Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 14

Ba ni da gata - Chapter 14

Ba ni da gata Chapter 14: Ba ni da gata Chapter 14. ..........Zaune su ke a parlourn k'asa akan center carpet, Fanan na koya mata letter sound. Kasancewar…

3,340 words

..........Zaune su ke a parlourn k'asa akan center carpet, Fanan na koya mata letter sound. Kasancewar tu ni ta iya ABCD har zuwa Z, yanzu letter sound ake koya mata. Sun kai letter p, sai dai Bintyn ba ta bambamce P sound da F sound. Fanan ta ce "Look Binty, kalli bakina, ki kalli yadda zan yi da ba ki ne. Shi F sound haka za ki yi ffffff kamar ki na hura abinci idan akwai zafi. Yanzu ki yi imaging, ina nufin ki d'auka kamar abinci ne a hannun ki, kuma akwai zafi, to hura abinci mu gani". Fad'in Fanan ta na kallon bakin Bintyn. Binty ta yi kamar yadda ta ce ta re da fitar da sautin, "Ffffffffff!". Ta na kallon Fanan d'in ko ta yi dai-dai. "Great! Haka ake fitar da sound d'in F. Kamar idan za ki ce flower, wanna sound d'in za ki sa a farko ba na P ba. Fffflower. Kin ga ne?". Fanan ta fad'a ta re da jann harafin F d'in "Fflower. Hakane ko?". Binty ta fad'a. "Yauwa Binty na. Haka ne. Sai kuma P sound. Shi kuma kamar za ki hure candle haka za ki yi, 'puff' haka. Kin ga ne. Ba ri na ba ki misali da pencil. Pa fencil ake cewa ba, pp pencil. Yan zu kin ga ne bambamcin?". "Eh nagane Fanan. P, pencil, sai Ffff flower". Fad'in Binty. Rungumeta Fanan ta yi ta re da fad'in, "Wallahi za ki yi k'ok'ari sosai. Ki na da saurin fahimta". Anna da ke zaune can gyefan su ta na jin su, kuma ita ma ta lura Binty na da saurin fahimta, tun da ko wajan girki yanzu ta na barin ta ta dafa indomie da kuma white rice, duk da ta na gyefe ta na kallon ta saboda sharrin gas. Kuma alhamdulillah ta iya. Tun ta na shinkafar ta na cab'ewa, har ta iya sosai. Ta ma fi Fanan shiga kitchen saboda ita ta na gida ba makaranta ta ke zuwa ba, shiyasa su ke samun ishashshan lokacin da Anna. Barrister Fu'ad ne ya yi sallama ta re da knocking, Fanan ce ta bud'e ta je ta bud'e masa k'ofa. Ta na ganin sa ta rungume sa. Ita ma Binty ta ta so da gudu ta je ta masa oyoyo........

*SORRY IDAN KIN GA TYPING ERROR, MATSALAR KEYBOARD NE KUMA BA NA EDITING*🙏🏻

*PAID BOOK 08128755583*

🌹 *27-28*🌹

Rungume su ya yi su duka ta re da manna ma su kiss a goshi. Ka na ya rik'o hannunsu ta re da k'arasowa wajan da Anna ta ke ya ce, "Anna ina wuni?". Ya fad'a ya na zama a k'asa. "Lafiya k'alau. Yau ba aiki ina ka je?". Anna ta fad'a. "Wallahi na je wajan Muhammad. Ya na ta min tsiya wai ban tab'a zuwa gidan sa ba. Kin san fa ba dani aka kai sa ba. To shine na je yau". Fad'in Fu'ad. "Ma sha Allah, to ya ka baro su?". Anna ta san ke tambaya. "Duk su na lafiya". Fu'ad ya fad'a ta re da kwanciya akan center carpet. "Ya barrister alk'awari na fa?". Fad'in Fanan ta na kallon Fu'ad cike da shagwab'a. "Kin fa ra ko? Alk'awarin mai na miki kuma?". Fu'ad ya fad'a ta re da k'ara gyara kwanciyar sa. "Yaya ba kai ka ce za ka kai ni shopping during weekend ba. Kuma yau Saturday". Fad'in Fanan. "Aikuwa ya Fu'ad haka ka ce ina wajan. Ni ma kuma ka ce idan har na iya nasi babu kuskure za ka siya min irin rigunan Fanan da cak'ulet". Fad'in Binty. "Ke dallah chocolate ake ce wa ba cak'ukate ba. Kar ki fara ba ni haushi mana". Fad'in Fanan ta na hararar ta. "Eh to shi, haka ka ce wallahi". Binty ta fad'a. "Ohhh Allah! Wai mi ya sa ba ku da mantuwa ne? To yanzu ya kuke so a yi?". "Ai kawai ka tashi mu tafi yanzu". Fad'in Fanan. "To uwar san yawo, to ba bu inda za ku". Anna ta fad'a. "Anna dan girman Allah ki yi hak'uri. Ya Fu'ad ka sa ka ba ki". Fanan ta fad'a ta na rik'o hannun Fu'ad d'in kamar za ta yi kuka. Shi kuwa Barrister Fu'ad har wani k'ara kwanciya ya yi ta re da lumshe idanu don da ma ba son fitar ya ke yi ba. Muryanta ya ji dai-dai cikin kunnan sa ta na fad'in, "Ya... Bar...rister, please ka sa ba ki". A hankali ya bud'e idanunsa ta re da saukewa a cikin na ta da ita ma ta zuba masa fararar idanuwan ta da su ke kamar zaiba a marairaice. "Har da ke Binty? Ba kya so Yayan ki ya huta ko?". Fu'ad ya fad'a shima a shagwab'e. "Yaya dan Allah". Fanan ta sa ke fad'i. Kamar had'in baki a ta re su ka kama hannun shi su na jijjigawa su na fad'in, "Yaya dan Allah, yaya dan Allah, yaya dan Allah". Sai su ka mai da abun kamar wak'a. Kallon Anna ya yi ta re sa fad'in, "Anna please ki yi hak'uri mu je, idan ba haka ba wad'annan yaran ba za su bar ni na huta ba, a can k'orafin mutane su ishe ni, anan kuma na su ya ishe ni". Kallon shi Anna ta yi ta re da fad'in, "Sai kun dawo, amma ka da Ku dad'e. Sannan ka tabbatar ka dawo min da su har cikin d'akin nan". "In sha Allah Anna. Sai Ku ta shi Ku je ku shirya mu ta fi". Ya k'arisa maganar ta re da mai da duban sa izuwa ga Binty da Fanan. Cike da farin ciki su ka kwasa zuwa sama. Dama sun yi wanka. Fanan ta yi wa Binty kwalliya ita ma ta yi wa kan ta. Ba k'aramin kyau su ka yi ba, musamman ma Binty da ke sanye da doguwar riga english wears kalar purple da tatsin fari. Sai ta ba ta farin takalmi mai d'an tudu ta re da farin baby hijjab bayan ta nad'e mata gashin ta a tsakiyar kan ta. Ita kuwa pink riga da wando ta saka. Sun yi kyau sosai. A ta re su ka sauko. Gaba d'aya idanun Fu'ad ya koma kan Binty ya na yaba irin kyawun da Allah ya yi mata. "Anna sai mun dawo". Fad'in su Binty ya yin da su ka nufi k'ofa. "To iyayanta zumud'i Ku dawo nan. Shi ko mik'ewa bai yi ba, amma kun saka kai za Ku fita. In ga wata ta saka k'afa a waje in karya k'afar". Fad'in Anna ta re da mai da duban ta izuwa ga Fu'ad ta ce, "Yarda za ku fita tare, haka na ke so ku dawo cikin d'akin nan ta re. Ka ji ni ko". "Yes Anna". Fad'in Fu'ad ta re da mik'ewa y kama hannun Fanan da Bintyn su ka fito.

Kicibis su ka yi da Suhail as usual sanye da 3quarter da arm less, wuyan shi kuma wata shegiyar sark'a ce har ciki kamar kare. Ga uban gashin nan da ya tara tsaf mace za ta kitse shi. Shi kan shi 3quartern an zazzago shi k'asan d'uwawu sai wa ni tafiya ya ke yi yan bouncing. Cak ya tsaya ya na k'arewa Binty kallo. Binty kuwa ta na had'a idanuwa da shi ta koma bayan Fu'ad ta ri'ke masa rigar sa jikinta har ya soma rawa. Zagayo da ita gaban shi ya yi ta re da fad'in, "Kwantar da hankalin ki, ina wajan ai. Babu abunda ya isa ya miki".

"Sai dai idan ban yi niyya ba". Fad'in Suhail ciki-ciki yadda Fu'ad d'in ba zai ji ba.

"Gidan uban wa za ka je kamar d'an arna?". Fu'ad ya fad'a a fusace. "Ahhhh, ni fa ba mace ba qur'an ba bu wanda ya isa ya takuran. Ai ba gadi na aka baiwa mutum ba. Kowa ya yi rayuwar sa. Ba ruwan ka da ni". Suhail ya fad'a cike da gungunai. "Uban mai ka ke cewa dan uban ka?". Fad'in Fu'ad ya na zazzaro masa idanuwa. Shafa k'eyarsa ya yi ta re da juya idanuwan sa gyefe. "Idan ka ce kai d'an iska ne, to in dawo gidan nan ban sa me ka ba. Ni kuma sai na nuna maka d'an guguwa ne ni. Dan iska kawai". Fu'ad ya fad'a ta re kama hannun Fanan da duk ita ma a firgice ta ke su kai parking load.

Dai-dai lokacin motar Mansura mahaifiyar Suhail ta danno kai, k'awarta na gyefan ta. A parking space d'in su ka yi parking. K'awar ta ta ce ta soma fitowa, idanuwan su ka sauka akan na Binty da ke yi wa Fanan magana ta na dariya. Kyawun ta ya bayyana sosai, ga lob'awar da kumatun ta da su ka yi duka biyun. Ga shi ta wani d'age girar ta d'aya. "Ya subhanallah! Inna lillahi. Zan mutu yau ni Zuwairah! Wannan kyakkyawar yarinyar fa?" Fad'in k'awar Hajiya Mansura ta na k'ara k'arewa Binty kallo. Hajiya Mansura ce ta fito daga motar ta na kallon inda Mansuran ta ke kallo. Cikin second 1 ta yi kicin-kicin da ranta ta re da watsawa Hajiya Zuwairah harara wacce ba ta ma San ta na yi ba, domin tuni ta mai da duban ta ga Binty da har ta shige mota. Shi ma kuma Fu'ad dakatawa ya yi daga shiga mortar kasancewar ya ga Hajiya Mansuran da k'awarta. K'arasawa ya yi inda su ke ta re da fad'in, "Sannu da zuwa Hajiya, ina wunin ku". Yak'e Hajiya Mansura ta yi ta re da fad'in, "Lafiya k'alau the great Barrister. Ya fama da jama'a?". Murmushi ya yi ta re da fad'in, "Alhamdulillah Hajiya". Fu'ad ya fad'a ta re da satar kallon k'awar Hajiya Mansurar da ko kallon shi ba ta yi ba saboda Binty da ta tafi da imanin ta. Juyawa Fu'ad ya yi ta re da komawa wajan mota ya bud'e ya shiga ta re da reverse ya bar wajan.

Ajiyar zuciya Hajiya Zuwairah ta sauke ta re da fad'in, "Mansura ina kuka samu kyakkyawar yarinya haka? Wallahi ta yi min. Ki shigo da ita harka mana. Wallahi zan biya ko nawa ne. Kuma zan iya sacrificing komai a kan ta wallahi. Kallon ta kawai da na yi, dai da zuciya ta ta buga da k'arfi. Wani irin mugun sha'awar ta na ke ji wallahi". Wani harara Hajiya Mansuran ta jefe ta da shi ka na ta ce, "Wallahi, kin san ko no wacece. Kin san abunda zan iya yi akan duk abunda na ke so. Saboda haka, ki fita harkan wancan yarinyar domin ta wa ce. Ina nan ina babban shiri a kan ta, don auran ta ma zan yi. Zan kula da ita, zan ba ta rayuwar da ba ta tab'a tunanin shi ko a cikin mafarkin ta ba. Don haka ki had'iye miyan ki ka da ya jawo miki bak'untan lahira. Ke kin san mace ko namiji ba su isa su had'a kishi da ni ba akan abunda na ke so. Na rantse da girman Allah duk wanda ya yi k'ok'arin shiga tsakani na da wannan yarinyar duk yadda mu ke da shi, ke ko da kuwa d'an ciki na ne, wallahi sai na kashe shi. Ko wad'annan matan da ki ke ganin mun had'a miji da su, wallahi na kyale su ne kawai saboda ba mijin ba ne a gaba na, kuma da ma aurar na yi shi ne kawai don gudun zargi. Don Zuwairah ka da ki saki ki nai mi shiga gona ta. Don duk yadda mu ke da ke, zan d'au tsatstsautar mataki a kan ki wallahi. Ba bu ruwan ki da Binty". Hajiya Mansura na gama fad'in haka ta yi hanyar part d'in ta. Hajiya Zuwairah kuwa, wani killer smile ta sa ki ta re da jijjiga kan ta, ka na ta bi bayan Hajiya Mansuran.

Da d'an gudu-gudu ta had'a saboda hajiyan ta yi ma ta nisa. Har bedroom ta bi Hajiya Mansuran da sai cika ta ke ta na batsewa. Gyalan jikin ta ta cire ta re da wurgi da shi a kan gadon. Ka na ta jinginar da kan ta a jikin gadon ta re da lumshe idanuwanta ta na ganin fuskan Binty na mata gizo a cikin idanuwanta. K'arasowa Hajiya Zuwairah ta yi ta re da hawa gadon ta kwanto kan hajiya Mansuran a cinyarta ta na shafa kanta ta re da fad'in, "Allah ya huci zuciyar shugaba, ki yafe ni akan abunda ya faru d'azu. Kuskure ne, ban san ta ki ba ce. Don Allah ki yi hak'uri. Yarinyar ta ki ce ke d'aya. Mai nai man kula ta mace ko namiji, ni da kai na zan ta ya ki yak'i a kan su. Yarinya kamar kin aure ta kin gama". Fad'in Hajiya Zuwairah ta na shashshafa jikin Hajiya mansuran. Wani irin mik'a Hajiya Mansura ta yi, domin ji ta ke kamar Bintyn ce ke shafata. Rungumo Hajiya Zuwairan ta yi ta re da had'e bakinsu. Hajiya Zuwairah kuma ta saka hannu ta zuge zip d'in rigar hajiya Mansura ta re da cire rigarta. Nan su ka fad'a duniyar halaka. Sai bayan sun gama iskancin su ne, sannan Hajiya Mansuran ta tashi ta isa wajan fridge d'in ta tare da bud'e shi da key ta d'auko kwalbar Brandy da cup su ka yi ta sha, sai da su ka yi mak'il ka na su ka zube su na bacci.

*SSS SUPER MARKET* Parking ya yi a wajan aje motoci, ka na ya fito ya bud'e gidan baya kasancewar duk su na gidan baya. Fanan ce ta soma fitowa, ya yin da Binty ta biyo ta a baya. Hannunsu ya rik'o su ka nufi cikin tangameman super market d'in Mai su na SSS ( *SABRIN SAIFULLAHI SAKNA*). "Kun san dai Anna ta ce ka da mu dad'e ko? Saboda ko wacce ta zab'i abunda ta ke so cikin sauri, ban san b'ata lokaci da nawa. Idan ba haka ba zan k'ara zuwa da ku shopping ba". "Yes ya barrister". Fad'in Fanan. Ciki su ka shiga wanda tsaruwar sa kawai b'ata baki ne. Fanan ta rik'o hannun Binty su ka d'auko d'an kwandon nan da ake tura kaya su ka nufi wajan chocolate. A wajan kawai sun kwashi chocolate ya kai guda hamsin, ka na su ka nufi wajan biscuit irin manya-manyan nan na kwali, nan ma su ka jida. Ka na su ka koma wajan teddies. A nan wajan kuma Fanan ta ji di ya kai goma irin manya-manyan nan. Kallon Binty ta yi da ta tsurawa wani elephant idanu da aka masa kwalliya da wani irin kyalkyali mai kyau. "Ki na so ne?". Fanan ta tambaye ta. Gyad'a mata kai ta yi. Fanan d'in ta ce, "To. D'auko mana, ai Yaya barrister ya ce mu d'auko duk abunda mu ke so. Yi sauri mu tafi ka da mu dad'e.". Binty ta nu fi wajan, dai dai lokacin Sabrin ta taho ta ga ba da cikin kyakkyawar gown red colour shwaraski stones mai kyalkyali. Kan ta ya sha gyara sai kyalli ya ke yi. Ta ka ma gashin nan a can gaban kai irin yadda y'an China ke yi. Ga wani dogon takalmi da ke k'afarta. Sai tafiya ta ke yi kamar za ta karye don yanga da yauk'i bakin ta na taunar cingam k'as, k'as, k'as kamar karuwar titi. Bangaje ta Binty ta yi ba ta re da ta lura da ita ba sai da ta fad'i k'asa ta yi zaman y'an bori. Ita kuwa Binty duk da ta bige ta, ba ta bi ta kan ta ba, burin ta kawai ta je ta d'auko wannan elephant d'in. Fuskan Sabrin kuwa har ja-ja-ja ya yi saboda tsabar fushi da b'acin rai. Wani irin mik'ewa ta yi ta re da finciko rigar Binty ta ba ya ta yar da ita a k'asa. Ta d'aga hannu kenan za ta d'auke ta da mari idanuwan ta ya sauka akan kyakkyawar fuskan Binty. Lumshe idanuwa Binty ta yi ta re da bud'e su a lokaci d'aya, sai hakan ya k'ara bayyanar da tsantsan kyawun ta. Gaban Sabrin d'in ya buga da k'arfi. Ta ke ta ji hannunta da jikinta na wani irin rawa. Sai kallon fuskan Bintyn ta ke yi without blinking. Fanan da tun sanda Binty ta bangaje Sabrin tai Sabrin b'oyewa don ta san tabbas idan har Sabrin su kai idanuwa hu'du da Binty sai ta ji zawo saboda kyawun ta. Dole ta muzanta don a yadda ta ke kururuta kyawun ta Bintyn ta fita sau hamsin. Cike da bak'in ciki, kishi, b'acin rai, zafin zuciya ta re da hassada ta nu na Binty da yatsa bakinta har rawa ya ke yi wajan furta, "Uban waye uban da ya haifi uban ki a k'asar nan da za ki bangaji d'iyar Alhaji Saifullahi mai Naira? Shin ba ki san gaba d'aya wannan wajan da ki ke na uba ba ne? Duk'a k'asa ki ba ni hak'uri ko in yi k'asa-k'asa da ke ko kuma in saka bodyguard d'ina su ba wa karnukan su ke su yi yaga-yaga da namar jikin ki a cikin nan wajan". "Ban san abunda na miki ba da zan ba ki hak'uri. Anna ta ce min ya na da kyau idan har ka yi wa mutum laifi ka ba shi hak'uri. Ki fad'a min abunda na miki sai in ba ki hak'uri kin ji". Wani haske Binty ta ga ni ya gilma ta fuskanta sai da ta yi saurin dafe kuncin ta saboda azababbar zugin da ta ji a wajan. Fanan da ke lab'e sai da ta zaro idanuwa jikin ta ya soma rawa domin ta san Binty ba ta san miye fad'a ba, domin ba za ta tab'a iya rama abunda Sabrin d'in ta mata ba. K'ok'arin fitowa ta soma yi daga mab'uyar ta domin ta isa wajan da su ke. K'amewa ta yi k'am, mamaki ya cika ta ta re da zaro idanuwan ta sakamakon wani irin mik'ewa da Binty ta yi ta d'auke fuskan Sabrin da mari ta re da fad'in, "Bazan d'auka ba. Anna ta fad'i min ka da na saki na zalinci wani, kuma ka da ba bari a zalince ni. Na tambaye ta menene zalinci, kuma ta min bayani. A bayanin da tai min, irin wannan abun da ki ka min yanzu, zalinci ne. Duk da Anna ta ce min in kasance mai hak'uri da juriya, amma ba zan iya hak'uri da wannan abun da ki ka min ba shiyasa na rama. Da kin fad'a min abundan na miki, da ni kuma zan ba ki hak'uri kamar yadda ki ka buk'ata. Ko yanzu ma ki ka fad'a min abunda na miki, zan ba ki hak'uri". Fad'in Binty ta na kallon cikin idanun Sabrin da ta mutu da mamaki. Domin idan aka cire mahaifiyar ta, babu wani mahaluk'in da ya tab'a saka hannu ya mari fuskan ta sai wannan yarinyar da ke gabanta da ta ke jin tsantsar tsanar ta har cikin b'argon ta.

"Binty, mai ki ka tsaya yi a nan wajan? Kun manta abunda na fad'a muku ko? To zo mu wuce. Ina Fanan d'in?". Ya Fu'ad ya fad'a. Saurin juyowa Binty ta yi ta re da nufo in da ya ke ta ce, "Yaya anan na bar ta, ban san in da ta yi ba". Fad'in Binty ta na waige-waige. Fanan na jin su, sai da su ka yi d'an nisa ka na ta kalli Sabrin da har a wannan lokacin ta na rik'e da kuncinta idanuwan nan na ta ya kad'a ya yi jazurr. Cikin sand'a Fanan ta bi bayan su Binty ba ta re da Sabrin d'in ta gan ta ba ta na jin wani irin farin ciki ya mamaye zuciyar ta saboda yadda Binty ta wanke fuskan Sabrin da mari.

Sabrin da ke tsaye kamar statue kuwa, ji ta ke kamar ta k'ona kan ta a wajan da ta ke. Abubuwa sun had'u mata goma da ashirin. Ga wanke fuskan ta da mari da Binty ta yi, ga kuma tsananin tashin hankalin da ta ke ciki na ganin wacce ta ninninkata a kyawu. Wani irin k'ara ta saki mai k'arfi wanda ya saka hankalin mutane dawowa gare ta, wasu kuma da gudu suka nufo inda ta ke...........

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull