Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 10

Ba ni da gata - Chapter 10

Ba ni da gata Chapter 10: Ba ni da gata Chapter 10. Cikin wani k'aton gidan gona ya yi parking. Makekan gidan gona ne in da ake kiwo kala-kala. Gyefe guda…

3,085 words

Cikin wani k'aton gidan gona ya yi parking. Makekan gidan gona ne in da ake kiwo kala-kala. Gyefe guda kuma wani rantsatstsan two bedroom ne. Shi kad'ai ya zo sai Binty da ke gaban mota ta yi tsamo-tsamo. Duk ya sallami sauran abokan sa da y'an matan sa da duk sun girme sa don gaba d'aya shekarunsa sha takwas ne, girman jiki ne Allah ya ba shi irin na mahaifiyar sa. Bud'e motar ya yi ta re da fitowa ka na ya zagaya ya bud'ewa Binty k'ofa ta re da murtuke fuska ya ce, "Sauko ki fito". Ya fad'a hakan da kausasshan muryan shi da shaye-shaye ya fasa. Binty jiki na rawa ta fito daga motar nan ta re da rukub'ewa a jikin k'ofa ta na kallon sa da idanuwan ta da har ya cicciko da hawaye. "Idan ki ka sa ke ki ka min kuka, kin ga dai girman gidan gonan nan ko, to daga ni sai ke ce a ciki. Zan iya yanka ki in bizne ki babu wanda ya sani, don haka kar ki sake ki min kuka. Duk abunda na ce ki yi kawai ki yi. Kin ji abunda na ce miki?". Jijjiga kai Binty ta yi jikinta na k'ara tsuma musamman da ta ji maganar yanka da biznewa. "Oya wuce muje". Fad'in Suhail ya na nuna mata hanya da hannun sa. Simi-simi ta yi gaba k'afarta na hard'ewa. Tawowa ya yi ya wuce ta ta re da isa wajan k'ofar ya bud'e ka na ya nuna mata cikin d'akin da hannu. Kallon shi ta yi idanuwan sun yi jazurr, hatta leb'anta rawa su ke yi kamar mai jin sanyi saboda tsabar yarda ta firgice. Shiga ta yi hawaye na zubowa daga idanunta tai saurin saka bayan hannunta ta goge. "Oya cire wannan hijjab d'in". Suhail ya fad'a ya na tsare ta da idanuwa. Hijjab d'in ta cire ta re da rik'e shi a hannun ta. Domin gaba d'aya ya firgitata, musamman muryan shi da ya ke kama da na rik'ak'k'un garada. "Ke ban san iskanci. Aje hijjab d'in nan ko in zo wajan nan in taka miki wuya". Suhail ya fad'a ya na zazzaro mata idanuwan shi. Saboda tsabar rud'ewan da ta yi, jifa ta yi da hijjab d'in a kan fridge d'in da ke d'akin ba ta re da ta sani ba. Kallon ta ya shiga yi from head to toes ta re da fad'in, "D'anya ce shataf, amma haka nan zan yi manaji a haka za ta girma musamman idan ta na jin taki". Zame wandon jeans d'in jikinsa ya yi, ya rage da ga shi sai boxer. Rigar jikin shi da singlet ya cire ta re da zama a kan three sitter ka na ya ce, "Zo nan". Ya fad'i hakan ne ya na shafa cikin sa. Binty kuwa tsaye ta ke a wajan ta ki zuwan sai kallon shi da ta ke yi. "Ba da ke na ke yi ba". Ya fad'a da k'arfi sai da ta firgita wanda ba ta san lokacin da ta isa gare shi ba. Jawo ta ya yi ta re sa da zaunar da ita a saman cinyar sa ka na ya zame hulan da ke kan ta. Kyakkyawan gashin kan ta bayyana. Yayin da jelar gashin ke tab'a masa gwiwar k'afarsa. "Wow!". Suhail ya fad'a ya na shafa kan tun daga tsakiyar kanta har k'arshan bindin gashin. Hancinsa ya kai wuyarta ya na sunsuna ta re da lumshe idanu saboda daddad'an kamshin man shafawan Fanan da Bintyn ta shafa. Ga wani fitinannan k'amshi da gashin kan na ta ke yi saboda gyaran da mai saloon d'in nan ta ma ta da kuma wanda Fanan ta ma ta d'azu. B'alle buturan rigar jikinta ya yi ta re da wurgi da rigar a kan tiles. Hannu ya kai ya na shafa ko ina a jikinta kamar ya na shafa jikin budurwa. Ita kuwa Binty ji ta yi kamar ana watsa mata ruwan zafi mai mugun zafi a jikinta. Mik'ewa ta yi a razane ta na susan jikinta don wani irin rad'ad'i da ta ke ji. "Ke ina wasa da ke ne? Waya ba ki izinin ta shi a kan jikina? Dawo ki zauna kuma duk abunda na mi ki ke ma ki min". Suhail ya fad'i ya na gwalalo mata idanuwa. K'in zuwa Binty ta yi ta na soshe-soshen jiki ta re da hawaye. Mik'ewa ya yi a zafafe ya d'auke ta da mari ta re hankad'ata ta fad'i k'asa. Cire belt d'n wandon da ya yi ta re da zame shi ya fad'i k'asa ka na ya damk'o gashin kan ta har sai da ta saki ihu. Ka yan jikinta ya cire kaf ka na ya kwantar da ita flat a kan 3three sitter ya Shiga k'ok'arin cire boxer d'in jikinsa. Dai dai lokacin Barrister Fu'ad ya banko k'ofar d'akin ya shigo. Idanuwan sa ya sauka akan Suhail da ke nai man afkawa yarinya. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Suhail kai wani irin d'an akuya ne? Dan uban ka wannan y'ar k'ank'anuwar yarinyar za kai rapping?" Barrister Fu'ad ya fad'a ta re da k'arasawa kusa da shi ya d'auke shi da maruka hagu da dama. Shi kuwa Suhail jan boxer d'in sa da ya fara cirewa ya yi ta re da jaa baya ya na fad'in, "Ni ai ba tilas nai ma ta ba, ita ta biyo ni". 'Kara d'auke shi da mari Barrister ya yi ta re da fad'in, "Uban ka na ce, Suhail. Wannan yarinyar mai ta sani da Har za ta bi yo ka? Yarinya k'ank'anuwa da ko balaga ba ta yi ba, ita ka ke so ka b'ata. Yanzu idan Fanan ko Sunaina a kai wa haka za ka ji dad'i!". "Oho! Idan su su ka kai kan su, to ni in ruwa na. Yanzu fa kowa fa abunda ya ga dama ya ke yi. Wa ya san kai me ka ke aikatawa". Suhail ya fad'a ya na wani ciccijewa kamar d'an daba. Wanka masa mari ya sa ke yi ta re da nu na shi da yatsa ya ce, "Dole ka ce oho tunda ba uwa d'aya ta haife ku da wad'anda na lissafo ba. Ku ma da ka ke cewa wa yasan abunda ni na ke aikatawa, an fad'a maka kowa d'an iska ne irin ka? To ba ri ka ji, wallahi, tallahi, duk ranar da ka sake attempting yi wa wata yarinya fyad'e, na rantse da girman Allah wannan a wannan karan ba zan saurari Anna da ta ke hanani ba. Ni ka d'ai na san hukuncin da zan d'auka. Ban key d'in gidan nan". Barrister Fu'ad ya fad'a ta re da mik'a masa hannun sa alamar ya sa ka masa key d'in a hannun sa. Suhail sai wa ni cicciza ya ke yi kamar ba zai ba da key d'in ba. Can kuma ya mik'a masa. Barrister ya kalli in da Binty ta ke jikin ta sai rawa ya ke yi ta re da fad'in, "Sauko ki d'auko kayan ki kisa mu tafi wajan Anna". Jikinta na rawa ta sauko daga kan kujerar ta re da d'aukar kayanta da ke yashe a k'asa. Saboda yadda jikinta ke rawa, sai ta kasa saka kayan. Barrister Fu'ad ya karb'i kayan ta re da saka mata, ka na ya kama hannunta ta re da kallon Suhail d'in ya ce, "Fita ka d'au motarka, zan kulle gidan". Barrister Fu'ad ya fad'a ya na antaya masa harara. Wa ni dogon tsaki ya ja ta re da fad'in, "Kill joy". Kamar zai bangaje sa ya fice daga d'akin. Barrister Fu'ad ma tsakin yaja ta re da yin kwafa ya ce, "Zan yi maganin ka soon. D'an iskan yaro kawai". Ya fad'i hakan ne ta re fitowa hannun shi rik'e da hannun Binty. Kulle k'ofar ya yi lokacin tuni Suhail ya ja mota da uban k'arfi ya bar gidan. Kasancewar mota Barrister na k'ofar gate. Kai tsaye fita su kai ya kulle gate d'in da key ya kuma saka kwad'o ta re da yin wajan mota ya bud'e gaban Binty ta shiga, shikuma ya zagaya ta re da shiga mazaunin driver ya kunna motar ta re da reverse. Sai da su ka hau hanya, sannan Barrister Fu'ad ya juyo ya kalli Binty wacce har a lokacin gaban ta bai dai na fad'uwa ba. "Me ya sa ki ka biyo sa". Barrister ya fad' ta re da mai da duban sa ga titi. "Shi ya ce dole sai na shiga mota. Shine ya kawo ni nan". Fad'in Binty muryanta na rawa. Don har yanzu ba ta dai na jin jikinta kamar ana yayyafa mata ruwan zafi ba. Don har turiri-turiri ta ke ji jikin na mata. "Daga yau ko ya kira ki ka da ki je. Ka da ma ki rik'a zuwa in da zai gan ki. Idan kuma kun had'u bi sa kuskure, ki yi gudo ki koma wajan Anna kin ji?". Barrister ya fad'a ya na kallon kyakkyawar fuskan da tsoran da ta ke ji ya k'ara bayyanar da kyawun fuskan ta. "Yauwa Malam ne ke mana karatu, shine ya kira ni. Kuma Fanan ce ta ce idan ban je ba karya ni zai yi". "Idan kuma ki ka je ya tab'a jikin ki, mutuwa za ki yi". Fad'in Barrister Fu'ad ya na kallon idanunta saboda ya ga reaction d'in ta. Aikuwa ta zaro idanuwa ta re da fad'in "Ba na so na mutu, Allah zan gudu idan na gan shi. Wajan Malam ma bazan k'ara zuwa ba". Fad'in Binty hawaye na silalo mata. "Oho ni dai na fad'a miki, ba shi kad'ai ba ma, duk namijin da ki ka sa ke ji ka yadda ya na wasa da jikin ki, ko ya na tab'a miki jikin ki, ko ya ke ji tab'a na da jikin, to mutuwa za ki yi murus, saboda haka ba ruwan ki da wasa da maza, kin ji". "Na ji, ba zan yi wasa da maza ba. Fanan kawai zan yi wasa da ita". "Good girl. Menene sunan ki?". Barrister ya fad'a. "Suna na Binty Hashimu mai goro. Kai kuma fa?". Binty ta fad'a ta na kallon shi. "Yaya Fu'ad, ko ki ce Yaya Barrister. Sannan daga yau ba Binty Hashimu sunan ki. Tsoffi ke cewa Hashimu. Daga yau duk wanda ya tambayi sunan ki, ki ce Binty Hisham mai goro kin ji?". "Binty Hisham mai goro". Binty ta maimaita ta na kallon shi. "Eh daga yau haka za ki rik'a fad'i". Fad'in Barrister Fu'ad. Hakanan ya ji y'ar k'aramar yarinyar da nai san alak'ar sa da ita ba ta shiga ran sa.

*DAN GIRMAN ALLAH KA DA KI KARANTA IDAN BA KI SIYA BA, BI YA #500 KI KARANTA NA HALAS D'IN KI BA NA SATA BA ZUWA WANNAN ACCOUNT D'IN 0592412800 ZULFAU SA'ID GTBANK. SAI KI TURO DA SHAIDAN BIYAN KI TA WANNAN NUNBER 08128755583*

*MATAR SAYYADEE*✍🏻 🌹 *21-22*🌹

Direct gida su ka yo. Horn Barrister Fu'ad ya yi. Oga Solomon ya ta shi da sauri ya bud'e masa gate. Kasancewar motar ta shi ba tinted, hakan ya ba shi damar ganin Binty da ke zaune a gaban mota. Wani dad'i ne ya mamaye zuciyar Oga Solomon ta re da sarawa Barrister Fu'ad ya na fad'in, "Welcome home Sir". Sauke glass d'in motar Barrister Fu'ad ya yi ta re da fad'in, "Solo, Solo. Solomon how you dey?". Ya fad'i hakan ne ya na dariya. "Ahh, Oga I dey fine wooo, ibi like say I wan dance in from you. I fell happy wallahe". Fad'in Oga Solomon ta re da k'ara gyarawa bindigarsa zama a kafad'arsa. Murmushi Barrister Fu'ad ya yi ba ta re da ya tambaye farin cikin mai ya ke yi ba. Don bai son surutu so kawai ya ke ya aje Binty ya koma wajan aiki don akwai case d'in da zai yi anjima kuma saura rabin awa. Gashi Solomon akwai d'an bura uban surutu kamar uban aku. Jan motarsa ya yi ta re da nufar second gate. Parking ya yi a farfajiyar gidan saboda ba dad'ewa zai yi ba shi yasa bai kai motar parking space ba. Fanan da ke gaban part d'in su, ta na hango Binty a gaban motar wan na ta ta yi wajan da gudu. Domin y'an awannin da su kai da. Bintyn ta mugun shiga ran ta har ta ke jin kamar sun shekara. Kuka kuwa ta yi shi ba bu adadi domin idanuwan ta sun kad'a sun yi jazurr, duk a tunanin ta yaya Suhail d'in ya ta fi karya Binty ne ko ma ya kashe ta. Don ita kan ta akwai wani duka da ya mata sai da ta kwanta a asibiti, sai daddy ya ma sa kaca-kaca akan dukanta ne ya d'an sarara kasancewar ya na shakkar sa. Annah kuwa ko k'ala ba ta cewa, a cewar ta, wai sun fi kusa ai y'ar uwarsa ce ya ma kashe ta. Rungume ta Fanan ta yi ta re da fad'in, "Alhamdulillah you're home sister. I'm so sorry for allowing you to follow him, I won't do that again. Please pardon me sister. But did he hurt you?". Fanan ta k'arisa ta na dudduba jikin ta domin ta ga ko akwai in da Suhail d'in ya ji mata ciwo da dukan. Sam ta manta ma idan za ta shekara ta na turanci Bintyn ba za ta San abunda ta ke ce wa ba. "Dalla matsa ko in bige ki a nan wajan. Da ma ke ki ka ce mata ta je wajan shi ko?". Fad'in Barrister Fu'ad ya na hararar Fanan d'in. "Ohhh brother lemme explain". Fad'in Fanan a marairaice. "Heey! Not a word. I don't need your explanation. Talkative". Fad'in Barrister ta re da matsar da Fanan ya ruk'o hannun Binty su kai part d'in Anna (Hajiya Na'ima). "Ohhh please bro, won't you hold my too?". Fanan ta sha gaban su ta re da mik'a hannunta. Girgiza kai Barrister ya yi ta re da rik'e hannunta ita ma. A parlourn k'asa su ka taras da Annah sai sama da marwa ta ke yi. Ka na ganin ta kasan hank'alinta a tashe ya ke. "Anna she's back. Bro Fu'ad brought her back. Look at her here". Da sauri Anna ta juyo ta re da sauke idanuwan ta a kan Binty. Wani sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke ta re da k'arisawa in da su ke ta rungume Bintyn. "Wannan beauty d'in fa za ta kwace miki autahood d'in ki". Barrister Fu'ad ya fad'awa Fanan a kunne at the same time kuma ya na mata dariya da gwalo. "Brooooo". Fanan cike da shagwab'a. Zaro mata idanuwa ya yi ta re da karyar da wuyarsa ka na ya ce, "Yessss. How may I help you?". Turo ba ki ta yi ta re da ita wajan su Anna da ke rungume da Binty ta ce, "Anna me too". Ta fad'i hakanne ta re da ware hannunta cike da shagwab'a. Murmushi Anna ta yi ta re da had'a su duka ta rungume su ta na kissing forehead d'in su. Mai da du ban ta ta yi ga Barrister ta yi ta re da fad'in, "Fu'ad, I hope he didn't do anything to this little girl? Cus wallahi this time I can't hold it". Ajiyar zuciya Barrister ya sauke ta re da fad'in, "He's about to, sai Allah ya kawo ni da sauri. Maganar gaskiya Anna ki bar ni in d'au mataki a kan wannan d'an iskan yaro da ya ke nai ma ya lalata mana sunan gida kuma uwar sa na sane ba za ta iya d'aukan mataki ba. Wallahi jiya sai da wani abokin aiki na ya min magana akan in rik'a kula da shi saboda last 3 days gasa su kai a kan kwayar doki, kuma shi ya ci gasar. Yaro duk ya bi ya lalata kan shi, k'arami da shi. Ko nineteen years fa bai yi ba. He's just eighteen. Haba Anna, dan Allah ki bar ni na d'au mataki. Ki na ganin da ya Julaibib ya na nan zai kyale shi ya yi duk abunda ya ga da ma ne. Wallahi duk ranar da yaya zai sauke k'asar nan ya ji labarin abunda Suhail ya ke yi, to wallahi sai ya karya shi. Ke Anna ai kin fi kowa sanin halin sa. Dan Allah ki bar ni in gyarawa yaran nan zama tun kamin yaya ya dawo ni ma ya had'a da ni. Don cewa zai yi ina kallo ya lalace". "Enough barrister! You can go back to your work. Ku ba ku san abunda na sa ni ba. Duk abunda na ke yi ina da dalili na. Suhail d'an uwan ku ne, ni kuma d'an mijina ne da na ke ma sa kallon d'an ciki na kamar kai da ka ke ga ba na. So just do as I say". "As you wish Anna". Fad'in Barrister in a cool way. Cus har ga Allah ya na son d'auka mataki kwakkwara akan d'an uwan na sa. Domin idan ya lalace kamar shi ne ko Zaid k'anin sa ne ya lalace. "Anna I'm going". Barrister Fu'ad ya sa ke fad'i ya na kallon Binty da ita ma shi ta ke kallo. Kuma Sam ta ka sa fahimtar mai su ke cewa kasancewar su na had'a turanci a cikin maganganun su. "OK". Anna ta fad'a a tak'aice ta re da rik'e hannun Fanan da Binty su ka nufi stairs. "Anna, why not malamin ya rik'a shigowa har parlourn nan k'asa ya na masu karatun? Cus zaman su a waje is not safe for the little girl". Ba ta re da Anna ta juyo ba ta ce, "Zan masa magana, ni ma hakan na tsara". Ta fad'i hakane su na hayewa steps d'in. Ajiyar zuciya Barrister Fu'ad ya sa ki, ya na son tambayar Anna wacece Binty, amma yadda ya ga Anna ta yi kicin-kicin da fuska sai ya had'iye tambayar sa ya fi ce don ka da ya yi latti. Shiga mota ya yi ta re da reverse ya fi ce. Ya kai gate d'in k'arshe wato gate d'in su Oga Solomon ya sauke glass ta re da yafito Solomon d'in da ke rik'e da gate d'in da ya bud'e masa. Da sauri Oga Solomon ya isa wajan motar tare da sarawa Barrister. "I need to talk to you, but leter in the night when I come back". Fad'in Barrister Fu'ad. "OK sir". Oga Solomon ya fad'a ta re da k'ara sarawa Barrister Fu'ad. Mai da glass d'in sama ya yi ta re da ficewa daga gidan. Shi kuma Solomon ya rufe gate d'in ta re da dawowa wajan zaman shi ya soma wak'an yaran su.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull