Ba ni da gata - Chapter 17
Ba ni da gata Chapter 17: Ba ni da gata Chapter 17. *Ku yi min afuwa masoya. Ku yi hak'uri da wannan. In sha Allah za ku ji ni anjima da yamma*
3,291 words
*Ku yi min afuwa masoya. Ku yi hak'uri da wannan. In sha Allah za ku ji ni anjima da yamma*
*paid book 08128755583* 🌹 *33-34*🌹 .........K'awayan Fanan da gudu su ka zo su ka zagaye su. Rukayya wacce su ke kira da Saje ta kalli Fanan ta re da fad'in, "Wannan ita ce surprise d'in da ki ka ce za ki taho mana da shi idan mun dawo first term. Lallai kam zuciyar Sabrin sai ta buga. Ba bu shakka sai an cire ta a sarauniyar kyawun *Lead British*, please sister will you be my friend?". Saje ta k'arishe maganar ta re da kallon Binty a marairaice. Murmushi Binty ta yi ta re da mik'awa Saje hannu ta ce, "Friend". Ka min Saje ta ce wani abu, gaba d'aya k'awayan Fanan su ka rik'e hannun binty ta re da fad'in, "Friends for rever and ever". Sun fad'i hakane ta re da d'aga hannun sama su na dariya. Dai-dai lokacin tawagar k'awayan Sabrin su ka k'araso in da su Binty su ke a tsaye. "Ku matsa mu na son ganin fuskan newcomer da ta zo yau". D'aya daga cikin k'awayan Sabrin mai su na Rufaida ta fad'a. Gaba d'ayan su su ka dare su ka bar Binty a tsakiya ta na kallon Rufaidan. Gaban Rufaida ne ta buga da k'arfi. Domin yadda students su ka zo su na fad'i masu irin kyawun newcomer d'in sai ta ga ta fi haka sosai. Juyawa Rufaida ta yi ta re da kallon sauran k'awayan da su ma tsananin kyawun Bintyn su ke kallo da mamaki. Ba ta re da fad'in komai ba, su ka juya su ka bar wajan ta re da nufar class inda Sabrin ke zaune idanuwan ta jazur, ga dukkan alama ma kuka ta ci. "Yana yin fuskokin ku kawai ya tabbatar min da abunda students su ka zo su ka fad'a. Ke nan ku na nufin kuma kyawun yarinyar ya haukata ku haka? Ku na nufin yanzu za'a samu wacce za ta done ni a kyau a cikin makarantar nan? Ba zai yu ba. Wallahi ko fuskan yarinyar ba na k'aunar ga ni. Ba na son in san ta ko in ga fuskan ta har in bar makarantar nan yau". Fad'in Sabrin ta re da rushewa da kuka. "Haba Ella. Kin san Allah, duk yadda ake fad'in kyawun yarinyar nan ko, kururutawa ne kawai amma ko k'unban ki ba ta kama ba. Kawai hasken fata ne irin bauu d'in nan kamar zabaya. Amma kin san Allah, kin fi ta komai, ba ma had'i". Fad'in Shamsiya Uba. D'ago kai Sabrin ta yi ta re da fad'in, "Duk wacce ta yi adoring yarinyar, ku ma idan har cikin team d'ina ta ke, a cire ta kuma za ta fuskanci hukunci". Fad'in Sabrin ta re da mik'ewa kasancewar an danna bell d'in assembly. A cikin k'aton hall d'in da ake gabatar da assembly, bayan kowa ya natsu, an gabatar da addu'a da kuma assembly. proprietor ya fito ya yi jawabi da kuma yi ma su barka da dawowa first term. Sanna ya k'ara da karanto wasu dokoki kamar haka cikin harshan turanci. "Kamar yadda ku ka sami, wannan makaranta ce da ake koyar da ilimi da kuma tarbiya. A kwai wasu dokoki da ni shugaba na shimfid'a sakamakon wasu abubuwa da su ka faru a shekarar da ta wuce. To hak'ik'a wannan karan idan haka ta k'ara faruwa, to za mu d'auki hukunci tsatstsaura akan ko wanenen. Ba ruwa da ko baban ka shine shugaban k'asa, idan ki/kai laifi, to hukuman makaranta za ta yi hukunci akan ko waye. Na farko, ba bu d'aukaf hukunci a hannu, duk abunda wani ya maka, ka kai k'arar shi, ba biyu ba'a yarda wani d'alibi/d'aliba ya takurawa wani ba, sannan ba a yarda ko waye ka d'auki bulala ka da ki wani ba ko da kuwa malami ne, sannan kuma duk house d'in da ka/ki ke, ba a yadda do ba ka san house d'in nan ka canza ba. Sannan duk abunda malami/malama ta saka ki/ka, wajibi ne ki yo idan har abun nan bai sab'awa dokar makaranta ba. Ina fatan kowa yaji bayani na". Fad'in proprietor. Gaba d'aya students d'in nan su ka amsa da, "Yes sir". Sallamar su ya yi kowa ya soma mik'ewa zuwa ajujuwan su. D'agowar da Sabrin za ta yi, su ka had'a idanu da Binty. Gaban ta ne ya buga da k'arfi ta wa ni zaro idanuwan ta. K'awayan ta da su ka ga abunda ke faruwa, da sauri su ka zagaye ta ta re da fad'in, "Ella ka da ki firgita, wallahi ba bu abunda ta fi ki da shi". K'ank'ance idanuwa Sabrin ta yi ta re da fad'in, "Da ma ita ce. Makarantar nan ta shigo kenan. Wallahi sai na saka ta gudu da k'afafun ta. Sai na d'aura mata k'ullin da ba za ta tab'a iya warware shi ba billahi". Fanan hannun Bintyn ta ka ma ta re da fad'in, "Mu je in nu na miki ajin ku, kin san amana Anna ta ba ni ke". Sai da ta kai ta har ajin su primary three, ka na ta wuce na su ajin P-4. Ka min teacher ta shigo ajin na su, kusan gaba d'aya y'an ajin su ka zo kan Binty su na mata magana. Kowa na san ya yi k'awa da ita. Kowa sai gabatar mata da kan sa ya ke a wajan ta. Class captain d'in ta kalli Binty ta re da fad'in, "I'm Na'ima Ahmad, and you?". Kasancewar ba laifi Binty na ga ne English sosai, sai ta kalli Na'ima ta re da fad'in, "I'm Binty Hisham mai goro". Ta fad'i hakane murmushi d'auke a fuskan ta. Teacher ce ta shigo ajin, kowa ya koma wajan zaman shi ta re da kunna computern da ke gaban shi. Binty kuwa sai raba idanuwa ta ke yi domin ba ta iya operating computern ba. Zayyishatou da ke gyefenta ta saka hannu ta kunna mata computer ta re da nu na mata yadda yi. Godiya ta mata ta re da mai da hankali a kan teacher da ke baya ni. Kad'an-kad'an Binty ke fahintar abunda teachern ke baya ni akai kasancewar turancin ya ma ta tsauri. Bayan ta kammala ta fita, Binty ta kalli Zayyishatou ta re da fad'in, "Ban ga ne abunda ta koyar ba, ban jin turanci sosai. Dan Allah ki min baya ni idan ke kin ga ne". Murmushi Zayyishatou ta yi ta re da fad'in, "Kar ki da mu, duk abunda ba ki ga ne ba, zan ko ya miki in dai za ki yadda in zama babbar k'awar ki". "A'a za dai ki zama ta biyu. Babbar k'awa ta Yaya ta ce Fanan. Anna ta ce min Fanan ta girme ni. Yayata ce kuma k'awata ce". Fad'in Binty. "To ai ba bu damuwa, sai in zama k'awar ki ta biyu" fad'in Zayyishatou. "Kin ma zama ai. Ke ce k'awata ta biyu. Ki koya min dan Allah". Gyara zama Zayyi ta yi ta re da matso da kujeran ta kusa da Binty sosai ta shiga koya mata abunda duk malamar ta koya masu. Kasancewar ta mai bud'ad'd'iyar kwakwalwa, tuni har ta fahimta. An fita break, Fanan ta zo ita da k'awayanta su ka fita zuwa capteria har da Zayyi sabuwar k'awar Binty. Zama s ka yi a wajan cin abincin, bayan sun fad'i abunda su ke son a kawo masu. Sabrin ce da zugar k'awayan ta su ka zagaye table d'in da su Bintyn su ke zaune. "Ke!". Sabrin ta daka mata tsawa. D'agowa Binty ta yi a razane kasancewar mai saurin tsorata ta kalli Sabrin d'in da ke tsaye a gaban ta. "Au ke ce. Kin zo ne ki fad'a min abunda na mini na ba ki hak'uri?". Fad'in Binty ta na kallon ta. "Ke ba ki da tarbiya ko? Kin zo har cikin mall d'in ubana kin bangaje ni, amma da ya ke ke dak'ik'iya ce sai ki ka wuce ba ta re da kin yi apologizing ba ko". Fad'in Sabrin ba ta re da ta fad'i cewar Bintyn ta mare ta ba, domin fad'in hakan a gaban mutane kamar zubar da k'imar ta ne a gaban su. Zaro idanuwa Binty ta yi ta re da mik'ewa ta ce, "Dan Allah ki yi hak'uri, wallahi ban san na bige ki ba. Shiyasa ki ka mare ni ashe. Da na sani ai da ban r........". "Ke dalla rufewa mutane baki". Sabrin tai saurin katse ta ba ta re da ta k'arisa abunda ta ke son fad'i ba. "To ai ba ba ki hak'uri. In sha Allah hakan ba zai sa ke faruwa ba. Ki yi hak'uri. Anna da daddy sun ce ka da na saki na yi fad'a da kowa a makaranta. Karatu aka turo mu ba fad'a ba". Fad'in Binty. "Wanna kuma ruwan ki. Ina mi ki gargad'i da shiga gona ta, idan kin kiyaye, kin tsira. Idan kuma ba ki kiyaye ba, za ko sha mamaki. Sai na saki kin koma ki na jan d'uwawu a cikin makarantar nan". Fad'in Sabrin. "Akan wani dalili kenan? Ina ce ta ba ki hak'uri. To dan Allah malama ki kwashi komatsatstsun k'awayan ki Ku yi gaba". Fad'in Fanan. "Ke! Ki shiga hankalin ki da ni a cikin makarantar nan. Idan ba haka ba, wallahi zan ba ki mamaki. Ba ruwa na da ko waye mahaifin ki a garin nan". Fad'in Sabrin. "To fah! Mi ya kawo maganar mahaifi a cikin maganar nan idan har ba kishi ki ke yi da mahaifin na ba". Fad'in Fanan ta na dariya k'asa-k'asa. Sabrin za ta yi magana, k'awarta Shamsiya ta dakatar da ita ta re da fad'in, "Haba Queen, wai ba ki fahimta ba ne. Fanan fa ta na zan ki da magana ne saboda ta zama cele a cikin school d'in nan ne. Ba ki ga gaba d'aya students d'in da ke capteria nan sun dawo da hankalin su nan ba ne. Hakan ai zai ja mata fans ne, kuma da ma abunda ta ke so kenan". Wani juya idanuwa Sabrin d'in ta yi ta re da fad'in, "Kuma hakane fa, na tsaya ina wasting sliver d'ina a ban za. Mu je dan Allah ban san yawan tsayuwa". Fad'in Sabrin ta re da yin gaba zugan k'awayan ta su ka bi ta a baya. Dariya ce ta kwacewa Fanan d'in. Kallon k'awayan ta ta yi ta re da fad'in, "Wai kun san mai ya faru kuwa?". "A'a sai kin fad'a". Ga ba d'ayan su su ka ba ta amsa. Nan fanan ta zayyane masu abunda ya faru a mall. Aiko gaba d'aya su ka kwashe da dariya ta re da cizan yatsa ina ma a gaban su ne aka Binty ta wanke fuskan Sabrin d'in da mari. Ita kuma Binty duk sai ta ji ba dad'i har ta ke dana sani akan marin da ta yi wa Sabrin d'in duk da ita ta fara marin ta.
Alhamdulillah! Binty na gane duk abunda ake koya mata a makaranta. Tun ba ta iya amfani da computer ba, har ta zo ta kware da taimakon Zayyishatou. Kowa a school d'in nan Binty. Wata d'ayan da ta yi a makaranta, ba k'aramin k'ara waye wa ta yi ba. Sosai kwakwalwarta ke bud'ewa ga ta da shegen tambaya akan abunda ba ta sa ni ba. Babban bak'in cikin Sabrin shi ne kasancewar su a house d'aya(Red house). Hakan ba k'aramin bak'anta mata ya yi ba. Gashi House Captain d'in su na planning akan cire Sabrin a matsayin Queen su nad'ata princess of the house, Binty Ku ma ta maye gurbin ta a matsayin Queen. Da ya ke a makaranta ko test a ka yi, a na fitar da first second and third position. Na'ima wacce ita ce class captain ita ta zo na d'aya, Zayyishatou ta zo na biyu, yayin da Binty ta kasance na uku. Sosai Binty ta ji dad'i ta re da d'aukar alwashi in sha Allah second CA ita za ta zo na d'aya. Ko da su ka koma gida, sosai Anna ta yi farin ciki. Yaya Fu'ad ku wa d'aukar so ya yi ranar sun sha yawo. Mayan kwalam sai da ya cika boat d'in motar sa. Sannna kuma ya sayan masu Laptop Apple su dukan su biyun. Ba k'aramin dad'i hakan ya yi masu ba. Hakan ya sa Binty k'ara zagewa da dagewa. Cikin ikon ubangiji da aka yi jarabawar first term sai ga ta ta zo second position. Tun daga wannan lokacin Binty ta kwace ta yi wa y'an ajin nan fintinkau. Idan Binty na turanci, za ka d'auko ana bud'e dictionary a ka tsince ta a ciki saboda tsabar yarda ta ke karya harshe da fitar da ko wani sauti yadda ya kamata. Kwanci tashi ba bu wuya wajan ubangiji, sai ga su a zango na uku, wato third term. Sai shirye-shiryen inter house ake yi. Tu ni captain d'in Red house da ta kasance a SS3 ta mai da Binty a matsayin Queen of red house, Sabrin Ku ma princess. Sabrin har zazzab'i ta yi saboda bak'in ciki da tashin hankali. Ji ta yi ta k'ara tsanar Binty har cikin can cikin kwaryar zuciyar ta. Kullum cikin practical su ke na game and sport d'in da za su gabatar ranar hutu. Tu ni har an gwada Binty kasancewar gown red colour za ta saka ranar inter house d'in nan. Binty ta k'ara haske ta yi b'ul-b'ul abunda. Sai dad'a girma ta ke yi. Don yanzu shekarunta goma sha d'aya ta ma fita cikin na sha biyu ta ke. Ya yin da Fanan ke da cikin na sha uku. Sai dai kan su d'aya kasancewar Fanan d'in ba ta da girman jiki sosai. Yauwa dai su ke rubuta final paper d'in su, hakan ya yi dai-dai da saura kwana hud'u inter house d'in su. Bayan sun dawo gida, sun yi sallah sun ci abinci sun kimtsa, Binty ta d'auki wayar Anna kasancewar ta na ba su suyi game. Numbern barrister Fu'ad ta dannawa kira, lokacin ya na can cikin high coat su na wasu case har wayar ta gama ringing bai daga ba don wayar ma ta na Do not disturb. Sai da ta masa kira biyar ka na ta hak'ura. Sai bayan sun gama wannan shari'ar ya fito ya koma office d'in don harhad'a kayan shi ya dawo gida sannan ya ga miss calls d'in Anna. Hankalin ta she ya bi kiran lokacin wayar na hannun Fanan. D'agawa ta yi ta re da fad'in, "Ya Fu'ad Binty ce ta dunga kiran ka d'azu". Ajiyar zuciya Fu'ad ya sauke ta re da fad'in, "Ok. Yanzu ina ita Binty ta ke??". "Ta na parlourn k'asa ta na jira na mu wuce islamiya". Fad'in Fanan. "To ke mi kike yi da ba za ki wuce Ku tafi ba". "Yaya uniform ni ke sakawa". Fanan ta ba shi amsa. "To maza Ku wuce, ni ma na kusa dawowa. Zan zo na d'auke Ku idan kun ta shi". Fad'in Fu'ad ta re da yanke wayar. Cikin sauri-sauri Fanan ta k'arisa shirin ta fito ta re da samun Bintyn su ka fita ta re da shiga mota driver ya ja su zuwa islamiya.
Kamar yadda ya Fu'ad ha yi alk'awari, shi ya je har ya d'auko su da aka ta shi daga islamiyan. Suna tafiya a cikin motar Fu'ad ya juyo ya kalli Binty ta re da fad'in, "Ki na ta kira na d'azu da yawar Anna, mi ya faru?". "Dama in tuna maka ne yau saura kwana hud'u inter house d'in mu, kuma ranar za mu yi hutu. Idan ba ka zo ba, za mu kwance da kai". "Aiko kamar na zo na gama, don bazan yarda mu kwance da sanyin idaniya ta ba". "Ya Fu'ad minene sanyin idaniya?". "Sai kin k'ara girma za ko sani. Yanzu ba za ki ga ne ba". "To shikenan, idan na k'ara girma zan zo na tambaye ka". "Ni kuma a wannan lokacin zan fad'a miki". Fad'in Fu'ad ta re da danna horn, Oga Solomon ya bud'e masu k'ofa su ka shiga ciki.
*INTER HOUSE DAY* Finally, yau ce dai ranar da ake gudanar da inter house. Makarantar ta cika sosai da y'an uwa da iyayan yara. Kowa ya na son ya ga k'ok'arin y'ay'an. Anna ma ba'a barta a baya ba.
Binty na hango sanye da Gown irin mai bud'e wan nan a k'asa red colour. Ba shi da hannu sai wani safa irin mai net d'in nan shi ma red colour a hannun ta har guiwar hannu. Gashin nan na ta yasha gyara an nannad'o ta re da saka wasu beat ma su kyalkyali red colour sai aka saki jelar har d'uwawun ta. Fuskan nan ya sha make up. Hannun ta rik'e da wani dunk'ulallan flowers red colour masu kyau a hannun ta. A gaban ta wasu k'ananan yara ne su ma cikin gown red colour hannun su rik'e da flowers. A bayan ta kuma wasu y'an mata ne cikin sport wear red colour su na rik'e da bindin kayanta da ke sharar k'asa. Gyefan daman ta wani kyakykyan yaro ne da ba zai wuce sa'an ta ba cikin shigar suit red colour. Gyefan hagun ta kuma Sabrin ce ita cikin grown red colour ta yi kyau sosai amma fuskan nan a murtuk'e k'iris ta ke jira ta fashe da kuka. A hankali su ke tafiya wasu cikin tawagar su suna watsa masu flowers. Sai sauran tawagar red house kuma, wasu na matching ta re da rubuta welcome to red house. Abun dai gwanin burgewa mutane sai d'auka su ke yi a waya. Sai da su ka je har gaban proprietor su ka gaishe shi ta re sa manyan bak'i ka na su ka dawo matsayar su. Haka gaba d'aya sauran houses 'din ma su ka yi. Bayan an gama gabatar da inter house d'in ne, aka fad'i sakamakon house d'in da su ka zo na farko. Kamar ko da yaushe red house dai ita ta zo na farko, ka na green house su ka zo na biyu sai yellow na uku. Nan aka kira su aka ba su kyaututtuka. Bayan an gama duk wannan, aka soma kiran students d'in da su ka zo first position a ko wa ni aji sai iyaye da kuma d'a/y'ar da aka kira iyayan ta su zo su karb'ar mata result ta re da kyautar ta. Lokacin da aka kira Binty Hisham mai goro a matsayin wacce ta zo na d'aya, Ya Fu'ad ne ya fito ya karb'an mata result d'in ta re da kyautar ta ka na aka masu hoto. Har sun kai tsakiyar fili za su koma wajan zaman su aka sake kiran sunan ta a matsayin mai saurin fahimta da kuma kwanya har PC ya fad'a mata suna Genius bayan ya gama wasa ta wanda a baya Sabrin akewa duk wannan. Wannan karan ma sun kusa isa wajan zaman su aka sake kiran ta aka bata muk'amin *Queen of Lead British* ta re da d'aura mata crown a kan ta. A take Sabrin ta fad'i ta su ma. Sosai hankalin Alhaji Saifullahi ya tashi. Bikin da ba'a k'arisa ba da su kenan. Aunty Junaina su ka yi kan ta su ka sa ka ta a cikin mota sai asibiti. Doctor da ya ke duba ta ya ce masu zuciyar da ke ciwo ne ya motsa sakamakon wani tashin hankali da ta shiga. Kuma idan shawara zai ba su kawai su d'auke ta su yi *CANADA* da ita wajan doctor da ya saba duba ta idan ta shiga irin wannan yanayin. Hankali ta shi Alhaji Saifullahi ya kira can k'asar *CANADA* akan a taimaka a yankar masa ticket d'in had'uwa da Doctor Salis Usman Mai rabo (Julaibib).
*GA SH NAN, ALK'AWARIN DA NA MAKU JIYA NA BI YA. DUK DA DAI BA NA POSTING SATURDAY AND SUNDAY. A SHA WEEKEND LAFIYA*