Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 12

Ba ni da gata - Chapter 12

Ba ni da gata Chapter 12: Ba ni da gata Chapter 12. *WASHA GARI* Da asubar fari Anna ta je ta ta so su Fanan da Binty ta re da umartar su da su yi wanka ta…

2,307 words

*WASHA GARI* Da asubar fari Anna ta je ta ta so su Fanan da Binty ta re da umartar su da su yi wanka ta re da d'aura alwala su gabatar da sallah. Binty kuwa a tsayin rayuwarta bata tab'a baccin mai dad'i irin wannan da ta yi ba a katifa mai laushi ga sanyin AC har yawo yaso ya mata don sai da ta ja bargo har kanta. Fanan d'in ce ta soma wanka ta re da d'auro alwala, ka na Binty ita ma ta je ta yi. Ta re su kai sallar, duk abunda Fanan ta yi, haka Binty ke yin. Sai wannan karan, wus wus wus, ta ke ta fad'i kasancewar ta ji sautin fitar karatun Fanan d'in sai ta yi tunanin haka ake cewa. Bayan sun idar, Fanan ta d'auko su ka shafa. Ka na Fanan d'in ta d'auko gogaggun uniform d'in ta, ta saka. Skirts d'in ta saka, ka na ta saka vest sannan ta saka rigar sama mai dogon hannu. Ka na ta d'aura suite d'in a sama ta re da b'ame botur. Ba k'aramin kyau kayan su ke ma jikinta ba. Ta je gashinta ta yi ta re parking d'in sa a tsakiya kamar yadda ta saba idan za ta school, ka na ta saka hula ta re da baby hijjab. "Fanan kin yi kyau a cikin wannan kayan". Binty ta fad'a ta na k'ara kallon kayan jikinta. "Ke ma kin kusa sa ka su very soon". Fad'in Fanan ta na saka white socks a k'afarta. "Dan Allah dagaske ni ma zan sa ka? Zan rik'a zuwa makarantar ku?". Fad'in Binty out of exited. "Sosai ma kuwa. Na yi wa Anna magana kuma ta ce za ta saka ki". Fad'in Fanan d'in ta na saka workbook d'in da ta yi assignment jiya a cikin Jakarta. "Na ji dad'i sosai. Ni ma zan shiga makaranta in rik'a yaren da ku ke yi da Anna". "Ke wannan yaran Anna ne ai. Fulatanci ne. Ku ma ke ma idan mu na yi a gaban ki a hankali za ki iya". "To ku rik'a yi dan Allah, ni ma na koya. Ko kuma idan za mu yi bacci, ki rik'a ko ya min". Fad'in Binty. "To shikenan, za mu fara daga yau idan na dawo school. Yanzu tashi mu je mu gaida Anna da Daddy". Fad'in Fanan ta re da yin hanyar k'ofa Binty ta mara ma ra baya. Part d'in daddy da ke sama su ka nufa. Kusan zan iya cewa parlourn sa ya fi duka parlourn da ke part d'in kyau da kuma tsaruwa. Zaune ya ke akan 1sitter ya na kallon BBC news, hannun shi rik'e d'an karamin cup irin na buzaye, amma na shi na glass ne mai kyau ya na sipping shayin da ya ji kayan k'amshi. A gaban shi a kan centre table flasks ne mai d'auke da shayi a ciki. Sai kwalin sugar cube a gyefe. Sallama su ka yi ta re da tsayawa a ba su izini tukun. Don k'a'idar Alhaji Usman ne sai ya ba ka izini ka min na shigo masa d'aki. Amsa sallamar ya yi ta re da ba su izinin shigowa. Fanan ta kama hannun Binty su ka shiga. Duk'awa Fanan ta yi, Bintyn ma ta duk'a kamar yadda Fanan d'in ta yi a gaban daddy da ke kallon su ya na murmushi. "Ina kwana dad?". Binty ma ta kalli daddyn ta re da fad'in abunda Fanan ta ce. Kallon Bintyn ya yi, domin yana nazartar ta. Domin jiya kusan raba dare su kai shi da Hajiya Na'ima su na magana a kan ta. "Lafiya k'alau daughters. Har kin yi shirin makaranta Fanan?". "Eh dad. Da 7:00am ya yi zan wuce. Breakfast kawai zan yi". "Masha Allah!". Daddy ya fad'a ta re da mai da kallon sa izuwa ga Binty ya ce, "Binty ya sabon waje? Hope kin ji dad'in zuwan ki gidan nan?". Kasancewar sauran maganar da Hausa ya yi, shiyasa ta fahimci mai ya ke nufi. Ta ba shi amsa da, "Eh dard (Dad). Na ji dad'i sosai. Mutanan gidan su na da kirki. Har da ya Fu'ad ba". Fad'in Binty ci ke da farin ciki. "In sha Allah za mu yi magana da wacce ta kawo ki nan, ta yi wa iyayanki magana KI dawo nan gaba d'aya da zama sai mu saki a makaranta ke ma ki yi karatu kamar yadda kowace yarinya mai gata ta ke yi. Ke ma ki samu wannan gatan. Kin ji". "Nagode dard (dad)". Fad'in Binty kamar ta taka rawa. Fanan kuwa sai k'umshe dariyar ta ke yi saboda yadda Binty ke pronouncing dad. "Ku ta shi ku je ku karya ka da ki yi latti. Seven d'in ta kusa". Fad'in dad ta re da sipping tea d'in shi.

Tashi su kai yi ta re da fita su kai part d'in Anna. Gadon ta su ka taras ta na gyarawa. Don ita sam ba ta yadda y'ar aiki ta gyara mata d'aki ba. Babu y'ar aikin ma da za ta iya cewa ta san kalar d'akin. Da kan ta ta ke gyara d'akin ta. Sai idan weekend ne sai ta saka Fanan d'in ta wanke mata bayi da kuma gyara d'akin. Duk da kuwa kasancewar Hajiya Na'ima d'iyar k'anin Sarkin Gombe. Hakan bai sa ta d'auki d'abi'ar nan na komai baiwa ta yi maka ba. Kuma hakan koyarwa mahaifiyar su ce. Lokacin auran ta ma sai da aka gad'o ta da kuyangu kusan bakwai, amma ta ce ita ba ta so, bautan ubangiji ta zo ba zama a mata hidima ba.

"Anna sannu da aiki. Ba ri na k'arisa gyaran gadon". Fad'in Fanan ta na k'arisawa wajan Annan d'in. "No bar shi ai na gama". Anna ta fad'a ta na shimfid'a bargo a gyefan gado. "Ina kwana Anna?". Fanan ta fad'a. Ka min Anna ta amsa, Binty ma ta ce, "Anna ina kwana?". "Lafiya k'alau yara na. Kun dai yi sallah ko?". "Tun da ki ka tashe mu ai ba mu ko ma ba. Mun yi sallah. Kuma yau ta re mu ka yi. Duk abunda na yi, shi ta yi ita ma. Yau ba daga sujada ta fara sallah ba". "Alhamdulillah! Ki yi ko ya mata, za ta iya a hankali. Yanzu mu je ku yi breakfast ki wuce makaranta, kar ki yi latti". "To Anna". Fad'in Fanan. "Anna dan Allah wanene kwana da yinin da kullum safe da rana sai in ji mutane da yawa su na nai man shi?". Fad'in Binty ta na kallon Anna. "Ban ga ne ba Binty, a ina ki ka ji a na nai man na su?". Fad'in Anna ta na kallon Bintyn. "To Anna d'azu munje wajan dard mun ce masa ina kwana. Yanzu ma mun zo mun ce miki. Kuma duk lafiya ku ke cewa. To shi kwanan ya na ina? Ba'a ganin shi sai dai ai ta nai man shi". Dariya ce ta kufcewa Anna da Fanan suka kuwa da ra sosai. Anna ta ce, "Rai dai Binty. In sha Allah idan Allah ya ara mana rai wata rana sai na tsokane ki da wannan tambaya ta ki. Yanzu ku je ku karya kun ji. Komai ya na nan shirye a dinning". Da to su ka amsa mata ta re da fita daga d'akin su kai wajan dinning da ke nan sama. Fanan ce ta had'a ma su tea d'in a cup ta turawa Binty na ta a gabanta ta re da chips. Sosai ta zuba mata chips d'in don ta ga ba laifi a kwai ta da ci. Bayan sun gaba me, Fanan ta goge bakin ta da tissue ta re da mik'ewa ta d'auko jakarta a d'aki. Wajan Anna ta koma ta re da mata sallama ka na ta dawo parlour ta sa mi Binty a kan 3sitter har ta yi bacci. Ficewa ta yi daga parlour ta sauka k'asa. Fasila ta ga ni rik'e da k'aton plate shak'e da abincin ta nufi hanyar fita daga parlour za ta koma side d'in su na maids. Fasila na jin takun tafiya duk ta daburce. Juyowa ta yi, idanuwan ta su ka sauka a kan Fanan ta na kallon ta. Guilty ya ka ma ta, ta ka sa magana sai yak'e ta ke yi. Fanan kuwa k'arasow ta yi ta gitta ta ta re da ficewa daga d'akin don ba yau ba ne na farko da ta kama Fasilan na ma su satan abinci, duk da kuwa ta san idan ta tambaya ba hana ta za'ayi ba. Driver ta sa mu a gaban side d'in su kad'an ya na jiran ta. Hango Suhail da ta yi ya na tahowa ya sa ta ari na kare ta re da saurin shiga mota ta na cewa driver, "Muje, muje please ka min ya iske mu ya kashe ni da safan nan". Jazuli driver kuwa ya yi wa mota key da sauri ta re da reverse ya nu fi gate. Hankalin Fanan bai kwanta ba, sai da ta ga sun fita daga gate d'in k'arshe (gate d'in Solomon) sun d'au hanyar school d'in su. Dogon ajiyar zuciya ta sa ki ta re da kwantar da kanta a jikin motar.

*LEAD BRITISH INTERNATIONAL ACADEMY ABUJA*

Tun daga tsarin gate d'in makarantar kawai mutum zai kalla zai tabbatar wa kan sa makaranta ce irin na y'ay'an ma su fad'a aji. Kyawawa kuma masu tsadar motoci ne ke parking a harabar makarantar su na sauke d'alibai wannan na wane wannan. Domin duk yarinyar da ka ga ni cikin makarantar to hak'ik'a ubanta wani. Registration d'in makarantar kawai 1m ne. Du term kuma 700 thousands. Cikin makarantar kuwa, tsaruwar ta ya fi gaban kwatance. Za ki rantse da Allah a k'asar waje ki ke ba Nigeria ba. Fanan da ce ta nuna IDcard d'in ta ka na ta shiga makarantar ita da k'awayanta su hud'u. Jamila Muhammad Giwa, Asiya Abdulwahab Girai, Rukayyah Adam Saje, da Salima Mustapha Yawale. Sai it's cikon na biyar d'in Fanan Usman Mai rabo. "Pinky, jiya an yi show a capteria lokacin ki na library. Na so na ba ki labari sai drivern ki ya zo da wuri". Fad'in Asiya Abdulwahab Girai. Wacce su ke kira da Girai to make the name short. "Mai ya faru? Na san ba zai wuce akan Cinderella ba. What did she do again?". Fad'in Fanan still tafiya su ke yi don zuwa assembly. "She slapped Fayrouz in the present of everybody". "What? Do you mean slap?". Fanan ta fad'a ta na shafa fuskan ta. "You de hell did she think is she. Wallahi a hate that girl with passion. She's so proud, just because she's beautiful". Fad'in Salima wacce su ke kira da yawale. Wa ni killer smile Binty ta sa ki ta re da fad'in, "Cool down babes, ba dai tak'amar ta kyau ba? Wallahi cikin Month d'in nan ko kuma next term sai na bata mamaki. Sai na kawar da taurarin ta da ke haske a makarantar nan". Fad'in Fanan ta na murmushi. "Wait Fanan? What are you planning for her. Dan Allah ka da ki watsa mata acid". Fad'in Ruk'ayya wacce su ke kira da Saje. "Allah ya kiyaye. Ban tab'a wannan tunanin ba. Amma dai just wait and see". Fad'in Fanan dai-dai lokacin da su ka is a assembly ground da kallon shi kad'ai ma ya isa ya rikita mutum.

*BA NI DA GATA ISN'T FREE, IDAN KIN GA YA NA YAWO A GROUPS KUAM BA KI SIYA BA, DAN ALLAH KAR KI KARANTA. CONTACT THIS NUMBER 08128755583* 🌹 *25-26*🌹

*Bonus ✋🏻😂* *Naji k'orafe-k'orafen ku, to k'orafi ya karb'u. Na mai da Normal group #300, VIP kuma #500. Sai ki hanzarta ki bi ya ta wannan account numbern, 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK. Sai ki tura evidence d'in ki zuwa ga wannan number 08128755583*

Sanye ta ke cikin suit kalar dark purple, sai na cikin shi kuma light purple, coat d'in rik'e a hannunta wanda ya kasance shi ma dark purple. Sai baby hijjab d'in da ke jikinta shi ma dark purple. Skirt d'in dai-dai gwiwarta. Sai fara k'al d'in safa da da ya wuce wuyan sahunta. Takalmin k'afarta mai bala'in kyau kalar dark purple. Jakarta light purple sagale a kafad'arta. Yadda ta ke wani shan k'amshi da wasu abubuwa, za ka rantse budurwa ce. Nan kuwa shekararta goma cikin na sha d'aya. Gaba d'aya k'awayan ta y'an koranta suna kusa da ita. Su su ke k'ara fasa mata kanta ta ke jin duk duniya ta fi kowa. "Cinderella, kalli can, yarinyar can Pinky ta zo. Kalli sai wani shan k'amshi ta ke yi". Wani d'ago idanuwan ta yi ta kalli pinkyn da ta ke jin k'ololuwar tsanarta duk fad'in school d'in nan na su. Ji ta ke da a ce Allah zai ce ta kashe mutum d'aya a duniya kuma ba ta da laifi, to tabbas za ta kashe Fanan. Kasancewar mahaifin Fanan d'in ya fi mahaifin ta kud'i. Da kaf school d'in mahaifin Sabrin ya fi kowa kud'i. Lokaci guda Fanan ta shigo makarantar. Kuma tun daga teachers d'in har students, shakkarta su ke yi saboda kud'in mahaifin ta da yadda ya yi su na a garin Abuja da ma wasu garuruwan. D'auke kai ta yi daga kallonta ta re da jan tsaki a bayyane ka na ta ce, "Don't ever show her face to me again. If not, you're out of this team". Fad'in Sabrin ci ke da gadara. "As you wish Ella". Fad'in k'awarta Saudat Lere. Bayan sun gama gabatar da assembly kowa ya tafi zuwa various classes d'in sa. Ajujuwan su kawai abun kallo ne. Ko wani d'alibi akwai laptop a gabansa da ke kan wani table. Ya yin da malami ke can sama shi ma da nashi laptop d'in a gaban sa. A haka ake masu karatun. Duk da akwai k'aton White board a class. Sai lokaci bayan lokaci ake masu amfani dashi. Musamma calculation subjects. Irin su maths da quantitative.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull