Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 21

Ba ni da gata - Chapter 21

Ba ni da gata Chapter 21: Ba ni da gata Chapter 21. *MATAR SAYYADEE* 🌹 *41-42*🌹 .............Wani ihu mai k'arfi ta saki sakamakon jikinsu da ya had'u…

3,241 words

*MATAR SAYYADEE* 🌹 *41-42*🌹 .............Wani ihu mai k'arfi ta saki sakamakon jikinsu da ya had'u waje d'aya da ya haifar mata da wani azaba a saman fatanta kamar ana d'iga mata ruwan dalma. Hannun shi ya saka ta re da toshe mata baki, d'ayan hannun Ku ma ya soma yawo da shi a jikinta. Binty ba ta san sanda ta saka duka k'arfinta ta cire hannun shi a kan bakinta ba ta re da k'ara sakin wani k'aran. Saboda the more hannun shi na tab'a jikinta, the more azabar da ta ke ji a jikinta na k'aruwa. "Hasbunallahu wani'imal wakeel, inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un. Dan girman Allah ka dai na tab'a ni. Fatan jikina na k'onewa. Na shiga uku Anna ki cece ni". Binty ta fad'i da k'arfi, amma babu mai jin ta saboda d'akin a rufe ya ke, ku ma ko za ta kwana ta na ihu babu mai jin ta. Mari ya d'auke ta da shi ta re da fad'in, "Uban baban ki, wallahi ko wa ya tsaya miki yau sai na d'and'ana roman ki, ba zai yu ki zauna a gidan nan mahaifi na na kula da ke ba, ba dangin iya ban mori wannan kyakkyawan jikin na ki ba. So gwara ma ki tsaya mu yi cikin jin dad'i, in ji dad'i ke ma ki ji". Fad'in Suhail ya na k'ok'arin farke rigar jikin na ta. Wani irin nin kin azaba ta ke jin a jikinta duk sa'adda ko farcensa ne ya tab'a jikinta. Bakin shi ya kai zai had'e da nata ta yi wani irin nishin azabar da ta ke ji ta re da wani irin huci wanda Suhail bai san sanda ya yi k'undun bala ya fad'o daga kan gadon ba, sakamakon hucin da ya fito daga bakin ta ya tab'a leb'an shi, sai ya ji kamar kyasta masa wuta aka yi a kan leb'an nasa, don har wajan ya tashi ya yi wani irin bororo kamar ya k'one. Ita kuwa Binty da ta ga ya d'aga ta ya koma gefe, wani irin tsalle ta yi ta sauko daga kan gadon ko hijjab d'in ta da d'an kwalinta da ke yashe a k'asan d'akin ba ta yi ba ta fita ta bud'e d'akin, da gudu ta yi side d'in su ta na kuka ta na soshe-soshe ta re da kwala kiran sunan Anna. Da gudu Anna da tun d'azu ta dawo ta zauna a parlour ta na jiran dawowar Binty ita da Barr Fu'ad da ke gefen Anna ya na cin apple su ka fito. Fanan da ke kitchen har ta riga su isa wajan da Bintyn ta ke ta re da ruk'o su. "Anna na shiga uku, Anna na shiga uku. Bayana, jiki na, Anna k'onewa na ke yi ki taimake ni". Fad'in Binty ta re da kwace jikinta a jikin Fanan d'in ta na wani irin kuka ta re da birgima a k'asa. "Na shiga uku, Fu'ad taimake ni ka d'auko min ita ka kawo ta d'aki". Fad'in Anna hankali ta she. Da sauri Barr Fu'ad ya je in da Binty ta ke ta re da ciccib'arta. Aikuwa ta Ku ma tsandara wani uban k'ara sakamakon jikin Barr Fu'ad da ya had'u da nata jikin sai azabar ya k'aru. "Wayyooooo Annah mutuwa zan yi wallahi. Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, na shiga uku". Binty ta sa ke fad'i. "Anna muje asibiti kawai". Fad'in Barr Fu'ad ta re da nufar parking space hannunsa rungume da Bintyn da sai zamewa ta ke yi ya na sa ke rik'eta ta na fizge-fizge kamar mai shigar aljanu. "Muje kawai, ke Fanan ki koma ki kula da girki". Fad'in Anna ta re da nufar parking space. Da gudu-gudu Fanan d'in ta bi bayan Anna ta na kuka ta re da fad'in, "Anna dan girman Allah ki ba ri na ni Ku, wallahi ba zan iya natsuwa ba idan har ban san halin da Binty ta ke ciki ba". Ba ta re da Anna ta sa ke cewa komai ba ta bud'e gidan baya ta shiga, Fanan ma ta yi saurin shiga motar. Da gudu Barr Fu'ad ya motar su ka bar gidan. Wani irin gudu ya ke yi wanda ya wuce misali, amma saboda tashin hankalin da Anna ta ke ciki, ba ta iya kwab'a masa ba har su ka isa asibiti. Parking ma ba mai kyau ya yi ba, hakanan duk su ka fito gaba d'ayan su. Barr Fu'ad ya fiddo Binty da ke ta kuka a gaban mota. Jikin su na kuma had'uwa ta tsandara wani irin ihun da sai da ya zawo hankulan jama'ar da ke farfajiyar asibitin. Gudu-gudu Barr ya nufi cikin asibitin, aikuwa cikin sauri nurses su ka kawo wanna gadon gungura marasa lafiya Fu'ad ya d'aura ta akai. Da shi aka gungura ta zuwa d'akin taimakon gaggawa, sai da su na zuwa bakin k'ofar aka hana Barr Fu'ad shiga. Anna da Fanan su ka k'araso in da ya ke hankalin su gaba d'aya a ta she. Babu wanda ya iya cewa kowa k'ala a cikin su. Idanuwa Barr Fu'ad ya kad'a ya yi jazur, ya yin da Annah sai share hawaye te yi. Fanan kuwa riris ta ke yin kuka. Sai da su ka kwashi awanni biyu a kan ta, ka na su ka fito da ita su ka kai ta d'akin hutu amma sun hana kowa ya shiga. Doctor ne da ya fito ya ce su bi shi office. Don tashin hankali gaba d'ayan su ka bi shi office d'in. Ko zama sun kasa yi, sai da doctor ya nu na masu wajan zama ka na su ka zauna. Gyaran murya doctor ya so ma yi ta re da fad'in, "Amma garin Yaya ta k'one haka a jikinta? Man gyad'a ne ya fallatsan mata ko kuma gobara ce ta tashi ta soma cin jikinta aka kawo mata d'auki?". Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Anna, Barr Fu'ad da kuma Fanan. Can dai Anna ta ce, "Wallahi doctor ba mu san mai ya same ta ba, ihunta kawai muka ji ta na fad'in jikinta na k'onewa". Ajiyar zuciya doctor ya sauke ta re da fad'in, "To Allah ya kyauta, amma dan Allah mu rik'a saka idanuwa akan yaran mu, domin idan wani abu ya same su, mune da asara. Sannan yanzu dai munyi iya abunda za mu yi, sauran mun barwa Allah, amma magana ta gaskiya, jikinta ba bu kyawun gani don duk ya sale ya yi bororo alaman k'una ce sosai ta yi". Fashewa da kuka Fanan ta yi har da shashshek'a. Anna da Barr Fu'ad kuma salati kawai su ka dunga yi, don Anna jikinta har wani rawa ya ke yi ta re da tunanin waye ya k'ona mata d'iyar. Kuma k'udurta a ran ta sai ta d'auki tsattsauran mataki akai. Bayan sun fito daga office d'in ne, Barr Fu'ad ya kalli Anna ta re da fad'in, "Wallahi tallahi wannan karan ba zan hak'ura ba, sai mun shiga kotu da ko ma wanene wanda ya aikata mata wannan d'anyan aiki". "Kwarai ina bayan ka 100%, ba zai yu a kashe y'ar mutane da aka bar min amana ba. Ga shi ni saboda tashin hankali na manta da waya ta a gida balle in kira Kandala in sanar mata da halin da y'arta ta ke ciki". Fad'in Anna. "To ba ri mu koma gidan ni da Fanan, sai mu harhad'o abubuwan da zamu buk'ata a nan d'in, daga nan sai mu tawo da wayar ta ki". Fu'ad ya fad'a. "Hakan ya kamata, amma yanzu ga ban wayar ka, ko kuma kira min baban ku in shaida masa muna asibiti". Fad'in Anna. Wayarsa ya fiddo ta re da dailing numbern mahaifin na su, ya na soma ringing ya mik'a mata wayar. "Assalamu alaikum, the great Barrister ya aka yi ne?". "Ameen wa'alaikumussalam, ba shi ba ne ni ce". Hankali ta she Alhaji Usman mai rabo ya ce, "Lafiya Ummu Julaibib?". "Da sauk'i dai kam. Yanzu haka muna asibiti Binty ta k'one". Fad'in Anna. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ba Fu'ad wayan yanzu". Fad'in Alhaji Usman mai rabo. Mik'awa Fu'ad wayan ta yi. Karb'a ya yi ta re da d'aurawa a kunne. "Ka na ji na? Ka yi min text d'in address d'in asibitin yanzu ga ni nan zuwa". "OK dad". Fad'in Fu'ad ta re da yanke wayar in one minute ya tura maka address d'in ta re da kallon Fanan da ke ta kuka har fuskan ta ya canza kala ta re da fad'in, "Muje gida mu d'auko abunda ya kamata mu dawo". Ya na gama fad'in haka ya yi hanyar waje ta ni sa abaya ta na sharar hawaye. Bayan fitar su ne wata nurse ta zo wajan Anna ta re da shaida mata za ta iya shi ga in da Bintyn ta ke, amma kar ta yi hayaniya a kan majinyaciyar. Jiki a mace ta mik'e ta yi wajan d'akin da aka aje Bintyn. A hankali ta tura k'ofar ka na ta shiga. Binty lullub'e ta ke da blue d'in zani tun daga k'afarta har wuyar ta, kuma a ruf da ciki ta ke. K'arasa ta yi wajan hawaye na d'igowa daga idanunta ta d'aga zanin. Wani irin ja baya Anna ta yi ta re da zaro idanuwa jikinta na wani irin b'ari. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Allahumma arji'ini fi musibati, aklifni khairan minha. La'ila ha illallah muhammadar rasulillah. Mai zan ga ni haka Binty". Anna ta fad'a ta re da rushewa da kuka ta yi sauri to she bakin ta saboda kar k'arar ya fita. A karo na biyu ta k'ara zuwa ta d'aga zanin nan, tun daga k'ugunta har kafad'unta ya d'aye alamar k'una, ya yi wani iri ba kyawun gani. Hannunta da dama kuwa, gaba d'aya fatan ya sale, gyefan wuyanta ma haka. Sai bayan sandar k'afarta da ya yi wani irin bororo. Daga ita sai wani d'an gajeran wando iya cinyarta inda k'unan bai tab'a ba. Sosai Anna ke kuka ta na k'ara jin wani tururi na fitowa daga k'asan zuciyar ta re da k'ara d'aukar alwashin sai ta d'au fansa ba za ta kyale wannan ba. K'aran k'ofa ta ji ana turowa a hankali, saurin juyawa ta yi idanuwanta su ka sauka akan na Alhaji Usman mai rabo da zuwan shi kenan asibitin. Ai ta na ganin shi sai rauninta ya k'aru ba ta san ta fashe da kuka mai sauti ba. Da sauri Alhaji Usman mai rabo ya k'ariso ta re da jawo ta jikinsa ya soma lallashinta, sai da ya ga ta d'an natsu, ka na ya zaunar da ita akan kujera ta re da juyawa ya kalli inda Binty ta ke a kwance, kasancewar Anna ba ta rufe jikin Binty ba, hakan ya baiwa Alhaji Usman mai rabo ganin halin da ta ke ciki. Ba k'aramin dauriya ya yi ba wajan shanye fargabansa ba, domin ka da Anna ta k'ara shiga tashin hankali. K'arasawa ya yi ya rufe jikin ta re da kallon Anna ya ce, "Garin Yaya ta k'one haka Ummu Julaibib?". D'ago da jajayan idanuwanta ta yi ta re da fad'in, "Ni ma wallahi ban sani ba, na dawo daga wajan Rakiya sai na tambayi ta na ina don ban ji motsinta a kitchen ba, don idan na fita rige-rige su ke yi ita da Fanan wajan yi min oyoyo, sai na tambayi Fanan ta na iya sai Fanan ta ce min Mansura ce ta kirata ta na can part d'in ta tun d'azu. To bayan minti sha biyar mu na zaune da Fu'ad da shi ma bai jima da shigowar ba, sai kawai muryanta ta na ihu ta na kiran sunana ta na fad'in jikinta na k'onewa". Anna ta k'arisa maganar ta na kuka. Shuru Alhaji Usman mai rabo ya yi na y'an dak'ik'u ka na ya fiddo wayarsa daga aljihunsa ta re da dialing numbern Hajiya Mansura.

"Ke Fasila kin tabbata da abunda ki ke fad'amin kuwa? Lafiya fa ta bar d'akin nan". Fad'in Hajiya Mansura. "To wallahi dai hajiya yanzu haka sun yi asibiti tun d'azu ma, ina lek'e ta window ba ki ga yadda yarinyar ta ke yi ba kamar mai tashin aljanu". Hankali Hajiya Mansura ya tashi, ba ta san lokacin da ta mik'e daga kan gadon ba ta re da nufar wardrobe d'in ta ta d'auko doguwar riga ta saka ba. Wayar ce ta soma ringing, Fasila ta d'auki wayar ta re da mik'amata. Hajiya Mansura kuwa ganin wanda ke kiranta a wayar sai da gabanta ya fad'i, amsa wayar ta yi ta re da karawa a kunnanta. Ka min ta yi sallama muryan Alhaji Usman ya daki kunnanta, "Mai ya sa mi Binty a part d'in ki? Mai ki ka mata?". "Binty kuma? Mai ya same ta Alhaji?". Hajiya Mansura ta fad'a kamar ba ta san abunda ke faruwa ba. "Ina tambayar ki, ki na tambaya ta. To ta k'one a jikinta, kuma daga part d'in ki ta fito ta na ihun jikinta na k'onewa. Ki fad'a min mai ki ka yi wa y'ar mutane?". Fad'in Alhaji Usman mai rabo rai b'ace. "Na rantse da girman ubangiji Alhaji ban mata komai ba. Wallahi ban san mai ya same ta ba. Lafiya ta bar part d'ina. Ku na wani asibiti ne?". Fad'in Hajiya Mansura. K'it ya katse wayarsa ta re da kallon Anna ya ce, "Ta yi rantsuwa da girman ubangiji ba ta san abunda ya sa mu Binty ba, kuma wai lafiya k'alau ta bar part d'inta. Shuru kawai Anna ta yi, don ita fa zuciyarta Hajiya Mansuran ta ke zargi, amma tunda ga Binty da ranta ba ta mutu ba, idan ta farka za ta fad'a masu ko ma menene ya faru da ita.

Hajiya Mansura kuwa, Alhaji Usman na katse wayar ta figi hijjab d'inta ta re da fitowa daga dak'in hankali ta she. Don har ga Allah ta ji zan can k'unan da aka ce Binty ta yi har cikin zuciyar ta, don a wajanta idan wani abu ya sa mu Binty kamar ita ya sama kasancewar ta matar da ta ke so ta aura ba za ta so wani abu ya tab'a lafiyar jikinta ba. Don ba ta tunanin ko Anna ta kai ta son ta. Kicib'is su ka yi da Barrister Fu'ad da Fanan sun dawo kwasan abunda za su yi amfani da shi a asibiti. "Fu'ad ashe abunda ya faru kenan? To garin yaya ta k'one?". "Muma ba mu sa ni ba, an dai ce daga part d'in ki ta ke". Fad'in Barr Fu'ad a dak'ile don ita ce first suspect d'in shi. "Wallahi tallahi Fu'ad, Binty lafiya k'alau ta fito daga part d'ina. Ban san a ina ta k'one ba". Fanan da ba ta tsaya sauraran su ba, ciki ta shiga domin soma harhad'o duk wani abunda za su yi amfani da shi a asibitin. "Idan ta farka, ko ma wanene ya mata haka za muji". Fad'in barrister Fu'ad d'in ta re da nufar part d'in Anna. Da sauri-sauri ta biyo bayan shi ta re da fad'in, "Wani asibiti ta ke ne? Ina son zuwa yanzu". "Mu ma kaya muka zo d'auka, yanzu za mu koma asibitin". Fad'in Fu'ad. "OK to ba ri na jira ku sai mu koma ta re". Hajiya Mansura ta fad'a ta re da bin bayan Fu'ad da har ya shige d'aki. Cikin mintuna goma har Binty ta gama had'a komai. Barr Fu'ad ya taimaka mata da wasu kayan su ka fito Hajiya Mansura na biye da su a baya. A both su ka sa ka kayan, Fanan ta shiga gaba, Hajiya Mansura ta shiga bayan mota. Barrister Fu'ad tuk'i ya ke yi amma gefe guda tunani ya ke ta yadda zai yi shari'a da ko ma uban waye ya k'ona masa sanyin idaniyarsa. Wayarsa ce ta yi ringing, kallon screen d'in wayar ya yi da ke gefen sa. *Yaya Bibi* ya ga ni a jikin screen d'in. Duk da halin da ya ke ciki, sai da ya yi murmushi ta re da picking wayar ya kara a kunnansa ta re da fad'in, "Hello ya Bibi ina wuni?". Daga d'ayan b'angaran Julaibib ya ce, "Ina wuni a k'asar ku kenan, nan ko seven na safe bai yi ba". "Ohhh hakane fa, mancewa na yi ai". Fad'in Fu'ad. "Mai ya sa mu wayar Anna? Na kira ya fi sau uku a'a d'aga ba." Fad'in Julaibib cikin sanyin muryan shi. "Wallahi Anna dai na asibiti Binty ba lafiya, ga wayar yanzu muka dawo gida mu ka d'auko mata". "Wacece haka kuma?". Fad'in ya Bibi. "Kullum dai na kira sunan ta sai ka tambaya, yarinyar da Anna ke rik'e wan nan fa". Fad'in Fu'ad. "Allah ya sawwak'e". K'it ya kashe wayar. Ajiyar wayar ya yi a gyefe ta re da k'ara gudun motar. Su na isa asibitin ya yi parking ta re da fitowa. Fanan ma ta fito. Hajiya Mansura kuwa har ta yi gaba duk da ba sanin d'akin ta yi ba. "Daddy ya zo". Fad'in Fanan. "Kallon ta barrister ya yi ta re da fad'in, "Ya aka yi ki ka sani?". Barrister ya fad'a ta re da fiddo kayan da ke both. "Ga motar shi can, fad'in Fanan ita ma ta saka hannu su na fito da kayan ciki. Rufe both d'in ya yi ta re da kallon motar daddy ka na su ka nufi cikin asibitin. A tsaye su ka taras da Hajiya Mansura ta na nai man d'akin da aka aje Bintyn. "Ga d'akin can". Fad'in Fu'ad ya na nunawa Hajiya Mansura da hannu. Ta na ga ba su na bi ye da ita a baya. Ita ta tura k'ofar dai-dai lokacin da nurse ta d'aga zanin da aka lullub'e jikin Binty za ta shafa mata magani. Zaro idanuwa Hajiya Mansura ta yi, ya yin da Fanan da ke biye da ita ta yanke jiki ta suma sakamakon arba da ta yi da k'onannan jikin Binty. Barrister Fu'ad kuma saura ka d'an ya kai k'asa saboda kad'uwa. Cikin azama Daddy ya rik'o Fanan da ba ta ida kai wa k'asa ba amma ta suma. Barrister Fu'ad kuwa hawaye su ka soma saukowa cur-cur a idanunsa. Ya yin da Hajiya Mansura ta fashe da kuka ta re da k'arisawa in da Binty ta ke a kwance......

*PAID BOOK 08128755583* 🌹 *43-44*🌹

*"AYYIRIRIIIIIII AHAYYEEEEE, IYEEEE NANAYEEEEEE,"*

*"TO FA!! MATAR SAYYADEE, MI KE TSALLE NE HAKA YAU NA GAN KI CIKIN FARIN CIKI DA ANNASHUWA HAKA SAI GUD'A KI KE YI KAMAR ANYI BAK'UWAR AMARYA? SANNA KUMA GA Y'AN DUBU-DUBU NAN KI NA K'IRGAWA A HANNUN KI*"

*KEEE TAKWARA! IDAN BA KI YI BA NI WAJE. AI NI YANZU WALLAHI SHARRR, Y'AR GABAN GOSHI NA KE WALLAHI*"

*" NA GA ALAMA WALLAHI, JIYA BAN GAN KI A TSAKAR GIDA BA, SAI DOGON WUYA DA Y'AN WAK'E-WAK'E NA KE KO ZA KI JI MURYA TA KI FITO, AMMA SAI NA JI MULUNKWI*".

*AI TAKWARA TUNDA MAMAN KHAIRAT TA KAWO MIN WANNAN SHU'UMIN HUMRAN NA WUCE RAINI, KE DAI ABUN BA'A MAGANA SAI KIN GWADA KAWAI*.

*HABA! HABA MATAR SAYYADEE, ASHE HAKA ZAMAN TA RE YA KE, KI SA MU ABUN ARZIKI HAKA AMMA SAI KI SHA RE AMINIYAR TA KI KI YI LIKIMO A D'AKI KU NA SAN SOYAYYA DA MAI GIDA*.

*"HABA TAKWARA, MAI ZAN JI NA K'ARUWA A DUNIYAR NAN DA BA ZAN FAD'A MIKI BA KE MA KI K'ARU, AI SHIYASA NA BUGA GUD'A DON KI JI KI FITO IN SHAIDA MIKI ABUN ARZIKIN*".

*"INA JIN KI AMINIYAR KWARAI, ZAYYANO MIN*".

*BA MA KE KAD'AI BA, SHELA ZAN YI HAR MAK'OTA SU JI DOMIN KO WACCE UWARGIDA DA AMARYA SU JI*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull