Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 31

Ba ni da gata - Chapter 31

Ba ni da gata Chapter 31: Ba ni da gata Chapter 31. *________________* ............Abu kamar wasa, sai da su Suhail su ka washi wata tara a India ka min…

3,309 words

*________________* ............Abu kamar wasa, sai da su Suhail su ka washi wata tara a India ka min Suhail ya samu sauk'i cikin hukuncin ubangiji, kuma ya yi wa kan sa alk'awarin da Binty zai fara gwada lafiyar mazantakarsa. Ya yin da a gefe guda Hajiya Mansura ta yi bala'in rama saboda sawa zuciyarta soyayya da sha'awarta cikin zuciyarta ta re da k'osawa su dawo Nigeria domin nufar da k'udirinta. Yau dai su ka duro k'asar, Julaibib bai yi jinkiri ba, har d'akin uwarsa ya tadda sa ta re da shimfid'a masa concrete warning akan y'an aikin gida da kuma Binty wacce ya yi masa alk'awarin ko yatsarsa ya yi k'ok'arin kai wa jikinta, wannan karan mazantakar na shi gaba d'aya zai cire masa. Kuma a gaban Hajiya Mansura ya fad'i haka wanda ya kusa saka ta fitsari a tsayan da ta ke yi saboda hango wani b'oyayyan sirri a idanuwan Julaibib a game da Binty wacce ta d'auki d'amarar mai da ita abokiyar shaid'ancin ta. "Lallai akwai babban bala'in da ke tunkaro gidan nan soon akan duk wanda ke k'ok'arin shiga tsakani na da buri na". Fad'in Hajiya Mansura cikin zuciyarta.

*BAYAN SATI GUDA* ............Wayar Binty ce ta yi k'ara alamar shigowar kira. Kallon screen d'in wayar ta yi. Gabanta ne ya buga da mugun k'arfi har sai da ta dafe k'irjin na ta ganin sunan Kandala b'aro-b'aro a jikin screen d'in. Hannunta na rawa ta d'aga wayar ta re da karawakarawa a kunnanta ba ta re da ta yi ko tari ba. "Yanzu nan ki je d'akin Hajiya Mansura, kuma ka da ki saki wani ya gan ki. Ina fatan kuma ba ki manta da sharud'd'an da na karanto miki ba idan ki ka sab'a?". Fad'in Kandala. "Ban man ta ba". Fad'in Binty ba ki na rawa. "Madallah. Sai ki hanzarta". Fad'in Kandala ta re da yanke wayar.

*PAID BOOK 08128755583*

*YAN ZU BA ZA KU RIK'A GANIN UPDATE DA SASSAFE BA SABODA AN KO MA SCHOOL KUMA NI D'IN TEACHER CE. DOLE SAI NA DAWO DAGA SCHOOL SANNA ZAN MA KU TYPING NAGODE* : 🌹 *61-62*🌹

💃🏻🔥🔥 _Ku na inahh nee?🗣️ to maza ku firfito ka da wannan garab'asar ta wuce ku. Shin ko kun san Mrs Abubakar ta k'ara zuwan maku da zuma gangariya mai jawo maki martaba da soyayya a wajan mijin ki?_

_Ta shi maza ki karb'o kud'in adashen ki da ki ke zubi wajan Ladidi domin ki siya ke ma ki zama sarauniya_💃🏻💃🏻💃🏻 _Gangarar gangariyar zuma mai k'ara kuzari da ni'ima ta re da k'ara miki sha'awa. Ta na sa ka wani dad'i da d'and'ano na musamman ta re da saka mai gida sambatu da zumar miyau 🙈 da gigicewa. Wannan zuma guarantee ne sai kin gwada na tabbata sai kin godewa Hassana (Mrs Abubakar). Haka kazalika ina macen da ke k'orafi akan miji bai kai mata? To kwantar da hankalin ki Mrs Abubakar ta kawo miki waraka da izinin Allah domin idan ki ka yi amfani da wannan zuma mijin ki zai jima bai yi inzali ba kuma ya na k'ara ruwan maniyyi da lafiya a jikin mai gida_ _Maza garzaya ki nai mi Mrs Abubakar a lambar wayarta kamar haka_ _+234 814 193 4442_ _Sayan nagari, mai da kud'i gida_🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️💃🏻💃🏻🔥

...............Gaba d'aya hankalin Binty ya gama tashi musamman da ta ji part d'in Hajiya Mansura za ta. Tunanin ta dunga yi wani sirri ne za su yi da Hajiyan da har za ta kafa mata wad'annan sharud'd'a haka. Da kyar ta iya jan k'afafuwanta ta sauko daga sama. Babu kowa a parlourn, hakan ya mata dad'i. Cikin sauri ta fita daga part d'in ta yi part d'in Hajiya Mansura ta na waige-waige. Murd'a handle d'in k'ofar ta yi gabanta na dukan tara-tara don ba ta san abunda za ta taras ba. Ba bu kowa a parlour, kai tsaye stairs d'in ta hau ta isa k'ofar d'akin Hajiya Mansura zuciyara na tsananta bugawa. Kwankwasawa ta yi, da ga ciki Hajiya Mansura ta ce ta shigo. Tura k'ofar ta yi ta re da shiga zuciyarta na bugawa. Tsaye ta sa mu Hajiya Mansura hannunta biyu goye a bayanta ta kuma zuba mata idanuwa. "Ina wuni Hajiya". Fad'in Binty bakinta na wani irin rawa. Wani malalacin murmushi Hajiya Mansura ta yi ta re da matsawa kusa da Binty ta kamo kafad'unta ta re da zaunar da ita a bakin gado ka na ta duk'a a gabanta ta na kallon tun daga kanta har k'afafunta ka na ta ce, "Binty ki kwantar da hankalin ki, ni ba cutar da ke ba zan yi ba. Na san Kandala ta riga da ta miki duk wani bayani so akan rashin bin umarni na, kuma wallahi har cikin zuciya idan har ki ka sab'a umarni na, zan kashe su kuma dole ki yi abunda na ke so don na san ke wacece. Ke ba komai ba ce face *MARA GATA* wacce uwarta ta yi cikinta ta yasar da ita a kan bola. Kin ga kenan b'atar da ke ba zai min wahala ba don na buga da wad'and'a su ke da *GA TA* ma kuma ni na ci riba. Don haka kawai ko ba da kai ki ceci rayuwar masoyanki na asali idan har za ki masu halacci". Ta k'arisa maganar ta na wani shu'umin murmushi. Jikin Binty har tsuma ya ke tsabar tsoratar da ta yi, hawaye har ya wanke idanunta, cikin kuka ta ce, "Dan Allah ki fad'amin abunda ki ke so min in miki. Dan Allah kar ki cutar da Anna ta". Mik'ewa Hajiya Mansura ta yi ta re da k'arisawa wajan k'ofa ta murza key ka na ta dawo inda Binty ta ke zaune ta cire hulan da ke kanta kasancewar doguwar riga ce mai hula a jikinta. Dogon gashin kanta ya zubo har bayanta. Hannu ta kai ta shafo wuyanta zuwa bakinta, ka na ta mata kiss a goshi. Mamaki ya kashe Binty da ke zaune zuciyarta na k'aryata abunda kwakwalwarta na hasaso mata. Doguwar rigar atampar da ke jikinta ta zame kasancewar ta zuge zip rigar sai ya fad'o k'asa ta kasance haihuwar uwarta don ko brezia da pant ba bu. A gigice Binty ta mik'e ta re da runtse idanunwanta ta na maimaita, "Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un, Astagfurullah, Allahumma arji'ini fi musibati". Jikinta rawa ya ke yi sosai ta na mai dana sanin zuwan da ta. Dariya Hajiya Mansura ta fashe da ita ta re da kwanciya a kan gado ta yi pillow da hannayanta ta na kallon Binty da ke tsaye idanuwanta rufe kuma jikinta na wani irin rawa. "Hmmm! Yarinya ka da ki wasa da wuta za ta k'ona ki. Wannan shi ne abunda na ke so mu ruk'a yi ni da ke. Zan aure ki in kula da ke, zan mai da ke sarauniya. Ki amince da wannan harka za ki k'aru kuma za ki samu dukiya mai tarin yawa. Ba zan tab'a bari ko yatsa mace ko namiji su d'aga mi ki ba. Kar ki da mu, ko na aure ki, zan bar ki ki auri namiji don gudun zargin mutane, ni kai na abunda ya sa na yi auran kenan ba wai don namiji na gaba na ba, don namiji babu abunda zai iya min. Amma for now ba zan takuraki ki aminta dole ba, sai dai za'a fara zaman makoki a gidan nan, don tabbas sai na kashe su, kuma Na'ima ita ce first target d'ina, daga ita sai Fanan sai Fu'ad, wani ma na nan shigowa wanda mutuwarki shi ne ta ki". Hajiya Mansura ta k'arisa maganar ta re da wani shu'umin dariya da ihu-ihu. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Hajiya ki ji tsoran Allah. Wannan abu da ki ke so mu aikata ba k'aramin bala'i da masifa ba ne. Don darajar Allah ki yi hak'uri ki janye wannan maganar na miki alk'awarin rufa miki asiri babu wanda zai ji har gaban abada. Kuma ke ma ki tuba don ki na cikin bala'i da tsinuwar ubangiji kuma wallahi ki ka mutu a haka wuta za ki ba makawa". Fad'in Binty still idanuwanta a rufe don ba ta k'aunar sa ke arba da tsiraicin wacce ta isa ta haifi irinta guda biyar. "Ke! Ba wa'azi na kira ki min ba, idan wa'azi ne, wajan ki ka zo don ni mahaifina ma malami ne. Saboda haka wa'azin ki ba zai yi tasiri a nan ba. Kuma dole ki yarda ki aure ni mu rik'a biyawa junan mu buk'ata". Fad'in Hajiya Mansura a tsawace. "Wallahi ba zan yi wannan masifa da bala'i ba. Ba zan aikata wannan sab'on ba, kuma wallahi babu abunda ki ka isa ki yi wa Anna don mu na tare da ubangiji kuma zan kai k'aran ki wajan sa. Kuma na tabbata idan na amince da buk'atarki don in tseratar da Allah daga abunda ki ka shirya masu, wallahi Anna ba za ta tab'a yafe min ba don wannan ba tarbiyanta ba ne, no wonder d'an ki ya kasance kamar bunsuru, a she a nono ya tsotsa. Ina sha Allah ke da d'an ki ba za ku tab'a samun abunda ku ke so a waje na ba". Fad'in Binty ta re da nufar k'ofa. "Yarinya kenan, da k'afafuwarki za ki zo ki na rok'ona lokacin da lokaci ya riga ya k'ure miki don tabbas Anna sai ta bak'unci lahira". Cikin sauri Binty ta murd'a key d'in ta fice saboda lokacin da Hajiya Mansura ta kulle ba ta zare key d'in ba. Sai da ta goge hawayanta sosai ka na ta fito daga part d'in, amma duk da haka duk wanda ya ganta zai ga ne ta na cikin firgici. Ta shawo kwana su ka yi kicib'is da Julaibib shi kuma zai wuce part d'in sa don yin wanka zai fita an kira shi. Kallonta ya yi from head to toes, ita kuwa zuciyarta ce ta tsananta bugu har wanda ke kusa da ita ya na iya jiyo bugun zuciyarta. Hannunta ya damk'a ta re da nufar part d'in sa da ita ran shi a b'ace. Sai da ya bud'e k'ofar da d'aya hannunsa ka na ya tura ta ciki ya shigo ciki ka na ya mai da k'ofar ya rufe ta re da k'ura mata idanuwa ko kyaftawa ba ya yi. Ita kuwa kallo d'aya ta yi masa ta sunkuyar da kanta ta saboda yadda zuciyarta ke bugawa kuma ba za ta iya jurar kallon cikin idanuwansa ba. "Binty asara ki ke so ki min?". Fad'in Julaibib in a very cool voice ya na kuma kallonta. Saurin d'agowa Binty ta yi ta kalle sa ta na mamakin asarar mai kuma za ta masa. "Daga ina kike? D'akin Suhail ko?". Ya sa ke fad'i. Girgiza kai ta soma yi tuni har hawaye sun wanke mata idanuwa ta re da fad'in, "Wallahi yaya Bibi ban je d'akin shi ba. Ni tun da su ka dawo ma ban gan shi ba. Yaya mai zai kai ni d'akinsa kuma? Wallahi ba daga can na ke ba". Fad'in Binty ta na hawaye. "To daga ina kike? Kuma mai ya ke damun ki? Dole akwai abunda ya b'ata ran ki don naga mode d'in ki alamu ya nuna ki na cikin firgici. Kin san I study psychology, zan iya karantar ki tsaf". Fad'in Julaibib. Tsoro ne ya cika Binty, kuwa ba ta tunanin za ta iya fad'a masa abunda ke faruwa sam. Kallon sa ta yi for one second ka na ta ce, "Ina jin ba dad'i ne na rashin fara school d'in mu bayan Fanan ta samu admission amma ta k'i fara makaranta saboda ni ban samu ba. Kuma na yi da ita ta fara idan ya so next year ni kuma sai in fara in sha Allah amma ta k'i. Kuma gashi gaba d'aya y'an set d'in mu duk su na school". Kallonta ya ke yi har na kusan minti biyu ka na ya k'ara rage muryansa ta re da fad'in, "OK to ki kwantar da hankalin ki kin ji? Ban son ku na damuwa kin san ni doctor ne kuma damuwa na saka ciwo a zuciya, idan har na bar ki kina yawan tunanin Anna ba za ta ji dad'i ba za ta ce ni yayan banza ne, kuma kin ga dole in tashi tsaye in kula da ku ka da wani abu ya samu lafiyar ku, ko ba haka ba?". Sosai mamaki ya ka ma Binty, don ba ta tab'a tunanin yaya Bibi ya iya rarrashi haka ba, saboda ta san shi mutum mara son magana da hayaniya ga zuciya, kuma bai cika sake mata fuska ba. "Ko ba haka ba?". Julaibib ya sa ke fad'a. Murmushi ta yi ko in ce yak'e ta re da fad'in, "Hakane yaya Bibi". "Good girl, yanzu ki je d'aki ki kuma dai na tunanin komai. Da kin ji tunanin zai zo miki ki d'au Qur'ani ki karanta ko kuma ki yi alwala ki yi sallah kin ji". Fad'in Julaibib. Gyad'a kai Binty ta yi ta re da fad'in, "Nagode yaya Bibi". Ta fad'i hakane ta re da fita daga d'akin. Ya kai minti biyar ya na kallon k'ofar d'akin ka min ya saki ajiyar zuciya ya shige bedroom.

"Ke ina ki ka je ina ta nai man ki? Anacin ki sai kira ya ke yi a waya kamar zai fasa wayan. Da ya katse wani kiran ya ke k'ara shigowa". Fad'in Fanan. "Kin san yanzu jiki sai ka na yi ka na motsa shi saboda kar in yi kib'a kamar *MATAR SAYYADEE*". Fad'in Binty. "To ai sai ki je ki kira d'an anacin na ki ya na can sai faman kira ya ke yi. Ni gajiya ma na yi ba bar d'akin". "Kar dai ki za ge shi wallahi". Fad'in Binty ta re da hayewa sama. Ko da ta shiga d'aki, kashe wayar ta yi gaba d'aya ta fad'a duniyar tunanin abubda ya faru. Can kuma ta d'auki shawarar da Ya Bibi ya ba ta shiga bayi ta re da d'auro alwala ta yi raka'a biyu ta re rok'on Allah ya tseratar da Anna da zuri'arta daga Hajiya Mansura.

Kullum Binty cikin zullumin abunda Hajiya Mansura za ta yi was su Anna ta ke yi, har hakan sai da ya haifar mata da y'ar rama. Gashi ta saka numbern Kandala a blacklist saboda yawan damunta da kira da ta ke yi ta na k'ara tsoratar da ita. An kwashi sati d'aya, biyu har uku ba ta re da Binty ta ga wani yunk'uri daga hajiya Mansura ba. Sai hakan ya d'an kwantar da hankalinta har ta saki jiki ta cigaba da walwalarta saboda a tunaninta Hajiya Mansura ta tuba ta hak'ura.

*_______________* Hankali ta she ta ke kallon screen d'in wayarsa har k'ara gwalo idanuwanta ta ke yi ta na kallon fuskan Binty da ta yi wani irin kyau. Riga da wando ne da ya fito da shape d'inta, sai hulan sanyin da ke kan ta, ana kuma ganin gashin kanta da ta ra ba shi gida biyu, d'aya ya zubo har k'an k'irjinta, d'aya kuma zube a bayanta hannunta d'auke da irin k'aton lollipop d'in nan ta saka shi a bakinta ta na tsotsa, sannan ga emoji na heart k'ato a d'an sama daga gefe. Gabanta haka ya ke bugawa fat-fat-fat saboda tsabar rikicewa da mugun kishi da kuma tashin hankali. Kallon shi ta ke yi hannun shi rik'e da ice-cream ya na tawowa in da ta ke a zaune. Idanuwanta sun kad'a sun yi jazur. "Yaya Bibi wacece wannan a wajan ka?". Fad'in Sabrin da ta ke ji kamar zuciyarta zai fasa k'irjinta ya fito don tsabar kishi. Aje ice cream d'in ya yi a kan d'an teburin gabansa ta re da karb'an wayar. Sai da ya sake kallon hoton ya yi murmushi ta re da saka wayar a aljihun gaban rigar shi ka na ya zauna ta re da fad'in, "Ga ice-cream nan sha mu tafi". "Ba zan sha sai ka fad'a min wacece wannan". Fad'in Sabrin hawaye na zubo mata daga idanuwanta. Wani irin kallo ya watsa mata ta re da fad'in, "Ki na hauka ne za ki tasa ni ki na min kuka kamar na miki wani abu? Ma ye ruwan ki da ita, menene damuwan ki da sanin alak'ana da ita?". "Saboda ina son ka ina k'aunar ka. Kuma ba na k'aunar ko wacce mace kusa da kai idan ba ni ba. Haba ya Bibi, za ka ce min ba ka fahinci irin son da na ke maka ba? Tun ina k'ank'anuwata lokaci da ma ceto rayuwata na ji duk duniya babu namijin da na ke son kasancewa ta re da shi idan ba kai ba. Kai ka d'ai na ke gani naji kwarin guiwar cigaba da rayuwa a doran k'asa. Dan Allah ka da ma bari wata ta kwace min kai. Wallahi na fita komai". Fad'in Sabrin cikin kuka ta re da ka mo hannun Julaibib. "Ki na hauka ne? Ni na tab'a cewa ina son ki ne? Duk wasu abubuwan da na ke mini da kulawan da na ke ba ki, aiki na na ke yi da kuma tausaya mi ki saboda irin lalurar da ki ke d'auke da shi. Amma ba na tuna nin akwai wata macen da na tab'a bawa lokaci na har na ke jure surutunki kuma na ke zuwa irin wajajan nan da ita idan ba ke ba har k'anwata da mu ke ciki d'aya da ita wanda na sa nta dad's ta na fatan haka. OK hakane ya ba ki damar yi min rashin kunya har ki ce ki na sona ko? To data yau Kim dai na ganin hak'ora na a wake balls har ki samu in fita da ke. Kuma yarinyar da ki ka gani a wallpaper na, ita na ke da burin aura, ban ga wata macen da ta fita ba a waje na. Kin ji ko ba ki ji ba?". Fad'in Julaibib. Wani irin gunjin kuka Sabrin ta saki ta re da d'aukar Jakarta da ke kan teburin ta yi hanyar da zai fitar da ita daga part d'in da gudu. Tsaki Julaibib ya yi ta re da mik'ewa, juyawar da zai yi idanuwansa su ka sauka a kan ta ta na wani irin dariya cikin nishad'i ita da wani saurayi da kuma y'an mata guda biyu. Gaban shi ne ya buga da k'arfi ya na tunanin mai ya kawo ta wajan nan a wannan lokacin su da ba fita su ke yi ba. A fusace ya mik'e dai-dai lokacin da su ma su ka mik'e su ka shiga wani waje. Da sauri ya bi bayansu, amma bai ga ko kyallinsu ba. Cizon yatsar shi ya yi k'udurta irin Fad'an da zai yi mata. Ya dad'e ya na dudduba si bai gan su ba, dag bisani ya fito ya yi wajan motarsa ta re da yi mata key. Kai tsaye gida ya nufa. Parking ya yi, kai tsaye ya nufi part d'in Anna ya na huci. Murd'a handle d'in ya yi ta re da shiga, da ita ya soma cin karo kunnanta mak'ale da earpies ta na miming wak'ar namenj ba ta ma san ya shigo don ta k'ure wak'ar. Fizge earpiece d'in ya yi ya tsittsinka. A furgice ta mik'e za ta gudi ya damk'o ta aiko ta ce, "Annaaahhh ki cece ni ya Bibi zai karya ni". Da gudu Anna ta fito saga kitchen Fanan a bayanta. "Da uban wa na gan ki a park? Shine don munafurci har kin dawo kin canza kaya ko. Za ki yi magana ko sai na ta ka maki kai". "Wallahi wallahi wani billahil azeem yau ko k'ofar nan ban je ba kuma ka tambayi Anna ka ji through out mu na ta re".

*WASAN YA SO MA*

_MATAR SAYYADEE_ 🌹 *63-64*🌹

💃🏻🔥🔥 _Ku na inahh nee?🗣️ to maza ku firfito ka da wannan garab'asar ta wuce ku. Shin ko kun san Mrs Abubakar ta k'ara zuwan maku da zuma gangariya mai jawo maki martaba da soyayya a wajan mijin ki?_

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull