Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 19

Ba ni da gata - Chapter 19

Ba ni da gata Chapter 19: Ba ni da gata Chapter 19. .............Sanye ta ke cikin riga da wando pallazo kalar orange. Sai dogon takalmi mai tsini a…

2,938 words

.............Sanye ta ke cikin riga da wando pallazo kalar orange. Sai dogon takalmi mai tsini a k'afarta kalar fari. Gashin nan na ta ya sha gyara ta yi parking d'in shi a tsakiyar kan ta. Hannunta rik'e da wani jaka da ak'alla zai kai 48k Kalar fari. Sai glasses mai shape d'in love d'in da ta saka da ya cinye kusan rabin fuskan ta da ya sha make-up. Waya ce a kunnenta ta na waya cike da nisha'di. "Ayyaaah Ya Bibi dan Allah kar ka yi fushi da ni, Allah ina shan magani na. Yaushe rabon da mu zo *CANADA* domin ka duba ni ciwo na ya tashi? Ai sai dai kawai muzo checkup. Allah ina kula da kai na ya Bibi". Ban san abunda wanda ta ke wayar da shi na ya ce, sai ce wa ta yi, "Dan Allah ya Bibi na ka dawo, Allah kuwa zan yi kuka. Wai to ko kewan su mom d'in ka ba ka yi ne? Dan Allah ka dawo ko in yi kuka". Ga dukkan alamu cewa ya yi ba zai dawo, ai kuwa sai ta saki kuka ta re da bubbuga k'afa a k'asa kamar ya na ganin ta ta na fad'in, "Please yaaa Bibi ka dawo dan Allah". Washe baki ta yi ta re da yin tsalle ko tsoro ba ta yi ta turgud'e saboda dogon takalmim da ke k'afarta ta ce, "Yeeeeeee! I'm soo sooo happy you're coming back in next to month. Can't wait to see you Bibi". Katse wayar ya yi daga can b'angaran, ita kuma ta soma saukowa daga stairs takalmin ta na ba da sautin k'os k'os k'os. Hajiya Sakna da ke zaune a parlour ta na kallon TV ta d'ago ta kalli inda ta ke jin k'aran takalmi. K'ura mata idanuwa ta yi har ta k'araso wajan mom d'in na ta, ta ce, "Mom zan je gidan aunty, Best friend na birthday yau. Yanzu haka ma ina waya da doctor ya min miss call ya fi goma, so I've to be hurry". "To ni ba lalatacciyar uwa ba ce ba Sabrin, yanzu a haka a wannan shigar za ki fita? To idan kin ga kin fita a haka, to Allah ka ya ki ka canza". Buga k'afa Sabrin ta soma yi ta re da fa'din, "Ni wallahi mom sai na fita, mai shigar na wa ya yi. Hijjab ki ke so in saka a birthday d'in *HAMDAN*, ai wallahi cewa zai yi wulak'anci na zo yi masa. Kamar ni classic babe in saka hijjab, never". Fad'in Sabrin ta na turo ba ki. "Ubanki, uban da ya haife ki na ce Sabrin. Kin ji ko baki ji ba in sake mai-maita maki". Fad'in Fauwaz da shigowar shi kenan. Kallon Fauwaz d'in ta yi ta re da sakar masa harara ta kalli gefe. "Ubanki ki ka harara". Fauwaz ya fad'a. "Ga ni nan ai". Fad'in Alhaji Saifullahi da shigowar shi kenan ya na buga malum-malun. Da gudu Sabrin ta koma bayan shi ta tsaya ta re da rik'e masa malum-malum.

*ARE YOU READY??? TO KU GYARA ZAMA KU KIMTSA, DOMIN YANZU LABARIN ZAI SO MA. AN GAMA SHIMFID'A, YANZU ZA KU SHIGA TSUNDUM CIKIN LABARIN*.

*@DARMA* *@FAREEDA HARUNA DA SAURAN DA BAN KIRA SU NA BA,* *KU FEK'E ALK'ALUMAN KU, DOMIN YANZU COMMENT ZAI HWARA*

*MATAR SAYYADEE* *PAID BOOK 08128755583* 🌹 *37-38*🌹 ..........."Kun gama antaya min kwandon zagin kai da mahaifiyar ta ka? Na ce kun gama?". Fad'in Alhaji Saifullahi da ke kallon cikin idanun Fauwaz ya na buga malum-malum. Sunkuyar da kai Fauwaz d'in ya yi ta re da susa kyeyarsa ta re da fad'in, "I'm sorry dad, ita d'in ce ta ke wa Mom rashin kunya don kawai ta ce mata ba za ta fita da wannan shigar ba". "To ina ruwan ka? Shegen yaro mai ido a tsakiyar kai. Wannan wani irin bala'i ne haka? Yanzu har da kai Fauwaz ake ga na wa y'ar uwar ka uk'uba? Ko tausayin irin lalurar da ta ke d'auke da shi ba kwa yi. To shikenan, billahi duk na san maganin ku, kuma idan ba saka idanuwa da bak'in ciki ba, mi ye aibu a shigar da Sabrin ta yi? Wallahi ku kiyaye ni kai da uwar ka". Alhaji Saifullahi ya k'arishe maganar da kwafa ta re da kallon Sabrin d'in ya ce, "Shalele rabu da su kin ji. Duk za su sha mamaki. Yi tafiyar ki. Ina ce gidan mummyn ki Saratu za ki". Alhaji Saifullahi ya fad'a ya na shafa kan ta. Ita kuma sai narkewa ta ke yi wai ita daddy's girl. D'aga masa kai ta yi ta re da fad'in, "Eh daddy can za ni. Hamdan ne ke birthday. Kasan best friend d'i na ne shi". "To wani gift ki ka shirya masa?". Fad'in Alhaji Saifullahi. "Daddy suprice na ke son na ba shi, kawo kunnan ka ka ji". Fad'in Sabrin ta re da kai bakin ta dai-dai kunnansa. Hajiya Sakna da Fauwaz, sakin baki su ka yi su na kallon iskancin da Sabrin d'in ta ke zubawa, Alhaji Saifullahi na d'aure mata gindi. Fashewa da dariya Alhaji Saifullahi ya yi ta re da mik'awa Sabrin d'in hannu su ka tafa kamar k'awaye. Alhaji Saifullahi ya ce, "Kwarai kuwa wannan kyautar ta yi, na ma tuna ai shekaran jiya ki ka sa na miki transfern 1.2 zuwa account d'in ki. Gaskiya kin iya zab'e kuwa. Yi maza ki je ka da ki makara". Fauwaz da Hajiya Sakna zaro idanuwa su ka yi ta re da fad'in, "One point two million?". "Eh ina ruwan ku? Ko ku kuke nai mo min kud'in da za ku wani zazzaro min idanuwa kamar agolan nupawa". Gimtse baki Fauwaz ya yi ta re da yin hanyar stairs saboda idan ya cigaba da tsayuwa a wajan zuciyar tafarfasa za ta rik'a yi. Gaba d'aya daddy ya riga da ya gama lalata Sabrin. Hajiya Sakna kuwa galala haka ta bi su da idanuwa har Sabrin d'in ta b'acewa ganin ta. Alhaji Saifullahi kuwa dogon tsaki ya ja ta re da nufar hanyar part d'in sanyin idaniyar shi wato Junaina. Kasancewar ta na ta ya shi nunawa Sabrin d'in k'auna a cewar shi.

.............Sabrin d'in na fitowa su ka yi kicib'is da Amrah sanye da lace toques blue da ratsin milk a jiki wanda akai mata doguwar riga abuja bubu. Ka na ta d'auko gyale milk colour ta yafa a kafad'arta ta re da flat shoe shi ma milk colour, sai wayar ta k'irar infinix a hannun ta. "Sister sai ina? Kin ga yadda ki ka had'u kuwa? Ka da fa ki sa go slow a hanya". Fad'in Amrah, kasancewar sannu a hankali aunty Junaina ta koya masu dabarun cin ribar zama da Sabrin d'in. Wani farrr da idanu Sabrin d'in ta yi ta re da jin dad'in kod'atan da Amrahn ta yi ta re da fad'in, "Yau ne birthday d'in best friend, shi ne na ke son na je. Na san yanzu haka ya na can ya na jira kamar zai yi bingiga". "To ko in zo muje ne? Kin ga sai in yi driving, don bai kamata yadda ki ka had'un nan ba ace ke za ki yi driving da kan ki". Ba ta re da Sabrin d'in ta ce komai ba ta jefe ta da key d'in motar ta, wanda a gidan bayan Ya Fauwaz da, mom da aunty Junaina ba bu wanda ke da mota sai ita. Kuma ko Yaya Fauwaz d'in, bai isa ya had'a motar shi da tata ba. Don duk shekara Alhaji Saifullahi ya ke canza mata mota. Gaba ta yi, Amrah na bin ta a baya ta re da antayawa bayan na ta harara.

.............Tun daga bakin gate mutum zai fahimci ana wani shagali a gidan. Domin hatta gate sai da ya sha decoration da balloons sannan an ruba *IT'S ANOTHER YEAR* da wani abu mai kyalkyali. Horn Amrah ta yi, mai gadi ya wangale mata gate d'in gidan ta tura hancin motor ciki ta re da nai man waje ta yi parking kasancewar harabar gidan motoci ne da yawa a wajan na abokan *Hamdan* d'in. Tun daga shigowar motar, wani kyakkyawan matashin saurayin sanye da wasu tsadaddun k'ananan kaya, ba zai wuce 22 years ba ya ke ta sakin murmushin don ya san mai motar. Fitowar ta daga cikin motar ne ya saka saurin kallon dandazon abokan sa ta re da fad'in, "Guys, besty ta iso. Ya kuka ga best friend d'in tawa? Ba ri na k'arasa ka da na yi latti". Fad'in *Hamdan* ta re da nufar in da Sabrin d'in ta ke a jingine da jikin motar. Cire glasses d'in fuskarta ta yi ta re da nufar wajan sa ta bud'e hannayanta alamar oyoyo. Hamadan na isowa ya rungumeta ta re da fido wayar shi a cikin aljihun wandonsa ya shiga yi masu selfie su na yin different styles. Amrah da ke gyefe kuma, tsayawa ta yi ta na kallon ikon Allah don kuwa ta san bai da ce ba runguman junan da su ke yi tun da akwai aure tsakanin su. Su kuwa ba su d'auki hakan ba a matsayin komai fa ce wayewa. "Hannunta ya rik'o su ka isa filin da aka zagaye shi da kujeru ta re masa decoration mai kyau. Gyefe kuma DJ ne da kayan sautin sa. "Hello everyone! May I present you my best friend, Queen Sabrin". Fad'in Hamdan. Gaba d'aya wajan suka hau tafi duk da ba yau ba ce rana ta farko wasu daga cikin su su ka fara ganin ta. Don duk shekaran haihuwar *Hamdan* d'in ya zagayo, sai sun yi shagali. Sabrin wani fari ta yi ta re da d'aga masu hannu kamar mai campaign. Hamdan ya cigaba da fad'in, "Kun gan ta ko, kyakkyawa yarinyar, wacce ko India, k'asar larabawa aka je, samun kwatankwacin ta abun ne mai matuk'ar wuya balle a samu wacce ta fita. Ita d'in ta daban ce. Kyawun ba wai daga kayan da ta ke sakawa ba ne, daga jikin ne. Domin kaf matan da su ke nan, da za su yi kwaikwaiyon irin dressing d'in ta don su ga su ma sun haska, to fa ba za su kamo ko k'umbar ta ba, domin kyawun daga jikin ne". Sabrin da ke tsaye, ji ta ke kan ta har wani k'ara kumbura ya ke yi kamar zai fashe. Sosai ta ke jin dad'in abunda *Hamdan* ta ke fad'i har cikin b'argon ta. Ta na matuk'ar so a yabe ta. Kallon DJ *Hamdan* ya yi ta re da fad'in, "DJ, sakar mana sauti". Hamdan ya fad'i hakane ta re da kamo hannun ta duka biyun. DJ kuwa ya sakin masu wak'ar Assique, Hamdan ya shiga juya ta a cikin filin ya na bin wak'ar kamar haka,

🎻 *Hum tere bin ab reh nahi sakte* *Tere bina kya wajood mera x (2)*

*Tujh se juda gar ho jaayenge* *To khud se hi ho jaayenge juda* *Kyun ki Tum hi ho, ab tum hi ho* *Ki zindagi ab tum hi ho* *Chain bhi, mera dard bhi* *Meri aashiqui ab tum hi ho*

*Tera mera rishta hai kaisa* *Ek pal door gawara nahi* *Tere liye har roz hain jeete* *Tujhko diya mera waqt sabhi* *Koi lamha mera na ho tere bina* *Har saans pe naam tera* *Kyun ki tum hi ho, ab tum hi ho* *Zindagi ab tum hi ho* *Chain bhi, mera dard bhi* *Meri aashiqui ab tum hi ho*

*Tum hi ho, tumhi ho*

*Tere liye hi jiyaa main* *Khud ko jo yoon de diya hai* *Teri wafaa ne mujhko sambhala* *Saare gamon ko dil se nikaala* *Tere sath mera hai naseeb judaa* *Tujhe paa ke adhoora na raha* *Kyun ki tum hi ho, ab tum hi ho* *Zindagi ab tum hi ho* *Chain bhi, mera dard bhi* *Meri aashiqui ab tum hi ho*

*Kyun ki tum hi ho, ab tum hi ho* *Zindagi ab tum hi ho* *Chain bhi, mera dard bhi* *Meri aashiqui ab tum hi ho*🎻

Yadda *Hamdan* ke bin wak'ar da yadda ya ke rawa da Sabrin d'in, za ka d'auka ba indiye ne shi da itan. Bayan wak'ar ya k'are, su ka tafi su ka yanka cake, aiko ta yi masa kaca-kaca da shi a fuskan shi ta kuma k'i bari ya shafa mata a fuska sai guje-guje su ke yi a filin. Bayan nan kowa da ke wajan ya shiga ba shi masa gift. Gimbiya kuwa wajan motor ta ta koma ta re da d'auko jakar magi star ta mik'a masa. Kowa a wajan ya shiga mamaki, kasancewar wannan shekarar ne kawai ta tab'a masa haka. Duk shekara gangariyar abu ta ke ba sa. Wani zuciyar ta ce masa ya bud'e ledar. Aikuwa ya na bud'e makullin power bike ya fad'o. Machine d'in da ya ke matuk'ar k'auna a rayuwar sa. Danna bottun d'in da ke jikin key d'in ya yi, aikuwa machine d'in da ke can gefe sabuwa dal da babu wanda ya lura da ita ta soma k'ara. Aikuwa bai san sanda ya buga wani tsalle ya rungume ta ba ya na murna. Gaba d'aya duk kyautukan da aka kawo masa babu kyautar da ta fi tafiya da shi kama power bike d'in nan. Bayan ya gama ihun jin dad'in shi, su ka cigaba da shagali ta re da rak'ashewa, sai watse-watsen sham pen su ke yi wa junan su a jiki. Sai bayan kowa ya watse ne, Sabrin da Hamdan su ka kwashi gift d'in shi su ka yi d'akin shi da shi. Zama Sabrin d'in ta yi a kan resting chair da ke d'akin na shi ta re da fad'in, "Washhh! I'm tired. Anya bazan kwana gidan nan ba kuwa, don wallahi ba zan iya driving ba, sai dai idan za ka kai ni gida". "Ba ta re Ku ka zo da k'anwar ki ba, ai kamar idan ba idanuwa na ba ne, na gan ta lokacin da mu ke rawa". Fad'in Hamdan. "Ita ce, ta wuce gida maman ta ta kira ta". Fad'in Sabrin ta re da kwanciya a kan resting chair d'in. "To ba ri na yi wanka, sai na raka ki. Ni ma ina son zuwa Kaduna jibi in sha Allah". Hamdan ya fad'a. Wani d'agowa Sabrin d'in ta yi ta watsa masa harara ta re da sakin dogon tsaki ka na ta ce, "Wahalallan banza kawai, ba Kaduna ba ka zagaye duniyar. Wallahi na san ba uncle Sauban za ka je ga ni ba, wannan gantalalliyar yarinyar y'ar kan bolan da kullum ka ke ishen mutum da labarin ta za ka nai ma, kuma wallahi idan ba kai wasa ba, sai na Shiva wajan mummy na fad'a mata". "Dan Allah ki fi jirgi gudu. Da ya ke ma iya mummyn da kan ta za ta aike ni Kadunan. Kuma idan dai Beauty ce, wallahi ba zan ga ji da nai man ta ba har sai Allah ya sake had'a fuskokin mu idan Allah ya k'adarta hakan a gaba. Wallahi ni fa duk wanda bai k'aunar Beauty, ni ma fa bai k'auna ta. A matsayin ki na Besty na, wallahi bai ka ma ta ki rik'a k'in Beauty ba. Na san ko ke kika gan ta, sai ta burge ki. Very beautiful girl. Ban tab'a ganin mace mai kyau irin ta ba". Fad'in Hamdan. Haba tuni Sabrin ta kawo wuya. A zafafe ta mik'e ta re da fad'in, "Mak'aryacin banza da wofi. D'azu a wajan birthday party d'in ka ka gama fad'awa mutane I'm the most beautiful girl you have ever seen, shi ne yanzu za ka ce wai wani ba ka tab'a ganin kyakkyawa kamar ta ba. Mayaudari kawai mai kan gwanda. I hate you. Kuma wallahi na fi ta kyau. Ita da *BA TA DA GATA*, y'ar *BOLA* da ita. Duk yarinyar da ka ga an yar da ita a bola, to *ZINA* a kan yi da uwarta aka haife ta. Shi ne har za ka tsaftatacciya kamar ni da datti irin ta. I hate.........". Ka fin ta k'arisa maganar Hamdan ya katse ta da fad'in, "Out..! Fitar min a d'aki right now. Sau nawa zan dunga fad'a mi ki akan ki bar kiran Beauty da y'ar *ZINA*? Idan ma haka aka yi aka haife ta, ai ba laifin ta ba ne. Ke ma ba dabarar ki ba ce da aka haife ki da aure. Out now before I loss my control". Hamdan ya k'arisa fad'in maganar da tsawa. Mik'ewa Sabrin d'in ta yi ta re da fad'in, "It Isn't your fault wallahi. Laifi na ne da Har na yi attending birthday party d'in ka shiyasa ka ke min wulak'anci. Kai da ba dan cousin d'ina ba ne, wallahi da yau ba za ka kwana a gidan uban ka ba, amma from now ka rubuta ka aje, ba ni ba ka, ni ba best friend d'in ka ba ce Ku ma. Kar ka sake kira na a waya. I'm deleting your number right now". Fad'in Sabrin ta re da fiddo wayarta ta yi deleting numbern Hamdan d'in ta re da fita daga d'angin ta bugo masa k'ofar. Kicib'is su ka yi da mummy Saudat, rab'e ta ta yi ta re da wuce wa ko gaishe ta ba ta yi ba. Mummy Saudat na kwad'a mata kira, amma ko juyowa ba ta yi ba ta wuce wajan motarta ta re da baron gidan. D'akin Hamdan d'in ta nufa ta na dariya ci kin zuciyar ta, domin idan da saboda Sabrin da Hamdan sun saba irin wannan fad'in, kuma cikin kwana biyu su shirya kan su, shiyasa ba mai shiga tsakanin su, don idan za ta iya tunawa, to wannan fad'an na su shine na d'ari da Saba'in kuma su na shirya kan su ba ta re da Sanin kowa ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull