Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 29

Ba ni da gata - Chapter 29

Ba ni da gata Chapter 29: Ba ni da gata Chapter 29. *PAID BOOK 08128755583* *57-58*🌹 .............Dam! Dam! Dam! Haka zuciyar Binty ke bugawa kamar zai…

2,797 words

*PAID BOOK 08128755583* *57-58*🌹 .............Dam! Dam! Dam! Haka zuciyar Binty ke bugawa kamar zai tsaga k'irjinta ya fito har Kandala da ke gabanta ta na jin bugun k'irjin na ta wanda hakan ya tabbatar mata da lallai Binty ta tsorata da abunda ta ce mata. "Dan girman ubangijin halitta ka da ku tab'a mahaifiyata da y'an uwana, idan ku ka min haka ba ku min adalci ba. Baaba Kandala ka da ki alkhairi da sharri, ka da ki manta na san babu abunda na had'a da ke, amma dalili na ki ke amsar kud'in da ko wani ma'aikacin gwantanin bai samun haka amma na yi shuru na rufa miki asiri don ta sanadin ki na samu duk abunda na ke tak'ama da shi yanzu. *BA NI DA GATA*, ina rayuwa ne a kan bola cike da tarin jahilci da daud'a, amma yanzu na samu ilimi na addini da na boko duk ta sanadiyar Anna da ta mai da ni tamkar d'iyar cikinta ko in ce fiye da hakan, don say ta ri ta min abu ba ta re da ta yi wa Fanan ba. To ki na tunanin zan iya bari wani abu ya cutar da ita ko zuri'arta? Zan iya yin komai don Allah ta rayu in dai ba kauce hanya ba ne. Dan Allah ka da komai ya sa my Anna ta". Fad'in Binty ta re da k'arishe maganar da kuka mai sauti. Tab'e baki Kandala ta yi ta re da harararta ka na ta ce, "Ni ba kuka na kira ki ki min a nan ba, na dai fad'a miki sharud'd'an kin ji. Kuma wallahi ina mai k'ara tabbatar mi ki da cewar fitar da maganar ko rashin bin umarnita shi zai yanki tikitin salwantar rayuwar Anna da y'ay'anta. Kuma da ki ke maganar rama alkhairi da sharri, ni nan idan naga kud'i babu abunda ba zan iya yi ba, ku ma kud'in da aka ba ni, zan iya gyara k'auyan nan kaf in mai da shi ginin zamani, to ya kike tunanin zan iya ganin wad'annan kud'an nan in rintse idanuwana. Ai ba zai yuwu ba". Fad'in Kandala. "Ki ji tsoron Allah, ki tuna ya na ganin duk abubuwan da ki ke aikatawa kuma da sannu za ki girbi abunda ki ke shukawa. Ki gaggawan fad'a min abunda zan maku don in bar garin nan gobe". Fad'in Binty. "Hehehehhh! Kwantar da hankalin ki, da ma kwana ukun za ku yi ku koma, saboda biyo kin da wancan sha-sha-shar ta yi, da ace ba ta biyo ki ba, da ko garin nan ba za mu zo ba, za mu yi abun mu cikin kwanciyar hankali, amma tunda ta biyo ki, dole mu yi hak'uri har sai kin koma. Sannan abu na gaba, mutane biyu ne za ku yi wannan sirrin ta re, sai dai d'aya ba za ta tab'a sanin d'aya ta na sirrin da ke ba. Ke! Wallahi ya kamata ma ma ki dode min don ke kowa k'aunar ki ya ke yi za ki zama ta gaban goshi". Fad'in Kandala ta re da washe hak'ora. Harara Binty ta watsa mata ta re da kau da kai ta na tunanin wannan wani irin sirri ne da za ta yi da wasu. Fatan ta dai Allah ya sa ba abunda zai cutar da Anna ba ne ko kuma ya cutar da wanda ba su ji ba ku ma ba su gani ba. "Ki ta shi ki je ka da y'ar uwar ta ki ta ji shurun ya yi yawa. Dama ni abunda na kira in fad'a miki kenan". Fad'in Kandala. Matar Buba da ke mak'ale a jikin taga ta yi saurin yin hanyar kewaye don gudun ka da Binty ko Kandala su fito su ganta a wajan su ga ne ta ji duka tattaunawar su. Binty ce ta fito ta re da wuce wa sasan Goggo Shatu. Buta ta d'auka kamar za ta zaga ta shige ba yi ta re da had'e kai da bango ta na wani irin kukan da ke fitowa tun daga k'asan zuciyarta. Ba ta tabbatar da lallai cewar *BA TA DA GATA* ba sai yau.yau da ace da iyayanta kusa da ita wa ya isa ya mata wannan abu. Gashi yanzu ta dalilinta ta na naiman jefa wanda ba su ji ba, ba su gani ba a halaka. Ta kusa minti talatin a bayin ka na ta fito. Allah ya so ma babu wanda ya yi k'ok'arin shiga bayin. Amma idanuwanta sun yi ja jawur alamar ta ci kuka ma'ishi. Ko da ta shiga d'akin Goggo Shatu, hankali tashe Fanan ta k'ariso wajanta ta na fad'in, "Sister mai ya faru? Wa ya saki kuka?". Ta fad'i hakane gaba d'aya hankalinta a matuk'ar tashe kamar za ta saki kukan itama. Goggo da ke goga goro a magogi ita ma ta zubo masu idanuwa ta na tambayar abunda ya sa mu Binty. Ita kuwa Binty ganin yadda Fanan d'in ta rud'e saboda ganin halin da ta me ciki, sai hakan ya k'ara zaburar da tashin hankalinta ta saki kukan mai sauti ta re da rungume Fanan d'in ta na fad'in, "Ku ka d'ai gare ni, idan har babu ku ba zan iya rayuwa ba. Wallahi ina matuk'ar k'aunar Anna da zuri'arta. Ba zan ba ri wani abu ya same ku ba, zan iya ba da lafiya da rai na wa ku. Ina son ku Fanan". Binty ta fad'a cikin wani irin rikitacciyar muryan kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Wani irin kuka Fanan ita ma ta saki ta re da k'ara ruk'unk'ume Binty ta ma kasa magana. Goggo Shatu kuwa wani irin jan d'uwawu ta yi ta re da rarrafe ta dafa bango ta mik'e ta rungumo Fanan da Binty ta re da fad'in, "Ku bar kuka y'ay'an nan dan Allah. Ke kuma Binty dole ne ki yi kuka saboda rashin iyaye ai babban abu ne. Mu kan mu run da Hashimu ya mutu katanga ya zube. Ga shi kin zo kin ga irin rayuwar da mu ke yi a cikin k'auye ke kuma ki na can cikin daula wajan mutanan kirki. Ai Kandala ta hwad'i min komai. Kwarankwatsi ni kai na zan so ganin wannan uwa ta ki mai karamci baiwar Allah". Goggo ta k'arishe maganar ta re da mai da kallonta izuwa ga Fanan da ke gunjin kuka. "Goggo ki ce ta dai na kuka dan Allah, wallahi ban son kukan ta. Na san Anna na can gabanta na fad'uwa". Fad'in Fanan. "Kin ji ko? Dan Allah ki bar kuka idan ba so kike kan yarinyar mutane ya yi ciwo ba". Fad'in Goggo ta re da kama hanna yansu ta zaunar da su a bakin gado. Da sauri ta saka bayan hannunta ta goge fuskan ta re da kallon Fanan ta ce, "Sister na bar kukan, dan Allah ka da ki bari kan ki ya yi ciwo kin ji?". Fad'in Fanan ta na k'are share fuskanta. "Na dai na, ke ma ki daina dan Allah". Fanan ta fad'a ta na had'iye kukan da ke tawo mata. "Yauwa y'an albarka ku bar kuka kun ji. Ke kuma Binty addu'a da biyayya shine kawai za ki yi wa marik'anki ki biya su ba kuka ba, kin ji?". Fad'in Goggo. Gyad'a kai Binty ta yi ta na mai had'iye sauran kukan da ke taho mata a duk sa'ar da ta tuna da maganar da Kandala ta yi mata ba cewar idan ba ta amince da sirrin nan ba to a bakin ran Anna da y'ay'anta.

*ABUJA* ............."Anna ni fa zan je Saminakar nan in d'auko su Binty. Gidan ba bu dad'i ko kad'an wallahi. Ke kan ki Anna na san dauriya kawai ki ke yi amma ki na missing d'in su over and over". Fad'in Barrister Fu'ad. Wani wawan kallo Ya Bibi ya bi sa da shi ta re da fad'in, "Yanzu ma za ka iya hawa hanya ka je ka d'auko su". Sosa k'eya Barrister ya yi ta re da kallon Anna da ita kan ta gidan bai mata dad'i. "To ya za mu yi Fu'ad? Dole mu yi hak'uri tunda wajan y'an uwanta ta je, su ma su na da buk'atarta. Ai saura kwana hud'u su dawo". Fad'in Anna. "Ni babu abunda me b'atan rai kamar rashin network a garin. Ba dama ka kira ka ji wani hali su ke ciki". Fu'ad ya sake fad'i. Tsaki Julaibib ya ja ta re da d'aukar key d'in motar shi, dama abinci ya gama ci ta re da kallon Anna ya ce, "Sai na dawo Anna". Ya na gama fad'in haka ya fice daga parlourn. "Anna dan Allah ki bari na je na d'auko su". "Kai ta shi ka ban waje tun da ba ka da hankali". Anna ta fad'a ta re da hararar shi. "Na yi shuru to". Fu'ad ya fad'a ta re da gyara kwanciya a kan three sitter.

..............Yaune su ka cika kwana hud'u a Saminaka, kuma yau ne su ke shirin komawa Abuja. Kwana hud'un nan kawai Binty da yi bala'in ramewa saboda tunanin abunda Kandala ta fad'a mata. Mak'ota sai kawo tsaraba su ke su na basu dangin su kalwa, kub'ewa, kuka, barkono, da shambo har da su goruba da taura. Sai da su ka cika babban bako na kayan tsaraba. Goggo Shatu kuwa har da matsar kwalla ta re da musu alk'awarin in sha Allah za ta zo. Shatar mota Kandala ta yi masu har garin Abuja. Kasancewar fitar sassafe su ka yi, k'arfe hud'u a Abuja ta musu, kuma da ya ke mota ce golf mai kyau kuma driver ya san hannunsa. Gaban Binty fad'uwa ya ke yi sosai duk san da ta tino da maganar Kandala. A k'ofar tank'ameman gate d'in ya yi parking su ka fito. Kandala ta biya shi kud'in sa lokacin tuni har Fanan ta isa gate ta re da kwankwasa gate. "Who be that". Fad'in Oga Solomon. "It's me, open the gate". Fad'in Fanan a gajiye saboda zaman motar da su ka yi". Bud'e gate d'in ya yi ta re da washe hak'ora. "Welcome back madam". Fad'in Oga Soloman. "Welcome". Fanan ta fad'a a gajarce ta re da shiga ciki Binty na biye da ita a baya. "Ah'ahhh beauty, beauty. Welcome home". Solomon ya fad'a ya na washe ba ki. Murmushi kawai Binty ta masa ta re da wuce sa. Kandala kuwa sai k'ik'i k'ik'i ta ke da k'atuwar bakon hannunta. Tab'e baki ya yi ka na ya juya ya kalli Baban Haruna ta re fad'in "Helf that human carry her load". Tasowa Baban Haruna ya yi ta re da d'aukar jakar ya d'aura a ka ita kuma ta shige ta na hararar Solomon. Kasancewar akwai nisa tsakanin first gate da ainahin cika gida, Binty da Fanan kamar za su fad'i don gajiya. Barrister Fu'ad ne ya fito daga part d'in sa sanye da kaftan kasancewar yau juma'a ce kuma bai je aiki ba, yanzu ne ya ke son ya fitan. Idanuwansa ne ya sauka a kan Binty da ke tafiya da kyar kamar an tilasta mata tafiyar. "Bintyyyyyyyyyyy!". Barrister Fu'ad ya fad'a da k'arfi kuma cike da jin dad'i. Cikin sassarfa ya nufi wajansu ya na washe bakin jin dad'in dawowar ta su. Ita kuwa Binty sai ta k'ara shagwab'ewa ita alan dole ta gaji. "Wannan wani irin surprise ne mai dad'i haka? Gaskiya na ji dad'in dawowar ku. Dubi tantabarun gidan nan, su kan su dad'in dawowar ku su ke ji gasu nan sai oyoyo su ke maku". Fad'in Barr Fu'ad ya na nu na tantabarun da gaba d'ayan su su ka sauko k'asa gwanin sha'awa. "Yaya we miss you irin lodi-lodi d'in nan". Fad'in Binty. Fanan kuwa d'aura kanta ta yi a kafad'ar shi ta na fad'in, "Yaya garin akwai nisa, we're very tired". "Ai ni ma na fasa fita, muje ciki". Fad'in Barr Fu'ad ta re da rik'o hannunsu. Kandala kallon bayansu ta yi ta re da tab'e baki ta na harararsu. Ba bu kowa a parlour gaba d'ayansu sama su ka yi su na kwad'a kiran sunan Anna. Anna da ke zaune a parlour ta na tunanin autares d'inta ta jiyo muryansu. Cikin sauri ta mik'e ta re sa nufar k'ofar parlourn. Kicib'is su ka yi da juna, aikuwa gaba d'aya suka daka tsalle su ka d'are jikinta. Rungume su ta yi ita tana jin dad'in ganinsu. "Ya aka yi ku ka dawo yau? Ai na d'auka sai kun yi sati ka min ku dawo". Fad'in Anna. "Anna kewarku ce ta hana mu sukuni wallahi". Fad'in Binty. "To ku dawa ku ka dawo?" Fad'in Anna. "Mu da Baaba Kandala, ta na parlourn k'asa". Fanan ta fad'a. "To maza aje ayi wanka ayi sallah azo aci abinci". Fad'in Anna ita kuwa ta sauka zuwa wajan Kandala. Barr Fu'ad ku ma wani tsallan murna ya yi na jin dad'in dawowar sahibar shi. Su Binty kuwa bayan sun yi wanka sun yi sallah, ko bi ta kan abinci ba su yi ba su ka bi lafiyar gado don yin baccin gajiya. Ko da Anna ta sallami Kandala wacce ta yi da ita a kan ta kwana gobe ta juya amma ta yi ta kawo mata excuses akan akwai buk'atar komawarta yau. D'akin su Bintyn ta shiga ta tadda su su na ta sharar barcin gajiya. Ta da su ta yi ta re da fad'in, "Ku ta shi daga wannan barcin haka, haramun ne bacci bayan la'asar". Haka nan ba don sun so ba su ka tashi. Abincin ma zai ciwu musu ba sai after isha'i lokacin cin abincin dare Wanda su ne na k'arshan zuwa kan dinning d'in. Kallo d'aya yaya Bibi ya yi masu ta re da d'auke kan sa ya na mamakin yaushe su ka dawo amma ya basar don bai son raini. "Yaya Bibi ina yini?". Su ka had'a baki wajan fad'i. "Lafiya". Ya fad'a a tak'aice ta re da cigaba da cin abincinsa. As usual shi ya riga su ta shi ta re da goge bakinsa da tissue ya fita. Kai tsaye d'akin Suhail ya nufa. Key ya saka ya bud'e ta re da shiga ka na ya mai da k'ofar ya rufe. Har k'uryan d'akin ya shiga inda Suhail ya ke a k'ulle da kaca a k'afarsa har hannu. Key ya saka ya bud'e kwad'on ta re da kwance masa hannun ya kuma yage seletep d'in da ke bakinsa ka na ya ce, "Ka shirya yin magana ko mu cigaba a haka?". Fad'in Julaibib. Tsabar taurin kai irin na Suhail ya k'i magana. "So be it". Fad'in Julaibib ta re da fiddo burger a cikin aljihunsa ya mik'a masa. Cikin sauri ya karb'a ya cinye ya na hawaye. Mai da kwado ya yi ta re saka masa seletep d'in a baki ka na ya juya zai fita. Ni shi sosai Suhail ya soma yi alamar ya na son yin magana ta re da girgiza kansa. Dawowa baya Julaibib ya yi ta re da yage seletep d'in bakinsa ya ya na kallon shi. "Dan Allah ka yi hak'uri yaya Bibi, wallahi zan yi magana, zan fad'a". Fad'in Suhail. Duk'awa ya yi a gaban Suhail d'in ta re kallonsa alamar ina jinka. "Kusan kaf yaran da ake kawo wa daga k'auyan don su yi aiki a gidan nan, sai na yi amfani da su duk k'ank'antarsu. Akwai wata ma da har ta baya na ke amfani da ita, yarinyar da ke wajan Anna ma sau biyu ina yunk'urin keta mata haddi amma Allah bai ba ni nasara ba"... "What?". Julaibib ya fad'a a matuk'ar k'ausashe ta re da d'auke shi da wani magigicin mari sai da jini ya fito daga ramukan hancinsa. Ta ke ku ma ya ji d'au sautin sa ya dod'e na wucin gadi. "Fad'a min, ka yi mata wani abu ko baka yi ba? Na ce fad'a min ko in kashe ka a d'akin nan". Julaibib ya fad'a ya na haurin ko ina ya samu a jikinsa, har a gabansa da ke a kumbure saboda dukan da ya masa wancan lokacin. "Wallahi wallahi wallahi ban mata komai ba, na farko Fu'ad ya kawo mata d'auki, na biyi kum.....". Wani naushi da ya kai masa a ciki ne ya saka ya yi saurin shanye maganar da zai yi saboda azabar da yaji. Da gudu Alhaji Usman da ke kallon duk abunda ke faruwa daga d'akinsa na side d'in haijya Mansura, kasancewa a kowa ni part ya na da computer da ku ma CCTV a wajan, ya fito da gudu ya hajiya Mansura ma ta biyo bayansa kasancewar ta ga fitowarsa. D'akin Fu'ad d'in su ka nufo hajiya Mansura na biye da shi a baya, hankali ta she kasancewar d'akin tilon d'anta namiji wanda ta kuma kwallafa rai a Kansa. Shigansu d'akin ya yi dai-dai da lokacin da Julaibib ya saka k'afa ya take gaban Suhail d'in. A take kuwa ya numfashinsa ya tsaya cak, idanuwansa su ka kakkafe.

Please manage za mu had'e gobe.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull