Ba ni da gata - Chapter 32
Ba ni da gata Chapter 32: Ba ni da gata Chapter 32. _Ta shi maza ki karb'o kud'in adashen ki da ki ke zubi wajan Ladidi domin ki siya ke ma ki zama…
2,968 words
_Ta shi maza ki karb'o kud'in adashen ki da ki ke zubi wajan Ladidi domin ki siya ke ma ki zama sarauniya_💃🏻💃🏻💃🏻 _Gangararriyar gangariyar zuma mai k'ara kuzari da ni'ima ta re da k'ara miki sha'awa da kuma sa ka miki wani dad'i da d'and'ano na musamman ta re da saka mai gida sambatu da zubar miyau 🙈 da gigicewa. Wannan zuma guarantee ne sai kin gwada na tabbata sai kin godewa Hassana (Mrs Abubakar). Haka kazalika ina macen da ke k'orafi akan miji bai kai mata? To kwantar da hankalin ki Mrs Abubakar ta kawo miki waraka da izinin Allah domin idan ki ka yi amfani da wannan zuma mijin ki zai jima bai yi inzali ba kuma ya na k'ara ruwan maniyyi da lafiya a jikin mai gida_ _Maza garzaya ki nai mi Mrs Abubakar a lambar wayarta kamar haka_ _+234 814 193 4442_ _Sayan nagari, mai da kud'i gida_🤸🏻♀️🤸🏻♀️💃🏻💃🏻🔥
..............Wani harara ya watsa mata ta re da mai da dubansa izuwa ga Anna ka na ya ce, "Kin san a ina naga yarinyar kuwa Anna? A park fa, ita da wasu k'awayanta guda biyu da wani saurayi wanda sam ni ban yarda da shi ba. Da ma kenan haka ake barin su sakaka su na fita su na had'uwa da kowani kare da doki? Sam ba zai yu ba wallahi". Fad'in Julaibib har ya soma in'ina. "To Mr Julaibib ka gama?". Fad'in Anna ta na kallon shi don tsaf tuni ta dad'e da harbo jirginsa akan Binty. "Anna ban gama ba fa, wallahi yaran nan su ka k'ara fita daga gidan nan, sai na b'alla k'afarsu". Fad'in Julaibib. "Amma wai ba ka ji abunda ta ce ba ne? Yaran nan ba bu in da su ka je yau wallahi. Kuma ko fita ne, idan har ba da driver ko Yayan su Fu'ad ba ban yar da su fita". Fad'in Anna. "To daga yau na hana. Duk in da za su je su fad'amin ni da kai na zan kai su, ban son abunda za'a zo a ce ni babban banza ne. Dole in kula da su in kuma kare mutuncin k'annai na". Fad'in Julaibib. Har Anna ta bud'e ba ki za ta ce da ya ke CANADA wa ke kula da su, sai kuma ta fasa ta re da fad'in, "To naji uban y'an zuciya". Sai da ya kalli Binty ta re da yin kwafa ka na ya fice daga d'akin. Ita kuwa Binty doguwar ajiyar zuciya ta saki ta na kuma tunanin shin wa ya gani mai kama da ita haka. Julaibib kuwa da ya isa d'akinsa mamaki ya ke tayaya haka har yarinya k'arama ta soma yi masa gizo. "Kai tabbas ita ce". Julaibib ya fad'a kamar wani zautacce. "Sai na binciki yarinyar nan. Ba zan iya jura ba wallahi". Ya sa ke maimaitawa ta re da d'aukar wayarshi ya shiga kallon hotonta da ke kan wallpapern shi.
*___________* Tun da mahaifiyarta ta haifeta, ba ta tab'a tafiyan k'afa ba sai yau. Domin tun daga park d'in nan haka ta tako har Wuse II da k'afarta ta na tafiya ta na hawaye. Kai tsaye part d'in aunty Junaina ta nufa har bedroom d'in ta. Hanan da Amrah ido su ka bi ta da shi ta re da tab'e baki su ka mai da duban su ga Tv. Fad'awa jikin aunty Junaina ta yi ta re da fashewa da kuka har da shasshek'a. Sai da aunty Junaina ta tab'e baki ka na ta d'ago kafad'unta ta re da fad'in, "Sabrin lafiya? Wa ya tab'a min ke?". Fad'in aunty Junaina cike da damuwa. "Aunty na shiga uku, ta ki bari na. Duk in da na bi sai ta bini. Ta kwace min komai a *LEAD BRITISH*, har makarantar na hak'ura na bar mata. Yanzu kuma ta kwace min shi". Ta gama fad'in hakane ta re da rushewa da kuka. Shafa bayanta aunty Junaina ta yi ta re da fad'in, "Ban fahimce ki ba, yi min bayani domin in ga ne". "Aunty ya Bibi ya ce bai tab'a so na ba, wai tausayi na ya ke ji kuma wai ita zai aura ba ni ba". Sabrin ta fad'a kamar numfashinta zai fita. "Ban ga ne ba, wace yarinya ce wannan?". Fad'in aunty Junaina. Fiddo wayarta ta yi daga cikin Jakarta ta shiga gallery ta re da fiddo hoton Binty wanda ta tura a wayarta ta nu na wa aunty Junainan. Wani irin waro idanuwa aunty Junaina ta yi ta re da fad'in, "Wannan ai yarinyar da Zuwairah ta nu na min ce. Tabbas ita ce. Idan ko hakane zan jefi tsun-tsu biyu da dutsi d'aya yasin". Duk cikin zuciyarta ta yi maganar a fili kuma wani murmurshi ta yi ta re da fad'in, "Maza share hawayanki Sabrin. Wallahi wannan yarinyar ta bar ta da miki da hankali. Kawo kunnen ki kiji". Ba ta re da ta jira Sabrin d'in ta kawo kunne ba ita ta kai bakinta kunnan Sabrin d'in ta yi mata wasu maganganu. Cikin sauri Binty ta kalli aunty Junaina ta re da fad'in, "Really?". "I'm very sure my lovely daughter". Ta fad'i hakane ta re da ba shi hannu su ka tafa.
..............Fitowarshi kenan daga cikin asibitin ya nufi wajan motarshi hannunsa rik'e da fara k'al d'in rigar likitoci idanuwansa su ka sauka a kanta ta na yi wa wata mata magana hannunta rik'e da wani kyakkyawan yaron da ba zai wuce 8 years ba. Wannan saurayin da ya gan su ta re da shi a park shi ne ya bud'e ma su mota su ka shiga shi kuma ya zagaya ya shiga driver seat ya ta da mota. Cikin azama Julaibib ya shiga motar ta re da yi mata key, sai dai abun takaici a kwai wata mota da ta yi blocking d'in sa. Tsaki ya yi mai tsawo ka na ya bud'e murfin motar ya fito ya nufi motar da ya ga ta shiga. Sai dai kash tuni har sun fice daga asibitin. "Kaiiiiiiiiiii! Dam it". Shine abunda fad'a ta re da buga gaban wata motar da ke gefensa. Can kuma ya juya ya nufi cikin asibitin ya na balbale fad'a akan wanda ya yi blocking d'in sa. Cikin sauri mai motar ya fito ya na ta na shi hak'uri ta re da matsar da motarsa. Shiga motar ya yi ta re da nufar gida direct. Saboda gudun da ya ke yi, cikin mintuna k'alilan ya isa gida. Sai dai abunda ya ba shi mamaki, ya na parking Alhaji Usman na parking kuma ta re su ke da Binty, Fanan har da Anna. Sosai mamaki ya bayyana a kan fuskan shi ya na tunanin to wa ya gani a hospital. Hakanan ya had'iye duk abunda ya taho da shi ta re da isa wajan su ya gaida daddy da Anna ka na ya wuce side d'in sa cike da sak'e-sak'e.
Binty kuwa tunda Anna ta hana su fita kamar yadda Julaibib d'in ya tsara sai ta shiga tashin hankalin rashin ganin masoyinta Yousouf. Daga baya ta tsiri fita ta na had'uwa da shi a can gaban layin su kad'an ba ta re da sanin ko Fanan ba. Oga Soloman dai kullum ya na ganin ta na fita, amma ba shi da damar magana tun da ba huruminsa ba ne.
Yauwa kamar kullum Yousouf ya kira ta, ta fita. Bayan sun gama zancan su ta shafo hanya za ta dawo gida, daidai lokacin Julaibib ya danno hancin motarsa layin. Gaban shi ne ya buga saboda ganinta da ya yi ta na ta sauri domin zuwa gida. Parking ya yi ta re da fitowa, cikin sauri ya k'arasa wajanta ta re da fincikota ya wanka mata mari ka na ya nufi wajan mota da ita ya bud'e ta re da tura ta ciki shi ma ya zagaya ya Shiga. Babu abunda k'irjinta ya ke yi fa ce bugawa dam dam dam har su ka isa cikin gida. Ko parking mai kyai bai yi ba ya kamo hannunta ta re da yin part d'in Anna da ita. "Alhamdulillah Anna ga ta nan". Fad'in Barr Fu'ad da su ka ci nai man Binty ba su ganta ba, hankalin Anna ya yi mugun tashi. "Ina ki ka je Binty?". Fad'in Anna ta re da k'arisa wajanta. "Ba na fad'a mini yarinyar nan fita ta ke yi waje ba ta re da izini ba baki yarda ba. To can na ganta ta na ta zuba sauri za ta dawo gida". Gaban Anna da na Fu'ad a ta re su ka buga dam dam dam. Dai-dai lokacin Alhaji Usman ke saukowa daga stairs. "Binty ki ji tsoran Allah ki fad'a min gaskiya in da ki ke zuwa". Hawaye tuni sun soma wanke fuskan Binty jikinta sai rawa ya ke yi har da Fanan da ke gefe wacce tasan idan magana ta fito ta shiga uku don ta sha taimaka mata ta na fita su had'u da Yousouf su fa ke da zuwa saloon ko shopping. "Ba da ke ake magana". Julaibib ya fad'a da tsawa. "Kai ban san hauka. Ku yi mata a hankali. Zo nan y'ata ki fad'a min in da ki ke zuwa". Fad'in Alhaji Usman. Mik'ewa Binty ta yi kamar an tsoma jab'a a koko ta isa wajan Alhaji Usman ta re da tsugunawa. Zama ya yi a kan kujera ta re da fad'in, "Da wa ki ke had'uwa idan kin fita?". Bakinta na rawa ta ce, "Ka yi hak'uri daddy ba zan k'ara ba". "Waye shi?". Daddy ya sa ke fad'i. "Sunan sa Yousouf Muhammad Ahlam". Ta fad'a bakinta na rawa. "Yousouf Muhammad Ahlam". Julaibib ya maimata sunan. Yayin da Barr Fu'ad ya ji wani jiri na nai man kaisa k'asa ya yi saurin dafe bango. "Abun mai sauk'i ne ai. Ai mahaifinsa aminina ne ta re mu ka yi makaranta. Da shi d'in doctorn sarkin Adamawa ne wanda ya rasu. Ai gidan mutanan kirki ne. Da ma d'azu ai na ke maka magana a kan ku shirya kai da Fu'ad za mu je gaida wani d'an sa da ya dad'e bai da lafiya". Fad'in daddy ya na mai kallon Julaibib da idanuwansa su ka yi jazur. "Ke Binty ka da ki sake yin irin wannan kuskuran kin ji abunda na fad'a miki ko?". Gyad'a Kai ta yi ta re da fad'in, "Nagode daddy". Anna ko haushi ne ya kamata domin ko cikin mafarkinta ba ta tab'a kawo Binty za ta iya fita su had'u da wani a waje ba don ba tarbiyan da ta d'aura su akai ba kenan. Ba ta re da Julaibib ya ce komai ba ya fice daga d'akin haka ma Fu'ad. Binty kuwa da Fanan saurin hayewa sama su ka yi. Su na shiga d'aki Fanan ta turo k'ofa har da murza key ka na ta kalli Binty ta re da fad'in, "Ke ki na hauka ne Binty? Da ma fita ki ke yi ku na had'uwa da Yousouf duk da an hana mu fita? Mai yasa bakya jin magane Binty?". Fad'in Fanan. "Ki yi hak'uri Fanan, wallahi idan ya kira ni ne ban iya hak'uri har sai mun had'u tukun na ke samun salama. Wallahi ina matuk'ar k'aunar Yousouf". Fad'in Binty. "Na san ki na son shi sis, but d'an Allah ki rik'a controlling feelings d'in ki". Fad'in Fanan. "Ni wallahi tsoro na Anna, na san sai ta yi fushi da ni sosai". "Gaskiya kam wallahi. Don ba ki ga yadda ta yi da fuska ba". Fanan ta fad'a. Zama Binty ta yi ta re da zuba tagumi hannu bibbiyu.
*AFTER ISHA* Gaba d'ayansu cikin shiga iri d'aya. Shadda ce gezna mai matuk'ar kyau da maik'o kalar sararin samaniya a jikinsu. Fu'ad ne ke tuk'i yayin da Julaibib ke gidan gaba Alhaji Usman kuma a gidan baya su ka nufi gidan Alhaji Muhammad Ahlam da ke Maitama. A gaban babban gate d'in gidan Barr da ke ji kamar zuciyarsa za ta buga ya danna horn. Cikin 'y'an seconni mai gadi ya wangale gate d'in gidan. Alhaji Muhammad Ahlam da kan shi ya zo ya ta re su cike da fara'a ta re da kai su parlourn bak'i. Nan da nan aka cika masu gabansu da abinci da kuma drinks. "Alhaji mu k'ara gaisawa, ina wuni ya harkoki da kuma iyalai?". Fad'in Alhaji Muhammad Ahlam. "Alhamdulillah, ya na k'ara harkokin da kuma mai jiki?". Fad'in Alhaji Usman. "To, sai dai mu ce alhamdulillah". Fad'in Alhaji Muhammad Ahlam a sanyaye. Ajiyar zuciya ya saki ta re da fad'in, "Allah ubangiji ya ba shi lafiya". Fad'in Alhaji Usman. Gaba d'aya daga Barrister har Julaibib su ka gaishe sa ta re da tambayansa ya mai jiki. Amsa masu ya yi da alhamdulillah ta re da fad'in, "Wannan shine babban d'an ka Julaibib ko? Shugaban gwagwaran Africa ko?". Alhaji Muhammad ya fad'i hakane ya na dariya. Shima Julaibib d'in murmushin yak'e ya yi don shi ka d'ai yasan mai ya ke ji a zuciyarsa. "Shi ne nan". Fad'in Alhaji Usman. Kallon shi Alhaji Muhammad Ahlam ya yi ta re da fad'in, "Kai Julaibib, ga mata nan da yawa a gari. Ka fiddo mata ko mu yi maka irin na da". Fad'in Alhaji Muhammad ya na dariya. Murmushin dai ya sake yi wanda bai kai ciki ba. "Mu je ciki ku ga jikin na shi ko". Fad'in Alhaji Muhammad Ahlam. "OK muje". Fad'in Alhaji Usman ta re da mik'ewa dukan su suka fito daga part d'in su ka yi cikin gida. Kusan gaba d'aya gidan ne a kan mara lafiyan wasu na kuka wasu na addu'a. Su kan su Julaibib, Fu'ad da Alhaji Usman sai da jikinsu ya yi matuk'ar sanyi. Ga mutun nan dai a kwance amma kamar gawa, abinci ta drip ake ba shi. Sosai su ka masa addu'a ka na su ka fito jiki a mace. D'akin bak'i su ka koma su na k'ara jajantawa Alhaji Muhammad Ahlam d'in. Alhaji Usman ne ya gyara zama ta re da fuskantar Alhaji Muhammad Ahlam ta re da fad'in, "Ni ko a cikin y'ay'an ka wanene yusouf?". Kallon shi Alhaji Muhammad Ahlam ya yi ci ke da mamaki ta re da fad'in, "Yawan y'ay'an har ya sa ba ka iya banbance su kenan? Ai Yousouf shi ne mara lafiyan da ke kwance. Yanzu haka watan shi biyar a kwance wanda a da k'ark'ari wata uku ya ke yi ya mik'e, amma wanna karan ya kai har wata biyar, ko lokacin ne ya yi". Fad'in Alhaji Muhammad Ahlam. Daga Alhaji Usman, Fu'ad da barrister gaba d'aya zaro idanuwa su ka yi su na kallon Alhaji Muhammad cike da mamaki. "To idan har Yousouf na kwance wata biyar bai motsi, wanene wanda Binty ke fita su na had'uwa?". Fad'in Julaibib a zuciya wanda Fu'ad shi ma tunanin da ya ke yi kenan.
*_______________* "Hello ki na jina kuwa?". Da fad'in Yousouf. "Ina jin ka masoyi, na k'osa ka fad'amin wallahi". "Kin tuna min yi wa junan mu alk'awatrin zamu rayu da junan mu a kowani irin hali, kuma d'aya ba zai guji d'aya ba?". Fad'in Yousouf. "Kwari kuwa, kuma ba zan tab'a canzawa a kan haka ba". Fad'in Binty da ke juyi a kan gado ta na kallon zoben da ke hannunta da Yousouf ya sa ka mata. "Binty akwai abunda na dad's ina b'oye miki saboda gudun ka da ki gujemin". "Haba reality, mai ba ka guje min ba bayan ka san ni ba kowa ba ce, sai ni CE zan guje maka. Sam ba zan tab'a guje maka ba ko kai wanene". Fad'in Binty. "Kin tabbata mai sona?". Fad'in Yousouf. "Na tabbata masoyi". Fad'in Binty. "Mai sons ni da ke jinsun mu ba d'aya ba ne. Ma'ana ni aljani ne". Dariya Binty ta bushe da shi ta re da fad'in, "Yau kuma zolaya ka ke jin yi?". Fad'in Binty ta na dariya. "Ba ki yarda ba kenan? To ban minti d'aya". Ya na fad'in haka ya kashe wayar. Kallon screen d'in ta yi still ta na dariya. Wani irin zabura ta yi ta re da mik'ewa ta zaro damuwa sakamakon ganin Yousouf da ta yi a jikin bango zaune a kan kujera. "Binty kar ki tsorata, bayyana miki wanene ni ya zama dole saboda tone-tone da babanki na nan gidan da y'ay'ansa su ka yi. Binty na dad'e ina d'awainiya da ke tun ki na jaririya. Ke ce macen da na fara so....". Wani irin ihuu Binty ta yi ta re da zubewa a k'asa sumammiya. Dai dai lokacin Fanan ta turo k'ofar ta shigo........
*DAN DAN DAN! MUJE ZUWA*
*PAID BOOK 08128755583* 🌹 *65-66*🌹 .............."Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Binty, Binty, mai ya sa me ki?". Fad'in Fanan ta re da k'arasawa wajanta ta na jijjigata amma ko motsi ba ta yi. Da gudu Fanan d'in ta sauko k'asa ta na ihun kiran Anna da ke zuba Andrew liver salt a cikin cup saboda cikinta da ya lumbura sakamakon cin alale mai zafin da ta yi. A zubure Anna ke kallonta ta re da fad'in "Mai ya faru ke?". "Anna Binty ce.... Ta.. Ta mutu. Ta na kwance ko motsi ba ta yi". Fad'in Fanan jikinta na rawa. Da gudu-guda Anna ta yi sama ta re da tura d'akin su Binty da k'arfi saboda yadda ta rud'e ta yi wajan Bintyn da ke ya she a k'asa ba numfashi. Jijjigata ta soma yi ta na salati da kiran sunanta amma shuru. "Ban ruwa Fanan". Fad'in Anna ta na k'ara jijjiga Binty. Cikin sauri Fanan ta yi cikin toilet saboda rud'ewa ta d'ebo ruwan ta kawo mata. Hannu hannunta har rawa ya ke yi wajan karb'a ta d'iba ta shafa mata har sau uku a fuskanta, amma shuru ba ta farfad'o ba. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Fanan d'auko min wayata a parlour". Fad'in Anna. Da gudu Fanan da ke kuka ta fito ta d'auko wayar Anna ta re da dawowa d'akin ta mik'awa Anna wayar. "Kira min Julaibib ki saka a hands free".