Ba ni da gata - Chapter 30
Ba ni da gata Chapter 30: Ba ni da gata Chapter 30. 🌹 *59-60*🌹 ............."Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Julaibib mai yasa ba ka amfani da…
3,463 words
🌹 *59-60*🌹 ............."Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Julaibib mai yasa ba ka amfani da hankali idan za ka yi hukunci ne? Yan zu idan ya mutu fa? Ka san jagulewa zai yi ya dawo kan ka ko. Ka rik'a abu da natsuwa mana". Fad'in Alhaji Usman rai b'ace ta re da nufar in da Suhail d'in ya ke a kwance ba ya numfashi. Kuka Hajiya Mansura ke yi kamar za ta shid'e na ganin halin da tilon d'anta namiji ya ke ciki. "Ya mutu ko Alhaji? Wani irin mugunta da azaba ne haka? Ai ko kisan kai ya yi sai haka. Dubi irin yadda aka k'ulle shi da kaca sai kace k'asurgumin b'arawo". Hajiya Mansura ta fad'i ta na sharar hawaye. "Umarni na ke ba ka a matsayina na mahaifinka idan har na isa kuma ina da wannan matsayin. Ka duba d'an uwanka ka na shi taimakon gaggawa yanzu haka". Tsabar zuciya Julaibib ya shiga taune harshansa jikinsa na wani irin rawa kamar yana k'asar Moscow ba suwaita a jikinsa. "Ba ka ji abunda na ce ba ne Salis?". Alhaji Usman ya fad'a a tsawace ya na kallon cikin idanuwan Julaibib da su ka rine kamar gauta kuma still ya na taune harshansa. A hankali ya ta tawo har inda Suhail d'in ya ke a kwance ya duk'a ta re da d'aura d'an yatsansa biyu a wuyansa da kuma k'ofofin hancinsa. Ka na ya mik'e ya isa in da goron ruwa a kan center table ya bud'e ta re da tsiyayar ruwan ya dawo wajan Suhail d'in ta re da shafa masa ruwan cike da mugunta. A matuk'ar razane ya farfad'o ta re da wawwaro idanuwa ya na fad'in, "Na tuba, wallahi ba zan sakewa ko wacce yarinya fyad'e ba. Wallahi ita ma ban mata komai ba". Fad'in Suhail. "Wani magana ya ke yi haka? Wa ya yiwa fyad'en a cikin gidan nan?". Fad'in Hajiya Mansura a birkice. "Fito da mota mu kai shi asibiti, ba ka ganin yadda gaban shi ya kumbura". Fad'in Alhaji Usman ta re da k'ok'arin warware sark'an da ke jikinsa. Mik'a masa key d'in da ya kulle kacan Julaibib ya yi ta re da ficewa daga d'akin ya nufi side d'in Anna rai b'ace. Ganinsa kawai su ka yi a kansa. Ba su kad'ai ba hatta Anna sai da ta tsorata da yanayin sa. Barr Fu'ad kuwa wani k'undunbala ya yi kasancewar ya na kan kujera ne ya na facing su Binty da har yanzu su ke kan dinning duk da sun gama cin abinci su na baiwa Anna da Ya Fu'ad d'in labarin k'auye. Kau kau kau! Julaibib ya tsinke fuskan Binty da mari hagu da ya sa ta ji tsigar jikinta ya tashi ta re da jin wani shocking na bin jikinta saboda azabar marin da ya sauka akan kuncinta. "Ubbbban... Me yya kkai ki d'd'aakin Suhhaiil har ya nai mi rrraping d'inki?". Fad'in Julaibib cike da in'ina. Daga Anna har barrister waro idanuwa su ka yi ta re da fad'in, "Raping kuma?". Binty kuwa hanyar nai man wajan b'uya ta ke yi amma ba hanya don ya yi fankan-fankan a kan hanya. Jikinta sai b'ari ya ke yi ta ma kasa kuka sai fiki-fiki ta ke yi da idanuwa. Hannu ya k'ara d'agawa zai wanketa da mari ta saki wani gigitaccan k'ara don ta tabbatar wannan karan idan har ya samu fuskanta to babu shakka sai ta kurmance. Caraf Anna ta rik'e hannun ta re da tura shi gefe amma ko motsi bai yi ba, sai taunan harce ya ke yi da har ya soma jini. "Kar ka sake tab'a ta Julaibib. Wallahi ka sake tab'a y'ar nan sai ranka ya mummunar b'aci. Sakarai kawai wanda wanda bai iya controling fushin sa ba". Fad'in Anna, amma can k'asan zuciyarta dad'i ta ke ji saboda wani abu da ta hango a fuskan d'an na ta. Huci ya ke yi kamar za ki, can kuma ya juya ta re da ficewa daga d'akin kamar zai fashe. Hanyar gate ya nufa. Fitar shi ko minti d'aya bai yi ba, Alhaji Usman ya shigo ta re da fad'in, "Maza Fu'ad fito mu kai d'an Uwanka asibiti bai da lafiya, d'an uwanka ya masa mummunan illa". Fad'in Alhaji Usman. Saurin bin bayansa Fu'ad ya yi, Anna ma ta bi bayansu hankali ta she. Numfashin Suhail sai sama da k'asa ya ke yi kamar zai tafi gaba d'aya. Ya yin da Hajiya Mansura ke tsugunne ta tallabe da kansa ta na kuka sosai. Ita kan ta Anna ganin yadda gaban Suhail ya wani irin kumbura sai da ta na da baya ta dafe k'irji ta na salati da sallallami. Ciccib'arsa Fu'ad ya yi har wajan mota, Alhaji Usman ya shiga gidan gaba, Anna da Hajiya Mansura su ma su ka shiga. Kan Suhail na kan cinyar Anna sai fad'in, "Na shiga uku na lalace, wallahi mutuwa zan yi". Duk ya ce haka sai Hajiya Mansura ta tsananta kukanta. Anna ce ke shafa kansa ta re da tofa masa addu'a a kansa har su ka isa asibiti.
*________________* Tun su Binty na tsammanin ganin su Anna nan kusa har bacci ya yi awon gaba da su cike da zullumin abunda ya faru, barin ma Binty da ke tunanin ta yaya ya Bibi ya san Suhail ya yi yunk'urin yi mata fyad'e. Fanan ma sai da ta mata wannan tambayar, kuma ba ta b'oye mata komai ba ta shaida mata komai da ya faru a wancan ranar. Ranar dai daddare Yousouf bai gane kanta ba, kuma ya yi da ita ta fad'a masa abunda ke damunta, amma sai ta ce masa ita babu abunda ke damunta kawai gajiyar tafiya ce. Haka ya hak'ura ya kyaleta. Da kumburarriyar fuska Binty ta tashi, sai dai still ba su ga Anna a gida ba hakane ya tabbatar masu da Anna a can ta kwana. Ko karyawa sun kasa yi, duk sun yi jugum-jugum a parlour su na jiran dawowar Anna ko ya Fu'ad. Murd'a handle d'in kofar aka yi za'a shigo. Gaba d'aya suka zubawa k'ofar idanuwa su na jiran ganin wa zai shigo. Wani irin mik'ewa su ka yi gaba d'ayansu cike da tsoro. Don Binty har wani zawo-zawo ta soma ji kamar zai zubo mata. "Zo nan". Julaibib ya fad'a ya na kallon Binty. Alamu ya nuna ba a gidan ya kwana ba. Domin kayan jiya ne a jikinsa. Jikin Binty na rawa ta taka ta isa gaban shi ta re da fad'in, "Yaya Bibi ina kwana?". Ta fad'i haka muryanta na rawa sosai. "Ki had'a min tea ki kawo min d'aki na yanzun nan". Ya fad'a ta re da juyawa ya fice. A tare su ka sauke ajiyar zuciya ita da Fanan. "Wallahi ki yi sauri, don dad'ewarki zai jawo maki wasu zafafan marukan da yafi na jiya dama gashi fuskan ta ki ba ta gama sacewa ba". Fad'in Fanan. Ba ta re da Binty ta ce komai ba, ta isa wajan dinning d'in ta re da tattaro duk wani natsuwarta ta soma had'a shayin. A kan wani kyakkyawan ture ta d'aura ka na ta kalli Fanan ta re da fad'in, "Sister dan Allah ki raka ni". Da gudu Fanan ta yi stairs, sai da ta kai na k'arshe ka na ta tsaya ta re da juyowa ta ce, "Wallahi idan kin ganni a lahira kai ni aka yi. Ke dai ki je tunda ke ya sa. Yanzu ina bin ki zan jawo wa kai na duka da sassafe ban karya ba ga shi Anna ba ta nan balle ta ceceni". Rausayar da kai Binty ta yi idanuwanta sun yi kwal-kwal ta re da nufar k'ofar. Ta kusa minti biyar a bakin k'ofar shi ka na ta saka hannu ta kwankwasa. Sai da ta yo knocking sau uku ba'a amsa ba. Har za ta aje farantin a k'ofar d'akin wani zuciyar ya gargad'eta. Murd'a handle d'in ta yi ta re da shiga ciki. Babu kowa a parlour. Wajan center table d'in shi ta nufa ta re da d'aura parantin. A nan ta ci karo da wani k'aramin paper da wani kyakkyawan gajeran rubutu. D'aukar papern ta yi ta soma karantawa cikin zuciya kamar haka, "Ki zauna ki jira ni har in fito". Gabanta ne ya buga dam ta re da fad'in, "Kashi na ya bushe billahil lazi". Jikinta na rawa ta d'an d'osana d'uwawunta a kan kujeran 1sitter sai rarraba idanuwa ta ke yi. Kusan mintuna sha biyar ka na ya fito sanye da sweatpant da rigarsa farare k'al-k'al. Gashin kan shi sai shinning ya ke yi. Ga kwantaccan sajansa da ke k'ara masa kyau. Agogon hannu ya ke k'ok'ari sakawa a hannunshi. Kallo d'aya ta yi masa ta re da saurin kau da kai gudun ka da ta yi laifi don ta ga alamar ya tsani kallo. Julaibib kuwa ya na kallonta ta gefen idanuwa ta re da tab'e bakinsa. Ba ta re da ya ce mata komai ba ya nai mi waje ya zauna a kan 2sitter ta re da jawo farantin kusa da shi ya d'au cup d'in ta re da kai shi ba ki ya yi sipping shayin. Saurin aje cup d'in ya yi ta re da kallonta da har hantar cikinta sai da ya katsa. Had'a wani wannan ya yi min sanyi". Yanda ya yi maganar kamar ba daga bakinsa ya fito ba. Jiki ba kwari Binty ta mik'e ta re da yin hanyar k'ofa. "Dawo wan". Ta tsinkayi muryansa a cikin kunnanta. A hankali ta dawo baya ta re da fad'in, "Ga ni yaya Bibi". "Na gan ki. Ina za ki je da ki ka yi hanyar k'ofa". Fad'in Julaibib. "Zan je part d'in mu ne in had'o maka wani tea d'in". Binty ta fad'a ta na kallon k'asa. "To ki je ga kitchen can ki had'o a can. Kuma ki min sauri". Fad'in Julaibib ta re da nu na mata hanyar kitchen d'in. Sum-sum ta nufi kitchen d'in. A tsanake ta had'a komai ka na ta dawo parlour ta aje masa a kan center table d'in da ke gabansa. "Zauna ki jira ni". Ya fad'a a tak'aice ta re da d'aukar cup d'in ya soma sipping ya na lumshe idanuwa. Zama ta yi kamar yadda ya buk'ata. Sai da ya gama shanye tea d'in ya aje cup ka na ya juyo ta re da fuskantarta. "Ina son ki bud'e bakinki ki fad'amin gaskiya. Domin gaskiyar ce za ta cece ki. Kin san dai daga ni sai ke a d'akin nan ko? To gwara ki fad'a min gaskiya". "Zan fad'a maka gaskiya duk abunda ka tambaye ni yaya Bibi". Fad'in Binty. "Good". Fad'in Julaibib ta re da k'ara gyara zama ya na fuskantarta. "Sau nawa ya tab'a amfani da ke?". Dam dam gabanta ya buga ta zuba masa idanuwa ba ta re da ta iya cewa komai ba. "Ba ki ji tambayar da na miki ba ne?". Fad'in Julaibib ta re da watso mata idanuwansa. "Yaya ban gane tambayar ka ba ne". Binty ta fad'a. "Ina nufin sau nawa Suhail ya kwanta dake a d'akinsa". Waro masa idanuwa ta yi har da su dafe k'irji sai da ta ba shi dariya amma ya gimtse don ba wasa ya kira ta ya mata ba. Shi ma waro mata idanuwan ya yi. "Wallahi wallahi wallahi ko sau d'aya bai tab'a ba. Ya dai tab'a yink'urin yi min fyad'e Allah ya tseratar da ni". Fad'in Binty ta na son fashewa da kuka. "Shshsss! Ba kuka na kira ki min ba, naji bai tab'a. Kuma ki bud'e kunnan ki da kyau, ka da ki kuskura ko a cikin mafarki na in gan ki da wani ko hannun ki ya rik'e , idan haka ta faru, karya ki zan yi. Don ni ba yayan banza ba ne da zan bar k'annai na su lallace a banza ba. Kin dai ji abunda na fad'a miki ko?". Fad'in Julaibib har da rik'e kunnansa. Cikin sauri ta gyad'a kanta ta na share hawayan da ya silalo mata daga idanuwanta. "Yauwa. Kuma maza yanzu ki je ku karya ke da Fanan, idan kuma ku ka k'i karyawa, ni zan zo na karya ku". Fad'in Julaibib ta re da mik'ewa ya nufi bedroom d'in sa. Binty na ganin haka, ta fice da sauri har da had'awa da gudu-gudu.
Sai da ta ganta a bedroom d'in su, ka na ta sauke ajiyar zuciya. Kallo Fanan ta yi wacce ta lullub'e har kai ta re da fashewa da dariya ta kuma yaye bargon. "Ya aka yi, dukan ki ya yi ko?". Fad'in Fanan. "Eh. Ke ma ya ce ki je ki amshi na ki rabon". Fad'in Binty. "Dan Allah ki bar wasa ki fad'a min gaskiya". Fanan ta fad'a. "Gaskiyan kenan ya ce idan har ba mu karya ba, shi zai zo ya karya mu". Fad'in Binty. Wani wuntsilowa Fanan ta yi ta re da nufar k'ofa Binty ta mara mata baya. Su na cikin karyawarne Anna ta turo k'ofa ta shigo. Da gudu su ka nufe ta su ka rungume ta tare da fad'in, "Anna we miss you". "Ni ma haka. Yayan ku Suhail ne jikin sai dai Alhamdulillah, yanzu haka ma cuku-cikun fitar da shi k'asan baban ku ke yi". "Ayya Allah ya ba shi lafiya". Fad'in Fanan da Binty. Ta re su ka haura sama, Anna ta shiga d'akinta domin yin wanka ta kuma karya. K'asan ranta kuma ta k'udurta yin banza da Julaibib ta re da share sa saboda irin b'arnan da ya tafka. Don Suhail dai sai an kai shi India saboda mazantakarshi ta samu matsalar da ba zai tab'a iya mu'amala da mace ba har sai an masa aiki shi ma babu tabbacin zai warke ya dawo normal.
..........Bayan Kwana uku Hajiya Mansura da da Suhail har da Fu'ad wanda ya d'au excuse wajan aiki su ka lula India domin rashin lafiyar Suhail. Sai da Alhaji Usman da Fu'ad sun dawo bayan kwana biyar saboda aikin su ya yin da su ka bar Hajiya Mansura da babbar y'arta mace wacce ta zo daga baya.
Anna kuwa Sam ta fita daga harkan Julaibib, ko gaisheta ya yi daga Lafiya babu abunda ta ke k'ara ce masa. Binty kuwa kasancewar Kandala ba ta sake mata magana ba akan sirrin da ta ce za su yi ita da wasu, sai hankalinta ya kwanta har ta tattara zancan ta watsar da shi. Wanda shurun da taji ya samu ne saboda tafiya jinya da Hajiya Mansura ta yi. Binty Kuwa kusan duk bayan kwana biyu sai sun had'a dabara ita da Fanan wacce ke taimakonta wajan had'uwa da sahibinta wato Yousouf wanda yanzu soyayyarsa da k'aunarsa ya wuce misali a zuciyarta. Yauwa kamar kullum sun had'u a wonderland su na shan soyayyarsu. Yousouf ya kalleta ta re da fad'in, "Mai sona, ni fa na gaji da wannan b'oye-b'oyen da muke yi. Dan Allah ki gabatar da ni a gidan ku muyi aure. Wallahi ba zan hanaki karatu ba". Fad'in Yousouf. Dogon ajiyar zuciya Binty ta sauke ta re da fad'in, "Reality". "Na'am mai sona". Yousouf ya amsa ya na kallon ta. "Akwai wata magana mai mahimmanci da na ke so muyi da kai wanda na dad's ina son yi maka amma ina jin tsoran rasa ka". Ta fad'i hakane idanuwanta na ciccikowa da hawaye. Tuni hankalin Yousouf ya ta shi sosai saboda ganin hawaye kwance cikin idanuwanta . Cikin sauri ya tashi ta re da zagayowa ya duk'a a gabanta ta re da fad'in, "Idan har akwai ranar da hawaye za su zubo daga idanuwanki idan ba na farin ciki ba ne kuma a gaba na, to zan yi fatan mutuwata ka min wannan ranar mai sona. Dan girman Allah ka da ki bari wannan hawayan su zubo a kan kyakkyawan fuskanki". Fad'in Yousouf in a cracking voice shi ma kamar zai yi kukan. Saurin mai da hawayan ta yi ta re da kallon shi ka na ta ce, "Reality za ka iya had'a zuri'a dani ko da ace ni d'in *BA NI DA GATA*? Ina nufin ban da uwa kuma ban da uba, babu dangi da zan yi tutiya ta re da nunawa duniya in ce wad'annna jini na ne". "Mai sona, wace irin magana ce wannan? Har ki na da shakku haka a kai na? wallahi Allah ka nan, ko da ace cutar HIV ki ke da ita, zan iya zama da ke a matsayin matata kuma inyi kowaccce irin mu'amala na aure da ke, idan na ce mu'amala ina nufin ko wacce. Ina fatan kin fahimce ni". Jijjiga Kai Binty ta yi ta na jin wutan k'aunar shi na ruruwa a zuciyarta. "Reality ni d'in nan da ka ke gani ba kowa ba ce face wacce ta ke cin arziki a gidansu Fanan. Babu wata alak'a tsakanina da su na jini sai tarin kyautatawa da soyayyar da ta haifar har na ke jin tamkar ni su d'in jini na ne. Ban san kowa nawa ba. Ta shi na yi na tsinci kai na a bola har Allah ya had'a ni da mutanan arzikin da su ka d'auke ni kamkar y'arsu ta cikinsu. Mai zan yi wa mutanan nan da su ka mai da ni yadda na ke yanzu". Binty ta k'arisa maganar ta re da k'ok'arin mai da kukan da ke taho mata. Ajiyar zuciya Yousouf ya sauke mai k'arfi ta re da fad'in, "Wannan shine abunda tashin hankali da har ki ke son yi min asarar hawayan ki? To ki sani, ni zan aure ki a duk yadda ki ke. Ko kin manta da alk'awarin da mu ka yi wa junan mu ne? Ba ki da matsala da ni da kuma y'an uwa na. Saboda haka ka da in k'ara ji kin ce *BA KI DA GATA*, Allah shi ne ga tan ki, kuma ni ne nan gatan ki". Fad'in Yousouf. "Nagode da k'aunar da ka ke nuna min a ko wani irin hali". "I love unconditionaly Binty". Fad'in Yousouf. "Same to me here". Binty ta fad'a ta na mai sakar masa murmushi. "Haba ko ke fa, ta shi in miki wak'a kin ji masoyiya". Fad'in Yousouf. Mik'ewa ta yi, shikuma ya bud'e wayar shi a key ka na ya shiga video ta re da soma d'aukarsu ta re ya na bin wak'ar kamar haka, 🎻 _*Duba ki ga yadda son ki yai mini, duk da na san ki na sa ne. Ki kalli cikin idanuwa naahh na san za su zayyane. Wannan al'ajab na so neee da k'auna, aiki na kiran ki ne. Dana fad'a kiji, ki ba ni agaji, in dai na rangajiii ki d'an yi tsokaci. Ki ba ni ma'ajih, ba zancan nagaji, ki kauda k'uduji, a so b yaaji. Labarin zuciyaaah, ni za ki tambaya, abinda nakkajiiii ya zarce duniyaaah. Idan na waiwaya, ko ko na sunkuya, amsar guda na ke ji kin zaman habibiya. Da sonki na banu, a kan ki na sanu, abunda baki so nai nai tai in bar shi na hanu, ke da sirri zai ganu, ki damk'am a hannu, shi zai fi min yau sauk'i in bar maganganu. Ki zo ki daf dani, so zai min lahani, ki tausayawa ruhina ki ce ki nai da niiii. Ba na ji ban gani, to wa zai kula da ni, I Dan ya zamma sab'aninki to a bar ni ni. Ina k'ulafuci, sai kin ci za ni ci, har wanda za na cin ki ci tun da ba bu rikkici. Ya za ai in burge wacce na ke so da k'auna, ya zaaa'ayi? Kalamai na sun kad'anta fahimce ni sannan ba hanyaaa. Kalamainaah sun kad'anta fahimce ni sannan baaa hanyaah. Ina so ta soni ni ba guru ba bu laya, babu d'age babu k'arya, ni bani san riyah. Ba dan kwalliya ba kuma ba dan dukiya ba, ba dan zantuka ba kullum tai min maraba. Ina son ki , ina son ki , ina sonki. Ina son ki so na gaske ba yaudara ba. Ina son ki, ina son ki, ina son kiiii. Ina son ki so na gaske ba yaudara baaaaah*_🎻 Ya k'arisa ina son ki so na gaske ba yaudara ba ta re da kashe wayan ya na kallon idanuwanta. "Ina son ka ni ma yousouf ba da yaudara ba". Fad'in Binty. "Naji dad'i sosai da na saki cikin nishad'i. Wannan videon shi ne zai zama abun kallo na through out yau idan na koma gida". "To ni ma ka tura min". Fad'in Binty. "Ina son ka, zamu kasance ta re har abada". Fad'in Binty. "Wannan maganar mai dad'i da ki ka min ma kawai ya ishe ni. Shiva xender in tura miki, ko kuma zan tura mi ki ta WhatsApp". Fad'in Yousouf. "OK to shikenan, raka ni gate, ka min sister ta fara jera min kiran da zai kashe min waya yanzu". Fad'in Binty. "You wish is my command my lady". Fad'in Yousouf ta re da yin gaba ta na biye da shi a baya.