Ba ni da gata - Chapter 25
Ba ni da gata Chapter 25: Ba ni da gata Chapter 25. Tun da su ke saukowa Anna ta zubawa Binty idanuwa ta re da k'arewa hannun na ta kallo ta na mamakin…
3,302 words
Tun da su ke saukowa Anna ta zubawa Binty idanuwa ta re da k'arewa hannun na ta kallo ta na mamakin yadda lokaci guda hannun ya sab'e. Barrister Fu'ad ma kallon ta ya ke yi ya na sakar mata murmushi. Shi kuwa gogon da k'amshin turaransa ya game d'akin ko kallon inda su ke bai yi ba. Sakwaran sa ya ke ci kicin natsuwa. "Zo ki zauna a nan daughter". Anna ta nunawa Binty kujeran da ke kusa da ita, kuma shi ya ke fuskantar inda ya Bibi ya ke zaune. "Queen ya hannun?". Fad'in Barrister Fu'ad ya na kallon Binty. "Da sauk'i yaya. Na ma dai na jin ciwon kamar ban fad'i ba. Ka gani". Binty ta k'arisa maganar ta re da jujjuya hannun har da lankwasa shi ta na dariya. "Ah Alhamdulillah. Har na ji dad'i da na gan ki haka". Wani wawan kallo Ya Bibi ya jefi Barr Fu'ad da shi ta re da fad'in, "Idan surutun za ku yi, kwashesu ku yi can part d'in ka da su. Ka fi kowa sanin ban san yawan surutu a kai na, beside abinci mu ke yi". Fad'in Julaibib fuska a d'aure. "I'm sorry big bro". Fad'in Fu'ad ta re da kashewa k'annan na sa idanuwa. Binty kuwa kallon Julaibib d'in ta yi ta re da turo baki. Karaf su ka had'a idanuwa ta yi saurin saka tafukan hannunta ta rufe bakin ta na zare idanuwa. Shikuwa kallo d'aya ya mata ta re da jan tsaki k'asa-k'asa ya cigaba da cin abuncin sa. Duk d'agowar Binty sai ta kalle shi, shi ma kuma duk d'agowarta ya na kallonta ta gefen idanunsa wanda ita ba ta sani ba. Jan kujera baya ya yi ta re da d'aukar tissues ya goge bakinsa ka na ya kalli Anna ta re da fad'in, "Zan shiga cikin gida na gaida mutanan gida, sannan zan d'an kwanta in huta don gobe da asubha zan fita. Asibiti biyar su ke nai ma na. Wanda su kad'ai na yanke zan je a goben, amma idan zan biyewa mutanan da suke kira na, bazan samu lokaci na ko minti biyar ba idan ba sallah ba". "Gaskiya kam, gwara ka je ka huta. Kuma daddyn ku ma nasan ya na dawowa zai nai me ka". Fad'in Anna. "A nan side d'in ya ke ne?". Fad'in Julaibib. "A'a ya na part d'in Huriya ne". Anna ta fad'a. Binty kuwa zuba masa idanuwa ta yi ta na mamakin yadda ya ke magana kamar wanda aka sa shi dole sai ya yi. "Bar kallo na ko in zo in kwakwule idanuwanki". Fad'in Julaibib ta re da zazzaro mata idanuwa. Binty ta yi saurin Kai da idanuwanta ta re da tura baki tana guna guni. Juyawa ya yi ta re da ficewa daga d'akin. "Na fad'a ma ku sai kun kiyaye shi ai". Fad'in Anna ta re da mik'ewa ita ma ta bar wajan. Barrister Fu'ad ya kalli su Binty ta re da fad'in, "Ya Bibi ba mugu ba ne, wanda ya zauna da shi sosai zan gane hakan. Kawai shi bai son surutu da hayaniya ne. Idan ya na waje ku rik'a k'ok'arin gimtsewa. Yanzu zan je court, mai zan taho maku da shi idan zan dawo. "Vanilla ice cream". Fad'in Binty. "Ni ba na son ice cream, pizza na ke so sai strawberry". Fad'in Fanan. "To shikenan. Duk zan sayo maku. Sai na dawo". Fad'in Fu'ad ta re da barin wajan shima. "Ba ri na je na lallab'o Anna mu samu damar fita". Fad'in Fanan. "Yauwa sister dan Allah yi sauri. Kar ki fito sai ta amince". Binty ta fad'a.
Bayan minti biyar Fanan ta sauko fuskan nan b'utu-b'utu kamar za ta fashe da kuka. Tun da Binty ta ga hakan jikinta ya yi sanyi ta san Anna ba ta amince ba kenan. "I'm sorry sister, Anna ta ce muje ka da mu dad'e". Wani tsalle Binty ta yi ta re da rungume Fanan d'in duk su ka sa dariya.
Cikin abunda bai fi minti goma ba, su ka kammala shirin su su ka fito, kai tsaye wajan motarsu suka nufa, dama tunda driver ya hango su ya san fita ce, tuni ya riga su isa wajan motar. Su na shiga ya ja motar su ka fice. Supermarket ya fara kai su, ka na ya kai su wajan yin lalle. Kasancewar Fanan cewa Anna ta yi za su lalle kuma za su siyo pad na su ya k'are kuna Fanan d'in na gab da ganin al'adarta. Dalilin hakane ma yasa Anna ta amince su ka fita. Binty aka so ma yai wa lalle bak'i da ja a hannunta. Ba k'aramin kyau ya mata ba. Sai wanke mata kai da akayi ta re da busarwa da handryer. A na gama mata kamin a fara yi wa Fanan su ka d'auki excuse su ka fita. Ta baya su ka zaga saboda ka da driver ya gan su. "Binty Dan Allah ki tabbata biyar ta miki a nan wajan mu koma gida. Dan Allah ka da ki dad'e". Fad'in Fanan. "In sha Allah ba zan dad'e ba Fanan". Fad'in Binty ta re da saurin yin a gaba. Ta na fita ta samu taxi ta re da tare shi ta ce masa drop ya kai ta wonderland. Tun a cikin taxi d'in ta yi wa yousouf text a kan ta na hanya su had'u a can. Replay ya mata da shi ya na can ma tun tuni. Ba su wani jima sosai na su ka isa wajan. Kud'i ta ciro ta mik'a masa ta re da shiga wajan kasancewar ya Fu'ad ya na yawan kawo su wajan. Wayarta ta fido za ta kira shi. K'amshin wani turare mai dad'i ya daki hamcinta. A hankali ya juya bayanta idanuwan su suka had'u da na juna. Luuu ta yi da idanunta ta re da bud'e su a kan sa. Bak'aramin kyau ya mata ba. Sanye ya ke cikin wani d'anyan shadda kalar silver-silver, ash-ash. Gajeran riga ce mai gajeran hannu, sai hulla da ya turo shi gaban kan shi kad'an, kwantancan gashin kan shi kwance a k'eyarsa. Sai bak'in glasses da ya manna a fuskan shi hannun shi d'aya cikin aljihun wandonsa. Murmushi ya sakar mata ta re da zare glasses d'in da ke fuskan shi ta re da nuna mata hanya alamar su yi gaba. Binty ta kasa magana sai gaba da ta yi ya na bi ye da ita a baya. "Yauwa, to zauna ana gimbiya". Muryan shi mai dad'i ya daki dodon kunnanta. Sai da ta lumshe idanuwa ka min ta zauna a inda ya nuna mata, shi kuma ya zauna ya na fuskantar ta. Ka sa cigaba da had'a idanu da shi ta yi ta re sa sakin murmushi ta kalli k'asa ta re da furta, "Ina wuni". Cikin wani irin salo da bata san ma ta iya shi ba. Bai iya amsawa ba, sai kafe ta da idanuwa da yi for 1minute ka na a hankali ya furta, "Binty ina sonki, ina k'aunar ki har cikin jini na. Dan Allah ki so ni ko da kwatan yadda na ke son ki ne. Tun ranar da na fara ganin ki a shop rite, ki ka tafi da natsuwata. Y'an uwa da abokai na, sun kasa gane kai na. Wannan shine karo na na farko da na fad'a soyayya. Shin Binty za ki iya ba ni so?". Wani dad'i Binty ta ke ji tun daga can k'asan ranta na ta so mata. A hankali ta d'ago ta kalli idanuwan shi. Saurin janyewa ta yi saboda wani kunya da ya kama ta. Dariya ta ke yi a hankali ta re da murza d'an yatsan ta. "Binty dan Allah ka da ki ji kunya ta. Ba zan takura ki ba idan har akwai wanda ki ke so, amma na san dai ba zan kai labari ba idan har ki ka ce ba ki so na Binty. Dan Allah ka da ki ji kunya. Ki fad'a min ki na so na". Yousouf ya sake fad'i ya na kallonta. "Kullum tambayar kenan ko a message. Da ban son ka ba zan baka lokaci na ba har mu rik'a musayan kalamai. Ko a haka kawai zai tabbatar maka da ka karb'u a zuciya ta". Fad'in Binty kan ta a k'asa. Wani lumshe idanuwa Yousouf ya yi ta re da bud'e su ya na kallon cikin idanun Binty cike da shauk'i. "Ki min alk'awari ki na ta re da ni Binty duk runtsi. Ni ma kuka bazan tab'a guje miki ba a duk halin da kika ciki. Mu yi wa juna alk'awarin kasancewa da juna sai mutuwa za ta raba mu". Fad'in Yousouf. Ba ta re da wani dogon tunani ba Binty ta ce, "Yousouf na yi alka'warin kasancewa da kai a kowani irin hali sai mutuwa ce za ta raba mu. Ina k'aunar ka Yousouf". Binty ta fad'a babu d'ar ta na kallon cikin idanun Yousouf. Lumshe idanuwa Yousouf ya yi wanda ya kasance d'abi'ar sa ka na ya sa ka hannu cikin aljihun wandonsa ya fiddo wani d'an akwati ya aje akan table ta re da fad'in "Bud'e Binty, wannan shine zai zama shaidan alk'awarin mu". Bud'ewa Binty ta yi, zoben diamond ne mai kyau da shek'i har guda biyu. D'aukar babban ya yi ta re da mik'awa Binty ka na ya mata alama da idanu akan ta sa ka masa zoben a yatsan sa. Karb'a ta yi, ta re da kai hannu za ta sa ka masa ya yi saurin janye hannu ta re da girgiza kai ya ce, "Ki mai-maita abunda ki ka ce kamin ki sa ka min". "Na yi alk'awarin kasancewa da kai a ko wani irin hali sai mutuwa ce za ta raba mu". Ta na gama fad'in haka ta zura masa zoben a hannunsa. Sai dai a lokacin da hannunsu ya had'u sai taji wannan tururin ya daki hannunta har ba ta san lokacin da ta yi saurin janye hannunta ba. "Lafiya?". Yousouf ya tambaya saboda ganin reaction d'in ta. Murmushi ta sakar masa ta re da fad'in, "Ba ko mai". Ta fad'i hakane ta na d'an murza hannunta da har ya soma yi mata zafi. "Ba ni d'an yatsar ki". Fad'in Yousouf. Mik'awa d'an yatsar hannun hagunta ta yi, shi kuma ya fiddo zoben a cikin box d'in ta re da fad'in "Na yi alk'awarin kasancewa da kai har k'arshan numfashi na, sannna zan kula da ke fiye da kai na, ba zan bari abun cutarwa ya zo kusa da ke ba, zan kare ki da iya k'arfin da Allah ya ba ni, zan nu na miki so zan kuma kare ki daga ko wani irin cuta in sha Allah". Ya na gama fad'in haka ya zura mata zoben a yatsarta. Hannun shi da ya tab'a fatar yatsarta, ji ta yi kamar wajan ya sale saboda rad'ad'in da ta ji. Amma haka ta daure har ya gama saka mata. "Allah ne shaidan mu akan haka". A ta re su ka had'a baki wajan fad'in haka. "Bari na je na kawo miki drinks da snack". Ba ta re da ya ji ra'ayin ta ba ya yi saurin barin wajan. A hanyar shi ta dawo wa su ka had'u da abokinsa Ramadan shi ma yazo da budurwansa. "Kai wa na ke gani kamar Yousouf?". Fad'in Ramadan. "Ni ne wallahi". Fad'in Yousouf ya na shafa k'eyarsa. "Shegen gora, mai ka ke yi a nan?". Ya sa ke tambayan sa. Ba ta re sa Yousouf ya ba shi amsa ba ya kalli in da Binty ta ke a zaune ta na waya. Zaro idanuwa Ramadan ya yi ta re da fad'in, "Iyyeee, yau ina su Fauwaz in fad'a masu ka shigo hannu. Da ma mun fad'a maka ai". Fad'in Ramadan. "Na bar baby ita kad'ai. Kar ta ji ba dad'i kai ma yi wajan ta ka babyn". Fad'in Yousouf. Dariya Ramadan ya yi ta re da fad'in, "Naga wannan salon". Ya fad'i hakane ta re da mik'a masa hannu su ka tafa. K'arasowa ya yi wajan Binty ta re da zama ya aje mata drinks d'in da ya kawo mata da straw a jiki, shi ma ya ajiye na shi a gaban shi ya na kallon ta. "Ya dai, kallon fa?". Fad'in Binty ta re da d'age gira. "Da wa ki ke waya?". Fad'in Yousouf ta re da tsare ta da idanu. Farrr ta yi da idanu ta re da fad'in, "Saurayi na ne ya kira ni". Tsare ta da idanuwa ya yi ta re da fad'in, "Aiko zan kashe shi". Zaro idanuwa ta yi ta re da fad'in, "Wayyo! Ka dai na maganar kisa. Ni ba da namiji na ke waya ba. Fanan ce ta kira ni akan in yi sauri in dawo. Kasan gidan mu ba'a ba ri mu na fita. Yauwa dabara mu ka yi wa Anna". "Wallahi da gaske na ke. A kan ki zan iya ko mai. Zan iya kashe mutum ko aljani idan ya yi k'ok'arin zuwa kusa da ke Binty. Ban tab'a son wata mace ba sai a kan ki, kuma ban tab'a jin ina jin matsanaicin kishi mace ba sai a kan ki. Dan Allah kar ki yarda wani namiji ya yi kusa da ke don wallahi zuciyata za ta buga Binty. Yanzu mu ka had'u da aboki na tun na yarinta, ko shi ban yadda ya zo in da ki ke ba har ya yi dogon magana da ke ya ji dad'i a ransa, hakan yasa na masa dubura bai biyo ni domin ganin fuskan ki ba. Binty dan Allah ni kad'ai, ni kad'ai a ran ki". Fad'in Yousouf. Gaban Binty haka ya ke bugawa dum-dum-dum saboda kalmar kisan da ya furta. "Naji, na amince kai kad'ai za ka kasance cikin zuciya ta, amma dan Allah ka janye kalmar kisan kai da ka ambata. A musulunce ma haramun ne. Kuma duk wanda ya kashe wani rai wuta zai shiga". Fad'in Binty. Ajiyar zuciya ya sauke ta re da fad'in, "To shikenan mai sona, amma ke ma sai kin ta ya ni kiyaye hakan kin ji?". Fad'in Yousouf. Gyad'a masa kai ta yi ta re da fad'in, "Zan koma ka da Fanan ta yi ta jira na". "To yanzu kuma sai yaushe? Tun dai gidan ku ba barin fita ake yi ba". Fad'in Yousouf. "Laa! Na manta ban fad'a maka ba, jibi zan yi tafiya zan je garin mu, amma ba zan dad'e ba. Idan na dawo za mu had'u". Fad'in Binty.
*PAID BOOK 08128755583* 🌹 *49-50*🌹 ............."Gaskiya zan bi ki, mu tafi ta re kawai don ba zan juri rashin ki har na tsawon sati guda ba, zan samu matsala". Fad'in Yousouf. Dariya Binty ta yi sai da kumatun ya lob'a ta re da rera masa baiti cikin zazzak'ar muryanta, " *Sai wata rana masoyi zan bar ka, sai wata rana rabuwa ba mutuwa ba. D'an uwa rabin raina ban so mu yo rabuwa*" "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Mai sona sassauta muryan ki dan Allah ka da wani ya ji. Don na tabbata wannan zazzak'ar muryan ta ki zai iya haifar wa da mazaje da dama matsalar da zai jawo abunda ki ke gudu kuma ki ka hana ni furtawa". Fad'in Yousouf. Hannu ta sa ka ta rufe bakinta ta re da fad'in, "Afwan Reality, hakan ba za ta sake faruwa ba. Ka san ban k'aunar b'acin ran ka". "A'a, hakan fa za ta sake faruwa, amma sai muna a kad'aice in da babu wani namijin da zai ji muryan ki sai ni d'aya". Fad'in Yousouf ta re da lumshe idanuwansa. "An gama my reality, daga yau rowan muryata zan rik'awa mutane". "Da kin kuwa kyauta wa Yousouf". Dariya su ka yi gaba d'ayan su. Hanya ya nuna mata ta re da fad'in, "Mu je ko in kai ki ka da sister Fanan ta ji shuru". Yousouf ya fad'a. Jerawa su ka yi su na tafiya ta re da hira cikin nisha'di irin na saurayi da budurwa.
Sanye ta ke cikin riga da wando pallazo red colour, as usual ta yi parking d'in gashin ta a tsakiyar kan ta. Sai d'an siririn farin gyale da ta yafa a wuyanta zuwa kafad'unta da kuma farin takalmi mai tsini. Ba k'aramin kyau ta yi ba, sai dai gaba d'aya suran jikinta a waje ya ke. Duk inda su ka wuce maza da mata kallonta ake yi. "Besty ba ka ganin yadda ake bi na da idanuwa kamar za'a cinye ni. Ni kai na na san ni mai kyau ne. Ni madubin dubawa ce ga jama'a wallahi". "Hmm". Shi ne abubda Hamdan ya fad'a ta re da kallonta ta gefen idanu. Duka ta d'aka masa a tsakiyar baya ta re da fad'in, "Uban hmm, na tsane ka! Na gama koro magana sai ka wani ce min hmm kamar bai ciwon hak'ori". Fad'in Sabrin. "Ai ni matsala ta da ke kenan gajen hak'uri gare ki. So fa na ke na ce miki ai ke d'in ce kyan ki ya yi yawa. Ba ki ga wani har kusan fad'awa kan wata budurwa ya yi ba garin kallon ki". Hamdan ya fad'a. "Shege ina kallon shi ai, kuma ni kwalelen sa ce. Back to maganar mu, mai ka ke tunanin zan yi in burgesa? Shi mutum ne mara son magana da hayaniya. Wallahi besty ina matuk'ar son shi sosai. Ban tab'a son wani namiji a duniya ba kamar sa. Ya ce min in sha Allah zai samu lokaci ya zo next tomorrow. Dan Allah wani tarba zan masa ya burge sa?". Fad'in Sabrin dai-dai lokacin lokacin da za su shigo ta wani k'ofa, su Binty kuma za su fita. Ba ta re da gaba d'ayansu sun kula da juna ba, Sabrin ta bangaje ta. K'urawa juna idanu su ka yi. Shi kuma Hamdan wani d'an allura ya soki takalminsa ya duk'a ya na k'ok'arin zarewa. "Binty lafiya?". Fad'in Yousouf. "Lafiya k'alau Binty ta yi saurin fad'a ta re da yin gaba. "Binty Hisham mai goro?". Sabrin ta fad'a gabanta na tsananta fad'uwa. Cak Binty ta tsaya, dama zargi ta ke yi amma kiran cikakkiyar sunanta da Sabrin d'in ta yi ne ya sa ta tabbar ita d'in ce. Juyowa ta yi ta re da d'an sakin murmushi ta re da fad'in, "Kamar Sabrin ko?". Ta fad'i hakane ta re da d'an matsowa. Sai da Sabrin ta isa daf da ita, ka na ta ce, "Wanna fuska ta ki ba zai yi sauri mantuwa a waje na ba, billahi na yi alk'awarin in dai ni jinin Alhaji Saifullahi ce, sai na lallata wannan d'an k'aramin kyawun da ki ke tak'ama da shi". Ta na gama fad'in haka shi kuma Hamdan ya d'ago ta re da kallon in da Sabrin d'in ta ke. Hakanan ya ji gabansa ya buga da k'arfi ya na k'ara k'arewa Binty kallo zuciyar sa na wani irin zillo da buguwa. Juyo wa Sabrin d'in ta yi ta re da dawowa wajan Hamdan ta ce, "Mu je". Ta fad'i hakane ta re da yin kicin-kicin da fuska. Shikuwa Hamdan sai kallon Binty ya ke yi da ta tsaya kamar statue ta na kallon Sabrin d'in. Yousouf da ke gefe ya k'araso kusa da Binty ta re da fad'in, "Mai sona lafiya? Ya naga duk jikin ki ya yi sanyi. Kin san ta ne?". K'ak'alo murmushi ta yi ta re da fad'in, "Eh na santa, ta re mu ka yi primary school a *Lead British*". "OK. Mu je to". Fad'in Yousouf ta re da sa ta a gaba ya na biye da ita a baya. "Ko za ka bi ta ne?". Fad'in Sabrin a k'ufule. "Wallahi haka na ke ji a jikina kamar na Santa". Fad'in Hamdan. Banzan kallo ta watsa masa ta re sa yin tsaki ta yi gaba. Shikuwa Hamdan sai da ya k'ara bin su Binty da kallo ka min ya bi bayan Sabrin da ta ke ji kamar ta buga saboda ganin halittar da ta tsana a duniya.