Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 11

Ba ni da gata - Chapter 11

Ba ni da gata Chapter 11: Ba ni da gata Chapter 11. .........."Kar ko da wasa wanda ya fita da ke yau ya sa ke kiran ki, ki bishi. Kin ji abunda na ce…

3,481 words

.........."Kar ko da wasa wanda ya fita da ke yau ya sa ke kiran ki, ki bishi. Kin ji abunda na ce miki?". Anna ta fad'a ta re da rik'e kunnanta d'aya. "Eh Anna na ji. Yaya Fu'ad ma ya ce min haka. Wai idan na saki wani namiji ya tab'a ni, zan mutu. Ya ce ka na yi wasa da maza idan ba haka ba zan mutu". "Abunda ya fad'a gaskiya ne. Ba ke kad'ai ba, dukkan ku har da ke Fanan". Fad'in Anna ta re da mai da dubanta ga Fanan d'in da ke kwalalo idanuwa. "Now go and perform ablution and pray. And don't forget to teach her how to pray". Fad'in Anna saboda kiran sallar la'asar d'in da ake yi. Fanan ce ta soma mik'ewa saboda Binty ba ta san mai Anna ta ce ba kasancewar da turanci tai maganar. Hannun Binty ta rik'e ta re da fad'in, "Mu je mu yi sallah sis". "A'a ni bazan yi ba, ke ki je ki yi. Ni na gaji yau bazan yi ba sai gobe da safe. Dama ni sau d'aya kawai na ke yi. Shi ma Hadaan ne ya ce na rik'a yi idan ba haka ba Allah zai saka ni a wuta". Fad'in Binty ta re da zame Hannunta ta kwanta a kan carpet. Zaro idanuwa Anna ta yi ta re da fad'in, "Binty ai duk wanda bai sallah wuta zai shiga. Banbancin mu da arna kenan ai. Dole ne ki yi duka salloli guda biyar a kowace rana". "Anna menene arna? su waye arna? Su ma mutane ne?". Kallonta Anna ta yi cike da tausayi da kuma mamakin daga wani k'auye ta fito da ba su san addini ba haka. "Binty ina ne k'auyan ku?". Fad'in Anna ta na kallon ta. Shuru Binty ta yi ta na tunanin sunan da Kandala ta fad'a mata idan an tambaye ta garin su. Can ta ce, "Can k'auyan Saminaka". Fad'in Binty ci ke da jin dad'in tuno sunan da ta yi. Jinjina kai Annah ta yi ta re da fad'in, "Binty Arna su ne wad'anda ba su bin duk abunda Allah ya ce ayi. Ba sa sallah, Ku ma ba su yadda da fiyayyan halitta Annabi Muhammad SAW ba, sanna ba su yadda Annabi Isa ba Allah ba ne". Fad'in Anna. "Annah wanene Annabi Muhammad, kuma wanene Annabi Isah?" Fad'in Binty ita ma ta na kallon Anna. "Ohhh may God! Binty ba ki san su ba? Amma dai ba kya zuwa islamiya ko? Ai duk musulmi ya san tarihin su. Kuma yasan su Annabawa ne da Allah ya aikowa mutane". "Quiet please". Anna ta fad'a ta re da kallon Fanan d'in. "Annabi Muhammad SWA shine manzo na k'arshe da Allah ya turo. Allah ya turo shi ne domin ya wa'azantar da al'ummar sa domin su bi hanya na gaskiya. Haka shi ma Annabi Isa". "Menene wa'azi Anna? Kuma su waye su ke bin hanyar dai-dai, kuma suwa su ke bin wanda ba dai-dai ba?". Binty ta sake fad'i. Ajiyar zuciya Anna ta sauke ta re fad'in, "Binty ku je ku yi sallah, a hankali za ki ga ne komai idan har za ki nutsu wajan malam. Zai koya miki komai. Kuma ki masa duk tambayar da ki ke son yi kin ji? Kuma ka da ki sake cewa ba za ki sallah ba. Sallah wajibi ne akan kowani musulmi". "To Anna. Daga yau kullum zan rik'a sallah". "Good girl. Allah ya mu ku albarka. Ku je ku yi sallah". Fad'in Anna. Mik'ewa Binty ta yi, Fanan ta ka ma hannunta su ka wuce d'akin Fanan d'in don gabatar da alwala da kuma sallah.

Sosai hankalin Anna ya ta shi da irin jahilcin da Binty da kuma jama'ar k'auyan su ke fama da shi. Yanzu kenan duk kallan da su ke wa Kandala ita d'in jahila ce. "Wannan yarinya Sam ba da aikatau ta da ce ba, da makaranta ta da ce. Ga kyau iya kyau amma kwakwalwa cushe ya ke da kashin kafinta. Dole na yi tsaye a kan yarinyar nan ta yi makaranta kamar yadda zan yi a kan Fanna. Wannan yarinya na zama uwarta da ubanta. Babu wanda ya isa ya karb'e ta a hannu na. Zan tsaya iya tsayin daka naga ta samu ingattaccan ilimi da izinin Allah. Ta yadda za ta ceto k'auyan su daga halakar da su ke ciki. Ya Allah ka taimaka min a kan haka". Fad'in Anna ta re da d'aga hannu sama ta na rok'an Allah.

*8:15pm* Wasu had'ad'd'un motoci guda tara ne su ka danno cikin layin. Hu'du a gaba, hu'du a baya. Sai guda d'aya a tsakiya wanda Alhaji Usman Mai rabo ya ke ciki ya na duba sak'on email a wayarsa. Horn su ka danna. Oga Solomon da ke magana k'asa-k'asa da Baban Haruna ya zabura ya mik'e ta re da fad'in, "Baban Haruna, Alhaji is back". Ya fad'i hakane ta re da sauri isa ya wangale gate d'in. Takwas d'in farkon nan su ka shiga ciki ka na motar da Alhaji Usman ke ciki ya danno kai. Tsayawa driver ya yi, domin ya san Alhaji a nan ya ke sauka domin ya duba ma'aikatan sa. Duk nisan da ke tsakanin gate d'in farko da kuma ainahin cikin gida, haka ya ke tafiya a k'afa don kaf sai ya ji lafiyar ma'aika da kuma idan su na buk'atar wani abun ka min ya k'arasa wajan iyalansa. Aje tsaleliyar wayarsa ya yi a kan briefcase d'in sa. D'aya daga cikin bodyguard d'in sa ya fito da sauri ya bud'e masa murfin mota. Kyakkyawan k'afarsa ya fara fito da shi, ka na ya fito da gangan jikinsa. Saboda yadda gaba d'aya gidan ta ko'ina akwai globes farare, dai gidan yai haske kamar ba dare ba. Ko babu wutan nepa su na da k'aton jen *MIKANO* standby a gidan. Babu yadda za'ayi kazo gidan ka ga ba wuta. Gaba d'aya ma'aikata da su ke wajan su ka k'araso su na kwasar gaisuwa. Shi kuwa dattijo cike da fara'a da kamala ya ke amsa masu kamar ba ma'aikatan sa ba. Babu wani d'auke kai ko nuna isa irin na ubangida da bawan sa. "Baban Haruna, Soloman, D'an kwairo, Tanimu, ina fatan dai babu wata matsala ko?". Fad'in Alhaji Usman fuskan shi fad'ad'e da fara'a. "Yallab'ai babu matsalar komai wallahi". Gaba d'ayansu su ka amsa". Cike da farin ciki Alhaji Usman ya jinjina kai. Kallon Solomon ya yi, duk da yasan ya na jin wani hausan, sai dai mayarwan ne ke masa wuya. Don fita hak'k'i sai ya ce, "Is there any problem Solomon? If there's, fell free to say it". "No, no sir. There's no problem sir". Fad'in Solomon ya na girgiza kan sa. "OK. But have you eaten?". Alhaji Usman ya sa ke tambayan sa. "Yes sir. We are full". Jinjina kai ya sake yi ta re da mai da duban sa izuwa ga su Baban Haruna ya ce, "Ina fatan duk kun yi sallah, kuma kun ci abincin". "Eh yallab'ai. Mun yi sallah kuma mun ci abincin". Fad'in su Baban Haruna. "Alhamdulillah! Ba ri na k'arisa ciki". Fad'in Alhaji Usman ta re da yin gaba don duba sauran ma'aikata. Dama tuni motocin da su ka kawo shi sun yi ciki don sun riga da sun san da k'afa zai k'ariso. Sai ya duba ma'aikata sa kaf ya tabbatar da lafiyan su ya ke shiga ya ci abinci ya yi bacci. Yauwa sai da ya kwashi kimanin mintuna arba'in ya duba ma'aikatansa, sannan ya shiga main part d'in gidan. Da part d'in Hajiya Mansura matar shi ta biyu ya soma. Part d'in wacce ya ke d'akinta ne na k'arshe haka k'a'idar sa ya ke. Kullum sai ya duba lafiyar matan shi da y'ay'an shi kamin ya kwanta. Sallama ya yi ta re da murza key ta re da tura k'ofar ya shiga. Babu kowa a parlour kamar yadda ya yi tsammani. Sama ya hau. Ana ne ya d'an ji motsi a d'akin Hajiya Mansuran. Kwankwasawa ya yi ya d'an jira domin ta zo ta bud'e masa k'ofa. K'ofar aka bud'e, Wasila y'ar aikin Hajiya Mansura ta fito kanta a k'asa ta re da fad'in "Sannu da zuwa yallab'ai. Ina wuni?". Kallon ta ya yi daga sama har k'asa ka na ya girgiza kai ta re da fad'in, "Lafiya k'alau". Ya fad'i hakane ta re da shigewa d'akin Mansuran. Kwance ya same ta lullub'e da bargo har wuyanta. Zama ya yi a bakin gadon ta re da fad'in, "Mansura lafiya dai ko? Na ga ba sanyi ake ba amma kin lullub'e kan ki. In ce dai lafiya". Ya fad'i hakan ya na kallon ta. "Mtsw". Hajiya Mansura ta d'an ja tsaki ta re da fad'in, "Sannu da zuwa. Kai na ne ke d'an sara min, ga d'an zazzab'i da ke son kama ni". "Tashi maza muje asibiti". Fad'in Alhaji Usman ta re da mik'ewa. "A'a ba sai munje ba. Ba ka ga fitan Wasila ba, ai yanzu nasa ta ba ni magani da ruwa na sha. In sha Allah ka min safe zan warware". Fad'in Mansura. "Kin tabbata?". Fad'in Alhaji Usman ya na tab'a goshinta da ke sanyi k'alau ba alamar zazzab'i. Jinjina masa kai ta yi ta na k'ara jan bargo. K'ara gyara mata bargon ya yi ta re da manna mata kiss a goshi, ka na ya ce, "Ki yi addu'a ka min ki yi bacci. Allah ya k'ara ma ki lafiya. Sai da safe. Amma dan Allah ki rage saka Wasila aiki da daddare haka. Ai dare mahutan bawa ne. Kusan kullum fa da daddare sai na ganta a side d'in nan. Har tausayi ta ke ba ni wallahi".. "In sha Allah zan kiya ye. Allah ya ta she mu lafiya". Ta fad'i in a cool voice. Sai da ya kashe mata wutan d'akin ka na ya fito ta re da kulle mata k'ofa.

Ya na fita ta saki ajiyar zuciya ta re da yaye bargon. Daga ita sai pant. Da sand'a ta fito ta re da bud'e k'ofar a hankali don ganin ko ya fice daga part d'in ta gaba d'aya. Shurun da ta ji ne ya sa ta koma d'aki ta re da d'aukar wayarta ta danna numbern Wasila da ke can d'akin ma'aikata mata. Wasila na d'aga wayar Hajiya Mansura ta ce, "Dawo maza-maza ya fice, kuma kar ki bari a gan ki". Ta na gama fad'in haka ta yanke wayar.

Daga nan d'akin matar shi ta biyu ya nufa, wato Hajiya Huriya (Business woman kenan). Ita a parlourn k'asa ya same ta da uban kaya a gaban ta, gyefe guda kuma kud'ad'e ne sai uban lissafi ta ke yi. Ga uban y'an aiki a gabanta sai had'a mata kaya su ke yi su na saka wa a cikin wani kwali su na manne kwalin da salatep. Alhaji Usman na sallama, gaba d'aya y'an aikin nan su ka mik'e su na kwasan gaisuwa ta re da k'ok'ak'in barin parlourn. Dakatar da su ya yi ta re da fad'in ku yi zaman ku. Ni ma wuce wa zan yi yanzu". Komawa su kai su ka zauna su na kallon Hajiya Huriya da ko kallon Alhaji Usman d'in ba ta yi ba, sai faman lissafi ta ke yi. Murmushi Alhaji Usman d'in ya yi ta re da fad'in, "Barka hajiya y'ar kasuwa". Sai a lokacin ta d'ago da kan ta ta re da fad'in, "Ohhh sorry Alhaji, na bar ka tsaye ina ta faman lissafi. Kaya ne nai ordern su, shi ne su ka iso yau na ke dubawa". "Masha Allah! Allah ya kawo kasuwa. Babu wani matsala ko?". Fad'in Alhaji Usman d'in. "Babu". Ta fad'i ba ta re da ta kalle shi ba. "To sai da safe. Amma dan Allah ki d'an sallami bayin Allahn nan su ma su samu su huta. Dare mahutan bawa. Tun safe su ke aiki". "In sha Allah yanzu za mu gama su tafi su kwanta". Fad'in Hajiya Huriya. "Mu kwana lafiya". Fad'in Alhaji Usman ta re da ficewa daga d'akin ya nufi part d'in Suhail. Sallah ya tarar da shi ya na yi. Ja masa k'ofar ya yi ta re da furta Alhamdulillah cikin zuciyar sa. Daga nan kuma ya nufi in da ya ke wato d'akin Hajiya Na'ima.

Ya na tura k'ofar wani k'amshi ya daki hancinsa sai da ya lumshe idanunsa. "Alhamdulillah, masha Allah". Fad'in Alhaji Usman ta re da k'ara bud'e k'ofofin hanci ya na shak'ar daddad'an k'amshin da ke fesowa daga cikin d'akin. Tsit d'akin ya ke. Babu kowa a parlourn k'asa. Kasancewar tu ni Hajiya Na'ima ta sallami y'an aikin ta. Saboda ba komai ta ke bari su ke mata ba. Musamman girki, har yanzu ita ta ke abunta da kan ta. Kuma babu girkin da ba ta iya ba. Daga na zamani har na gargajiyan.

Sama ya nufa, nan ma sai da ya lumshe idanunsa saboda k'amshin ya fi wanda yaji a parlourn k'asa. Kallon dining ya yi da ke jere da kulolin abunci da kuma fruit. "Ke ta musamman ce Na'ima". Fad'in Alhaji Usman ya na nufar dining d'in.

*BA NI DA GATA ISN'T FREE, PAY #500 THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800, SAID ZULFAU GTBANK. SCREENSHOT YOUR EVIDENCE AND SEND IT TO THIS NUMBER 08128755583👆*

*MRS SAYYADEE*✍🏻 🌹 *23-24*🌹

Bud'e kular farko ya yi, ya yi arba da favourite d'insa wato mashed potato da ya ji bushashshan kifi sai zuba k'amshi ya ke yi. Duk da daddare abinci light ya ke ci, sai da miyan shi ya tsinke da ganin mashed potato d'in nan. D'ayan kulan kuma zallar bushashshan kifin ne ta masa farfesun sa. Ko kad'an ba k'arni kasancewar gona ce wajan gyara kifi. Ga yankakkun fruits nan a k'aton tire dangin su apple, banana, pineapple, watermelon, grapes da sauran su. Grapes d'in ya d'auka ta re da sakawa a bakin sa ta re da lumshe idanuwa. Dai-dai lokacin Hajiya Na'ima ta fito daga d'akin su Fanan domin du ba su. Da murmushi ta k'ariso wajan ta re da fad'in, "Barka da dawowa Abu Julaibib. Ya gajiyan hanya?". Hajiya Na'ima ta fad'a ta re da k'ariso ta tsiyayi ruwa a dispensers ta mik'a masa har da d'an duk'awa. Karb'a ya yi ta re da fad'in, "Alhamdulillah Ummu Julaibib. Allah ya sa ka miki da alkhairi ya k'ara shirya miki zuri'ar ki baki d'aya". "Ameen". Ta fad'a ta re da jawo masa kujera ya zauna, ka na ita ma ta ja ta zauna ta re da soma serving d'in shi. Favourite d'in sa ta zuba masa ta re da mik'ewa ta kai har gabansa, ka na ta dawo wajan zamanta ta na kallon sa. Aje cup d'in ruwan da ke hannunsa ya yi, ta re jan kujera baya ya mik'ewa. Kallon shi ta yi ta re da fad'in, "Abu Julaibib lafiya ka tashi?". "Zan je na wanke hannu na ne. I preferred using my hand than spoon. Abunci ma ya fi dad'i wallahi". Alhaji Usman ya fad'a. "Please come back and sit. Ba ri na kawo maka bowl ka wanke hannun a ciki". Fad'in Hajiya Na'ima ta re da mik'ewa. Dawowa ya yi ta re da zama kamar yadda ta buk'ata. Ita kuma ta kawo masa bowl d'in ya wanke hannunsa ta re da yin bismillah ya soma ci. Ko loma hud'u bai ba, Barrister Fu'ad ya yi sallama a k'ofar parlour. Sai da Anna ta ba shi izinin shigowa ka na ya shigo shi ma ya ja kujera ya zauna ta re da fad'in, "Dad ina wuni? Ka dawo lafiya?". "Lafiya k'alau Barrister. Ya aikin?". Fad'in Alhaji Usman. "Alhamdulillah daddy. Anna ina wuni?". Fu'ad ya fad'a ta re da mai da duban sa ga Anna. "Lafiya k'alau. Have eating?". Hajiya Na'ima ta amsa ta re da tambayan sa. Shafa cikin sa ya yi ta re da fad'in, "I eat nothing since afternoon". Dariya Alhaji Usman ya yi ta re fad'in, "You better find a wife before your momma stop giving you her food". "Ohooooo, you better tell him". Fad'in Anna ta na dariya. "Hmm! Anna, I don't wanna rush my self. Women, now adays. Hmm sai dai alhamdulillah". "Son pray, in Allah, Allah will here you and give you a better one". Fad'in Alhaji Usman. "Ameen". Fad'in Fu'ad ta re da jawo plate ya zuba mashed potato ta re da bismillah ya soma ci. "Hmm, ana maganar Fu'ad, to ina ki ka bar shugaban gwagwaran Africa? Baban boko. Boko mu ka zo yi duniya. Muna nan da ke, ya na dawo wa, zai kuma cewa wani degree d'in zai sa ke yi a wani fannin daban. Degree biyar fa gare shi". Fad'in Alhaji Usman ya na kai farfesun kishi baki. "Hmmm, I'm tired of that boy, ina ga auran dole zan mishi. Tun da na ke ban tab'a ji ko a mafarki an ce ga budurwansa ba. Ina ga hatta Zaid da Suhail sai sun riga shi aure. Sai an Kai hotunan sa masallaci ka min ya samu matar aure. Don ma ya ci sa'a bai da jiki da fuskan tsufa ko kad'an. Wasu ma cewa su ke Fu'ad ne yaya". "Anna na gan ku a rana ke da Yaya bibi. Ke da ki ke backing d'in sa amma yau har da ke ake masa haka". Fad'in Fu'ad. "Na yi d'in. In dai a kan aure ne, mun dunga kenan. Mutun sai k'ara shekaru ya ke yi, amma ya zauna sai ya ga k'arshan biro. Mongol pack ma dai ya mutu ya bar boko, shi da ya k'irk'iri dictionary". Daga Alhaji Usman har Fu'ad dariya su ka saka. "Yauwa Anna, dan wannan y'ar kyakkyawar yarinya ta d'azu, d'iyar wacece?". "Y'ar aiki ce. Kandala ta ka wo ta d'azu da safe". Fad'in Anna. Shak'ewa Fu'ad ya yi ta re da jero tarurruka sai da Alhaji Usman ya ba shi ruwa ya sha. Tuni har idanuwan sa sun kad'a sun yi jazur saboda shak'ewar da ya yi. "Anna, y'ar aiki fa ki ka ce? Wannan y'ar yarinyar kuma wani aiki za a kawo ta yi? Ai kamata ya yi ta na gaban iyayanta ta na karatu. Wai meyasa wasu mutanan dai kamar dabbobi su ke ne? Dan Allah Anna ku dai na k'arban k'ananan yara idan an kawo maku su a matsayin y'an aiki. Wallahi wannan child abuse ne. Idan human right su ka ji wannan, Allah abun kai k'ara kotu ne a nai mo mata hakkin ta a wajan wad'and'a su ke kawo su. Kuma wallahi wasun su mostly iyayan su ba su sani ba". Fad'in Barrister Fu'ad kamar zai yi kuka. "Hmm, maganar da na ke son in yi da mahaifin ka kenan. Na yanke shawarar yarinyar za ta zauna da ni har ta kammala karatun ta ba bu wani maganar aiki. Domin akwai ciwon jahilci a kwakwalwar yarinyar da ma k'auyan su baki d'aya. Domin da kana nan d'azu ta ke min wasu irin tambayoyi, wallahi sai ka yi kuka. Sam ba su san addini ba, balle akai ga zancan boko. Alhaji idan ka amince min, zan yi magana da baabar ta wacce ta kawo ta aiki, a tambayan min iyayanta idan sun yarda zan rik'e ta har ta samu miji ta yi aure bayan ta yi karatu. Don wallahi yarinyar ta shiga rai na ba kad'an ba". Fad'in Anna ta na kallon Alhaji Usman. "In dai wannan ne ai ba matsala Na'ima. Haka nake so in ga kuna taimakon mabuk'ata. Allah dai ya sa ka mi ki da alkhairi. Ni kuma idan har iyayanta sun amince, zan biya duk wani abunda za ta yi har tai aure. Ita ma ta zama d'aya daga cikin family na ba y'ar aikin gida na ba". Fad'in Alhaji Usman. "Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i". Fad'in Anna da Fu'ad. "Ameen". Ya fad'a ta re da goge bakinsa da hannun sa da tissue ka na ya wanke hannun ya wuce bedroom d'in sa. "Idan ka gama ka tabbatar ka rufe min k'ofa". Fad'in Anna ta re da mik'ewa ta yi hanyar bedroom d'in ta domin ta kimtsa ta je wajan mijin ta. Bayan mahaifiyar sa na sa ya yi da idanuwa ya na jin wani soyayyarta na k'ara huda zuciyar sa. "Mummy like no other" Fu'ad ya fad'a ta re da goge hannunsa da tissue ya bud'e goran ruwa ya sha ta re da fita daga parlourn ya kullo k'ofar, haka ma main parlour ka na yai part d'in sa da ke gaban na Suhail. Sai da ya fara lek'a d'akin Suhail d'in ta window. Duk da ya kashe wuta, amma haske waje da ya haska windown sa, sai da ya sa ya gane shaye-shaye ya ke yi saboda hayak'in da ke fitowa. Girgiza kai ya yi ta re da shigewa side d'in sa ya kullo k'ofa. Wanka ya yi ta re da gabatar da shafa'i da wuturi, ka na ya hau gado ta re da kunna data ya hau WhatsApp ya d'an yi chatting kad'an saboda baccin da yaji ya soma cika masa idanuwa. Addu'a ya yi tare da kwanciya ya ja bargo.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull