Ba ni da gata - Chapter 35
Ba ni da gata Chapter 35: Ba ni da gata Chapter 35. ππ .............Kuka Binty ke yi sosai tsugune a gaban Junaina da Hajiya Zuwairah ta re da fad'in,β¦
2,169 words
ππ .............Kuka Binty ke yi sosai tsugune a gaban Junaina da Hajiya Zuwairah ta re da fad'in, "Mai yasa za ku yi min haka? Ban cutar da ku ba ka da ku cutar da ni ba, don kun ga *BA NI DA GATA* shiyasa Ku ke gwara rayuwata kamar kwallo? Duk abunda Ku ke buk'ata da in yi maku abu d'aya kawai zan iya yin sa shine rayuwa a matsayin baiwar Sabrin har k'arshan rayuwata in dai har Anna ba za ta cutu ba. Ka da ku cutar da bayin Allahn nan don soyayyar da Allah ke wa manzon my SAW. Na rok'e ku". Fad'in Binty ta na kuka sosai ta re da had'e hannayanta biyu. "Mu dai kin ji abunda mu ka ce miki don abunda Mansura ta yi kad'an ne a kan Wanda mu za mu yi mata. Mun ba ki nan da wata d'aya ki yi shawara". Fad'in Hajiya Zuwairah ta re da mik'ewa ta kalli aunty Junaina ta re da fad'in, "Na yi nan, sai kin ji daga gare ni". Ta na gama fad'in haka ta fice daga parlourn. Aunty Junaina kallon Binty da ke durk'ushe ta yi ta re da fad'in, "Ki zagaya ta baya, ta na can wajan garden ki je ki tab'a k'afafuwanta ki nai mi gafararta". Ita ma ta na gama fad'in haka ta haye sama. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!'. Fad'in Binty ta re da mik'ewa ta nufi waje. Amrah da ke mak'ale jikin labule ta na hawaye ta fito da sauri ta yi d'akinta.
"Besty ka ba ni shawara ya zan yi da wannan guy d'in dan Allah. Wallahi ina matuk'ar son shi sosai". Fad'in Sabrin da ke kallon Hamdan hannun shi rik'e da smoothie ya na sipping. "Hmm, ni dai idan da za ki ji shawarata, to ki fita harkan shi tun da ya nu na miki shi ba son ki ya ke ba". Fad'in Hamdan. "Ni ba zan iya rayuwa babu shi ba". Fad'in Sabrin ta re da marairaicewa. "Da ai da babu shi ki na rayuwan ki, saboda haka yanzu ma za ki iya rayuwar ki ko ba bu shi". Fad'in Hamdan. Sabrin ta bud'e baki za ta yi magana ta hangi Binty na zuwa. Wani murmushin jin dad'i ta yi saboda yanayin Bintyn ka d'ai ya isa ya fallasa abundan ta zo yi. Binty na k'arasowa wajan ta rik'e kafafun Sabrin ta na hawaye ta re da fad'in, "Ki min aikin gafara da yin sa'in sa da ke, kuskure ne da kuma sharrin shaid'an amma ko kusa ke ba tsara ta na ce. Kin min fintinkau a komai. Ke d'in cikakkiyar d'iya ce ni kuma ba komai ba ce face *MARA GATA* wacce ta ke ba ta da kowa sai bolan da ta ke rayuwa a kai. Ta yaya kamar ni zan had'a kai na da cikakkiyar d'iya kamar ki, don Allah ki wa Binty y'ar bola aikin gafara da yau za ta kasance a matsayin baiwarki har k'arshan rayuwarta". Wani irin mik'ewa Hamdan ya yi bakinsa na rawa ta re da fad'in, "Binty! Binty na. Bintyn Hamdan. Ki ce min ke ce dan Allah ba mafarki na ke ba Binty na k'arasowa wajan ta rik'e kafafun Sabrin ta na hawaye ta re da fad'in, "Ki min aikin gafara da yin sa'in sa da ke, kuskure ne da kuma sharrin shaid'an amma ko kusa ke ba tsara ta na ce. Kin min fintinkau a komai. Ke d'in cikakkiyar d'iya ce ni kuma ba komai ba ce face *MARA GATA* wacce ta ke ba ta da kowa sai bolan da ta ke rayuwa a kai. Ta yaya kamar ni zan had'a kai na da cikakkiyar d'iya kamar ki, don Allah ki wa Binty y'ar bola aikin gafara da yau za ta kasance a matsayin baiwarki har k'arshan rayuwarta". Wani irin mik'ewa Hamdan ya yi bakinsa na rawa ta re da fad'in, "Binty! Binty na. Bintyn Hamdan. Ki ce min ke ce dan Allah ba mafarki na ke ba, Beauty da ma zan k'ara ganinki?". Fad'in Hamdan ya na kallonta jikinsa na rawa hawaye na taruwa a idanuwansa. Sabrin kuwa ganin yadda Hamdan d'in ya wani rikice ya na kiran Binty haushi da takaici ya turnik'e. Juice d'in da ke cikin glass cup a gabanta ta d'auka ta re da watsawa Binty a fuska ka na ta saka k'afarta mai d'auke da dogon takalmi mai tsini ta tokareta a ciki sai da ta wuntsila. Binty saurin mik'ewa ta yi ta na kallon fuskan Hamdan hawaye na k'ara gudu a fuskanta ta na son kiran sunansa bakinta na rawa.
............Gidan Alhaji Usman kuwa, bincike ya yi bincike har Alhaji Usman da kan shi ya shiga d'akin sirrinsa shi da kuma Barr Fu'ad kasancewar Julaibib ya tafi wonderland don nai man Binty kasancewar Fanan ta fad'a masa a can su ke had'uwa da Yousouf idan ya kira ta. Alhaji Usman ne da kan shi ya kunna Computer kasancewar ya saka b'oyayyiyar cemara a ko wani sak'o na gidan shi don ganin hali da kuma abunda ma'aikata da kuma y'ay'an na sa ke yi a cikin gidan har da kuwa d'akunan matansa. Daga d'akin Barr Fu'ad ya soma bincikensa, bai ci karo da wani abu kaico ba, daga nan ya yi d'akin Julaibib, shi kuwa ba shi da aiki sai na kallon hoton Binty ya na wak'a sai kuma shan lemun tsami, daga nan ya yi d'akin Suhail, nan ne ya ci karo da abun assha wanda wasu daga ciki ya sani har kok'arin raping Binty da yi sai da su ka gani a nan ne kuma su ka gane daga d'akinsa ta fito ta na ihun k'onewar nan amma ba su ga wani alama da ke nu na ya na da hannu a b'acewar Binty ba. Daga nan part d'in y'an aikin aka shiga, nan aka yi katari da b'arayi irin su Fasila masu satar abinci. Wasila kuwa har muciya ta ke amfani da shi ta na yin masturbation cikin sauri alhaji Usman ya mayar sha-shin Huriya, ita kuma babu abunda ta ke yi sai kasuwanci da mugun sa aiki, don y'an aikinta ba su hutawa. Ko da ya koma shashin Hajiya Mansura, zuciyarsa ce ta kusa bugawa saboda ganin yadda ta ke lalata y'an aiki da mad'igo. Barr Fu'ad kuwa saurin rintse idanuwa ya yi. Forwarding alhaji Usman ya yi daidai wajan da hajiya Mansura ke threatening Binty akan ta amince da buk'atunta ko kuwa ta kashe su Anna da barrister. Zufa babu ta Inda baya tsattsafowa Alhaji Usman da Barrister Fu'ad. Cemaran waje ya kunna, a nan ne kuma ya ga lokacin hajiya Zuwairah ta ja Binty zuwa garden ta yi mata wad'annan maganganun da kuma lokacin da Binty ta shiga motar hajiya Zuwairah su ka fice daga gidan.
............Waige-waige kawai ya ke yi a cikin wonderland d'in nan ko Allah zai sa ya gan ta amma ko kyallinta bai ga ni ba. Dafe kan shi ya yi ya na jin wani tuk'uk'in bak'in ciki a ransa. Gitta shi ta re da tattaro gashin kanta ta na k'ok'arin nad'e shi ta kuma d'aure da ribom, saurin d'agowa ya yi ya ta re da kallon bayanta. Gaban shi ne ya buga da k'arfi ta re da waro idanuwa sakamakon tambarin d'awisun da ya gani a k'eyarta jiya. Kamar an kafashi a wajan haka ya tsaya ya na kallonta ta na yi wa wannan saurayin dai da ya na gan su rannar a nan wonderland d'in da kuma harabar asibiti. Ganin za su yi mass nisa ya yi saurin bin bayansu.
*GA SHI NAN NA CIKA MA KU ALK'AWARIN KU, MU HAD'E MONDAY πΉ *71-72*πΉ ..............Cikin rashin sa'a wannan karan ma sun b'acewa ganinsa. Hannunsa ya buga a jikin bango sai da hannu ya karce ta re da soma zuban jini saboda. Wayarshi da ke aljihu ne ta yi k'ara, ko damuwa da ya fiddo wayan cikin aljihunsa bai yi ba ya cigaba da zaga cikin park d'in ko Allah zai sa ya ganta. An kira wayar ya kusa sau goma ba ta re da ya fiddo wayar daga aljihu ya ga mai kiran ba. Sai da ya gaji da zagayan ka na ya nai mi wani waje ya zauna ta re da duk'ar da kan shi ya na kallon ciyawar da ke kwance a wajan idanunsa sun yi jazurr. Wayarce ta k'ara yin k'ara, wannan karan ya fiddo wayar daga aljihun. Kasancewar bak'uwar number ce, kamar ba zai d'aga ba, sai wata zuciyar ta ba shi shawarar da ya d'aga. D'agawa ya yi ta re da karawa a kunnansa ba ta re da ya ce komai ba. "Assalamu alaikum, dan Allah ina magana da doctorn da ke duba Sabrin ne, doctor Julaibib?". A dak'ile ya amsa ya bata amsa da, "Eh shine menene?". "Yarinyar da Ku ke nai ma ta na gidan mu, ina nufin Binty". Wani irin mik'ewa Julaibib ya yi ta re da fad'in, "Wacece ke? Ina ne gidan na Ku? A wani unguwa ki ke?". Duk ya koro mata tambayoyi. "Ni y'ar uwar Sabrin ce da ka ke dubawa a Canada. Wallahi Binty na gidan mu yanzu haka". "Alhamdulillah". Fad'in Julaibib ta re da yanke wayar daidai lokacin da kiran Barr Fu'ad ya shigo wayarsa. D'aga kiran ya yi bai jira Barr ya ce wani abu, shi ya riga shi magana, "Maza-maza ka fito ka same ni a wajan spicy d'in nan, na gano in da Binty ta ke". Julaibib na gama fad'in haka ya yanke wayar.
Barr Fu'ad kallon daddy da idanuwansa su ka kad'a saboda abubuwan da ya yi katari da su ya yi ta re da fad'in, "Yaya Bibi ya ce ya gano in da Binty ta ke ya ce in sa me shi a Spicy yanzu". "Je ka, ni kuma yanzu zan kira commissioner of police a turo min da mota uku na police". Fad'in Alhaji Usman. "Shikenan daddy, ba ri na yi maza na je mu had'u da ya Bibi". Fad'in Fu'ad. Gyad'a masa kai ya yi ta re da danna number commissioner a wayansa.
.............Sosai bakinta ke rawa ta re da fad'in, "Hadan, kai ne? Kai na ke gani yau da idanuwata?". Wani haske ta ga ni ya gilma ta idanunta. A ta ke ta ji ta dai na gani na wucin gadi saboda yadda zafin marin ya shigeta. Glass cup d'in da ta watsa mata juice a fuska ta dauka ta re da ratsa mata a goshi nan da nan kuwa jini ya b'alle. A gigice Hamdan ya yi kan ta ya na duba mata goshinta da ta saka hannu ta dafe ya na kuma zubda jini. Wani irin juyawa Hamdan d'in ya yi ta re da d'auke fuskan Sabrin da mari hagu da dama ka na ya yi ball da ita sai da ta wuntsila baya. Ba ta gama dawowa cikin hayyacinta ba ya kuma kai mata wani marin a tsakiyar fuskanta wanda sai da ta saki wani ihu ta re da rarrafe saboda gigicewa. Binty kuwa tuni ta manta da jinin da ke zuba a fuskanta ta shiga tsakiyan su da sauri ta re da duk'awa ta na fad'in, "Don rahamar ubangiji ka da ka k'ara kai hannu jikinta in dai don ni ka ke yi hakan. Yau ni na shiga uku ni Binty, daga wannan sai wancan. Yaushe zan samu salama da natsuwa ne ni kam? Ka san irin bala'in da za ka jawo min sanadiyar dukanta da ka yi? Ka san asarar da za ka jawo min kuwa? Idan wani abu ya samu Anna ba zan tab'a yafe maka ba wallahi". "Bintyyy!". Da wani irin sauri ta juya sakamakon muryan Fu'ad da ta ji ya daki dodon kunnanta. Wani irin zaro idanuwa ta yi gabanta na wani irin bugawa saboda arba da ta yi da Ya Bibi da Ya Fu'ad su na dumfaro so. "Me ki ke yi ana? Mai ya kawo ki gidan nan?". Fad'in Barr Fu'ad. Julaibib kuwa ya na zuwa hannunta ya fizgo ta re da wanke fuskanta da mari kasancewar a hanyar su ta zuba barrister ya shaida masa da komai da su ka ga ni a CCTV camera "Ki na hauka ne? Mai ya sa ba ki fad'amin ko Anna ko Fu'ad abunda ke faruwa ba? Da yanzu wani abu ya sa me ki fa ya ki ke so in yi? Kar ko da wasa ki sake gangancin maimaita wannan kuskuren Binty. Kuma wallahi Allah kenan, duk Wanda ke da hannu a cikin wannan abu ko waye shi ba zan bar shi ba. Ta ho mu wuce gida kuma ki sai kin fad'amin abunda ki ke zuwa yi ke da wannan d'an iskan yaron da na ke ganin ku da shi a wonderland da wasu wajajan". Fad'in Julaibib. Ka min Binty ta yi magana, wani guguwa mai bala'in k'arfi ya ta so ya lullub'e su har ba sa ina ganin na kusa da su. Guguwan nan ta kusa minti biyar ta na ta shi ka min daga bisani ta tsaya cak ta re da yin rimi a sama ka na ta b'ace b'at ta re da su gaba d'aya....