Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 13

Ba ni da gata - Chapter 13

Ba ni da gata Chapter 13: Ba ni da gata Chapter 13. ............Hajiya Nai'ma zaune da waya a hannunta ta na lalubo number Kandala. Da kyar ta iya gano…

3,090 words

............Hajiya Nai'ma zaune da waya a hannunta ta na lalubo number Kandala. Da kyar ta iya gano numbern ta re da danna mata kira. Kandala da ke can kwance a kan k'atuwar katifat Datu k'awarta sai gwarti ta ke saki. K'arar wayarta ya dawo da ita duniyar mutane. A firgice ta farka ta re da laluban wayar ta danna madannin d'auka ta re da kara wayar a kunne ta ce, "Hallo". Cike da muryan bacci ta fad' hakan. "Assalamu alaikum". Fad'in Anna daga d'ayan b'angaran. "Ameen". Kandala ta amsa ta re da ware daga baccin da ta ke yi. Don ta ji muryan wacce ta kira ta bai mata kama da gajojin murya ba. Addu'a ta ke Allah ya sa samu ne. Don ba ta da number Anna. Annan ma ba ta tab'a kiran ta ba. "Ina magana da Kandala ne?". Fad'in Anna ta na k'ara gyara zaman ta. "Eh ita ce. Allah ya sa dai lafiya". "Lafiya k'alau ki kwantar da hankalin ki. Ki na magana da Hajiya Na'ima matar Alhaji Usman ne". Wani irin wuntsulowa ta yi daga kan katifar. Hantar cikinta ya wani irin murd'ewa waje d'aya saboda tsabar gigicewan da ta yi. Don duk a zaton ta asirin ta ne ya tonu. Su Hajiya Na'iman sun ga no ba ta da alak'a da Bintyn. "Na shiga uku ni Kande. Azabar son kud'i ne yau ya jawo min hukuncin kisan kai". Fad'in Kandala cikin zuciyar ta. Tuni har zufa ya jik'a ta. "Hello Kandala ki na ji na kuwa?". Fad'in Anna. "Hajiya dan darajar Allah wani laifin na yi? Ko kuma ita yarinyar ce ta mi ki wani abun?". Fad'in Kandala jiki na rawa. "Kandala na ce ki kwantar da hankalin ki. Ba ki yi komai ba. Asalima alkhairi ne. Idan ba damuwa ki zo yanzu ina nai man ki". Fad'in Anna ta re da katse wayar. D'aura hannu Kandala ta yi a kai ta re da rusa kuka kamar wacce aka ce mata uwarta ta mutu. Da gudu Datu ta shigo d'akin ta re da fad'in, "Ke Kandala lafiya ki ke kuka haka kamar an aiko miki Lami (Mahaifiyar Kandala) ta mutu?". "Ai idan Lamin ce ma ta mutu da sauk'i Datu. Kuka ne zan yi na kwana uku da jimami ya wuce da a ce gidan Alhaji Usman Mai rabo na tuhuma ta da sato y'ar mutane. Na shiga uku yai ni Kande. Yau zan had'u baba Shitu mahaifi gare ni ban gama jin dad'in duniyar ba". Fad'in Kandala ta na kuka har da fyace majina. "Ke ni fa wallahi wani lokaci haushi ki ke ba ni kamar na hau ki da duka. Ki min bayani dan Allah". Fad'in Datu da ke tsaye kan Kandala. Sai da ta k'ara fyace majina da bakin zaninta, ka na ta ce, "Datu, yanzu Hajiya Na'ima uwargidan Alhaji Usman Mai rabo ta kira ni akan in zo yanzu ta na nai ma ne. Duk da dai ta ce min in kwantar da hankali na ba matsala ba ce, wallahi hankali na bai kwanta ba. Sai na ke jin kamar k'ullalliya aka had'a min". "Mtswww! Wallahi ke sakaryace Kande. Ki ka sani alheri ne ke kiran ki tsiya na hana ki. To ni dai wallahi a nau shawarar ki je. Don irin wad'annan mutane ba k'ananan mutane ba ne. Ki cire tsoro kije wallahi ba bu komai. Amma fa idan kin ji. Idan kuma ba ki yadda ba, kar ki je ki yi wa kan ki". Fad'in Datu. "Ni gaskiya wallahi tsoro na ke ji, amma tunda kin ce haka, za ni. Amma dan Allah mu je ki raka ni". Fad'in Kandala. "Wa? Ni? Allah ya sauwak'e. Kin manta wani zuwa da ki ka yi da ni ke nan. Ai ban manta karo na da wanna shegen k'aton arnen da ke gadin k'ofar farko ba. Mai ya ke da suna, salaman ne ko Salemon? Oho. Wallahi ban zuwa. Kare fa ya sako mana. Uhmm wallahi a'a kam ba bu inda zani. Ke dai sai kin dawo". Fad'in Datu ta re da ficewa daga d'akin ta na k'ara maimai ta "Inahh". Fita Kandala ta yi ta je ba yi ta re da buga kwaskwarima ka na ta dawo ta d'auko bio-clear d'in ta ta mutstsika a jikinta da fuskanta. Sannan aka d'auko hota aka ranbad'a ta re da jan gira da kwalli. Fuskan nan ta fito ranba'dau kamar an shafawa jaki powder. Ka na ta bud'e ghana must go d'in ta ta fiddo brezia irin mai tsinin nan ta saka ta re da saka wata doguwar rigar atampa robber cotten irin na fita anguwan nan. Ta d'auko gyalan nan na ta tissue ta saka ta re flat shoe na roba da kuma latest jakarta ta rataya ta fito. Da ma tuni Datu ta bar gidan ta yi mak'ota don shan sigari kasancewar mai gidan ya hana shan sigari a gidan sa. Jawo k'ofar ta yi ta re da ficewa daga gidan. Sai da ta yi d'an tafiya sannan ta samu taxi. Nan ma sai da su ka kwashi kimanin mintuna talatin ka min su ka iso layin su Alhaji Usman. Gaban gate d'in ta nu fa gaban ta na fad'uwa don ba ta san abubda za ta taras ba a gidan. Kwankwasa gate d'in ta yi hannunta har ya na rawa. "Who be that?". Oga Solomon ya fad'a sai da gaban ta ya fad'i. "Na me Kandala". Fad'in Kandala bakinta har rawa ya ke. "U mean dat stupid old bitch way they bring small pikin to work here?". Fad'in Solomon. "Yes na me". Fad'in Kandala. Tsaki Solomon ya yi ta re da bud'e k'aramin gate d'in ya na kallon ta from head to toes. "Enter abeg. Use less human. God go punish you". Fad'in Solomon ta re da matsa mata ya na kuma fatan Allah ya sa kiran ta a ka yi domin ta mai da yarinya gaban iyayan ta saboda abunda ya faru jiya-jiya daga zuwan ta gidan. Sum-sum Kandala ta shige ta na hararar gaban ta ala dole da Solomon d'in ta ke da bai ma San ta na yi ba sai antaya mata zagi ya ke da yaran Ibgo ta re da d'ebe mata albarka. Side d'in Hajiya Na'ima ta nu fa ta na mai addu'ar Allah ya sa ka da d'aya daga cikin y'an aikin Hajiya Mansura su gan ta su je su shaida mata. Don kan ta ba zai iya d'auka matsalar ba. Sallama ta yi a parlour. Fasila da ke mopping ta amsa mata ta re da ce mata ta shigo. Shigowa ta yi ta re da zama a kan lallausar center carpet d'in d'akin har da tankwashe k'afa. Fasila kuwa, cigaba ta yi da goge-gogen ta. Don ba ta da damar haurawa sama idan ba izinin aka ba ta ba ta je ta d'auko wanki ta kai washing room. Shuru-shurun da Kandala ta ji ne, ya sa ta fiddo wayar wacce ake kira da sha k'idan ka bak'auye ta danna number Hajiya Na'ima kasancewar shine last call d'in da ta yi receiving. Sai da wayar ta kusa tsinkewa ka na Hajiya ta d'aga. Cikin sauri Kandala ta ce, "Barka Hajiya. Tun d'azu ina parlour". Fad'in Kandala har da rusunawa kamar Hajiya Na'iman na ganin ta. "Ok. Jira ni ga ni nan zuwa". Hajiya Na'ima ta fad'a ta re da katse wayar. Mintuna goma ta fito cikin kyakkyawan shiga. Sanye ta ke cikin doguwar rigar shadda d'in kin y'an Senegal da ya amshi jikin ta. Babu yadda za'ayi ka kalle ta ka ce ta kusa hamsin saboda sam kyawun jikinta da yadda ta ke gyara kan ta ya b'oye tsufan ta. "Yi hak'uri Kandala na barki ki na ta jira. Ba ri na sa a kawo miki abun tab'awa". Fad'in Anna ta re da kiran Fasila da ke kitchen. Cikin sauri Fasila ta k'ariso ta re da duk'awa ta ce, "Hajiya ga ni". "Had'o mata abinci da lemu ki kawo mata". Anna ta fad'a ta re da mai da duban ta ga Kandalan. "Ina kwana Hajiya?". Fad'in Kandala ta na wani russunar da kai k'asa kamar ta kirki. "Lafiya k'alau. Idan kin ga ma cin abincin ki min magana ta waya. Zan sauko sai mu yi maganar". Fad'in Anna ta re da mik'ewa daga kan kujera ta yi hanyar upstairs. Ajiyar zuciya Kandala ta saki dai-dai lokacin da Fasila ke ajiye mata yam bones da tea a gaban ta. Da ma ci ke ta ke da yunwa. Aikuwa ta cinye tas ta re da shanye tea d'in ka na ta d'auki wayarta ta re da danna numbern Hajiya Na'ima ta shaida mata ta ga ma. Minti biyar Hajiya Na'ima ta sauko hannunta d'auke da wayarta a kunnanta ta na waya. Har ta k'araso ta zauna ba ta gama wayar ba. Ta kusa minti goma ka min ta gama waya da babban d'an na ta Julaibib. "Yi hak'uri Kande, na barki ki na ta jira na". Fad'in Anna. "Ahh wallahiba komai Hajiya". Kandala ta fad'a ta na sunkuyar da kai gabanta ba fad'uwa. Don ta k'osa ta ji abunda ya faru Hajiyan ta kira ta. "Kandala ba komai ya sa na kira ki ba sai akan d'iyar ki Binty". Ta ke cikin Kandala ya ba da sautin k'ulululu. Ta kalli Hajiya ta re da fad'in, "Allah ya sa ba wa ni laifin ta miki ba". Fad'in Kandala a marairaice. "Babu abunda ta yi Kandala. Sai dai ni ne ke da wani buk'ata idan har iyayanta za su amince". Fad'in Anna ta na kallon idanun Kandala da ya yi fik'i-fik'i. "Hajiya faf'i buk'atar ki idan bai fi k'arfi na ba mai zai ha na in miki. Ai kin wuce haka a waje na". Kandala ta fad'a. "Kandala so na ke in rik'e Binty a waje na har in aurar da ita kuma ba matsayin y'ar aiki ba idan har iyayanta za su yarda. Kuma ka da su da mu, nasan kud'i su ka turo ta ta nai ma. Ni na yi alk'awarin duk wata zan rik'a ba ku dubu hamsin ku yi hidiman ku. Ni Binty kawai na ke so in rik'e in saka ta a makaranta domin ba aiki ba ne ya kama ce ta, karatu ne ya da ce da ita. Amma fa idan kun amince". Fad'in Anna. Hawaye Kandala ta so na yi tare da sharewa da k'asan rigarta ta na fad'in, "Hajiya Allah ya sa ka miki da alkhairi. Wallahi ban da bakin da zan iya miki godiya. Wannan yarinya da ki ke ga ni. Ni ce komai na ta, ni ce uwarta ni ce ubanta. Marainiya ce gaba da bayanta, k'ani na uwa d'aya uba d'aya ya haife ta. Tun ta na ciki yan bindiga dad'i su ka shiga k'auyan mu su kai kashe-kashe, a ciki har da mahaifinta da sauran y'an uwa na. Mahaifiyar ta kuma ta na haihuwarta Allah ya amshi abunsa. Tun daga lokacin ta ke waje na. Ni kai na a wannan kashe-kashen a ka kashe nawa mijin ga ni da marayu har shidda, idan kin ha'da Binty sun ka ma bakwai. Wannan dalilin ne ya sa mu ke yawon aikatau birni don mu samu muci abinci. Binty ce kawai ban tab'a kaiwa aikatau ba. Amma saura y'ay'a na mata hud'u duk su na aikatau. Mazan ne k'anana ke gaba na su ma kuma duk na saka su sana'a. Ita ma Binty ganin ta kawo girma ne, nan da shekaru biyu za ki ha manema sun fito. Shiyasa na turo ta nan domin ta yi aiki mu samu mu tattala kud'in ai mata kayan d'aki da su. Wayyo Binty marainiyar Allah". Kandala ta k'arisa maganar ta re da rushewa da kuka. Sosai Hajiya Na'ima ta ji tausayi ya ka ma ta. Yanzu "Kenan yanzu wannan yarinya ba dan Allah ya turo ta nan ba, da yanzu nan da wasu shekaru biyu masu zuwa aure za'a mata kenan da duhun jahilci a kan ta. Gaskiya dole ma yarinyar nan ta dawo waje na". Fad'in Anna cikin zuciyar ta, a zahiri kuma ce wa ta yi, "Allah sarki! Allah ya jik'an mahaifan ta da kuma mijin ki. Allah ya k'ara maku hak'urin rashi. Amma tabbas ku abin tausayi ne. Idan har za ki amince min, ina son Binty ta kasance a waje na. Sannan saboda marayun da ke gaban ki, na k'ara miki hamsin akan kud'in da zan ba ki duk wata sun zama dubu d'ari sai ki kula da sauran marayun da ke gaban ki, ki kuma sa ka su a makarantar islamiya da na boko. Don zama da jahilci bai yi ba". "Wallahi Hajiya in dai Binty ce na bar miki ita halak, malak. Wallahi na ba ki. Ai nasan gidan mutunci na kawo ta. Hajiya nagode, nagode Allah ya sa ka miki da alkhairi ya k'ara girma". "Ba bu komai Kandala, ai yi wa kai ne. Sannan duk wani abu da ki ke buk'ata ki min magana ka da ki ji kunya. Yanzu idan za ki tafi, zan had'a ki da kayan abinci, sai driver ya kai ki. Bintyn bacci ta ke yi, shiyasa ba ta zo kun gaisa ba". "Ai babu komai Hajiya, idan na sa ke zuwa ma gaisa ai". Fad'in Kandala cike da farin cikin riba biyu da ta sa mu.

Kamar yarda Hajiya ta ma ta alk'awari, da za ta tafi ta had'a ta da babban buhun shinkafa foreign buhu hud'u, buhun semo guda hud'u, couscous katon biyu, taliya da macaroni katan uku-uku. Baban gwangwanin madara guda hudu, suger loka ashirin, mangyad'a rabin abod, manja ma haka. Sai maggi star katon biyu ta re da k'arin dubu d'ari. Haka aka loda mata a mota. Sosai Kandala ta b'arke da kuka harda fyace-fyacen majina. Ba kukan komai ta ke yi ba face na dad'i. Ta tabbatar wa kanta Binty sa'ar da alkhairin ta ce. "Dan Allah ki bar kukan nan Kandala. Duk wani abunda ki ke buk'ata ki ma ni magana". Fad'in Anna. "Nagode sosai Hajiya. Allah k'ara girma". Fad'in Kandala ta re da shiga mota driver ya ja ta re da kai ta har k'ofar gidan Datu aminiyarta. Ganin irin uban kayan abincin da ake ta shigowa da shi ne ya sa Datu fitowa k'ofar gidan don ganin waye zai bud'e shago sai idanuwan ta ya sauka akan Kandala ta na baiwa yaran da ke shigar mata da kaya umarni. Ai k'arisa fitowa Datu aka cigaba da shigar da kaya ta re da ita. Sai bayan sun shigar da komai d'akin Datun ka na Datun ta kalli Kandala ta re da fad'in, "K'awas ya na gan ki da sha tara haka?". "K'awa ai ni kaka ta ta yanke sak'a wallahi". Tu ni Kandala ta zayyane wa Datu duk yadda su kai da Hajiya Na'ima da kuma irin k'aryar da ta shatata wa Hajiyan. Sai dai ba ta fad'a ma ta ainahin yawan kud'in da Hajiya Na'ima ta ce za ta rik'a ba ta duk wata ba. "Kin ga abunda na ke fad'a miki ko? Da kin ma kan kin salalar tsiya wallahi. Ah gaskiya Kande kin shigo Habuja da k'afar da ma. Yanzun ya za ki yi da wad'annan uban kayan abincin?". Fad'in Datu. "Sayar da su zan yi, amma zan aje mana wanda za mu rik'a ci ai". Fad'in Kandala. "To ni kuma miye nawa kason a cikin dubu arba'in d'in da za ki rik'a karb'a duk wata?". Datu ta fad'a. "Zan rik'a ba ki dubu goma duk wata. Sannan zan rik'a ajiye dubu biyar duk wata na haya. Daga yanzu na d'auke miki biyan kud'in haya". Kandala ta fad'a. "Kai shiyasa na ke k'aunar ki k'awata. Hanzarta maza in raka ki ki sai do da kayan, kin san na fi ki sanin kan kasuwa. Kin san ni ai". Fad'in Datu. "Aiko dai bari in ta shi". Kandala ta fad'a.

..........Bayan Alhaji Usman ya dawo da daddare, Hajiya Na'ima ta shaida masa duk yadda su ka yi da Kandala. Shi kan shi sai da ya tausaya masu, kuma ya umarci Hajiya Na'ima akan duk wata idan ta zo karb'an kud'i, to a had'a mata har da kayan abinci ma'ishi. Sosai hakan ya yi wa Hajiya Na'ima dad'i.

Tun daga wannan ranar Anna ta d'auki d'ammarar kula da Binty. Da kan ta ta ke koya ma ta wasu abubuwa na addini. Idan malam ya d'aura mata karatu, kullum Anna sai ta tsare ta ta yi ma ta karatun da malam d'in ya masu. Gyefe guda kuma, kullum da daddare dai sun yi bitan yaran fulatanci ita da Fanan. Kuma da ya ke Allah ya mata kwakwalwa, nan da nan ta ke d'auke abun. Gaba d'aya satin ta d'aya da zuwa, amma ta haddace suratul fatiha kuma babu kuskure. Ga ta da zak'in murya. Anna kuwa ko k'ofar parlour ba ta ba ri ta je balle ta fita waje Suhaila ko mahaifiyar sa su gan ta. Maganar boko kuwa, Anna ta ce sai first term, shekara mai zuwa kenan. Don so ta ke ta d'auko lesson teachern da zai koya mata karatu kwakwalwar ta ya bud'e tukun. Fanan ba ta ji dad'in haka ba, amma haka nan ta hak'ura. Anna ba'a nan ta tsaya ba, kasancewar gwana ce wajan girki, duk lokacin da za ta had'awa Alhaji Usman girki, da Binty ta ke zuwa ta yi ko mai a gabanta duk da dai ba ta tab'a ba ta wani abun ta yi ba. Don ranar da ta fara shiga kitchen da ita ta kunna gas. Binty rud'ewa ta yi ta re da fasa ihuu ta fita daga kitchen d'in da gudun. Ba k'aramin tsoro gas d'in ya ba ta ba. Da kyar ta yadda ta soma tsayawa a gaban gas d'in amma ta na d'ari-d'ari. Kasancewar ta na da tambaya, duk abunda ta ga Anna ta yi sai ta yi tambaya a kai, hakan ya sa ta ke sanin wasu abubuwa sosai ga me da girki. Don ko ruwa Anna ta k'ara a girki ko ta saka ingredients sai Binty ta tambaye ta miye dalili. Anna kuwa ba ta gajiya da ba ta amsa. Tuni har Anna ta samo mata lesson teacher mai su na Mashkur. Daga k'arfe 10-12 su ke karatun boko. Na islamiya kuwa k'arfe uku don sai Fanan ta dawo daga school saboda ta re ake ma su karatun kuma ana parlourn k'asa. Tuni Binty ta sa ki jikin ta kamar dama y'ar gidan ce. Fasila kuwa duk duniya ji ta ke babu wacce ta tsana kamar Bintyn. Don gani ta ke ita da ta d'au shekaru a gidan ba'a mata irin wannan gatan ba sai ita da ta zo jiya-jiya. Wannan dalilin ne ya sa ta ke jin haushin ta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull