Ba ni da gata - Chapter 1
Ba ni da gata Chapter 1: Ba ni da gata Chapter 1. πΌ πΉ πΉ πΌ πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ πΉ BA NI DA GATA*πΉ πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ πΌ. πΌ πΉ πΉ πΉ πΉ πΉ
3,659 words
πΌ πΉ πΉ πΌ πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ πΉ BA NI DA GATA*πΉ πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ πΌ. πΌ πΉ πΉ πΉ πΉ πΉ
*α΄α΄Ιͺα΄ Κα΄α΄α΄*
*STORY & WRITTEN BY* *ZULFA'U SA'EED IBRAHIM* ( *_MATAR SAYYADEE_*)
βοΈ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*βοΈ ( *Home of quality and trusted writer's of the nation*)πͺπ»
*πππππππππ ππ πππ ππππ πππππππ ππ πππππ ππ πππ πππππ πππππ (ππ ππππππ)*. *πππππ ππ πππ'ππ ππ ππ βπΈβπΈππΈ*
*___________________* *π½βπΌπΌ βπΈπΎπΌ 1&2* *___________________*
...........Garin ya yi luf-luf cike da ni'ima. Ga wani 'dan sanyi-sanyi da ke busowa gami da k'amshin k'asa sakamakon hadarin da ya ha'du sosai, ko wani irin lokaci ruwa zai iya tsugewa. Gefe guda kusa da wani tarin bola da ta yi tsini, wata kyakkyawar yarinya ce da bazata wuce ten years ba du'ke a wajan sai rawar d'ari ta ke yi sakamakon wannan hadari da ya taho da iska da kuma sanyin da ke biyo iskan. Gashi ba wani kayan arziki ba ne a jikin wannan yarinya da ko 'dan kwali babu a kanta sai uban tulun gashin da ya zubo har kafa'dunta. 'Yar 'karamar shimi (vest) ne a jikin ta, sai wani kod'ad'd'an wando da ya yayyage ta wajan d'uwawunta da kuma guiwar wandon. Shi kan shi wandon iya k'aurin ta ya tsaya. Ha'koranta har ha'duwa su ke da juna saboda tsabar sanyin da ta ke ji, gashi kuma da ma da d'an zazzab'i a jikin ta. Ruwa ne ya kece kamar da bakin kwarya. Cikin abunda bai fi minti 'daya ba wannan yarinya ta ji'ke sharkaf. Da gudu ta mi'ke ta yi bayan wannan tulin bolan da ke cikin wani rusassan kangon da kad'an ya ke jira ya gama zubewa sakamakon wannan uban bola da ake zubawa a wajan. Inda baiwar Allahn nan ta koma bai hana ruwa dukanta ba, domin babu wajan da za ta gujewa ruwan a wajan. Haka nan ta cigaba da tsugunno a wajan kusan kimanin awa biyu kamin ruwan nan ya tsagaita. A wannan lokacin kuwa har kakkafewa take yi saboda tsabar sanyi. Gashi magriba ta gabato. Ta na nan kwance a wajan ta soma jin takun tafiyan mutane ga dukkan alamu masallaci za su je. 'Dan le'ko da kanta ta yi ta wani 'dan huji ta na kallon mutanen da suke wucewa ta na addu'ar Allah ya sa ta ga Hamdan. Addu'an ta ya kar'bu, sai dai kash! tare su ke da ankul ( uncle) Saban (Sauban) kamar yadda ta ji Hamdan 'din na kiran shi. Ajiyar zuciya ta yi tare da komawa ta lafe a wajan kasancewar ta riga da ta ha'kura da abincin yau. Wasu siraran hawaye ne su ka Shiga zirarowa daga idanunta. Bayan hannunta ta saka ta share tare da fa'din, "Allah ni ba ka bani mama da baba ba kamar kowa. Ni bola ce ta haife ni. Kuma bola ba ta ba ni abinci mai kyau, ba ta kai ni makaranta, ba ta saya min kaya masu kyau, kuma bata wanke min jiki na. Mutane ba sa sona. To meyasa ni ma ban zama bola ba kamar yar da mama na ta ke? Mutane haka suke kira na 'yar bola, kuma wai *BA NI DA GATA*, Allah ni ma ka mayar da ni bola kamar yadda mamata take ni ma nai ta girma kamar ta. Kowa ba ya sona, Hadaan (Hamdan) ne kawai ke so na. Shike sammin abinci daga gidan su. Shi ya kawo min wannan kayan ma da ke jiki na. Allah ni ma ka mayar da ni bola kamar mama saboda mutane su dai na gudu na". Ta fa'di hakane ta na kuka, domin a nata wautan bolan da ke wajan ita ta haifeta, ita ce uwarta, ita ce ubanta. Saboda kuma jama'a na kiran ta *Y'AR BOLA* sai ta ke 'dauka ai bolan ce mahaifiyar ta. Ita kullum burinta, ta zama bola don ta yi magana da mahaifiyar ta suma su koma gidan su. Har an idar da sallah, kasancewar had'a sallah aka yi, tunda kowa ya shige gida sai garin yai tsit. Gashi dama ruwan ba d'aukewa ya yi gaba d'aya ba. Har yanzu ana yayyafi kuma alamar ruwan sake tsugewa zai yi. Don irin ruwan nan ne da ake kwana ana tsugashi. Tun ta na ri'ke ciki ta na kukan yunwa, har bacci yai gaba da ita anan wajan sauro na zu'kan jinin ta. Can cikin baccin ta taji ana dukan k'afafunta a hankali tare da kiran sunan ta, wanda Hamdan ne ya ra'da mata sunan wato binty (beauty). Beautyn ne ba ta iya kira ba ta ke cewa binty. A da idan wani ya tambaye ta miye sunanta, cewa ta ke yi *Y'AR BOLA* kamar yadda ta ji mutane su na fa'di. Idan aka ce mata *Y'AR BOLA* ba su na ba ne. Sai ta ce Binty (beauty) a hankali ku ma sunan na ta ya koma Binty, wasu kuma su ce Binty *Y'AR BOLA*. A hankali ta ke bu'de idanuwanta har ta bu'de shi tas a kansa. Duk da akwai duhu ta shaida shi, domin karfe tara ta wuce na dare. Hannu ta kai ta shafi fuskan shi tare da fa'din, "Hadaan (Hamdan), ina ta jiran ka yunwa na ke ji. Na gan ka za ka sallah kai da ankul Saban, har na cire rai zaka kawo min abinci". "Beauty ni ma hankalina na kan ki, ina ta so na fito, amma Mummy ta ki barin sitting room balle in samu in fito in kawo miki food ki ci, now wash your hands with this detergent and water before eaten, it's a very good hygiene. Understand?". Fa'din wani kyakkyawan farin yaro da ba zai wuce 13years ba. Ita dai Binty (Beauty) ba ta san mai ya ke cewa ba, 'ko'karin ta kawai ta 'karbi take awayn dake hannun sa. Shikuma yak'i ba ta wannan damar. "Hey! Easy mana beauty. Zan ba ki, amma firstly sai kin fara wanke hannun ki saboda gudun cuta. Our teacher always tells us to wash our hands before and after every meal. Saboda haka, ga ruwa da detergent nan, ki wanke hannun ki sai in baki Irish and plantain 'din ki ci". Ya fa'di hakane tare da jawo hannun ta ya zazzaga mata detergent 'din tare da ruwa. Sai da ya sata ta wanke hannun sau bakwai, ka na ya mi'ka mata takeaway 'din tare da fork na roba. Cikin sauri ta kar'ba ta soma cikin. Shida-shida ta ke ta ha'dawa har ta cinye tas. Ka na ta yar da cokalin tare da saka hannu ta su'de robar tas, sannan ta yar tare da sakin k'atuwar gyasa ta koma ta kwanta a nan 'kasan wajan ta na mayar da numfashi. "Imaging! How can a human being live and survive here, Allah na gode maka da ni'imar da kai min". Hamdan ya fa'di hakan ya na mai 'karewa beauty kallo cike da tausayi da har bacci ya soma 'daukar. "She's very beautiful with long hair. Who must be her parent? Why is she all alone in this garbage? Da ni babba ne da na ne mo mata iyayan ta ita ma ta rayu da su kamar ni da Mummy da Appa". Hamdan ya sake fad'i ya na shafa dogon gashin da ke kanta da ya yi dak'an-dak'an har cukurku'dewa ya yi ya na so ya koma dada. Ganin da yai ta yi bacci sosai, sai ya fiddo bedsheet a cikin ledan da ya zo da shi ya rufa mata tare da kunna mata maganin sauro da lighter, duk da yasan babu abunda maganin zai kare mata, don ko kamfanin *SUPER KILL* aka saka a wajan ba zai hana sauro cizon ta ba. Don sauran zamanin yanzu, ka na jan bargo suna ja.π€£π€£ Kamar zai yi hawaye ya mi'ke tare da barin wajan ya lallab'a ya tura get ya shiga gidan da san'da har ya shige 'dakin sa tare da hawa gado ka na ya saki ajiyar zuciya tare da fa'din, "Thank God, nobody saw me".
*ππΈπβπΈ πΎπΈβπ* Sai da rana ta fito sannan Binty ta farka tare da sakin mi'ka gami da doguwar hamma. Gashin da ya barbazo ya rufe mata fuska ta mayar da shi baya tare da janye zanin gadon da Hamdan ya lullub'eta da shi ka na ta mi'ke tsaye. Idanuwan ta ne ya sauka akan pure wata guda uku da brush da maclean a kan wani bulo. Wajan ta nufa domin ta san Hamdan ne ya aje mata su a wajan, domin ya ce a kullum ta tashi da safe ta ri'ka alwala tare da wanke bakin ta da brush, don har koya mata yadda ake brush 'din sai da ya yi. Brush 'din ta fara yi ka na ta yi alwala ko in ce shirme. Domin ko alwalar ba ta iya ba, balle a kai ga zancan sallah. Bayan ta gama alwalar da brush 'din, ta zo ta hau kan wannan zanin gadon ta soma sallah haka nan ko 'dan kwali babu a kan ta sai buyagin gashin ta. Dunguran-dunguran banza tai ta yi. Domin sallar daga sujada aka fara, sannan aka d'ago a kai ruku'u ka na aka k'ara tafiya sujada. Haka tai ta dungurawa har ta kammala kusan raka'a goma. Fitowa tai tare da hawa kan bolan nan tare da fa'din, "To mama, zan tafi in nai mi abincin da zan 'karya da shi tunda dai bakya sona. Na san Hadaan ya tafi makaranta, ankul Saban ba zai barshi ya kawo min abinci ba. Zan je na nai mo da kai na". Ta na gama fa'din haka ta soma saukowa daga can saman bolan. Kallon gyefan daman ta ta yi, idanuwan ta suka sauka akan wani tsoho tukuf, gashin sa fari fat har kafa'da, hannun shi ri'ke da sandar da ya ke dogarawa, ya na mata murmushi. Cikin sauri da wani irin zumu'di ta 'karisa wajan shi tare da fa'dawa jikin sa ta ruk'unk'ume shi tare da fa'din, "Kaka!" Sai kuma ta fashe da kuka tare da 'kara rungume shi. Shafa kanta wannan tsohon ya yi yana murmushi tare da fa'din, "Haba Bintyn Hadaan! Mi ye na kukan? Ba ga ni na dawo ba". "Guduwa zakayi ka sake bari na a nan, babu wanda ke sona. Yara su na tsokana ta, ba na samun abinci, Hadaan ya je makaranta. Yanzu ma ban karya ba". Fa'din Binty. "Ki yi ha'kuri Binty, ko mai ya yi tsanani ya na tare da sau'ki. Wannan waje da ki ke, shine kad'ai mafita a gare ki. Yanzu duk bayanin da zan miki, ba za ki ta'ba ganewa ba don kwakwalwar ki ba za ta 'dauka ba. Amma ki yi hak'uri. Ina mai tabbatar miki maki'yan ki sai sun rusuna a gaban ki. Sai kin zama filita mai haskakawa. Ki yi hak'uri ki daure ki ci jarabawar ki. Tun da har Allah ya raya ki a cikin bola tun ki na 'kan'kanuwar ki har izuwa yanzu, to lallai Allah ya na so ya nunawa magauta ishara da Isar sa ne. Lallai ubangiji shine ke rayawa da kashewa". Sam Binty ba ta fahimci ko kalma 'daya daga cikin maganganun kakan na ta ba. Sai ma jefa masa tambaya da ta yi. "Kaka yaushe zan zama bola irin mamana kowa ya dai na tsana ta?". Murmushi wannan tsoho ya yi tare da fa'din "Binty na, ba za ki zama bola ba, sai dai in sha Allah za ki zama abun kwatance a cikin al'umma, tabbas sai ma'kiyan ki sun duk'a a gaban ki. Tabbas idan rana ta fito tafin hannu ba zai ta'ba iya kare ta ba Binty na". "To kaka yaushe ne ranar zata fito? Kuma yaushe ne zan zama abun kwatance?". Binty ta kuma jefa masa tambaya. "Ranar na nan zuwa Binty na. Ki je Allah ya albarkaci rayuwar ki. So na ke ki yi gwagwarmaya, ta yadda nan gaba ko mai zai zo miki da sau'ki". Fa'din Kaka. "To kaka, bari na je na yi bara na samu abinci yunwa na ke ji". "To Binty na, Allah ya sa a da ce". Ya na gama fa'din haka Binty ta bar jikin shi tare da gangarowa daga kan bolan. Sai da ta sauko gaba 'daya ta 'daga kanta sama, wayam ta ga ni a wajan. Ko alamar kaka ba ta gani ba. Murmushi ta yi tare da fa'din, "Kaka ya 'kara guduwa ya bar ni".
*ASSALAMU ALAIKUM READERS, GA NI NA ZO MA KU DA SABON LITTAFI NA MAI SUNA A SAMA, WANDA YA ZO DA ZAFI-ZAFIN SA, KUMA NA TABBATA ZA KU JI DAD'IN SA. BA ZAN CI KA KU DA SURUTU BA, KAWAI KU BI NI A FREE PAGES, KU DA KAN KU ZA KU GA NE BOOK D'IN NA DABAN NE. KAWAI KU NU NA MIN ONE LOVE WAJAN SIYAN BOOK D'IN AKAN FARASHI AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA:*
*Normal group shine mutum zai bi ya 500 idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300.*
*VIP kuma 1000 ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700.*
*MUTANAN NIGER KUMA ZA SU BI YA KAMAR HAKA*:
*Normal group shine mutum zai bi ya 500F idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300F.*
*VIP kuma 1000F ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700F.*
*Κα΄ΚΙͺΚα΄α΄Ιͺα΄κ± α΄ α΄Ι΄ Ι’ΙͺΚα΄α΄Ι΄ α΄ΚΚα΄Κ α΄α΄ Ι΄α΄ Ι΄α΄ α΄ΙͺΙ΄ Κα΄α΄ α΄ α΄‘α΄α΄α΄Ι΄ κ±Κα΄ΚΙͺΙ΄Ι’* πΌ πΉ πΉ πΌ πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ πΉ*BA NI DA GATA*πΉ πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ πΌ. πΌ πΉ πΉ πΉ πΉ πΉ
*α΄α΄Ιͺα΄ Κα΄α΄α΄*
*STORY & WRITTEN BY* *ZULFA'U SA'EED IBRAHIM* ( *_MATAR SAYYADEE_*)
βοΈ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*βοΈπͺ ( *Home of quality and trusted writer's of the nation*)πͺπ»
*DEDICATED TO THE MOST BEAUTIFUL WOMAN IN THE WHOLE WORLD (MY MOTHER). ALLAH YA JIK'AN KI DA βπΈβπΈππΈ*
*________________* *FREE PAGE 3&4* *________________*
.............Juyawa ta yi ta soma tafiya ta na 'dan tsalle-tsalle gashin kanta na sama na 'kasa. Wasu 'dandazon almajirai ta gani sun yi layi suna karb'an sadaka. K'arasa ta yi ita ma tai layin. Sun rage saura su hu'du, abun sadakar ya k'are. B'ata fuska ta yi ta na kallon sauran ukun da su ma ba su samu sadakar ba. D'aya daga cikin su mai dogon goshi ya kwad'a mata d'an chinan hannun sa tare da fa'din, "Shegiya y'ar bola mai bak'in jini. Ke ce kika sa ba mu samu sadaka ba. Bar nan ko in zane ki". Yaron ya fa'da tare da yo wa kan ta kamar zai mazge ta. Da sauri Binty ta ja baya tare da barin wajan. Idan da sabo Binty ta saba da hantarar mutane. Wajan wani mai shayi ta 'karisa tare da rakub'ewa ta na kallon jama'ar da ke wajan su na shan shayi. Wani 'dan tsamurarran gaye ne ya kai shayi bakinsa idanuwan sa suka sauka akan Binty dak'an-dak'an ta na had'iyar yawu. Aiko ya fesar da shayin bakinsa tare da fa'din, "D'an Liti wannan wani irin iskanci ne za ka ri'ka bari irin wad'annan yaran suna tsayawa gaban mutane idan su na cin abinci. Wannan ai iskanci ne. Yanzu haka ji na ke kamar na amayar da hanjin ciki na wallahi". D'an Litin ne ya zagayo tare da kama kunnan Binty ya murd'a da k'arfi tare da fad'in, "Dan iyayan ki mata ba na hanaki zuwa wajan nan ba. Shegiya yarinyar kawai mai d'an banzan nacin tsiya. Ni anya ma yarinyar nan ba aljana ba ce? Shegiyar yarinya tun ta na da shekara uku ta ke rayuwa ita kad'ai a saman bola kuma ta rayu har izuwa yanzu. Ni wallahi tsoro ma ta ke ba ni yarinyar. Sai shegen kyau kamar ita tai kanta". "Kai kuwa d'an Liti ai Allah shi ke rayawa kuma shi ke kashewa. Ba abun mamaki ba ne dan ta rayu ita kad'ai a saman bola. Kai dai idan zaka taimaketa ka ba ta buredi da shayi ka ba ta, ba ka tsaya kana wani surutan banza a wajan ba". Fa'din wani mutum da ke cin taliyar 'yan yara (Indomie). "To bazan ba da ba. Idan kuma kai ka basheni jalin, sai ka d'iba ka bata". Fa'din D'an Liti. "Yo to ai abunda za ka ce kenan. Ke yarinya zo ungo wannan sauran taliyar ki cinye duk da dai kad'an ya rage". Fa'din mutumin nan. "Idan wanga d'iya ta ci taliyar nan a cikin robata Allah gwada maka yai. Sai dai ka juye mata a cikin leda". Fa'din d'an Liti. "Haka ka ce d'an Liti?". Fa'din bawan Allah nan. "Awo wallah". D'an Liti ya fa'da ya na buga cinya irin na y'an daudu. Girgiza kai bawan Allah ya yi tare da d'aukar ledar da aka b'are indomie ya juye mata a ciki tare da mik'a mata. Da uban sauri Binty ta karb'i ledan. Nan wajan a tsaye tai loma biyu ta cinye tass tare da zubawa wannan bawan Allah idanu alamar nai man k'ari. Da gudu 'dan Liti ya biyo ta tare da fa'din, "Bar nan ko in halako ki walleh". Gudu ta yi sosai, duk da D'an Liti ya dai na bin ta ba ta zai na gudu ba. Sai da ta ga ta yi nisa sosai sannan ta tsaya ta na mai da numfashi. Haka tai ta gararanba a cikin anguwanni. Duk in da ta je kyamatar ta ake yi. Musamman wajan ma su sai da abinci. Idan Allah ya ba ta sa'a wani ya ci ya rage tai wuf da shi ta cinye. Idan kuma aka kamata ta sha kirb'a. Haka tai ta yawo ga rana kuma ba takalmi da d'ankwali a kan ta. Hatta kayan da ke jikin ta ma ba na kirki ba ne. Sai da rana ta fa'di ka na Binty ta dawo wajan bolan nan ta zauna ta na sauke numfashi. Bakin ta duk ya bushe. Sosai ta ke jin k'ishirwan ruwa. Kallon himilin bolan nan ta yi tare da fad'in, "Mama yau ban samu abinci sosai ba. Yunwa na ke ji. Ina jin k'ishi sosai". Daga bayan ta taji an saka hannu an rufe mata idanu. Wani farin ciki ne ya lullub'e ta tare da fad'in, "Hadaan, kai ne ko? Nasan kai ne. Ai kai kad'ai ne kawai ke zuwa waje na". Zagayowa yai ta tare da fad'in, "Yau ma kin je yawo ko? Ai tun d'azu na ke ta nai man ki, na kawo miki abinci ki ci ban gan ki ba na bawa kare ya cinye". Kwal-kwal ta yi da idanu tare da fad'in, "Hadaan yunwa na ke ji, dan Allah ka ba ni abinci, yau na yi bara ban sa mu ba. Ina jin k'ishi sosai zan mutu". Sosai tausayin ta ya kamashi, ji ya ke dama zai iya convincing mummy ta yadda Beauty ta dawo gidan su da zama. Amma ya san ko mutuwa zai yi hakan ba zai faru ba. Juyawa ya yi tare da d'auko wani d'an basket da ya zo da shi sai ya boye a bayan wani bulo tare da ajewa a tsakiyar ta. Cikin sauri ta soma kiciniyar bu'de abunda ke cikin basket 'din. Rik'e hannun ta ya yi tare da girgiza kan sa ya na fad'in, "You've already know the rules. Wash your hands before eating". A cikin maganganun sa, kalmar wash kawai ta rik'e, shiyasa da ya yi dogon turancin sa idan ta ji the word `wash` ta san mai ya ke nufi. Wato ta wanke hannun ta. Mi'ka masa hannuwan ta yi alamar ya zuba mata abunda ya saba zuba matan idan zata wanke hannunta. Zazzaga mata detergent ya yi tare da ruwa sannan ta soma mitstsike hannun. Sai da ta wanke sau goma. Har ta k'osa ka na ya fiddo plate tare da bu'de kula ya zuba mata lafiyayyan fried rice da ya ji kayan lambu ga mi da hanta. Aikuwa ko kallon cokalin da ya ke mik'a mata ba tai ba ta zunduma hannu ta soma ci. Kasancewar shi ko da cokali za ta ci abinci ba ruwan shi sai ta wanke hannun ta. Cikin abunda bai fi mintuna uku ba har ta lamushe ta na kuma buk'atar k'ari. Sauran na cikin kulan ya juye mata tare da cinyar kaza da baya. Aikuwa ta cinye tas har da tauna k'ashi murus ta kuma d'ad'd'ake goran ruwan faro ta saki gyatsa tare da jingina da bangon kangon ta na mayar da numfashi. Shikuwa Hamdam tun ya na jin mamakin irin cin abincin da Binty ke yi har ya dai na. Don shi ko kashe shi za'ayi ba zai iya cin ko kwata ba. Wani wawan mari yaji an sauke masa a kan fuskan sa wanda k'arar marin ya saka Binty firgita daga baccin da ya soma d'aukar ta. Don ita haka take da cikin ta ya d'auka za ta soma gyangyad'i. "D'an uban baban ka ba na hanaka zuwa wajan nan ba? D'an iskan yaro ya na so ya jawo mana fitina. Wani d'an iskan ne ka ga ya na zuwa inda ta ke idan ba kai ba. To yau sai na ci uban ka, kuma wallahi dole ba bi su kulsum ku wuce Abuja. Bazan iya da iskancin ka ba. Ke kuma idan ma wani abun ki ka wa d'ana aniyar ki ta bi ki, ba bu abunda zan miki balle anjima da daddare a turo min bak'ak'en aljanu su ga baya na. D'ana kuma daga yau ba za ki k'ara ganin sa ba. Shegiya". Hajiya Saratu mahaifiyar Hamdan ke fad'in haka tare da jan hannunsa, 'dayan hannun ta kuma na kan hancin ta. Uncle Sauban da ke can gyefe tsaye sai aikawa Binty da harara ya ke yi. Shi kuwa Hamdan sai ihu ya ke ya na fad'in shi bazai koma abuja ba. Daga nan wajan bolan mota aka jefa Hamdan 'din, dama already an saka kayan sa cikin mota. Binty fitowa tai da gudu ta na kallon abunda ke faruwa ta na kuka. Ta na hango Hamdan daga cikin mota ya na dukan glass ya na kallon ta ya na hawaye. Da gudu ta shiga bin motar ta na kuka ta na 'daga masa hannu, shi ma kuma ya na kallonta ta glass 'din baya yana mata waving. Ba ta dai na bin motar da gudu ba sai da motar ya b'ace mata da gani. Haka ta dawo cikin kangon bolan nan ta na kuka sosai.