Ba ni da gata - Chapter 20
Ba ni da gata Chapter 20: Ba ni da gata Chapter 20. *_____________________* ............."Dan Allah Fanan ki yi sauri, wallahi na k'osa mu fita ka min Anna…
3,282 words
*_____________________* ............."Dan Allah Fanan ki yi sauri, wallahi na k'osa mu fita ka min Anna ta dawo ta ce ba za mu fita ba. Kin san fa ba nisa ta yi ba ". Fad'in Binty da ke tsaye a kan Fanan da ke kwalliya a jikin madubin d'akin na su. Sanye ta ke cikin atampa doguwar riga kamar maroon da toch of golden. Doguwar riga ce d'inkin zamani irin mai aljihun nan. Ba k'aramin kyau kayan su ka mata ba. D'aurin zamani, duk da nannad'e gashin ta da ta yi, sai da gashin ya fito ta k'asan d'aurin da ta yi. Sai dai ribom d'in da ta saka ta kama gashin, shi ya d'ago da d'an kwalin ta kamar ta yi irin ture ka ga tsiyan nan. Siririn gyale kalar maroon ne a k'afarta, sai flat shoe shi ma kalar maroon a k'afar na ta. Babu abunda ya fi d'aukar hanakali a jikinta kamar jan lallan da ke kan y'an yatsun ta da ya k'ara fito da kyawun hannun kasancewar ta farar mace. "Dan Allah one minute. Yanzu zan gama". Fad'in Fanan da ke shafa jan baki a leb'anta. Mik'ewa ta yi ta re da d'aukar gyalanta, ita ma irin shigar da ke jikin Binty shi ke jikinta. "Muje ka da ki cinye ni d'anya". Fad'in Fanan. Wayar ta da ke kan mirror ta d'auka ta re da fita Fanan na biye da ita a baya. Su na fitowa Hajiya Mansura ita ma ta fito za ta fita, kallon Bintyn ta ke yi from head to toes ka na ta ce, "Ina za ku je da ranar nan?". Ka min su ba ta amsa sai da su ka gaishe ta, ka na Fanan ta ce, "Za mu ce saloon ne, daga nan kuma za mu bi ya mu d'an yi shopping". "To Ku kula da kan ku. Ke idan kun dawo ki zo part d'ina ki same ni". Hajiya Mansura ta k'arisa maganar ta na kallon Bintyn. "To Hajiya". Fad'in Binty ta na kallon k'asa, don haka nan ta ji ta na mugun tsanar ta, shiyasa ko duk in da ta san za su had'u, ba ta bi ta wajan. Ganin sun fito, tuni driver ya d'auko mota ya nufo har in da su ke, kasancewar umarni Anna ta ba shi akan duk in da za su, idan har ba Ya Fu'ad ba ne zai fita da su, to ba ta yadda su fita su d'aya ba, ya kai su. Shiga motar su ka yi, saloon d'in su ka fara zuwa. Sun jima a wajan kasancewar gashin Binty na da yawa sosai. Ko da su ka fito su ka zo wajan mota, Kamale driver har ya soma bacci sai da su ka ta da shi. Daga nan shop rite su ka nufa. Wajan kayan shafa su ka soma zuwa kasancewar turare da kayan kwalliyan su sun k'are, kit kuma su ke so su sake had'awa. Bayan sun gama da nan kuma su ka koma wajan da su ka fi auki wato wajan kwalama. Juyowar da Binty za ta yi, idanuwan ta su ka sauka a kan shi. Gaban ta ne ya buga da k'arfi. Da sauri ta dafe saitin zuciyar ta da ke buga fat fat fat. Dogone sosai, irin kyakkyawan nan ajin k'arshe. Fari ne sosai don duk hasken fatan ta ya fi ta fari, ya fi kama da irin farin Indiyawa. Ya na da manya idanuwa da dogon hanci, bak'in shi k'arami irin wanda akewa lak'abi da pink lips d'in nan. Ga sajan da ya k'ara k'awata fuskan shi ta re da d'an gemu irin na gayun nan da ya aje bak'ik'k'irin. Ya na da dimple a both chick d'in sa wanda motsa bakin ya yi sai ya lob'a. Siriri ne amma ba irin can d'in nan ba. K'irjin shi a bud'e ya ke amma ba can sosai ba. Kasancewar ya na facing d'in ta ne shiyasa ta iya k'are masa kallo haka, amma Sam shi hankalin shi ma ba ya kan ta. "Uncle Yusuf chocolate please". Fad'in wata kyakkyawar yarinyar da ba za ta wuce 8 years ba ta fad'a ta na jan hannun shi. Kallan gefen da ta ke ya yi, Binty ba ta san lokacin da ta furta, "Hasbunallahu wani'imal wakeel. Wayyo Allah!". Ta fad'i hakane sakamakon side view d'in sa da ta ga ni, sai ta ga ya fi kyau idan ya kalli gefe. Chocolate ya d'auko ta re da mik'awa wannan kyakkyawar yarinyarta re da sakin mata murmushi. Yuuu Binty ta tafi za ta fad'i, Fanan da tun san da Binty ta k'urawa wannan bawan Allah idanu wanda ita kan ta ya tafi da imaninta ta ke kallon ta ta yi d'aurin taro Bintyn ta re da fad'in, "Haba sis kar ki ba da mu mana. Behave your self".........
*PAID BOOK 08128755583* 🌹 *39-40*🌹 ............."Fanan ki na ganin abunda na ke ga ni kuwa? Wallahi guy d'in nan ya had'u sosai". Fad'in Binty. "To ko za ki je ki masa magana ne? Tun da ba ki da aji. Idan rabon ki ne, ki na nan zai zo ya kula ki. Dan Allah ki nutsu". Fanan ta fad'a a d'an zafafe. Sai a lokacin Binty ta dawo hayyacinta ta re da shan mur ta kuma dai-dai ta natsuwarta. Amma har a wannan lokacin ba ta dai na satar kallon shi ba. Hannunta Fanan ta rik'e ta re da barin wajan su ka nufi wajan biyan kud'in abunda su ka saya. Bayan sun biya an saka masu abubuwan a leda, Binty ta na d'auka ta na mai addu'ar Allah ya sa ta sa ke ganin wannan mutumin ko sau d'aya ne ka min ta bar shop rite d'in. Juyawar da za ta yi su ka ban ga ji juna, sai da kayan da ke hannunta ya watse, shi kuma tsadaddiyar wayar da ke hannunsa ya sub'uce ya fad'i, a ta ke screen d'in wayar ta yi watsa-watsa. "Yah subhanallah!". Guy d'in nan ya fad'i ta re da saurin duk'awa ya soma tattaro mata kayanta da su ka watse. Fanan kuwa saurin zuwa ta yi ta d'aga ta ta re da fad'in, "Kin ga irin abunda na ke guje miki ko. Ai Gashi nan garin kallon sa kin fad'i. Ai sai ki ta shi". "Ni wallahi ba shi na ke kallo ba, karo mu ka yi ban san ya na baya na ba". Binty ta fad'a ya yin da ta ke mik'ewa kamar za ta yi kuka. Wannan guy d'in k'arasowa ya yi hannun shi d'auke da ledar kayan Binty, wannan kyakkyawar yarinyar na biye da shi a baya ta na shan chocolate d'in da ke hannunta. "I'm very sorry ma'am, hope you're okay". Fad'in guy cikin wata zazzak'ar muryan da ya sumar da Binty ta shiga bin bakin shi da kallo ba ta re da ta ce uffan ba. Tsungilin ta Fanan ta yi a cinya wanda shi ya dawo da ita cikin hayyacinta ta re da saurin fad'in, "I'm.... I'm okay. I'm very sorry too". Fad'in Binty cike da rawar murya ka na kuma ta mayar da duban ta izuwa ga wayarsa da ke ya she a k'asa a farfashe. Cikin sauri ta k'arisa wajan wayar ta re da d'auko shi ta ce, "Na shiga uku na fasa masa waya". "Ohhh kar ki damu, tsautsayi ne ai ba laifin ki ba ne ba". Fad'in guy d'in nan ya na sakin murmushi da ke k'ara bayyanar da bayyanan nan kyawun sa. Daga Binty har Fanan sakin baki su ka yi su na kallon shi, domin ba su tab'a tunanin za su ji Hausa a bakinsa ba. Duk a tunanin idan yaruka su ka wuce ukun nan, to ba su tsammanin ya na jin wasu yaran, wato English, Hindi ko Arabic. "Ku na mamaki ne? Ina jin hausa sosai kamar jakin kano. By the way, I'm Yusuf Muhammad Ahlam. Can I know yours?". Binty ta kasa magana, domin muryan shi ba k'aramin rikita ta ya ke yi ba. Guy d'in ya yi ne sosai. Fanan ce ta iya k'arfin halin fad'in, "I'm Fanan Usman mai goro, and my sister, Binty". "Very nice name. You all have beautiful name". Fad'in guy d'in. "No one Care's about mine? Hmm my name is Ayeesha Fairuz Ahlam, his youngest niece. I'm the last born". Kyakkyawar yarinyar nan ta fad'i ta na dariya. Kamannin su d'aya da wanda ya kira kan shi da Yusuf, ko ba ta fad'a duk wanda ya gan ta ya ga k'anwar sa ko y'ar sa. "Ohhh you're soo beautiful dear". Fad'in Fanan ta re da rik'e kuncin yarinyar. "I knew it". Fad'in yarinyar ta re da sa ka chocolate a bakin ta. Gaba d'aya dariya su ka fashe da shi har da Binty da ta kasa magana. "If you don't mind, can I drop you?". Fad'in Yusuf. "Ohh no, don't worry, we are with our driver, he's waiting outside". Fad'in Fanan. Murmushi ya yi wanda hakan ya kasance d'abi'ar sa ne ta re da kallon Binty ya ce, "Hey miss Beauty, can't you talk?". Kunya duk ta rufe Binty, duk sai ta daburce ta rasa mai za ta ce. "She's so beautiful, please can we take a salfie?". Fad'in Ayeesha. "Indeed she's beautiful. Please za ki ba ni ita in aure ta?". Fad'in Yusuf ta re da kallon Fanan. Binty kuwa ba ta san lokacin da ta kwasa da sauri ba ta yi hanyar waje gabanta na fad'uwa at the same time kuwa ta na jin wani dad'i na mamaye zuciyarta. Bud'e mota ta yi ta shiga, driver na mata magana ko sauraran shi ba ta yi ba. "Indeed she's beautiful. Please za ki ba ni ita in aure ta". Maganar Yusuf ya k'ara yi ma ta gizo a kunnanta. Dariya ta yi ta re da saka kan ta a tsakanin cinyoyinta. Kusan mintuna goma Fanan ta taho da kayan da su ka siya. Both ta bud'e ta re da saka kayan, sannan ta zagayo ta bud'e gidan baya in da Bintyn ke zaune ta re da rufo motar. Driver na ganin haka ya ja motar ta re da kallo baya ya ce, "Gida mu ka nufa, ko kuwa akwai wani wajan da za ku sake zuwa?". "Ah mun gama komai, gida mu ka yi". Fanan ta ba shi amsa. Kallon ta Fanan ta yi ta re da fad'in, "Juliet ta had'u da Romeo d'in ta". "Ban ga ne ba, mai ki ke nufi da hakan?". Fad'in Binty ta na maka mata hararar wasa. "Love at first sight ko? Na ga wannan. Wannan irin kasa control d'in kai haka, lallai Yusuf ya daki zuciyar ki lokaci guda. To ki kwantar da hankalin ki, domin shi ma ya fowler, ba kuma ba shi numbern ki, sai ku yi ta k'onewa, amma kuma kar ki sake Anna ko ya Barrister su sani, na san ba ki manta dukan da ya barrister ya wa wannan anacin da ya din ga biyo ki tun daga wajan saloon ba har cikin gidan nan. Kar ki manta ya Barrister ya ce ba yanzu za mu fara kula samari ba, kuma Anna ta goyi da bayan shi. Saboda secret love za ku yi kamin a ba mu dama". Ya mutsa fuska Binty ta yi ta re da fad'in, "I don't understand, ki na nufin kin ba shi number ta, to wa ya saki? Ni fa kawai burge ni ya yi ba wai son shi na ke ba. Kin b'ata min rai. Ai wannan jawo min zubewar aji za ki yi". Fad'in Binty har da wani shan mur. "Iyyyeeee, to ki sa ni bariki dai babu riba. Ki fad'a uban da bai san halin ki ba. Ke ni fa ko da d'uwawu ki ka yi magana sai na fahimci abunda ki ka ce bare na ga abu b'aro-b'aro. Maza ki kula da titi". Dariya Binty ta yi sosai ta re da fad'in, "Ban ga ne in kula da titi ba". "Eh saboda motoci mana". Fad'in Fanan ta na hararar Binty. Dariya Binty ta yi ta re da fad'in, "Wai dan Allah dagaske ya karb'i number ta?". "Ni ma ban sa ni ba". Fad'in Fanan ta re da kallon window. "Haba sister, dan Allah ki fad'a min mana. Na bar miki autan, yanzu ke ce autares d'in Annan mu". Harara Fanan d'in ta k'ara sakar mata ta re fad'in, "Bariki". "Ke dai kalmar bariki ta ka ma bakin ki. Dan Allah Sister ya ki ka ga guy d'in, ya had'u sosai ko?". Fad'in Binty. "Kamar saman alalen gwangwani kuwa". Fad'in Fanan ta na dariya. "Wallahi k'arya ki ke yi, sai dai idan ba za ki fad'i gaskiya ba. Amma Yusuf had'ad'd'an guy ne wallahi. Komai na shi mai kyau ne. Fuskan shi, tsayin shi, maganar shi, murmushin shi, kai infact everything". Ba ki sa ke Fanan ke kallonta ta re da fad'in, "Har yaushe ki ka san shi haka da za ki ce everything about him? Yaushe ki ka san everything d'in?". "Man ta kawai, amma sincerely speaking guy d'in ya yi over". Fad'in Binty. "Kar dai ki haukace". Fanan ta fad'a ta re da daukar wayar Bintyn da ke kan ciyarta ta yi kwafe numbern Yusuf a wayarta ta re da sakawa a wayar Bintyn ta yi mata saving da Mr Right ta re da mik'a mata wayar. "Ga shi nan na miki saving numbern shi, kin ga da ya kira kin san ko waye, saura ki yi shirme". Fad'in Fanan. Karb'ar wayar ta yi ta re da tsurawa numbers d'in idanuwa. Cikin minti d'aya ta haddace numbers d'in kasancewar special number ce. Labarin Yusuf su ka din ga yi har su ka kai gida. Cikin ikon Allah kuwa, har wannan lokacin Annah ba ta dawo ba.
...........Ko da su ka shiga d'akin su, sallar la'asar su ka yi kasancewar a hanya ta riske su. Bayan sun idar kuma su ka d'aura hirar Yusuf. Sai k'arfe biyar su ka sauko don d'aura girki saboda tun sa su ka kammala makaranta su ke girkin dare. Idan wannan ta yi yau, gobe wannan za ta yi, ko kuma su had'u su duka su yi ta re, haka Anna ta tsara masu. Su na kitchen Fanan na gyara kayan miya, Binty kuma na blending, Fasila ta shigo. Sai da ta fakaici idanu ta watsawa Binty harara wacce ba ta ma San ta na yi ba, ka na ta yi gyaran murya duk su ka juyo su ka kalle ta ta re da fad'in, "Aunty Fasila ke ce?". Hakan su ke kiran ta, kasancewar ta girme su kusan da shekaru biyar. Don ita za ta kai ishirin da uku, su kuma sha takwas gare su. "Autan Anna sannun ku da aiki". Fad'in Fasila ta na murmushi. "Yauwa aunty Fasila". Ga ba d'ayan su suka amsa. Fasila mai da duban ta ta yi izuwa ga Binty ta re da fad'in, "Binty Hajiya Mansura na kiran ki, ta ce ki zo yanzu". Zaro idanuwa Binty ta yi ta re da fad'in, "Na shiga uku! Wallahi na man ce ta ce idan mun dawo in zo in sa me ta". "To ai sai ki hanzarta yanzu ki je ki ji kiran da ta ke miki. Ba ri ni na taya Fanan mu yi aiki". Binty ta ce, "To aunty nagode". Ta fad'i hakane ta re da tara hannun ta a panpo ta wanke ka na ta goge hannun ta towel ta re da cire apron d'in da ke ji jikinta ta aje a wajan da ake rataye shi a nan kitchen d'in ka na ta fito daga kitchen d'in ta d'auki hijjab d'in ta da ke parlour ta saka ta fito ta yi hanyar part d'in Hajiya Mansura. Za ta iya rantsewa da Allah yau ne karo na hud'u shigowarta part d'in Hajiya Mansuran. Gwara ma part d'in Hajiya Huriya, kasancewar ta na da d'iya mai suna Sunaina, to su kan d'an shiga wajan don ita kan ta Sunaina irin d'abi'ar mahaifiyar ta gare ta na nai man kud'i. Ka na duba status d'in ba bu abunda za ka ga ni sai uban kayan kitchen da lesis da atampopi har da kayan yara da ta ke ordering d'in su idan mutane sun mata magana su na so sai a kawo mata ta ruwa, sea shipping. Ba bu kowa a parlour, sai y'ar aikin ta Wasila da ke goge dinning. Kallon ta Wasilan ta yi ta re da hararar ta k'asa-k'asa ka na ta ce, "Ki hau sama, ta na can ta ke idan kin shigo ki je ki same ta". Fad'in Wasila kamar ta na da cuta a mak'ogwaro. Ba ta re da Binty ta ce komai ba ta haura sama. Sai da ta yi knocking aka ba ta izinin shiga kamin ta saka kai cikin d'akin. Kwance ta taras da Hajiya Mansuran daga ita sai brezia da underwear, ga ta ba ka d'an, don Mansura irin shiirgegiyar matan nan ne kamar giwa. Kawar da kai Binty ta yi don ta ji kunya da ta ga Hajiya Mansuran a haka. "Ina wuni Hajiya?". Binty ta fad'a ba ta re da ta kalle ta ba. "Lafiya lau. Ya a ka yi na ce idan kun dawo ki zo ki same ni, amma ba ki zo ba. Ko Na'ima ta hana ki zuwa waje na ne?". Fad'in Hajiya Mansuran. Girgiza kai Binty ta yi ta re da fad'in, "A'a wallahi. Anna ma ba ta nan. Mancewa na yi da muka dawo shiyasa ban zo ba". Kallon Binty ta ke yi ta na jin kamar ta tashi ta rungumeta ta re da sauke sha'awarta. Ji ta ke wani irin wutar sha'awar Bintyn na taso mata tun daga kwakwalwarta. "Zo ki zauna a nan, wani d'an abu za ki min". Fad'in Mansura ta re da nuna mata gefen ta. K'arasowa Bintyn ta yi ta re da zama a wajan da Hajiya Mansuran ta nu na mata. Shafa bayan Binty ta yi ta re da fad'in, "Yarinya ta tubarkalla ki na da kyau mai d'aukar hankali, ina ma ki zamo suruka ta". Banbara kwai haka Binty ta ji maganar, wai suruka. Tur Allah ya kiyaye mai za'a yi da Suhail a matsayin miji. Duk cikin zuciyar ta ta yi wannan maganar. "Jiki na duk ya min tsami wallahi. Kin san jikin tsufa. Dan Allah massage na ke so ki min in ji dad'in jikin nawa". Hajiya Mansura ta fad'a ta na k'ara shafa bayan Bintyn. Binty ba ta kawo komai a ranta ba, don Annah ma ta na sa su ita da Fanan su danna mata jikin ta har k'afafu. Ruf da ciki Hajiya Mansura ta yi, ita kuma ta shiga danna mata jikin tun daga k'eyarta har k'afafunta. Tuni Hajiya Mansura ta soma lumshe idanuwa, kasancewar ta saka wani abu daban a cikin zuciyar ta, sai ta ke ji kamar Bintyn romancing d'in ta ta ke yi. Binty ta fi k'arfi minti talatin ta na yi was Hajiya Mansura massage. Sai da Hajiya Mansura ta gamsu don bala'i, ka na ta ce wa Binty ya isa ta re da kwararo mata godiya har da mata kiss a kumatu. Ita kuwa baiwar Allah ba ta kawo komai a ranta ba, ta fice daga d'akin. A k'ofar fita daga part d'in su ka yi kicib'is da Suhail shi kuma zai shiga wajan mahaifiyar sa. "Keee!". Suhail ya fad'i ya na k'are mata kallo har da had'iyar yawu. Gitta shi ta zo yi za ta wuce, aikuwa ya damk'i hannunta da k'arfi ta re yin side d'in shi da ita. Binty turjewa ta ke yi, amma Sam ya k'i sakin ta gashi ba bu kowa balle wani ya cece ta. Sai da ya kai ta har kan gadon shi, ka na ya yasar da ita ta re da yi mata rumfa..........
*PLEASE MANAGE, WALLAHI INA WANI AIKI NE MAI MAHIMMANCI*