Ba ni da gata - Chapter 34
Ba ni da gata Chapter 34: Ba ni da gata Chapter 34. Abu kamar wasa ciwon Anna sai dad'a gaba ya ke yi, don yanzu ba ta iya gane kowa. K'ok'arin fita da ita…
3,323 words
Abu kamar wasa ciwon Anna sai dad'a gaba ya ke yi, don yanzu ba ta iya gane kowa. K'ok'arin fita da ita k'asar ma ake yi zuwa India. Zaune ta ke a d'akin su ta zuba uban tagumi, ta yi wani bala'in rama babu abunda ka ke hangowa a fuskanta sai karan hancinta. Idanuwanta duk sun zurma. Wayarta ce ta soma k'ara, kallon wayar ta yi ta ga bak'uwar number ce ke kiranta. Sai da ta kusa tsinkewa ka na ta d'aga ta re da karawa a kunne ta yi cikakkiyar sallama. Daga d'ayan b'angaran ba ta re da an amsa mata sallamar ba ta soma fad'in, "Ki na tunanin zan fad'i magana ce na kuma kasa cikawa? To kin yi kuskure y'an mata. Idanuwan ki dai sun gane miki yadda na yi da Annan ki, kuma ina mai tabbatar miki idan asibitin duniyar nan za'a zagaye baza'a tab'a samun maganin matsalarta ba. Ni da na saka mata cutar, ni kad'ai zan iya warware wa. Saboda haka zab'i na gare ki, Anna za ta iya warkewa amma da sharad'in amincewarki ki zamo matata mai d'auke min sha'awata, idan ba haka ba, nan da kwana biyu za'ayi kukan mutuwarta, daga nan kuma sai Fanan". K'it ta katse wayar. Hankali a matukar ta she har ta na mik'ewa ta re da zaman y'an bori a k'asa ta re da rarrafe ta fita daga d'akin ka na ta mik'e. Da gudu-gudu ta sauko daga stairs d'in ta fita daga part d'in ta nufi part d'in Hajiya Mansura. Caraf ta ji an cafki hannunta daga baya ta re da jan ta har garden d'in da ke gidan kasancewar bai fi taku goma ba daga in da su ke zuwa garden d'in. "Natsu ki kwantar da hankalinki. Na san duk abunda ke faruwa, kuma ni nan da ki ke ga ni na zo ne domin ceton ki ta re da tseratar da ke daga muguwar matan nan Mansura". Fad'in Hajiya Zuwairah da ke kallo Binty cikin zuciya ta na had'iyar miyau. "Na san duk wani sharrin da ta ke bin ki da shi, kuma na san abunda ta aikatawa Anna. Asiri ta mata mai matuk'ar k'arfi wanda zai iya salwantar da rayuwarta har abada. Idan ki na buk'ata zan iya taimakonki". Fad'in Hajiya Zuwairah. "Dan girman Allah ki taimake ni wallahi zan mutu idan har Anna ta wani abu ya sa me ta". Fad'in Binty ta na kuma ta re da rik'e hannun Zuwairah k'am. "Abu d'aya ne zai karya asirin da Mansura ta yi wa Anna, ba kuma wani abu ba ne fa ce barin ki cikin gidan nan". Fad'in Zuwairah ta na mai kallonta. A zabure ta mik'e ta na kallon ta re da fad'in, "Na shiga uku! Idan har na bar nan wallahi ban da wajan zuw...". Na ta k'arisa maganar ba saboda fad'owar da Yousouf ya yo mata a rai. "Kar ki da mu, ni ina da in da zan kai ki, sai dai za ki d'an zauna ne na wani lokaci ka min ki samu wajan zama. Tausayinki da maraicin ki na duba shiyasa na ke son taimakar ki wanda hakan ni ma zai iya jawo min babbar masifa idan ta gano ni ta taimake ki. Yanzu ki yanke, shin za ki bar gidan nan ki ceci Anna ko kuwa za ki cigaba da zama ki mai da Fanan marainiya kamar ki, sannan ita kan ta ki salwantar da rayuwarta da yayunta?". Ba ta re da wani dogon tunani ba Binty ta CE, "Na zab'i barin gida domin ceton rayuwar mahaifiyata, zan bi ki in zauna a ta re da ke na kwanaki bakwai ka min na tafi in da zani. Nagode ta taimakon ki a gare ni". Fad'in Binty ta na sharar hawaye. "Yauwa, wanna shine right time na guduwa saboda mazan gidan ba su nan, amma yanzu zan shiga wajan Mansura gudun zargi, ke kuma ki yi dabara ba ta re da wani ya gan ki ba ki shige motata ki kwanta a back seat, ba zan dad'e ba zan fito mu wuce". Fad'in Zuwairah. Gyad'a mata kai Binty ta yi ta re da yin hanyar part d'in Anna ta na mai jin tsananin kewar Anna da Fanan tun ka min ta bar gidan. Ta na tura k'ofar ta yi kicib'is da shi ya na tsaye a parlourn, cikin sauri ta nufe shi ta re da fad'in, "Yayanmu ya jikin Annar mu?". Ta fad'i hakane hawaye na zuba. "Ki kwantar da hankalinki kin ji? Anna za ta sa mu lafiya". Julaibib ya fad'a ta re da shafa kan ta ya na kallon fuskanta. Langab'ar da kan ta ta yi, tsautsayi ya sa d'an kunnna kunnanta ya ka ma hulan sanyin da ke kanta. Zame hukar ya yi ta re da cire d'an kunnan da ya mak'ale a hankali. Idanunsa ne ya sauka a k'eyarta, k'urawa wajan idanu ya yi har sai da ya kai hannu ya shafi wajan don tabbatarwa. "Mai ya faru yaya?". Fad'in Binty ita ma ta na shafa wajan. "Babu komai, ki je d'aki zan koma asibiti yanzu, anjima zan zo in kai ku. Ku kula da kan ku kun ji?". Gyad'a masa kai ta yi hawaye na zuba. Hannu ya sa ka ya share mata hawayan ta re da nuna mata stairs. Wajan ta nufa ta na tafiya ta na juyowa ta na kallon, duk san da ta juya tsaye ta ke ganinsa ya na kallonta har ta shige ka na ya fita. Fanan ta sa mu ta na saka masu kayan guga a cikin wardrobe. Ta baya ta rungume Fanan d'in ta re da fad'in, "Ina k'aunar ku Fanan irin wanda ba zan iya misaltawa ba". Juyowa Fanan d'in ta yi ta re da sakar mata murmushi ta re da fad'in, "Mu ma muna k'aunarki sister". Bayi Binty ta yi saurin shigewa ta turo k'ofar ta kunna panpo ta re da rushewa da kuka. Ta jima ta na kuka a bayin ka min ta fito. Ko da ta fito ba ta samu Fanan a d'akin ba. Saukowa k'asa ta yi, nan ma ba Fanan. Ta kitchen ta fita ta k'ofar baya cikin sauri-sauri ta re da nufar motar Hajiya Zuwairah ta yi saurin bud'ewa ta shiga gidan baya ta kwanta. "Da har na cire rai ba za ki zo ba saboda ganin wannan babban wan na ku ya fito ya bar gidan". Fad'in Hajiya Zuwairah da ta dad'e a cikin motar ta na jiran zuwan Bintyn. "Ki yi sauri mu bar gidan nan". Fad'in Binty. Ta da mota Hajiya Zuwairah ta yi ta re da reverse su ka nufi gate. Tafiya su ka yi ba tsawon mintuna sha biyar ka na Hajiya Zuwairan ta yi parking a bayan wata mota. "Jira ni ina zuwa". Fad'in hajiya Zuwairah ta re da fita daga motar ta nufi motar gabanta. Kwankwasa tinted glass d'in ta yi. Zuge glass d'in ta ciki ta yi. "Kin bar ni ina ta jira Zuwairah". Fad'in matar cikin motar. "Ke dai ba ri Junaina, da har na d'auka plan d'in mu ba zai yi aiki ba saboda dawowar babban d'an ta daga asibiti, cikin sa'a kuma bai dad'e ba ya fita. Yanzu haka ma muna ta re ita ta na mota". Fad'in Hajiya Zuwairah. "To ki je ki zo da ita". Fad'in Hajiya Zuwairah. Juyawa Hajiya Zuwairah ta yi ta re da komawa wajan motarta. "Yauwa fito Binty". Fad'in Hajiya Zuwairah. Fitowa Binty ta yi ta na kallon Hajiya Zuwairah ta na son k'arin bayani. "Yauwa kin ga ba dama in aje ki a gida na saboda Hajiya Mansura ta na yawan zuwa waje na, kuma idan ta gan ki wani bala'in ne zai biyo baya, shiyasa na yanke shawarar ki bi k'awata ki zauna ka min komai ya daidaita, ko y'an aikace-aikace kya tayata". Shuru Binty ta yi ra d'an wasu dak'ik'u ka min daga bi sa ni ta ce, "To shikenan zan zauna a wajanta d'in in dai hakan shi zai fitar da Anna daga halin da ta ke ciki.
*A SHA WEEKEND LAFIYA🤪🤪🤪* 🌹 *69-70*🌹 ..............."Gaskiya ki na son Anna sosai, kuma kin kyauta don wannan shi ake kira halacci. Mu je ki shiga mota ku wuce". Fad'in Hajiya Zuwairah. Gaba Binty ta yi ta re da nufar motar Junaina hajiya Zuwairan na biye da ita a baya. "To Junaina ga ta nan, sai kin ji ni". Fad'in Zuwairah ta re da komawa wajan motarta. Ita kuma Binty zagayawa ta yi ta re da bud'e gidan gaba ta shiga ta re da gaida Junaina. Aunty Junaina ka sa amsawa ta yi saboda ganin tsananin kyawun Binty a fili ya zarce na hoto. Murmushi kawai ta yi ta re da tada motar. Sai da su ka isa bakin gate sannan Junaina ta kashe mota ta re da kallon Binty da ke hawayen kewan Fanan da Anna har da ya barrister tun San da su ka soma tafiya. "Yarinya ki na jina? Na amincewa Zuwairah za ki zauna da ni a cikin gidan nan bisa ga sharad'i guda biyu ne kawai. Na farko, mai gida na ba zai amince ki zauna da ni ba har sai dai idan matsayin y'ar aiki za ki shiga. Kar ki damu, aikin ba wani mai wahala ba ne, kula za ki rik'a yi da y'ar mijina ta re da yi mata biyyata da kuma gudun b'acin ranta. Sharad'i na biyu kuwa, sai nan gama zan fad'a miki, ina fatan kin fahimta". Shuru Binty ta yi ta na mai jin gudun hawaye a kan fuskanta. Jinjiga kai ta yi alamun ta aminci don duk a tunaninta yarinyar da za Junaina ta ce za ta kula da ita ba ta wuce three years ba. Ba ta re da ta k'ara magana ba ta tada mota ta re da yi wasa gate man horn. Cikin sauri ya wangale gate ita kuma ta tura hancin motar ciki ta re da nai man waje ta yi parking. Junaina ce ta fara fitowa ka na Binty ta fito. Kai tsaye part d'in Junaina su ka nufa ta na gaba Binty na biye da ita a baya wanda haka nan ta ji gabanta na fad'uwa. Murd'a handle d'in ta yi ta re da kutsa kai ciki sa'annan Binty ma ta biyo baya. Zaune ta ke a kan two sitter cikin riga da wato da tasha tocking gashin nan ya sha gyara ta kuma yi parking d'in sa a gefe, fuskanta ya sha glasses da ya kusa cinye rabin fuskanta ta re d'aura k'afa d'aya a kan d'aya ta na taunar cingam k'as-k'as-k'as. "Yauwa k'araso ciki, kin ga wacce za ki yi wa hidima nan, ki kuma tabbatar kin yi mata duk wani abunda ta ke buk'ata ban san jin k'orafinta". Fad'in aunty Junaina ta na mai nunawa Binty Sabrin d'in. Cire glasses d'in fuskanta ta yi ta re da huro cingam d'in bakinta ya yi kwai ka na ta fasa ta re da mik'ewa ta na kallon Binty da mamaki ya gama kasheta baki sake sakamakon ganin fuskan Sabrin. Sabrin d'in kuwa zagayeta ta soma yi ta re da k'are mata kallo ta na wani shu'umin murmushi ta re da hura mata cingam a fuska. Aunty Junaina dariya ta yi ta re da wucewa side d'inta da ke upstairs. "Wa ma ki ke da suna? Binty ki ke ko wa?". Fad'in Sabrin ta na dariya. Wani murmushi Binty ta yi mai k'ona zuciyar wanda aka yi wa gashi ya k'ara fito da tsantsan kyawunta ka na ta ce, "Lallai! Ashe na tsaya a ran ki haka? Gaskiya a gaishe ni domin tsayin shekaru kin ka sa manta ni, hakan na nufin ina d'aya daga cikin mutanan da ki ke tsoro su ke kuma sa ki fargaba". "Ki iya bakinki yarinya! Domin ki na cikin gidana ne, gidan ubana". Fad'in Sabrin a tsawace. "Haba? Sannu dodon kod'i wanda ko wani lokaci shi da gidansa ya ke yawo". Fad'in Binty. "Lallai ni na ke fad'e ki na fad'e a cikin gidan ubana? Sai na koya miki hankali, sai na b'ata wannan banzan fuskan da ki ke tak'ama da shi ta yadda ba za ki k'ara burge wani d'a namiji a raguwarki ba. Ba ki isa ki kwace duk wani abu da ya ke mallaki na ba. Julaibib nawa ne ni d'aya, babu wata mace da ta isa in yi takara da ita, kin tafka babban kuskure a rayuwarki na son duk wani abunda ya ke mallakin Sabrin". Fad'in Sabrin ta na nuna Binty da yatsa. "Ke ba ki kai matsayin da zan yi takara da abu d'aya da ke ba, hasali ke ce ki ke bakin ciki kasancewar na fiki komai. Ba ri ki ji in fad'a miki wani abu, tun lokacin da ki ka bar *LEAD BRITISH*, na manta da wata yarinya mai suna Sabrin, ni ba kya rai na saboda ban d'auke ki komai ba, ke ce na tsayawa anan". Fad'in Binty ta re da nuna mak'ogoranta. "Waye ubanki? Kin san ko ni wacece kuwa?". Fad'in Sabrin a fusace. "Ke wacece ki ke tambayata? To saurara ki ji, ke ba komai ba ce face d'igon maniyi, wacce a hankali ki ka koma gudan jini ki ka ko ma tsoka akai ma ki halitta sannan aka busa ma ki rai, kuma a karshe za ki mutu a binne ki a k'asa a barki daga ke sai halinki, aikin da ki ka shuka a duniya walau na khairi ko akasin haka, shi za girbe". Hannu Sabrin ta d'aga za ta wanke fuskanta da mari, caraf Binty ta rik'e hannun. Sabrin ta yi- ta yi ta kwace amma ta kasa sai da Binty ita da kanta saki hannun da izza ta ra da fad'in, "Kada ki k'ara tunanin kwatanta haka, za ki yi nadama don na san ba ki manta had'uwan mu na farko ba a mall d'in babanki". "Za ki yi nadamar abunda ki ka aikata, sai kin duk'a bisa k'afafuna ki na nai man gafarata, ni kuma wallahi ba zan yafe miki ba, sai na koya miki hankali, banza wacce ba'asan asalinta ba". Fad'in Sabrin ta re da hayewa sama ta na huci. Zama Binty ta yi a kan kujera ta re da rik'e kanta ta na jin sam ba za ta iya zaman gidan ba.
Murd'a handle d'in k'ofar ta yi ta re da shiga ta yi banging k'ofar. Aunty Junaina da ke cire d'an kunne a gaban mirror ta yi saurin juyawa ta kalleta. "Kin saka na tura miki 10million a account d'in ba ta re da daddy ya sani ba, ki ka kuma k'ara buk'atar wa ni 5million na kuma d'aukar wayar daddy na miki transfer shi ma ba ta re da ya sani ba duk a dalilin alk'awarin da ki ka min na cewar za ki kawo min Binty har cikin gidan nan kuma sai ta duk'a min. Tabbas kin kawo ta ga ta can a k'asa, amma ba ta duk'a min ba sai maganganu da ta yi min masu zafi da k'ona zuciya, dama kin shirya hakane don zuciyata ta buga in mutu?". Fad'in Sabrin ta na nuna saitin zuciyarta. Kamo ta aunty Junaina ta yi ta re da zaunar da ita a bakin gado ka na ta ce, "Relax my daughter, tabbas yarinyar nan sai ta duk'a a gabanki, za ki juyata fiye da tunaninki. Sai dai ina so ki nutsu mu yi komai cikin natsuwa. Yau ta zo gidan nan, mun d'ana mata tarkon da dole ne ma ta duk'a miki, ke dai ba ni daga nan zuwa kwana uku". Fad'in aunty Junaina. Ajiyar zuciya Sabrin ta saki, ba ta re sa ta sake cewa komai ba ta d'auki wayarta da ke kan gadon ta fice daga d'akin. Ko da ta sauko k'asa, sai da ta watsawa Binty wani irin kallo wacce kan ta ke duk'e a k'asa ta ba sak'e-sak'e cikin zuciyarta. Kwata ta yi ta re da fita ta buga k'ofar wanda k'arar k'ofar ya firgita Binty da ta lula duniyar tunani.
Binty ta kusa awa biyu a zaune ka na Amrah da Hanan su ka shigo wanda dawowansu kenan daga gidan kakarsu da ke suleja. Kallonta su ka yi ka na su ka juya su ka kalli juna. Tab'e baki Hanan ta yi ta re da shigewa side d'in su. Ya yin da Amrah ta ke kallonta ta re da fad'awa kogin tunanin maganganun kawar mummyn na su da su ke tattaunawa. Ajiyar zuciya Amrah ta yi ta re da bin bayan Hanan zuwa d'aki ba ta re da sun ce mata k'ala ba ita ma kuma ba ta masu magana ba don a ganinta su ya ka ma ta su yi mata sallama tunda su su ka shigo su ka same ta.
............"Sister wai ki na ina ne?". Fad'in Fanan da ke ta faman kwalawa Binty kira ta re da duba lungu da sak'o na part d'in na su. K'ofar bayi ta nufa ta re da kwankwasawa, nan ma shuru. Tura bayin ta yi, nan ma ta ga wayam. Fita ta yi daga part d'in ta nufi garden, nan ma ta duba sak'o da lungu ba ta ganta ba. "To ina ta ke? Ba dai ta sake fita sun don had'uwa da mayaudarin nan ba mai k'arya da sunan wani?". Fad'in Fanan cikin zuciyarta. Komawa part d'in su ta yi da gudu ta haura sama ta re da d'auko wayarta ta re da kiran numbern Bintyn amma sai ta ji wayar na k'ara a d'akin. D'auko wayar ta yi da ke k'ark'ashin pilo gabanta na fad'uwa. Wani gudun ta kwasa ta re da yowa k'asa. Kicib'isa su ka yi da Barr Fu'ad hannun shi d'auke da kaya, sai ya Bibi hannun shi rik'e da hannun Anna da ta warke sumul ga kuma Daddy a bayansu ya na murmushi. "Annaaaaaah!". Fad'in Fanan ta re da nufarta da gudu ta rungumeta ta na hawayan murnar ganin Anna ta warke. "Kin ga Annar ki kamar mai cutar jinnu ko, gobe fa muke shirin fita k'asar, cikin hukuncin ubangiji sai ga Anna sumul k'afa sun sace har ta na takawa da kafarta ko ina, shi ne fa ta kafa k'ahon zuwa dole sai an dawo gida kuma na san saboda ku ne, ta yi kewarku". Fad'in Daddy. Rungumeta Fanan ta kuma yi ta re da fad'in, "Anna munyi kuka kamar idon mu zai fita". Anna da ke murmushi ta ce, "To gani nan ai, kuka ya k'are naji sauk'i. Ina autata?". Sai a lokacin gaban Fanan ya buga ta shiga zare idanuwa ta na kallonsu. "Ta na ina?". Fad'in Julaibib tashin hankali bayyane a fuskan shi. "Yaya Bibi wallahi ni ma ban sani ba, tun d'azu na ke ta nai man ta har garden ban ganta ba. Kuma na kira wayarta na ji ta na ringing a d'aki". Fad'in Fanan. Da gudu Julaibib ya nufi upstairs ta re da bubbud'e ko ina amma wayam. Anna kuwa ji ta yi cikinta ya wani irin murd'awa yayin da Barr Fu'ad ya nufi wajen gida domin dubo ta. Daddy kuwa hankalinshi bai wani tashi ba don a tunanin shi Binty ba za ta b'ace ba ta na gidan sai dai idan wani wajan ta shiga. Abu kamar wasa har dare ba Binty ba labarinta. Julaibib ya yi wajan su Oga Solomon ta re da tambayansu ko Binty ta fita, amma su ka shaida masa cewar ko wajan first gate Binty ba ta je ba balle ta fita. Tun alhaji Usman na d'aukar abun da sauk'i har shi ma hankalinsa ya ta shi don shi ma ya soma tunanin ko Binty ta bi saurayin da ya yi mata karya da sunan Yousouf d'an gidan abokinsa. Anna da Fanan kuwa kuka kawai su ke yi. Ranar dai gaba d'ayansu babu wanda ya yi bacci don wani irin bincike a ka shiga yi har d'akin Suhail in da aka ci karo da manya-manyan kwalaye guda arba'in na cocaine da kuma ticket na zuwa k'asar hongkong guda hamsin. Hatta d'akin Hajiya Mansura bai tsira ba wajan bincike, don Julaibib haukace masu ya yi kamar zaki.