Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 26

Ba ni da gata - Chapter 26

Ba ni da gata Chapter 26: Ba ni da gata Chapter 26. Bud'e mata gidan gaba ya yi, sai da ta shiga ya rufe ka na ya zagaya ya shiga driver seat ta re da rufe…

3,305 words

Bud'e mata gidan gaba ya yi, sai da ta shiga ya rufe ka na ya zagaya ya shiga driver seat ta re da rufe motar. Ita kuwa Binty gaba d'aya jikinta ne ya yi sanyi k'alau da maganar da Sabrin d'in ta fad'a mata. Ta d'auka Sabrin d'in za ta canza a gaba, amma sai ta ga kamar abun na ta k'aruwa ya yi. "Ba zan yi wa motar nan key ba idan har ba ki fad'a min abunda ke damun ki ba, wallahi ko da hakan na nufin za mu kai sha biyun dare a nan wajan". Fad'in Yousouf da ya zuba mata fararan idanuwansa. Saurin kallon sa ta yi ta re da k'ak'alo murmushi ta ce, "Ba fa abunda ke damu na, kawai schoolmate d'ina ce da na ga ni ta ba ni mamaki". Fad'in Binty. "Wani irin mamaki kenan ta ba ki?". Ya sake je ho mata tambaya ta re da tsare ta da idanu. "Ta na da isa da tak'ama ne tun muna yara, sai na ga abun bai ragu ba ko da mu ka girma, shi ne abun ke ba ni mamaki". Murmushi Yousouf ya yi ta re da fad'in, "To hakan ya dai na damun ki, ko wani mutun da ki ka gani a duniya da irin yanayin sa da kuma d'abi'ar sa. Ki saki jikin ki, ko mu kwana a nan". Zaro idanuwa ta yi ta re da fad'in, "Wallahi na saki, mu tafi". Ta fad'i hakane ta re sa sakin fuskanta. Dariya ya yi ta re sa yi wa motar key ya yi reverse ta re da fita daga wajan. Ita ta yi masa kwantance har su ka iso wajan. Sai da ya k'ara rik'e ta kusan mintuna biyar ya na k'ara zayyane mata yadda ya ke jin ta a zuciyar sa da kuma jaddada mata alk'awarin su Ka na ya bar ta ta wuce. Ta baya ta biyo kamar yadda ta fita ta baya. Ko da ta shiga shagon, tuni har an kammalawa Fanan lalle har ta wanke. Kan ta ake busar mata. Fanan d'in na ganinta ta saki ajiyar zuciya ta re da fad'in, "Ina nan ina zullumi wallahi. Gaskiya kin kyauta da ba ki makara ba". Ta fad'i hakane ta re da karb'an ribom a hannun mai saloon d'in ta kama gashin da kan ta, ka na ta mik'e ta kakkab'e jikinta ta re da ba mai saloon d'in kud'inta har da na lalle ka na su ka fito. Driver na zaune a mota ya na sauraran labarai a wayar shi, ya na ganin su ya gyara zama ta re da yi wa mota key. Su na shiga ya d'aga su ka nausa titi. K'arfe shidda saura minti goma su ka shigo gida. Da ya Fu'ad su ka ci karo a parlour ya na cin pop corn ya na kuma kallon wani Indian series mai suna *JODHA AKBAR* a tashar Bollywood, sam shi ba ma fahimta ya ke yi ba, kawai ya canza tasha ne ya ga su na yi kawai ya bar shi. "Kai, ina ku ka je ku ka yi yamma haka?". Fad'in ya Fu'ad ya na kallon su. K'arasawa wajan sa su ka yi ta re da zama a gyefansa. Binty na gefen dama, Fanan kuma na hagu ta re sa saka hannu su ka soma cin pop corn d'in. "Ba ma sai kun ban amsa ba, hannun ku kawai ya shaida min inda ku ka je. Masha Allah lalle ya yi kyau". Fad'in Ya Fu'ad ya na kallon zanen lallan hannun Binty da ya yi bala'in yi mata kyau kamar dan ita aka k'irk'ire shi. "Anna ta ce in ce maku idan kun dawo ku d'aura girki. Kuma ku nutsu don yaya Bibi zai ci abincin kuma ta re za su zo da abokinsa. Don haka kallo ba na ku ba ne, aje a sauya kaya a shiga kitchen". Fad'in ya Fu'ad. Ai har rige-rigen wuntsulowa su ka yi ta re da nufar sama don canza kaya su shiga kitchen d'in. Barr Fu'ad ba masu dariya.

*WAYE YOUSOUF MUHAMMAD AHLAM* ..........Cikakken bakatsine ne haifaffan garin Abuja. Mahaifin ya tara dukiya sosai do min shi ya ke da *SUNCITY ESTATE*. Mahaifin sa mace d'aya gare shi mai suna Saratu. Y'ay'an su takwas, hud'u maza hud'u mata. Sai dai estate d'in damk'am ya ke da zuri'arsa. Muhammad Ahlam mutum ne mai k'aunar zumuni, wannan dalilin ne ya sa gaba estate d'in shi, zuri'ar sa ne. Ana kiran sunan estates d'in da gidan kyawawa kasancewar mazan su da matan su kyawawa ne. Yousouf shi ne d'a na biyu a cikin y'ay'an Dr Muhammad wanda ya kasance a da shi d'in likitan Tsohon sarkin Adamawa ne wanda ya mutu d'an sa ya hau, kasancewar sa mai amana ya sa ya zama kamar family a masarautar Adamawa kuma har gobe bai dai na ziyarta su ba duk da ya yi retired. Yousouf ya yi karatunsa a k'asar *US*, engineer na'ura ne. Kamar yadda cikakkiya mace ta kware a sarrafa tukunya, haka Yousouf ya kware wajan sarrafa computer ko da kuwa idanuwansa a rufe ya ke. Kullum cikin busy ya ke, wannan dalilin ne ya sa ko kusa mata ba sa gabansa. Computers d'in sa su ne matansa. Mace ba ta gaban sa sam, kuma hakan ba Wai ya na nufin bai da lafiya ba ne. K'alau ya ke. Abokansa sun yi tsiyar har sun gaji sun kyalesa. Yousouf na da matuk'ar kishin abunda ya ke so, hakan na d'aya daga cikin dalilan da ya sa ye gujewa mata saboda ya na da matuk'ar saka abu a zuciyarsa. Idan har ya na son abu to fa ya na san shi har abada kuma bai son a kusanci abun nan. Yousouf na da wani ciwo tun ya na yaro, babu k'asar da ba'a je ba domin nai ma masa magani ba, amma har yanzu cutar ba ta warke ba, sai da kuma ya na dad'ewa bai ta shi ba. Wata cuta ce da idan ta taso masa, zai iya wata biyu zuwa uku a kwance, ba ci ba sha, kuma sai dai a ba shi abinci a drip. Sannan kuma bai motsi sai dai ya yi ta bin mutane da idanuwa. Hankalin ahalin Dr Muhammad ba k'aramin tashi ya ke yi ba duk san da ciwon Yousouf ya ta shi. Kwatsam kuma sai ga shi ya had'u da sahibul ruhinsa da ya ji ya na matuk'ar k'aunarta kuma zai iya ko mai saboda ita. Har cikin ran shi ya ke jin ta. _wannan kenan._

*_____________________* Cikin abunda bai fi awa guda ba, har sun kammala girki. Lafiyayyan tuwon shinkafa su ka girka da miyan wake da yaji bushasshen kifi da nama, sannan kuma su ka sake yin miyan ayoyo da kuma stew a gefe. Sai da su ka jera komai a dinning ka na su ka haura sama don yin wanka. 7miss calls Binty ta ga ni a wayanta duk na Yousouf. Ba ta bi bayan call d'in ba sai da ta yi wanka ta re da d'aura alwala don an kusa kira isha'i. Su na girki aka yi magriba su ka sake su ka je su ka yi. Mai kawai Binty ta murzawa jikinta ta zura doguwar riga mai hula ta re da saka dogon hijjab don har an riga da an yi kiran sallar isha'i. Bayan ta idar da sallar ne ta bi kiran Yousouf. Katse kiran ya yi ta re da bin bayan kiran na ta. Ringing biyu ta d'aga ta re da karawa a kunnanta, "Amincin Allah ya tabbata a gare ki mai sona". Fad'in Yousouf. "Ameen ta re da kai *Reality*". Binty ta fad'i ta re da kwanciya flat a kan gado. "Ya ki ka ko ma gida?". "Alhamdulillah! Kai fa?". Fad'in Binty. "Cike da tunanin ni". Anna ce ta turo k'ofar ta shigo ta re da fad'in, "Da wa ki ke waya Binty?".......

*KU YI HAK'URI DA WANNAN MU HAD'E GOBE* 🌹 *51-52*🌹 ............Cikin saurin ta yanke wayar ta re da mik'ewa zaune ta ce, "Annah da school mate d'ina ce, mu na magana ne akan admission da zai fito". "To maza ki sauko ki zo ku ci abinci, ke kad'ai ake jira a k'asa". Fad'in Annah. "To Anna ga ni nan". Binty ta fad'a ta re da saukowa daga kan gadon ta bi bayan Anna da ta fita. Gaba d'ayan su ne zaune akan dinning d'in. Yanzu ma Binty a kan kujeran da ta zauna d'azu ta zauna, ta na fuskantar ya Bibi. Ganin ba bu abokin ya Bibi da ya Fu'ad ya ce ta re za su zo, kallon ya Fu'ad d'in ta yi ta re da masa nu ni da hannu alamar ina abokin na shi. D'aga mata kafad'a ya yi alamar oho ta re da jan zip a bakinsa ya kuma nu na mata ya Bibin alamar ta yi shuru. Sai da su ka kammala cin abincin ka na Ya Bibi ya kalli Anna ta re da fad'in, "Anna ba ki ganin ya kamata Zaid ya dawo kusa damu? Kin san fa rik'on d'a sai iyayansa". Saurin d'agowa Binty ta yi ta re da zuba masa idanuwa saboda kalmar rik'on d'a sai iyayansa da ya furta. Harara Anna ta ma ka masa ta re da fad'in, "Ya fad'a maka ana kankaran naman jikinsa ne a can? To ba zai dawo ba d'in. Idan kuma kai ne ubansa, sai ka je ka d'auko sa a wajan mai martaba. Don Zaid ya bar hannun Dattijo ya na wajan uwar gidan mai martaba". Fad'in Anna. Kasancewar Zaid mai bi ma Fu'ad tun wajan yaye mahaifiyar Anna ta amshe shi, ita kuma uwar gidan mai martaba ta yi mata fin k'arfi ita ma ta amshe shi. Da Julaibib d'in ma su ka so amshewa. "Allah ya huci zuciyar ki Anna, dama kawai yadda na ga duk kan mu zuri'ar ki muna cin abinci a waje d'aya, shiyasa shi ma na yi masa kwad'ayin haka". Fad'in Julaibib ta re da mik'ewa. "Kai ma ka kusa dai na cin abincin ta re da mu a nan kuma nan kusa don kwanaki zan yanke maka ka fiddo matar aure". Fad'in Anna ta re da harararsa. "Anna a gaba yara. Dan Allah ki dai na min maganar aure a gaban su kar su raina ni". "Au na manta fa, kai ka yankewa k'asa cibi. (Kwafa) kar ka fiddo macan aure sai na baka mamaki nan kusa". Anna ta sake fad'i. "Ku bar nan ko in karya k'afafuwan ku". Julaibib ya fad'a ya na zazzarowa su Binty idanuwan sa. Aikuwa da sauri su ka bar wajan, Binty kuwa saura kad'an ta zame, ya Fu'ad ya yi sauri kai hannu zai rik'o ta Allah ya ba ta sa'a ta dafa bango. Anna har ta mik'e. Julaibib d'in kuwa wani arnen harara ya jefi Fu'ad da shi ka na ya juya ta re da nufar k'ofa don zuwa wajan mahaifin sa. Girgiza kai Anna ta yi ta re da kallon Fu'ad ta ce, "Yauwa Fu'ad, gobe idan Allah ya kai mu, za ka d'auki Binty da Fanan ka kai su supermarket ka yi masu siyayya sosai, jibi za ta je k'auyansu ganin gida". Fad'in Anna. Gaban ya Fu'ad d'in ne ya buga dam dam ta re da kallon Anna da sauri ya ce, "Anna kuma kin yarda su tafi d'in?". "Ka ji wani maganar banza da wofi. Na ce maka wajan danginta za ta je kuma sai ka ce na yarda ni da aka min kara da kawaici tsawon shekaru ba ta je ba run da ta zo nan. Amma ba ka da hankalin Fu'ad". Fad'in Anna. "Anna wallahi ni kawai matar ce ba ta kwanta min a rai ba". Fad'in Fu'ad. Harara Anna ta ma ka masa ta re da fad'in, "Ka dai ji abunda na fad'a maka ko? Karfe sha d'aya na ke so ku tafi". "To Anna Allah ya kai mu". Fad'in Fu'ad jiki a sanyaye. Harara ta k'ara maka mashi ka min ta yi hanyar stairs.

Julaibib na fita hanyar part d'in Hajiya Huriya ya nufa domin ganawa da mahaifin sa. Ya gitta side d'in Suhail kad'an ya yi saurin dawowa baya saboda warin wiwin da ya ji ta k'ofofin hancinsa da kuma hayak'in da ya ke gani ya na fita duk da d'akin a kulle ya ke. Hanyar k'ofar ya yi ran shi a matuk'ar b'ace ta re da dukan k'ofar da k'arfi kamar zai karya. "Wani d'an hegiyar ne ya ke dukan k'ofata haka iyeeee". Fad'in Suhail cike da maye. K'ara dukan k'ofar Julaibib ya yi da mugun k'arfi. A zafafe Suhail ya taso ya na rangaji daga shi sai boxer, tattoo d'in nan ya fito rad'o rad'o a jikinsa sai wani uban chain a wuyan shi har ciki, karuwarsa kuma ta na kwance a three sitter ta na zuk'an sigari da ga ita sai wani arnan rigar baccin da gaba d'aya jikinta ana ganinsa a waje. Gadan gadan k'ofar ya nufo ta re da bud'e shi kamar zai kifa. Wani irin kallo Julaibib d'in ya ke bin sa da shi har jikinsa ya so ma rawa don hatta naman kumatun shi rawa su ke yi. Tuni har idanuwansa sun kad'a. Shi kuwa Suhail duk da ya na cikin maye hakan bai hana shi wani iri zabura ba ta re da komawa baya, don ko a mafarki bai tab'a tunanin Julaibib ba ne. Don shi bai da labarin ma ya dawo k'asar. "Yyyyyyaya Bibi". Fad'in Suhail bakinsa na rawa kamar zai fad'o. Wani wawan mari Ya Bibi ya d'auke sa da shi sai da ya kifa k'asa wanwar. "Baby whats going on". Karuwar Suhail ta fad'a ta re da tasowa daga in da ta ke ta na rangaji. Wani irin tuk'uk'in bak'in ciki ne ya k'ara mamaye zuciyar Julaibib har bai san san da ya saka k'afa ya take gaban Suhail d'in ba da k'arfi. Wani irin ihu Suhail d'in ya saki ta re saka hannu biyu ya rik'e gabansa ya na tumbling. Ita kuwa karuwar jikinta ne ya soma b'ari, saurin d'aukar hijjab d'inta har k'asa ta yi ta saka ta na k'ok'arin fita daga d'akin. Wani irin fincikota ya yi ta re da yasar da ita a tsakar d'akin sai da ta kwallara k'ara saboda cikinta da ya bugu da k'asa. K'arasawa wajan kayan kallo Julaibib ya yi ta re da fizgo wata waya ya shiga lafka masu ta ko ina a jikinsu dai dai lokacin Ya Fu'ad ya fad'o d'akin sakamakon ihun Suhail da kuma na mace da ya ji. Fu'ad jikinsa b'ari ya soma yi saboda irin dukan da Julaibib d'in ya ke ma su. Ran shi ya yi b'acin da zai iya aikata komai. Da gudu Fu'ad d'in ya juya domin kiran Anna. Ko kafin Anna ta shigo, Suhail da karuwansa sun yi suma uku su na farfad'owa. "Julaibib ka bari na ce!". Amma ta fad'a a tsawace. Amma inah Julaibib bai ma san ta na yi ba sai dad'a dagewa ya ke yi ya na bugun su. "Julaibib ba da kai na ke magana ba". Anna ta sake fad'i amma duk da hakan bai bari ba. "Salissssss!". Anna ta kira ainahin sunan sa a tsawace sai da d'akin ya d'auka. Sai a lokacin ya yar da bulalan da har ya tsintsinke saboda irin dukan da Julaibib ya yi masu. Suhail numfashi sama sama ya ke yi, ya yin da karuwar ta sa ko motsi ba ta yi. Fu'ad bai ankara ba ya ji an d'auke sa da maruka har kala uku masu gigitarwa ka na ya nuna sa da yatsa, "Kkkkkana kalll'o yii yah ron nan ya na is...kkan cin nan am..ma baza kullll...a da shi ba". Fad'in Julaibib cike da in'i na saboda b'acin ran da ya ke ciki. Kauuuuuuuuuu! Anna ta d'auke shi da mari hagu da dama ta re da fad'in, "Ban isa ba ko? Ni ban isa in fad'a maka ka bari ka yi ba ko? Yanzu idan ka yi kisan kai fa?". Julaibib na son yin magana amma ya kasa saboda in inar da ta ci k'arfin sa. Hargitsa gashin kansa ya so ma yi ta re da soma buga k'afarshi a k'asa. Hankalin Anna ne ya yi mugun tashi don ta san halin d'an na ta. "Wuce side d'in nan right now". Anna ta fad'a wa Fu'ad. Cikin sauri Fu'ad d'in ya fita saboda ya san wanene wan na shi. Ita kuwa Anna hannun Julaibib d'in ta kama ta re da nufar side d'in sa. Sai da ta aje sa akan kujera ka na ta d'auko ruwa mai sanyi a fridge ta tsiyaya masa a cup ta re da mik'a masa. Ba musu ya karb'a ya shanye. K'ara masa ta kuma yi, nan ma ya kuma shanye wa. "Ta shi ka shiga ba yi ka je ka yi alwala ka yi sallah ka kwanta". Anna ta fad'a. Ba musu ya yi wajan bayi, ita kuma ajiyar zuciya ta saki ta re da fita ta koma part d'in Suhail d'in. Yadda ta bar su, haka ta sa me su. Ruwa ta d'auko a fridge ta re da bud'ewa ta d'iba ta shafa a fuskan yarinyar. Wawiyar ajiyar zuciya ta sauke ta re da rushewa da kuka. "Ta shi ki wuce gidan ku tun kafin ki rasa k'afar ki d'aya a cikin gidan nan". Fad'in Anna. Cikin sauri yarinyar ta mik'e ta re da d'aukar takalminta mai tsini a hannu. Har ta kai k'ofa Anna ta ce, "Ki ji tsoran Allah yarinya. Ka da ki manta ke macece, zaman gidan iyayanki ko gidan miji shi ya kamace ki ba bin gidajan samari ba su na yaudarar ki da kud'i da kayan shaye-shaye ba. Ki ko ma gaban iyayan ki kk ji tsoran Allah". "Nagode". Shine abubda yarinyar ta fad'a ta re da saurin barin wajan gabanta ba fad'uwa don ba ta tab'a zaton za ta farka ba ta ji ta a kabari ba. kallon Suhail da ke ta murd'e murd'e hannunsa rik'e da al'aurarsa ta yi ta re da fad'in, "Ka d'an ka ga ni in dai ba za ka kiyayi duniya ka kuma natsu ba". Ta na gama fad'in haka ta yi waje.

*WASHA GARI* 🌙🌙🌙

Fuska kumbure Fu'ad ya tashi saboda marin da ya sha a wajan babban yaya. Shikuwa Julaibib a masallaci wajan sallar asubha su ka had'u da daddy su ka gaisa, bai tambayesa dalilin rashin zuwansa ba, kasancewar ya na ganin duk abunda ya faru daga CCTV CAMERA da ke d'akinsa. Duk abunda Suhail d'in ya ke yi, Alhaji Usman na sane, wani abu ya ke jira akan sa saboda mummunar shiri da yake masa don har safarar cocaine d'in da ya ke yi ya na sane da shi. Julaibib daga masallaci ya wuce asibiti ko saboda jiransa da ake yi kuma ya yi wa Sabrin alk'awarin zai za wajanta yau da daddare idan ya gama abunda ya ke yi da wuri.

"Fu'ad, mai ya samu fuskan ka?" Fad'in Anna wanda hakan ya sa daga Binty har Fanan da ke breakfast su ka juya su na kallon shi. Binty har sai da ta b'arar da shayin da ke gabanta wajan mik'ewa. Sai da ta isa gaban Fu'ad ka na ta ce, "Yaya na mai ya samu fuskan ka?". Ta fad'i hakane siraran hawaye na zubowa daga idanuwan ta. "No kar ki kuka beauty, kwanciya na yi a kan tiles kuma jikina bai san sanyi shiyasa wajan ya kumbura, kuma zuwa anjima ma zai sace". Fad'in Fu'ad ya na sakin murmushi. "Dan Allah Yaya kar ka k'ara kwanciya a k'asa". Fad'in Binty a marairaice. "In sha Allah". Fad'in Fu'ad ta re da nufar dinning d'in. Sai da ya je dai-dai kunnan Anna ka na ya ce, "Anna ke ki ka jawo min jin hannu maza a fuskata, aradu har na yi bacci ina jin zugi. Da kin bar ni na d'au mataki da ban samu kafta a fuska ba". Fad'in Fu'ad ta re da jan kujera ya zauna.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull