Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 18

Ba ni da gata - Chapter 18

Ba ni da gata Chapter 18: Ba ni da gata Chapter 18. *MATAR SAYYADEE* 🌹 *35-36*🌹 ............. Cikin rashin sa'a aka shaida masu ya tafi US daran jiya,…

3,092 words

*MATAR SAYYADEE* 🌹 *35-36*🌹 ............. Cikin rashin sa'a aka shaida masu ya tafi US daran jiya, amma zai dawo nan da kwana biyar. Gaba d'aya Alhaji Saifullahi ya rasa natsuwarsa. Tuni har ya je ya yanki ticket d'in zuwa *CANADA* shi da matar sa Junaina. Hajiya Sakna kuwa, ko da ta ji labarin abunda ya faru wajan su twins kasancewar su ma sun baro na su makarantar sun zo ganin inter house a nan *LEAD BRITISH*, ta ji dad'in yadda hakan ta kasance da Sabrin d'in, amma gyefe guda kuma ta na jin tsananin tausayi irin na uwa da d'a saboda halin da Sabrin ta shiga. Ta yi fatan Allah ya sa hakan ya zama silar shiryiwarta. Abun ya yi wa Hajiya Sakna ciwo kasancewar ba da ita za'a je jinyar y'arta ba. Ta ka sa daurewa har sai da ta yi wa Alhaji Saifullahi magana. Ya ko ta so mata kamar zai cinye ta d'anya ta re da ce mata har ta na da bakin da za ta ce ba'a mata adalci ba bayan ba k'aunar Sabrin d'in ta ke yi ba. Ita kuwa Hajiya Sakna ta san a can d'in ma, k'ara gurb'ata mata tunanin ta za su yi daga Junaina har Alhaji Saifullahin. Washa gari kuwa, Alhaji Saifullahi da Junaina su ka haura gajimare su ka lula k'asar *CANADA* da Sabrin da ta ke kamar gawa don har oxygen aka saka mata a hancin ta.

.............Binty tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha. Ba ta tab'a tunanin cewa akwai ranar da jama'a za su sota ba. Sai ga shi yau ko ta ina ta gitta magana ake mata ta re da son d'aukar hoto da ita. Yaya Fu'ad kuwa, ba za ta iya k'irga hotunan da su ka yi da shi ba. Camera man ya d'auke su, sannan shi kan shi Ya Fu'ad d'in ya masu salfie da wayar shi ya fi a k'irga. Wasu su yi su hud'u, shi, Binty da Anna da kuma Fanan, wa su kuma su uku, shi da Binty da Fanan. Wanda su ka yi su biyu kuwa, shi da Bintyn ya fi a k'irga. Sai wanda ya masu ita da Fanan. Haka su ka cika boat da gift d'in Binty da Fanan. Don Fanan ita ta zo second position a class d'in su. Bayan sun dawo gida, kaya kawai su ka canza ya Fu'ad ya kwashe su su ka je yawo. Ba su su ka dawo ba sai gab da magriba. Bayan sun idar da sallah su ka shiga bud'e gift d'insu su na gani su na murna. Daddy ma kan shi da ya dawo, sosai ya ji dad'in yadda y'ay'an na da su ke dagewa a makaranta. Shi kan shi sai da ya ba su na shi gift d'in. Don mota sabuwa dal ya canza masu wanda driver zai rik'a kai su makaranta. Sannan ya kuma cire rana d'aya a cikin ranakun sa masu matuk'ar amfani ha fita da su zuwa shopping. Ranar hatta front seat sai da aka cika da tarkacan kaya kamar a bishiya ake tsunko kud'i.

*AFTER SEVEN DAYS* *CANADA* ...........Cikin hukuncin ubangiji ranar da su Alhaji Saifullahi su ka sauka a k'asar *CANADA*, shi kuma da kwana uku Julaibib ya sauka a k'asar, kasancewar shi da kan shi Alhaji Saifullahi ya yi magana da shi a waya ya na kuka saboda yadda numfashin Sabrin ya ke sama, sai ta yi kusan minti biyu kamin ya dawo k'asa. Haka ta ke ta yi. Hakan ne kuma ya firgita Alhaji Saifullahi har ya ke ganin zai rasa y'arsa. Da gudu ya fito daga d'akin da aka aje Sabrin d'in ya shiga office d'in wani doctor ya na kuka ya rok'on sa akan ya ba shi number Julaibib. Yadda Doctor ya ga babban mutum ya na kuka haka, sai ya d'aga mashi hankali. Kwantar masa da hankali ya shiga yi ka na daga bisani ya kira masa doctor Julaibib d'in, don ko ya ba shi numbern sa idan zai shekara ya na kira ba zai sa me shi ba. Doctor Julaibib na d'aga wayar Alhaji Saifullahi ya fashe masa da kuka ta re da soma rok'on sa akan ya dawo ya duba masa lafiyar y'arsa ka da ta mutu. Julaibib da a duniya ya tsani ya ji kukan mutum a kusa da shi, balle ma ace mutumin nan shi ya sa ka shi kuka ko kuma wani alfarma ya ke nai ma a wajan shi. Ga shi ya tsani a yi masa magana a cikin kunnan sa da ihu ko kuma da kuka, kai ko yaro ne bai son ya ji kukan sa a kusa da shi. Sam ya tsani surutu, hayaniya kk tashin hankali a inda ya ke, hakane ma ya sa ya ke yakon keb'ance k'ansa shi kad'ai don gudun b'acin rai saboda ya na da mugun zuciya. Katse kiran kawai ya yi ta re da saka hannunsa ya dafe goshin sa. Can kuma ya d'auki wayar sa ta re sa booking flight d'in *CANADA*. Alhaji Saifullahi kuwa ya na jin Julaibib ya katse kiran hankalin shi ya d'uk'unzuma domin a tunanin shi, wulak'anci Julaibib d'in ya masa. Kallon doctor da ya taimake shi ya kira masa Julaibib d'in ya yi ta re da fa'din, "He.. He just off the phone. What I'm I gonna do now". "Calm down sir, I a sure you he will be on his way tomorrow. Just go and rest". Fad'in wannan baturan doctorn. Alhaji Saifullahi zai sa ke magana, doctor Stephen ya yi saurin katse sa ta re da fa'din, "Sir please trust me. You daughter will get better by the grace of God. Just go back and rest". Doctor ya fad'a ta re da D'an bugun kafad'ar shi. Ajiyar zuciya Alhaji Saifullahi ya yi ta re da koma wa d'akin da Sabrin d'in ta ke still nunfashin ta na wannan sama da k'asar. Tsura mata idanuwa ya yi ya na mai k'ara jin k'aunar y'ar ta sa na huda zuciyar shi. A fakaice Junaina ta dallara masa harara ta re da fa'din k'asa-k'asa yadda Alhaji Saifullahi ba zai ji abunda ta fad'i ba, "Sai ma mun koma da gawarta shegiyar d'iyar ta ka za ka yi kuka mai tushe. Mara tsoran Allah kawai. Da sannu zan koya maku hankali daga kai har y'ar iskar uwar gidan na ka. Mtsw". Ta k'arishe maganar da tsaki k'asa-k'asa. "Nagode Junaina". Fad'in Alhaji Saifullahi. Gaban Junaina ne ya buga daam, har ba ta san lokacin da ta zaro idanuwa ta re da fa'din, "Alhaji godiya kuma ta me ka ke min?". "Yadda ki ke kula min da Sabrin kamar d'iyar cikin ki, Allah ya saka miki da alkhairi. Nagode sosai. Na mi ki alk'awarin Bugatti idan mun koma Nigeria in har Sabrin ta sa mu lafiya". Fad'in Alhaji Saifullahi. K'ara Zaro idanuwa Junaina ta yi ta re da fa'din, "Haba Alhaji! Har sai ka min godiya akan kula da d'iya ta. Ai ni kamar yadda na ke jin su Amrah da Hanan a rai na, haka na ke jin Sabrin. Fata na kawai ta samu lafiya". Cikin zuciyar ta kuwa fad'i ta ke, "Dan uwar ki ka da kk mutu, ki yi ta rik'e numfashin ki har Doctorn ki ya zo ya duba ki mu koma Nigeria da ran ki domin mahaifin ki ya cika min alk'awari na idan ya so bayan nan kya fad'i ki mutu, wa ya damu". "Ni kai na nasan duka ki ka d'auke su Junaina. Abunda Sakina ta kasa ganewa kenan". Hawayan munafurci ta soma sharcewa ta re da fa'din, "Hausawa sun ce mai d'a wawa ne, amma wannan maganar ba haka ta ke a wajan Sakna ba. Domin kullum ita gani ta ke ban k'aunar Sabrin. Kuma ni Allah ya san zuciya ta". "Allah ya san zuciyar ki, kuma ni ma nasan na ki. Saboda ki dai na damuwa akan Sakina. Ina ganin harda kishi ke d'awainiya da ita". Fad'in Alhaji Saifullahi. "Allah dai ya baiwa Sabrin lafiya. Shi ne fatana kawai". Fad'in aunty Junaina ta na share kwallar munahinci. "Ameen" Fad'in Alhaji Saifullahi ta re da zama akan kujera ta re da rik'o hannun Sabrin d'in.

*WASHA GARI*

...........K'arfe 4:00pm a *MOUNT SINAI HOSPITAL* ta yi wa doctor Julaibib. Da Peter John ya ci karo ya na k'ok'arin fita daga asibitin. Tsaya cak ya yi murmushi d'auke a fuskan ci ta re da mik'awa Julaibib hannu don su yi musabaha. "I don't sake hands with an alcoholic. Get out of my way". Fad'in Julaibib ta re da murtuke fuska. "Ohhh come on, I sweat by god I'll never repeat such a thing again. Please stop avoiding me Julieby (Julaibib)". Ajiyar zuciya Julaibib ya yi, har ji ya yi kan shi ya soma sarawa saboda d'an maganar da Peter John ya tsare shi da shi. "OK, but don't repeat again". Ya na gama fad'in haka ya rab'e shi ya wuce office d'in shi direct. Girgiza kai Peter John ya yi ta re da fa'din, "Bibi, hmmm. My Best friend for ever". Ya fad'i hakane ya na tafiya zuwa wajan motar shi.

Julaibib na gama abunda zai yi a office ya nufi office d'in doctor Stephen. Kwankwasa k'ofar ya yi ta re da turawa ya shiga ciki. D'ago kai doctor Stephen ya yi. Cikin second ya mik'e fuskan shi fad'ad'e da murmushi ta re da fa'din, "I knew it". Ta re da barin inda ya ke a zaune ya nufo doctor Julaibib d'in ta re da mik'a masa hannu ya ce, "Welcome sir, the patient is in room number 6 *DQR*". Ya yi saurin dad'in hakan ne saboda kowa na cikin asibitin ya san shi da rashin son magana da surutu a kai. Juyawa kawai doctor Julaibib d'in ya yi ta re da nufar Room 6 *DQR*. Julaibib na shiga ya ga halin da Sabrin ta ke ciki ya sa a ka yi *INTENSIVE CARE UNIT (ICU)* da ita cikin gaggawa. Da shi da Doctor Joshuah su ka rufar mata su na ba ta taimakon gaggawa. Sosai Julaibib ya shiga tashin hankali ganin yarinyar da ba ta wuce 11-12years ba ta har ta kai wannan stage d'in na ciwon zuciya. Bayan sun shawo kan matsalar ne, Doctor Julaibib ya fito daga *ICU* ya nufi office d'in shi bayan ya sa ka an kira masa Alhaji Saifullahi. Jiki na b'ari Alhaji Saifullahi ya zauna a kujerar da ta ke fuskantar na doctor Julaibib d'in ta re da zuba masa idanuwa ya ma kasa tambayar shi mai ke faruwa saboda yadda zuciyar sa ke bugawa. D'agowa Julaibib ya yi ta re da kallon Alhaji Saifullahi ta re da fa'din, "Amma dan Allah idan ban takura ba, zan so sanin shin yarinyar nan ta na hannun mahaifiyar ta ne, ko kuma hannun ruk'o ta ke?". Fad'in Julaibib har da sakin ajiyar zuciya. Domin ba k'aramin k'ok'ari ya yi ba wajan furta kalamar nan. Don shi sam magana na masa wuyar furtawa. "Doctor mai ya sa ka min wannan tambayar?". Fad'in Alhaji Saifullahi. "Saboda yarinyar ka ta kai mataki na biyu a cikin wannan ciwon, kuma idan har aka cigaba da gallaza mata, za ta kai matakin k'arshe da zai yi sanadin bugawar zuciyar ta. Kuma idan haka ta kasance, mutuwa za tayi" Zaro idanuwa Alhaji Saifullahi ya yi ta re da fa'din, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Doctor wallahi a hannun mahaifiyarta ke, mahaifiyar ce wani lokacin ta ke k'ok'arin takura mata. Amma wallahi sosai na ke d'aukar mataki a kan haka, dan girman Allah doctor ka ceci y'ata". Wani file da ke gaban shi ya bud'e ta re da yin rubuta ka na ta d'ago ya kalli Alhaji Saifullahi ta re da fa'din, "Allah ya kyauta. Yanzu dai y'ar ka ta fita daga matsala, sai dai Ku yi k'ok'ari Ku ga ne ko Ku tambaye ta abunda ke damun ta Ku yi mata shi. Saboda the more ta na shiga damuwa, the more ciwon na k'ara tafiya gaba". "In sha Allah doctor zan yi wannan k'ok'arin". Fad'in Alhaji Saifullahi. "Allah ya ba ta lafiya. Za ka iya tafiya". Fad'in Julaibib ta re da d'aukar briefcase d'in sa shi ma ya mik'e.

*NIGERIA* ............Abubuwa na ta tafiya Binty normal. Ya yin da duk k'arshan wata sai Kandala ta zo ta karb'i y'an karancy (currency) ta re da uban kayan abinci. Sai da su ka yi wata biyu a gida ka na su ka koma school, kai tsaye aka yi wa Binty double promotion zuwa akin su Fanan wato primary five saboda yanayin kwazon ta da kuma k'ok'arin ta. Sai dai wannan karan Sabrin ba ta dawo makarantar ba don tuni Alhaji Saifullahi ya canza mata makaranta bayan dawowan su daga *CANADA* ya tsare ta ta fad'a mishi duk abunda ya ke damun ta. Ta fad'a mashi wata newcomer aka kawo da ta kwace mata duk wani abu na ta. Kuma ta tsani yarinyar. Wannan dalilin ne ya saka Alhaji Saifullahi ya canza mata makaranta ta koma *NIGERIAN TURKISH* da ke Kaduna. Ta koma boarding school. In da ana ne ta kuma had'uwa da k'awaye y'an k'arya kala-kala irin ta. Kuma tafiyar su ta zo d'aya kasancewar ta samu ma su zuga ta kamar daddyn ta da kuma aunty Junaina.

................Binty kuwa, sai k'ara girma ta ke yi, ya yin da kyawun ta da hasken ta ta re da ilimin da kuma shegen surutun (kamar zuly ta haife ta😂😂😂) ta ya ke dad'a fitowa fili. Gyefe guda kuma Ya Barrister ya na k'ara killace k'aunar Bintyn a ran shi domin har ga Allah har cikin zuciyar shi, rainon Bintyn ya ke yi kuma so ya ke ta zame ma sa uwar y'ay'an sa a nan gaba. D'ayan b'arin kuwa, Hajiya Mansura na nan na babban shiri a kan Binty. Gyefe guda k'awarta Juwairiyya ma na nata shirin. Suhail ne dai ya mance da wata Binty a gidan kasancewar ba ganin ta ya ke yi ba. Harkar shaye-shayan sa ya ke yi ta re da sai da tabar wiwi da cocaine a b'oye. Yanzu abun na shi ya girmama izuwa safarar y'ay'an mutane ya na tura su karuwanci k'asashan waje.

...........Binty sun yi Common entrance, an shiga JSS1. Idan Ku ka ga Binty ba za Ku tab'a gane ta ba. Domin shekarunta sha uku. Duk wani halitta na d'iya mace ya bayyana a jikinta, ba Wai k'iba ta yi can ba. Amma doguwa ce sosai, ga k'ira kamar ita ta yi kan ta. Halittan jikinta gaba d'aya ya fito don ta fi Fanan da ta girme ta cikan jiki. Sannan kuma ta fad'i (balaga) domin ta riga Fanan balaga ma. Don fanan ma ba bu komai a k'irjin ta sab'anin Binty da ba ma za'a kira shi da k'irgan dangi ba. Sannan hankali ya shige ta sosai. Ta fahinci ita wacece, ta kuma ga ne ita ba komai ba ce fa ce tsintacciya da ke cin arziki a gidan su Fanan d'in. Sannan ba ta manta rayuwar ta na kan bola ba, hatta Hamdan ba ta mance da shi ba kuma ta na fatan wata rana Allah ya had'a ta dashi. Ta kan yi kuka sosai a d'aki idan ta tuna cewar *BA TA DA GATA*, tabbas ba ta rasa komai ba a in da ta ke, kuma ta san Anna mutum ce kuma uwa wacce har gaban abada ba za ta mance da ita ba. Ba ta tunanin za ta iya compering Anna da ko wacce mace a duniya. Domin Anna ita ta fito da ita a cikin duhun jahilcin da ta ke ciki har ta san ubangijin ta da kuma yadda za ta bauta mishi. Sanna kuma ta bata ilimin zamani, wannan abun da ta mata kawai ba isa ta biya ta ba. Ta d'auke ta tamkar Fanan. Sannan kuma ta kasa fad'awa Anna ba bu abunda su ka had'a da Kandala ko don mak'udan kud'in da Anna da daddy su ke ba ta a d'aukar su duk abunda Kandalan ta fad'a gaskiya ne. Har gaban gobe ba ta tunanin za ta dai na kukan akan rashin sanin ita wacece, menene dalilin zaman ta akan bola, wani laifin ta aikata aka ya da ta a kan bola. A tunanin ta ko ta hanyar banza aka Samar da ita, bai kamata a yar da ita a kan bola ba. Duk lokacin da tunanin nan ya bijiro mata wuni ta ke yi ta na kuka a d'aki. Ranar rasa gane kan ta ake yi har da Anna. Ya Barrister ne kawai ke iya shawo kan ta. Fita ya ke yi da ita yai ta zaga gari da ita ta re da kai ta ice cream parlour har sai natsuwa ya dawo mata su ke dawowa gida. Kuma a yi tambayar duniya, ta k'i fad'in abunda ke da mun ta.

*AFTER FOUR YEARS*

........Wata kyakkyawar yarinya ce sanye da graduation gown kalar blue, hannunta rik'e da hukar nan ta graduation. "Binty zo nan mu d'auki na tarihi dan Allah" Fad'in wata yarinya. K'arasawa Binty ta yi su ka d'auki hoton. Ta na barin wajan wasu dandazon su ma su ka rik'ota su ka d'auki hoton ta re. Da zarar ta yi can, za'a rik'o ta a d'au hoto da ita. So ta ke ta je su d'auka da ya Fu'ad da ke jingine da mota ya na kallon ta ya na murmushi. Da kyar ta iya kaucewa mutane ta tawo wajan Fu'ad ta re da fa'din, "Ya Fu'ad I'm sorry, sun hana ni zuwa mu d'auki hoto da sweet bro d'ina. Zo mu d'auka ta re". Fad'in Binty ta re da matsowa kusa da Ya Fu'ad. Camera man na d'auka shi ma ya na d'auka da wayar shi. Su na cikin d'aukar hoton, tawagar k'awayan ta su ka zo su ka jata. Bin su da idanuwa Ya Fu'ad ya yi ta re jin robar k'aunar Binty na narkewa a cikin zuciyar ta. Sai k'arfe biyu su ka ta shi daga makaranta bayan sun gama karb'an kyaututtuka cike da kewar k'awayan su. Sai dai sun karb'i numbers d'in junan su, duk da su Fanan numbern Anna su ka bayar kasancewar har yanzu ba su da waya. Bayan sun dawo Anna ta shirya masu walima kasancewar saura sati d'aya graduation d'in su suka sauke alqur'ani mai girma. Ranar kuwa Binty da ya Fu'ad zagewa su ka yi su ka d'ika rawa Fanan na masu video. Da daddare Ya Fu'ad ya kawo masu surprise d'in da har sai da Binty ta rungume shi don murna. Waya ce dalleliya k'irar IPhone 13pro max. Sosai su ka yi ta tsallen murna ta re da kwasa sai d'akin Anna su ka nuna mata ita ma ta taya su murna.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull