Ba ni da gata - Chapter 2
Ba ni da gata Chapter 2: Ba ni da gata Chapter 2. *ᗩᗷᑌᒍᗩ*
2,860 words
*ᗩᗷᑌᒍᗩ*
Wata kyakkyawar yarinya ce da ba za ta wuce ten years ba, sanye da wando pencil sai wata riga mai matu'kar kyau iya guiwarta. Gashinta tai parking d'in shi a tsakiyar kan ta wanda ya kasance jajaja, maroon-maroon. Kyakkyawa ce sosai kuma fara ce. Fuskan nan na ta ya ci make-up kamar wata babbar budurwa. Hannun ta kuwa tasha zanan lalli. Kallon wata kyakkyar mace ta yi da ke zaune akan 1sitter ta na yanke farcenta. Kallon ta yi ta re da fa'din, "First love ya ki na ganin?". Wacce ta kira da first love 'din ko kallon ta ba ta yi ba, a yadda kanta ke k'asa ta ce, "Looking good!". Sautin kuka yarinyar ta ji ya kara'de d'akin. Cikin sauri matar ta d'ago ta kalle ta tare da fad'in, "Sabrin mai ya same ki?". Sosai Sabrin ke kuka tare da fad'in, "Mom ko kallo na fa ba ki yi ba balle ki ce na yi kyau kuma na fi kowacce mace kyau a duniyar nan. Sai cewa kawai ki ka yi Wai looking good". Baki bu'de Hajiya Sakna ke kallon autar tata tare da fad'in, "Me ke damun ki ne Sabrin? Ta yaya zan miki k'arya in ce kin fi kowace mace kyau a duniya. Ke ma kin san k'arya ki ke yi. Ki na da kyau Sabrin sosai, amma ba ki fi kowa kyau ba. Akwai wanda su ka fiki sosai". "No way! Everyone in school said that I'm the Queen of the country. We have wealth, Education, beauty and rest. And I am also the Queen of our school. Duk makarantar mu ba bu Wanda ya kai ni kyau, duk ajin mu na fi kowa k'ok'ari. Daddy na ya fi daddyn kowa kud'i a makarantar. Ba na son kowa ya fi ni, ina so in ga na iya komai ta yadda babu kamar ni in the whole world". "Sabrin, whole word?". Mom ta fa'da cike da tashin hankali da mamaki. Domin kuwa sosai halin Sabrin ke ba ta tsoro. Ta na da wani irn kishi da ya wuce misali. Ita burinta ta kasance ta fi kowa, babu Wanda zai fita. Idan kuwa ko cikin k'awayanta ta ga wa ta ta fi ta da wani abu, to fa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya k'are har sai ta fi wannan da ta fita za ta sa mu natsuwa. Sosai Sabrin ke da mugun hali. Hatta mom d'in ta kishi ta ke da ita. Ko wani abu daddyn ta ya siyawa mom in dai ya fi abubda aka sai mata to babu zaman lafiya sai ita ma an sayo mata. Kuma daddyn ta ya d'aure mata gindi wanda hakan na matu'kar k'ona ran mom don ta tabbata idan Sabrin ta ta shi da wannan halin zata sha wuya a rayuwa don gidan wani zata. "Of course mom. Babu wanda zai fi ni a cikin duniyar na. Ko mai nawa ne ni kad'ai. Nagode miki da kika haife ni mai kyau.". Mom ta kasa cewa komai, don har ga Allah sosai lamarin Sabrin ke ba ta tsoro. Juyawa Sabrin 'din ta yi tare da fad'in bari na je side d'in aunty, nasan ita za ta min maganar da zan ji da'di. Ta fi ki sona". Ta na gama fad'in haka tai side 'din kishiyar mahaifiyar ta da ke k'ara dulmiyar da ita.
*ASSALAMU ALAIKUM READERS, GA NI NA ZO MA KU DA SABON LITTAFI NA MAI SUNA A SAMA, WANDA YA ZO DA ZAFI-ZAFIN SA, KUMA NA TABBATA ZA KU JI DAD'IN SA. BA ZAN CI KA KU DA SURUTU BA, KAWAI KU BI NI A FREE PAGES, KU DA KAN KU ZA KU GA NE BOOK D'IN NA DABAN NE. KAWAI KU NU NA MIN ONE LOVE WAJAN SIYAN BOOK D'IN AKAN FARASHI AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA:*
*Normal group shine mutum zai bi ya 500 idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300.*
*VIP kuma 1000 ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700.*
*MUTANAN NIGER KUMA ZA SU BI YA KAMAR HAKA*:
*Normal group shine mutum zai bi ya 500F idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300F.*
*VIP kuma 1000F ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700F.* *ʜᴀʙɪʙᴀᴛɪᴇꜱ ᴅᴀɴ ɢɪʀᴍᴀɴ ᴀʟʟᴀʜ ᴋᴜ ɴᴜ ɴᴀ ᴍɪɴ ʟᴏᴠᴇ ᴡᴀᴊᴀɴ ꜱʜᴀʀɪɴɢ* 🌼 🌹 🌹 🌼 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BA NI DA GATA*🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌼. 🌼 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹
*ᴘᴀɪᴅ ʙᴏᴏᴋ*
*NARRATED & WRITTEN BY* *ZULFA'U SA'EED IBRAHIM* ( *_MATAR SAYYADEE_*)
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*☀️💪 ( *Home of quality and trusted writer's of the nation*)💪🏻
*DEDICATED TO THE MOST BEAUTIFUL WOMAN IN THE WHOLE WORLD (MY MOTHER). ALLAH YA JIK'AN KI DA ℝ𝔸ℍ𝔸𝕄𝔸*
*________________* *FREE PAGE 5&6* *________________*
.............."Ohhh my gosh! Queen kin ganki kuwa? Looking more and more beautiful dear. Wa ne Barbie. Ai ko ita ta gan ki sai 'kishi ya kama ta. Daughter zan fa ci kud'i a nan. Gaskiya wanda za ki aura sai ya kasance classic guy ne. Irin kyakkyawan nan, mai kud'i na nunawa sa'a. Amma fa duk kyan shi ba zai kai ki had'uwa ba domin daga ke aka rufe babin kyawawan mata". Fa'din aunty Junaina, kishiya a wajan mahaifiyar Sabrin. Da ita da Alhaji Saifullahi su ne musabbabin k'ara tab'arb'arewar Sabrin d'in. Domin duk abunda ta yi nuna mata suke ta na kan gaskiya. Rungumeta Sabrin ta yi tare da fad'in, "Ohh sweet aunty. That why I love you soon much. Dan Allah aunty kullum ki ri'ka fad'amin irin wannan maganar. Allah ji na ke kai na na k'ara girma". "Do you know what dear? I'm not saying all this to impress you, I'm saying the fact. You're soo adorable my Queen". Wani irin duk'awa Sabrin ta yi tare da kamo hannun aunty Junainan irin yadda akewa princess ko Queen idan ana son rawa da su. Ta ce, "I love you soo much my aunty. Me kike so in yi miki?". "Abu d'aya kawai na ke so ki yi min. Kawai ki yi ta kyau ki na k'ara kyau a cikin kyau". Fad'in aunty Junaina. "Ohhh ba ki da wannan matsalar. Yau na ji gidan shuru, ina sauran y'an matan gidan su ke?". Sosai dariya ya kusa kufcewa aunty Junainan. Wai y'an mata. Duk sa'o'in ta ne y'an shekaru goma. Aunty Junaina na da 'yan mata guda biyu Wanda su ka kasance 'yan biyu kuma lokaci guda aka haife su da Sabrin, sai dai ta girme su da sati biyu. Wannan dalilin ne ya sa ta ke d'aga masu kai. A cewar ta, ta fisu kyau da komai ma. Kamar yadda ta ke auta, suma autan ne a wajan aunty Junaina. "Sun je wanke kai kin san gobe Monday". Fa'din aunty Junaina. Ta'be ba ki ta yi tare da fa'din, "Ni ba ko wa ni beauty saloon na ke zuwa ba. Sai after zuhur prayer zan sa driver ya kai ni. Don ba ni son rana". Yadda Sabrin ta ke wasu manyancan, wallahi za ka d'auka wata k'atuwar budurwa ce.
*BINTY* Gaba 'daya duniyar ji ta ke tai mata zafi. Ko kyankyaso ta ga ni ya wuce, sai ta ce dama Allah ya mai da ni kyankyaso in huta. Ranar da daddare ko nai man abinci ba tai ba. Ita ce har sha biyu idanunta biyu ta kasa bacci. Wasu samari ne guda biyu a bige su ka zo wucewa ta wannan bolar da ko da kud'i aka had'a ka bazaka zauna a wajan da rana ba balle da daddare. Haskata su kai da torch light. D'ayan da bai bugu sosai ba ya ta'ba d'an uwansa tare da fa'din, "Babaa! Ni fa wancan yarinyar da ke rayuwar bolan can zan rufar mata in rage yawa. Dan naga ehh, ba yawa ta na da garin jiki, zan yi maleji a hakan. Dan ka fa san ehhh, kwana biyu Safara yawa ta ke min don ban da kud'i. Kawai dan rannan na d'an yi ehhh, ban ba ta ko sisi ba shine ta dai na duba min. Kawai zan farwa yarinyar can in rage yawa. Ni wallahi babaa idan har tai min ma zan iya d'auke ta in raine ta tunda dai ba ta da ehhh, ina nufin iyaye". Ya na maganar ne irin yadda y'an daba su ke yi d'in nan. "Sata kawai babaa, zan jira ka a nan. Idan ka gama kai min fito ni ma inzo inyi ehhh, irin in samu nawa share d'in nan". "Ba ka da case ba ri na je". Ya na gama fad'in haka yai wajan kangon da Binty ta ke. Ita kuwa Binty ta kasa bacci, ta na nan zaune ta ha'da kai da guiwa ta na kuka. Sai ji muryan mutum a tsawace tai a kan ta ya ce, "Ke mik'e!". Sosai ta firgita tare da mik'ewa ta na raba idanuwa. Shikuwa d'an iskan sai lashe baki ya ke yi kamar yaga cikakkiyar budurwa. Hannu ya kai ya fincikota tare da matseta a jikinsa sosai. Ita kuma Binty duk ta gama rikicewa jikinta sai rawa ya ke yi. Wannan ce rana ta farko da wani namiji ya mata haka idan aka cire kaka. Matsar da ita gyefe ya yi tare zuge zip 'din wandon sa ya sauka a kan k'afafunsa. "Ke dan uban ki kama min nan. Matsa min maza ko in yanka wuyarki ki mutu, da safe sai dai aga gawarki". 'Dan iskan nan ya fad'a. Ita kuwa Binty ta k'i yin yadda ya ce sai gwalalo idanuwa ta ke yi a cikin duhu. Ji ya yi an cafke masa mazantakarsa da k'arfi kamar za'a cire. Wani irin ihu ya yi tare da fad'in, "Ke dan uwar uban ki ba da k'arfi ba a hankali za ki yi. Sa ke min abu na ko in ci uwarki ana wajan". Ya fad'a cike da wahala don har ya soma hawaye. Ita kuwa Binty da ke gaban shi a tsaye sai mamaki ya kama ta. Don ita dai ta san ba ta kama masa komai ba amma yake ta ihu wai ta sakar masa abunsa. Ko mi ye abun nasa oho". Wani gigitaccan mari yaji an sakar masa hagu da dama a fuskar sa wanda ya saka sai da ya yi k'undun bala akan bolan da ke zubowa k'asa. A matu'kar hargitse ya mik'e ya na waige-waige. Binty dai na nan tsaye ko motsawa ba ta yi ba. Tu ni tsoro ya dabaibaye shi, hankalin shi ya ta shi. Wani duka yaji an kai masa a k'eyarsa sai da ya yi taga taga zai fa'di. Saurin juyawa yai bai ga kowa ba. Can kuma sai ya soma jin k'arar kofato ya na yowa in da ya ke a tsaye. Ai bai san sadda ya cire wadon da ya ke hard'e shi a k'afa ba, ga shi ko boxer ba mu a jikinsa, yai wurgi da shi ya soma gudu ya na fad'in, "Marados ka gudu wallahi mun shigo sansanin aljanai. Wallahi maganar da mutane su ke fad'i akan yar bolan ce gaskiya ne. Tabbas aljana ce. Ka gudu ka ceci kan ka". Ya na fa'din haka ne ya na falla gudu gashi babu wando Allah ya so shi dare ne. Shi kuwa wanda a ka kira Marados da ya soma 'dan gyangyad'awa a firgice ya mik'e shi ma ya shiga gudu. Gaba d'ayan su kuma su na jin takun kofaton nan kamar ana tseran doki. Marados ne yaji an d'aga shi cak, aikuwa ya shiga sakin fitsari tare da fad'in "Wa innahu min sulaiman, wa'innahu bismillahi rahmanir rahim. Ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba. Bawan Allah aljani, dan rahamar ubangiji kai min rai. Wallahi ko ta layin nan idan na k'ara bi ka kashe ni. Dan girman Allah yallab'ai aljani". Shikuwa d'ayan da akai nasarar cafko shi, zawo ya yi ta saki kamar farar kura. Daga sama suka ji an ha'dasu waje d'aya ka na aka sake su timmm a k'asa. Sannan su ka ji wata murya abun tsoratarwa ya na fad'in, "Duk ranar da na sake ganin ku wajan bolan nan, kashe ku zan yi. Kuma ko ba binty ba, ku ka k'ara k'ok'arin yi wa wata yarinyar fyad'e to sai na kashe ku. Daga yau na fara bibiyar al'amuran ku kenan. Ku bar nan ko kuma in yanke mazantakar ku". Ai a sittin suka arce. Ba su suka tsaya ba sai da su ka isa rumfar fale falen da su ke kwana su na ta sakin ajiyar zuciya.
*ᴡᴀꜱʜᴀ ɢᴀʀɪ* Binty haka ta ta shi sukuku. Gaba d'aya kewar Hadaan ta ke yi. Musamman da ba ta ga pure water da MacLean da brush d'in da ya saba ajiye mata ba. Hawaye ta ji su na sauko mata daga idanunta. "Kaka, ka na ina". Binty ta fa'da can cikin zuciyar ta. Mi'kewa ta yi ta haye can saman bolan. Bolan na da tsini sosai, domin bene ya yi, amma sam bai mata wuyan hawa. Sai da ta kai k'arshe ka na ta duk'a a kan gwiwowinta ta na hawaye ta re da fad'in, "Ni ma zan tafi wata duniyar daban ba nan ba. Babu abunda na ke samu a nan. Nan ba duniya ta ba ce. Wanda ya ke so na d'in ma ya tafi ya barni. Ni ma zan tafi. Ba zan sake dawowa ba. Idan kin ki kewa ta ki ne me ni a wata bolar na wani duniya da ban". Binty na kuka ta ke fad'in hakan. Mik'ewa ta yi tare da soma saukowa. Sai da ta sauko gaba d'aya ka na ta d'aga kanta ta kalli bolan ko za ta ga kaka, sai dai wayam babu kowa a wajan. Share hawayanta ta yi ta soma tafiya ta na waigen bolan. Tafiya ta yi mai tsayi har ta shigo wani unguwa. Unguwan tsit ya ke, irin unguwan nin masu kud'in nan. Zama ta yi a dandamalin wani tanfatsetsan gida tare da tsinko wasu furannin da aka shuka a k'ofar gidan ta na gutsirawa tare da jefawa a cikin kwata. Wata jibgegiyar mota ce tai parking dab da gidan. Wani jibgegen mutum ne a cikin motar. Tumbinsa har tab'a steering ya ke yi. Bak'i ne sosai har wani shinning ya ke yi. Akwai hak'orin maka golden colour a bakin sa. Wayar sa da ke ringing ya 'dauka a gefan sa tare da kara wayar a kunnensa. Ka min yai magana Wanda ya kira shin ya soma fad'in, "Sammani ka na wasa da k'ungiya wallahi. Saboda kai sabon shiga ne shi ya sa har su ke d'aga maka k'afa. Yau kimanin shekaru biyu ke nan ana fama da kai ka samo yarinya yar shekaru goma ka sadaukar da budurcinta da jininta wa dodon tsafi amma sai wasa da hankalin su ka ke. To ka bud'e kunnan ka ka ji da kyau. Saboda yadda mu ke da kai ne shi ya sa ma zan fad'a maka. Wallahi kwana uku aka ba ka idan baka kawo abunda aka buk'ace ka da shi ba, Durdus da kan shi zai aika Dobak'o ya d'auko masa matarka da babban d'anka a yanka su a kuma shanye jinin su a gaban ka kuma harda kai, idan kuma kak'i sha kai ma a sha jinin ka. Saboda haka ya rage gareka. Kuma ka da ka manta akwai meeting yau k'arfe biyu zuwa asuba, ka da ka sake kai fashi. Don Durdus na nan ya na k'irga fashin ka". Kamin sammani yai magana idanuwansa su ka sauka akan Binty da ke wasa da flower. Wani farin cikin ne ya lullub'eshi tare da fad'in, "Mai nasara yau zan kawo yarinyar nan ba sai jibi ba. Yanzu haka ma ga ta a gaba na". "Na ta ya ka murna. Kuma ka rufawa kan ka asiri". Fad'in Mai nasara tare da yanke waya. Shikuwa Alhaji Sammani bud'e murfin mota ya yi tare da fitowa ya nufi in da Binty ta ke a zaune.
*𝘼𝙎𝙎𝘼𝙇𝘼𝙈𝙐 𝘼𝙇𝘼𝙄𝙆𝙐𝙈 𝙍𝙀𝘼𝘿𝙀𝙍S, 𝙂𝘼 𝙉𝙄 𝙉𝘼 𝙕𝙊 𝙈𝘼 𝙆𝙐 𝘿𝘼 𝙎𝘼𝘽𝙊𝙉 𝙇𝙄𝙏𝙏𝘼𝙁𝙄 𝙉𝘼 𝙈𝘼𝙄 𝙎𝙐𝙉𝘼 𝘼 *ASSALAMU ALAIKUM READERS, GA NI NA ZO MA KU DA SABON LITTAFI NA MAI SUNA A SAMA, WANDA YA ZO DA ZAFI-ZAFIN SA, KUMA NA TABBATA ZA KU JI DAD'IN SA. BA ZAN CI KA KU DA SURUTU BA, KAWAI KU BI NI A FREE PAGES, KU DA KAN KU ZA KU GA NE BOOK D'IN NA DABAN NE. KAWAI KU NU NA MIN ONE LOVE WAJAN SIYAN BOOK D'IN AKAN FARASHI AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA:*
*Normal group shine mutum zai bi ya 500 idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300.*
*VIP kuma 1000 ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700.*
*MUTANAN NIGER KUMA ZA SU BI YA KAMAR HAKA*:
*Normal group shine mutum zai bi ya 500F idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300F.*
*VIP kuma 1000F ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700F.* 🌼 🌹 🌹 🌼 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 BA NI DA GATA*🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌼. 🌼 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹
*ᴘᴀɪᴅ ʙᴏᴏᴋ*
*NARRATED & WRITTEN BY* *ZULFA'U SA'EED IBRAHIM* ( *_MATAR SAYYADEE_*)
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*☀️💪 ( *Home of quality and trusted writer's of the nation*)💪🏻
*DEDICATED TO THE MOST BEAUTIFUL WOMAN IN THE WHOLE WORLD (MY MOTHER). ALLAH YA JIK'AN KI DA ℝ𝔸ℍ𝔸𝕄𝔸*
*________________* *FREE PAGE 7&8* *________________*