Ba ni da gata - Chapter 36
Ba ni da gata Chapter 36: Ba ni da gata Chapter 36. ............Cikin abunda bai fi awa guda ba motocin police guda uku su ka iso gidan Alhaji Usman. Kai…
3,454 words
............Cikin abunda bai fi awa guda ba motocin police guda uku su ka iso gidan Alhaji Usman. Kai tsaye d'akin Suhail ya fara yi da su ta re da nu na masu cocaine da wiwin da Suhail d'in ya aje a d'akinsa da kuma wad'annan tickets d'in na k'asar Hongkong. Kasancewar Suhail na d'akin mahaifiyarsa bai san wainar da ake toyawa ba shi da mahaifiyar ta sa. Police d'in tsayawa su ka yi a waje su na jiran umarni daga alhaji Usman. Sama alhaji Usman ya nufa ta re da tura d'akin Hajiya Mansura. Zaune ta ke a bakin gado, ya yin da Suhail ke zaune a kan stool ya na cin Apple. "Ku fito ku duka Ku na da bak'i a waje" Fad'in Alhaji Usman. "Bak'i kuma? To suwaye?". Fad'in hajiya Mansura. "Idan kun fito kwa gan su". Alhaji Usman ya fad'a ta re ficewa ya sauko k'asa. Hajiya Mansura kallon Suhail ta yi wanda shi ma itan ya ke kallo ta re da fad'in, "Ta shi muje mu ga kk su waye ne". A tare su ka fito ita da Suhail d'in. Turus su ka tsaya su na kallon polisawan da ke bakin kofar na ta. "Alhaji wad'annan fa? Mai su ka zo yi ne haka har nan wajan?". Fad'in Hajiya Mansura. "Ku tafi da su" Fad'in Alhaji Usman. Gaba d'aya kallonsa su ka yi a razane don Suhail har ya na tumbling ta re da fad'in, "Dad...." "Ka nai mi wani uban daga yau don ni na yafe ka daga cikin y'ay'ana, ai ba kai kad'ai gare ni ba, kuma wannna ta yi ma ku jagora har gidan k'awarta Zuwairah, ita ma Ku had'a da ita". Fad'in Alhaji Usman. "An gama yallab'ai". Fad'in wani police ta re da sakawa Hajiya Mansura ankwa a hannunta ita da Suhail su ka ta sa k'eyarsu. Sai da su ka bi ya su ka d'auko hajiya Mansura wacce su yi da ga da ita ka min ta bi su ka na su ka wuce police station. Gaba d'ayansu bayan kanta aka watsa su ba ko d'an kunne a kunnan su. Don shi Suhail ma daga shi sai gajeran wando duk case d'in sa ya fi na kowa a cikinsu. Kasancewar sun san Hajiya Mansura matar Alhaji Usman ce, dalilinsa shiyasa ba su san tozartata, don sun yi sun yi ta magantu, amma fad'i ta ke ita ba ta san komai ba, ganin haka ita Zuwairah ta ce ba ta sa ni ba, shi ma Suhail ya ce bai san daga in da Cocaine d'in nan da tickets d'in nan su ka fito ba har da wani ciccijewa. Mai da su bayan kanta ya sa aka yi ka na ya kira Alhaji Usman ya masa bayani ta re da ce masa kunyansa fa su ke ji shiyasa ba su d'auki tsattsauran mataki ba. Magana Alhaji Usman ya yi da shi mai tsawo shi kuwa sai cewa ya ke ''OK sir''. A ranar aka d'ebe su sai state CID. Tun shigar su wajan Suhail ya soma sakin zawo ganin irin nau'ikan azabar da akewa mutane a wajan. Hajiya Mansura kuwa zufa har ta d'uwawunta, ya yin da Zuwairah tai ta sakin tusoshin tsoro ta re da son zagayawa zuwa ban d'aki. Da ma tuni an yi was babban su bayanin komai kamin a tura su zuwa can. Shiyasa a na zuwa da su ya ce a sa su a dak'in duhu na awa awa d'aya. D'akin duhun nan ko tafin hannunsa mutum bai iya gani ga shi window Ku ma idan za ka shekara ka na ihu ba mai jin ka. Wasu ma idan an saka su a wajan aka fito da su sanadiyar makancewar su kenan. Ko na minti ko aka tura mutum d'akin duhu sai ya gwammaci mutuwa ba re har na awa d'aya. Bayan awa d'aya ya cika, DSP ya sa aka ciro su idawuwansu a rufe sun bala'in jigata. Gaba d'ayansu zarni su ke yi ta re da warin kashi saboda zawowi da su ka dunga saki. Suhail kuwa sai cewa ya ke yi, "Wallahi zan fad'i komai, zan fad'i gaskiya". Wa ni d'akin aka kai su, ta kan Suhail d'in aka soma tuhuma, "Ka shirya bayani ko a sai an sa ke mai da ka d'akin duhu?". Idanuwansa a kulle har da d'aga hannu sama ta re da fad'in, "Wallahi na shirya, zan fad'i komai yasin". "Muna jin ka". Oga ya sa ke fad'a. "Ni na ke sa abokai na da ke Mexico su na shigo min da Cocaine ina sayarwa a nan k'asar. Da a can mu ke sana'ar mu. To mahaifina da ya kai min ziyara ya ga irin shiriritar da na ke yi shi ne ya mai do ni k'asata. Ni kuma ba zan ita dai na wa ba sai mu ka yi shawara da friends d'i na na can shi ne su ke turo min ta nan, sannan kuma wannan tickets d'in na wasu y'an matane da wata hajiya ta ke kawo min daga k'auye ina turasu karuwanci k'asashe daban-daban ita kuma a duk yarinya d'aya ina ba ta dubu d'ari da hamsin. Hatta y'an aikin gidan mahaifina akwai wad'anda na tura, sannan ba zan iya k'irga y'an aikin gidan mu da na yi wa fyad'e ba, wasu ma har ta duburansu na ke amfani da su ta re da yi ma su barazana da bindiga idan su ka k'i amincewa". Hajiya Mansura jin bayanin da d'anta ya ke yi ba ta san ta na sakin zawo a in da ta ke ba saboda tsananin firgita. "Ke nan har da safarar makamai ka ke yi?". Oga ya sa ke tambayansa. "Eh shi ma na kan d'an tab'a". Fad'in Suhail. "Wa Ku ke sayarwa wa?". Ya sa ke tambayarsa. "Ni dai wani mutum na ke kai wa, shike sayewa duka ban san mai ya ke yi da su ba". Jinjiga kai Police d'in nan ya yi ta re da fad'in, "Cigaba ina jin ka". "Wallahi yallab'ai shikenan, na gama fad'in komai". Suhail ya fad'a. "Ke nan ba ka da hannu a b'acewar yarinyar gidan ke nan?". Fad'in Police d'in. "Wallahi ban san ko mai a kan haka ba, ni dai na san ina ta d'ana mata tarko don yi mata mummunar fyad'e, amma ta na tsallakewa". Fad'in Suhail. Mai da kallonsa ya yi izuwa ga Hajiya Mansura da ta yi wik'i-wik'i idanuwanta sun yi jazur sun k'ank'ance saboda shigarsu d'akin duhunnan. Tun ka min ya yi magana ta soma bayani, "Tun ina budurwa na ke harkan mad'igo (lesbian) kasancewar makaranta kwana na yi, a can na ko yi wannan d'abi'ar da babu wanda ya san ina aikatawa a zuri'a ta, don ni d'iyar malamai ne, idan ka na jin malam Hafizu Nazifi mai almajirai, shi ne mahaifina, tun muna yi yamu-yamu k'awaye har abun ya bunk'asa mu ka kafa k'ungiyar mu wanda ni ce shugabarsu. Na yi aure ne ba dan komai ba sai don gudun zargin zama'a amma ni sam namiji bai gabana. Mu na amfani da asiri ta yadda duk yarinyar da muka gani ko d'iyar uban wacece ita da kan ta za ta nai me mu don yin mad'igo da ita don saka mata sha'awarmu da k'aunar mu muke a zukatun duk wacce mu ke so. Yanzu haka ni mata na sha takwas wanda na aure su, bayan ni ba bu wacce ta isa ta yi mad'igo da su. Binty kuma tun ranar da na fara ganinta na ji k'aunarta da sha'awarta ya darsu cikin rai na. Sai dai abun mamaki, na yi asiri a kan ta amma bai kamata ba, hakan ya sa na kafa tarko da Hajiya Na'ima da kuma y'ay'anta akan idan ba ta amince da ni ba zan kashe su. Kuma duk mun had'a hakane da wacce ta yi sanadiyar zuwanta gidan wato Kandala wacce babu abunda su ka had'a da ita, ita ma tsintarta ta yi ta kawo gidan matsayin y'ar aiki su kuma su ka rik'e ta tamkar y'ar su. Na yi amfani da Anna don in sa mu Binty, ni na yi wa Anna asiri ta re da taimakon y'ar aikinta Fasila mu ka zuba mata magani ta ta ka shi ne k'afafuwanta su ka kumbuta har aka kai ta asibiti. Ni kuma na kira Binty na ce ko ta amince ko kuma Anna ta mutu yay'anta su biyo bayanta. Bayan na kashe wayar na kwanta cike da farin ciki da kuma tabbacin Binty za ta zo har in da na ke in yi mad'igo da ita kuma in aure ta. Amma wallahi wallahi ban san in da ta ke ba a yanzu haka, ba ni na b'oye ta ba". Ta k'arisa maganar ta na kuka. K'ura mata idanuwa police d'in nan ya yi ka na ya mai da kallonsa izuwa wajan Zuwairah da ta yi saurin sunkuyar da kai k'asa. "Ba na buk'atar ba ki umarnin yin magana" Fad'in officern nan. Hajiya Zuwairah ta fara magana cikin kuka kamar haka, "Duk abubuwan da Mansura ta lissafo ta re mu ke yin sa, ita ce shugaba ni kuma mataimakiyar ta, kamar yarda ta ka mu da K'aunar Binty, ni ma haka na ka mu da k'aunarta. Sai dai ta ja min dogon layi akan fita daga harkarta idan kuma ba haka ba za ta b'atar da ni. Na nu na mata na bar maganar Binty, amma cikin zuciyata ban bari ba, lokacin da ta buk'aci Kandala da ta d'auko Binty ta re da yi wa uwargidan ta k'aryan cewa za ta kai ta wajan danginta sai ita kuma ta kai Binty wajanta a wani gida daban ta re da tsoratar da ita akan idan ba ta yarda da buk'atarta ba to za ta ka she Hajiya Na'ima da iyalanta. Kandala ta amince da buk'atun Mansura sakamakon naira million biyu da ta ba ta. Ni kuma na k'arawa Kandala million uku a kan ta ba ni Binty ni na san yanda zan b'ullowa al'amarin, to bisa tsauyayi sai y'ar wajan Hajiya Na'ima ta bi su wanda hakan ne ya lalata mana shiri. Kuma ni na san shirin Mansura kasancewar komai ta re mu ke yi. To bayan sun dawo daga can Saminaka ne Mansura ta yi wa uwargidanta asiri a har ta shiga wannan hali na ciwon k'afa wanda ta dasa tarko da shi, ni kuma a ranar na zo gidan na yi wa Binty k'aryan zan taimake ta ta kuma fad'a tarkona na kai ta gidan d'aya daga cikin members d'in mu wanda ita ma ta na da na ta k'udurin a kan mu, yanzu haka ta na can gidan". A matukar firgice da kuma tsananin Hajiya Mansura ta ke kallon Zuwairah ta re da fad'in, "Zuwairah ni ki ka ciwa amana? Lallai za ki san kin ci amanata". Tsawa police d'in nan ya daka ma su ta re da fad'in duk sai kun gwammaci mutuwa da aikata wad'annan abubuwan da Ku ka yi. Ya kalli Zuwairah ta re da fad'in, "Za ki ba mu address d'in ita wannan matar domin mu kwamusota ita ma". Ya mai da du ban sa ga hajiya Mansura ta re da fad'in, "Duk sauran members d'in ku su ma sai kun fiddo da su ta re da y'ar iskan Kandalan nan. Shegu y'an iska ma su b'ata tarbiyyan y'ay'an jama'a". "Kai kuma, na ka case d'in babba ne, sunan ka CC condemn. Duk wad'annan abokan na ka sai ka fito da su ta re da wannan d'an iskan da ka ke kai wa makamai ya siya. D'an iska ubanka na k'ok'ari da kai ba ka rasa komai ba amma ka na naiman zubar masa da mutunci kai da shaid'aniyar uwarka, ka mai da su d'akin hayaki su d'an d'umamu na iya lokacin da Alhaji Usman zai d'auka ka min ya k'araso state CIDn nan. Yanzu zan kira shi"...
*YA KA MA TA KU HAUKATA NI DA RUWAN COMMENTS SABODA GARAB'ASAR SATI DA LAHADIN NAN DA NA BAKU. KAMAR YANDA NA FARANTA MA KU, NI MA KU FARANTA MIN* 😌😌🤓 🌹 *73-74*🌹 .............Fita ya yi ta re da dannawa Alhaji Usman kira ya yin da ya ke nufar office d'insa. Bugu biyu Alhaji Usman ya d'aga ta re da sallam kasancewar da ma su na da contact d'in ju na. Amsa sallamar Officern ya yi ta re da fad'in, "Yallab'ai sun yi confessing, yanzu kai muke jira sannan akwai wasu mutanan da su ka ambata wanda na ke so a taho min da su nan, sannan kai ma ina son ka ji duk abunda su ka fad'a da kunnanka don komai mu nan sai mun yi recording". "Haka na ke so ai, bari na kira y'ay'ana my taho ta re yanzu". Fad'in Alhaji Usman ta re da katse wayar. Bayan ya katse wayar ya shiga lalubar numbern Julaibib sai dai abun mamaki ya kira ya fi sau shurin masak'i amsa d'aya ake ba shi *THE NUMBER YOU'RE TRYING TO CALL IS NOT REACHABLE AT THIS MOMENT, PLEASE TRY AGAIN LATER*. Duk a tunaninsa sharrin network ne, mai da ak'alar kiran ya yi zuwa ga Barrister Fu'ad, sai dai shi ma hakan ta kasance. D'an tsuka ya ja ta re da yi wa drivern sa magana zai fita. Nan da nan driver ya fito da mota, sannan ya yi umarni da sauran su dakata da mota d'aya kawai zai fita. Sai da ya fara zuwa part d'in Anna su ka fito ta re kasancewar da ita ya ke so su je saboda ayi komai a gabanta tun da su Julaibib d'in bai samu numbers d'in su ta shiga ba. Mintuna arba'in ya kawo su State CID kasancewar bai k'aunar gudu a mota a hankali ya ake tafiya da shi. Cikin mutunci da karramawa aka yi Office d'in Officern da case d'in ke hannunsa da su. Anna kuwa duk a rud'e da tashin hankali ta ke, burinta kawai ta ga Binty hankalinta ya kwanta. Ko zama ba su yi ba officer ya yi d'akin bincike da su ta re da kunna wani computer videon su Hajiya Na'ima ya bayyana. Anna kuka shab'e-shab'e da idanuwanta ganin halin da aka bai nai mi jefa Binty da kuma sacrificing d'in da ta yi a kanta. Sannan ta sha mamaki da kuma tsoron jin abunda Mansura da Zuwairah su ke aikatawa. Babu abunda ya fi bata mamaki kamar zanzan da Mansura ta yi na cewar Binty ba ta had'a komai da Kandala ba da kuma b'arnar da Suhail d'in ya yi ta aikatawa a cikin gidan. Sosai Anna ta yi da na sanin hana Fu'ad d'aukar matakin da ya so yi tun farko. Wani police ne ya shigo ta re sa sarawa wannan Officern ka na ya ce, "Sir ga sunan zo da su duka, su na d'akin tuhuma". "OK to ga ni nan zuwa". Fad'in Officer ta re da kashe computer ka na ya ce wa Alhaji Usman su ta so su je. Anna k'afafuwanta har wani sanyi su ka mata saboda abubuwan tashin hankalin da ta ji. Can d'akin su ka shiga, Kandala kuwa ta yi fitsari sau babu adadi, suma kuwa ta yi sau bakwai a na farfad'o da ita da ruwan k'ank'ara. Junaina kuwa sai gwalalo idanuwa ta ke yi kamar an tsare kwarto a d'aki. Shi kuwa tirk'ek'en Alhajin nan ko a jikinsa don wannan ba shi ne karon farkon kama shi ba manya k'asar su na sawa ana sako sa. "Are you ready to confess?". Fad'in Officern nan ya na kallonsu d'aya bayan d'aya kasancewar su ma sun shiga d'akin duhu don sun riga Alhaji Usman k'arasowa. Kuma ta re aka fito da su har da su Mansura wanda gaba d'aya sun canza kamanni saboda d'akin hayakin da aka kai su. Akwai wani makeken glass da ke tsakaninsu don da mic su ke magana da ke kai masu maganar can b'angaransu haka suma. Ta kan Kandala aka fara tuhuma. Aikuwa kamar kanya haka ta shiga zuba, "Yallab'ai ayi min afuwa wallahi sharrin shaid'an, tabbas babu abunda na had'a da Binty, asalima ni a hanya na cintse ta ta na kuka a kai ta wajan wani da ta kira sunan sa da ba zan iya tunawa ba, wallahi har ga Allah ban so cutar da ita ba, musamman yadda ta san cewar ban had'a komai da ita ba, amma ba ta fad'i gaskiyar haka wajan uwar rik'onta