Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 27

Ba ni da gata - Chapter 27

Ba ni da gata Chapter 27: Ba ni da gata Chapter 27. *Walleh ban yi niyyar yi ba yau, kawai tausay ma ku na yi. Amma ga shi nan ku d'and'ana* ๐ŸŒน *53-54*๐ŸŒนโ€ฆ

2,663 words

*Walleh ban yi niyyar yi ba yau, kawai tausay ma ku na yi. Amma ga shi nan ku d'and'ana* ๐ŸŒน *53-54*๐ŸŒน ............Gimtse dariya Anna ta yi, don fisabilillah Fu'ad ya ba ta tausayi kuma ya ba ta dariya. "Ka ba ri zan kai su supermarket d'in da kai na, kai na je ka huta kawai". Fad'in Anna. "Anna a kan me? Zan iya kai su da kai na Allah, ba sai kin je ba". Fad'in Fu'ad da sauri. "To ai shikenan, idan lokacin ya yi, sai ka zo ka karb'i ATM d'i na, don tafiyarta gobe ne". Anna ta fad'a ta re da cigaba da kurb'an tea. "Ina da kud'i enough a account d'i na ba sai na karb'i ATM d'in ki ba". Fad'in ya Fu'ad. Binty kuwa sai da ta had'a wani kasancewar ta zubar da na ta garin tashi ta je wajan ya Fu'ad don jin abunda ya same shi a fuskan shi. "Anna amma ta re zamu tafi ko?". Fad'in Fanan ta na kallon Anna. "Eh ta re za ku tafi mana". Anna ta fad'a duk a tunanin ta supermarket d'in ta ke nu fi. Dad'i ne ya kama Fanan kamar ta tashi ta taka rawa. Bayan sun gama breakfast d'in ne, su ka tattara kayan wajan su ka kai kitchen ta re da wanke su, don haka Anna ta ce masu in dai suna gida to su za su yi aikin gida ka da su je gidan miji ba su iya komai ba.

K'arfe goma da rabi Fanan da Binty su ka yi wanka ta re da kimtsawa cikin wani ora Orange less wanda aka masu d'inkin riga da skirt. D'inkin ya amshi jikin su. Farin gyale su ka yafa ta re da farin takalmi. Ko man su iri d'aya su ka saka har d'an kunne. "Anna mun shirya". Fad'in Binty". Fad'in Binty. "Ku sauka ku jira shi a k'asa, nasan shi ma jiran ku ya ke yi". Anna ta fad'a. Saukowan su ka yi, aikuwa su ka yi arba da Ya Fu'ad d'in zaune a kan kujera ya na jiran su. Ya na ganin su ya mik'e ta re da fad'in, "Yauwa muje ko?" Ya fad'i haka ne ta re da yin gaba su ma su na biye da shi a baya. A tsakar gidan ya fiddo wayar shi ta re da yi masu salfie su duka, ka na ya yi da Binty ya kuma ko ma ya yi da Fanan. Ba k'aramin kaya su ka jida ba, har Binty ta ga abun ya yi yawa ta ce masa ya isa haka. Sai bayan azahar su ka shigo gida da kaya nik'i nik'i. Anna sai sa masa albarka ta ke yi. Sama su ka hau su ka gabatar da sallar Azahar ka na ko wacce ta shiga had'a kayanta a cikin jaka da duk wani abun da za su buk'ata.

*8:30pm* .............Sanye ya ke cikin k'ananan kaya wanda ya ke fito da shi kamar k'aramin yaro. Sosai ya yi kyau gashin kan nan nashi ya kwanta luf-luf, ga sajen nan da ya ke k'ara fito da kyawun sa. Babu abunda ke tashi a jikinsa sai k'amshin turaren Karen Kelly da vesace eros. Sallama ya yi can k'asan mak'oshinsa ka na ya murd'a handle d'in k'ofar ya shigo parlour. "Wallahi ban yarda ba wannan ai cuta ce, zan ta da ke ki ka wuce min da na baya kuma ki ka mai da ni gida. Allah sai an sake game d'in nan". Fad'in Fanan ta na k'ok'arin kwace wayar da ke hannun Binty ita kuma sai dariya ta ke yi ta k'i ba ta dama wanda hakan ya sa ba su ji k'a ran bud'e k'ofar da Julaibib d'in ya yi ba. "Ke!" Wa ni tsawa ya da ka masu wanda gaba d'ayan su ba su san lokacin da su ka hantsila daka kan kujeran da su ke kai ta baya ma ta re da mik'ewa a guje su ka yi sama. Fu'ad da ke gefe kuma da shi ake buga Ludo d'in sai sunnar da kai k'asa ya ke yi ta re da tuno azabar da ya gifta ta kuncinsa jiya da daddare. Wani uban harara Julaibib d'in ya maka masa ta re da yin kwafa ka na ya bi stairs don zuwa d'akin Anna. Ya na juya baya Fu'ad ya sulale ya bar d'akin don gudun tsautsayi. "Assalamu alaikum". Julaibib ya fad'a a k'ofar d'akin Anna ta re da kwankwasawa. "Shigo". Shi ne abunda Anna ta ce ba yan ta amsa sallamar kasancewar k'ofar ba a datse ta ke ba. Tura kai ya yi ta re da shiga d'akin, zama ya yi a kusa da ita, ita kuma ta juya kanta gefe. "Annata ina wuni?". Fad'in Julaibib. "Da ban wuni ba za ka ganni? D'azu da ba ka zo da safe ka gaida ni ba saboda ka na fushi da ni, mutuwa na yi?". "Anna I'm sorry". Julaibib ya fad'a a marairaice don ya san Anna ba za ta juri dogon fushi da shi ba. "Ka rage wannan zuciyar fa Ina fad'a maka. Don Allah ba bu wanda zai yarda ya ba ka y'ar shi ka illatata a banza". Fad'in Anna. "Anna ni kuma mai zai kai ni dukan mace, macen ma matata". Julaibib ya fad'a har da wani karya wuya. "To wa ya sani. Du bi dai irin dukan da ka yi wa d'an uwan ka da wannan yarinyar". Anna ta fad'a. Nan da nan ran shi ya b'aci saboda tuno masa da abunda k'anin na sa ya ke yi a cikin gidan ubansa. Magana ya soma yi cikin in'ina, "Annn..na yanzu abun.....da yyyaron nan yyyyy....yyyy... yake yyyyi". "Yi hak'uri ka yi shuru, Sam na san bai kyauta ba. Kuma maganar gaskiya k'anin ka Fu'ad ya na iya kacin bakin k'ok'arin sa ni ke hana sa". Anna ta yi saurin katse ta don yanzu sai ya fara bubbuga mata k'afa a k'asa ya na dukan kan shi. "Amma An....." "Yi hakuri ka bar maganar dan Allah". Anna ta k'ara katse yi. Mik'ewa ya yi ta re da fad'in, "Zan d'an.... D'an je wwwani waje". Ya sa ke fad'i cike da in'ina saboda har yanzu ya na cikin b'acin rai, kuma in har ya na cikin b'acin rai bai iya magana sai da in'ina. "Sai ka dawo Allah ya tsare". Anna ta fad'a. Ba ta re da ya ce komai ba ya juya ta re da fita daga d'akin. Bayansa ta bi da kallo ta re da fad'in, "Allah ya ye maka wannan bak'ar zuciya".

๐Ÿช‚๐Ÿช‚๐Ÿช‚ ...........Horn ya yi a k'ofar gate d'in, mai gadi ya wangale masa gate d'in shi kuma ya danna hancin motar ciki ta re da nai man waje ya yi parking. K'afarshi d'aya ya zaro waje ta re da d'aukar wayar shi ya shiga contact ya yi searching my p (my patient) ta re da dialing. Sabrin da ke zaune a gyefen Hamdan sanye da wani wando jean mai kyau ta re da rigar shi, ka na ta daura komono a kai kan ta ba d'an kwali as usual sai parking gashin da ta yi a gefe. "Duk kin wani rud'e kamar wacce sarkin maka zai kawo wa ziyara". Fad'in Hamdan ta re da hararar ta. "Are you joulos?" Sabrin ta fad'a ta re da murgud'a masa baki. "Why? Sai ka ce Beautyna ce wani zai kawo mata ziyara ta ke rawan jiki haka". Fad'in Hamdan ya na yamutsa baki. Nuna shi ta yi da yatsa za ta yi magana wayarta da ke hannunta ya soma ringing. Kallon screen d'in ta yi ta re da zaro idanuwa ta ce, "He's calling". Ta fad'a out of exited. Tab'e baki Hamdan ya yi ta re da fad'in, "Yauwa dai zan ga wannan Bibi d'in da ake kurantawa always". Ba ta re da ta ba shi amsa ba ta yi picking call d'in ta kara a kunne. Julaibib bai jira ta yi magana ya ce, "Ina waje". Ta re da katse kiran ya fito daga motar gaba d'aya. Da gudu Sabrin ta yi sama don shaidawa Mom d'in ta ya Bibi is outside. Sallah ta taras da mom d'in na ta ba yi, saukowa ta yi ta fita daga side d'in ta yi side d'in aunty Junaina kasancewar daddyn ta a can ya ke. Murd'a handle ta yi ta re da fad'awa d'akin, zaune su ke a kan dinning su na cin abincin har da su twince. "Daddy daddy daddy, ya zo ya na waje. Aunty Junaina ya ya Bibi ya zo ya na waje". Mik'ewa aunty Junaina ta yi cike da fara'a ta re da fad'in, "Ahhh muna da babban bak'o, maza kai shi parlourn bak'i ka da ya gaji da jira". Ta fad'i haka ne ta re da mai da dubanta izuwa ga y'an biyu ta ce, "Maza ku tashi ku je ku kai masa snacks da drink ka min ya isa d'akin". Daddy kuwa tu ni ya bar cin abincin ya kama hannun Sabrin d'in ta re da fita daga d'akin. Twins kuwa ba dan sun so ba su ka fita zuwa abunda maman na su ta sa ka su.

Hannun Alhaji Saifullahi cikin na Sabrin su ka isa in da Julaibib ya ke. Ba bu kunya Sabrin d'in ta nufi Julaibib ta re da rungume sa a gaban mahaifin ta. Shikuwa Julaibib kunya ce duk ta ka ma shi sai sunnar da kai ya ke yi. Hannu Alhaji Saifullahi ya mik'a masa su ka yi musabah ka na Julaibib d'in ya d'an rusuna ta re da fad'in, "Ina wuni daddy, mun sa me ku lafiya?". D'an rungumo shi Alhaji Saifullahi ya yi ta re da fad'in "Lafiya k'alau doctor, ya fama da patients?". "Alhamdulillah". Fad'in Julaibib. Hannun shi ya ka ma har parlourn bak'i, ana d'in ma k'ara gaisawa su ka yi, ita kuwa Sabrin d'in dad'i ya gama kasheta yau ga Yaya Bibin ta a cikin gidan su. Lallai hak'anta zai cimma ruwa. Fita daga d'akin Alhaji Saifullahi ya yi don ba su waje su gana. Zama ta yi kusa da shi ta re da fad'in, "Ya ya Bibi na". "My patient ya ki ke? Ina fatan yanzu dai babu wani matsala ko?". Duk da ta ji wani irin saboda sunan da ya kira ta da shi wanda da ma haka ya ke kiran ta da shi, amma sai ta yi murmushi ta re da fad'in, "Ka dawo lafiya?". "Alhamdulillah!" Ya fad'a a gajarce. Dai-dai lokacin Hamdan ya shigo da sallama a bakin sa. Gaba d'aya su ka amsa masa, murmushi akan fuskan Sabrin ta ce, "Yaya Bibi sannan shi ne best friend d'ina da na ke ba ka labari, kuma shi cousin d'i na ne, yaron k'anwar mama ne". Kallon shi Julaibib ya yi, shi kuma ya yi saurin fad'in, "Barka da zuwa ya Bibi? Ka dawo lafiya?". "Lafiya k'alau alhamdulillah. Ya karatu? A na dai yi ko? K'awarka ta ke min ta kammala secondary". "Eh ya ya Bibi ta kammala. Ni kuma ina 200level ina karanta civil engineering". Fad'in Hamdan. "Masha Allah, Allah ya taimaka". Fad'in Julaibib. "Besty, sai da safe na ga Yaya Bibi zan koma gida dare na yi". Fad'in Hamdan. "To bye sai da safe". Fad'in Sabrin. Ficewa Hamdan ya yi cikin zuciyar sa kuwa ya na jinjinawa Sabrin d'in don tabbas ta iya zab'e. Bai dad'e ba ya yi mata sallama zai koma gida. Aikuwa ta shiga buga k'afa ta na shagwaba akan bai dade ba kuma bai ci komai ba. Shi kuma ya ce mata dare ya yi, ina sha Allah idan ya sake dawowa zai ci. Sosai ta ji dad'i da ta ji zai sake dawowa, shikuma ya fad'a ne kawai don kauce mata don ya lura ta na da shegen rawan kai da surutu kamar uwar aku, shi kuma sam bai son hayaniya. Har mota ta raka shi ta na masa bye-bye. Sai da ta ga motar ta fice ka na ta juya ta koma cikin gida cike da farin ciki.

*The next day* ...........Tun asuba Fanan da Binty ke kuka da su ka ji ba da Fanan d'in za'a tafi ba. Anna ta yi lallashin har ta gaji ta yi banza da su. Shi kuwa Fu'ad tun 7:00am ya fita saboda kiran gaggawan da aka masa a court. "Ni wallahi Anna ba zan je ba in dai ba da Fanan za mu tafi ba". Fad'in Binty ta na shasshek'ar kuka. "Haba Binty, ni ban isa in fad'a maku magana ba kenan? To shikenan ku yi abunda kuka ga dama". Anna ta fad'a a tunanin ta za su saduda. Amma ga mamakin ta sai ta ga Fanan d'in ta hau sama ta re da jawo jakar kayanta dai-dai lokacin Julaibib ya shigo d'akin fuskan nan b'utu-b'utu sanye cikin farin coat, na cikin kuma ja da ya fito da kyawunsa. "Alhamdulillah! Julaibib yi min maganin wad'annan yaran. Tafiya Binty za ta yi wajan danginta, ka ga Baabarta nan ta fi k'arfin awa guda da zuwa amma Binty ta k'i ta bita wai ita dole sai da Fanan za ta tafi, ni kuma na fi son Binty ta je ta shiga y'an uwanta tun da ta kai kusan shekara takwas rabonta da gida, wasu ma duk ba su santa ba. Amma yarinyar nan ka gan ta ta k'i bin baabar tata". Fad'in Anna. Tun ka min Julaibib ya ce wani abu Fanan ta yar da jakar hannunta ta re da fashewa da kuka ta yi sama da gudu. Ita ma Bintyn kuka ta fashe da shi ta re da rungume Anna. Tuni har Anna ta ji hawaye sun cicciko mata a idanuwan ta. Kallon Kandala ta yi ta re da fad'in, "Kama ta ku wuce Kandala, rana na yi kuma za ku yi doguwar tafiya. Allah ya tsare hanya". Fad'in Anna ta re da janye jikinta Binty na dad'a kwakwume ta. "Anna su tafi da Fanan d'in". Fad'in Julaibib. Saurin kallon shi Kandala ta yi karaf su ka had'a idanuwa ta yi saurin janye na ta. Hanyar stairs d'in ya nufa, minti biyu sai ga shi rik'e da hannun Fanan d'in. "Su tafi tare Anna, ni ina ganin tafiyar ta su ta re zai fi". Julaibib ya sake fad'i. Dad'i ne ya mamaye zuciyar Fanan da Binty. "To kandala kin ji abunda wan su ya ce, ina fatan hakan ba matsala?". Yak'e ta yi wanda ya fi kuka ciwo ka na ta ce, "Aahh ba matsala wallahi, ai da Binty da Fanan duk d'aya ne a waje na". "To Allah ya kiyaye hanya". Fad'in Anna. "Ku kula da kan ku ban da yawo". Julaibib ya fad'a, amma idan ka kalle shi ba za ka tab'a yarda shi ya yi maganar ba. Kayan su su ka d'auka har wajan motar su kasancewar drivern gidan ne zai kai su. D'agawa Anna hannu su ka yi ta re da shiga motar driver ya ja. Kandala kuwa zufa ce ke ta wanke mata jikinta don ba haka ta so ba, kuma idan Hajiya Mansura ta ji hakan, za ta iya kwace kud'in da ta bata. Dad'in ta d'aya ma ta riga da ta gama tsara komai a can Saminakan.

............Tafiya su ka yi mik'ak'k'a duk sun gaji saboda ba su saba irin wannan doguwar tafiya ba, don ita Binty za ta iya cewa wannan shine karonta na biyu, lokacin da zo garin Abuja da kuma yau, Fanan d'in ma dai haka ne, sau d'aya ta tab'a zuwa Gombe sai kuma yau, gomben ma ba za ta iya cewa ga yanayin nisan ba don tun ta na yarinya ne. Sai gab da magriba su ka shigo k'auyan Saminaka. Yara sai bin motar su ke yi da gudu. Hatta manyan ma bin motar su ke yi da idanuwa. Kandala ce ta soma fitowa, aikuwa wad'and'a su ka san ta su ka yi mata caaaa su na mata oyoyo. Matan gida kuwa duk an firfito waje, wasu ma daga su sai d'aurin kirji. Wasu kuma yara ne d'auke a hannunsu su na shan nono amma haka su ka fito waje su na lek'e.

*KO YA ZA'A KWASHE A K'AUYAN SAMINAKA?*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull