Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 23

Ba ni da gata - Chapter 23

Ba ni da gata Chapter 23: Ba ni da gata Chapter 23. Yaya Fu'ad da ke kallon ta ba ta re da sanin abunda ta ke yi a cikin wayar ba, ya na jin son ta na…

2,565 words

Yaya Fu'ad da ke kallon ta ba ta re da sanin abunda ta ke yi a cikin wayar ba, ya na jin son ta na k'ara huda ko wani sashe na jikinsa. "Fanan ki d'auko key d'in part d'in ya Bibi Ku je ke da Binty ku gyara masa tsaf, kin san bai san y'an aiki na shigar masa d'aki. Maza ku ta shi yanzu". Fad'in Anna. Ta shi Fanan ta yi ta re da kallon Binty da ke kallon sak'on da Yousouf ya sake turo mata yanzu sakamakon replay d'in da ta masa. Fizge wayar Fanan ta yi ta re da yin sama da gudu, sai a lokacin Binty ta dawo cikin natsuwarta ta re da bin bayan Fanan d'in da gudu ita ma. Har kan gado Binty ta ni ta ta re da fizge wayar ta maka mata harara, ka na ta cigaba da karantawa message d'in Yousouf d'in ta re da kwanciya a kan gado har da wani lumshe idanu. "Idan za ki ta shi ma gwara ki ta shi muje mu gyara d'akin ya Bibi". Fad'in Fanan. "Ki je ki yi ke d'aya, ni love na ke yi. Aikin ne ba za ki iya yi ke d'aya sai na ta ya ki?". Fad'in Binty. "To ba ri na je na fad'a wacce ta ce mu yi ni da ke, idan ya so sai ki ke da kan ki ki fad'a mata ke ba za ki yi ba". Fad'in Fanan ta re da sauka daga kan gadon. Rik'o hannunta Binty ta yi ta re da fad'in, "Ke fa muguwa ce, to na aje wayar muje. Kill joy kawai saboda ta ga ba ta da mai tura mata hot messages". Fad'in Binty. Tab'e baki Fanan ta yi ta re da fad'in, "Ni ma nawa Prince d'in ya na kan hanya". Fitowa su ka yi su ka nufi side d'in ya Bibi da ya kusan sumar da Binty saboda tsaruwarsa, da ta d'auka ba za'a samu d'akin da ya fi na Daddy kyau ba, sai ga na Julaibib ya ninninka na daddyn. Mai makon su tsaya su gyara d'akin da kyau, sai su ka b'ige da masa bincike a d'akin su na kallon old picture d'in sa. Hoton sa Binty ta ga ni lokacin da ya kammala degree d'in sa na farko hannunsa rik'e da award. "Kaiii ku kyawawa ne Fanan, yayan ki kyakkyawa ne sosai". "Ya su ke da Yousouf d'in ki?". Fad'in Fanan. Saurin ajiye hoton Binty ta yi, ka na ta kalli Fanan d'in ta re da fad'in, "Ko kusa ba bu had'i, wallahi Yousouf d'i na ya fi shi kyau". "Beauty is in the eyes of the beholder". Fad'in Fanan ta re da soma kakkab'e gadon. Haka su ka yi aikin ba cikin natsuwa ba, don su na yi sai su aje su ko ma kallon wani abun. Daga k'arshe ma haka su ka gama su ka manta ba su wanke bayi ba.

Yaya Fu'ad da ke kallon ta ba ta re da sanin abunda ta ke yi a cikin wayar ba, ya na jin son ta na k'ara huda ko wani sashe na jikinsa. "Fanan ki d'auko key d'in part d'in ya Bibi Ku je ke da Binty ku gyara masa tsaf, kin san bai san y'an aiki na shigar masa d'aki. Maza ku ta shi yanzu". Fad'in Anna. Ta shi Fanan ta yi ta re da kallon Binty da ke kallon sak'on da Yousouf ya sake turo mata yanzu sakamakon replay d'in da ta masa. Fizge wayar Fanan ta yi ta re da yin sama da gudu, sai a lokacin Binty ta dawo cikin natsuwarta ta re da bin bayan Fanan d'in da gudu ita ma. Har kan gado Binty ta ni ta ta re da fizge wayar ta maka mata harara, ka na ta cigaba da karantawa message d'in Yousouf d'in ta re da kwanciya a kan gado har da wani lumshe idanu. "Idan za ki ta shi ma gwara ki ta shi muje mu gyara d'akin ya Bibi". Fad'in Fanan. "Ki je ki yi ke d'aya, ni love na ke yi. Aikin ne ba za ki iya yi ke d'aya sai na ta ya ki?". Fad'in Binty. "To ba ri na je na fad'a wacce ta ce mu yi ni da ke, idan ya so sai ki ke da kan ki ki fad'a mata ke ba za ki yi ba". Fad'in Fanan ta re da sauka daga kan gadon. Rik'o hannunta Binty ta yi ta re da fad'in, "Ke fa muguwa ce, to na aje wayar muje. Kill joy kawai saboda ta ga ba ta da mai tura mata hot messages". Fad'in Binty. Tab'e baki Fanan ta yi ta re da fad'in, "Ni ma nawa Prince d'in ya na kan hanya". Fitowa su ka yi su ka nufi side d'in ya Bibi da ya kusan sumar da Binty saboda tsaruwarsa, da ta d'auka ba za'a samu d'akin da ya fi na Daddy kyau ba, sai ga na Julaibib ya ninninka na daddyn. Mai makon su tsaya su gyara d'akin da kyau, sai su ka b'ige da masa bincike a d'akin su na kallon old picture d'in sa. Hoton sa Binty ta ga ni lokacin da ya kammala degree d'in sa na farko hannunsa rik'e da award. "Kaiii ku kyawawa ne Fanan, yayan ki kyakkyawa ne sosai". "Ya su ke da Yousouf d'in ki?". Fad'in Fanan. Saurin ajiye hoton Binty ta yi, ka na ta kalli Fanan d'in ta re da fad'in, "Ko kusa ba bu had'i, wallahi Yousouf d'i na ya fi shi kyau". "Beauty is in the eyes of the beholder". Fad'in Fanan ta re da soma kakkab'e gadon. Haka su ka yi aikin ba cikin natsuwa ba, don su na yi sai su aje su ko ma kallon wani abun. Daga k'arshe ma haka su ka gama su ka manta ba su wanke bayi ba......

..............."Haba besty na, idan ki ka guje ni ina za ni. Dan Allah ki yi hak'uri mu shirya beauty". Fad'in Hamdan tsugunne a gaban Sabrin da ta had'a k'afa d'aya a kan d'aya ta na shan ice-cream ko kallon shi ba ta yi ba. "Dan Allah ki min magana Love, idan ki ka yi fushi da ni zan fad'a wancan sweeming pool d'in can in mutu". Fad'in Hamdan.. "Really? Mu je wajan to mu ga ni". Fad'in Sabrin ta re da hararar sa ta re da mik'ewa ta yi wajan pool d'in. Bin ta ya yi a baya ta re da cigaba da magiya. Sai da ta tabbar ya zo kusa da pool d'in ka na ta daddage ta tura shi ciki ta na masa dariya da gwalo ka na ta ce, "Beautyn ta ka ta zo ta cece ka. Ta yi tsuntsuwa daga kan bola ta zo ta ciro ka". "Haba ai Ke ce beauty na. A kwai wacce ta kai best friend d'ina kyau kuwa, ina tunanin fa ko Beauty a wajan ki aka sammata". "Hmm, sweet mouth. I hate you". Fad'in Sabrin da k'arfi. "And I love you besty". Fad'in Hamdan da k'arfi. Ko juyawa ba ta yi na ta so ma tafiya. Da sauri-sauri ya fito ruwa na d'iga a jikins ya nufi wajanta da har ta bud'e mota. Shi ma bud'e gaba ya yi ta re da shiga. Kallon shi ta yi ta re da yamutsa fuska ta ce, "Disgusting, please out". Ruwan goran da ke gyefan shi ya bud'e ya watsa mata a jiki ya na dariya. Ihu ta yi ta re da soma kukan shagwab'a ta na fad'in, "I hate you, I hate you, I hate youuuuuuuuuu". Fitowa ya yi daga motar ya jawo ta daga driver seat ya mai da ita in da ya tashi ta re da rufe mata k'ofa ka na ya ko ma driver seat d'in ya ja motar su ka bar park d'in.

*PAID BOOK 08128755583* 🌹 *45-46*🌹

*Bonus*✋🏻😂 ( *BARKA DA SABUWAR SHEK'ARA. YA UBANGIJI HALITTA, SA DA MU DA ALKHAIRI WANNAN SABUWAR SHEKARA DA MUKA SHIGA, SA'ANNAN KA KORE MANA FITINTINU DA BALA'IN DA KE CIKIN TA ALFARMAR FIYAYYAN HALITTA (AMEEN)*)

............."Besty dan Allah ki dai na saurin fushi haka, ki ga ne ke d'in ta daban ce. Amma fa ita ma Binty..." "Enough! Za ka saka in bud'e motar nan in fita idan har ka cigaba da kururta y'ar bolan ka a gaba na. Ka ba ri idan za ka fad'i kyawunta sai ba na wajan dan zan shak'e ka ka mutu in kuma canza besty". Fad'in Sabrin. "Da kad'an Binty na ta fiki kyau". Fad'in Hamdan ta re da yi mata gwalo. Shak'e shi ta yi ta ta re da fad'in, "Sai na kashe ka, sai na kashe ka, mai kan goruba kawai". Dariya ya shiga yi ta re da k'ok'arin kwace wuyar rigarsa da ta rik'e. Saura kad'an su yi karo da wata mota ya yi saurin juya steary ta re da ta ka burki. "Kin ga abunda ki ke so jawo mana ko?". Fad'in Hamdan ta re da dungure mata kai. "Drive jo! Sanyi na ke ji in yi ina son canza kaya". Fad'in Binty ta re da ja masa hancinsa. "Sannu ni kuma in ce me da kika tura ni cikin pool. Du be ni gaba d'aya na a jike na ke har d'iga na ke yi". Hamdan ya fad'a ta re da kunna motar ya soma tafiya a hankali. "Ai kai ka ja, idan za ka rik'a maganar beauty a gaba na zan to she ka yasin-yasin yaro". Fad'in Sabrin. "Ke wanene yaron? Na fasa miki baki". Turo bakin ta yi ta re da fad'in, "In ka fasa". Figar motar ya yi da guda sannan ya soma jan giyar ta na gama ta na bayan kamar ta na jacking. Hannun shi ta kai wa cizo shikuma ya saki k'ara ta re da fad'in, "Auuch! Wallahi sai dai ke ki yi driving, idan ba haka ba kuma mu kwana a nan". Hamdan ya fad'a ta re da folding hannunsa ya na kallonta. "Driving ko? Zan ko yi". Fad'in Sabrin ta re da fitowa daga cikin motar ta zagaya, shikuma ba ta re da ya fito ba ya koma inda ta tashi. "Ka tabbatar ka saka belt". Fad'in Sabrin ta re da saka belt a jikinta, shi ma Hamdan ya saka. Key ta yi wa motar ta re da figar motar da uban gudu. Da ba din Hamdan ya saka belt ba, sai ya yi tsalle ka na zai dawo wajan zaman sa. "Ki yi wa girman uban giji ki yi parking zan koma gida a k'afa". Fad'in Hamdan saboda irin uban gudun da Sabrin d'in ta ke yi, don motarsu har karkacewa ta ke yi kamar b'arayi y'an sanda sun biyo su.

*________________* ............Gaba d'aya y'an aiki sai kai wa da komowa ake yi sakamakon babban d'an mai gidan da zai dawo yau daga k'asar *CANADA*. Anna da kanta yau ta shiga kitchen ta na had'awa shalelen na ta abuncin da ya fiso, gefe kuma Fanan da Binty na ta ya ta da wasu abubuwan. Wayar Bintyn ce ya yi k'ara, fiddo da wayar ta yi daga cikin aljihun apron d'in da ke jikinta. Text message Yousouf ya turo mata, murmushi ta saki ta re satar kallon Anna ta ga Sam hankalinta bai kan ta. Sak'on ta shiga karantawa ta na sakin murmushi har hak'oranta sai da su ka bayyana. Sai da ta gama karantawa tsaf, ka na ta shiga yi masa replay da dad'ad'an kalamai kamar yadda su ka saba. "Amma ban yi maku warning akan shigo da waya kitchen ba? Na fad'a maku ba'a zuwa da waya a in da akwai gas amma Sam ba kwa jin magana". Fad'in Anna ta na kallon Binty da ta yi saurin mayar da wayar cikin aljihun apron d'in gabanta na fad'uwa kuma ta na addu'ar Allah ya sa ka da Anna ta ce ta ba ta wayar ka da ta ga abunda ta ke yi. "Anna ita dai, don ni kam ban shigo da waya kitchen". Fad'in Fanan ta na yi wa Binty gwalo. "Keep quite, ai halin ku d'aya. Thank God Yayan ku na hanya, duk zai gyara maku zama ai". Fad'in Anna ta na hararar su duka. Dariya Binty ta yi ta re da yi wa Fanan gwalo kamar yadda ita ma ta yi mata. "Anna ki na ganin ta ta na min gwalo ko. Ki fad'a mata ni yayarta ce fa. Zan zane ta". Fad'in Fanan. Kallon Binty Anna ta yi ta re da fad'in, "Maza ki je ki aje wayar nan ki dawo. Ban son in k'ara ganin Ku da waya a hannun Ku in dai za Ku shigo kitchen. Idan kuma ba za Ku kiyaye ba, to zan kwace wayar". "Anna ki yi hak'uri za mu kiyaye". Gaba d'aya su ka fad'a saboda kwace waya da su ka ji Anna ta ce, don sun san hakan ba k'aramin aikin ta ba ne.

Fitowa daga kitchen d'in Binty ta yi ta re da saurawa sama da sauri. Ta na shiga d'akin su ta k'arisa typing message d'in ta re da tura masa. Cikin second minti d'aya ya sake turo mata da wani message d'in. Ita ma ta sake masa replay. Kamar wasa su ka yi ta wa junan su musayan kalamai, su Binty har da kwanciya a kan gado, shaf ta ma manta da batun girki da su ke yi. " *_Mai yasa ka fiye son aiko min da sak'o fiye da ka k'ira ni a waya? Kwata-kwata sau biyu kawai mu ka tab'a yin magana ta waya_*". Ta na gama typing ta tura masa. Karan message ne ya shigo wayar ta. Bud'e message d'in ta yi. " *_I preferred message than talk, that the reason_*". Murmushi ta yi ta re da typing message. " *_Muryata ba dad'i ko? Na san haka ne ai_*". Wayar ta ce ta so ma k'ara. Sai da gabanta ya fad'i da ta ga shi ne ke kiran ta a waya. Kasa picking ta yi har wayar ta gama k'ara. Wayar na yankewa, ya tura mata message. " *_Ban tab'a jin murya mai dad'i kamar ta ki ba. Golden voice gare ki. Mai ya sa ki ka k'i picking call d'in? Are you angry?_*". Dad'i ne ya mamiye zuciyarta, message ta shiga yi masa typing. " *_Haka nan na ji na kasa d'aukar wayar. I'm not angry with you_*". Message d'in da ya sa ke turo mata ne ya sa k'irjinta bugawa. Kallon message d'in ta yi ta re da k'ara karantawa. " *_Idan ba matsala, mu had'u a wonderland by 4:00pm_*".. Ta karanta message d'in ya kusa sau goma. Wani message d'in ne ya sa ke shigowa. " *_Still waiting for your replay_*". Ta na gama karantawa ta kashe wayar gaba d'aya ta re da sauka daga kan gadon. Apron d'in da ta ga ni a jikinta, shi ya tuna mata abunci su ke yi a kitchen. "Wayyo Allah na". Shine abunda ta fad'a ta re da fita da gudu. Da gudu-gudu ta ke saukowa daga steps d'in, aikuwa tsautsayi ya sa ta yi missing step ta dunga gungurowa har ta fad'o can k'asa. K'aran ihunta ne ya fito da Anna da Fanan da ke kitchen da gudu. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!". Anna da Sabrin su ka fad'i ta re da nufar in da ta ke. A dai-dai lokacin ne kuma, motar Barrister Fu'ad ta dannawa Oga Solomon horn, dawowar shi kenan daga airport ya je ya d'auko ya Bibi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull