Ba ni da gata - Chapter 8
Ba ni da gata Chapter 8: Ba ni da gata Chapter 8. Bubu abunda ka ke ga ni a d'akin sai hayak'in shi-sha da ya turnik'e d'akin kamar d'akin boko. Sai k'arar…
3,197 words
Bubu abunda ka ke ga ni a d'akin sai hayak'in shi-sha da ya turnik'e d'akin kamar d'akin boko. Sai k'arar kid'an da ke ta shi kamar gidan casu. Zuk'ar shi-shan ya ke yi cike da kwarewa ya na fesar da hayak'i. Y'an mata ne guda hud'u. D'aya ta na wajan kan sa ta na masa massage a kansa. D'aya kuma ta na shashshafa jikinsa. D'aya kuma ta na mammatsa masa k'afarsa. D'ayar ta karshe kuma ta na jujjuya jikinta a gaban sa. Gyefe guda kuma cuncurundon abokansa ne su takwas ko wanne da shi-sha port da ya ji mix da kayan ma ye a ciki. Biyu daga cikin abokan sa kuma su na cikin d'aki d'aya da y'an matansu su na amfani da su. "Hey Suhail, har yanzu fa ba'a kawo ma na abinci ba, ko y'an aikin gidan ku sun k'are ne?". Wani bu'de idanu Suhail ya yi ta re da kulle su, ka na ya lallubi wayarsa da ke kan center table d'in gyefar kujeran da ya ke kai. Dialing Sweet mom ya yi ta re da karawa a kunnan sa.
"Ke saboda ke bak'ar annamimiya ce, munafuka shi ne ki ka kai mata y'ar aikin da na ce ki ka wo min ko? To ko ki je duk yadda za ki yi ki maido ta waje na, ko kuma wallahi zaman abuja ya ga gare ki wallahi". Fad'in Hajiya Mansura kamar za ta kwad'awa Kandala ma ri. "Hajiya ki min rai dan girman uban giji, wallahi ke nai niyyar ka wo ma wa ita shine ta ce na bar mata ita ke kuma na sa mo ma ki wata. Dan Allah ki yi hak'uri ki ba no zuwa jibi wallahi zan sa mo mi ki wacce ta fi wannan girma da ko mai, wacce za ta iya duk ayyukan da za ki saka ta". Fad'in Kandala. "Za ki rufan ba ki ko sai na kwad'a mi ki mari. Ita wancan yarinyar na ke so. Duk yadda za ki yi, ke ki ka sani". Ka min Kandala ta k'ara magana, wayar Hajiya Mansura yai k'ara. D'aukar wayar ta yi a kan kujera, ganin mai kiran wayar ne ya sa Hajiya Mansura ta sallami Kandala da hannu ta re da d'aga kiran ta ce, "Son ya aka yi? Wani abu ka ke buk'ata?". Kasancewar Suhail ya tsumu da shaye-shaye, muryan sa har fashewa ta yi, idan yai magana za ka d'auka gardi ne d'an shekaru talatin, nan kuwa ko shekaru ashirin bai yi ba. "Mom, we need food right now. Amma kar ki turo min wannan y'ar iskan yarinyar". "Ka da ka damu son, ai tuni na kore ta yau d'in nan. Har na sa an kawo maka wata ma. Kyakkyawa da ita, wacce za ta iya duk aikin da ka saka ta. Ba ma za ta wuce shekaru goma ba. Sai dai fa wancan matar ta yi ma na overtaking". Yamutsa fuska ya yi ta re da fad'in, "Wacece wannan a cikin gidan nan da za ta mi ki overtaking ki na kallon ta kuma". "Wacece kuwa ban da matar uban ka mai isa wai ita jinin sarauta". "To ina ruwa na da jinin sarautar ta. Ko da a ce sarkin ne uban ta, ya min ba kyale shi zan ba. Don haka a karb'o yarinyar nan ko ta halin k'ak'a, ku ma a kawo min abinci in five minutes". Suhail na ga ma fad'in haka ya datse kiran ta re da kwantar da kan shi a jikin kujera. Don har hankalin shi ya tashi da ya ji an samu yarinyar y'ar shekaru goma. Lallai ashe zai more.
**********Hannun ta d'auke da faranti ta dawo parlourn. Murmushi ta yi saboda ganin Binty da ke wajan labule sai shafawa ta ke yi. Aje farantin ta yi a kan center carpet d'in da ke shimfid'e a parlour. K'arar ajiye farantin ne ya dawo da hankalin Binty wajan Hajiya Na'ima da ke tsaye ta na kallon ta. "Dawo nan ki zauna kici abinci". Fad'in Hajiya Na'ima ta re da nu na mata abincin. K'arasowa ta yi ta re da zama a k'asa ka na ta bud'e plate d'in saman da aka rufe abincin. Zaro idanuwa Binty ta yi ta na kallon farfesun kaza da ya sha kayan lambu harda irish poteto a ciki ta re da fad'in, "Duka wannan nawa ne?". Ta fad'i haka ne ta na kallon Hajiya Na'ima da ita ma kallon na ta ta ke yi. "Eh duk na ki ne ke d'aya. Ciki sai ya ishe ki, idan ba ki k'oshi ba ki yi min magana zan k'aro mi ki". Fad'in Hajiya Na'ima. "Kai amma nagode mi ki sosai. Gaskiya garin nan Ku na da kirki, ku na ba wa mutane abincin ma su dad'i sosai". Ta fad'i hakane ta re da d'aukar tsokar cinyar kaza ta yaga". "Wayyiwooooo dad'i kashe ni. Wannan na ma da dad'i ya ke. Dan Allah ki rik'a ba ni kullum zan rik'a miki duk abunda ki ke so". Binty ta fad'a ta na karkad'a kan ta. Girgiza kai Hajiya Na'ima ta yi ta re da murmushi ta yi hanyar da zai sa da ta da bedroom d'in ta. Sai da Binty ta cinye farfesun rabin kazan nan da Irish d'in nan tas. Ka na ta kafa kai ta shanye roman ta re da sud'e hannunta ta d'auki goran ruwa ta kafa baki ta sha fiye da rabi, ka na ta ajiye ta re da sakin gyatsa ta jingina da kujeran. Cikin k'ank'anin lokaci bacci ya yi awon gaba da ita.
*DAN GIRMAN UBANGIJI KA DA KI FITAR MIN DA BOOK. IDAN KIN SAN ZA KI FITAR DAN ALLAH KI MIN MAGANA NA MAYAR MI KI DA KUD'IN KI*
*DAN ALLAH IDAN KIN GA NI BA KI SIYA BA KA DA KI KARANTA KU MA KAR KI YI SHARING, KI NAI MI NUMBER 08128755583 KI SI YA SABODA KI KARANTA DA GUMIN KI BA NA SATA BA*.
*_BA NA TYPING SATURDAY AND SUNDAY_*
*MATAR SAYYADEE* 🌹 *17-18*🌹
K'arfe biyu da rabi na rana wata y'ar budurwa wacce ba za ta wuce 13-14 years ba ta shigo d'akin sanye da uniform dark purple suit da skirt shi ma dark blue. Sai rigar ciki da ta kasance light purple. A jikin gaban suit d'in akwai logo na makaranta mai d'auke da tambarin makarantar da kuma logon su. Sai baby hijjab dai-dai wuyanta shi ma da ya kasance dark purple. Jakarta fashion mai kyau shi ma dark sagale a kafad'ar ta. Ba k'aramin kyau kayan su ka mata ba. Tsaye ta yi a kan Binty da ke ta sharar bacci gaban rigar nan ya yi biji-biji da roman farfesun kazan da ta gama shi. "What a beautiful creature!". Fad'in Fanan da ta d'an duk'o ta na shafa gashin kan Binty don ta tabbar shin na ta ne ko kuwa attachment a ka sa ka mata. Murmushi Binty sabod mafarkin da ta ke yi ta re da mirginawa k'afarta ya sauka akan plate d'in da ta gama cin abincin. Ita kuwa Fanan mutuwar tsaye ta yi saboda wa ni mugun kyau da murmushi nan ya k'ara fad'ad'a kyawun fuskanta sakamakon dimples d'in ta da ya lob'a. Ko ma wa side d'in da ta juya Fanan ta yi ta re da tsugunnawa ta na kallon fuskan Binty. "Ke kyakkyawa ce". Fanan d'in ta fad'a ta na tab'a kumatun ta in da ya lob'a. "Idan kin ga ma k'are mata kallon, sai ki wuce ki je ki cire uniform ki yi wanka ki zo ki ci abinci". Fad'in Hajiya Na'ima da ta fito hannunta rik'e da waya ta na dannawa. Ta shi Fanan ta yi ta re da isa wajan mahaifiyarta ta re da rungume ta ta ce, "Anna I'm home". Fanan ta fad'a ta re da sakin Hajiya Na'ima ta mai da kallon ta izuwa ga Binty da har yanzu ke bacci ta ce, "`D'un `b'ingum umoy'e? (Wa cece wancan?)". "O inkesse mu'aiki. Unangai taimakima I aaki. (Sabuwar y'ar aiki ce, za ta rik'a taimaka maki da aiki.)". "B'ingil gehil igillab'i. (Yarinyar kyakkyawa ce) muheb'b'i higo munangaimi labari imakko. (Na samu k'awar da za mu rik'a labari da ita). Anna gad'amu tu makaranta amin. Muhwalloimu to makaranta amil onni. (Anna ki saka ta a makarantar mu. Zan nu na wa y'an makarantar mu ita.)". Fad'in Fanan da harcan fulatanci. "Ta wan nu muwad'aimu tu makaranta d'um, yahu itta ka ya ma d'a gara nyama abinci. (Kar ki da mu, zan sa ta a makaranta. Je ki can za ka ya ki zo ki ci abinci)". Fad'in Hajiya Na'ima da harshan fulatanci. "Migodeki Anna imiyid'd'uma. (Nagode Anna ina son ki)". "Mimma imiyid'd'uma Fanan. (Ni ma ina son ki Fanan)". Fad'in Hajiya Na'ima ta na murmushi ta re da jin k'aunar y'ar autar ta ta. Ita kuma Fanan ta bi corridor ta wuce d'akin ta ta na jin dad'in sabuwar k'awa da aka kawo mata. K'arisawa wajan da ta ke kwance Hajiya Na'ima ta yi ta re bubbuga k'afarta a hankali. "Hadaan kai ne?". Binty ta fad'a ta re da bud'e idanuwanta a kan Hajiya Na'ima. "Au ke ce? Ashe mafarki na ke yi". Fad'in Binty ta na mitsike idanuwan ta. "Ki kira ni da Anna ba ke ba, kin ji?". Fad'in Hajiya Na'ima ta re da d'ago Bintyn ta tashi zaune. "Anna fitsari na ke ji". Binty ta fad'a ta kamar za ta yi kuka. "To ta shi mu je in kai ki d'akin Fanan sai ki yi a can har da wanka ta re da alwalama sai ki yi sallah kin ji". Hajiya Na'ima ta fad'i ta re da ruk'o hannun Binty su kai hanyar d'akin Fanan d'in. Knocking Hajiya ta yi ta re da tura k'ofar ta shiga. Babu kowa a d'akin dai k'arar ruwa da ta ke ji daga bayin. Haka ne ya tabbar ma ta da Fanan d'in ta na ci ki ta fara wanka. Binty kuwa sai bin d'akin ta ke da kallo da komai ya kasance baby pink. Ga hotunan Barbie nan a jikin bango da kuma manya manyan teddies nan a kan gad'on da shi kan shi pink colour ne har da zanin gad'on. "Zauna a nan ki jira ta fito, sai ke ma ki Shiga ki yi wankan". Fad'in Hajiya Na'ima. Ka min Binty ta ce wa ni abu Fanan ta bud'e k'ofar ta fito d'aure da towel a jikin ta. Zaro idanuwa Fanan ta yi cike da murna ta re da fad'in, "Beauty kin tashi?". Ta fad'i hakane ta re da ka mo hannun Bintyn ta zaunar da ita a ba kin gado. Binty kuwa mamaki ne ya kashe ta yadda kowa a nan garin ya san sunan ta. "Hammu d'oho kullamu nu'uwatta amfani i`bayi, sai kukkama dirkaya ma d'a uwad'a. (Ga tanan ki koya mata yadda za ta yi amfani da ba yi. Sai ki ba ta daga cikin ka yan ki ta saka). Da ra mu had'a na mu gite o`juli. (Ki sa ka ma ta idanu tai sallah)". Fad'in Hajiya Na'ima cikin harshan fullanci. "To Anna. Dussu du a`han, hunanga taka waliki? (D'aki na za ta rik'a kwana?)". Fanan ta fad'a ta na kallon Anna. "Eh, d'an nangutun kawaliki tugu`u. (Eh a nan za ku rik'a kwana ta re)". Fad'in Hajiya Na'ima. "Yauwa Anna, mihiggimmi. (Yauwa Anna haka na ke so)". Fad'in Fanan. Har Hajiya Na'ima ta kai bakin k'ofa Fanan d'in ta sa ke cewa, "Anna daga k'auye gard'a d'o? (Anna daga k'auye ta zo?)". "Eh". Shi abunda Anna ta ce ta re da ficewa daga d'akin.
Ka mo hannun Binty Fanan ta yi ta re da fad'in, "Menene sunan ki? Ni suna na Fanan Usman Mai Rabo. Ke fa?". "Suna na Binty ummmm, ummm Binty.... Binty.... Yauwa, Binty Hashimu mai goro". Binty ta fad'a ta na mai jin dad'in tuno sunan da Kandala ta fad'a mata a kan duk wanda ya tambaye ta sunan mahaifin ta. "Nice name. Amma sunan ki kenan Binty ko kuwa Nick name d'in ki ne?". Fad'in Fanan. "Nee name? Menene nee name kuma?". Dariya ce ta zo wa Fanan d'in, ai kuwa ta sake shi har towel d'in jikin ya kusan za me wa. "Ba ki tab'a zuwa boko ba ne?". Fad'in Fanan. "Ni ban tab'a zuwa ba. Hadaan ne kawai ke zuwa". Fad'in Binty. "Wa ye kuma Hadaan?". Fanan ta tambaya. "Ba ki san shi ba". Binty ta ba ta amsa ta re da sa ke fad'in, "Fitsari na ke ji sosai". "Oh sorry, ta so mu je in nu na mi ki yadda za ki yi amfani da bayin". Fanan ta fad'a ta re da nufar bayin Binty na bin ta a ba ya. Kai hannu Fanan ta yi kan wani kyakkyawan panfo sai ga ruwa shaaa. Wani irin tsalle Binty ta yi ta re da ficewa daga bayin da gudu jikinta na rawa. Da gudu ita ma Fanan ta bi bayanta ta re da fad'in, "Lafiya Binty? Mai ya faru?'. "Hannu na ga kin kai a jikin irin wannan abun mai kama da panfo kawai sai na ga ruwa ya zubo. To Allah akwai dodo a cikin bayin nan". Dariya Fanan ta yi ta re da ka ma hannun Bintyn su ka ko ma ba yin. "Ki kwantar da hankalin ki babu wani dodo a cikin ba yi. Zan ko ya miki yadda a ke amfani da komai a cikin nan wajan". Sai da Fanan ta ko ya mata yadda ake amfani da komai, kasancewar Binty ta na da saurin fahimta da d'auke abu a kai, ta fahimci yadda ake amfani da bayin. Don Fanan ba ta fita ba sai da Binty ta gwada amfani da wa su abun tukun ta fita. Ko da Binty ta fito tu ni har Fanan ta gama shiryawa cikin wando pink da riga white, sai tai parking gashin ta a gyefe da pink d'in ribom, kasancewar ita d'in y'ar kwalliya ce kuma ita ma ta na da gashi ba laifi don ya zubo a kafad'arta. "Yauwa kin yi alwala?". Fanan ta tambayi Binty. "A'a ban yi ba". Binty ta ba ta amsa. "To ko ma ki je ki yi, lokacin sallah na ta wuce wa. Ba kyau wasa da sallah". Fad'in Fanan. Komawa cikin bayin ta yi ta re da d'auro alwala ko in ce shirme ka na ta dawo da'kin. Tu ni har Fanan ta fiddo ma ta da wani riga da skirt y'an kanti kalar pink da ratsin purple a jiki. Don Fanan gaba d'aya kayanta da wuya ka ga babu pink colour a jiki. Don ko a school sunan ta pinky. "Na yi alwalar". Binty ta fad'a. "Yauwa goge jikin ki sai ki shafa wannan mai d'in ki saka wad'annan kayan ki sai ki sallah ga praying mat nan na shimfid'a miki". Kallon mai d'in ta din ga yi ta re da fad'in, "To Fanan ya ake shafawa? Ban iya ba". Cike da mamaki Fanan d'in ke kallonta ta re da fad'in, "Na tab'a so d'aya, amma ba ni na shafa ba, wata ce ta shafa min". "Lord in heaven". Fad'in Fanan ta re da rik'e goshin ta. "Mai ki ka ce?". Binty ta fad'a ta na kallon Fanan d'in. "Ohhh nothing. Ban ce komai ba. Yanzu dai kalli ki ga yadda ake shafawa". Fanan ta fad'a ta re da matso lotion d'in ta shafa a jikin. Ita ma Binty ta yi kamar yadda ta ga Fanan d'in ta yi. Powders Fanan ta d'auko ta shafa mata ta re da taje mata gashin kan ta da ya zubo har tsakiyar bayanta ta kuma ka ma mata shi da ribom ta bar jelar ba ta re da ta nad'e ba. "Ki na da gashi Binty". Fad'in Fanan d'in. "Ke ma ki na da shi Fanan. Na ki ba b'aki ba ne irin na wa, ya fi na wa kyau". "Ke! Allah na ki ya fi kyau, du ba fa, ga cika da tsawo ga shi bak'i sosai. Yanzu dai ta shi ki yi sallah sai mu je parlour". Fad'in Fanan ta re da mik'a mata hijjab. Kayan da Fanan d'in ta fito mata da shi ta saka ta re da hijjab d'in ka na ta hau kan darduman. Kai tsaye ba wani tada ik'ama bare a kai ga karatun sallah ta tafi sujada. Waro idanuwa Fanan ta yi ta na kallon Bintyn ci ke da tsoro da kuma tsan-tsan mamaki. Ita kuwa Binty bayan ta d'ago daga Sujadar sai ta yi ruku'u ta kuma k'ara yin sujadar. Ha ka ta din ga yi har sai da ta yi raka'a takwas ka na ta ce, "Assalammaa alaiku". sau biyar ta re da mik'ewa ta kalli Fanan ta re da fad'in, "Fanan na gama". Ba ki sake Fanan ta ce, "Yanzu wannan sallah ce ki ka yi? Haka ake sallan?". "Eh haka naga a na yi a garin mu". "Lallai! Wallahi to duk y'an garin ku ba su iya sallah ba. Ku ma muje wajan Anna ki je". Fad'in Fanan ta re da yin hanyar parlour Bintyn na bi ye da ita a baya. A parlour su ka samu Anna d'in ta na kallan tashar Arewa 24 su na haska shirin mata a yau. "Anna, wallahi i`matsala. Onni owawa julde. Owi b'e gari rimab'b'e, nihib'b'e julirta. (Anna akwai matsala. Wannan yarinya ba ta iya sallah ba. Kuma ta ce y'an garin su duk haka su ke sallar)". Kallon ta Anna ta yi ta re da fad'in, "Innoye ojulurta? (Yaya ta ke salar)". "Daga sujjada ohud'd'i julde. Ko jande julde uwatta. (Daga sujada ta ke fara sallar. Ko karatun sallah ba ta yi)". "Gaskiya i`matsala. Unangai yaki jande to modibbo mud'un ware. (Gaskiya akwai matsala. Za ku rik'a zuwa karatu ta re idan malamin ku ya zo). Amma nan ga ka, ekki tukimo i hankali. (Ke ma ki rik'a koya mata a hankali)". "To Anna, mi'ekki taimu jande". Fad'in Fanan. "To yahun yama abinci". Fad'in Anna ta re da mai da duban ta ga TV, amma sam hankalin ta ya bar TVn ya ko ma tunanin Binty gaba d'aya. "Lallai yarinyar nan ta na buk'atar taimako". Fad'in Anna cikin zuciyar ta.
Fanan kuwa Dining d'in da ke parlourn ta nu fa ta re da zama ta zuba farfesun Kaza da kuma sinasir, ka na ta zuba wa Bintyn. Da kyar Fanan ta iya cinye rabin sinasir ta re da cinyar kaza ta tura plate d'in gaba. Ita ma Bintyn kasancewar ta k'oshi rabin sinasir d'in taci. Kazan ne dai ta k'ara cin cinya da wani tsokar nama har ta lalata gaban rigar ta da roman farfesun Kazan nan. "Oh my God! Du bi yadda ki ka lalata gaban rigar ki, ga shi malam ya ku sa zuwa ku ma ta re za mu je mu ko yi karatu a wajan shi. Mu je in ba ki wata rigar ki canza". Fad'in Fanan ta re da mik'ewa. Ita ma Bintyn mik'ewa ta yi ta re da bin bayan Fanan zuwa d'akin ta.
*_________* Tsaye ya ke gaban katotan plasma da ke manne a jikin bango d'akin. Hanu ya kai ta re da k'aro volume d'in home theatern, ka na ya canza music ta cikin wayar da ke hannun sa kasancewar da AUX ya ke amfani. Wakar D'banj ya saka fall in love ya shi ga bin wak'ar kamar haka.