ba, haka duk wata na ke karb'an dubu d'ari da kayan abinci ina sayarwa ta re baiwa aminiyata Datu ta na juya min y'an currency. Kwatsam sai ita wannan hajiya Mansura ta kawo min wani ba tu ta re da tayin naira million biyu, jin kud'i masu yawa haka sai na amince da buk'atar na auran Binty ta mai da ta y'ar mad'igo, to a gaban ita wannan hajiya Zuwairah mu ka yi komai, shi ne ita kuma ta k'ara min million uku a kan ita ma za ta rik'a mad'igo da ita Binty amma in yi shiru da ba ki na ka da ita Hajiya Mansura ta san da zan can. Wallahi na san na yi kuskure kuma na zalinci hajiya Na'ima mutuniyar kirki wacce duk na ziyarceta sai ta ba ni kud'i da kayan abinci masu uban yawa kuma a had'ani da driver don kai ni gida". Kandala ta k'arisa maganar ta na kuka har da majina don ta ci azaba a d'akin duhun nan. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un". Shi ne abunda Anna ta ke ta maimaitawa a fili. Kan Junaina aka koma wacce ke ta wik'i-wik'i da idanuwa. "Wallahi tallahi ni ba amshi Binty don yin mad'igo da ita ba, kuma ba saboda haka na sa aka kawo Binty gida na ba, ni saboda d'iyar mijina na sa aka kawo ta. Mijina ya kasance azzalumi mara adalci a kan y'ay'ansa. Banbanci sosai y'ay'ana su ke gani aka y'ar uwargina. Sabrin ta kasance mai son kan ta tun ta na k'arama ta re da son ta burge mutum, sai dai ta na da lalurar ciwon zuciya wacce aka haifata da ita kuma hakan ne ya sakawa mahaifinta tsananin k'aunarta fiye da duka y'ay'ansa. Haka na min ciwo a zuciyata sosai saboda yanda y'ay'a na kullum ke kukan yadda mahaifinsu ke nuna bambanci a kan su. Haka ya sa na je wajan boka ya ba ni maganin da idan na sakawa Sabrin jijji da kan ta da kuma san rai ta re da son ta fi kowa a duniya zai nin Ku sau dubu a kan yadda ta ke. Tabbas sabrin na da duka halayan nan da na lissafo sai dai a kashi d'arin yadda ta ke a yanzu, ni na k'ara mata kashi casa'in saboda nasan dole-dole sai ta gamu da wad'and'a su ka fita wanda idan haka ta kasance saboda tsabar kishin da na saka mata zai iya sanadin bugawar zuciyarta ta mutu kowa ya huta. Na yi hakane saboda na fi son ta mutu ta hanyar buguwar zuciyata ta yadda mahaifinta shi ma zuciyarsa ta bugu mu tattare dukiyarsa ni da y'ay'a na mu yi gaba. Tabbas ina cikin k'ungiyar mad'igo, amma ni ba buri na ba ne in yi mad'igo da Binty don ni a cikin k'ungiyar ma ni k'aramar member ce kuma na shiga ne saboda k'ungiyar akwai har kan samun kud'i saboda sun had'a da tsafi don duk lokacin da aka kawo budurwar da ba ta tab'a sanin d'a namiji ba ta yi joining kud'i su ke samu wanda ak'alla zai kai billion bakwai duk sacrifice d'aya". Ta fad'i haka ta na mai fashewa da kuka. Anna saboda firgici har fitsari sai da ya cika mata mararta. Alhajin nan da aka so kan shi sai wani ciccijewa ya ke yi ya k'i ya yi magana. "Ku kai shi d'akin lantarki, bai horu ba". Fad'in Officer. "Alhaji ku ko ma gida, duk yan da ake ciki zan kira ka, sai dai fa akwai matsala, ba'a San in da y'ay'anka su ke ba, mai gadi kuma ya tabbatar mana da sun shiga amma ba su fito ba, kuma mun ga motocinsa, sai dai akwai wani abun tashin hankali da mu ka ga ni a gidan, domin sawun dawakai mu ka gani wanda ba zai k'irgu ba ta re da wani rami mai zurfin gaske, kum...........". Bai k'arasa ba Anna ta fashe da kuka mai sauti ta re da fad'in "Wallahi duk in da y'ay'ana su ke sai an fito min da su ba zan yarda ba". "Hajiya ki kwantar da hankalin ki, duk in da y'ay'an ki su ke za su bayyana da izinin lillahi". Fad'in Officer ci ke da lallami. Alhaji Usman ne ya kamata su ka fita ya na lallashinta har wajan mota ya sata ciki. Sun kai kusan 15minutes su na tattaunawa da officer ka na ya shiga mota driver ya ja wanda a hanya sai aikin lallashi ya ke saboda yadda Anna duk ta bi ta d'aga hankalinta.