Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 24

Ba ni da gata - Chapter 24

Ba ni da gata Chapter 24: Ba ni da gata Chapter 24. Kasancewar bai son magana da hayaniya, shiyasa jama'a da dama su ke zaton shi d'in mai girman kai ne.…

3,531 words

Kasancewar bai son magana da hayaniya, shiyasa jama'a da dama su ke zaton shi d'in mai girman kai ne. Wannan k'aron ba sai da ya yi wa Fu'ad warning akan ya tabbatar motar da zai zo d'aukar shi ta na da tinted. Hakan ne ya sa jama'ar gidan ba su san da shigowar sa ba. Ya Fu'ad na parking ya yi saurin fitowa, cikin tafiyar shi na ingarman namiji ya nufi side d'in Anna saboda bai k'aunar gaishe-gaishen nan sa y'an aiki su ke yi. Sallamar ya yi cikin siririyar muryansa ta re da kutsa kai cikin parlour ya na sakin ajiyar zuciya. Ita kuwa Anna ko sallamar shi ba ta ji ba, ta na duk'e a in da Binty ta ke kwance ta na fad'in, "Inna lillahi, wayyo Anna ta". Da ma ga ta da shegen raki. Anna kuwa cike da tausayawa har ta fara hawaye. Idanuwan Julaibib ne ya sauka akan Anna da ke sharan hawaye. Gaban shi ne ya ba da sautin dam, domin adunya ba ya k'aunar kukan mace, musamman ma a ce abun k'aunar na da duk duniya babu kamar ta ce ke yi. "Subhanallah!". Julaibib ya fad'a a hankali ta re da nufar wajan da su ke. Duk'awa ya yi ta re da ka mo hannun Anna ya ce, "Anna what's the problem? I'm here". Julaibib ga fad'a in a very cool voice da ke bayya tashin hankalin shi. Saurin kallon fuskan shi Anna ta yi ta re da fad'in, "Thanks God! Julaibin du ba min marainiyar Allah don Allah. Fad'owa ta yi daga sama". Fad'in Anna. Kallon gefen da ta ke ya yi sau d'aya ta re da saurin kau da kansa ya mai da kan Anna ta re da narke fuska kamar wani k'aramin yaro ya ce, "Anna zuwa na fa kenan, ko ruwa ban sha ba sai in fara aiki". "Do as I said now". Anna ta ba shi umarni cike da tsare gida don sarai ta san halin d'an nata abu mai sauk'i ne a wajan shi ya ce ba zai yi duba ta ba. "Wash, wash, wash! Wayyoooooh Allah na, Anna hannu na". Fad'in Binty da idamunta ke a kulle sai faman raki da kiran sunan Anna ta ke. Ya Fu'ad da shigowar sa ke nan ya yi saurin k'arasowa wajan ta re da fad'in, "Anna mai........". Bai k'arasa maganar ba idauwansa su ka sauka akan Binty da ke ya she a k'asa sai fad'in wayyo hannunta ta ke yi. Fu'ad bai san sanda ya d'auke ta cak ya aje ta akan three sitter ba ya shiga fad'in, "Beauty Anna lafiya? Mai ya same ki?". A rud'e ya fad'i haka ta re da kallon Anna ya sa ke fad'in, "Anna mai ya sa me Binty?". "Ta yi missing step ne". Anna ta fad'a ta re da kallon Julaibib ta antaya masa harara. Hannu Julaibib ya sa ka ga dafe kan shi, don ihun ''wayyo hannu na'' da Bintyn ta ke yi har ya soma damun shi. Ya Fu'ad kuwa kallo Binty ya yi ta re da fad'in, "Sannu kin ji Binty, ga ya Bibi nan zai du ba ki". Harara Julaibib ya makawa Fu'ad da bai ma san ya na yi ba. Yamutsa fuska ya yi ta re da nufar wajan da Bintyn ta ke a kwance ya d'an rankwafa ta re da rik'o hannun da ya ke mata ciwon. Wani k'ara ta kwalla ta re da rik'e hannun Julaibib d'in da d'ayan hannunta. Don lokaci d'aya ta ji wani azaba biyu ya ziyarci hannun. Na farko zafin da hannun ya ke mata, ba biyu kuma wani irin k'aik'aci mai kama da k'unan wuta da ta ji yayin da ya rik'e hannun na ta. D'an tsaki ya yi ta re da d'aure fuska ya ce, "Sake min hannu ko in mazge ki anan wajan. Sai shegen raki da shagwab'ar tsiya. 'Anya wayyoo hayyunaa'. Dallah matsa can". Julaibib ya maimaita abunda ta ke fad'i kamar yaro na magana. Duk irin tausayin da Fanan ke mata sai da ta dara saboda yadda Ya Bibi ya yi maganar. "Ka rai na ni ko Julaibib?". Fad'in Anna ta na kallon shi. "Anna ba laifi na ba ne. Y'ar ki za ki yi wa magana ta natsu in duba mata hannun. Kuma ma fa buguwa ce kawai ta yi tsabar raki ne kamar ta karye ko ta samu gocewar k'ashi". Julaibib ya k'arisa maganar ya na maka mata harara. Zama a gefen in da ta ke Anna ta yi ta re da shafa kan ta ka na ta ce, "Auta na ji tsaya yayanku ya duba miki hannunki kin ji ko, in sha Allah zai warke ya dai na miki zafi". Fad'in Anna a tausashe. "Annan mu dan Allah ace masa ya min a hankali. Zafi na ke ji". Fad'in Binty cikin shasshek'ar kuka. "To zan fad'a mishi, amma kar ki gardama kin ji Binty na". Fad'in Anna. Gyad'a mata kai Binty ta yi ta ra da kallon Julaibib ta wani narke fuska. Harara ya watsa mata ta re da kamo hannu. Wannan karan ba ta ji turirin azaba kamar ta k'one ba, sai azabar yadda yake murd'a hannun. Wani irin ihu ta saki da k'arfi har ba ta san san da ta afka jikinsa ba ta re da ruk'unk'ume shi ta na fad'in, "Wayyiooo Annah zai kashe mi ki ni. Dan Allah ki taimake ni". Shi kuwa Julaibib, ihunta har cikin kwanyar shi ya ji shi, ji ya yi kunnan shi ya yi masa wani duummmm. A hankali ya b'amb'are ta daga jikinsa ya bar ta nan kwance k'asa ta re mik'ewa tsam ya saka hannun shi biyu a kan kunnansa ka na ya juya ya soma tafiya. Da sauri ya Fu'ad ya bi bayansa Anna ta yi saurin dakatar da shi ta re da girgiza masa kai. Dawowa ya yi inda Binty ta ke ta re da sungumar ya mai da ta kan kujera. Julaibib be ya juyo ta re da watsa masa harara kamar zai yi magana, sai kuma ya fasa ya fice daga d'akin. "Fu'ad ina ganin gasa hannun za'a yi". Fad'in Anna. "Gasawa kuma Anna?". Fu'ad ya fad'a a marairaice ya na kallon idanunta. "Eh. Ba ka ji abunda ya ce ba. Ba karaya ba ce kuma ba tsagewar k'ashi ba ne. Buguwa ce. Saboda haka gasawa za'a yi sai a shafa mata maganin zafi". "To Anna ina da maganin zafi a d'aki na, ba ri na d'auko". Ya fad'i hakane ta re da mik'ewa ya fice daga d'akin. "Sister sannu kin ji". Fad'in Fanan kamar za ta yi kuka ta na kallon Binty da ke gunjin kuku. "Ba ri ba d'ai bo ruwan zafi a kitchen, ki zauna da ita". Fad'in Anna ta re da nufar kitchen.

Fu'ad kuwa d'akin Julaibib ya so zuwa, nocking ya yi, sai da Julaibib d'in ya ba shi izinin shiga ka na ya shiga. Zaune ya sa me shi a bakin gado ya rik'e kan shi da hannu bibbiyu daga shi sai dogon wandon jikinsa da kuma singlet. D'ago jajayan idanuwan shi ya yi ta re da watsawa Fu'ad wani kallo sai da hantar cikinsa ya motsa. Mai da idanuwan shi ya yi ta re da lumshe su ka na ya mai da ya rufe. "Kar tsautsayi ya sa ka k'ara d'aukar yarinyar nan, ka san dai ba muharramar ka ba ce. Ka ba ri Anna da Fanan su taimaka mata. Ka ji abunda na ce?". Sai da Fu'ad ya had'iye wani bushasshen miyau har sai da Adams apple d'in shi ya motsa ka na ya ce, "In sha Allah haka ba zai sa ke faruwa ba Ya Bibi". Gyad'a kai kawai Julaibib ya yi ta re da mik'ewa ya nu fi toilet. Fu'ad na ganin haka, shi ma ya mik'e ya fice daga d'akin domin d'auko maganin zafi. Ko da Ya Fu'ad ya dawo, tu ni har Anna ta kawo ruwan zafi da tsumma shi kawai ta ke jira. Tsummar ta sa ka a ruwan ka na ta matse ta shiga dannawa a hannun na ta a hankali. "Wayyiiiiooo Annah zan yi fitsari wallahi. Dan Allah akwai zafi. Zafi, zafi zafi zafi zafiiiiiiiiii". Fanan ba ta san sanda ta b'arke da dariya ba saboda "Anna zan yi fitsarin" da Binty ta ce. "Bar nan ko in watsa miki ruwan zafin nan a wuya da sai kin yi fitsari ka min ita ta yi". Fad'in Ya Fu'ad ya na gintse dariyar shi bai so ya yi. Wani dariyar Fanan ta Ku ma bushewa da shi ka na ta ce, "Wallahi ya barrister kai ma ka d'ana. Ba ri Binty ta warke, kai da ita be ba ruwa na".

"Assalamu alaikum". Muryan Kandala ta katsewa ya Fu'ad maganar da zai yi. Gaba d'aya su ka amsa mata sallamar har Anna da ta juya ta na kallon ta. "Ah! Kandala ke ce? K'araso ciki mana". Fad'in Anna murmushi d'auke a fuskan ta. K'arasowa Kandala ta yi, ta yi dumurmur da ita har wani haske ta yi. Kayan jikinta kawai idan mutum ya kalla zai san ta mugun samun sauyi a rayuwarta. Tsayunta biyu sanye da zinari da guda d'aya kawai kud'insa zai kai dubu d'ari shidda. "Maza kawo mata ruwa da abincin". Fad'in Anna ta na kallon Fanan. "Ina wuni?". Fu'ad ya fad'a ta re da mik'ewa ya nufi hanyar waje, don shi har ga Allah bai san mai ya sa ba, bai k'aunar matan sam. Ta na amsa mashi gaisuwar ma ko sauraranta bai yi ba. "Ina wuni Hajiya? Mun same ku lafiya?". Fad'in Kandala cike da fara'a a fuska. "To Alhamdulillah, sai dai d'iyar ta ki ce ta yi missing step ta gunguro daga sama hannunta ya bugu". Fad'in Anna ta na kallon Binty da ke ta raki a hankali. "Subhanallah! Allah ya kiyaye gaba. Sannu kin ji Binty". Sai a lokacin Binty ta d'ago ta kalle ta ta re da fad'in, "Ina wuni Baaba, kin zo lafiya?". "Lafiya k'alau Binty, ya k'arfin jiki". Fad'in Kandala cike da tausayawar bariki. "Da sauk'i". Binty ta fad'a a gajarce ta re da kallon gefe. Fanan ta aje mata faranti a gabanta. Sakwara ce miyan egusi da yaji stockfish da bushasshan kifi irin mai tsokar nan. Sai ruwan gora ta re juice d'in carrot. Favorite d'in Julaibib ke nan. Shiyasa Anna ta shiga kitchen da kan ta ta had'a masa. Babu kunya Kandala ta baje ta kwashi abinci babu algus. Wayar Anna ta ta yi k'ara. Ta na zubawa ta ga sunan Julaibibin ta na ke kira. Murmushi ta yi ta re da d'aga wayar. "Anna ba'a gyara min d'aki ba, toilet d'in ba bu tsafta ba zan iya amfani da shi ba". Fad'in Julaibib. "OK ban minti biyar". Fad'in Anna ta re da yanke wayar. Kallon Fanan da ke danna wayarta ta yi ta re da fad'in, "Da ma da na tura ku Ku gyarawa yayanku d'akin ba Ku gyara ba ko?". Fad'in Anna ta re da tsare Fanan da idanu. Zaro idanuwa Fanan ta yi ta re da, "Fad'in Allah Anna mun gyara". "To k'arya ya ke yi kenan? Ya ce ba Ku wanke masa toilet ba". Zaro ido Fanan ta sake yi ta re da kallon Binty da ke kwance. Ita kuwa Binty ta yi saurin mai da idanuwanta ta rufe don ka da Anna ma ta yi mata magana. "Maza yanzu ki je ki wanke masa, ke ya ke jira zai shiga ba yi". Fad'in Anna. Yarfe hannu Fanan ta so ma yai ta re da fad'in, "Anna na shiga uku, Annah dan Allah ba ni ba ki sa wata. Zai kashe ni". "Ai na fi son ya lallasa ki, tun da dai ban isa in saka Ku aiki ku yi ba. Haka zan maku aure Ku je ku na yi". Fad'in Anna. "Anna wayyo, Anna wayyo Allah". "Wallahi idan ba ki wuce ba na tashi za ki ji jiki". Fad'in Anna. Fanan har da guntun hawayanta ka na ta fita ta na addu'a a cikin zuciyarta. Knocking ta soma yi ka na ta shiga, su na had'a idanu da Julaibib ta tafi da gudu ta rungume shi ta re da fad'in, "Oyoyo Yaya Bibi na, welcome home my sweet bro. Na fa fi son ka a kan ya Fu'ad". Fad'in Fanan. "Wuce ki je ki wanke min bayi". Ya fad'a a murtuke. Cikin sauri ta yi wajan bayin ta re. Ba bu ma wani datti. Sosai ta natsu ta wanke shi tass, ka na ta fito ta re da fad'in, "Na gama Yaya". Ta fad'in hakane ta na jiran hukuncin ta na rashin wanke bayin da ba ta yi ba. Tasowa ya yi ta re da rab'e ta ya wuce bayin. Nannauyan ajiyar zuciya ta sa ki ta re da ficewa daga bayin.

"Ina jin ki Kandala". Fad'in Anna. "Eh to, Hajiya dama dai Binty ce na ke so a ba ni ita za mu je Saminaka ta je ganin gida, kin san tun da ta zo nan ba ta sake lek'awa ba. To kin san mutane. Shine ake mini tunanin ko sai da ita na yi. Shine na ke so muje ta yi ko da sati ne sai mu dawo". "Dan Allah ki yafe min Kandala. Duk laifi na ne da ko sau d'aya ban tab'a wannan tunanin ba. Amma in sha Allah za ki tafi da Binty ta je ta ga gida ita ma. Ni ma kai na zan so bin Ku, sai dai hakan ba zai samu ba saboda wani d'an uzuri nawa, amma in sha Allah idan kun dawo ba za ta rufe wata biyu ba zan saka driver ya d'auke mu ni da ita da Fanan sai muje muga k'auyan na Ku. Amma yaushe tafiyar? Zan so ya kai jibi saboda in sa mu in mata tsaraba". Anna ta fad'a. "Ayya ai babu komai Hajiya, ki dai na rok'on gafarata. Binty d'iyarki ce ai". Kandala ta fad'a ta re da share zufar da ta tsiyayo mata a goshin ta. "Nagode Kandala. Jibi ki zo ki d'auke ta sai Ku tafi". Fad'in Anna ta na kallon fuskan Binty da ta yi kicin-kicin.

🌹 *47-48*🌹 ............."To Hajiya nagode Allah ya k'ara girma. Ni zan koma ka da dare ya min". Fad'in Kandala ta re da satar kallon Binty da ko in da ta ke bata k'ara kallo ba tun da ta gaishe ta. "D'an jira ni ina zuwa". Fad'in Anna kuma dai-dai lokacin Fanan ta shigo d'akin ta re da zama kusa da Binty a inda Anna ta tashi. Ita kuwa Binty zuciyar ta ne ya rabu gida biyu. Na farko ta na son sanin menene manufar Kandala a kan ta, na biyu kuma ta yadda za ta samu damar fita ta je wonderland park su had'u da Yousouf. "Ke tunanin me kike yi ki ka yi shuru haka?". Fad'in Fanan ta re da girgiza Binty. "Tunanin ta ke za ta yi tafiya har na tsawon sati guda ta barki. Kewarki ta soma yi". Kandala ta yi saurin baiwa Fanan amsa. Tuni har Fanan ta rud'e ta re da kallon Binty ta ce, "Sister ina za ki tafi ko bar ni? Dan Allah kar ki je ko ina". Fad'in Fanan har kwalla ya ciko mata a idanunta. "Hak'uri za ki yi Fanan. Ita ma za ta je ta ga y'an uwanta ne. Ai ba jima za ta yi ba". Fad'in Anna da saukowarta kenan hannunta rik'e da wata babbar leda. "Anna wallahi gidan ba zai min dad'i ba idan har ba bu Binty. Dan Allah ta fasa zuwa". Fanan ta fad'a hawaye na gangarowa daga idanunta. "Gidan ku Fanan. Allah ki ka min shirme zan had'a ki da yayan ku ya ci min k'aniyar ki. So gwara ma ki natsu. Na ce miki ba dad'ewa za ta yi ba. Sati za ta yi". Fad'in Anna wacce ita kanta bata k'aunar Binty ta yi nesa da ita kawai dauriya ta ke yi saboda tabbas ya kamata Binty ta ga y'an uwanta. Ta shi Fanan ta yi da gudu Fanan yi hanyar sama har saura kad'an ta fad'i sai da Binty ta saki wani dogon ajiyar zuciya na jin dad'in Fanan d'in ba ta kai k'asa ba. "Allah sarki, sun shak'u matuk'a ne". Fad'in Kandala wacce ta ke ta addu'ar Allah ya sa Anna ka da ta ce Fanan d'in ta bi su. Don idan ta ce haka, za ta b'ata mata shirin da ta yi. "Ga wannan Kandala, kya rabawa y'an uwa da abokan arziki. Wannan kuma ki yi kud'in mota. Allah ya kiyaye hanya". Fad'in Anna ta re da mik'a mata ledan da kuma dubu ashirin. Sosai Kandala ta yi ta godiya kamar za ta duk'a, ka na ta kalli Binty ta re da fad'in, "To Binty Allah ya k'ara sauk'i. Sai na zo d'aukar ki". Ba ta re da Bintyn ta kalle ta ba ta ce, "Allah ya kiyaye hanya". Ta fad'i hakane ta na jin wasu kwalla na zubo mata don ita kanta ba ta k'aunar matsawa kusa da Anna da Fanan don su ne duniyarta. Waya Anna ta d'aga ta kira ya Fu'ad ta re da shaida masa ya zo part d'in ta yanzu, kuma ka min ya zo ya biya ya kira Julaibib shi ma ya zo. Bayan ta gama wayarne ta nufi kitchen don kai abincin dinning d'in da ke nan parlour. Binty kuwa tuni ta mik'e ta yi saman don zuwa ganin halin da y'ar uwarta ta ke ciki. Ka min ta shiga corridorn da zai sa da ta da bedroom d'in su, ta ji kamar an rik'e hannun da ke mata zafi wanda sai da ta tallabo shi da d'ayan hannunta saboda ba za ta iya sakin shi ta yi tafiya ba. Azaba ta dunga ji har cikin kwanyanta kuma kamar an toshe bakinta ta kasa kuka. Sai da ta yi kusan minti uku kamin ta ji an saki hannun. Don har kwallar azaba sai da ta yi. Amma abunda ya matuk'ar ba ta mamaki, shine hannun na ta ya dai na mata zafi ko kad'an, kamar ba ta fad'i ba. Har gwada jujjuya hannun sai da ta yi, kuma lafiya k'alau hannun bai mata ciwo ba. "Ikon Allah!". Binty ta fad'i ta re da shiga bin corridor ta murd'a handle d'in d'akin su ta re da shiga ciki. Kwance ta samu Fanan ta na shasshek'ar kuka. Hawa kan gadon ta yi ta re da juyo da fuskan Fanan d'in ta ce, "Sister ki dai na kuka, wa ya isa ya raba mu. Ko aure ne, dole mazajan mu su hak'ura mu zauna a waje d'aya. Ga part d'i na ga na ki. Ko wannan tafiyar ma k'afa ta k'afar ki. Idan har ba za ki ba, to ni ma babu inda zan je". Saurin ta shi Fanan ta yi ta re da fad'in, "Kai amma ni wawiya ce, Sam ban kawo haka ba. Dama ni ban tab'a tafiya wani garin mai nisa ba Idan ba Gombe ba, shi ma ina k'arama mu ka je dukkan mu har da su ya Bibi". "K'afa ta k'afar ki ai". Binty ta fad'a ta re da d'aga pillow ta d'auko wayar ta ta kunna. "Ke wai har hannun ya warke". Fad'in Fanan cike da mamaki. Don ko d'an kumburin da ya yi ma ya sace. "Wallahi kam. Ni ma haka nagani. Abu kamar tsafi". Fad'in Binty. "Anya maganar ya Bibi ba gaskiya ba ce kuwa, har da d'an banzan rakin ki". Fad'in Fanan. Harara ta maka mata ta re da shiga message ta soma typing. " *Mu had'u 4:30. Ka jira ni a wajan*". Ta na gama rubutawan ta kalli Fanan ta re da fad'in, "Sister wani taimaki za ki min dan girman Allah". "Wani irin taimako kenan? Fad'a min. Babu taimakon da ba zan iya miki shi ba Idan har zan iya yin sa". Fanan ta fad'a ta re da ba ta natsuwarta. Shuru Binty ta na tunanin ta inda za ta fara maganar. Can ta nisa ta re da fad'in, "Fita na ke so na yi daga gidan nan. Zan had'u da Yousouf a wonderland by 4:30". Wani irin zaro idanuwa Fanan ta yi ta re da fad'in, "Are you out of your sense. Fita fa ki ka ce? Ta yaya za ki iya barin first and second gate ba ta re da an gan ki ba?". " Shiyasa na ce ina buk'atar taimakon ki ai. Ke za ki taimake ni in fita ai". Fad'in Binty. "Lallai kin d'auko ta da zafi. Kin san dai fire to fire ya dawo ko, sannan Anna ba ta bari mu fita kk bakin first gate ne sai da driver ko ya Fu'ad". Fanan ta fad'a ta na kallonta. Kwal-kwal Binty ta yi kamar za ta yi hawaye ta na kallon Fanan. Can sai ga hawaye shaaaaaa. "Na shiga uku! Why are you crying? Dan Allah ki ba ri. Zan yi k'ok'arin yi wa Anna magana sai mu fita ta re da driver, sai ki je ki ga romeo d'in na ki". Fad'in Fanan. Rungumeta Binty ta yi ta re da fad'in, "That's why I love you my beloved sis". Wayar Fanan d'in ce ta yi ringing, kallon wayar ta yi ta re da kallon Binty ka na ta ce, "Let go downstairs, Anna is calling". Fanan ta fad'i ta re da sauka daga kan gadon.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull