Ba ni da gata - Chapter 9
Ba ni da gata Chapter 9: Ba ni da gata Chapter 9. 🎻 _I'm D'banj or skibanj like my Jamaica friends call me_ _When the koko master fall in love_ _You know…
2,979 words
🎻 _I'm D'banj or skibanj like my Jamaica friends call me_ _When the koko master fall in love_ _You know say water water don pass garri_ _Hmmmmn_ _I'm in love, are you in love?_ _Omo you don make me fall in love (you don make me)_ _Fall in love oh, fall in love(you don make me)_ _We suppose marry, 'cause you don make me fall in love (you don make me)_ _Fall in love (you don make me)_ _Fall in love_ (you don make me) _My sweet potato_ _I wanna tell you my mind, wanna tell you my mind oh_ _I no understand oh_ _'Cause I dey see well-well but them say love is blind oh_ _You see as you dey so_ _you are the love of my life, you are the love of my life oh_ _I cannot deny woo_ _I wanna make you my wife, make you my wife ohh_ _see, I never though that I'll find someone like you_ _That will capture my heart, and there's nothing I can do_ _But since I set my eyes on you_ _Omo you don make me fall in love(you don make me)_ _Fall in love(you don make me)_ _Fall in love(you don make me)_ _We suppose marry, 'cause yo don make me fall in love oh (you don make me)_ _Fall in love(you don make me)_ _Fall in love(you don make me)_ _Fall in love oh_ 🎻
A matuk'ar fusace ta banko k'ofar ta re da shigowa tta kashe home theater ta re da buga wayar da bango ka na ta juyo ta kalle shi idanuwan sun kad'a saboda b'acin rai ta ce, "Abu Sufyan ba za ku kashe ni ba wallahi sai lokaci na ya yi. Yanzu da girman ka saboda kai sha-sha-sha ne ba ka san in da ke ma ka ciwo za ka cika min part d'ina da hayaniyar wak'e wak'en banzan ka. To wallahi ka ki ya ye ni. Da ku manya zan ji ko kuma da k'anwar ku Sabrin da ke nai man saka min hawan jini mahaifin ku na d'aure mata gindi? Ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, Abu Sufyan ba kai sallar asubha ba. Mai makon ku da Ku ke maza ku ma manya ku tsaya min a kan k'anwar ku da ke nai man fin k'arfi na, amma ku kan ku nai ma Ku ke ku hauka ta ni. Haba Abu, kun yi min adalci kenan? Ana zuga ku kuna k'ara tab'arb'arewa ku a naku tunanin k'aunar ku a ke yi ko? To wallahi idan za ka natsu, ka natsu. Shekara uku kamar yau ne a wajan ubangiji. Ai Babban wan na Ku zai dawo". Hajiya Sakna na gama fad'in hakan ta juya ta fice ta na jin wani k'una a k'asa zuciyar ta. Ta na fita Abu Sufyan ya ta'be baki ta re da fad'in, "Mom wallahi ki na da matsala. Dad'in aunty Junaina ke nan, ba ruwan ta da sakawa mutum idanu". Ya fad'i hakane ta re da kunna home theatern ya rage volume d'in ta re da cigaba da miming ya na rawa.
"Ya Allah ka na kallon komai. Ka taimaka min ga me da lamarin y'ay'ana". "Sannu wacce duk duniyar nan ita d'aya ke da y'ay'a. Ni fa wallahi akan takurawa y'ay'ana wallahi za mu samu mugun sab'ani da ke Sakina. Ke ba za ki koyi da Junaina ba? Ba ki ganin yadda ta ke yi da y'ay'an ta har da ma na ki y'ay'an kamar k'awayan ta. Ta na barin su suyi duk abunda su ke so in dai ba zai cutar da su ba". "Cutarwa ke ce Alhaji? Cutarwa ku ma na nawa? Ai Junaina da kai kun dad'e ku na cutar min da y'ay'a wajan d'aura su a hanya mara b'illewa barin ma Sabrin da Ku ka riga ku ka halakar da ita. Kuma wallahi tallahi sai Allah ya tambaye ku a kan hakan da Ku ke yi. Kun sa Sabrin ta fi k'arfi na. Yanzu haka ka duba agogo almost to 4 amma yarinyar nan ba ta dawo daga makaranta ba bayan an tashi tun 2:00pm. Kuma na aika driver ya ce makarantar a kulle ba ta can. Na ma ka magana ka ce min ai tasan garin ba b'acewa za ta yi ba. Haba! Haba!! Haba!!! Alhaji. Kai ka na ganin hakan dai dai ne? Ina ta ke zuwa? Da izinin wa ta ke fita? Yadda yanzu kidnapping ya yi yawa a gari. Idan aka sace ta fa?". Duk maganganun da Hajiya Sakna ta yi bai shige sa ba, sai maganar sace Sabrin d'in da ta yi ne ya girgiza shi. Wayar sa ya zaro daga cikin aljihu ta re da fita da sauri ya yi wajan mota ya na kwalawa driver kira. Da gudu driver ya zo ta re da duk'awa a gaban Alhaji Saifullahi. Wawan mari Alhaji Saifullahi ya d'auke Shafi'u driver da shi sai da ya kifa k'asa. Ka na ya nu na masa hannu ta re da fad'in, "Wallahi duk ranar da ka k'ara shigowa gidan nan ba ta re da Sabrin ba, a bakin aikin ka kuma sai mun yi shari'a da kai. Kai wallahi ba zai yuwu ba. Bodyguard zan d'auko wa y'a ta". Kamar mahaukaci haka Alhaji Saifullahi ya bangaje Shafi'u ta re da shiga mota ya ja a guje ya bar gidan da tuni mai gadi ya bud'e don ya na ganin duk abunda ke faruwa ka da shi ma ya samu ba shi rabon.
Ta re su ka fito Binty na bi ye da ita a baya sanye da hijjab. Wani waje da aka zagaye da fararan kujeru su ka nufa in da Malam Abdulrazaq ya ke zaune ya na jiran su k'araso. Sallama su ka yi ta re da zama ka na su ka gaishe sa. Amsawa ya yi ya na kallon Binty kasancewar Hajiya Na'ima (Anna) ta kira sa ta masa bayani a kan Bintyn, ta kuma ce masa ya taimaka ya lura da ita ta iya duk abubuwan da ya kamata. Kuma ya yi mata alk'awarin in sha Allah zai yi hakan. "Mai nene sunan sabuwar d'alibar tawa?". Malam ya fad'a ya na mai kallon Bintyn. "Suna na Binty Hashimu Mai goro". Fad'in Binty. "Masha Allah. Da fatan za ki natsu ki kuma ba ni hankalin ki saboda ki koya ta re da fahintar abunda zan koya miki?". "Eh zan yi Malam". Fad'in Binty. Kasancewar sai da Anna tai ma ta fad'a sosai akan duk abunda Malam ya koya mata ta tabbatar ta iya shi. Domin idan har ba ta iya ba sai ta Zane mata jikinta. "To Alhamdulillah, yanzu za mu fara da ummul kitab wato fatiha. Bud'e Qur'anin ki". Malam ya fad'a. Upside down ta rik'e Qur'anin. Don iya tsayin rayuwar ta ma ba ta tab'a ganin shi ba. Karb'a Fanan ta yi ta re da nuna mata yadda ake rik'e Qur'anin. Tun a wajan bismillah Malam ya san akwai babbar matsala. Domin ba ta iya ba. Sai dai in da hankalin shi ya kwanta, yadda Bintyn ta ke da saurin d'auke abu a kwakwalwarta.
Sanye ya ke da three quarter da riga armless, sai wani shegen glass da ya kwama a fuska. Hannun shi rik'e da goran fanta da yaji kayan maye a ciki. Zugan abokan sa da kuma 'yan matansa da na abokan ba shi a bayan shi cikin shiga na rashin d'a'a. Cak ya tsaya ya na k'arewa wajan da su Binty su ke zaune malam na ko ya masu karatu. Takawa ya yi har in da su ke ta re da k'urawa Binty idanuwa ko kyaftawa ba ya yi. Ita kuwa Fanan ganin wan na ta ya nufi wajan da su, tu ni jikinta ya d'au rawa. Don mawiyacin abu ne su had'u bai mata mummunar duka ba. "Zo nan dan uwar kiii"
*_MATAR SAYYADEE_* 🌹 *19-20*🌹
Jikin Fanan na wani irin rawa ta mik'e ta soma takawa a hankali ta na tsoran irin dukan da zai yi mata. Shi kuwa malam zubawa sarautar Allah idanu ya yi, domin ba wannan ba ce rana ta farko da Suhail d'in ya ke hakan idan su na karatu ba. "Dan kutumar uwar ki, in ta tsayuwa ina jiran ki? Kin tsaya ki na wani tafiya simi-simi kamar macijiya. Wallahi na k'irga uku ba ki k'araso nan ba, sai na karya k'ashin k'afar ki". Fad'in Suhail ya na wani muzurai. Da gudu-gudu Fanan ta k'arasa wajan sa ta re da fad'in, "Ya Suhail ga ni. Wa ni abun zan yi maka". Ta fad'i hakan ne bakinta na rawa kamar wacce tai k'arya. Sai da ya k'ara kallon in da Binty ta ke, ka na ya dawo da duban sa izuwa ga Fanan d'in ta re da fad'in, "Wa cece wancan yarinyar?". Suhail ya fad'a ya na wani yamutsa fuskan shi. Kallon Bintyn ta yi, ka na ta mai da du ban ta ga Suhail ta re da fad'in, "Anna ta ce min y'ar aiki ce, za ta rik'a ta ya ni ayyukan gida". "Y'ar aiki". Suhail ya maimaita cikin zuciyar sa ta re da k'ara mai da du ban sa ga Bintyn da ta mai da hankalin ta gaba ga karatun suratul Fatihan da malam ke koya mata. "Kai! Malam ka ke ko malum-malum, sako yarinyar nan ta zo nan". Fad'in Suhail ya na wa malam d'in wani kallon k'ask'an ci. Kamar malam zai ce wani abu, sai kuma ya kalli Binty ta re da fad'in, "Je ki ana kiran ki". Ya fad'i hakan ne ta re da mai da duban sa a kan Qur'anin sa. Binty kuwa mik'ewa ta yi ta re da nufo in da Fanan da ya Suhail su ke a tsaye. Ta na zuwa wajan ta tsaya k'ak'am ta na kallon fuskan Suhail da ke kallon ta from head to toes. "Fanan mai ya sa ki ka tsaya a nan bayan malam na jiran mu zai mana karatu? Har na fara iyawa Allah. Malam ya ce zan yi k'ok'ari sosai". "Ke biyo ni". Fad'in Suhail ta re da wucewa gaba. Ita kuwa Binty ba ta san ma da ita ya ke yi ba. Ganin ya yi gaba ita ma ta juya za ta koma wajan malam domin ya cigaba da koya mata karatu. Ruk'o hannunta Fanan ta yi ta re da fad'in, "Binty Yaya Suhail fa da ke ya ke magana. Ya ce ki bishi. Kuma idan ya juyo ya ga ba ki bi sa ba, zan karya miki k'afa da duka wallahi". Zaro idanuwa Binty ta yi ta re da fad'in, "Da ni ya ke yi? Ai na d'auka da ke ya ke yi. To mai zan masa?". "Oho ni ma ban sani ba, dan Allah ki je ka da ya juyo ya ga bai gan ki a bayan sa ba. Ku ma ya fara miki nisa fa". Fad'in Fanan. Ai da gudu Binty ta bi bayan Suhail d'in har ta isa inda ta ke ta na haki don ya mata nisa. Ga gidan da shegen fad'i da tsayi. "Ga ni Yaya, Fanan ta ce wai ka na kira na". Fad'in Binty ta na haki. Juyowa ya yi ya kalle ta ta re da fad'in, "Shiga mota". Ya fad'i hakane ta re da bud'e gaban mota, shikuma ya zagaya ya shiga mazaunin driver. Ya yin da uku daga cikin y'an matan shi su ka shiga gidan baya. Sauran abokan sa kuma su ka shiga na su motocin kasancewar sun zo da ita. Har lokacin Binty na tsaye a wajan ba ta da niyyar shiga cikin mota. "Ke dan uwar ki zan ta tsayawa ne ina jiran ki ba za ki shiga mota ba?". Suhail ya fad'a ya na zazzaro mata idanuwan sa da suka juye irin na masu shaye-shaye. Saboda yadda ya yi maganar da k'arfi Binty ba ta san sadda ta shige gaban motan ba ta na zazzaro idanuwa. Mik'owa hannunsa ya yi ta re da rufe motar ka na ya yi mata key ta re da reverse ka na ya fito daga parking load d'in. Fanan kuwa wani ajiyar zuciya ta sauke ta re da nufar wajan malam. Shi kuwa Malam tun sanda Binty ta ruga ta bi bayan Suhail gabansa ke bugawa don sarai ya san halin Suhail d'in ciki da bai. Yaron da a k'asar waje ya yi primary da secondary d'in sa. Lalacewar da ya so ma yi ne ya sa Alhaji Usman da kan shi ya dawo da shi gida Nigeria a wani zuwan bazata da ya yi masa ya tarar da abun asshan da ya ke yi da mata da kuma abokan sa turawa su ke yi. Babu irin kwayar da Suhail bai sha. Har safarar cocaine ya na yi ba ta re da sanin iyayansa ba. Mutum uku ya ke shakka a rayuwarsa, wato mahaifinsa da Hajiya Na'ima uwargidan mahaifin na sa. Duk rashin kunyar sa bai iya yin ta a gaban ta, sai kuma babba d'a ga Alhaji Usman da hajiya Na'ima, wato Julaibib Usman Mai rabo, wanda a yanzu haka ya na US ya na Masters degree d'in sa.
Malam ya kalli Fanan da ta zauna akan kujera ta na sakin ajiyar zuciya ta re da fad'in, "Ina ki ka baro Bintyn?". Ya fad'i haka ne ya na kallon cikin idanuwan ta gaban sa na fad'uwa ka da Suhail d'in ya lalata y'ar mutane. "Ya Suhail ya ce ta bi shi". Fad'in Fanan in I don't care manner, don ita Sam ba ta d'auka wani abun zai ma ta na cutarwa ba. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Maza Fanan je ki fad'a Hajiya da sauri". Fad'in Malam. "Malam mai ya faru?" Fad'in Fanan zuciyar ta na bugawa saboda yadda malam ya yi magana. "Kar ki yi tambaya Fanan, ke dai yi sauri je ki fad'awa Hajiya Suhail ya ta fi da Binty". Fad'in malam. Da sauri Binty ta mik'e ta re da yin part d'in Anna da gudu don zuwa fad'in abunda malam ya aiketa ta fad'i.
Kusada gate d'in k'arshe, wato gate d'in da Oga Solomon ke gadi Suhail ya rage gudun mota ta re da ciro sigari a cikin aljihun wandon sa ya saka a baki.
"Baba Haruna, see that stupid boy. He finish chop the girls, now he wan return them back to their houses". Fad'in Oga Solomon ya na tab'a k'afar Baban Haruna. "Mtsww, I pray for da boy may him get HIV, may be he will stop following womens. Mtsee very bad pikin". Fad'in Baban Haruna.
Wani irin horn Suhail ke dannawa kamar zai cire kunnuwan Oga Solomon da Baban Haruna. Da gudu Oga Solomon d'in ya ta shi ta re da wangale gate d'in gidan. Sai da Suhail ya zo gab da Oga Solomon d'in ka na ya sauke glass d'in motar ta re da turo kan sa waje ya saka sigari a baki ya na kallon Oga Solomon. Oga Solomon ya soma lalube-lalube a jikin wandon shi ya Ciro lighter ta re da kunnawa Suhail d'in sigarin. Idanuwan sa ne su ka sauka a kan Binty da ke ta zare idanuwa. Gaban Oga Solomon ne ya buga da k'arfi ta re da fad'i cikin zuciyar sa, "This girl don finish. Jesus helf her".
Da mugun gudu ya ja motar ta re da barin gidan. Oga Solomon kuwa cikin hanzari ya kulle gate d'in ta re da dawowa wajan da Baban Haruna ya ke zaune ta re da fad'in, "Heeeyyy! Baba Haruna dis girl don finish wallahe". "Which girl?". Fad'in Baban Haruna ya na kallon Oga Solomon d'in. "Da pretty girl way dat stupid old bitch bring dis money". "Watin come happing to her?". Baban Haruna ya fad'a a firgice. "I saw her with my eyes open in dat stupid boy car. I known he will go and rape that girl. Chaii! I pity for her". Oga Solomon ya fad'a kamar zai yi kuka. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allah dai ya tsinewa yaron nan. How did she even follow him? Kai Allah ya cece ki yarinya". Fad'in Baban Haruna ci ke da jimamai.
"Anna! Anna!! Anna!!! Ki na ina?". Fanan ta fad'a tun ta na hawa sama har ta k'arisa shiga parlourn saman. Kicib'is su ka yi da Anna da ta fito a gigice. "Lafiya Fanan ki ke min irin wannan kiran? Ina Binty?". Anna ta fad'a ta re da rik'o kafad'un ta. "Yaya Suhail ya tafi da ita a mota". Fad'in Fanan. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un3×". Hajiya Na'ima ta fad'a ta re da d'aukar wayar ta akan center table ta nufo stairs don saukowa parlourn k'asa Fanan bi ye da ita. Wasu numbobi ta danna a wayarta ta re da kara wayar a kunnanta. Ringi d'aya cikin ba biyu wanda ta kira ya d'aga ta re da fad'in, "Assalamu alaikum Anna....." Katse shi ta yi ta re da fad'in, "Wa'alaikumussalam. Fu'ad zo gida yanzu ina nai man ka. Ko kuma ka da ka zo gida, duk in da Suhail ya ke ka naimo shi ka dawo min da yarinyar da ya fita da ita. Za ka gan ta ba ta wuce Fanan ba. Dan Allah ka hanzarta yanzu ka naimo shi tun kamin ya lalata amanar da aka bar min". "Yanzun nan kuwa Anna". Fad'in barrister Fu'ad ta re da katse wayar. Wa ni number ya yi dialing bugu d'aya aka d'aga, ta re da fad'in, "Sai Oga, da girman kujeran Barrister". "Ka na ji na ko kacha, yanzan nan na ba ka minti biyar ka binciko min in da Suhail ya ke ka kira ni ka fad'a". "An gama Barrister". Fad'in kacha ta re da katse kiran. Barrister Fu'ad kuwa mik'ewa ya yi ta re da tattara files d'in da ke gaban shi ya jawo drawer ya saka ta re da d'aukar key d'in motar shi ya fito ya kulle office d'in shi ya fito zuwa wajan da motar shi ta ke ya shiga ta re da mata key ya bar High court d'in don cika umarnin mahaifiyar sa.