummul zasu k'ulla alak'a mai kyau tsakaninsu.. Zasu k'aunaci juna a hankali. Domin da zaran an sallamesa ni Kwaise zan shirya gagarumin bikin na gaske. Za'ayi komai cikin mutunci da karramawa kaman yanda yake a al'ada. Za'a sallami Haidar ne tareda bikin tafiyarsa da matars in sha Allah. Ni da kaina zan tafi wajen dangin Ummul muyi masu gaisuwa a k'ulla alak'a da zumunci mai tsafta.." Ta k'arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta.
A hankali Anisa ta soma jada baya.. Shigowan da batai ba kenan ta soma tafiya jiri na neman kada ita.
Tana fita ta soma neman layin Hisham. Bugu biyu a na uku Ya d'aga.
"Tell me your location." Abinda kawai Anisa tace kenan…
Hisham na sanar da ita location d'insa tasa kai zata fice sai kuma taja birki ta tsaya kaman wacce ta tuna wani abu. Ji tai ta k'agu ta tunk'ari Haidar da Ummul ta sanar dasu irin Auren yaudara da Mommy ta k'ulla tsakaninsu.
A b'angaren su Ummul kuwa tana nan lamo jingine jikin k'ofan bathroom taji motsin tab'a k'ofan alamun zai fito. Tai k'ok'arin saita kanta tana mai taimaka masa da bud'e k'ofan.
Suka dubi juna sai ta kauda fuskarta kad'an. Gaba d'aya saima ta rasa mai zatai musamman da taga yanda yake dubanta daga nan yanda yake tsaye dafe da garu.
Baice da ita komai ba sai soma takowa da yai. Ta yunk'ura da zummar magana saiji Tai ya kuma kamo k'ugunta had'ida tallafo kafad'an ta guda. Sukai tsaye nan haka suna duban juna.
A haka Anisa ta turo k'ofa taci karo dasu rungume da juna suna duban juna ga jikkunansu duk a jik'e. Takaici yakai Anisa k'ololuwa. Banda sakin huci bata komai. Wai Haidar Maitama ne dai take gani rungume da wann kucakar harma kaman ya makance a shauk'in kallonta baisan an tab'a k'ofa ba balle Ya kula da Wanda Ya shigo. A zuciye Anisa ta janyo k'ofar ta fice, kukan da ta rasa na takaici ne ko na kishin Abun k'aunarta Haidar ne na kufce mata. Haka ta fice tana kuka shar shar take driving. Da alama duk wani effort dinta a banza yake tafiya dan duk k'ok'arin taga Haidar da Ummul basu samu kusanci ba kaman k'ara rura wutan abun take.
Koda ta isa location d'in Hisham bata daina kuka ba.
Hisham Ya tsareta sosai da ido had'ida bata lokaci dan ta fitar da k'uncin dake ranta. Ganin dai kukan Anisa bazai k'are ba dan tinda tazo yanda yake kul take ta kasa cewa komai.
Hisham yai tsaki kad'an "Ke enough please. Ya isa haka mana.! Wai meye kikazo kika saka ni gaba kina kuka.? Ok dama kin nemi sanin yanda nake ne kawai dan ki cika mun kunnuwa da sautin kukan ki. Ai da baki b'ata mana lokaci ba daga ni har Ke tinda idan kinyi a waya ma zanji."
Anisa ta d'ago tana huci "We can't let them be happy while we are stuck here just.. Freaking miserable you know..! Wllhi na tsani Ummul.. Na tsaneta.. Na tsani Mommy da taima Haidar AUREN WATA UKU.. Auren karya asiri da ita.. I hope she dies kaman yanda Boka yace.!"
Da mugun mamaki Hisham ke kallonta.. Ya girgiza Kai cikin rashin Fahimta "Mai kike nufi..?!"
SameenaAleeyou📚