Ba ni da gata - Chapter 4
Ba ni da gata Chapter 4: Ba ni da gata Chapter 4. ..............Bayan an gama busar da kan, aunty Raliya ta mai da ta kan kujeran ta re da k'ara gyara kan…
3,173 words
..............Bayan an gama busar da kan, aunty Raliya ta mai da ta kan kujeran ta re da k'ara gyara kan tai parking d'insa a tsakiya ta re da yi mata donut, sannan kuma ta saki jelar har tsakiyar bayan ta da shi ma ya sha stones ma su kyau, ta kuma sa ka mata wani kwalliya ma su kyalli da ya k'ara k'awata gashin na ta akan donut d'in. Wad'annan matan da su ka rik'e Binty a kai mata gyaran kai kuwa bakin su ya k'i rufuwa sai adoring gashin su ke yi. Wata doguwar gown kalar pink Raliya ta fito da shi a cikin wani kwali da fad'ar tsaruwar shi b'ata ba ki ne. Pant ta fa ra saka mata fari k'al da shi ka na ta saka mata wannan had'ad'd'an gown d'in. Powder kawai ta shafa mata ta re da lipstick. "Wow!". Fad'in Raliya sai k'ara kallon Bintyn ta ke yi kamar ta lashe ta. Domin fad'in irin kyawun da Binty ta yi b'ata baki ne. Za ka rantse y'ar shugaban k'asa ce ko kuma 'dan majalisa. Hannunta Raliya ta ka ma su ka fito daga cikin wannan d'akin. Duk in da su ka wuce sai ido ya koma kan su ta re da gabon kyawun da Bintyn ta yi. Wasu ma har hoto su ke mata. Ita kan ta aunty Raliyar ta ma ta hoto ya kai kala ashirin. Akwai wanda su ka yi su biyu da kuma wanda ta yi ma ta ita kad'ai. Ko da su ka zo wajan motar Alhaji Sammani, bai ga ne Binty ba, sai ce wa ya yi, "Raliya kun dad'e fa, ina ita yarinyar ta ke?". Nu na Binty ta yi ta na murmushi tare da fad'in, "Alhaji ba ga tanan ba. Ka ga ta canza ko?". Waro idanuwa Alhaji Sammani ya yi tare da fad'in, "Haba dai? Wannan ita ce yarinyar da na zo da ita. Kai ina there must be mistake somewhere, wannan ba yarinyar da na kawo ba ce". Fad'in Alhaji Sammani ya na k'ara gwale idanuwa ya na kallon Bintyn da ke ta zuba masa murmushi kumatukanta na lob'awa. "Wallahi sir itace, ita ce, ni kai na da na gyara ta ba k'aramin mamaki na ke da kyawun da Allah ya ni'imtata da shi. Don Allah Alhaji kar ka ce na cika tambaya, ya ka ke da ita?". Shan mur Alhaji Sammani ya yi ta re da fad'in, "Wannan ba matsalar ki ba ce, forward your account details in tura ma ki kud'in ki tun da kin ga ma aikin ki". Tsuke baki Raliya ta yi ta re da daddanna wayarta. Cikin abunda bai fi minti biyu ba, har Alhaji Sammani ya turawa Raliya dubu d'ari biyu. "Thank you Sir". Raliya ta fad'a ta re da shafa kan Binty ta ce, "To Beauty sai mun sa ke had'uwa. Ki kula da kan ki kin ji?". "To" shi ne kawai abunda Binty ta fad'a. Shi kuwa Alhaji Sammani ce wa ya yi cikin zuciyar sa, "Shegiya sai dai a lahira, don wallahi na tabbata yau na kai wannan kyakkyawar yarinya k'ungiya, sai an ba ni muk'ami na musamman". Ya na gama fad'in hakan ya ka ma Binty ya d'aga ta ta re da sa ka ta gaban mota, ka na ya zagaya ya shiga mazaunin driver ya yi wa motar key ta re da reverse ya bar Saloon d'in ya nu fi wa ni eatery da ita domin ta ci abincin, don har an yi kiran sallar magriba. Waitress ce ta zo ta ka wo ma sa menu ya zab'i abunda za'a kawo ma su. Shi bai yi ordering ko mai ba, Binty ka wai ya sa a ka kawo wa pounded yam da miyan egusi da yaji stockfish da ganda a ciki. Ko da Binty ta ga abincin sai ta dinga bin abincin da idanuwa domin bata tab'a ganin irin wannan abincin ba a rayuwar ta. "Ci mana Binty, ki yi sauri mu ta fi dare na yi". Fad'in Alhaji Sammani. "Ni ban san abincin ba, ya ake yin sa? Ban tab'a ganin sa ba". Binty ta fad'a. "Zan ci uwar yarinyar nan wallahi". Alhaji Sammani ya fad'a cikin zuciyar sa. Amma a zahiri sai ce wa ya yi, "Ki gutsiri wannan, sai ki sa ka a cikin miyar ki sa ka a bakin ki, akwai dad'i". Ya fad'i hakane ya na mata demonstrating. Kamar yadda ya gwada ma ta haka ta yi, aikuwa ta wa ni lumshe ido tare da fad'in, "Kaiiiii wallahi akwai dad'iiiiiiii, kamar in ta ci kar ya k'are". "Duk lokacin da ki ke so ki min magana zan kawo ki nan sai ki k'ara ci". Fad'in Alhaji Sammani ci ke da k'osawa. Ba ta sa ke cewa ko mai ba, sai faman loma ta ke yi ta na jujjuya kai ta re da k'anana-k'ananan wak'a. Miyan kuma duk ya b'ata gaban pink 'din rigarta. Sai da ta ci sakwara biyar duk da cewar k'anana ne sai da Alhaji Sammani ya saki baki ya na kallon ta ci ke da mamaki cin abincin ta. "Tun da kin gama tashi mu tafi kar mu yi dare". Binty da ke lashe hannunta ta mik'e tare da share sauran miyan a jikin rigarta ka na ta d'au goran ruwan dake wajan ta yi gaba. Alhaji Sammani kuwa kiran waitress d'in ya yi ta re da bi yan kud'in ka na ya bi yo bayan Binty da ke tafiya ta na kwankwad'ar ruwan gora. Bu'de mota ya yi ta re da sa ka taa ciki shikuma ya juya ya koma mazaunin driver. Hotel d'in da ya sauka can ya nufa ta re da ruk'o hannun Bintyn ka har d'akin da ya ka ma. Makeken d'aki ne mai d'auke da royal bed da kuma wani rantsantsan Chinese carpet mai d'ankaran laushi. Ga kuma makeken gado samfarin italy. Gaba d'aya Binty rud'ewa ta yi da ganin wannan d'akin, sai kalle-kalle ta ke yi ta re da k'if-k'if da idanuwa. K'afarta ta d'aga ta re da saukewa a kan wannan Chinese carpet d'in mai laushi. Wani ihu ta kwandara da ya firgita Alhaji Sammani, duk a tunanin sa ta hango abunda ke cikin jakar da ya shigo da ita ne. Domin ta kulle idanunta ne ta re da k'ank'ame jikinta. "Ke lafiyan ki?" Alhaji Sammani ya fa'da ya na matsowa in da ta ke. "Sansanin macijai na fad'a. Ka taimaka ka ciro min k'afata ka min na mutu. Na d'aura k'afata a kan maciji mai taushi". Dariya ce ta sub'ucewa Alhaji Sammani, aiko ya kyakyata har da rik'e ciki ka na ya ce, "Kwantar da hankalin ki Binty. Ba'a kan maciji ki ke ba, akan carpet ki ke mai laushi. Ba bu maciji a ciki n hotel d'in nan". Fad'in Alhaji Sammani ya na murmushi. Sai a lokacin Binty ta soma bud'e idanunta kwara d'aya, ka na shi ma d'ayan ta bu'de sa. Doguwar ajiyar zuciya ta yi ta re da fad'in "Kaiii amma Allah na gode ma ka. Na d'auka mutuwa zan yi ai. Yanzu wanna shi ne kapur? To menene kapur 'din? Me ya sa ake saka sa a nan d'in?". Binty ta fad'a ta re da duk'awa ta na shafa carpet d'in ta na dariya. "Kapur d'in akwai d'an ban zan laushi. Hannuna lumewa ya ke yi a ciki. Kalla fa?". Binty ta sa ke fad'i ta na k'ara cusa hannunta a ciki n carpet d'in. "Ammafin shi ke nan ai kwalliyar d'aki da shi". Fad'in Alhaji Sammani ta re da wucewa toilet ya bar ta a wajan sai zuba k'auyanci ta ke yi. Hatta bedside lamp sai da ta shafa ta na mamakin wannan miye. Har Alhaji Sammani ya ga ma abunda zai yi ya fito daga toilet Binty na nan ta shafa wannan, ta shafa wancan. "Ki kwanta a kan fado ki bacci, gobe da sassafe zan kai ki wajan Hadaan d'in ki, kin ji?". Ci ke da farin ciki Binty ta kalli Alhaji Sammani ta re da fad'in, "A wannan abun mai kyau zan kwanta? Kai amma na ji dad'i". Binty ta fad'a ta re da hawa kan gadon. Wani ihu ta sa ki ta re da mik'ewa ta zauna a tsakiyan gadon ta kuma gantsaro ba yan ta ta re da fad'in, "Wayyoo Allah bola uwata ba ya na zai karye." Alhaji Sammani tsaye ya yi ya na kallon ta, har ga Allah ya so kungiya ba ta buk'aci ya kai yarinyar k'arama kuma virgin ba, da ba bu abunda zai ha na shi d'aukar yarinyar nan ya kai ta gidan shi ko dan ya rik'a shan dariya da irin shirman ta. Ita kuwa Binty da ba ta ta'ba kwanciya ko a kan kara ba shiyasa yau da ta kwanta a katifa autopadic ta ji kamar ba yan ta zai b'alle don katifar gand'and'an haka ta ke. Irin na ma su ciwon ba ya ne. "Ni wallahi ban kwanciya a nan, k'asa zan kwanta idan ba haka ba ba ya na karyewa zai yi." Binty ta fad'a ta re da saukowa daga kan gadon ta ko ma kan centre carpet d'in nan ta kwanta ta re da fad'in, "Yauwa ai gwara nan. Ga laushi ga dad'i. Wallahi nan zan yi kwanciya ta. Kai ka yi ta kwanciyar ka a kan dutsen can, amma ni nan zan kwana". Alhaji Sammani bai ce ma ta k'ala ba, ya kashe wuta ya hau gado ya kwanta ya na jiran lokacin zuwa meeting ya yi.
..........."Dadddd!" Sabrin ta kwala kiran sunan daddyn na ta kamar ta na kiran sunan sa'an ta. Abunda zai ba ku mamaki daddyn na ta na kusa da ita. "Wallahi ba za su shiga makarantar nan ba, idan kuma za su shi ga sai dai ni a cire ni a mai da ni *lead British*, kai daddy ni yanzu ma ban san *Hampos Academy* d'in, su a sa ka su, ni kuma a kai ni *Lead British*, amma ba zan shiga makarantar da su ke ba, kuma su ma ba za su shi ga in da na ke ba. That's the final decision. I'm clear dad?" Wani irin mik'ewa haijya Sakna ta yi ta re da isa wajan da Sabrin d'in ta ke ta d'aga hannu za ta sauke mata lafiyayyan mari a kan kuncin ta, Alhaji Saifullahi ya yi saurin ta re hannun Hajiya Sakna ta re da fad'in, "Ahir d'in ki da tab'a fuskan y'ata. Mai ta yi ma ki? Ni fa ba na son irin wannan abun da ki ke yi fa Sakina. Yarinyar nan kin san yarinya ce, a hankali ya ka ma ta a rik'a bin ta. Kin fi kowa sanin yarinyar nan ba ta da isasshen lafiya. Da ciwon zuciya a ki ka haife ta. So ki ke ki kashe min 'ya Sakna?". "Yanzu Alhaji ka na ga nin wannan hanya bai b'ullewa ce? Yarinyar fa k'ara lalacewa ta ke yi. Kar ka manta wata rana gidan wani za ta. Wallahi ba bu wanda zai d'auki wannan iskancin na ta. A ce yarinyar k'ank'anuwa da ita amma bak'in ciki da hassada ya mamace zuciyar ta. Hatta ni d'in nan mahaifiyar ta kishi ta ke yi dani. Ka duba ka ga ni, wad'annan gaba d'aya y'an uwan ta ne, amma ta ke ik'irarin ba za ta yi karatu a makaranta d'aya da su ba. Ka san saboda mai ya sa ta ce haka? To saboda aji su na bearing the same surname da su ne. Ita a rayuwarta ba ta k'aunar wa ni yai abu iri d'aya da ita ko kuma ya fi ta a wani abu. Sabrin ba ta k'i a ce daga ita ni da kai da Junaina ba mu sa ke haihuwa ba don ta kasance ita ce d'aya d'iyar mu. Ku ma wallahi ku ne ma su k'ara dulmiyar da ita wajan nu na mata abubda ta ke yi dai-dai ne. Kuma wallahi Alhaji ba'a saka 'yan biyu a makarantar da su ke so ba to kuwa ba ai ma su adalci ba. Ko da ya ke, adalci ka ke yi ma. Ko mai fa idan za ka sayawa wad'annan y'ay'a to fa na Sabrin sai ya fi kyau da tsada saboda ita d'in ta daban ce a wajan ka. Kuma wallahi yaran nan su na ganin ko mai. Wa ni abu ka ke da sa ma su a cikin zuciyar su wan da wallahi nan ga ba za kai nadama. Ku ma idan har ni mahaifiyar Sabrin ce, ban yadda a raba masu makaranta da y'an biyu ba. Idan *Lead British* za ta ko ma, to su koma ta re. Idan ku ma Hampos 'din za ta cigaba da zuwa, to su cigaba da zuwa ta re. Ai su ma y'ay'an ka ne kamar yadda ta ke y'ar ka. Matsayinsu d'aya". "Never! Matsayin mu ba d'aya ba ne wallahi mom". Fad'in Sabrin ta na turo ba ki gaba. Wawan mari Hajiya Sakna ta sakarwa Sabrin sai da ta gigice ta kifa k'asa. Alhaji ya harzuk'a shi ma ya d'aga hannu ya daddage ya wanke fuskan Hajiya Sakna da mari sai da ta yi taga-taga za ta fad'i. Aunty Junaina kuwa wani irin murmushi ta sak'i wanda ba bu wanda ya lura da ita sai d'aya daga cikin y'an biyu mai su na Amrah.
*ASSALAMU ALAIKUM READERS, GA NI NA ZO MA KU DA SABON LITTAFI NA MAI SUNA A SAMA, WANDA YA ZO DA ZAFI-ZAFIN SA, KUMA NA TABBATA ZA KU JI DAD'IN SA. BA ZAN CI KA KU DA SURUTU BA, KAWAI KU BI NI A FREE PAGES, KU DA KAN KU ZA KU GA NE BOOK D'IN NA DABAN NE. KAWAI KU NU NA MIN ONE LOVE WAJAN SIYAN BOOK D'IN AKAN FARASHI AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA:*
*Normal group shine mutum zai bi ya 500 idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300.*
*VIP kuma 1000 ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700.*
*MUTANAN NIGER KUMA ZA SU BI YA KAMAR HAKA*:
*Normal group shine mutum zai bi ya 500F idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300F.*
*VIP kuma 1000F ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700F.*
*EVIDENCE OF PAYMENT 08128755583*
*MATAR SAYYADEE CE*
SHARE AND COMMENT PLEASE
🌼 🌹 🌹 🌼 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 *BA NI DA GATA*🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌼. 🌼 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹
*PAID BOOK*
*NARRATED & WRITTEN BY* *ZULFA'U SA'EED IBRAHIM* ( *_MATAR SAYYADEE_*)
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*☀️💪 ( *Home of quality and trusted writer's of the nation*)💪🏻
*DEDICATED TO THE MOST BEAUTIFUL WOMAN IN THE WHOLE WORLD (MY MOTHER). ALLAH YA JIK'AN KI DA RAHAMA*
*KU HANZAR TO KU HWARA PAYMENT, KA DA KU BA RI A BA KU LABARI. NORMAL GROUP, D'ARIN KI BIYAR #500 KACAL ZAI BI YA MI KI BUK'ATA, SHI MA IDAN KATI ZA KI TURO, IDAN KUMA TA ACCOUNT NE, D'ARIN KI UKU #300 YA ISHE KI. VIP KUMA #1000 IDAN KATI NE, IDAN KUMA TA ACCOUNT NE D'ARIN KI BAKWAI #700 ZAI BI YA MI KI BUK'ATAR KI. KI HAN ZAR TA KAR A BA KI LABARI. 0592412800, SAI KI TURO DA SHAIDAN BIYAN KI A WANNAN NUMBER 08128755583. SAYAN NA GARI, MAI DA KUD'I GIDA*
*____________________* *FREE PAGE 11&12* *____________________*
............."Alhaji ni ka mara saboda ina ko ya wa y'ata tarbiya?". Fad'in Hajiya Sakna rik'e da kunci ta na kallon Alhaji Saifullahi. "An mareki d'in, ki yi abunda za ki yi. Wannan ba tarbiya ce, kawai ba ki son ta ne shiyasa ki ke ga na mata azaba. Kuma idan har NI ne mahaifin su, kuma ni ke biyan kud'in makarantar, Sai in da Sabrin ta zab'a za ta shiga. Kuma kamar yadda ta ce ba za ta yi karatun a makaranta d'aya da su y'an biyu ba, hakan zan yi. Za ta ko ma *LEAD BRITISH* kamar yadda ta buk'ata, su kuma twince su ta fi *HAMPOS* d'in. That's my final decision". Alhaji Saifullahi ya fad'i a tsawace. Aunty Junaina kuwa, cike da mak'irci da mubafunci ta kalli Hajiya Sakna ta re da fad'in, "Mummyn Zaid, ki yi hak'uri ta je makaranta da ta ke so, ai ba bu komai, su kan su y'an uwan na ta ai sun san halin da ta ke ciki. Su kan su su na supporting ai ma ta abunda ta ke so saboda lalurar ta. Ni na san ba sa jin komai a hakan haka. Ko ba haka ba Amrah". Aunty Junaina ta k'arishe maganar ta na kallon fuskan Amrah da tai kicin-kicin da rai. "Bar ta kawai Junaina, tun ba yau ba na fahimci Sakna kishi ta ke yi da Sabrin kamar ba d'iyarta ba. Ta fi k'aunar sha-sha-shan can Zaid da babu abubda ya sa ni Sai fad'i da rashin jin magana. Ku ma wallahi ni babu wanda ya isa ya raba min kan y'ay'a". Alhaji Saifullahi ya fad'a ya na buga babbar rigar shi cike da masifa. Sabrin kuwa sai murmushin jin dad'i ta ke yi saboda yadda daddyn ta a ko'ina ya ke nuna ita d'in ta musamman ce a wajan shi. Hakan na matuk'ar burgeta. Duk da ta mi wani iri kad'an da daddyn na ta ya wanke fuskan mahaifiyar na ta da mari. Hanan tagwainiyar Amrah kuwa ji ta ke kamar tai bindiga saboda tsabar b'acin rai da yadda daddyn na su ke nuna banbanci b'aro-b'aro a tsakanin su da y'ar uwar ta su. Hakan ya jefa masu mugun tsanar Sabrin d'in a cikin zuciyar su wanda ko k'aunar ganin ta ba sa yi. Hajiya Sakna da ke tsaye dafe da kuncinta ta na hawayen bak'in ciki saboda lallata mata y'a da Junaina da daddynta su ke yi wanda tun tuni ta ga ne Junaina ba k'aunar Sabrin d'in ta ke yi ba. Kawai so ta ke ta lalace, don ita kan ta kishi ta ke da abubda mahaifin na su ya ke wa Sabrin d'in kamar ita ce kad'ai y'arsa don bai had'a Sabrin d'in da kowa ba. Ju ya wa ta yi a fusace ta ha ye sama da sassarfa ta shige d'akinta ta re da turo k'ofa ta fad'a kan gado ta saki kuka mai d'an sauti. Alhaji Saifullahi kuwa, kama hannun Sabrin ya yi ta re sa fad'in, "Sorry my Queen, mu je in d'an yawata da ke a gari hankalin ki ya kwanta kin ji daughter. Don't mind your mother". "Daddy zan je ni ma". Fad'in Hanan". Fad'in Hanan. Wawan mintsili mahaifiyarta ta kai mata a kan cinyarta ta re da antaya mata harara. Hakan ya yi dai-dai da lokacin da Sabrin ita ma ta sauke mata wani irin kallo mai cike da gargad'i ta re da harara. Mahaifin na su kuwa cewa ya yi, "No Hanan, wannan fitar ta queen ce. Ku je ku ta ya mom d'in ku da aiki ka min mu dawo. And make sure you cook her favourite before we come back". Ya k'arisa maganar ne ya na kallon aunty Junaina kasancewar ita ke da girki. "In sha Allah". Fad'in aunty Junaina murmushi kwance a fuskan ta, yayin da zuciyar ta ke wani irin gurnanin wuta mai ci ke da tsantsar tsanar Sabrin d'in.