Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 3

Ba ni da gata - Chapter 3

Ba ni da gata Chapter 3: Ba ni da gata Chapter 3. ............"Yarinya ya sunan ki? Alhaji Sammani ya fad'a yayin da ya ke tsaye a gaban ta yana mata…

2,234 words

............"Yarinya ya sunan ki? Alhaji Sammani ya fad'a yayin da ya ke tsaye a gaban ta yana mata murmushi. D'agowa ta yi tare da zuba masa idanuwanta da suke kamar madara tare da fad'in, "Sunana Binty. Binty y'ar bola". Ta fad'a tare da cigaba da jefe flowers a cikin kwata. "Binty 'yar bola kuma? To ina iyayen ki su ke? Ina ne gidan ku?". Alhaji Sammani ya fad'a ta re da zama kusa da ita. "Ni ba mu da gida. A bola mu ke zama. Kuma mamana ce bolan, ita ta haife ni. A can na tashi". Wani farin ciki ya dabaibaye zuciyar Alhaji Sammani, domin ya ga ne d'aukar Binty ba zai masa wuya ba. "To yanzu me ki ke yi a nan wajen ke d'aya?". Alhaji Sammani ya sa ke jeho mata tambaya. "Ni ma ban sa ni ba, amma bazan sa ke ko ma wa bolan mu ba. Ban san wancan duniyar, kowa bai so na a can. Ina so in je duniyar da kowa zai so ni, kuma in rik'a samun abinci ina ci sau uku a rana. Ni ba dole sai na yi wanka ba. Amma ina son in canza wannan wandon na jiki na. Kalla duk ya yage. Ka san wa ya ba ni? Wallahi Hadaan ne ya kawo min, kuma maman shi ta d'auke min shi ta kai shi wani waje mai ni sa". Ta fad'i haka ne hawaye na zubowa daga idanunta. "Ayyaah kin ban tausayi. Amma ki kwantar da hankalin ki, zan kai ki in da za ki samu duk abunda ki ke so, za ki je duniyar da kowa zai k'aunace ki kin ji y'ar yarinya". Alhaji Sammani ya fad'a ta re da rik'o hannunta. "Dagaske? Har wajan Hadaan d'ina za ka kai ni?". Binty ta fad'a out of excited. "Sosai ma kuwa, muje ga motata can ki shiga mu tafi". Alhaji Sammani ya fad'a tare da kama hannunta su ka yi wajan mota. D'aga kan da Binty za ta yi ta hango Kaka a kan wani katanga ya na girgiza mata kai sannan kuma ya na maganar da ita kad'ai ke jin abunda ya ke fad'i. "Ka da ki bi shi Binty. Za ki halaka idan ki ka bi shi. Ki dawo ki koma ki zauna a in da ki ke. Shine alkhairi a gare ki. Za ki fad'a wani hannu daban da zaki sha wahalar rayuwa. Za ki kira k'addarar ki da kan ki Binty". Girgiza kai Binty ta yi ta re da fad'in, "Ni sai na bi shi, bayan wajan Hadaan zai kai ni. Ni ba ruwa na da kai, ai kai ma guduwa ka ke yi ka na bari na babu abunci". Binty ta fad'a ta na murgud'a baki. Kasancewar Alhaji Sammani ya d'an yi gaba kad'an shiyasa bai ji abunda Binty ke fad'i ba. "Binty kar ki bi sa". Kaka ya sa ke fad'i ya na girgiza kan shi. "Sai na je". Binty ta fa'da ta re da isa wajan motar. "Ke da wa ki ke magana Binty?" Alhaji Sammani ya fad'a ya na mai waiwaigawa don ganin da wa Binty ke magana. Ita kuwa Binty ba ta ba shi amsa ba ta shiga k'ok'arin shiga gaban motar da ya sha tinted, amma ta ka sa saboda ya mata tsayi. 'Dagata Alhaji Sammani ya yi ta re da d'aura ta a kan kujera shi kuma ya zagaya ya shiga mazaunin driver ta re da yin reverse ya ko ma ya hau highway zuwa garin Abuja babban birni, don a can ne su ke gudanar da tsafin su. A cikin wani katafaren hotel Alhaji Sammani ya yi parking tare da fita ya kulle Binty a ciki da ke ta bacci. Domin tunda aka haife ta bata tab'a irin wannan doguwar tafiya haka ba. In fact in her whole life ba ta tab'a shiga mota ba sai yau. Reception ya shiga tare da biyan kud'in d'aki na kwana d'aya kawai. Ka na ya karb'i key ta re da fitowa ya dawo cikin mota ya kunna ya yi reverse ya bar cikin hotel 'din. A wani katafaran saloon ya tsaya ta re da bubbuga Binty da ke bacci ta na mafarkin kaka na mata kashedi akan ta gudu ka da ta bi wannan mutumin da ta ke ta re da shi. Farkawa ta yi ta re da fa'din, "Ni sai na bi shi, bazan gudu ba kaka. Ka dai na tab'a ni. Shi ba mugu ba ne. Ya saya min kayan dad'i a hanya. Kuma wajan Hadaan d'ina zai kai ni". Idanuwa Alhaji Sammani ya zuba mata, Can kuma ya k'ara bugunta a hankali. Wannan karan gaba d'aya ta bu'de idanunta ta zuba masa ta re da fad'in, "Mun kawo in da za ka kai ni wajan Hadaan d'ina ne?" "A'a beauty ba mu kawo ba, nan mun zo in da za'a gyara ki ne ai miki wanka a gyara miki gashin ki, saboda in da zan kai ki ba su son k'azamin mutum, kuma ba za su yarda ki ga Hadaan d'in ki ba a haka". "Kai kai kai.. Hadaan ne ya fad'a maka yadda ya ke kiran suna na? Allah ni ban san wanka, amma tunda za ka kai ni wajan Hadaan zan yarda a min wankan". Binty ta fad'a cike da farin ciki a fuskan ta. "Yauwa to jira ni a cikin mota ina zuwa". Alhaji Sammani ya fad'a ta re da fita ya shiga cikin wannan dank'areran Saloon 'din. Mintuna goma su ka fito shi da wata kyakkyawan siririyar mata su na dariya ita da Alhaji Sammani. Wajan motar su ka yo, Alhaji Sammani ya bud'e ta re da sauko da Binty daga cikin mota ka na ya kalli wannan kyakkyawar matar da ta saki hanci da baki ta na kallon tsananin kyawun Binty. "Precious Lord in heaven! What a beautiful girl. Alhaji ina ka samo wannan kyakkyawar yarinya haka? Oh my God, dan Allah ka ba ni ita mana". "A'a ni ba za a ba ki ni ba, wajan Hadaan d'ina zai kai ni". Binty ta fad'a ta re da mak'e kafad'ar ta, ta kuma koma bayan alhaji Sammani ta b'uya. Kaka ta ga ni a bayan wannan kyakkyawar matar ya na girgiza ma ta kai ta re da fad'in, "Binty ki bi ta, idan ki ka bi ta ba za ki halaka ba. In har ki na son k'ara ganin Hadaan ki bi ta". Ita kad'ai ta ji maganar. Zaro idanuwa ta yi ta re da fad'in "Kaka nan ma sai da ka bi yo ni? Ni Allah ba zan bi ta ba. Wannan zan bi ya kai ni wajan Hadaan d'ina". Gaba d'aya daga alhaji Sammani har wannan matar kallon Binty su ka yi ci ke da mamaki ta re da kuma waigawa don su ga dawa ta ke magana, amma wayam su ka ga ni sai mutanan da su ke wuce wa d'aya-d'aya su na shiga Saloon d'in. "Binty dawa kike magana?" Alhaji Sammani ya fad'a ya na kallon ta at the same time kuma ya na kallon gefe da kuma bayan shi. Kasancewar gaba d'ayan su kallonta su ke yi. "Kaka ma na, sai cewa ya ke yi wai ka da na bi ka, na bi wannan". Ta fad'i maganar ne ta na nu na wannan matar. "Tun a in da ka d'auko ni ya ke ce wa wai ka da na bi ka. Yanzu kuma ya ce na bi wannan". Zaro idanuwa Alhaji sammani ya yi jikinsa har ya soma b'ari. "Ka da dai a ce aljana na 'dauko. Na shiga uku ni sammani". Ya fad'a cikin zuciyar sa. Can kuma wani zuciyar ta ce masa, kai Sammani kawai ka kai ta, idan ya so ko aljanar ce su su ka san yadda za su yi da ita. Kai dai ba ka kai ta ka fita ba. "Ke Mss Raliya kwantar da hankalin ki, haka ta ke. Ta na da 'dan matsala a kwakwalwarta ne kad'an. Wani lokacin haka ta ke behaving". Fad'in Alhaji Sammani da turanci ta re da murmushi ya na shafa kan Binty. Ajiyar zuciya Raliya ta saki ta re da fad'in, "Allah sarki, I pity her. Allah ya ba ta lafiya. Muje ko beauty". Ta fad'i hakanne ta re da kama hannun Binty su kai gaba. Ita kuwa Binty dad'i ne ya kashe ta kasancewar ta ji su na kiran ta da sunan da Hadaan ya ke kiran ta da shi. Ciki su ka shiga, shi kuma Alhaji Sammani ya zauna a cikin mota ya na jiran su. Binty baki da hanci ta saki ta na kallon cikin katafaran Saloon d'in nan. Wani 'katon d'aki su ka shiga mai wahalar fasaltawa saboda tsaruwarsa. "Zauna a nan ki jira ni". Raliya ta nuna mata wani kujera ta re da yin gaba ta shiga wani 'dan corridor da ke 'dauke da bathroom a ciki. Bayan minti biyar ta fito ta re da kiran Bintyn. Bintin ta tashi ta re da bin bayan ta. Cikin bathroom d'in su ka shiga. Raliya ta riga da ta had'a ruwan wanka da sai fitar da k'amshi ya ke. Ga sabon sponge nan da kuma toothpaste da brush a gefe. Cire mata kayan jikin ta ta yi tare da saka ta ta shiga cikin wani baf na wanka mai circle. Kai ta fara wanke mata wanda sai a wankewa na goma ya soma kumfa, don da sai wani irin coffee brown 'din datti ke fita da wani irin yauk'i yauk'i abun kyamma da k'azanta. A tak'aice dai sai da Raliya ta wanke kan nan sau goma sha bakwai ka na ya fita k'al k'al gashi bak'ik'k'irin da shi mai cika da tsayi har tsakiyar bayanta. "Subhanallah! Masha Allah!". Raliya ta fad'i domin tun da ta ke aikin saloon ba ta tab'a ganin yarinyar k'arama mai irin wannan uban gashin ba. Wai a hakan ma don ba'a ja shi da hand drayer ba. Wanka kuwa sai da farin sosan nan ya koma ruwan k'asa saboda dattin da ke fita daga jikin Binty. Sai da Raliya ta ga ta yi k'al jikin ta na sulb'i ka na ta na'dota cikin towel su ka dawo wani d'akin mai k'aton madubi gaba da baya. Ga kaya gyaran kai da su attachment nan kala-kala da su relaxer da sauran su a ciki. Wani man shafawa Raliya ta d'auko mai k'amshi ta shafe jikin Binty da shi ka na ta d'aurata akan wani dogon kujera. Wani irin juyowa Binty ta yi ta kalli Raliya ta re da fad'in, "Ni ce wannan a cikin wannan abun? A she ina da kyau. Kalli gashi na ya canza kala. Mai ki ka min na koma haka?". Binty ta fad'a kasancewar ta na da shegen surutu. Kuma duk lokacin Allah ya sa ta ga fuskan ta cikin madubin mota ko kuma irin shagunan nan ma su slide, dak'an-dak'an ta ke ganin ta, kuma wancan lokacin gashin ya rine da kalar k'asa da kuma bola a jiki. "Ke ce mana. Ai ke kyakkyawa ce. Ga ki da dimple da gashi mai kyau". Fad'in Raliya. "Da ki ka min wanka sai naji jikina ya min iska da dad'i. Wai ke ya sunan ki". Binty ta fad'a ta na k'ara kallon kan ta cikin madubi. "Sunana Raliya, amma ke ki kira ni da aunty Raliya kin ji?". Aunty Raliya ta fa'da ta na warware gashin kan Bintyn da ya zuba har bayan ta. Hand drayer ta kunna ta kai shi saitin kan Bintyn za ta fara busar mata da shi. Wani irin ihu Binty ta kwala ta re da wurgi da towel d'in jikin tai ta yi hanyar wa je da gudu. Da kyar Raliya ta ka mo ta. Amma fir tak'i tsayawa a busar da gashin nan, don bak'aramin tsoransa ta ke ji ba. Sai da Raliya ta ga dagaske fa Binty ba za ta tsaya ba sannan ta kashe hand drayan ta re da fita ta kirawo wasu mata guda uku su ka ri'ke mata Bintyn ta na ihu ka na aka jaa gashin nan da yai wani irn masifar tsawo da kyau sai kyalli ya ke yi.

*ASSALAMU ALAIKUM READERS, GA NI NA ZO MA KU DA SABON LITTAFI NA MAI SUNA A SAMA, WANDA YA ZO DA ZAFI-ZAFIN SA, KUMA NA TABBATA ZA KU JI DAD'IN SA. BA ZAN CI KA KU DA SURUTU BA, KAWAI KU BI NI A FREE PAGES, KU DA KAN KU ZA KU GA NE BOOK D'IN NA DABAN NE. KAWAI KU NU NA MIN ONE LOVE WAJAN SIYAN BOOK D'IN AKAN FARASHI AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA:*

*Normal group shine mutum zai bi ya 500 idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300.*

*VIP kuma 1000 ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700.*

*MUTANAN NIGER KUMA ZA SU BI YA KAMAR HAKA*:

*Normal group shine mutum zai bi ya 500F idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300F.*

*VIP kuma 1000F ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700F.* *ʜᴀʙɪʙᴀᴛɪᴇꜱ ᴅᴀɴ ɢɪʀᴍᴀɴ ᴀʟʟᴀʜ ᴋᴜ ɴᴜ ɴᴀ ᴍɪɴ ʟᴏᴠᴇ ᴡᴀᴊᴀɴ ꜱʜᴀʀɪɴɢ* 🌼 🌹 🌹 🌼 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BA NI DA GATA*🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌼. 🌼 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹

*ᴘᴀɪᴅ ʙᴏᴏᴋ*

*NARRATED & WRITTEN BY* *ZULFA'U SA'EED IBRAHIM* ( *_MATAR SAYYADEE_*)

☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*☀️💪 ( *Home of quality and trusted writer's of the nation*)💪🏻

*DEDICATED TO THE MOST BEAUTIFUL WOMAN IN THE WHOLE WORLD (MY MOTHER). ALLAH YA JIK'AN KI DA ℝ𝔸ℍ𝔸𝕄𝔸*

*__________________* *FREE PAGE 9&10* *__________________*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull