Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 22

Ba ni da gata - Chapter 22

Ba ni da gata Chapter 22: Ba ni da gata Chapter 22. *KU NA INAAA🗣️ KU FIRFITO MAZA KU JI ABUNDA NA KE TAFE DA SHI, SHARARRIYAR SHU'UMIN HUMRAH CE TA BAN…

3,329 words

*KU NA INAAA🗣️ KU FIRFITO MAZA KU JI ABUNDA NA KE TAFE DA SHI, SHARARRIYAR SHU'UMIN HUMRAH CE TA BAN MAMAKI MAI JAWO MIKI MIJIN DA SOYAYYAR SHI A KUSA DA KE. HUMRAH CE MAI MATUK'AR KYAU BA BU MIX, UWARGIDA KI GWADA, ZA KI BA NI LABARI, GUARANTEE NA KE BA KU DOMIN NA GWADA SHIYASA NI MA NA KE SO KU K'ARU. ZA KI GA SO, KULA DA TARAIRAYA A WAJAN MAI GIDA, RANAR DA KI KA YI AMFANI DA HUMRAN MAMAN KHAIRAT BA ZA KI K'ARA AMFANI DA WANI TURARE BA, KUMA NASAN SAI KIN GODE MIN. AKA CE SIYAN NAGARI, MAI DA KUD'I GIDA. ZA KI SAMU SHU'UMIN HUMRAH A WAJAN MAMAN KHAIRAT A KAN FARASHI MAI SAUK'I. YAR UWA BA ZA KI YI KUKAN KUD'IN KI BA. SAI AN GWADA A KAN SAN NA KWARAI. NAI MI MAMAN KHAIRAT A NUMBERN TA KAMAR HAKA👉🏻 07032294232*

..........."Dakata Hajiya kar ki matso nan wajan. Dan Allah ku fita waje ba'a son hayaniya a kusa da ita. Mutum d'aya kawai ya tsaya sauran duk ku fita please ". Fad'in nurse ta na kallan Hajiya Mansura da ta gama rud'ewa sakamakon arba da jikin Binty. Ruwan gora Fu'ad ya d'auko a kan drower ya mik'awa Alhaji Usman. Cikin sauri ya karb'i goran ta re da tsiyayar ruwan a hannunsa ya shafa mata a fuska, kasancewar Fu'ad d'in ya bud'e goran. Dogon ajiyar zuciya ta sauke ta re da bud'e idanunta ta soma kalle-kalle. Wani irin tsumamman kuka ta fashe da shi. Cikin sauri Barr Fu'ad ya kama hannun ta su ka fita daga d'akin su ka koma reception, daddy da Hajiya Mansura bi ye da su a baya. Lallashin Fanan Barrister ya dinga yi ta na kuka sosai. Daga k'arshe Alhaji Usman ya umarci Fu'ad d'in da ya mai da Fanan da Hajiya Mansura gida. Bayan ya kai su gida ya shiga bin diddigin ta inda Binty ta k'one. Gaba d'aya ma'aikatan gidan ya tattara ya na tambayan su akan su fad'a masa gaskiya ta yaya aka yi Binty ta k'one. Rantse-rantse su ka dinga masa har da kuka ta re da fad'in su ba su san yarda aka yi ta k'one ba. Kwafa ya yi ta re da sallamarsu su ka bar wajan. Bintoto mai kula da abincin kaji da ake kiwo a can bayan gida kuwa, ta ga san da Binty ta fito da gudu daga d'akin Suhail ta na soshe-soshen jiki ta na ihu, sai dai ka min ta k'arisa wajan Binty, Suhail ya fincikota ta fad'o d'akinsa kasancewar ya bi yo bayan Bintyn ne. Sai da ya wanka mata mari ka min ya mata gargad'i mai kyau akan idan har ta saki ta shaida wa wani cewar Binty daga d'akin shi ta fito to sai ya kashe ta. Kuma sosai Bintoto ta razana da maganar Suhail d'in don ta san wanene shi. Shine d'an iskan namijin da ya lalata rayuwarta wajan fara saninta a matsayin d'iya mace, kuma har gobe bai dai na lalata da ita ba. Wata rana ma a d'akin na shi ta ke kwana, ya kile ta kuma ya yi amfani da ita. Idan ma har ta sake kamin zuwan ta d'akinsa ba ta yi wanka ba, ranar sai ya mata mugun duka har da su fasa hanci kamin ya yi amfani da ita ta k'arfi tsiya, don har ta duburanta ya ke naiman ta, ya kai idan har ba amfani ya yi da ita ta duburanta ba, ba ta kwanciyar hankali, don ji ta ke kamar a na tsungumin duburan na ta. Duk wanda ya ga leb'an Suhail sai ya gudu saboda yadda ya yi wani irin bororo ta re da kumbura. Sai ya koma jawo da face marks.

.............Anna dai a asibiti ta kwana, don ba ta yadda wani ya tsaya akan Binty bayan ita ba. Fanan kuwa da sassafe ita ma ta dawo asibitin, dama shi Fu'ad ba shi ya bar asibitin ba bayan ya dawo sai sha biyu da re, shi ma sai da wata nurse ta zo ta masa magana. Binty ba ta farfad'o ba sai goma na daren washa garin da aka kawo ta. Kuma ta farka ba ta jin ko wani irin ciwo a jikinta sai kan ta da ke d'an sarawa. Babu abunda ya baiwa Anna matuk'ar mamaki, sai fatan Binty da ta koma sumul kamar ba bu abunda ya tab'a tab'a jikin na ta. Su kan su nurses da doctor mamaki su ke yi matuk'a, domin ko kusa ba su bata samun sauk'i nan kusa ba. Sosai ta gyare, idan ta na hira da Fanan ma ba za ka d'auka ita ce mara lafiyar da aka kawo rai hannun Allah ba. Anna ta tambaye ta yadda aka yi ta k'one. Ganin yadda ya Fu'ad da ita kan ta Anna su ka d'au zafi ne, shiyasa ba ta fad'i abunda Fu'ad ya mata ba. Sai ce ma su ta yi ta fito daga part d'in Hajiya Mansura ne ta soma jin k'aik'aci, ta na susawa shine ya soma yi mata azaba da rad'ad'i. Anna dai ta d'aura alamar tambaya akan Hajiya Mansura, haka shi ma Fu'ad, sai dai tun da ba su da wani hujja, haka su ka bar maganar. Kwanan su biyu aka sallamo su su ka dawo gida.

*_______________* .........Kwance ta ke a kan gadonsu ta na karanta wani novel da aka ba su da su ka siya jamb mai suna *INDEPENDENT* na *SARAH OLADIPO*, Fanan da ke gefen ta kuma ta na charting a wayarta. Wayar Binty ce ta soma fitar da sautin wak'ar p-square *I LOVE YOU*, jawo wayar ta yi, duk a tsammanin ta ya Fu'ad ne ko kuma k'awayanta na school, amma sai ta ga *MR RIGHT* a jikin screen d'in wayar. Wurgi ta yi da takardar hannuta ta re da fad'in, "Wayyo Allah, na shiga uku. Wallahi ya kira. Sabrin ya kira ni". Fad'in Binty ta re da toshe bakinta ta na kallon wayar har ya gama ringing ba ta d'aga ba. Tsaki Sabrin ta yi ta re da fad'in, "Wallahi Binty ki na da matsala, ya ki ka haukace a kan namiji lokaci d'aya haka? Ki fa natsu wallahi kar ya ga ne yadda ki ke son shi haka ya miki wulak'anci. Tom ni dai ba ruwana". Ka min Binty ta yi magana wayar ta sa ke k'ara, kallon Sabrin d'in ta yi ta re, "Ya sa ke kira wallahi. Yanzu d'auka zan yi?". "A'a barin shi za ki yi ya yi ta ringing. Shirme kawai. Dalla pick the call, kuma Sam kar ki nuna kin ga ne shi. Ki ja masa aji ku ma ki natsu". Fad'in Sabrin ta na hararar ta. Binty har da wani gyaran murya ka na ta d'auki wayar da ya ke gab da tsinkewa. "Who's on the line please?". Binty ta fad'a cikin lankwashashiyar muryar da ba ta ma san ta na da ita ba. "Ki na magana da Yousouf Muhammad Ahlam, wanda su ka had'u da shi a shop rite". Fad'in Yousouf cikin wani irin voice d'in shi mai sumar da y'an mata. Binty ba ta san sanda ta damk'i hannun Sabrin ba ta re da zaro idanuwa. Don jin muryan shi ta yi kamar busar sarewa. "Ki natsu kar ya raina ki fa". Sabrin ta fad'a a cikin kunnan Binty. "Gaskiya ban ga ne ka ba". Fad'in Binty har da wani d'an ya mutsa fuska kamar ya na ganin ta". Dariya ya yi mai d'an sauti wanda ya kusa tsayar da gudun numfashin Binty ka na ya ce, "Wanda mu ka bangaji juna har kayan da ke hannun ki su ka watse, na kuma ce ma sistern ki ta ba ni ke in aure ki ka ji kunya ki ka guduuuu". Sai da ya ja kalmar gudu wanda sai da ta ji shi har zuciyar ta. "OK" Shine abunda Binty ta fad'a. "Kin ga ne ni kenan?" Fad'in Yousouf. "Kamar haka". Fad'in Binty ta re da juya idanuwa kamar ya na ganin ta. "Hmm, to ya ki ke, ya kuka koma gida?". Fad'in Yousouf. "Lafiya k'alau alhamdulillah". Binty ta ba shi amsa. "Ina y'ar uwar ki? Ki ce ina gaishe ta". "Za ta ji in sha Allah". Binty ta fad'i ta na kallon Sabrin. "To ki kula da kan ki, sai na sa ke kiran ki". Fad'in Yousouf ta re da katse kiran. Tsalle ta yi akan gadon ta re da fad'in, "Wallahi ya kira ni, ya kira ni Sabrin. Na rantse miki ina matuk'ar son shi". Binty ta fad'a ta re da rungume Sabrin. "Dallah matsa can sakarya". Fad'in Sabrin ta re da ture ta a jikinta ka na ta cigaba da fad'in, "Na dai fad'a miki ka da ki saki ya ga wannan rawan kan na ki". Turo baki Binty ta yi ta re da fad'in, "To na ji big sis".

..............flowers ne a hannunshi wanda bai san adadin yawan su ba. D'aya bayan d'aya ya ke jefawa a cikin dustbin d'in gefen shi ya na fad'in, "In bayyana, a'a ba yanzun ba tukun". Idan ya jefa d'aya sai ya fad'i (In bayyana) idan ya kuma jefa d'aya sai ya ce (a'a ba yanzu ba). Haka ya dunga yi har ya rage saura kwara d'aya a hannun shi, kuma kalmar da ya rage ya fad'a shine, (A'a ba yanzu ba). Kallon shi Jabir amininshi kuma abokin aikin shi ya yi ta re da fad'in, "Fu'ad ni ko idan da za ka ji shawara ta, ka bayyana tun ka min kwad'o ya maka k'afa. Wallahi yanzu an dai na raino, sai ka ga ma raino wani ya wafce ya yi gaba da ita, amma idan ka ji shawara". "Hmm ka ke ganin haka Jabir. Yarinyar fa a gaba na ta ke. Ko fita ba sa yi ta ina za ta had'u da wani da har zai hure mata kunne. In sha Allah Binty tawa ce. Don tun ta na y'ar shekara goma na ke son abata, kuma ko Anna ba ta san da hakan ba. Kawai ka ta ya ni da addu'a kawai". "Hmm, tun da haka ka ce, zan ta ya ka. Allah ya sa rabon ka ce". Fad'in Jabir. "Ameen dai aboki na". Fad'in Fu'ad.

................. *CANADA* ................. Sosai ta ke kuwa ta re da fad'in, "Julieby, I swear to God I'm tired of him, all I want is divorce. I can't live with him ever again. I'm going back to my parents house". Fad'in matar Peter John. Ajiyar zuciya Julaibib ya sa ki mai k'arfi ka na ya kalle ta ta re da fad'in, "Where is he now?". "Club". Ta ba shi amsa ka tsaye ta na share jinin da ke gangarowa daga bakinta sakamakon make ta da Peter John ya yi kafin ya fita night Club d'in da ya saba zuwa. Don ko kwana a gidan ba ya yi. "Stay in the house, don't go anywhere. Just wait for me I'm coming back in 30minutes". Julaibib ya fad'a ta re da fita daga parlourn zuciyar sa na zafi. Don ya na d'aya daga cikin abunda ya tsana a rayuwar shi, wato dukan mace, ko wulak'antata bayan ka rabo ta daga gidan iyayanta. Kai tsaye Club d'in ya nufa, wanda a tarihin rayuwar shi bai tab'a zuwa ba sai dai ya wuce wajan da mota.

Parking ya yi ta re da fitowa daga cikin motar ya na yamutsa fuska sakamakon warin giyar da ya doki hancin sa. Tsartar da miyau ya yi ta re da nufar cikin wajan Wajan na da girma sosai, gefe guda a wajan kwalaban giya ne mak'il a wajan. Ga y'an mata nan cike a wajan ba su da maraba da tsirara. Ba haske sosai a wajan kasancewar irin globe d'in nan mai launin green, blue da kuma ja. Sauti na ke tashi matan wajan na rawar rashin d'a'a a jikin mazajan wajan. Julaibib har kan shi ya fara sarawa saboda hayaniyar sautin da ke wajan da kuma shige da ficen mutane. Wata budurwa ce daga ita sai brezia da pant hannunta rik'e da kwalbar giya da cup ta nufo shi ta na karairaya. Hannu ta kai za ta shafo jikin sa ya yi saurin matsawa ta re da watsa mata wani irin kallon da ba ta san lokacin da ta juya ta bar wajan ba har ta na hard'ewa saboda tsinin takalmin da ke k'afarta. Wajan wani da ya gani a gefe ya nufa ta re da masa magana. Sama mutumin ya nu na masa. Julaibib ya bi hanyar da mutumin ya nu na masa, duk in da ya bi sai ya kauce saboda yadda mata ke kawo jikinsu. Wani wajan ya shiga wanda girman shi bai wuce wa d'akin ba, VIP ne, mata ba su fi su goma ba, sai Kazan su takwas, wak'ar Rihanna ne ke tashi wata y'ar tsamurarriyar baturiya ta na rawa a gaban Peter John ta re da shafo jikinsa ta na kuma bin wak'ar kamar haka, 🎻 *Work, work, work, work, work, work* *He said me haffi work, work, work, work, work, work* *He see me do mi dirt, dirt, dirt, dirt, dirt, dirt* *so me put in work, work, work, work, work, work* *when you ah gon' learn, learn, learn, learn, learn, learn?* *Me nuh care if him hurt, hurt, hurt, hurt, hurt*🎻 🎻 *Dry, me ah desert him* *No time ti have you lurking* *Him ah go act like he nuh like it* *You know I dealt with you the nicest* *Nuh body touch me you nuh righteous* *Nuh badda text me in crisis* *I believed all of your dreams, adoration* *You took my heart and my keys and my petience* *You took my heart on my sleeve for decoration* *You mistaken my love for you for foundation* *All that I wanted from you was to give me something that I never had* *Something that you've never seen* *Something that you've never been,mmh* *But I wake up andd act like nothing's wrong* *So me put in work, work, work, work, work, work*🎻 To she kunnansa ya yi saboda yadda wak'ar ke hargitsa masa kwakwalwa ta re da nufar wajan da Peter John ya ke ya jawo hannunsa, amma kasancewar a bige ya ke, sai kallon Julaibib d'in ya yi ta re da fad'in, "Heyyy Julieby, let go of my hand. Or do wanna join me?". Ya fad'a a bige. Mari Julaibib ya watsa masa ta re da fad'in, "Let go home now". Idanunshi har ya rine. Kwalbar giyan da ke hannun karuwarsa Julie ya fizge ta re da kai wa Julaibib du ka da shi. Cikin azama Julaibib ya rik'e kwalbar ta re da hankad'a sa ya fad'i. Saboda zuciyar da ya kawo masa wuya, idan har ya cigaba da tsaya wa a wajan to lallai za a yi b'ar na. Kawai sai ya juya ta re da barin club d'in gaba d'àya ya za motar shi sai gida. Cikin daran ya shiga net ya duba ko akwai flight d'in da zai ta shi zuwa Nigeria sai ya ga ba bu sai na Dubai, booking flight d'in da zai ta shi zuwa Dubai d'in ya yi. Ya na gamawa ya soma harhad'a kayanshi don bai fi saura mintuna arba'in ba jirgin ya ta shi. Da ma ya gama tsara komawar shi k'asar shi Nigeria ji bi, saboda wannan abun da ya faru ya b'ata masa rai shiyasa ya ke son barin k'asar. Ya na zuwa airport ana kiran passenger. Cikin tafiyar shi sauri-sauri kuma cikin natsuwa ya soma tafiya. Ko da ya shiga jirgi air phone ya saka a kunnan sa ya na saurara karatun Al'qur'ani. Su na sauka a Dubai, hotel ya nai ma ya kama, ka na ya yi wanka ta re da kwanciya kasancewar bacci ya ke ji sosai. Don gobe ne ya ke son ya sauka a k'asar Nigeria bayan shekaru masu yawa.

*NIGERIA* "Anna, Ya Bibi ya min text d'azu wai gobe zai diro Nigeria, abunda ya sa ban kira shi ba, na san tun da ya min text bai son magana ne kuma ma a wajan su dare ne". Fad'in Ya Fu'ad. Wani sanyi Anna ta ji na ratsa zuciyar, don fisabillahi duka y'ay'anta ta na son su, amma Julaibib ne favourite d'in ta duk da ta na danne hakan a gaban sauran y'ay'an amma su kan su sin shan shak'uwar ta daban ce. Don takanas Anna na yankar ticket tun ya na *US* ta je wajan shi har ya koma *CANADA* ta na ziyartar shi ta yi kwana uku ta dawo. Don shi Alhaji Usman bai ci ka samun lokaci ba saboda kasuwancin sa, sun fi yin waya a kai a kai. "Kira min gaba d'aya ma'aikatan shashin nan right now". Anna ta fad'a farin ciki kwance a fuskan ta. "Aifa, su shalele za'a dawo. Har na ji tausayin su Binty, don fa Annan su za ta aje su gefe". Fad'in Fu'ad ta re da nufar maid quarters. Anna kuma wayarta ta d'auka ta kira Binty a waya ta ce su sauko k'asa ita da Fanan. Ta re su ka sauko, Binty ta kalli Fanan ta re da fad'in, "Me y'an aiki su ka yi wa Anna yau a kan ta ra su du ka a parlour?". "Ta re fa mu ka sauko, ma ji idan mu ka k'arasa". Fad'in Fanan. Ganin fuskan Anna k'umshe da farin ciki ya sa su ka ga ne ba laifi y'an aikin su ka yi ba. Nai man waje su ka yi kusa da Anna su ka zauna. Binty har da kwanciya a jikin Anna. "Hhuhmmm, yarinya na yau ne kawai, daga gobe idan ma ance ki zo kusa da Anna da k'afarki za ki gudu". Fad'in Barrister Fu'ad. "Anna kin ji shi ko, ba ni ce autares d'in ki ba. Wai haka ne abunda ya ce?". Fad'in Binty ci ke da shagwab'ar da ya k'ara mata kyau. "Rabu da shi kin ji, tsokanar ki ya ke yi. Wa ya isa ya hana ki zuwa jikin Annan ki". Gwalo Binty ta yi Wa barrister Fu'ad, shi kuma ya yi dariya ta re da kwafa. "Na ta ra ku anan ne domin in shaida muku babban d'a na ya na kan hanyar shi gobe in sha Allah, na san wasun Ku a nan sun san shi, wasun kuma ba su tab'a ganin sa ba. To magana ta gaskiya ya na da wani murd'ad'd'an hali. Sam ba ya san hayaniya da yawan magana a kan shi. Ga wanda bai san shi ba, zai d'auka kyamar mutane ya ke yi ko kuma shi d'in mugune saboda ya na sama da ku, amma ga wanda su ka san shi kuma su ka iya zama da shi, za su ga ne kyawawan halayen shi na wai dan ya na d'ana ba. Sannan ya na da matuk'ar zuciya sosai wanda a wasu lokutan ni kai na da na ke mahaifiyar sa, ba na iya shawo kah cikin sauk'i. So dan Allah ko wacce ta kiyaye ta tsira da aikinta". Fad'in Anna ta na kallon y'an aikin na ta. Cike da girmamawa su ka ce, "In sha Allah za mu kiyaye Hajiya". "Za Ku iya tafiya". Fad'in Anna. Ga ba d'aya su ka mik'e su ka fice. "Annah, ya Bibi ne zai dawo? Wayyo Allah dad'i kuma haushi". Fad'in Fanan. "Mi ye dad'in, kuma mi ye haushin?". Anna ta tambaye ta. "Anna dad'in na yi shekaru ban ga ya Bibi ba. Haushin kuma zai hana mu sak'at a ciki n gidan nan. "Ai abun ba wuya, sai Ku kiyaye shi". Fad'in Anna. Ita kuwa Binty hankalinta ma ya bar wajansu ya koma kan screen d'in wayarta ta na karanta daddad'an text d'in da Yousouf ya turo mata. Don kafin ya kira ta ya na jimawa, sai dai fa kullum sai ya mata dad'ad'an texts, na safe da ban, na rana da ban na dare da ban. Ku ma ba ta tab'a yin k'urin yi masa replay ba sai yau kawai ta ji ta na son ta yi masa. Sau uku ta na rubutawa ta goge, a na hud'un ne kuma ta daure ta tura.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull