Ba ni da gata - Chapter 7
Ba ni da gata Chapter 7: Ba ni da gata Chapter 7. Hanci, baki, ido Binty ta saki ta na k'arewa wannan makeken gida da su ka shigo cike da k'auyan ci. Ga…
3,322 words
Hanci, baki, ido Binty ta saki ta na k'arewa wannan makeken gida da su ka shigo cike da k'auyan ci. Ga ma'aikata nan ta ko ina. Masu gyaran fulawa daban, masu bai wa fulawan daban. Masu kula da tantabaru daban, mata y'an aiki kuwa sun kai goma. Ka'totan gida mai d'auke da part part kusan goma. A gate na shida ne ma'aikatan gidan maza su ke da quarter d'in su. Su kuma mata quarter d'in su ya na cikin asalin gidan. Hakan tsarin mai gidan ne wato Alhaji Usman Mai Rabo. Wani shashi su ka fara nufa wanda shine shashin uwargidan Alhaji Usman Mai Nasara, auran saurayi da budurwa kenan tun bai da ko sisi. Zaune ta ke a kan d'aya daga cikin tantsama tantsaman kujerun d'akin. Sanye ta ke cikin wata doguwar rigar shadda wanda ya amshi jikinta. A k'allah za ta kai shekaru amsin a duniya, amma sam jikinta bai nuna hakan ba saboda kyawun jikinta da kuma hutu da gyara da jikin ke samu. Kyakykyawa ce sosai kuma fara tas. A ba kin ta akwai hak'orin maka har guda biyu gyefe da gyefe kalar golden wanda ke k'ara haskaka fararan hak'oran ta. Waya ce a hannunta ta na karanta Alqur'ani mai girma a cikin wayar. Sallama su ka yi, sai da Hajiya Na'ima ta kai aya sannan ta rufe wayar ta re da amsa sallamar ta na mai kallon bakin k'ofar. Shigowa Kandala ta yi ta re da zubewa a k'asa ta na gaida uwargida a wajan Alhaji Usman. Gyefe guda kuma ta na tsungulin k'afar Binty a kan ita ma ta gaida hajiyan, amma inaa Binty ba ta san ma ta na yi ba. Domin ta shagala da kallon tsararran d'akin da ya kusa tsayar da numfashin ta. "Kandala ya gida? D'azu kuwa idan ba kunne na ba ne, na ji kamar Fasila ta na fad'a min kin zo d'azu gaishe ni, ni kuma ina sallah". "Eh kwarai ni ce Hajiya. Na zo ki na sallah shi ya sa na tafi". Fad'in Kandala. Jinjina kai Hajiya Na'ima ta yi ta re da mai da kallon ta izuwa ga Binty da a kallon farko ta ji ta shiga ran ta, ta ce, "Kandala wannan kyakkyawar yarinya fa?". K'ara gyara zama Kandala ta yi ta re da fad'in, "Hajiya Mansura ce ta ce na kawo mata wata y'ar aikin wacce na kawo watan ba ya ba ta yin abunda ya da ce, shi ne na kawo wannan d'in". "Ita d'in wannan y'ar wacece? Kuma ki na da tabbacin za ta iya abunda wancan d'in ta kasa?". Hajiya Na'ima ta jeho mata tambaya ta re da tsare ta da idanuwa. "Em..ehyyy.. Ita d'in yar k'ani na ce a can Saminaka". Fad'in Kandala ci ke da in'ina. Haka nan Hajiya Na'ima ta ji ba ta gam su da zan can da Kandala ta fad'i ba. Musamman da ta ji ta na in'ina. "Me ye sunan ta?". Hajiya ta sa ke tambayan ta ta na mai tsare ta da idanuwa. A nan ne kuma gaban Kandala ya fad'i, domin Sam ba ta san sunan yarinyar ba. Ta man ta shaf ta tambaye ta. Tab'o Binty ta yi ta re da fad'in, "Ke wai ba ki iya gaisuwa ba ne? Ki gaishe da Hajiya mana". Sai a lokacin hankalin Binty ya dawo. Hajiya ta kalla ta re da fad'in, "Ina wuni?". Da ma Hamdan ya ko ya mata yadda ake gaisuwa. "Lafiya k'alau Beauty, ki zauna mana". Binty kuwa wani dad'i ne ya kusan sumar da ita saboda sunan da Hajiyan ta ki ra ta da shi. Kallon Kandala ta yi ta re da fad'in, "Kin ga ni, ita ma ta san Hadaan. Ga shi ta ki da ni da irin sunan da ya ke kira na da shi". Murmushi Hajiya Na'ima ta yi ta re da fad'in, "Yaya sunan ki y'an mata?". "Binty y'ar bola". Binty ta fad'a ta na murmushi. Kallon Kandala Hajiya ta yi, ka na ta mai da kallon ta izuwa ga Bintyn ta re da fad'in, "Binty 'yar bola kuma?". Kamin Binty tai k'arin bayani caraf Kandala ta amshe ta re da fad'in, "Binty ai a kwai shirme. A can garin mu ne fa ake kiran ta da haka kasancewar ba ta k'aunar wanka kullum dak'an-dak'an za ki ganta. Shi ne yara su ke kiran ta da Binty y'ar bola. Shine fa duk wanda ya tambayeta sunan ta sai ta ce Binty y'ar bola. Amma Sunan ta Binty ne". Dariya Hajiya Na'ima ta yi ta re da fad'in, "Duk yarinta ne za ta bari, wata rana ma idan aka ce tai kwana d'aya ba wanka ba za ta iya ba. Amma fa ni da ba din kin ce Mansura ta ce ki kai mata ita ba, ai da na ce ki bar min ita a waje na". "Ai ba matsala Hajiya, idan ki na son ta ki karb'e ta, idan ya so na kawo mata wata. Ai duk d'aya ne da ke da ita". Fad'in Kandala kamar mutuniyar kirki. "A'a ba za ai haka ba. Ai tun da ta riga da ta mi ki magana, ki kai mata ita kawai. Ni da ma ba y'an aiki na ke nai ma ba. Kawai yarinyar ce ta shiga rai na". Fad'in Hajiya Na'ima. "Wallahi Hajiya ba matsala ki d'auke ta kawai". Shuru Hajiya ta yi ta na wani tunani. Tabbas idan har ta ba ri Hajiya Mansura ta karb'i wannan yarinya to ba bu makawa d'an ta Suhail sai ya lalata ta kamar yarda ya saba lalata y'ay'an jama'a uwar sa ba d'aure masa gindi. "To ki bar min ita". Fad'in Hajiya Na'ima. Hankad'a labulan d'akin ta yi ta re da fad'in, "Wannan k'aya ne wallahi. Yarinya ni na saka a kawo min ita, kuma babu wacce ta isa ta karb'e ta idan ba ni ba".
*HMMM AKWAI FA CAKWAKIYA.*
*ASSALAMU ALAIKUM READERS, GA NI NA ZO MA KU DA SABON LITTAFI NA MAI SUNA A SAMA, WANDA YA ZO DA ZAFI-ZAFIN SA, KUMA NA TABBATA ZA KU JI DAD'IN SA. BA ZAN CI KA KU DA SURUTU BA, KAWAI KU BI NI A FREE PAGES, KU DA KAN KU ZA KU GA NE BOOK D'IN NA DABAN NE. KAWAI KU NU NA MIN ONE LOVE WAJAN SIYAN BOOK D'IN AKAN FARASHI AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA:*
*FREE PAGES SUN K'ARE*
*Normal group shine mutum zai bi ya 500 idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300.*
*VIP kuma 1000 ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700.*
*MUTANAN NIGER KUMA ZA SU BI YA KAMAR HAKA*:
*Normal group shine mutum zai bi ya 500F idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300F.*
*VIP kuma 1000F ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700F.*
*EVIDENCE OF PAYMENT 08128755583*
*IDAN HAR BA KI KARANTA BOOK D'IN NAN BA WALLAHI KIN YI MISSING.*
*DAN GIRMAN UBAN GIJIN HALITTA IDAN HAR KIN SAN ZA KI FITAR MIN DA BOOK, KA DA KI SA YA, WALLAHI BA NA BUK'ATAR KUD'IN KI. KI TAIMAKA DAN ALLAH*
*MATAR SAYYADEE* 🌹 *15-16*🌹
Wani kanne ido d'aya Hajiya Na'ima ta yi ta na kallon Hajiya Mansura wacce ita ce matar Alhaji Usman Mai Rabo ta uku, wa to ta tsakiya. "Ya ki ke haushi ke ba kare ba Mansura?". Hajiya Na'ima ta fad'i ta na sakin wani shu'umin murmushi. Hajiya Mansura kuwa kallon Hajiya Na'ima ta yi, ta kuma mai da du ban ta ga Kandala da tu ni ta jik'e da zufa sai sa ka hannunta ta ke ta na sharewa. Sa ke mai da du ban ta tai izuwa Hajiya Na'ima ta re da fad'in, "Ni ki ke dangantawa da kare a gaban wad'an nan fak'iran". "You made me sai that. Ba yan kin fi kowa sanin yadda na tsani ihu a kai na. Ku ma na sha mi ki warning a kan shigo min d'aki ba bu sallama. Yarinya ku ma na hana, ba zan ba ki ita ba. Ta sa mo mi ki wata. Wannan ta wa ce". Fad'in Hajiya Na'ima ta na kallon cikin idanun Hajiya Mansura da ke jin kamar tai bindiga. "Mu zu ba mu gani". Fad'in Hajiya Mansura ta re da watsawa Kandala wa ni mummunar kallo ka na ta nufi k'ofa. Sai da ta kai ba kin k'ofa ka na ta ce juyo ta kalli Kandala ta re da fad'in, "Ki sa me ni yanzu a sashe na". Ta na gama fad'in haka ta wuce fuuu.
Kallon ta Hajiya Na'ima ta yi ta re da mik'ewa daga kan kujeran da ta ke ta ce, "Ki jira ni yanzu ina zuwa". Ta na gama fad'in haka tai hanyar stairs. In ten minutes ta dawo parlourn hannun ta rik'e da wani babban ledan AYK da ke d'auke da tambarin fiffiken d'awisu a jiki. Atampopi ne guda uku masu tsada da kuma turare da kuma duba d'ari a ciki ta mik'awa Kandala ta re da fad'in, "Za ki iya tafiya yanzu". K'ara tankwashe k'afa ta yi za ta fara koro godiya Hajiya Na'ima ta d'aga mata hannu ta re da fad'in, "Ba na son jin komai, kawai ta shi ki tafi, idan ina buk'atar ki zan nai me ki". Mik'ewa Kandala ta yi ta re da nufar k'ofa. Da sauri Binty da tun d'azu sai k'ara k'arewa D'akin kallo ta ke yi ta bi ba yan ta ta re da fad'in, "Ina za ki ta fi ki bar ni kuma? Ina Hadaan d'in?". Kallon Kandala Hajiya Na'ima ta yi ta re da fad'in, "Zan haura sama, idan kun ga ma, ki turo min ita sama". "To Hajiya in sha Allah, Allah ya k'ara girma". Cikin zuciya Hajiya Na'ima ta furta ameen ta re da hayewa sama. Kallon ta Binty Kandala ta yi ta re da b'ata rai sosai ka na ta ce, "Kin man ta abunda na ce mi ki kenan? Ba na ce mi ki Hadaan ya je k'asar waje karatu ba. Kin yi alk'awari za ki yi duk abunda na ce ki yi. Hakan shi zai sa na kawo mi ki Hadin d'in ki. Amma idan har za ki rik'a bijirewa umarni na, to wallahi ba zan ka ko mi ki Hadin d'in ba. Ku ma daga yau duk wanda ya tambayi sunan ki, ka da ki sa ke ki k'ara ce wa Binty y'ar bola. Sunan ki Binty kawai. Kuma idan a ka tambaye ki ni wacece a wajan ki, ki ce ni baabar ki ce. Idan kuma a ka tambaye ki sunan garin ku ki ce Saminaka, sunan mahaifin ki kuma ki ce Hashimu mai goro, kin ji abunda na fad'a miki?". Kandala ta fad'i ta re da rik'e kunnanta. Gyad'a kai Binty ta yi ta re da fad'in, "Ke baaba ta ce, kuma sunan garin mu Saminaka, sannan sunan babana Hashimu mai goro. Na rik'e ai". Binty ta fad'i ta na murmushi. "Yauwa y'ar albarka. Haka za ki rik'a cewa duk a ka tambaye ki. Idan ki kai haka zan kai ki wajan Hadin cikin k'ank'anin lokaci" "To Baaba. Yan zu yau she za ki dawo?". Fad'in Binty. "Ba zan jima ba kin ji, ki yi duk abunda aka umarce ki da ki yi ban da shirme da wasa kin ji?". "To baaba zan yi duk abunda aka ce in yi tun da za ki kai ni wajan Hadaan". "Yauwa to yanzu abunda na ke so da ke shi ne ki bi can, in da ki ka ga Hajiya ta bi, za ta fad'a ma ki duk abubuwan da za ki rik'a yi a gidan nan kin ji?". Fad'in Kandala. Kallan stairs d'in Binty ta yi ka na ta mai da duban ta ga Kandala ta re da fad'in, "Yanzu can zan hau?". Ta fad'i hakan ne ta na nu na stairs d'in da hannunta. "Eh. Maza ki je ka da ta ga kin dad'e. Sai na da ke dawowa". Fad'in Kandala ta re da nufa hanyar waje ko waiwaye ba ta sa ke ba ta fice daga sasan gaba d'aya. Binty kuwa ajiyar zuciya ta sauke ta re da nufar stairs d'in da ke da zigzag kamar maciji. K'afarta ta fara d'aurawa guda d'aya, ka na ta d'ago d'ayan da k'er k'afafuwan na ta na wani irin rawa kamar za su tsinke. A step na biyu Binty ta kakare jikinta na b'ari. K'arshe dai crawling ta ko ma yi kamar yarinyar da ke koyan rarrafe. Ta na yi ta na hawaye. Fasila ce ta fito daga d'akin Hajiya Na'ima hannunta d'auke da kwandon kayan wanki za ta kai washing room, turus ta tsaya ta na kallon Binty da ke rarrafe ta re da hawaye shab'e-shab'e ta na hawowa sama. Dariya ce ta kufcewa Fasilan har laundry basket d'in hannunta ya kusa kufcewa ya fad'i tai saurin taro sa. "Lafiya ki ke rarrafe haka? Ba ki tab'a hawa irin wannan ba ne?". Fasila ta tambaya ta na dariya har da rik'e ciki. "Ni ban tab'a ganin irin wannan ba, wanda na tab'a ga ni bai da kwana-kwana haka, kuma ko shi d'in ma ban tab'a hawa ba". Fad'in Binty ta na hawaye. "Ta shi ki yi tafiya da k'afafun ki, ba bu abunda zai sa me ki, kin ji?". "Na k'i ban ta shi Allah! Salan in zurma na fad'a na mutu. Ni tsoro ma na ke ka da k'afata ta zurma ciki". Dariya Fasila ta k'ara bushewa da shi ta re da fad'in, "Ko irin ki da wad'anda su ka fi ki guda hamsin su ka ba za su zurma ba ba re Ku ma ke y'ar tatsitsiya da ke. Dallah ta shi ki yi tafiya da k'afafun ki ka da ki ba da mu". Fad'in Fasila. "Mai ke faruwa a wajan Fasila?". Hajiya Na'ima da fitowar ta kenan daga d'aki ta ji muryan Fasilan ta na b'ab'b'aka dariya. Saurin natsuwa Fasila ta yi ta re da sunkuyar da kan ta, ka na ta ce, "Wannan yarinyar ce ke rarrafe, wai tsoran ta ka wa ta ke yi". Kallon Binty da ke tsugunne a k'asa Hajiya Na'ima ta yi ta re da k'arisawa in da ta ke ta ka mo ta su ka k'arisa hayewa. "Har baabar ta ki ta wuce?". Hajiya ta fad'a ta na k'arewa Binty kallon. Ga dai rigar jikinta mai kyau da tsada sai dai duk ya yi butu-buti har da miya-miya a gaban rigar. "Eh yan zun nan ta wuce ai". Binty ta fa'da ta re da ju ya wa ta na kallon stairs d'in da ta hauro. "To mu je ki huta ki ci abinci, anjima zan fad'a mi ki abubuwan da za ki ri'ka yi". "To. Da ma yunwa na ke ji sosai". Fad'in Binty. Gaba Hajiya Na'ima ta yi, Binty na bi ye da ita a ba ya har zuwa wani tsararran k'aton parlourn da ke sama. "Zauna a nan, ina zuwa". Hajiya Na'ima ta fad'a ta re da bin wani corridorn da zai sa da ta da bedroom d'in ta. Za ma Binty ta yi a kan tamfatsetsan kujeran mai d'an karan laushi. Can ku ma ta mik'e ta na ta isa wajan labule ta na kallon su ta re da sha fa su.
"Ke Fasila shafa min dan Allah. Na ga wannan kyakkyawar yarinya da Kandala ta ka wo nan wajan Hajiya Babba ta bar ta. Ina ce Hajiyan tsakiya ce ta sa a can zo ta da Basira?". Fad'in Jummalo da ke ciro kaya a cikin washing machine. "To uwar gulma, ni ma ban sa ni ba. Ki je ki tambaye ta mana, ai kin san hanyar d'akin nata ai". Fad'in Fasila ta re da maka mata harara. Dafe k'irji Jummalo ta yi ta re da fad'in, "In mutu maza su kai ni ba mata ba. Ko ke sai da ki ka kwashi shekaru bakwai ka min Hajiya Babba ta fara ba ri ki ka fara haurawa sama, shi ma iya kacin ki d'akin aje kayan wanki ki fito da su ki kawo su nan a wanke, balle ni da zuwan jiya-jiya. Ko fa shekara ban yi ba a gidan nan. Satin gaba dai zan cike shekara guda. "Hmm to ai kuwa wannan kyakkyawar yarinya dai da sa'a ta zo, domin kuwa har babban parlourta ta shiga da ita. Zo ki ga yadda mamaki ya kusa kashe ni". Fad'in Fasila ta na kallon Jummalo da ta saki baki da hanci ta na kallon ta. "Haba dai Fasila? Hajiyan ce ta kai ta har parlourn ta wanda daga Alhaji sai y'ay'anta ke shiga?". "Yadda ki ka ji". Fad'in Fasila ta re da ficewa daga washing room d'in. "Kan bura uban caaaan! Lallai wannan yarinya kin zo da sa'a, duk da ya ke Hajiya ta kirki ce, sai dai ta na da mugun rashin yarda ne. Ko in ce duka matan Alhaji ha ka su ke. To wai ma ni ina ruwa na". Fad'in Jummalo ta re da cigaba da kwashe kayan cikin washing machine d'in.
"Oga Solomon, watin happen? You no dey talk since dat fat human wey hold that pretty girl hand pass here.". "Mtsww! Baba Haruna, Na something wey they kill me in this house. The thing way Alhaji son de so is no good, and his mother no everything way him de do. Yesternight if you see how he come back from club, ibi like say he wan kill me with his car. He horn like he wan remove my ear. He's drunk and na his baby who de drive the car. Mtsw no be that one de worry sef. Na that pretty girl who that stupid woman bring earlier, and she tell me say na madam se make she bring her to do work for that stupid child of her. I pitty for that cikili girl. I know that stupid he goat go spoil her, da boy na real ashawo. Every day him de bring three to four women to sleep with him. Imaging, this cikili pikin that is not up to twenty years. Chaiii! God they see everything". Oga Solomon ya fad'a cike da tausayi da jimami. "Huh! Mtsw. No be only you that thing they worry. Even me sef, I they pity for that girl. I cannot count the maids who that stupid little brat rape in this house. Even the girl that was fire, what's that her name? I can't remember". Baban Haruna ya fad'a ya na kallon Oga Solomon. "Sekina. Ohhh da girl is very cam". Oga Solomon ya fad'a. "Yauwa, dat her name, Sakina. He impregnate her, thats the reason why Hajiya Mansura fired her". "What? When did that happen". Oga Solomon ya fad'a da k'arfi. "Hey, ni fa matsala ta da kai kenan. Ba ka iya magana a hankali ba, yanzu idan wa ni yaji fa? Ku ma kasan dai akwai munafukai y'an kai report". Ajiyar zuciya Oga Solomon ya yi ta re da fad'in, "Mtsw, I'm sorry baba Haruna, I was shoked that's why. But the thing way Hajiya Mansora de do is not fair atol. Alhaji no nothing about this". Zaro idanuwa Baban Haruna ya yi ta re da fad'in, "I swear him no no everything about this. Alhaji na goodman. I swear if he no wating his wife and his son de do him go furnish them, he will send Hajiya Mansura to her parent house". "I pray may him come know everything way they happen in this house. I pray may hin send that old bitch to her parent house". Tab'a shi da k'afa Baban Haruna ya yi ta re da nu na masa D'an kwairo da ke ta ho wa wajan su. "An zauna ana sana'ar da aka saba kenan". Fad'in d'an kwairo ya na hararar su. Ba bu wanda ya kula su a cikin su. Oga Solomon ne ya bud'e masa k'aramar k'ofa kasancewar fi ta zai yi". "This dan kwero na original amebo". Fad'in Oga Solomon cikin rad'a. "I never see amebo before like him". Fad'in Baban Haruna ya na dariya ta re da mik'awa Oga Solomon hannu su ka tafa.